Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 18 Complete Novel

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

   EIGHTEEN📍

            “You must be joking sis! Toh wai meya miki hakane?”…..

Cewar jamila da mamaki ya isheta…….

             “Can you believe ni Saifuddeen yayi saving numberta da ‘this woman’?”….

Mami ta fada cike da takaici….. 

Wata muguwar dariya Jamila ta fashe da ita tana fadin;

      “Yanzu dama abinda yasa kikayi fushi dashi kenan? Haba you shouldn’t take it that serious ai”.

        “Ai dama you never take anything serious, bakya san lefinsa na riga nasan wannan karatun”……

Dariya ta karayi tace;

       “Niba haka nake nufi ba, yanzu dai we’re so sorry, in kika cire hannu a lamarinmu bamu san ya zamuyi ba”…….

Mami batace komai ba, amma har zuciyarta maganganun Jamila sun sanyaya zuciyarta…

Jamila is the real definition of a calm person, gata very jovial da wuya kaga tayi fushi amma fa intayi fushi ba wanda yake iya controlling dinta……

Parking mami tayi a harabar mansion dinta da kallo daya zaka masa kasan ba karamin dukiya aka narka gurin ginashi ba…. 

Fitowa sukayi a tare, mami tayi leading dinsu ciki….

Bayan sun gama kintsawa sun gama komai suka sake fitowa….

Direct hospital suka tafi domin su dubo yarinyar ganin yanda Jamila ta kagu taga abinda mami take fada akan yarinyar….. 

Office din Doctor suka nufa straight dan already mami tayi waya dashi akan suna hanya, shi ya dauka patient ma zasu kawo…..

Knocking sukayi ya basu izinin shiga…….

Zama sukayi suka dan gaggaisa sannan mami tace;

        “Doctor ya patient din tamu? Kajimu shiru ko, wallahi muna dan settling abubuwa ne”….

Murmushi yayi yace……

       “Yeah nasan dole zaku shiga busy dama, I hope dai sun sakeshi?”….

         “Zadai su sakeshi Insha Allah”…..

         “Ok, Allah ya yadda, about the other patient, wani yazo ya dauketa yace shi dan uwanta ne, na dauka ku kuka turoshi”……

          “Ayyah Allah sarki, toh ba damuwa”…..

Mami ta fada tana mikewa ganin tinda ba sanin yarinyar sukayi ba tayiwu yan uwanta sunji labarin accident din sunzo sukazo suka dauketa, so ba amfanin jan maganar kuma, saidai har zuciyarta bataji dadin yanda basu sami yarinyar ba, taso ace yar’uwarta jamila ta ganta wallahi…….

Godiya sukayiwa Doctor din sannan suka fita…..

Suna shiga mota jamila tace;

        “Gaskiya banji dadi ba da akace an dauke yarinyar, kinsan gidansu toh muje dan gaskiya I’m eager to see the girl gashi haryanzu baki fadamin abinda kika gani atattare da ita ba”…….

Ajiyar zuciya mami ta sauke tace;

       “Wlh bansan gidansu ba, gashi Deen yace shima besan ‘WACECE ITA BA’ even though he has met her before, sannan na manta abinda nagani a tattare da ita wallahi! Kamar wacce aka rikewa baki naji na kasa gayamiki ranar kuma shiyasa nace kizo ki gani da kanki”………

Zaro ido tayi tace;

       “Ikon Allah! Toh dan Allah muje gurin Saif din sai ya fada mana inda ya taba haduwa da ita, I’m so curious right wallahi, hankalina baze kwanta ba inba ganin yarinyar nan nayiba nima”…….

        “I want to teach him a lesson! Bayanzu zamuje ba, sai ya gane kuransa!”….

         “No sis, this is a serious case ko yaya muka matsa akai zaa iya cin galaba akanmu, kiyi hakuri agama case dinnan then punish him later, hannunka baya rubewa ka yar fah”…..

Girgiza kai mami tayi tanajin ko two days ne ya kamata tabashi ta yanda sai yayi losing hope kafin suje even though tasan ba lallai ya damu ba…..

          “Kinji sis, ko bazaki ba ki kaini pls, do it for the sake of baby tee inni bazakiyi dan ni ba”…… 

Shiru mami tayi jin an tabo dayan weak point dinta ko tace weak point dinsu duka, haka sukewa juna in suka kula dayansu bayasan abu, sai suyi using baby tee as a weapon…… 

Tada motar tayi batareda tace komai ba…..

