Halysaah Page 212 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 212…Washegari da rana Ajay na zaune gaban mota ya jünginar da kansa jikin kujeran motar idonsa a lumshe, Jay ya fito daga cikin gida da akwati a hannunsa, ya karasa har parking space din ya bude booth din motar ya ajiye box din a ciki sannan ya zaga ya bude front seat ya shiga ya zauna ya ciro wayarsa yana tura ma Hadiyah text, Ajay ya juya ya kallesa, after some seconds a hankali yace “Why not talk to her Jay, kasan fa tana jin maganar ka, but naga kamar you are even happy about her staying back home since you are not saying anything about it” Jay yayi dariyar da bai yi niyya ba yace “Ban gane i am happy ba, kai me ya hana ka yi mata maganar sai ni, beside tunda ta ce gida take son zaunawa let her stay for a while a gidan mana, a sanda baka nan i can count how many times ta yarda taje gidansu a shekaru biyun nan, kuma ko ta je bata wuce kwana biyu zuwa uku zata dawo gidan Sarki, wani lokacin ma yan gidan nasu basu sani ba take kamo hanyar Bauchi, so since she wants to stay back home now let her….” Ajay bai ce masa komai ba ya tada motar don har Jay din ma mugun haushi yake basa da yaga he is in support of his wife staying back home, Mai gadi ya bude gate din gidan ya figi motar ya fita daga compound, Jay yace”A’a bawan Allah jira, in driving din da zaka yi kenan ka tsaya in koma driver seat in tuka mu cikin aminci, Kar kaje ka kashe wa matana ni, don ka zama gauro yanxu shi ne zaka huce haushi a kan steering, na tun jiya da suka maida Khaleesat gida da rana basu sake komawa ba sai yanxu da za su je gidan, Hajja da su Mami duk sai da suka je har gidan suka gaisa da Umma daga nan kuma suka juya zuwa Bauchi gaba dayan su, Hadiyah ce kawai ta zauna gidansu Khaleesat har ta kwana, yanxu ma saboda ita Jay zai je gidan don zai dauketa za su tafi Bauchi, Sai da suka yi nisa Ajay ya ajiye haushin Jay da yake ji a gefe, kamar wanda aka tilasta yace “To kai me ma zaka je Bauchi kayi? Ko kana da wani hidden agenda ne a can?” Jay ya gyara zama yace “Eh ina da hidden agenda da matata” Ajay ya wani kallesa yace”Dalla Malam ka bari next week” Jay yace “In ci gaba da zama a Kano kai da matar ka kuyi ta shiga hakkin aurena ko? To i am missing my wife, gwara in dauketa mu bar maku garin nan, mu ma mu samu enough privacy Takaici yasa Ajay yaki tankasa, after almost 5 mins Ajay yace “To yanxu for the second time dai sai mutanen can sun kara yi min kallon makaryaci kenan? There is no way we can communicate with them su san uzurin mu na rashin komawa” Jay yace “Wasu mutane? Ko iyayen Hamisu take ko wa?” Ajay ya wani kallesa, dariya Jay yayi yace “Take a chill pill Ajay, nasan definitely idan na koma Bauchi sai Mai martaba yayi maganarsu tunda ka ga ko sanda mu ke Amurka ma yayi magana twice or so, mu fa bamu san butulci ba, tunda har nasan garin mutanen nan magana ta kare kuma ai, nasan Sarki zai iya cewa mu je mu dauko su cause it’s hard yaje garin gaskiya, su din ma ba tilasta su za ayi sai an taho da su Emiratenbasu amince da biyo mu ba, Sarki zai iya ba abinda yake yaje Benue, su ma su taho Benue din daga kauyen nasu su hadu da Mai martaba, ko kuma Mai martaba yayi communicating da Sarkin garin ta yanda za su amince da zuwa Bauchi, kai kuma babu ruwan ka a issue din nan kuma, just leave everything in my hand, tunda har ka koma garin ka nuna