Hausa novels

Ruwan Zuma Page 36 Hausa Novel

(36) “Ba yanda za’a yi a aika wani sai ni?�? Haydar ya tambayi Alhaji Abdul bayan ya gama fad’a masa tafiyar da zai yi zuwa Abuja. “Aikinka ne bana kowa ba.�? Ya bashi amsa tamkar bashi da damuwa a duniyar. “Shikenan.�? Da haka suka cigaba da magana kan abunda zai je yayi. Bayan sun gama Haydar ya koma office d’insa ya tattari kayansa ya koma gida domin a gobe zai yi tafiyar tare da wasu mutane biyu daga cikin company nasu. D’an achaba ya sauk’eshi a waje shi kuma ya biyashi kana ya shiga gidan. K’ofar falon daya zama nashi ya bud’e ya fara ajiye jakarshi a kan kujera yana kasa kunne ko zai jiyo motsin Laila duk da cewa bai ga motarta a waje ba. Yau kwana biyar kenan da yin fad’ansu wanda daga shi har ita kowa ya damu bana wasa ba. Zata mishi girki ta kawo mishi har side d’in da yake, sannan idan ya fita zata shigo ta gyara masa d’akinsa ta kuma kunna mishi turaren wuta kamar yanda ta saba. Sai dai shareshi da take yi yafi k’ona mishi rai domin ta nuna bazata bashi hak’uri ba balle kuma ta canja halayenta ba, kenan har lokacin tana kan bakanta na k’in haihuwa dashi. Daurewa kawai yake yi domin tunda ya aureta bai ta6a rabuwa da ita a makwanci ba sai wannan lokacin, sai yanzu ya gane cewa tayi tasiri a rayuwarsa yanda baya zato, domin yanda yake jinta a ranshi yanzu har yafi na daa. Sai da yayi wanka sannan ya dawo ya d’ibi abincin da ta saka mishi kad’an kamar loma uku, hakan na cikin puninshment d’inta domin yasan tana son yaci abincinta sannan ta k’i jinin yaci kad’an ya bar mata sauran. Yana zaune a falo bayan la’asar yana tunaninta wanda ya zame masa d’abi’a yaji shigowar motarta gidan. Duk da yasan cewa baza tazo gurinshi ba amma yaji dad’in dawowarta domin ko ba komai suna zaune a rufi d’aya. Yana ji ta bud’e falonta ta shiga ya kwanta a kan kujerar ya rufe idonsa yana jin zirga-zirganta tsakanin kitchen da falonta wanda ta d’aura musu abincin daren ta ba zai ci ba. Sai da Haydar ya fita sallan magrib sannan Laila ta shiga sashenshi ta samu ya cakali abincin ya bari. In ba don gudun kar abun ya wuce haka ba daa ta daina girkin gabad’aya, domin bata ga amfanin yin ba tunda ba ci yake yi ba, itama kuma damuwarta bai barta ta ci ba. Tuwon data mishi miyar d’anyen ku6ewa da tasan yana so ta ajiye mishi kana ta fita daga falon ta koma sashenta zuciyarta na k’una. Ta san da gangan yake mata haka amma yayi duk abunda zai yi domin har gobe tana kan bakanta. Shi kuma yana dawowa ya shiga d’akinsa ya fara had’a kayan da zai yi tafiya dasu gobe da asuba. Bayan ya gama ya dubi inda ta ajiye mishi abincin amma bai bud’e ba balle har yaji yana son ci, saboda shi In zai yi tafiya baya cin abinci da dare da kuma safiyar ranar gudun tsayawa a hanya ko gur6acewar ciki. K’arfe goma saura kwata yayi shirin bacci ya shiga sashenta yana jin kewarta da kuma wata muguwar son kad’aicewa da ita. A can d’akinta ya sameta kwance a kan gado kamar ma tayi bacci, hasken d’akin ya kunna idanunsa suka saisaita kan surar jikinta cikin night gown d’in da ta saka wanda ya bayyana wasu ga6o6in jikinta. Tsura mata ido yayi na wasu sakanni yanayinshi na canjawa yana jin kewarta a ranshi. Can kuma yayi gyaran murya ya kira sunanta. “Laila.