Novel Document

Gidan Aunty Complete Novel Document

Description/Story:

Gidan Aunty Complete Hausa Novel Document Written By Aysha Galadima

 

Description

TAHEE!!! TAHEE!!! “Naam oumma “ cewar wata yarinya wacce kallo daya zaka mata kasan bazata wuce 16 to 17 years ba, ta fito daga cikin wata kofa da kallo daya zaka mata kasan daga kitchen take, sabida flour da ya Dan bata mata jiki.” Har hanxu baki gama kwabin ba , kinsan abbanku ya kusan dawowa kuma kinsan inyazo ya taddaku haka ran mune zai baci duka ko!”kiyi hakuri oumma na kusa gamawa TAHEER nake jira ya taimakamun …”bata kammala magana ba sukaji anshigo falan ko sallama babu, Mai da hankalinsu sukayi kan kofa . Wata yarinyace itama da bazata wuce 15 to 16 ba a tsaye sai faman ya tsine take kamar wata babba, kura mata ido TAHEE tayi dan jiranjin mai zatace, dan tasan zuwan ameerah ba alkairi bane. Kamar kuwa ta shiga zuciyarta , “maryam dake da TAHEE wai Kuzo inji abba…, bata kammala maganar ta ba sabida saukar marukan da taji a waje maban banta. Kuka ta saki mai kara tana jiyowa. Karo taci da TAHEER da TAHEERA a tsaye sai faman huci suke saki, TAHEER ne ya soma magana “sau nawa zan fada miki duk lokacin da Kika kwaso rashin kuryarki ki dunga ajje ta a waje kafun ki tako mana daki, mahaifiyar Tamu kike dan baki da kunya “, kuka kawai ameerah take dan ba karamun zafin marin tajiba, dafe kuncinta tayi dagudu ta bar dakin .

Kallansu oumma tayi cikin hade rai,”sau nawa zan ja muku kunne kudinga hakuri da mutanan gidan nan, ko so kuke kudinga ganin raina yana baci” , kamar hadin baki TAHEER da TAHEERA suka ruke kunnuwansu ,”oumma kiyi hakuri bazamu sake ba “, Daman ta San halinsu, dungure musu kai tayi, atare suka saki dariya dan dama sunsan ba fushi tayiba.
Kamo hannayensu tayi tare da hadewa waje daya , TAHEE!! Naam oumma! TAHEERA ta amsa mata, maida kallanta tayi wajan taheer shima ta kira sunansa, amsa mata yayi shima yana kallanta. Numfashi oumma ta saki kafun ta soma magana cikin Sanyi , “ku kadai Allah ya bani, banaso kuna saurin fushinnan, inaso ko bayan raina kuzama masu kaunar juna kunji, ku zama masu hakuri da kawaici, Musamman Kai TAHEER , kafi saurin hawa”. Murmurmur taheer yayi tare da dan sosa keya, oumma kiyi hakuri, hararar wasa tasakar masa daman anan kafi kauri wajan bada hakuri. Kema taheera ki shiga taitayinki , hada ido Taheer da taheera sukai tare da hada baki , oumma kiyi hakuri bazamu sake ba .
Girgiza kai oumma tayi kawai, basuyi wata wata ba suka rungumeta, hado kansu tayi su biyun ta rungume a jikinta. Suna cikin zamannan sukajiyo bugun kofa da karfin gaske , duk mimmikewa sukai tsaye, bakowa bane face abba sai faman huci yake bayansa kuma mamy ce hannunta rike dana Ameerah sai faman cika take . Baiyi wata wata ba ya tsinkawa oumma mari, Maryam sau nawa zan fada miki ki fita harkar yata,me yasa bakyajin magana, Tom bari kiji na fada miki na gaji da wannan halayen naki, ki tattara kayanki kije na SAKEKI.
Kafun na dawo gidannan banaso naga fuskarki data yan iskan yayanki , sannan fuuu ya bar wajan. Shewa mamy ta saka toh maza maza azo abar mana gida tunda anzama bazawara, budar bakin ameerah sai cewa tayi da Yayan zawarawa sanin cewa ba mai tabata tunda uwarta na wajan , sai da mamy ta gama babatunta da zafesu tasss sannan takama hannun yarta sukabar wajan.

Zubewa umma tayi a kasa zuciyarta na faman ta farfasa ga kuncin da zuciyarta ke mata, fashe wa kawai tayi da kuka, TAHEE ma zubewa tayi a kasa tana kuka sosai, TAHEER ne mai dauriyar cikinsu yake lallashinsu, abun yayi masa ciwo sosai, asaki mahaifiyarsu agaban idansu dan basu da gata. Abbu nayi kewarka , ALLAH YAJIKANKA ABBU!! Shima sai ya fashe da kuka , haka suka kwashi kusan minti 15 suna abu daya , ganin sunki daina kukan Yasa oumma tsayar da nata kukan, tashiga lallashinsu.
Ganin sunyi shiru yasa ta mikewa, daki ta shiga ta tattaro musu Kayan sawarsu cikin jakunkunansu, sannan tasa taheer yasamo mata motar akurki dan kwashe mata kayansu, ba jimawa kuwa sai gasu, lokacin abba ya fita shiyasa mai akurkin ya shigo ya taimaka musu suka kwashe kayan.Mamy na labe ita da wata kawarta sai faman kwasan dariya suke , bayan sun gama kwashe komaine suka fito waje , oumma ta janyo kofar bangaransu Wanda ko cokali datasan natane bata bar musu shi ko daya ba.
Awaje ta tarar da mamy ta fito sai habaici take tana kwasar dariya kawarta na tayata, sabida rashin tarbiyya har ameerah ce ke kiransu zawarawa da yayan zawara wa uwarta na biyemata. TAHEER da TAHEERA kuwa suna gefe sun cika bamm ji suke Idan suka kama ameerah ba abunda zai hanasu lallasata .
Kamar oumma tasan abunda ke ransu takamo hannunsu suka fita , saida suka fita oumma ta fara tunanin ina zasu koma da zama.
Ba yadda ta iya dole su koma BUNKURE da zama , Wanda ba tsoran komawa take ba , aah yadda rayuwar yayanta Zata koma , batasan abunda zai kuntata wa yayanta, ganin tsayuwar ba mai anfani bace yasata yiwa me motar magana , bawan Allah bunkure zaka Kai mu nawa zan baka, 7k zaki bayar. Haba bawan Allah kadan duba mana, shikenan ku kawo 6k , kallan TAHEE da TAHEERA tayi da su shiga , ko wannansu jiki a sanyaye yashiga inda abunda suka tsana shine zuwa bunkure yadda ake gallazamusu suda mahaifiyarsu, ba adau lokaci ba suka fara tafiya kowa yayi jigum ba meyiwa wani magana kowa da abunda Ke cin ransa.

ASALINSU…..

 

File Name Gidan Aunty Hausa Novel Doc.
Title  Gidan Aunty...
Author  Aisha Galadima
Group Ai  Hausa Novels
Genre  Romantic Story
Published Date   02/03/2024
File Size   300Kb
Format Size    TXT
Phone No   07041879581
Download Gidan Aunty Complete Novel Document By Aysha Galadima

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button