appreciation din ka to ka gama part din ka, the rest part which is kyautata ma bayin Allahn nan is for the Emirate not you, kai kuma kayi concentrating a rayuwar auren ka, kasan wacece matar ka, ita ma tasan wanene kai, sannan kuyi rainon cikin ku don baza ka bar ta da rainon ciki ita kadai ba tunda ba ita tayi ma kanta ba, lastly duk wani abu da zaka gani fa ya zama dole ka shanye don masu ciki wasun su sun yi hannun riga da son zaman lafiya, and I sense Halysaah is of that Category” Shi dai Ajay bai ce komai ba amma duk yana sauraron abinda Jay ke cewa, har suka isa kofar gidansu Khaleesat babu wanda ya sake cewa komai a motar, Jay ya bude motar ya sauką yace “Zaka shigo duba matar taka ko kuma in ce mata kace kana gaisheta kawai?” Kallonsa kawai Ajay yake, Jay yayi dariya ya juya ya nufi cikin gidan, Nenne ce zaune parlorn da Khaleesat sai Hadiyah da Noor, sannan Abdul da ko minti biyar bai yi da shigowa gidan ba, Jay ya shigo parlon da sallama, Khaleesat dake zaune kan Carpet tana cin wainar flour da Hadiyah tayi mata ta kallesa ta ci gaba da cin abincin ta, da fara’a Nenne ke yi ma Jay sannu da zuwa, ya karasa ciki ya fara gaisawa da Abdul sannan ya zauna ya gaida Nenne yana dan murmushi, ta amsa tace “Ya gajiyar ku ta shekaranjiya da jiya? Haka muka kwana cikincimarasu kirki ga rashin kamun kai da sanindan Adam, ai ranan mun yi kwanan bakin cikı Jay Nenne tace “Ga ta nan jiki yayi kyau, tace bata jin komai yanxu, abinci kawai take narka tun safe” Jay ya daga kai ya amsa gaisuwar da Noor tayi masa, Hadiyah dai kallonsa kawai take don sosai tayi missing dinsa a few days din nan, shi ma ya dan kalleta, Khaleesat ta daga kai ta kallesa tace “Ina yini Ya Jawwad” Yace “Lafiya lau Halysaah, ya jikin?” Tace “Na ji sauki” Jay ya kalli Abdul yace “Ashe kana unguwan Barrister” Abdul yayi murmushi yace”Not long ago na shigo unguwan, zan yi dropping Haiydar a airport ne” Jay yace “Tafiya zai yi ne….” Nenne tayi karaf tace “Eh wallahi tafiya zai yi Jawwal, Allah sarki Haiydar za mu sha kewa, ko bayan duniya na aiki yaron nan babu kiwa zai je ya dawo, daxun nan ma ya fita daga Parlon nan shi ma duk bai son rabuwa da mu, zai koma Ingila kasan a can yake aiki, hutu ya zo, to shi ne Allah ya hadasa da Awdul, ai ko dai tasu ta zo daya, yanda baya son hayaniya yana nan shiru shiru ga kirki shi ma Awdul haka yake, ba sa wa ba hanawa, magana ma in bai saba da kai ba bazai yi ba in dai Awdul ne, yaron kirki da shi” Dai dai nan Ajay ya shigo parlon da sallama, sai da Khaleesat taji wainar flour din ya fita kanta jin sallamarsa, ta tura plate din daga gabanta ta kauda kai, tun da Ajay ya kalli Abdul sau daya ya dauke idonsa, ya karasa cikin parlon ya zauna kusa da Jay sannan ya gaida Nenne, Nenne ta amsa da fara’a tace “Ashe tare ku ke da Jawwal din na zata shi kadai ne, sannun ku da zuwa, dama na ajiye maku dambun nama da aka yi min jiya, bari in dauko maku” Tana kai wa nan ta mike da sauri zfidakinta, Ajay dai bai ce komai ba, banda gansa bakin kofar da juyawa zai yi kawai bazaishigo parlon ba, tun daga bakin kofar parlon yaji wani abu ya tsaya masa cak a kirji, wani karamin veil Khaleesat ta daura a iya kanta, duk wuyanta da saman shoulder dinta a bude yake, mayafin ko gama rufe dogon gashinta dake ta kyalli bai yi ba gaba daya, gashi in dai ka kalleta sai ka kara kallonta saboda irin hasken jikinta me daukar