Hausa novels

Gargadar So Chapter 2 By M Shakur

EPISODE 2Cikin muryan jinjinan ban girma DIG yace “I feel honored your excellency dahar kai tunani na in this difficult time, I have the best task force that can save Granddaughter ka Allah taimaki excellency, team of 3 ne, the tech genius, the powerhouse, saikuma the criminologist dakeda highest record na decoding, encoding, profiling and tracking kidnappers, trust me your Excellency this case is a piece of cake for Miss Hawwa!” Dasauri Dad yace “I think I’ve heard of this name Hawwa” dasauri DIG yace “you will definitely cus she’s a government asset, somehow somehow maybe takardunta ko work dinta yazo gabanka, thanks to her akai rescuing almost all our kidnapped victims dasuka zo Ecowas summit daga Washington DC” dasauri Dad yace “tabbas yanzu natuna sunan” DIG yace “yanzu dai wat will happen is, i need to bring them over suyi proper investigation and ask you people lot of questions and watch how they save Noor, 24hrs yamusu kadan inhar they gather information” dasauri Dad yace “okay but kuzo without uniform, and karkuzo da office car cus I think the kidnappers are watching movement na gidana” dasauri DIG yace “wannan ba matsala bane we will be there in an hour” ya katse wayan ijiye wayan Dad yayi kan table ya sauke ijiyan zuciya Musbahu yace “Khaleel zai yarda kuwa?” Anatse Dad yace “zaima yarda ne baida wani option, bazan folding hands ina kallonshi in pains ba”.Wayanshi yadaga yakara a kunne babu wasa akan fuskanshi yace “come to my office now” wasu maza guda biyu suna sanye da riguna da wando da tie kaman masu aikin bank sukazo wajen wani office sukai knocking kofan, suka shiga sannan aka sake knocking kofan DIG yace “come in” ahankali aka turo kofar office din, kafafunta ne suka fara lekowa cikin office din dake sanye cikin wani black cover shoe dakeda dan tudu zuwa dogon navy blue wando normal trouser length material dake jikinta zuwa wata shirt mai dogon hannu sky blue dake da stripes na white lines wanda shima bai kamata ba yakuma sauka dan yarufe bombom dinta yasauka kan cinyanta daidai tsakiya, saikuma gyale datai rolling na kashka navy blue dashi ma ya sauka yarufe kirjinta sai igiyan ID card nata data saka a wuya ID card din yasauka akan kirjinta wanda fuskanta da sunanta ke jiki, fuskanta babu kwalliya ko guda daya banda milky skin nata that is light brown in color dake sheki, ita ba fara ba and ba baka ba, sannan ba coffee ba, very light brown skin fata gareta da saura kadan yakoma fari, she’s tall about 6’0, tanada round eyes dasuke nan farare fattt ba manya ba kuma, sunada shape kaman na kifi da abun yakarama fuskanta classic v and symmetrical shape, tanada dogon karami hanci dan dass dashi, tanada small lips that are full and very pink, tanada gashin gira baki but baida fadi looking kaman tayi carving and tinting nasu nan ko batayi ba, akalla zatai 29 ko 30yrs hakanan cus she looks matured and calm, bin yan office din tayi da kallo ba yabo ba fallasa ta maida kofan tarufe sannan tazo gaban table din da DIG ke zaune yana kallonta ta saramai cikin zakakkiyar muryanta dake da dadi tace “Sir!” Dan murmushi yamata kadan yace “ease Hawwa” sauke hannun tayi tana kallonshi binsu duka ukun yayi da kallo yace “Hayatu, Abraham and Hawwa, the 3 of you are my biggest asset! I take joy and proud cewa ninai training naku kawowa this stage da kasarmu gabaki daya ke alfahari daku, they can never talk about crime solving batare da an ambato sunayenku ba sabida yanda kuke samawa kasa lafiya a sirrance, yanzu ma lokaci yazo dazaku kara baje bajintarku” yayi shiru duk suma sukai shiru suna kallonshi jan kujeran dayake kai baya yayi yamike tsaye yazagayo ta gaba inda suke yazauna akan table duk yana kallonsu yace “anyi kidnapping jikar Senate president dinmu Alhassan Mangal, yau is the 6th day datake hannu abductors dinta and she’s just 4yrs” dukansu kallonshi suke yadan sauke ijiyan zuciya yace “I don’t have full information na case din dan yanzu yanzun nan case din yazo table dina basuso suyi involving force sabida kidnappers din warned them not to kosu kashe yarinyar, but bayan sunkai 100M 2days ago har yau shiru ba kira ba yarinya yasa Excellency yabani kiran sirri” yadan sauko daga