Hausa novels

Mijin Malama Page 10 By Nimcy Sarauta

*🌈MIJIN MALAMA🌈*


Nimcyluv sarauta
*10……*

Masu Arewabooks follow my account👇🏾 akwai gift ga wanda suka fi kowa share da comments acan

https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv

Abraham ya zube gaban Uncle Isma’il ya ce “I want to convert to Islam, I want to become a Muslim, how much will I give” Uncle Isma’il da mamaki yake kallon Abraham ɗin, Yaushe ya dawo? Mene ya same shi yaga jikinsa da wannan raunin? Mene ya ja hankalin shi zuwa ga addinin Musulunci duk da sauri irin na mahaifinsa Denial, duk da kasancewar Kakansa Pasto a church ɗin da tafi ko wacce girma.
“Lafiyarka ɗaya? Mene yaja hankalinka zuwa ga Musulunci? Yaushe ka dawo?” Uncle Isma’il ya jerawa Abraham tambayoyin cike da mamakin domin kansa ya riga cushe. Abraham ya kasa cewa komai domin bashi da kalaman da za su iya fahimtar da Uncle halin da yake ciki,
But speaking the truth, he wants to be a complete, pure Muslim. Na gartaccen mutum mai tsafta. Al’amarin daya wakana akan idanunsa sun bashi malam tsoro da tu’ajujji wani abu mai sunun tsoro Abraham bai sani ba. that is the first way he will take to surprise Majeederh.
Uncle ya kalli ko’ina kafin ya tattausa murya ya ce
“Ka bari zuwa gobe sai muyi magana mu shiga ciki” Sai a lokacin cikin gurɓatacciyar Hausar shi ya ce “Uncly, Jee”

Also Download Wace ce ita (Who was she) Hausa Novel Complete Document

“Jee?” Uncle Isma’il ya maimaita kenan bai mance da ita ba?
“Abraham Maminka Majeederh bamu san inda take ba, we lost her” Ya faɗa cikin damuwa. Abraham ya ɗago kansa tare da saka hannunsa ya dafa cinyoyin Uncle Isma’il ya ce
“She slapped me, insulted me, said she hates me, babu ni rayuwarta abada” Baki sake Uncle Isma’il ya ce
“Ita Majeederh? Wait a ina ma ka ganta? Mene ya sanya harta mareka?” Ya ɗaga gajiyayyun idanunsa wanda babu ladama ko kaɗan a cikin su ya ce “Tana wajan Governor na garin, his prvt house” Uncle Isma’il ya dinga jinjina kai yana tunanin abinda ya kai Majeederh wajan His Excellency, mutum mai tsananin karamci da tausayin naƙasa da shi Al’ummar shi yana da tabbacin ba zai taɓa cutar da Majeederh ba. Ya duba agogon hannunsa yaga lokacin ya ja, gashi ance ma baya ƙasar yana Cameron. “dare ya riga da ya yi, gashi His Excellency ɗin ma baya ƙasar da nayi masa waya ina so contact nasa kai tsaye ba shamaki”
“Liar, yana nan infact shi ya sa a kai ni prison, a gabansa Jee ta mareni” Uncle ya yi shiru yana son fahimtar wani abu kafin ya ce “Me kayi mata?” Abraham ya ce
“Wai don na ce ni na bata ciki, am the father of her son, am the one who raped her, na rantse” maganganun Abraham su kayiwa Uncle girma a kunne ya fahimci akwai buƙatar neman Majeederh domin bai taɓa ji Abraham ya yi ƙarya ba, He is a man who stands by his words.
Uncle Isma’il ya ce “Amma me ya sa kayi haka Maminka ce fa?” Ya haɗe rai sosai yana ɓata fuska ya ce “Ni yanzu ban son Mamin, she’s my wife to be pls Uncle I need your help, Dadyna baya understanding my feelings, Jee bata duba feelings nawa” ya faɗa cikin damuwa da murya mai rauni.. “Ka aikata babban kuskure acikin tsarin addininmu na Islam, wanda ya sha bamban da naku Addinin na Christianity mabiya Yesu, a tsarin dokokin Muslunci role and regulations ga duk saurayin daya aikata Fyaɗe bulala ake masa, mai aure kuma jefe shi ake, wannan abin ƙazanta ce ma fi muni, ba zan goyi bayan haka ba Abraham, Maminka?”