�? Bata amsa ba hakan yasa yayi tunanin bacci take amma daya tuna cewa da zarar an kunna hasken wuta a kanta take farkawa sai ya gane da gangan ta shareshi. Hakan yasa ya murmusa kad’an sannan ya k’ara kiranta a karo na biyu. Can k’asan mak’oshinta ta amsa sannan ta gyara kwanciyarta ya bita da ido. “Zan yi tafiya gobe zan je Abuja. Watak’ila zamu kai sati ko kuma muyi kwana biyar.�? “Allah ya kiyaye hanya.�? Kawai tace dashi amma ya gane muryarta ya fara rawa. “Me kika ce?�? Ya tambayeta domin yana son gaskata kunnenshi. Jin tayi shiru yasa ya tsaya bai tafi ba, seconds goma da haka kuma yaga jikinta na rawa alamar kuka take yi. Babu abunda yafi karya masa zuciya irin kukan Laila kuma ya tsani ganin kukanta. Takawa yayi ya isa gurinta jin ba’asin kukanta, “Meya sameki kike kuka? Meya faru?�? Ya tambayeta yana d’age hannunta da ta rufe fuskarta dashi, sai dai bata bari ya bud’e mata fuskar ba sanin ya 6aci da hawaye. “Tambayanki nake yi kinyi shiru.�? “Babu.�? Ta bashi amsa a karo na farko. “Haka kawai da girmanki ki fara kuka babu abunda ya sameki Laila?�? “Nace babu komai.�? Ta fad’i hakan tana goge hawayen ba tare data yarda sun had’a ido ba. “Don zanyi tafiya kike kuka?�? Ya tambayeta yana d’aga ha6arta wanda hakan yasa ta kalli kwayar idanunshi a karon farko bayan sa6anin da suka samu kwana biyar da suka wuce. Marairaicewa tayi tare da shagala da kallonsa domin ba k’aramin kewarshi tayi ba dalilin wannan karon sun raba makwanci yanda babu mai ganin d’an uwansa. Karantar idanunsa da tayi kad’ai yasa ta fuskanci yanayin da yake ciki wanda in zata fad’i gaskiya itama tana buk’atar mijinta domin horon ya musu yawa dukansu. Tana ji ya kai hannunshi jikinta ta bada kai suka lula duniyar masoya. Bayan komai ya lafa Haydar ya koma gefe ya jawota jikinshi yana jin zuciyarsa fari tass har yana ganin wautarshi na nesanta kanshi da yayi da ita na tsawon wannan lokacin. “Komai ya wuce ko?�? Ya tambayeta yana tufke mata gashinta daya kunce mata d’azu da suke wata duniyar. Gyad’a mishi kai tayi kana ya sumbaci tsakiyar kanta ya gyara musu kwanciyar dalilin baccin da yake ji sosai. Laila da kanta ke k’irjinshi taci gaba da sauraron bugun zuciyarsa har bacci ya d’aukeshi amma ita nata k’ekau tana jiran baccin nashi yayi nauyi. A hankali ta zare jikinta sannan ta zura night gown d’inta dake yashe a k’asa. Cikin sand’a ta fita daga d’akin tayi hanyar kitchen. Sai data gama abunda zata yi sannan ta dawo ta samu babu Haydar a kan gadon. Zuciyarta ce ta buga da k’arfi ba dai ya biyota ba a karo na biyu? In bata manta ba hakan ne ya jawo musu fad’a kuma gashi da alama ya sake kamata a karo na biyu. A birkice ta fito falo ta isa bakin k’ofar da zai sadata da sashen nasa, sai dai tana murd’awa taji k’ofar a gark’ame alamar an saka makulli. Jijjiga k’ofar ta fara yi tana kiran sunanshi a hankali sanin dare yayi. Duk abun nan da take yi Haydar na zaune a