Bata tsaya ko ina ba sai cell din da Deen yake ciki……

      Zaune yake abun duniya ya ishesa, so yake ko yayane ace masa she’s fine, tinda yazo ba abinda yakeyi sai tinaninta, kota farka yanzu? Is she alright? Isn’t she injured? Ana kula da ita?…..  Wa’yannan tambayoyin su suka taru suka cika brain dinsa, hakan saiyasa masa ciwon kai, yana cikin wannan hali kuma saiga mami, yaji dadi sosai saboda yasan koyaya ze samu information a gurinta dan yasan mami da tausayi dole zataje ta kara duba yarinyar, amma sai stupid mistake dinsa ya janyo mami ta wuce ta barsa, abun dariya tana tafiya ya chanja sunan daga ‘this woman’ to ‘birth giver’ (ni ko nace daga baya kenan😹)….. 

Tinani yake kawai ta hanyar da ze gudu daga cell din ya samu yaje ya ganta, daya ganta ze kawo kansa da kansa, shidai kome ze faru ya faru bayan yasan ‘ WACECE ITA’,….. 

Yana cikin wannan halin ya hangota, abu kamar a mafarki cuz she’s the last person he’s expecting, mikewa yayi da sauri ya karaso inda take yanajin abinda ke damunsa na raguwa kadan kadan…. Hugging dinta yayi sosai kamar jaririn dake neman taimako a gurin uwarsa….

         “I miss you so much Umm na”……

Shida kansa ya rasa wani kalan so yake mata, yanda yakejin maganarta ko iyayensa bayajin maganarsu haka, hakan kuma baya rasa nasaba da irin son da itama take nuna masa…….

Turesa  jamila tayi tana fadin…….

           “Ni matsa chan mara kunya kawai”…..

Dariya yayi sosai yana kama kunnensa yace….

          “I’m sorry Umm, tell her that I’m sorry pls”..

Kunnensa ta kama ta murde sosai tace;

        “Ni ina ruwana, you thought you’re doing the right thing ko? Ka fiso kata dagawa mutane hankali ko? To wlh baka isa ba, kasan da yaya ta yarda ta kawo ni kuwa?”…..::

             “Ouch da zafi fa Umm na, it was a mistake, I promise you bazan karaba, nafa maida mata sunan to ’birth giver’ yanzu”……

Ya fada yana janye kunnenshi……..

Dariya tayi sosai sannan tace;

         “Ai gwara ya maka zafi sosai, kace ka maida mata me? Ba birth giver ba saura ‘labor doer’, ja iri kawai”……

Shima dariyar yayi ganin tana dariya, shiyasa yake sonta dan akwai ta da saukin kai, tana da wasa kuma sosai……. 

 Sunkuyar da kai yayi kamar wani na Allah yace;

         “Nafa tuba sosai”….

Rankwashi ta kai masa tace;

        “Karma ka tuba ka tsaya kana hadasu fada da ubanka sai kace wani karamin yaro, besides inace dai nima ba ‘that yeye woman’ kamin saving ba ko”..

Dariya ya fashe dashi harda rike ciki, da kyar ya daure ya tsagaita dariyar yana fadin;

          “Nooo, my love nasa miki”……

           “Karya kake wlh, better save that name for your future wife dan mudai ba sanmu kake ba, kila ita ka sota”…….

        “Haba Umm na ya zakice haka, niko nake sanku, musamman ke sonda nake miki is special, kuma ni ki dena min maganar wata future wife, nifa bazanyi aure ba”…….

       “Ah lallai, toh in ciwo ne Allah ya yaye maka, ka dai gamawa yan mata rashin mutunci ka kwaso yar mummuna abunka”…….

Ta fada tana dariya……

Bata rai yayi yace;

       “Niba ruwana da mata be it me kyau or mummuna”………

          “Yayi kyau, you’ll repeat that again”….

           “Umm ina mami toh?”….

         “Tana waje, I doubt in zata shigo, da kyar ta kawo ni, saida na hadata da little tee!”…..

Murmusawa yayi yace…..

       “Kunfiya ji da little tee dinnan, shiyasa nake kishi da ita”…..

          “Gwarama ka taimaki kanka ka dena, kato dakai kana kishi da yar yarinya”….

          “Zan kamata ne ai very soon”….

Shiru Umm tayi jin wani memories na dawo mata..