Also Download Nurul Kalb Hausa Novel Complete Document

Uncle ya faɗa rai ɓace. Abraham was just looking into uncle’s eye’s ya kasa bambance fari da baƙi, yana son fahimtar mene abin kuskure a tarayya da mace? Koda yake shi addinin musulunci ya sha bamban da sauran, komai nasu sai sun kawo hujja, A strong argument.
Ya dubi Uncle a lokacin baka iya gane mai idanun Bad boy ke faɗa sbd launin da suka sauya a taushashe ya ce.
“…. I Just gave her i kissed, i Little kissed on her neck, duk abinda ya faru it was a mistake”
“Mistake?” Uncle asked.
“I…. I… I am sorry Uncle”
Was the first time daya bawa wani haƙuri saɓanin Jee, yana mata abu immediately yake cewa “Sorry Malumana”
“Help” “Sai nayi bincike, idan ya tabbata dole ka amshi hukuncin Islama, bi ma’ana bulala, kuma na kafa maka sharuɗa”
“Accepted alrdy”
Uncle ya ce “Tashi muje, zan kira Dr ya duba ka”
Sai a lokacin ƙarfi yazo masa, da ƙyar ya miƙe kansa na juyawa. Cikin gidan shiru kowa ya yi barci Uncle ya nunawa Abraham wani bedroom, ya shiga ya haɗa masa warm water kana ya ɗakko masa wata jallabiya tare da barin bedroom. A daren Uncle ya kira Dr, kana ya kira Uncle Bello akan yana neman sa gobe by 11Am, daga nan ya turawa Abbu message akan umarni yake bashi gobe yazo yana nemansa.
Daga nan zama ya yi tare da buɗe system nasa ya shiga Gmail ya turawa zuwa ga email ɗin Governor Abu-turab Alƙasim na sirri akan yana buƙatar magana tare da full address da muhimmacinsa wajan Malama Majeederh Abdul’aziz Khan.
Washegari Abraham na zaune watching TV daga shi sai 3gauter da Armless mara nauyi wacce ta haska baƙar fatar jikinsa, gashin kansa sai ya yi kamar an gyara shi yadda ya cukurkuɗe kamar indomie, duk wajan ciwon anyi dressing nasa, idanunsa wanda suke always a haka He is so genius, and so romantic. Kana ganinsa kasan bashi da haƙuri zafin rai da taurin kansa, musamman physquie. Ba komai yake ɗauka ya zuba a brain nasa ba, amma ƙwaƙwalwarsa ta kasa mance ranar, komai ya faru cikin tsautsayi. Unconscious happenings, It is still fresh in his mind, he remembers it every day.

