Uncategorized

Macijine Shi Page 59-60 Hausa Novel

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 59/60

________________Ahankali nanny ta ke kallon Adeeb,kafin ta sauke ajiyar zuciya,tunani take ta yadda Adeeb zai karbi wannan magana,ta yaya zata sanar dashi cewar,amminsa itace silar faruwar komai?shin zai amince da abinda zata faÉ—a masa ko yaya? Wane irin kallo zai musu idan yasan cewa amminsa ce ta kashe sarauniya Nazli da yaranta tare da baban tareeÆ™,kuma abakinsu?anya kuwa basu barowa kansu aiki ba?

“Nanny kiyi magana mana kinyi shiru, ki sanar dani wake da hannu akan hadarin nan?”

Da sauri nanny ta dawo daga dogon tunanin data tafi,kallon tareeƙ tayi cike da karayar zuciya ,amma cikin ƙarfafa gwuiwa tareeƙ ya kalli nanny yana mai jinjina kai da nuna alamun ,kwantar da hankali.

Ajiyar zuciya nanny ta sauƙe Tana mai kallon fuskar Adeeb,kafin ta fara magana.

“Magajin fada kamar yadda na faÉ—a maka,wasu abubuwan muna kallonsu ne ba a yadda suke ba,ka sani abinda zan faÉ—a maka ba Æ™arya ,ba kuma cutarwa.shiru ta É—anyi tana jinjina maganar kafin taci gaba”ba kowa ya shirya wannan hadarin ba, face Amminka”nanny ta faÉ—a tana mai kure Adeeb da ido.

Da wani irin slow Adeeb ya mike tsaye bakinsa bude,zuciyarsa na wani irin bugawa kamar guduma, ji yayi kunnensa ya ɗauki wani ƙara ƙuuuuuuuu!!!

Sai yake jin maganar ta nanny Tana rarrabewa,kamar baiji me take faÉ—i  daidai ba,jikinsa rawa ya kama,ta yadda yana mikewa tsayen yaji kamar zai fadi dan haka da sauri ya koma ya zauna,idanunsa Æ™uri,akan fuskar nanny,

Cikin in-ina ya ke cewa”na…nan.,…y mek….Ike ..son….f..a…É—..I n..ee.” ya faÉ—a numfashinsa na rarrabewa,ji yake kamar zuciyarsa zata fito tsabar yadda take bugawa.

Karanta Littafi>>> Yar Harka Hausa Novel

Da sauri nanny ta Æ™araso kusa da Adeeb ta zauna ,cikin nutsuwa take shafa bayansa tare da kallon fuskarsa cikin tausayawa,dole yaji maganar tazo masa kamar saukar aradu.”ka nutsu Adeeb  domin Abinda nake faÉ—a maka yana buÆ™atar nutsuwa,tabbas Amminka itace ta shirya wannan hadari,tare da taimakon wani ma aikaci dake cikin gidan nan,mai kula da harkokin motocin gidan”nanny ta faÉ—a cikin sanyin murya tana jin zafin rashin mijinta da uwar dakinta kamar yau abin ya faru.

Kallonta Adeeb yake cikin wani irin yanayi na mamaki ,al’ajabi,tsoro,ruÉ—u dakuma firgici,ji yake kamar zuciyarsa zata iya fashewa ako  wane lokaci,wannan wane irin magana nanny keyi?anya kuwa tana cikin hayyacinta?yaushe nanny ta koma  maÆ™iyarsa ta hanyar hade kai da amma?dan su shiga tsakaninsa da amminsa? Dan kuwa yana tabbatar da cewa wannan shirin amma ne,lallai duniya ba tabbas .cikin zuciyarsa yake wannan maganar,kafin a fili ya kalli nanny ,sannan ya kalli tareeÆ™,sai kuma yayi murmushi wanda yafi kuka ciwo ,sannan ya miÆ™e tsaye yana mai sanya hannunsa cikin aljihu,sannan ya fara magana bayan ya juya bayansa yana kallon bango” ban taba tsammanin cewa matar data raineni tun Æ™uruciya zata iya hade kai da makiyana,É—an ganin sun shiga tsakanina da ammina ba ,yau na kara tabbatar da cewa lallai wanda kake kallonsa matsayin masoyi ,to shine makiyinka aboye, amma bantaba tsammanin haka daga gareki ba nanny;Adeeb ya faÉ—a cikin zazzafar murya yana mai juyowa ,idanunsa sun kada sunyi mugun jaa, kallo É—aya zaka masa kasan cewa zuciyarsa akaraye take.ci gaba yayi da cewa”nanny why ?why nanny me yasa zaki canja daga yadda na sanki?me yasa zaki so ganina cikin damuwa?na dauke ki tamkar mahaifiyata,duk wani abinda ya dameni ina zuwa gareki dan samun mafita,ammina tana kula dake da duk wani bukatun ki,amma meyasa kika hada kai da maÆ™iyanta?me yasa kika saida kanki dan bata alaka tsakanin da da mahaifiya?nanny why?tareeÆ™ me yasa nanny zatayi min haka?Adeeb ya faÉ—a yana mai riÆ™e kafadun tareeÆ™ idanunsa na zubda kwalla ,gaba É—aya jinsa yake kamar ba shiba, wani sashen na zuciyarsa yana son karbar maganar nanny,saidai sashe mafi rinjaye na zuciyarsa na tunatar dashi wacece ammi agareshi,dan me zai yarda da batun nanny?.

