Uncategorized

LABARINA SEASON 4 EPISODE 13 FROM SAIRA MOVIES

MARUBUCI:   Nasir S. Nasir Gwangwazokat! Ne a duniyar rubutu. Bana tantama ko shakkar alƙaminsa, gwani ne na yankan shakku. fikira da ƙwarewarsa sun tallafawa shirin wajen fuzgar zukatan masu kallo

UMARNI: Malam Aminu Saura, gwani ne da ya ƙware a harkar ba da umarni. Ya nuna gwaninta wajen sarrafa taurari tare da aje kowanne  a gurbinsa.

KAMFANI: Saira Movies.

TAURARI:

Sarkin Waƙa

Lukman

Rukayya

Ummi

Baba Rabiu

Sa’a

Bello

Atete

Kabir

Talatuwa

Bintalo

Murja

JIGO: 

Tsaro da soyayya.

FITA TA FARKO: Salo mai burgewa, kalamai ma su narkar da zuciya. Wa’azantarwa cikin hikima da gwaninta ba tare da jan aya ko hadisi ba. Tabbas an tsuma  mana zuciya da kalamai masu tausasawa.

KARANTA:

  Hukuncin Abincin Kirsimeti Ga Musulmi Fita ta farko

  Gwamnatin Tarayya zata dauki karin Matasa 400,000 aikin N-Power

 Kano State School Of Nurses and Midwife Enterance Examination 2021/2022

 Rahama Sadau Da Shatu Garba Mata biyu da suka fi shan ce-ce-ku-ce a shafin sada zumunta

FITA TA HUƊU: Hmm! Ziyarar Lukman da Ummi a gidan su Sumayya, ta zo da kalamai na bazata. Shin gaskiya ce ko abun kunya? Domin dai Ummi ta saki baki da yawa.

FITA TA ƘARSHE: Ta zo da abin da muka dade cikin lissafinmu. Wato haduwar Baba Rabiu da Presido.

1. Kalaman Umma a tataunawar su da Atete da Rukayya sun yi tsauri, kamar ta so ta sauka daga hanya.

2. An ɗaukko hanyar warware dukkan matsalolin shirin ciki hikima.

3. An sauya mana Sumayya cikin hikima. Tabbas ƙwaƙwalwa ta yi aiki.

Ƙorafi: Ma su kallo har da ni, muna kuka da tallan da ke janye yawan lokutan kafin fara shirin da kuma a cikinsa. Musamman ma na e-naira ɗin nan da kuma na Kano. Ya kamata a duba gaskiya.

Akwai sauran kallo a labarin nan!

     Mubarak Abubakar Saulawa

Kada na cika ku da surutu ku Danna bulun rubutun da aka saka Play Video ko kuma hoton dake ƙasa.

                             Play video


Back to top button