Hausa novels

Ajiya A Duhu Book 1 Page 10 Complete Novel

*_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU….💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_**_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._*_My TikTok account 👇_*https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1*_Instagram👇🏻_*https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv*_Arewabooks_*Read My Book “AJIYA A DUHU” on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_🅿️➖🔟______________Abubuwan da nake saidawa Atamfofi Laces Shadda Materials Takalma Jakunkuna Mayafai Trolley Sarka da dan kunne Oil perfumesNumbers 0803446968108135142610Handles Instagram @ummu_mahnoor_luxuriesTikTok username @ummu_mahnoor_luxuriesFacebook ummu_mahnoor_luxuries____________……..Fuska ta ɓata sosai kafin ta kallesa babu wasa. “Kasan fa bana son irin haka ko?”. Kansa ya ɗan rausayar gefe yana murmushi da raba idanunsa a kanta. Cikin raɗa-raɗa ya ce, “Sam ban sani ba sai dai yanzu da kika faɗa min”. Harararsa ta sake yi zata raɓasa ta wuce yay saurin shan gabanta yana ƙara faɗaɗa murmushinsa. “ALLAH idan kika ce sai kin fita tare zamu fita ne, kuma duk inda kika shiga sai na biki a gidan nan kin dai sani”. Ɗagowa tai da mamaki ta kallesa, “Ka bini fa?”. “Yes gwada kuma ki gani, kin dai sai ni nafi mayen ƙarfe ai garama ki koma ki zauna kawai”. Kanta kawai ta ɗan girgiza, a zuciyata tana faɗin (Kai guy ɗin nan bala’i ne). A fili kam sai kawai ta koma ta zauna a kujerar dake kusa da ƙofar dama anan ta tashi. Ajiyar zuciya ya sauke shima tare da komawa ya zauna a inda ya tashi. Sai da ya ɗiba abincin zai kai baki sannan ya ɗago ya kalleta. “Bismillah”. Kanta ta girgiza masa kawai batace komai ba. Shima sai bai damu ba ya cigaba da faɗin, “Ina su Aneesa?”. “Gida”. Ta faɗa a taƙaice. Kansa ya jinjina kawai shima. Sai kuma falon yay ɗan shiru, a can ƙasan zuciyarsa wani irin farin cikine ke ɗawainiya da shi. Har dai ya kasa dannewa sai da ya furta, “Ashe ma ni a gida nake farauta amma naita wahalar da kaina. Ya kuke da su Najma?”. Ɗagowa tayi na ɗan kallesa, ganin shima ita yake kallo sai ta maida kanta ga wayata kawai. “Humm zama da miskilin mutum dai sai haƙuri, shike nan tunda bazaki sanar min ba. In tai wari naji. Ni bara na faɗa miki nawa alaƙan da su to. Mahaifiyarta Yaya tace uwa ɗaya uba ɗaya. Nine autan ɗakinsu, shiyyasa kikaji Najma na kirana Uncle”. Har cikin rai sai da taji tashin hankalin alaƙar tasu. Amma sai ta dake a taƙaice ta ce, “Masha ALLAH”. Murmushi yayi da ɗan girgiza kansa. Dai-dai nan Hajiya Majdiya tayi sallama. Amsawa yay yana mai maida dubansa ga ƙofar tare da bata izinin shigowa. Koda ta shigo idonta a kansu, fuskarta kuma ƙawace da murmushi. “Auta na kasa haƙuri ne ALLAH, yanzu Najma taje mana da wani daddaɗan labari”. “Kai wannan yarinya da gulma take aunty”. Cikin dariya Hajiya Majdiya ta ce, “Aini gulmar tata ta biyani. Kai idan hakan ta kasance zanyi matuƙar farin ciki Rafeeq. Kaga tuwona maina kenan, ALLAH ya tabbatar da alkairi dai”. Ko kunya Babu ya amsa da, “Amin aunty. Sai kita tayani addu’a dan gimbiyar har yanzu taƙi bani babban fili koda na zuwa gidane a sanni. Kuma shekara ɗaya kenan muna tare”. “Kai haba shekara ɗaya fa? Wai kodai dama itace kake faɗa mana ni da Aunty Babba kwanaki wadda kuka haɗu a jos?”. “Tabbas itace aunty”. “Ikon ALLAH, ni ashema abu a kusa dani yake haka. Karka wani damu kanka Maanal yarinyar kirki ce kamar yanda kake mutumin kirki. Na tabbatar itama zata soka”. Ko kunya babu ya kalli Maanal yana wani ɗage gira da faɗin, “Wai haka?”