Kallon Umm yayi ganin yanda yanayinta ya chanja a lokaci daya, yasan hakan kuma baya rasa nasaba da maganar baby tee da sukayi, a kullum yana mata addu’a akan Allah ya yaye mata damuwarta, sai kaga mutum koda yaushe cikin farin ciki amma deep down shiyasan me yake going through…..

      “Umm na ni kadai”…. 

Ya fada to cheer her up…..

        “Yes son”….

       “Dan Allah ki taimaka min mami ta shigo, I want to apologize to her”…..

Ya fada yana marairaice fuska dan taji tausayinsa, nan ko so yake ya tambayeta kota koma asibiti ta duba masa distraction dinsa……

Tausayi Umm taji ya bata ta kallesa tace……

      “I’ll try”…

      “Kisake hadata da baby tee pls, nasan zata yarda”….

Harararshi tayi ta fita….. 

Saida suka kai ruwa suka kai tsaki kafin mami ta yarda tashiga, nanma wai for the sake of baby tee ne……

Tinda tashiga bata kulasa ba, tana dai sauraron ranting din da yakeyi da sunan bada hakuri, hakurin da yake bayarwa har cikin zuciyarsa kuma, ance uwa da da’ sai Allah, nan da nan taji zuciyarta tayi sanyi harya fara bata tausayi……

A yatsine kamar bata damu ba tace;

      “It’s ok”…

Murmushi me fadi yayi yace;

       “Thank you mom, na chanja miki to sweet name, in baki ki gani?”….

Wani harara ta watsa masa, Umm na tsaye tana musu dariya…..

       “Ba wannan ne ya kawoni ba, dan inta kaine bazan zo ba wlh”….

        “Toh Nagode”….

Sai taji ya kara bata tausayi ganin yayi sanyi kamar ba stubborn Saifuddeen dinta ba, kasa hakura tayi tace…….

      “Are they maltreating you here? Naga duk kayi wani iri!”…….

      “Not at all mami! Ko kallon banza basamin under their boss custody, boss dinsu yace akwai mutunci tsakaninku sosai, har waya suke kawomin for some minutes everyday, abinci ma sai an kawomin menu, na zaba, ancemin it’s from you, thanks alot”…..

Numfashi ta sauke tanajin hankalinta ya dan kwanta tace;

       “Kaci gidanku, ni kake cewa thank you kamar wata stranger?”…..

 Cike da ladabi yace;

              “Not at all ma’am”…

       “Saifuddeen meya canzaka haka? Sam na kasa gane kanka, where the respect and everything comes from? Kodai you’re hiding something ne!”……..

Dagasken mamaki yake bata kwanannan shiyasa ta kasa hakuri harta tambayesa…..

       “I’m not hiding anything wlh mami, I’m sorry for all that I’ve caused for you, na tuba sosai”……..

      “Idan duk jikina kunne ne bazan yarda da wannan tubar ba”….

Cewar Umm tana dariya……

 Murmushi mami tayi tace;

     “Ah toh nima ban yarda taubatun nasuha yayi ba, well got some questions I wanted asking you dazu”……

      “Umm hardake, nafa tuba da gaske nace, mami proceed with your questions”……

      “Hmmm, so nake ka bani labarin how you were kidnapped, da kuma yanda lady din ta taimakeka har kukayi accident tare”……..

Labari ya shiga basu sosai tindaga lokacin data kira tace masa yabar inda yake dukda besan dalilinta ba a tunanishi takurar data saba masa ne, har yanda aka shaka masa abu ya suma a lokacin, da kuma inda ya bude idonsa yagansa, da irin gatan daya samu a gidan har yana tinanin daddy ne yasa a daukeshi kamar yanda ya saba masa a duk lokacin daya dade beje gida ba, da yanda ya kasa hakuri da zaman gida (though be fadamata dalilinsa ba) har Allah ya taimakesa yayi coming up with idea din guduwa daga gurin wanda  hakan yasa  yayi overhearding conversation dinsu na contract din kashesa da aka basu, Allah ya basa sa’a ya shaka musu abu suka suma da daukan bindigarsu da yayi domin ya kare kansa har Allah ya taimakesa ya bar gidan da bindiga a hannu, sai binshi dasuka dingayi da yake suspecting wasu daga cikinsu ne dabe shakawa abu ba, da irin gudun dayayi kafin Allah ya taimakesa ya tsaida wata mota ya shiga, a motar kuma sukayi accident da yarinyar dake tukin, be kuma san yanda akayi ake accusing dinsa da kisa ba…..