hankali, ita kuma Hadiyah da tasan ciwon kanta ga shi ta rufe jikinta baka hango wuyanta balle shoulders dinta, da ace Jay ne kawai a parlon babu abinda zai ji a ransa, but seeing Abdul sitted in the parlor ji yayi kamar an soka masa mashi a kirji, yayi kamar bai ji gaisuwan da Abdul yayi masa ba ya fara danna wayarsa ya maida duk attention dinsa a kan wayar, Hadiyah ma ta gaishesa taji bai amsa ba, haka ma Noor, Abdul ya mike yana kallon Jay yace “Zan shiga gidan su Haiydar, naga he is wasting time bai fito ba har yanxu” Jay yace “To jira Kaka ta fito sai mu fita gaba daya mana, mu ma airport za mu tafi yanxu, we are leaving for Bauchi” Abdul yace “Alright to” Daga haka ya koma ya zauna, Mikewa Noor tayi ta tafi ta dauko ma su Jay ruwa da drink ta dawo parlon ta ajiye, Khaleesat na kallonta tace “Ina fruit din da Ya Abdul ya kawo min?” Ajay ya daga kai ya kalli Khaleesat, Noor tace “Na kai kitchen Aunty” Khaleesat tace “Debar min wanda zan sha ki wanke ki kawo min yanxu” Ajay dai kallonta kawai yake babu ko kiftawa, ko sanin yana yi Khaleesat bata yi ba tunda ba kallon inda yake tayi ba, Noor ta nufi kitchen, ba a dau lokaci ba sai gata ta dawo da Apple biyu da Grapes sai strawberry,ta wankesu tas, ta karaso ta ajiye ma Khaleesat fruits din, Ajay sai kallon fruits din kawai yake, Khaleesat ta dau strawberry daya ta sha taji da zaki, ta kalli Abdul tace “Ya Abdul duk sanda zaka zo irin wannan Strawberry din nake son ka dinga siyo min pls” Shi dai Abdul dan murmushi kawai yayi bai ce komai ba yana danna wayarsa, Jay dai kallon ikon Allah kawai yake, don ba karamin dariya Khaleesat ta basa ba, Jay ya dan kalli Ajay da gaba daya yanayinsa ya gama canzawa a parlon, Khaleesat ta mike ta dau bowl din fruits din tana kallon Jay tace “Ya Jawwad zan je daki, na gaji” Jay yana murmushi yace “To je ki huta” Juyawa tayi ta bar parton tayi tafiyarta dakin Nenne, Hadiyah dai ta bi ta da ido don babu irin maganar da bata yi mata ba tun daga jiya har zuwa yau ashe duk bata dau ko daya ba, Khaleesat na shiga daki taga Nenne ta dibar ma Jay da Ajay isassun dambun nama, sai kuma ta juya tana kallon Khaleesat tace “Ni dai gaskiya bazan ba Awdul ba, dambuna ba na sadaka bane wallahi, ta yaya ma zaka ba mutumin da baka yarda da shi ba abun hannun ka, har yau a tsorace nake da mutumin nan, haka kawai bazan kwashi dambun nama in ba tubabben dan daba ba” Khaleesat dake ta kallon Nenne ta juya ta dauko nata dambun da Nenne ta bata daxu, ta dungurar kusa da wanda Nenne ta debar ma su Jay tace “Sai ki basa nawa, baki yarda da shi ba amma kike zama kiyi hira me tsayi da shi” Nenne tace “A’a to meye kuma hira wanda iyakarsa fatar baki, a nan inda aka yi hiran fa nake zubarwa in tashi, zaman duniyar nan fa duu siyasa ce tunda kin ce a basa naki kason ai sai a basa sha min kai, dadin abun dai baza ki zo ki ce in bakiwani ba….” Ko tankata Khaleesat bata yi ba ta tafi ta zauna tana shan fruits dinta. Khaleesat sai da taji babu dadi sanda Hadiyah zasu tafi da Jay, tana kwance dakin Nenne bayan tafiyarsu, Nenne ta shigo dakin tana kallonta tace “Ke ya naga kamar sanda kika je yi ma facalarki rakiya mijin ki ya maki magana kin yi banza da shi, ko ba dake yake bane lokacin?” Khaleesat kamar bazata ce komai ba sai kuma tace “A’a ba da ni yake ba” Nenne tace “To amma ai ina daga gefe fa naji kamar ya tambayeki ko kina da bukatar