Also Download ABBAN SOJOJI BOOK 2 Hausa Novel Complete Document

Tsaki ya ja, babu abinda yake so a yanzu kamar barasa ita ce kawai zata ɗauke masa nauyin zuciyarsa.
Jawaad ne ya shiga hannunsa zube cikin Aljihu sai Sona dake bayansa tana cewa “Yaya Jawaad ka fiya ruwa, wallahi ko matarka sai tayi da gaske zata ci kuɗinka, ni mamakin ƴan matan da suke nace maka nake tunda ba komai za su samu ba” Jawaad ya yi murmushi yana zama kusa da Abraham ya ce “Yarinya ai mu akwai kalaman soyayya, mun san ta kan mace da kalma ɗaya take nake sace zuciya, kuɗi kuma ai Abba na zuba miki acct” Sona ta ce “Ni dai ba haka bros kewa sister’s na su ba”
“A’a, ba zan goyi bayan ɓarnatar da kuɗi ba, bayan baku san ciwonsa ba” Was abinda ta ce.
“To don Allah ka bani, just 50k” “Yarinya ko ƙwandala, na aure nake haɗawa” Ta kumbura fuska duk abinda suke Abraham na jin su..
“Yaa Abraham kai bani”
Ya buɗe idanunsa ya kalli Sona, kallon ɗaya kafin ya lumshe idanu ya ce
“Nawa?” “50k”
“Done” ta buga tsalle ta ce “Yes, thank you Yaa Abraham” Jawaad ya kalli Abraham sosai ya ce “Ni ma Yaa Abraham ka bani na siyi new car”
Abraham ya watsa masa harara ya ce “Bana ƙarawa mai…..”
Ya yi shiru yana zaro idanu alamar bai san ƙarshen karin maganar ba. Jawaad ya buga dariya ya ce “Ba a ƙarawa mai ƙarfi, ƙarfi Anji Hausa fa, wai bayan kayi hijara garin Katsinawa ka je ka koyo mana wasa”
“Mene ga hausa, Sometimes there is difficulty in pronouncing some words”
“Ni dai a bani kuɗin” ya juya ya kalleta ya yi shiru sai kuma ya miƙe yana riƙe kansa he’s trying to recovering something, kallonsa suke gabaɗaya ya yi ta zaga ɗakin ya haɗa zufa sosai idanunsa sukai jajir da sauri ya ce
“Joshua” Ya ƙara yin shiru for some seconds kana ya ce “Call this phone” Sona ta ɗauki wayarta ya shiga faɗa cikin sauri in a low voice.
Yana gama faɗa ta danna call, ringing ɗin farko Joshua ya ɗauka yana faɗin.
“Hey, who’s on the line?”
Sona ta miƙawa Abraham waya ya amsa tare da sanya handsfree sbd yanayinsa ya fara juyewa, Joshua ya yi ta magana shiru can Abraham ya ce “GANG”
“Bad boy” Joshua ya faɗa miƙewa da sauri yana cewa “Bad boy where are you? Gang team need you”
“Ka haɗa mini Gang team, right now” ya fesar da numfashi cikin murya mai sanyi ya ce “I’ll send you a acct number, kayi dropping 500k ciki” daga nan yare suka sauya kana ya kashe wayar ya ce Sona ta tura acct number. Daga nan kuma ya fara losing mind.

Download>>> Bintu Diyar Bayi Ce Book 1 Complete Document

Uncle Isma’il ya kalli Abraham ya ce “Go and change your dress, before nan let’s talk”
Abraham ya dai kalli Uncle bai fiya gane wasu kalaman ba ya ce.
“Faɗa mini duk abinda ya faru a can gidan His Excellency” ran Abraham ya ɓaci ya ji tamkar yanzu abin ke faruwa in brief ya faɗawa Uncle Isma’il everything. Ya jinjina kai ya ce.
“Ina son ka saurara, ba zanwa Majeederh dole ta so ka kota aureka ba, kuma ina bayan tayi maka hukunci daidai da laifukanka.”
“….No please Uncle, I’ll die idan ba Malumana”
“Kasan mene matsalarka ta farko, kai ba musulmi ba, ga team na ƴan iska, ga shan barasa, babu halarci a aurenka da Majeederh, amma I’ll Adviser you duk da cewa akwai wahala ta samun haɗin kanta, ka zama mutumin ƙwarai kuma ka zauna a gidana har sai lokacin dana amince da gyaruwarka, Kai Kiristan ita Musulma, kuma babbar malama wacce ta girmemaka, ta baka zatarar shekaru goma sha biyar Abraham,ta raineka ta ci kashi da fitsarinka akwai girma, akwai nauyi ko da ace kai Musulmi ne Majeederh nasa izza da kame kai bata ɗaukan raini, babu shakka ko auren akai zata rainaka”.
Abraham ya ce “Raini? A sbd ba zan iya bata ciki ba? Ina da ishasshiyar lafiya inma yara 100 zan bata cikin dare ɗaya….,”
“Stop it, what noises ni wan mahaifin Majeederh ka ke faɗawa haka ba kunya? To ɗabi’ata data Majeederh data Addinin musulunci tasha bamban da taku, akwai alkunya tsakanin surukai”
“Mene surukai Uncle?” Shi Abraham bai ɗauka laifi ya yi ba ya kuma kasa gane mene kuskuren shi a cikin maganarsa. Ya suruna cikin raunatacciyar murya ya ce.
“I am sorry, amma mene ya sa zata raina ni wallahi kullum zan iya bata ciki.,,”
“Get out Abraham Denial David, out tunda ba zaka nutsu ba” “Ka yafe, forgive me please, zan zama Muslunci ka taimaka” Uncle Isma’il ya ce “Mene ya ja ra’ayinka? Bayan iyayenka basa su”
“Shi ne first and simple way da zai mallaka mini Malumana” Uncle ya girgiza kai ya ce
“Ka fara tsarkake niyyarka, ba a taɓa musulunta sbd wani dalili ko neman yardar wani, ka musulunta sbd ka yarda addinin Musulunci shi ne addinin na gaskiya, ka musulunta sbd ka yarda da Allah da Manzonsa Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, ka yarda da su babu abokin tarayya, ka mance littafin injila ka ɗauki Alqur’ani da hannu bibbiyu”
“Ta zan yarda?” “Ka fara nutsuwa kasan mene ya sa ka ke son Musuluncin yanzu ka je ka shirya, kuma babu kai babu yiwa Majeederh magana, balle uzzura mata ko kai hannu zuwa jikinta yadda ta ce ka barta ta tsaneka to barta, ka ƙaura cewa ganinta, yanzu ne za ka yi faɗa, fight for your love, ka je bata da bazata, bazata ta sabon sauyin da kayi ka zama tsarkake” Abraham ya yi shiru yana tunanin ta ina zai iya all this, ba zai iya haɗa waje da Majeederh ba tare daya taɓa ta ba. Ya miƙe tare da shigewa bedroom.