Tafi mami tashigayi bayan yagama bata labarin komai, sakin baki yayi yana kallonta da mamaki dauke akan fuskarsa banda Umm dake murmushi itama…..

Girgiza kai mami tayi tace;

       “Bazance ubanka ne yayi kidnapping dinka ko bashi yayi kidnapping dinka ba at first, saidai koma waye yayi kidnapping dinka beyi niyar kasheka ba da farko, daga baya kuma yaga gwara ya kasheka kawai saboda wani selfish interest nasa, hakan beyuwa ba da Allah ya baka sa’a ka gudu, sai daga baya sukaji labarin accident kayi, an kuma tabbatar musu da bindiga ka fita daga gidan, kayi accident da ita a hannu, sai sukayi tinanin bari suyi using wannan against you, tinda harka taba dole da thumbprint dinka a jikin gun din, dama kuma ta bandits ce dole ace anyi kisa da ita, so they lay everything on you yanda zasu samu hukuma ta kasheka a sawwake, they thought they’re smart, but they’re not! And we’ll prove them wrong, in sun san wata basusan wata ba!!”…………

 Sai a lokacin Umm ta shiga nata tafin, cike da murmushin daya kasa barin fuskarta tace;

     “You’re so smart Justice Fatima! And I’ll gladly be his lawyer!, this case needs to be very confidential!”..

        “Yes Barrister Jam!, luckily nasan Supreme Court zaa kawo case din, I’ll be the judge to the case!”….

Dariya sukayi gaba dayansu har Deen dayake godewa Allah da irin ni’imar daya masa, mami ta zurfafa karatunta har saida takai matakin ‘chief justice’, ita kuma Umm tayi studying law amma batayi furthering ba, but tanada chamber dinta da take receiving cases achan, sannan kuma kwararriyar medical Doctor ce da ake ji da ita a fadin Nigeria da kasashen waje, kusan ita tayi pushing Deen harya karanci medicine ya zama medical Doctor dukda bayaso……

        “Mami kinje kinsake duba ta?”….

Ya katsesu da tambayar abinda ya tsaya masa arai…..

      “Wa kenan?”….

Cewar mami dan harga Allah bata gane ba….

        “The lady we had accident together”….

Ya fada zuciyarsa cike da addu’ar tace sunje sunga she’s fine, har tambayarsa tayi(tsabar zakewa😹)….

        “Yeah munje, amma family dinta sun tafi da ita”…….

Cikin tashin hankali jin wacce yake planning guduwa akan yaje ya ganta wai an tafi da ita, yace;

       “What?!!!”….

        “Yes anything?”…

Cewar mami da taga ya zabura….. 

     “Yanzu shikenan an tafi da ita ba’a jirani nazo ba?” …….

Cike da al’ajabi mami tace;

     “Ikon Allah! Toh kai awa da zaa jira harsai kazo?”.

      “Dan bakisan irin neman danayi mata bane kafin Allah ya hadani da ita, yanzu kuma dana ganta sai a dauketa?”……..

Sakin baki Mami da Umm sukayi suna kallonsa aka rasa me cewa wani abu a cikinsu…..

Jin sunyi shiru ya sashi gane baran baramar da yayi, cikin kokarin kare kai yace;

      “She’s my student, she’s suspicious of an illegal act in the school and I was assigned on the case shiyasa naketa nemanta”…….

Kasa cewa komai sukayi, mami taja hannun yar’uwarta suka fita…..

      

          Bin Fatima zainab Khaleel yayi har parlourn momma, yana tsaye ta haura sama ta sakko, shidai besan metayi ba, yadai ganta da karamin box…..

      “Wifey!”…..

Ya fada ganin tana shirin fita kamar bata gansa ba…

Nan ko bata ma so suyi magana ne dan ita kadai tasan irin shock din da take shirin basa very soon……

        “Bani hanya mallam!”…

Ta fada fuska a hade…..

Kamar zeyi kuka yace;

      “Why are you avoiding me like this? Mena miki haka?”…….

          “Ka fini sanin abinda kamin! You’re so shameless for asking me!”…..

         “Nace miki it was just a mistake, dan Allah kiyi hakuri!”…..

         “Aini yanzu nafi karfinka khaleel, saidai ubanka!!”… Ta fada kai tsaye 

Zaro ido yayi yace;

      “Me kike nufi?”…..

     “Abinda brain dinka ya baka!”…..

Tana fadin haka ta bangajeshi ta wuce……

Parking space ta tafi, tashiga wata Rolls Royce 2022, ya figeta a guje bayan me gadi ya bude mata gate..