Cikin damuwa da alhini tareeÆ™ ya kama hannun Adeeb ,cikin murya mai nuna tabbatarwa ,tareeÆ™ ke fadin, “yallaÉ“ai ka kwantar da hankalinka,kuma kayiwa maganar nanny kyakykyawar fahimta,da sannu zaka gano gaskiyar dake cikin batunta, yallaÉ“ai munsan abubuwa da dama wanda kai baka sansuba,amma da sannu zaka gane da kanka”tareeÆ™ ya faÉ—a cikin marairaita yana kallon Adeeb.

Fizge hannunsa Adeeb yayi tare da dafe kansa da yake jinsa kamar zai tarwatse,kafin ya kalli tareeÆ™ yana mai jinjina kai”well na gane ,na gane tareeÆ™ kaima kana bin bayan mahaifiyarka ko?da kai aka hada baki,am disappointed tareeÆ™” Adeeb  ya faÉ—a yana girgiza kai cikin karayar zuciya,idanunsa na fitar da hawaye mai tsananin zafi da Æ™una.ahankali ya juya ya nufi Æ™ofa yana dafe kansa .

Karanta Littafi>>> Matar Hariji Romantic Hausa Novel Complete

Cikin damuwa da zubda kwalla nanny ta miÆ™e da sauri tana kiran Adeeb” magajin fada karkayi saurin yanke hukunci akan maganata kana bukatar nutsuwa da bincike dan Allah ka yarda dani É—ana, bazan taÉ“a cutar da kaiba.”nanny ta fada cikin zubda hawaye .

Ko waiwayowa Adeeb baiyi ba ya fice daga É—akin ,cikin sauri, dan ko ganin fuskar nanny baya sonyi ahalin yanzu.zuciyarsa na tafarfasa ,ji yake kansa kamar zai kama da wuta.kai tsaye part É—in ammi ya nufa ko zai sami salama cikin zuciyarsa.

“TareeÆ™ ka gani ko?kaga Abinda nake faÉ—a maka,Adeeb ya riga ya makance,baya ganin laifin ammi ko kaÉ—an,yanzu bansan wane kallo zai rinÆ™a yi mana ba”nanny ta fada cikin kuka.

Kamata tareeÆ™ yayi ya zaunar da ita akan kujera ,hannunsa ya sanya yana share mata hawayen dake zuba daga idonta,kafin yace ” ummee na,ki kwantar da hankalinki,dama shi aikin alheri haka yake,dole saika fuskanci Æ™alubale,nasan yallaÉ“ai zaiyi fushinsa na wani lokacin kafin ya sauko,kuma nasan daga yau zai fara bincike akan abinda kika sanar dashi,In Sha Allah muke da nasara ,tunda  akan gaskiya muke”tareek ya faÉ—a cikin yanayin Æ™arfafawa mahaifiyar sa gwuiwa.

“In sha Allah tareeÆ™ ,Allah ya datar damu”nanny ta fada tana share hawayenta.

Ameen yace ,kafin suka ci gaba da tattaunawa akan matsalar.

Kai tsaye ya shiga part din na ammi,ko kula gaisauwar da hadimanta  keyi baiyi ba,dan zuciyarsa ba abinda take sai tafarfasa,bai taÉ“a tsammanin haka daga su nanny ba,lallai mutum bashi da tabbas.

Afalo ya ci karo da sarauniya suhaimat,tana zaune da yaranta,suna cin apple da ya’yan itaceya ,gefe guda kuma suna kallo.