falo ya dafe kanshi da hannunsa biyu idanunsa sun cika da hawaye amma ya k’i bari su zubo. Bak’in cikin da yake ji ya tsaya a mak’oshinsa yana jin azabar zafi a ranshi. Wai dama Laila haka ta tsaneshi bata son had’a zuriya dashi? Menene laifinshi don yana son haihuwa da ita? Me ta d’aukeshi sannan wani irin matsayi take bashi a rayuwar aurensu? Shin anya ta d’aukeshi a matsayin mijinta ko dai ta ajiyeshi ne a matsayin mai d’ebe mata kewa ba tare da sun haihu ba? Meyasa take son 6ata soyayya da kuma auren dake tsakaninsu? Ire-iren wad’annan tambayoyin ne a ranshi wanda yaji nan take ya fara tausayinshi kanshi daya d’aurawa kanshi son tara zuriya mai yawa kuma yake son babbar mace at the same time. Meyasa bai yi tunanin Laila zata k’i haihuwa ba? “Haydar ka bud’e mini don Allah ka saurareni.�? Fad’in Laila cikin magiya domin tasan yayi fushi mai tsanani wannan karon. Yana jin hakan ya tashi ya shige d’akinsa, kai tsaye ya shiga band’aki ya sakarwa kanshi ruwa ya fara wanka. D’azu bai jima ba dashi da ita duk suna cikin walwala da farin ciki amma lokaci d’aya tayi sanadiyyar wargajewar komai ta sanyashi cikin k’unci da yake jin d’acinsa tamkar mad’aci. Ko da ya fito bai ji motsinta a bakin k’ofar ba, a nan kuma zuciyarsa ta raya mishi cewa taje k’ara shan abunta ne. Wannan tunanin kad’ai yasa yaji bak’in cikinsa ya k’ara hauhawa yana son dukan abu, abu mafi kusa dashi ya d’auka yayi cilli dashi ya had’u da gini ya fad’i k’asa. Ya jima a tsaye yana nanata Lahaula a ranshi da kuma korar shaidan sannan yaji sauk’i kad’an ya zauna a bakin katifar yana tunanin wannan rayuwar daya tsinci kanshi a cikinta. Matarsa ta Sunnah ba dadironsa ba amma tana kyamar d’aukan cikinsa? Meya mata? Me zai yi? Washe gari da safe k’arfe shida Laila ta gama karyawa ta d’auka ta nufi sashen Haydar. Sanin cewa ya rufe k’ofar dake tsakaninsu yasa ta d’auki makullin main door d’in dake waje ta fita kai masa abincin tunda jiya ya fad’a mata cewa zai yi tafiya. Tana bud’e k’ofar ta kutsa kai ciki ta isa inda take ajiye mishi abincin taga wanda ta ajiye masa jiya ma bai ci ba, d’akin da yake kwana ta nufa tana neman kalmomin da zata yi amfani dasu still ba tare da ta amince da abunda yake so ba. Tana son fahimtar dashi me take gudu ko wannan karon zai gane idan ya saurareta da kyau. Kwankwasa k’ofar tayi tana sallama amma ba’a amsa mata ba, murd’a hannun tayi ta shiga sai dai bata ga Haydar kamar yanda tayi tsammani ba. Ba dai har ya tafi ba? Shine zai tafi bai mata sallama ba? A kan katifar tashi taga kud’in daya ajiye mata wanda ta sani na cefene da kuma in buk’atarta ta taso ne. Zama tayi a bakin katifar zuciyarta na mata rad’ad’i domin kamar tana cutar da yaron. Ita kanta ta sani yana kula da ita da kuma nuna mata tsantsar soyayyar da take tunanin har abada ba zai iya had’a soyayyarta da wata ‘ya mace ba. Amma shin ita tana masa wannan k’ok’arin da kuma jajircewar akan sonshi? Ta masa adalci kuwa? Shin ta kyauta masa? Yaya zata yi? Kwantar da kanta tayi akan pillow tana shakar asalin scent d’inshi na d’a namiji wanda yake mata