Sameer dake labe har lokacin data fita daga gidan, ya daga wayarsa da sauri jin tana ringing, banji me akace a dayan side dinba nadai ji sameer yace;

      “Yes you can start the job!”……

      Fitowar fatima zainab kenan daga wanka taji wayarta na ringing, da sauri ta karasa tana ayyana dalilin dayasa tabar wayar a kunne, luckily wanda take expecting ne kuwa, abu daya tasani shine dole ya amince ko yanaso ko bayaso….. 

Daukar wayar tayi ta kara a kunne, gaisawa suka farayi sannan yace mata;

      “Na amince! Zan aureki!”…:

Murmurshin daya kara fito da kyawun fuskarta me tsanin kyau tayi sannan tace;

      “Thank you husband to be!”…..

Wani iri daddy yaji ya dai daure yace;

     “You’re welcome! What are your plans for the wedding?”……..

Yaso yaki amincewa amma dayayi shawara da amininsa, sai yaga ba karamin saukaka masa abubuwa auren zeyi ba dukda besan dalilinta nasan auren ba,sannan ze samu ya jefi tsuntsu biyu da dutse daya…..

       “Well banaso ka fadawa kowa da bakinka har sai andaura auren, second inaso kabani personal card dinka na hadawa kaina lefe”……

               “It’s ok, zan aiko miki da card din yanzu, kina ina?”…..

          “Ina Transcorp hotel!”….

         “Ok, expect it soon”…..

         “Good”…

Ta fada tana kashe wayar….. 

Kamar yanda daddy yace basufi 30mins da gama waya ba sai gashi ana mata knocking wai there’s a delivery for her….. 

Karba tayi ta ajye tana lissafin perfect time daya kamata tashiga kasuwa, sai taga gwara kawai tayi ordern komai akawo mata har inda take…

A take tayi placing order kashi kashi, ko wannesu sukace zasuyi delivering in 3days time…….

Sosai hankalinta ya kwanta ganin three days din ze tafi da tsarinta…..

   

         Few days later……

       Horn takeyi ba kakkautawa a bakin get din gidan, me gadi dake zaune ya taso da sauri ya budemata, tin kafin ya bude zuciyarsa ke gaya masa itace dan ita kadai ke irin wannan horn din a gidan, kwata kwata bata da hakuri…….

Parking tayi ta yafitosa da hannu, jiki na rawa ya karasa inda take dan harga Allah kappa kappa yake da lamarinta……

Boot din motar ta bude ta nuna masa wani karamin akwati da kana ganinsa kasan me arhane sosai tamasa alamun ya fito dashi…..

 Dauka yayi da sauri ya bita a baya ganin harta fara tafiya,saida suka zo daidai part din mama sannan ta masa nuni da ya ajye ya tafi, ajyewa yayi da sauri ya koma bakin aikinsa…….

Daukan akwatin tayi ta banka kofar part din mama bako sallama, tana shiga tayi wurgi da akwatin a tsakiyar parlourn…… 

Imaan ce kadai a zaune a parlourn, ganin fatima zainab yasata mikewa da sauri tana kokarin guduwa, da sauri ta dakatar da ita da cewa;

      “Ke kiramin uwarki!”…

Da sauri Imaan ta haura sama har lokacin jikinta be dena rawa ba….. 

Sakkowa mama tayi tana taku daya bayan daya dan ita a nata haukar asirin da tayiwa daddy ne yasashi zuwa daukota da kansa daga cell dan be gayamata dalili ba gashi har hakuri ya bata akan wahalar daya bari tasha, sai ta hau kan keken bera ta zauna har lissafin ya kamata taje tayiwa mallam kyauta ta musamman takeyi….. 

            “Lafiya kike nema na munafukar Allah ta’ala”… 

Mama ta fada tana hararar fatima zainab…

  Murmurshi tayi tace;

       “Akwai munafurcin daya wuce wanda nazo miki dashi yanzu, dadin abun kinsanni munafuka ce!”

Sai a lokacin idan mama ya kai kan akwatin dake parlour, dagowa tayi tace;

     “Me kike nufi? Sannan wannan akwatin daga ina”..

Dariya fatima zainab tayi tace;

       “Kayan fadar kishiyarki ne, saboda tsabar matsayi kishiyarki ta kawo miki da kanta!!”….

    

Seriously your comments aren’t motivating at all!!

Your comments gonna determine next update!!🚶‍♀️

~Unique Barakancy~

Back to top button