kujeran standing straight yace “team!” Atare sukace “yes Sir!” Yakallesu duka yace “you have just 24hrs to rescue that little innocent girl, Hawwa!” Anatse Hawwa tace “Yes Sir!” Yace “I trust you! But ayau I just want you to make me extremely proud banso Excellency yayi nadaman kiransu dan haka saving that little gurl is a must! Am I clear”?Gyadamai kai tayi tace “yes sir” yace “okay you have 2min to get ready kudauki kome kuke bukata meet me downstairs da motana zamu” gyadamai kai sukayi suka wuce suka fita duk yabisu da kallo wani office tabude ta shiga dudda baida wani girma chanchan but it’s still very fine and okay ga shelves da award ne suka ciccikashi, wani drawer tajawo tabude tadauki wata karamar bindinga AR-15, tabude taduba bullet sannan ta maida ta hada ta daga riganta ta daura wani gun holder sannan ta makala bindingan aciki sannan ta maida rigan ta sauke tadauki wayanta tadan tsaya tai jimm sai chan tadanna wayan yabudu babu key hotonta dawata yarinya dasuke kama sosai yarinyar na mata kiss a kumatu sannan tabude wajen calls nata tai daily number datai saving da Baba ringing daya yadaga, cikin very sweet voice dinta ahankali tace “hello Baba” cikin muryan dattawa yace “na’am Hawwa ina jinki” abu ta hadiye awuya kafin tadan rage murya tace “Baba inada wani operation dazanje bansan ko zan iya dawowa da wuri ba shine nace bari na kira na sanar dakai” shiru Baba yayi kaman bazaiyi magana ba hakan yasa tace “Baba kaji”? Daga ta dayan bangaren yace “najiki ai, banga amfanin aikin nan kina diya mace dake saki yawon banza ba, saisa gashinan kinki auruwan ma kowa, duk mazan na gudun auren irinki, ace yarinyar na neman talatin takasa auruwa, yau batanan gobe bata chan, shikenan ai, Allah kyauta, Allah bada sa’a” yana maganan ya katse wayan, zaro wayan tayi daga kunnenta tarike wayan tana kallo akai knocking tareda bude kofan atare Abraham ne rikeda vest dinta a hannunshi dake tare bindiga ya shiga jikin mutum, yace “let’s go na dauko miki vest dinki, here grab” ya wurgomata vest din, chabewa tayi tarike tana kakalo dan murmushi cus Baba yayi ruining mood dinta already tace “thanks” a hannu kawai tarike vest din tadauki wayan nata dake kan table sannan tadauki wani dark sunshade tamakala a idanu sannan tabiyoshi suka fito tare, elevator suka shiga su ukun harda Hayatu daya kaisu kasa suna zuwa suka shiga jeep din DIG, shike driving Hayatu na gaba, itada Abraham abaya suka fice bini bini Abraham na kallonta yanda take taba wayanta, shidai kawai Miss Hawwa na burgeshi, she’s super brilliant, baitaba ganin Hausa girl that is as educated as Hawwa ba, she’s just a brain box, smart ass, fearless and bold, gata she’s so charismatic and carries herself well batason raini, he wants to be her friend so bad but bata bada room yarasa mesa, kodan dagashi har Hayatu ta girmesu ne oho, he’s 26, Hayatu kuma is 27, so tsakaninsu relationship dasuke sharing is strictly professional, ahaka yana tunane tunane sukakai gaban gidan.She has been to presidential villa for wani security conference before but koshi ba’a bincika motansu hakaba kodan da official office car sukaje oho, but the way ake duba motan da some machines zaka dauka wani president din duk duniya house sukazo almost 3min suka bata sannan aka barsu suka shiga, wani irin strange feelings taji ajikinta hakan yasa ta sauke ijiyan zuciya Abraham dake gefenta yace “all good Miss Hawwa?” Gyadamai kai tayi alamun yes aka sake budemusu another gate suka shiga gidan suka cigaba da tafiya for like 3min sannan sukakai wani gate, kafin abude musu gate din suka shiga wani gida inda taga wani security sanye da suit tsaye yana jiransu ya nuna musu inda zasuyi parking specially wanda ya banbanta dasauran wajen parking din har wani guest parking space aka rubuta awajen, parking DIG yayi yafito suma suka fito, tabude bayan motan sannan ta sauke kafanta kan grass carpet dake wajen, sanyi taji yabi jikinta amman tadaure tafito tanabin ko’ina da kallo batare data zare glasses nata daga kan idanunta ba security ya gaida da DIG yace “Excellency yace namuku iso to his office” yana maganan yayi gaba duk suka bishi abaya har zuwa mahaukacin office din duk aka basu wajen zama suka zazzauna.

Back to top button