dad’i. A maimakon hakan ya sakata farin ciki ko ya yaye mata damuwarta sai k’ara mata yayi taji idanunta sun cika da hawaye, a take suka fara sauka ta gefen fuskarta tana tuno rayuwarsu da matsalolin da suka fuskanta tun daga ranar d’aurin aurensu har rana mai kamar ta yau. Haydar kuma suna isa Abuja suka sauk’a a Hotel mafi kusa da inda zasu yi aikin daya kawosu. Tafiyar ranar ya yishi ne cikin shiru wanda abokan aikinsa wanda suka fara mutunci suna tsokanarshi wai ko yayi missing Madam ne? Murmushin k’arfin hali ya musu kana ya rufe idanunsa tamkar mai bacci wanda hakan yasa suka daina tsokanarshi suka cigaba da tad’insu. Bayan ya kimtsa a d’akin da aka bashi ya sauk’a k’asa gurin receptionist desk ya kira Ammi da telephone d’in gurin. Bayan sun gaisa ya fad’a mata sun isa lafiya. “To Alhamdulillah, Allah ya amfana ya bada sa’ar abunda aka je nema. Amma meyasa baka yi amfani da wayarka ba?�? Ta tambayeshi domin bak’uwar number da ta gani. “Wayar babu charge ne Ammi, kawai zamu dinga gaisawa ta nan yafi arha tunda ba biyansu zan yi ba.�? Dariya tayi mai sauti kana tace, “Ban sanka da son banza ba Ali. Ka huta gajiya.�? “Ammi.�? Ya kira sunanta wanda yasa ta tsaya daga kashe wayar da tayi niyyar yi. “Na’am Ali. Yaya dai?�? Ta tambayeshi cikin maida hankalinta kaf kanshi domin taji muryarsa ta canja. “Ina sonki Ammina.�? Ya fad’i hakan cikin murmushi. Ajiyar zuciya Ammi ta sauk’e kana tace, “Shiririta kawai. Ka ga gwanda kai, domin ni abinci zan tashi na d’aura.�? Itama zallar murmushi da farinciki a tata fuskar. “Eh naji you love me too. Sai anjima.�? Da haka ya kashe wayarsa yana jin d’an dama-dama a ranshi. Laila bata tashi a gurin ba sai k’arfe goma na safe dalilin baccin daya d’auketa a gurin wanda bata yi ba a daren jiya. Sai da ta kimtsa masa d’akin sannan ta fita bayan ta d’auki rigar daya cire ta manna a hancinta tana shak’ar k’amshin jikinta. Da haka ta koma sashenta ta samu kiran mutane barkatai ciki har dana ‘yan shagonta. Duk missed calls d’in ta tsallake ta sauk’a kan sunan Ruwan Zuma ta kirashi, sai dai nan take matar tace mata wayar is switch off. A iya saninta Haydar Sim d’aya gareshi bashi da wata, to yanzu ta yaya zata sameshi? Tana wannan tunanin aka k’ara kiranta wanda Mas’ud ne yake fad’a mata Ummii bata da lafiya har an kwantar da ita a gadon asibiti d’azu da safe. “Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun. A wani asibiti kuke?�? Ta tambayeshi cikin kid’ima tana bud’e wardrobe d’inta ta d’auko hijabi. “In da muke kaita kullum.�? Ya bata amsa kana taji ya fara magana da wasu a gefe. Hakan yasa ta kashe wayar ta saka hijabinta tare da d’aukan jaka ta saka duk abunda zata buk’ata a ciki kana ta fita daga gidan. Sai dai minti biyar da fitanta da dawo ta d’auki T-shirt d’in Haydar da ta d’auko daga sashensa ta manna a fuskarta ta k’ara fita. Ummii da jikin nata yayi sauk’i aka sallameta a ranar suka koma gida har da Laila wacce idan ta samu sarari sai ta kira layin Haydar wanda har lokacin a kashe take jinta. Bayan sun koma gida Mas’ud ya tafi ya bar Laila na kula da Ammi kafin Ya Madu ya dawo daga tafiyar da yayi shi da uwargidansa wacce dama ita ke kula da Ummiin. “Ummii meya faru ne ciwonki ya tashi?