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

Babban parlourn a cike yake, Uncle Isma’il, Uncle Bello, Abbu, Mami. Gefe guda kuma Bar Aliyu Sufyan Alhassan ne zaune cikin wani lallausan yadi, Sai Hajia da Papa iyayen Zaki. Daga ɗaya barin Masu garin ne bakiɗaya, Governor Abu-turab Alƙasim da Mama sai Haseenatou wacce ta ƙarasu. Abu-turab cikin wata dakakkiyar shadda fara tas sai ɗaukan Idanu take ɗinkin jamper da babbar riga, he was so looking anger na jin meke faruwa. Daga tsakiya Malama Majeederh ce zaune cikin wata blue black ɗin Abaya mai kyau tayi rolling kanta gefen fuskarta a rufe hannunta riƙe da Khalil.
A inda take zaune take jiyo ƙamshin perfume ɗin da har abada ba zata mance ba. Abinda bata sani ba dab da ita Oga Abraham Daniel David ne zaune cikin wani milk ɗin voyel mai manyan zane ana iya hango faffaɗan ƙirjinsa mai ɗauke da zanan tattoo kansa kwance luff yana ƙyalli sai sabga ƙamshin Boadicea The Victorious, idanunsa kafe a kanta babu ko ƙiftawa. Uncle Isma’il ya yi sallama kana yasa aka yi addu’a. Ya gyara zama ya ce.
“Bincike da result ya tabbatar Khalil jinin Abraham ne” a kusan tare Governor Abu-turab da Bar Aliyu suka ce..
“Ƙarya yake ɗana ne” Abraham ya lumshe idanunsa ya buɗe ya ce “Babu me zarar yi ma Jee ciki kaf cikin ku, I’m lucky ni me sa a ne” duk suka kalli Abraham Abbu kuma ji ya yi kamar ya shaƙe yaron.
“Ba musu za kuyi nan ba, kuna son rusa mini ƴar fahimtar da nayi, His Excellency, Barrister, Abraham na yarda duk kuna son Majeederh, shawara ɗaya zan baku Majeederh ba budurwa ba ce ƙaddara ta faɗa mata” Zaki ya ce “Zan zauna da ita haka”
Uncle ya girgiza kai ya ce “Kuyi faɗa, faɗa na samun soyayyar Majeederh zan ga waye MIJIN MALAMA, zanga mai zarrar sace zuciyarta, Ɗa dai na Abraham ne, ban san ya akayi aka samu cikin ba wanda gabaɗaya yanzu Abraham zai bamu labari anan zamu tabbatar da gaskiyar shi”.
“Idan tana da burin dawowa gidana to ta ɗauki shegen yaron nan mai gadon tsiya, wanda ya zo da ƙazanta zuwa gidan marayu, kuma ki zaɓi Abu-turab matsayin mijinki shi ne ya dace dake” lokacin guda Majeederh da Abraham da Aliyu suka kalli Abbu banda Abu-turab daya sauke wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya.
“Abbu gidan marayu, ni na haifeshi ina raye kuma zan kai shi gidan marayu?” “Idan kin yarda ni ne ubanki, ni ke da hakƙin zaɓa miki miji” ta runtse Idanunta zuciyarta na bugawa bata san lokacin da ta ce. “Na amince, na amince Abbu albarkar ka nake nema” idanun Abraham kamar za su faɗo. “You’re liar, ki auri wani,ni kuma na ci gaba da tarayya dake kina haifar shegu, ba zan barki ki zauna lafiya da wanda kika aura ba” tayi masa banza. Abbu ya kalli Abu-turab ya ce “Idan ka shirya kawo sadaki yanzu a ɗaura auren ka tafi da matarka” Abu-turab ya ce “A shirye nake Abbu” Majeederh na zaune ta ji an ɗagata cak tare da yin sama da ita har jaririn hannunta kafin kowa ya yunƙura Abraham ya yi waje da Majeederh yana zuwa ya saka key ya buɗe ƙofar mota ya cilla Majeederh ciki idanunsa rufe ƙwaƙwalwar taɓin hankalin na motsawa “Kai Mahaukaci ne?” Ya dubeta yana sunkuyawa dab da ita ya zura mata seat blt ya ɗaurawa kansa. A karo na biyu ta sake cewa “Kai Mahaukaci ne?” Ya buɗe ido ya ce “I don’t know, amma yau zan iya bamban cewa ni mahaukaci ne or not? Domin a yau zan ƙara baki wani cikin na kwanta take a karo na biyu, daman wancan i have been drug ban san ya ki ke ba, wannan shi ne aikin hankalina, wanda zan yi na hauka ya fi wannan,zan iya tsayawa tsakiyar titi babbar mota tabi ta kanmu, me, you, and our son duk mu mutu” Majeederh ta runtse Idanunta tasan tabbas zai aikata. Da gudu Bar ya fito Abu-turab na mara masa baya, suna fitowa motar Abraham Daniel David na fice daga cikin gidan da gudu…