. Da sauri ta ɗauke kanta zuciyata na wani irin gudu da sauri-sauri. Yayinda take jin wani irin takaicinsa na yanda ya ɗaureta gaba ɗaya a wajen matar da take matuƙar ganin girma da kimarta. (Ya ilahi, RK kuwa nada hankali?) Ta ayyana a zuciyarta tana jin kamar ta saki kuka. Ita sai ma taji tausayin Hajiya Majdiya ɗin yanda taketa farin ciki kamar ma ance an aura masa Maanal ɗin….. Bayan ficewarta ta kallesa da idanunta da suka kaɗa dan masifar dake cin ranta. Sai dai tana motsa baki zatayi magana ya mike yana dariya. “Koma mi kike son faɗa haɗiye abinki ni na tafi wajen ɗaurin aure, ALLAH yasa muma azo namu nan kusa”. Yay ficewarsa yana kashe min ido ɗaya ga dariyar rainin wayo yana yi. Yana fita baifi da mintuna biyu ba, kafin Maanal ta gama tattaro abinda ya dunƙule mata nunfashi Najma da Amra suka dawo. Rungumeta Najma tai tana farin ciki wai zata zama matar Uncle ɗinta. Surutanta take amma ita Maanal sam bata wani fahimtar komai…. _____________★ “Wai nikam lafiya duk kin zama wata sukuku ko duk gajiyar bikin ce haka Auta?”. Didi Shahidah ce mai maganar tana zama kusa da Manaal dake kwance a doguwar kujera idanunta a lumshe. Tunda suka shigo gidan ta zube a wajen tana bitar abinda ya faru a Zaria. Ƙaramin murmushi ta sakar ma ƴar uwar tata. Sai kuma ta yunƙura ta tashi zaune sosai. “Babu komai Didi. Kawai na kwanta ne dai”. Murmushi Didin tai mata, sai kuma ta kai hannu ta ɗan shafi fuskarta. “Auta gyaran jikin nan na amsarki sosai. Idan kika yosa duk sai ki canja kamar wata amarya dake”. Da sauri Maanal ta ɓata fuska. Zatai magana aka buga ƙofar falon da ƙarfi har duk sai da suka razana. Hajiya Yaya ce sai yaranta biyu biye da ita. Cikin hargagi da masifa ta shiga ƙwala kiran ainahin sunan Ammie. Duk miƙewa sukayi, dan yanda take a birkice zakasan babu lafiya. Ita kanta Ammie da sauri ta fito ɗankwalinta a hannu. “Ya salam Hajiya miya faru?”. Ammien ta faɗa tana ƙarasowa cikin falon da sassarfa. “Oh tambayata ma kike miya faru? Wai Asiya nikam kodai ke kika haifar min Yazeed a gidan nan ne?”. A hankali Ammie ta sauke ajiyar zuciya tana mai girgiza kanta. Sai kuma a nutsenta ta bata amsa da “Hajiya kiyi hakuri ban san akanmi kike magana ba. Yazeed ai kowa yasan kece kika haifesa”. “To kuwa tunda kin san ni na haifi abina ki fitar min sabgar yaro. Dan wlhy idan ma kina mafarki ne ki farka. Ki kuma je ki sanarma bokanki anan anfi ƙarfinki anfi ƙarfin tsafinsa. Alhajin dai da kika iya mallaka har kika aura kinci nasara, wataran kuma ruwa zai ƙarema ɗan kada shima. Amma Yazeed har gaban abada bazai auri wannan ƴar taki ba, wancan ya samu ya gudu da ƙyar ko nace uwarsa ta miƙe tsaye a kanku shine ni za’a ƙaƙudubar min yaro da tsafi da asiri a haɗashi da sauran ciwo. Kuma wlhy daga yau sai yau, kika sake ɗaukar min yaro ya kaiki anguwa duk abinda nai miki kece kika jashi a gidan nan, mayyar mata kawai…….” “Haba Mamma nafa miki bayani Daddy ne yace muje ba laifin Ammie bane ba”. Yazeed daya shigo falon ya katseta cikin sarƙewar murya. Kansa ta juya da masifa kamar zata cinyesa. Harda faɗin idan har bai rabu da Maanal ba ALLAH sai ta ɗaga masa mama. Sai kuma ta juyo ga Ammien ta cigaba da mata zagi na rashin mutunci da gori. Gaba ɗaya rayukansu Shahidah sun gama ɓaci, yayinda Amal ta kasa haƙuri ta yunƙura zata tanka mata Ammie ta hanata. Dole tai shiru. Da gudu Maanal tabar falon kuka