wani abu, amma sai naji kin yi shiru” Khaleesat tace “A’a mun yi waya kuma nace masa bana bukatar komai, da Hadiyah yake ba ni ba” Tana fadin haka ta rufe ido alamar bacci zata yi, Nenne tace “Dama can Jay ya fi sa faram faram da mutane yafi sa iya mu’amala, wani lokaci rasa gane kan mijin nan naki nake, yau dai yayi kicin kicin da fuska kamar wanda ke cikin kuncin rayuwa, ranan da aka kai ki asibiti ma ni kamar ko gaisheni bai yi ba, ranan ma duk babu fara’a tare da shi, likitocin ma yaki masu magana balle nas, miskilin bala’i ne mijin naki, don ma an masa cuwa cuwa an kwace masa rawaninsa na magajin sarki, koma wanene ya kwace masa yarima ya tanadi abinda zai gaya ma Ubangiji don wannan zalunci ne” Khaleesat dai taki tanka Nenne…. Tun bayan tafiyar su Jay kullum sai Ajay ya je gidansu Khaleesat amma firrr bata yarda ya ganta don tana jin kamshin turarensa take pretending kamar tana bacci, tashin duniya Nenne zata mata amma baza ta tashi ba, sai dai Ng takoma ta ce masa bacci take yi ko zai shigadubata, kawai sai dai yace ma Nenne ta kyaleta kar a tasheta, wani lokaci kuma tana daidaitan sanda yake zuwa sai ta shige makota Nenne ta rasa gidan da ta shiga, gashi daga ita sai Nenne ne a gida don Umma na tafiya islamiyya, haka ma su Mama Shatu da gorin Nenne yasa su ma duk suka koma islamiyyah ana koya masu tun daga huruful hijaiyah, yaran gidan kuwa idan basa boko to suna islamiyyah…. Yau da yamma Khaleesat ta fito daga dakin Nenne da mayafinta a hannun tana son fakan idon Nenne ta shige makota don Ikcn da Ajay ke zuwa gidan ya kusa, Abdul ne yayi sallama, Khaleesat ta warware veil dinta ta yafa a saman kanta sannan ta zauna a parlon, Nenne dake zaune ta amsa sallamar Abdul tace “Lallai ka cika dan halak Awdul, daxun nan fa na gama cigiyar ka nace kuma Awdul shikenan don Haiydar ya koma Ingila sai ya dena leko mu, wallahi duk mun yi kewar ka, don Allah ka dinga zuwa tunda an saba, gashi babu Haiydar babu kai, ai unguwan bazai mana dadi ba kuma” Khaleesat ta dinga kallon Nenne don daxun nan ta gama hamdalan Abdul ya dena zuwa masu sun huta da fargaba, Abdul ya karasa cikin parlon ya zauna ya gaida Nenne yana dan murmushi, Nenne ta amsa da fara’a tace “Don Allah ko jifa jifa ne ka dinga leko mu ka ji” Abdul yace “Na zo wucewa ne nace in shigo mu gaisa Nenne” Nenne tace “Gaskiya ka kyauta sosai, bari in kawo maka mantina da ruwa” Tashi tayi ta tafi dakinta, Khaleesat ta dan yi murmushi tace “Ya Abdul ina yini?” Yace “Lafiya lau Hajiya, ya kike?” Tace “I am good, ya jikin Momy fa?” Abdul yace “Da sauki, she will be flowndnext week in sha Allah” Duk da kamshin tura Khaleesat ta fara ji hakan bai hanata ci gaba da maganar da take ba, cike da damuwa tace “Wai har yanxu jikin nata?” Abdul yace “Eh har yanxu, ya naki jikin?” Tana murmushi tace “Naji sauki tuntuni, zan ma Nenne magana sai mu je tare da ita mu dubo Momy in sha Allah” Abdul yace “To Allah ya kai mu, ina Dr Ahmad Jawwad?” Khaleesat tace “Ya Jawwad yana Bauchi, a nan Kano kake aiki yanxu?” Abdul ya dan yi murmushi yace “Yeah, but I have something doing in Tanzania, once a while nake practicing discipline dina….” Khaleesat tace “Ohk, business kake a Tanzania?” Yace “Yea, i am managing my dad’s business there” Khaleesat tace”Maa sha Allah, where are your friends? I think akwai Umar da Maska” Kamar bazai ce komai ba, sai kuma yayi murmushi yace “Ai bani da friends yanxu, duk bana mu’amala da su, da Haiydar kawai nake mu’amala mostly now” Muryar Nenne suka ji tace “A’a Junaid, ya baka shigo ba ka tsaya bakin kofa kuma?” All this while duk Ajay na tsaye bakin kofar parlon yana jin conversation dinsu, ya sauke idonsa ya cire takalmansa kansa a kasa ya karasa cikin parlon duk da bai yi niyyar shiga ba sai gashi Nenne ta gansa, Mikewa Abdul yayi, Khaleesat tace”Har zaka tafi ya Abdul?” Yace “Yeah, zan koma” Nenne tace “To ga Mantinan, har ina son zubo maka abinci kuma” Abdul yace “A’a Nagode Nenne” Bottle water kawai ya amsa sannan ya gaisa da Ajay ya fita daga parlon, Mikewa Khaleesat tayi zata bar parlon Nenne tace “Ina kuma za ki ga mijin ki ya zo, jiya ma da ya zo kina ta bacci, shekaranjiya kuma kin shiga makota ke da babu ruwanki da shiga gidan n tane”Bata juyo ba tace “Zan je bandaki ne” Ajay ylakan kujera ya gaida Nenne, Nenne ta amsa da rara’a tace “Bara in kawo maka Lemon kwali” Shi dai bai ce komai ba ta juya ta tafi dakinta da sauri, ba a dau lokaci ba sai gata ta fito da Kwalin tsadadden lemo da ruwan gora biyu ta ajiye masa a gabansa, ta koma daki, bubbuga kofar bandaki da Khaleesat ta shiga ta fara yi tana cewa “Wai lafiyar ki kuwa Khaleesat, ni fa sai yanxun nan na kula kamar gudun mijin ki kike yi, Yau kwanaki nawa kenan ya jera yana zuwa gidan nan amma sai dai ya tarar kin shiga makota ko kina bacci, to wa ma ya sani ko baccin sharri kike yi, to wallahi bara in kira Malam Ali, don ban san me ke faruwa ba gaskiya, ban san komai ba” Khaleesat ta hade rai tace “To ce maki aka yi wani abu ya faru ne?” Nenne tace “Fito ki tafi gun mijin ki, ko kuma in kira Malam Ali da Zahra’u su dawo yanxun nan ince masu gida ba lafiya, don ban san ma’anar wannan abu da kike yi ba, ina ma wayar tawa take” Bude kofar bandakin Khaleesat tayi tana kallon Nenne tace “Shikenan kuma don ya zo kar in shiga bandaki inyi abinda zan yi Nenne?” Nenne tace “Oho dai fitar min daga kara, tun da can baki san kina da uxuri ba sai da ya shigo alhalin zama kika yi kina ta hira da Awdul ko tsoron mutumin baki ji bayan babu wanda yafi ki sanin halinsa” Ficewa Khaleesat tayi daga dakin, Nenne ta nemi gefen gado ta zauna cike da damuwa tace “Anya kuwa lafiya, ko dai jefe ta aka yi ta dinga gudun mijin?” da gaske sai yanxu Nenne ta kula da cewa haduwa ce Khaleesat bata son yi da Ajay shi yasa take kirkiran bacci idan ya zo ko kuma ta fice daga gidan tun kan ya zo, to ko dai cikin ne yasa take haka, in dai ikibane to gaskiya babu lafiya akwai lauje cik Nenne ta girgiza kai tace “Ban ga ta zama baTunlafiya akwai lauje cikin nadi, Nenne ta girgiza kai tace “Ban ga ta zama ba” tun da Khaleesat ta fito parlor Ajay ke bin ta da kallo yana juya counter din hannunsa, ta tafi kitchen ta dauko Apple ta dawo parlon ta kwanta kan kujera tana cin Apple din tana canza channel fuskarta babu yabo babu fallasa, shi dai kallonta kawai yake with different thoughts running his mind, bayan kusan minti biyar Nenne ta fito parlon amma sai da ta leko taga ko hira suke amma sai taga akasin haka, nan jikinta ya kara sanyi ta kara tabbatar da cewa lallai da wani abu a kasa, ta karasa cikin parlon tace “Bari a zubo maka abinci Yarima, abinci ne me kyau Zahra’u ta girka daxu* Sauke idonsa yayi yace “A’a na ci abinci Kaka, dama za mu tafi asibiti na yau, akwai gwaje-gwajen da za ayi mata…”