Da gudu su zayyad suka taso suka rungume Adeeb suna murnar ganinsa,kansu kawai ya shafa tare da rungumarsu,shima.

Kallonsa sarauniya suhaimat keyi,dan kuwa taga tarin damuwa cikin idanunsa.

“Sannu yarima ,ya jikin naka?dana yarinyar ?”sarauniya suhaimat ta fada cikin yanayi na nuna damuwa .

Lumshe ido Adeeb yayi cikin damuwa da yanayinsa  na rashin son magana yace “da sauÆ™i”  atakaice .

“Allah ya bata lafiya ” ta fada  da yanayi na damuwa.

“Ameen” Adeeb ya faÉ—a ahankali.

“Ammin naka tana ciki”sarauniya suhaimat ta fada cikin kulawa.

Kai kawai Adeeb ya jinjina mata kafin ya wuce zuwa cikin dakin.

Karanta Littafi>>> Ahalin Macizai Hausa Novel

” Bangane ba ?kamar ya nayi sakacin da kwalbar ta fashe,bayan irin kulawa da ita da nake?kasan irin kuÉ—in dana kashe akan akwatin da aka Æ™era na sanya kwalbar ciki?

Shiru tayi ,da alama tana sauraron abinda ake faÉ—ane daga can bangaren.

“Shikenan ,yanzu muna cikin alhini ne na wannan abun daya faru,dan haka kajira nan da kwana biyu,zan nemeka,dan awannan karon aiki nakeso ayimin na ban mamaki,bana kuma son asami matsala ” ammi ta faÉ—a cikin wani yanayi mai nuna ta shirya mugunta mai zafi cikin ranta.

Gaban Adeeb ne yayi wata irin faɗuwa da har saida ya dafe ƙirjinsa,wane akwati ammi ke magana akai?wace kwalbar ce ta fashe?da wa ammi ke waya?waɗan nan sune tambayoyin da Adeeb ke yiwa kansa,saidai bashi da amsar ko daya daga ciki.

Ganin ammin ta gama wayar kuma tana ƙoƙarin juyowa ne ,dan ta ba ƙofa baya,yasa Adeeb saurin saita kansa yayi sallama tare da shiga.

Da sauri aɗan razane ammi ta juyo tana kallon Adeeb ɗin,dan batayi tsammanin ganinsa yanzu ba, saidai da alama baiji me take faɗi ba,itafa wllh tsoronsa ma ta fara ji yanzu,amma saita maze ta saki murmushi,tare da miƙa masa hannu,alamun ya ƙaraso gareta.

Ahankali Adeeb ke takawa har yaje bakin gadon ya zauna,dan jikinsa sam ba kwari,murmushin ƙarfin hali yayiwa ammi yana kallon fuskarta,

“Habeebee ya jikinka? na tsorata sosai da yanayin dana ganka É—azu”ammi ta faÉ—a tana mai janyo Adeeb zuwa jikinta.

Sam yau Adeeb ji yayi baya wani jin dadin kwanciya akan cinyarta,Dan saiyajisa kamar akan Æ™aya, dan haka da sauri ya tashi daga kwanciyar da yayi,kafin ya dan saki murmushi,yana mai cewa”Æ™alau nake ammi,kada ki damu,ya naki jikin?”ya faÉ—a sam fuskarsa ba walwala.

“Shafa kansa tayi kafin tace naji sauki dana karka damu”ta faÉ—a tana kallon fuskarsa ,dan kuwa sam ba haka yake mataba,yau kam ba wannan shaukin da yake nuna mata idan suna tare.

Mikewa yayi yana mai faÉ—in ammi zanje in duba yarinyar can zan dawo anjima” yana faÉ—in haka yayi waje abinsa.

“Yawwa yarima ,ina son in duba yarinyar nan “sarauniya suhaimat ta fada tana mikewa lokacin da Adeeb ya zo zai wuce.

Shiru yayi yana É—an nazari,akwai bukatar ta duba ta ,tunda likita ce itama ,kuma fannin mata ta karanta.

Dan haka yace “ok muje ,tana part É—ina”

Ficewa sukayi tare suka nufi part din Adeeb.

Karanta Littafin>>> Yaro Ne Complete Novel Document

Toh masu karatu ,mubi su Adeeb dan duba Hulwa.

Sai mun hade next page.

Mrs babi ce 💘💘

Share and comment fisabilillah.

More comment

More typing.m

Back to top button