�? “Allah ba zai jarabci bawansa da cuta ba sai da dalili?�? Ta mayar mata da amsa cikin tambaya tana kwanciya akan gadonta da taimakon Lailan. “Naga wai sai ranki ya 6aci ne ko kuma kinga abunda bai miki ba.�? “Laila tunda tace babu komai ki bar maganar kawai, tunda ta samu lafiya Alhamdulillah. Nima zan wuce gida, idan Ya Madu ya dawo ki kirani ki fad’a mini.�? Fad’in Yayarta Ajidde wacce ke shirin tafiya. “Shikenan.�? Da haka Ajidde ta musu sallama ta barsu zaune su kad’ai basa magana. Dama dangantakar dake tsakaninsu yana da rauni fiye da tsakanin Ummii da sauran ‘yayanta. Sai gab da magriba sannan su Ya Madu suka dawo wanda kai tsaye sashen Ummii suka shigo a lokacin da Laila ke tambayar Ummii, “Tun kwanciyarki asibiti banga amaryar Ya Madu ba, kuma naga da ita suka barku a gidan da kuma yara. Bata nan ne?�? Ummii bata kula Laila ba illa k’ok’arin amsa sallamar Madu ta take yi duk da cewa muryarta bata fitowa sosai. Har cikin d’akin Madu ya shigo ya tsugunna a gefen gadon yana tambayarta lafiyar jikinta. Nan take Ummii ta fara hawaye wanda yasa hankalinsa ya tashi yana tambayarta meya sameta. Shi d’in ma bata fad’a mishi abunda yake damunta ba amma kalamansa yasa ta sauk’o ta daina hawayen kana ta juya musu baya alamar bata son damuwa. Laila dake tsaye a can gefe tare da Uwargidan Madu suna ganin komai ta bud’e bakinta ta gaishe da Yayan nata. Bai amsa ba kamar yanda tayi tsammani domin tun bayan aurenta da Haydar ya daina mata magana ya kuma daina amsa gaisuwarta. A take taji kamar ba’a buk’atarta a gurin, ita da mahaifiyarta amma tsakaninsu babu shak’uwan dake tsakanin d’a da mahaifiyarsa. Meyasa ita hakan ya kasance da ita? Sallama ta musu ta fita tana jin duniyar ta mata zafi domin a yanzu ta rasa tudun dafawa ga damuwa sun taru sun mata yawa. Bayan rashin Abul da halin Ummii yanzu kuma ya had’u da cewa Haydar ma na fushi da ita wanda a yanzu ta gane kashe wayar yayi don kar ta nemeshi. Mas’ud ne abokinta kuma mai taimaka mata a irin wad’annan yanayin da take shiga, to shima yanzu yayi aure wanda bai kamata da k’ara masa damuwa akan na iyalinshi ba. Ina zata yi? Wa zata samu suyi magana? Tana shiga motarta ta kama hanyar gida, sai dai kafin ta isa ta canja akalar motarta ta kama hanyar gidan Ammi wacce take tsammanin ita ce kad’ai zata iya magana da ita taji sauk’in abunda take ji a zuciyarta. A bakin k’ofar gidan tayi parking kana ta fito hannunta d’auke da kayan lambun da ta tsaya ta sayawa Ammi. Da sallamarta ta shiga gidan ta samu Ammi na sallah Magriba. Abun hannunta ta ajiye kana itama ta d’auki buta ta kewaya band’aki ta fito. Tana cikin alwalan tana tunanin mijinta taji muryar Ammi daga can gefen da take. “Hajiya kune a gidan namu?�? Murmushi Laila tayi kana ta maida idonta kanta tace, “Wallahi kuwa Ammi.�? “Marhaban sannunki da zuwa.