mai ƙarfi na ƙwace mata. Hakan yasa Amal bin bayanta itama zuciyarta kamar zata kama da wuta. Sam bata so Ammie ta hanata ba. Amma koba yau ba ta ɗauki alwashin sai ta gogema matar nan abinda ke kanta. Haba wanna abin ya isa haka mana. Tasara miyyasa mutanen nan basu da adalci sam, kowa dai Ammiensu kowa Amminsu sai kace itace kaɗai kishiyarsu. Taga dai suma kishiyoyin juna ne, amma basa fitinar juna sai Ammie, shin sai yaushe ne Ammiensu zataji daɗin rayuwar aurenta?. A gidan mahaifinsu bata zauna lafiya ba, fitinar miji data uwar miji, aka dawo ta kishiya har sai da ta bar musu gidan, yanzu kuma anan ta kishiyoyi har biyu…. Sosai Hajiya Yaya ta diga jidali da tujara wa Ammie kamar ta samu ɗiyarta. Ammien kuma bata tanka ba bata bar ƴaƴanta sun tanka ba. Hakan kuma shine mafi mata ciwo, kai su duka su wannan shirun da Ammien ke musu akoda yaushe na ƙona musu zuciya da ruhinsu. So da yawa suna mata abu dan ta tanka amma sai ta basar. Da ƙyar Yazeed ya lallaɓata ta fita. Suka bar Ammie da su Manaal cikin matsanancin ɓacin rai. Ga Ammie ta hana kowa maganar har dare sashen nasu babu daɗi. Hakan yasa duk suka kwanta da wuri. Sai can cikin dare Maanal ta bar ɗakinsu da ayanzu yake nata ita kaɗai sai idan sauran ƴan uwan nata sunzo gidan ne ta koma na Ammien. Ta sameta tana salla, dan haka itama ta fasa kwanciyar tayo alwala tabi sahunta. Sai da sukai sallar asubahi suka ɗan sake kwanciya Maanal ɗin dai nata daurewa dan bata jin daɗi…… ____________ “Wai Auta bazaki tashi a barcin nan naki ba haka nan. Jibafa lokaci ko kari bakiyi ba, ga ƴan uwanki na jiranki ki rakasu gidan mai gyaran jiki. Suna fara damunki kuma nasan zaki manta da yunwar cikinki ne ku tafi”. Kaɗan Maanal ta buɗe idanunta ta ɗan kalla Ammie mai maganar ta maida ta lumshe tare da sake naɗe jikinta waje guda. A yanayin mai barci da yanayin muryarta mai zurfi ta amsa da, “Ammie bana jin daɗi”. Da sauri Ammie ta ajiye abinda ke hannunta ta nufeta. Zama tai a bakin gadon tare da janye duvet ɗin da take a ciki ta ɗaura hannunta a goshinta, da sauri ta janye ta maida a wuyanta. “Ya salam, Manaal kinga tashi muje asibiti jikinki zafi, amma bayan kinyi sallar asubahi ne ma zazzaɓin nan dai?”. Hannun Ammien ta riƙo ta rungume a ƙirjinta. Cikin rauni ta furta, “Ammie abinne zai zo, ga kuma ƙirjina yamin nauyi, kwana biyu kenan kullum da safe nake zazzaɓin, shekaran jiya ma da muka taho banda lafiya”. Sosai rauni da damuwa suka bayyana a fuskar Ammie. Muryarta har rawa yake wajen furta, “Yaushe ya dawo yimiki kuma Maanal?”. “Ammie duka watannin nan da banzo gida ba yanayi. Na ƙarshen nan kwanana uku a hospital ma, hakkin ma ji nake kamar zai dawo”. “Ya arrahaman. Amma a watannin nan idan na tambaye ki kuma kita cewa babu damuwa. Haka kika dinga shiga cikin halin nan Manaal amma kina ɓoye min? Shiyyasa tunda naga duk kin sake figewa nasan kin ɓoyemin abubuwa ne. Nikam wannan ciwon naki na tayarmin da hankali, dan ALLAH Maanal ki cirema ranki duk wani abu, itafa rayuwa ɗaya ce, sannan bawa baya kasancewa a cikinta sai da jarabawa dama. Bakiga na haƙura nima na manta komai ba, hakama ƴan uwanki?”