Click Here To Read Page 11

End of free pages
In sha Allah a nan na tsaya da free pages mu haɗu a paid grp. Yanzu zamu je asalin labari nan tsakiya ne, book1 shi ne asalin tashin hankalin littafin duk wani abu daya faru a nan ya faru. Book2 anan zamu ji yadda jaruman namu za su yi faɗa akan Majeederh.

Ɗan waye?
Ya akai sai bayan shekara biyu ta haihu?
Dashe akai mata?
Cikin Aljanu ne?
Ko Abraham, ko Abu-turab ko kuma Zakin Hajia? Wa zai ci riba.

Book1 500
Book2 500
Gabaɗaya har mu kammala littafin 1k ne. Zaka iya fara biyan kuɗin book1 kafin mu fara book2…. 6850917335 Na’ima Shu’aibu Sulaiman fidelity bank… Evidence of payment 08119237616. Zamu fara posting as soon as kun kammala payment. THANK YOU💋❤️🥰

Kafin kammalawa Wannan page ɗin gabaɗaya sadaukarwa ne ga HASEENATOU AUTAR MANYA. ELEGANT ONLINE WRITER’S, MIJIN MALAMA GRP 1,2. ALLAH YA SAKA MUKU DA ALHERI☺️🥰.

TALLAH👇🏾
Shin kuna bibiyar littafin *DAUƊAR GORA!* Wanda *HAWA__B__KUMO (REAL-SMASHER)* ke kawo maku? Wai³ this is an emotional story ever,idan ba kya bi maza ki nema ki fara kada ayi babu ke,*DAUƊAR GORA!* Labari ne dake ƙunshe da sarƙaƙiya akan ƙaddarar wata baiwar Allah *AYSHATOU AYATULLAH* wacce tayi fama da matsalar yoyon fitsari at a very young age,she really went through tsananin rayuwa,ƙiyayyar Family’n uba,kowa yana ƙyamar zama da ita,saboda larurar data sameta lokaci ɗaya,ba kuma wai dan haifeta da shi ba,ku nema ku karanta kada ayi babu ku..