�? Ta fad’i hakan tana tashi tsaye ta d’auko mata tabarma da sallaya a d’akinta zata shimfid’a mata. Ganin haka yasa Laila tayi saurin isa gurinta ta kar6a ta shimfid’a da kanta dama ta gama alwalar. Sai da Laila tayi sallah sannan ta gaishe da Ammi wacce ke jingine da bangon d’akinta tana kallon Lailan. Bayan sun gama gaisawa Ammi ke cewa, “Ali kuma sai yayi tafiya Abuja? Yau da sassafe ya shigo ya mini sallama tare da fad’a mini tafiyar da zai yi.�?“Wallahi kuwa.�? Fad’in Laila tana sunkuyar da kanta k’asa domin bata so Ammi ta mata wata tambaya akan Haydar ta kasa bata amsa har ta fahimci halin da suke ciki. “Alhamdulillah tunda sun isa lafiya. Munyi waya d’azu bayan sun isa.�? Ajiyar zuciya Laila ta sauk’e domin an amsa mata tambayarta ba tare data furta ba. Wai duk dama cewa tunanin abunda ya faru da uban ‘yayanta yayi sauk’i a zuciyarta dalilin tsawon lokacin da aka d’auka, bai hanata jin d’arr ba matuk’ar wani nata yace zai yi tafiya. Basu jima ba Ammi ta kawo musu tuwo wanda Laila tace ta k’oshi, Ammi bata matsa mata ba ta kawar da abincin gefe suka cigaba da hiransu wanda jefi-jefi suna sako maganar Haydar wanda Laila ke jin dad’in hakan kwarai. Sai bayan isha Ammi tace ta koma gida kar dare ya mata a hanya tunda mijinta baya gari. Laila da bata so hakan ba ta tashi ta mata sallama amma a ranta ta ayyana zata dawo washegari domin magana da Ammi na yaye mata k’uncin da take ciki. Bayan ta koma gida ta gama abunda zata yi ciki har da kiran Ummii domin jin yanda jikinta yake, kana tayi shirin kwanciya ta jawo wayarta ta kira Haydar. ‘The number you have dialed is switch….�? Kafin matar ta k’arisa Laila har ta kashe wayar tare da jifa da ita kan gadon. Me yake nufi da zai kashe wayarsa? Fushin nashi har ya kai ya k’i yin magana da ita bayan yayi tafiya? Gyara kwanciyarta tayi kana ta kashe wutan d’akin tana jin zafin abunda Haydar ya mata. K’arar da wayarta take yi yasa tayi saurin mirginawa ta d’auka tana tunanin me zata fad’awa Haydar ya gane bai kyauta mata ba. Bak’uwar number ta gani wanda tayi saurin d’auka tace, “Salamu alaikum.�? “Mama.�? “Abul.�? Itama ta kira sunanshi wani abu kamar kibiya na sukarta a k’ahon zuciyarta. “Kina sha’aninki kin manta dani ko? Watak’ila ma murna kike yi dana tafi na baku guri ke da mijinki.�? “Allah ya shiryeka Abul, Allah ya nuna mini ranar da zaka yi hankali ka gane kanka kake cuta ba kowa ba.�? Ta fad’i hakan tana jin hawaye na taruwa a idonta ba tare data bari muryarta ta canja ya gane ba. “Zaki jima kuwa.�? Da haka ya kashe wayarsa ta bi wayar da kallo domin ya jima bai kirata ba. Sannan ta sani ko da ta kirashi bazata sameshi ba sanin kashe wayar zai yi ya kuma jefar da layin. A hankali wannan karon ta ajiye wayar abubuwan daya faru a ranar na yawo a kwanyarta, da suka mata yawa ta fara zubar hawaye tana addu’an Allah ya gyara mata rayuwarta ya yaye mata bak’in cikinta. Awannni uku da haka ta mik’e tsaye kamar wacce aka yiwa duka ta isa bakin mirrow inda ta ajiye jakar data fita dashi. Rigar Haydar data saka a ciki ta ciro kana ta shimfid’a akan pillow d’inta ta kwanta tana mamakin wannan sudden addiction d’in.

Mum Fateey 👌

Back to top button