. “ALLAH Ammie babu abinda na sakama raina, kune kuke ganin kamar har yanzu ina riƙe da abubuwa, amma sam ba haka bane ba. Nifa musulma ce, kuma nasan minene rayuwa da ƙaddara. Ki cigaba da min addu’a kawai Ammie”. “In sha ALLAHU koda yaushe cikin yi muku nake. Kuma Alhamdullah da sauyin rayuwa da UBANGIJI ya bamu mai tazara sosai, idan mukai dubi da baya. Tashi kiyi wanka naima bana maigadi magana ko zamuje wajen mai maganin nan tunda nasa anji daɗinsa”. “Amma Ammie shima kuma gashi ya dawo ai”. “Duk da haka Manaal, ai kin samu ban iska tunda an samu sassaucin wahalar nan da kike sha kusan na shekaru bakwai”. Kanta ta ɗan jinjina cike da damuwa. Dan ita kanta ciwon nan na ɗaga hankalinta, ga shi kusan duk sanda zatai period sai abun ya ƙwaɓe mata da ciwon mara da take fama da shi shima, dan kamar ciwon maran yana zama sanadin tada ciwon zuciyar ne sakamakon tuno mata da abubuwan da suka faru baya da hakan keyi a duk irin lokacin. Har rama take farayi idan akace maka lokacin nan ya matso mata. Dan ita kaɗai tasan irin kalar azabar da take sha a rayuwarta. Duk yanda zata misalta ba lallai a fahimta ba. Shiyyasa idan akace mata haihuwa nada ciwo sai taita mamaki da ganin anya zata kai azabar da take sha a ciwon mara idan zatai period. Itafa nata ma dabanne dana duk wanda ta taɓa sani, ƴan uwanta ma duk sunayin ciwon idan zasuyi prioud ɗin, amma bai kai ko rabin nata ba. Kuma sunayin aure duk suka daina. Ammie tace ita suka gado, dan itama tasha fama har sai da ta haihu sannan. To ita abin nata ya zama biyu ne, ga ciwon zuciya kuma, shiyyasa hankalin kowa ke matuƙar tashi a duk sanda irin haka ya taso musamman akan ita Manaal da nata yafi tsauri. Ammie da kanta ta taimaka mata har zuwa bayi bayan ta haɗa mata ruwan zafi. Haka ta daure tayo wankan ta fito sai kuma rawar sanyi. Kasa zaman shafa mai ma tayi ta haye gadon ta sake ƙudundunewa. Dai-dai nan Amaal da Shahidah da Ammie tai kira a waya ta sanar musu suma Baba maigadi magana akan maganin Maanal ɗin dan ɗan uwansa ne ke bata suka shigo ɗakin. Su kansu su Shahidahn duk fuskokinsu sun nuna damuwa. Ƙarasawa sukayi inda Manaal ɗin ke ƙudundune suna mata sannu. Sai kuma Shahidah ta juya ta fita tana faɗin bari na amso maganin dan kamar sallamar Baba maigadin. Ilai kuwa shine, dan babu jimawa ta dawo da magani a gora. Da taimakon Ammie suka bama Maanal ɗin saboda rashin sonta da magani. Tana gama sha kuwa sai amai, dama haka yake mata, sosai tayi aman har ta basu tausayi. Haka suka taimaka mata suka gyara mata jiki ta sake yo wanka ta canja kaya ta koma ta kwanta. Cikin amincin UBANGIJI sai kuma barci mai nauyi sosai yay awan gaba da ita. Ajiyar zuciya suka dinga saki a tare, saboda in sha ALLAHU suna ganin kuma shike nan. Barci kuwa tayi sosai, dan bata farka ba sai bayan azhar. Alhamdullah taji daɗin jikin, ta samu ta sake yin wanka Ammie da kanta ta bata abinci, sai da taci sosai dan Ammien nata lallaɓata ga kuma waya da sukai da Nene zata zo gobe in ALLAH ya kaimu ya sake sakata jin daɗi saboda matuƙar son Nene da take a rayuwarta. Ga kuma ƴan uwanta zagaye da ita. Hakkanne ya sake ƙarfafata zuwa bayan la’asar tace suje ta rakasu gidan mai gyaran jikin zata iya. Koda sukace a’a sai Ammie tace suje ai fitar zata saka ta sake jin ƙarfin jikinta ta kuma warware. Da wannan shawarar sukai amfani suka tafi……..✍️✨ZAFAFAN DAI ✨1 ƘALBIM (Mamu gee)2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)3 DUNIYAR MU (Huguma)4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)Book 1:-500Book 2:-1000Book 3:-1500Book 4:-20000022419171Access bankMaryam Sani GumiShaida:- 09033181070Kati MTN:- 09032345899Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF89825722Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Ajiya A Duhu Complete Novel Document Txt
Back to top button