DANƊANO

Kallon ƙyama Inna Tabawa matar ƙanin Babanta data kama baki kamar an yi pausing ɗinta ta bita da shi dawani murya take cewa “toh! Yau muke ganin tsiya da wasali.. Ke yanzu da girmanki gotai² sai ki saki fitsari a jikin kayanki? O’ohh! Ikon Allah.. Ni Tabawa na ga abunda ya isheni bai ishi Allah ba” ta riƙe haɓa tana sake jinjina al’amarin,kamar an cillota kuma kamar me jiran ayi da ita,Inna Larai tai wuff ta fito daga ɗaki jin maganganun da Tabawa ke faɗa ta ɗora da faɗin “ai Tabawa in faɗa maki iskanci ne da kuma ganin ta samu masu ɗaure mata,amma babu wani rashin lafiyar dake damun yarinyar nan,samun guri ne kawai.. Allah na tuba yau aka fara yin ciki? Kou a kanta aka fara haihuwa da za’a raina ma mutane hankali ace ta gamu da wani larurar dake hanata riƙe fitsari.. Zallar taɓara ce dai ke damunta,tou kuma kin san abunki da goyon kaka,babu abunda baza tayi ba da sunan larura” hawayen da suka ciko idonta tai saurin sa hannu ta goge,da sauri ta wuce za ta bar gurin,Inna Larai ta kalli yara²n gidan tace “Kaiii! Kui mata ihu kou za ta ji haushi ta dena abunda take,kui mata waƙar me fitsarin kwance ni na saku,duk wanda yayi kuma zan bashi Nera 5-5,manya kuma zan baku 20-20” ihu da tafi suka hau yi,kafin kace me ƙananan yaran gidan sun ɗauko murafen languna da ƙananun gallon suka fara kiɗa. Kamar cikin watan ramadhan lokacin tashe,haka muryoyin yara da manyan gidan masu jin haushinta babu gaira ba dalili suke tashi cikin waƙe suna faɗin “me fitsarin kwance,amalaala! Wace ce? Me fitsarin kwance.. Amalala.. Me fitsarin zaune.. Amalala.. Me fitsarin kwance!” Inna Larai tace “baku kama sunanta ba,ku faɗa ku ɗaga murya kowa yaji,idan tai zuciya gobe ta daina” kamar Inna Larai ta zugasu kuwa suka ci gaba da kiɗa suna waƙa “wace ce? Aya me fitsarin kwance,amalaala! Aya me fitsarin kwance.. Amalala.. Aya me fitsarin zaune.. Amalala.. Aya me fitsarin kwance!!” Ba waƙar da suke yi ne yafi taɓa mata zuciya ba,yanda wasu ciki ke zagayeta har suna kama mata zani suna janta,wasu na dungure mata kai shi ne abunda yafi komai sawa taji ta muzanta a idanun duniya,da wani irin sauri ta durƙushe bakin ƙofar ɗakinta,banda kuka babu abunda take kamar ranta zai fita,bata taɓa jin ta yi loosing hope ba irin yau,zuwa yanzu kam gaba ɗaya rayuwar ma ya fice mata a rai,musamman irin tozarci da wulaƙancin da take kan fuskanta daga danginta,abun yai mata yawan da ciwon zuciya yake neman kamata nan take,daga jiya zuwa yau sosai take cikin barazana/walaƙanci da tsokanarsu,har tunanin fita take kou wani uzuri ya kamata da dole zaisa ta haɗuwa da wani cikin mutanen gidan ba Baba Wada kou su Inna Asama’u ba,wani lokaci har ƙofar ɗakin ake zuwa ai mata ɗan kira…

Click Here To Read Page 11

#Za ku samu littafin DAUƊAR GORA! Na ɗaya kyauta. For 2 & 3 shi ne na kuɗi akan ₦500,SP 1k,za’a tura kuɗin ta wannan account ɗin 0060746882-Hauwa Muhammad Usman,access bank,kou a tura zuwa 8165726609 – Hauwa Usman Muhammad, Opay digital wallet. Mutanan Nijar/Mali zaku tura dala ɗari, SP jaka ɗaya, ku tura shaidarku zuwa 08165726609. Ku bi zazzafan alƙalamin #REAL-SMASHER domin samun cikakkiyar amsarku game da wannan matsala data taɓo wanda ya zama ruwan dare a ƙauyuka har da birni,labari ne mai cike da fa’idodi wanda sai kun bi za ku fahimci mene ne a cikinsa..

Back to top button