Zakuna Biyar Page 25 By Princess Teema
Muryanta har yana ɗan rawa ta ce. “Da…… Dadd…….. Daddy…. Are you okey?”…….. Ai bai san time da ya wani irin jan dogon numfashi ba. Kome ya tina kuma sai ya sassauta kallon da yake yi mata tare da cewa. “Cigaba da tambayarki”. Ya mata haka ne dan yana son sanin iya abin da ta sani kenan ko akwai wani abin. Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa. “Some of my classmate they said if you want to have sax ka yi using protection dan kada ka samu pregnant parents ɗinka and uncles ɗinka zasu hukuntaka”. Ta ɗan yi shiru tana kallon fuskansa. Watau idan ya fahimceta tana magan a kan zina, idan kuwa haka ne classmate ɗinta and roommates ɗinta suna aikatawa kenan? Room ɗinsu ɗaya da Rimsha, yasan da haka, kuma shi ya ce a haɗasu ɗaki ɗaya lokacin da ya kaita, shiyasa aka cire cikon yarinyar da take ɗakin aka canza mata room aka barwa Seraph filinta, kenan idan haka ne Rimsha ma ta taɓa yin zina?. Lokacin guda ya ji wani irin buga mashi kansa ta yi, kalaman daddyn Rimsha ne ya dawo mashi cikin kai, in da yake cewa. “Ko na mutu a yau ba zan taɓa yin danasani ba, saboda ina da Aryan, ba shakka zai kula da Rimsha tamkar shi ya haifeta, dan haka bana jin zafin cewa zan mutu in barta”. Waɗan nan sune kalaman daddynta na karshe-karshe a tsakaninsu kenan, hakika mahaifin Rimsha yana tsananin sonta tamkar ya yi mata numfashi, haka kuma yake kaunar Aryan.Tabbas Aryan ya yi iya kokarinsa a kan Rimsha, kawai baya son ganinta a kusa da shi ne saboda tana tuna mashi da mahaifiyarta, kun sa dole zai ji zafi, ku tina yadda ya shaku da daddynta, amma muguwar uwarta ta zo ta shiga tsakaninsu, ta karya mashi zuciya, ya mutu adalilinta, dole Aryan ya ji zafi, amma a bayan fage ya tsayawa Rimsha sosai, dik familyn Abba babu wanda ya tsaya a tarbiyarta kamar yadda ya tsaya mata, dik da ya tsani ganinta amma yana ƙoƙarin ganin ba nemi wani abu ta rasa ba, kuma shi ya kaita boarding school dan kada ya dinga ganin fuskarta a gidan, amma ya sanya mata matakan tsaro sosai wanda bata sani ba, kawai in da yake ne ya tsani ganinta.Hankalinsa ya yi balain tashi jin kalaman Seraphina, amma sai ya daure dan ya kara jin wasu bayanai, da kyar ya iya ce mata. “What’s next?”…….. Jujjuya idanunta sama ta ɗan yi kafin ta ce. “My roommate said that sex between ladies ya fi ladies and mens daɗi, wai idan zaku yi sex da mace ya fi, Laurat said that sex is sweet especially idan zaka yi sucking penis na boyfriend ɗinka with your mouth, and Aana tana taking wasu drugs wai dan kada ta samu pregnant idan zata bi su Robert yawon dare, to ranar da Senior ya ce in zo mu je ni da Rimsha Aana ta bamu drugs ɗin dan mu sha ni da Rimsha wai kada mu samu pregnant, wai sunan grugs ɗin family planning……….”. Ai gagara iya jura ta gama ya yi, cikin tsananin zafa ya damko dogon wutar nan nata, gabaɗaya ilahirin jikinsa tsuma yake yi, gashin dake kwance a wajen hannunsa sai da suka mimmiƙe saboda tashin hankali, gabaɗaya ya canza lokaci guda, sai wani irin huci yake. A fusace ya ce. “Kema kina aikata abin da suke yi? Kuna aikatawa ke da Rimsha? Kun taɓa aikatawa?!…” Tsabar tashin hankali da ɓacin rai maganarsa rawa take yi, zuciyarsa na harbawa da sauri-sauri, yana jin zai iya kashe director ɗin makarantar nan a yanzu da zai gansa! Lallai lokaci ya yi da IRON FIST zata yi aiki a kan gurɓatattun makarantu da malaman da basu san aikinsu ba, a basu amanar kula da yara su saki yara har ana aikata wannan abin? Dole su gyara masu zama!.Ai wani irin mahaukacin razana ta yi, ta zazzaro mashi ido tamkar kwayar zasu faɗo ƙasa, take jikinta ya soma kerma, ta gagara amsa mashi….. Wayarsa dake aljihunsa ya ciro, kunna light na wayar ya yi, pressing ɗinta yai for few seconds tare da mayarwa cikin aljihun nasa.Kara shaketa da karfi ya yi kafin ya ce. “Dikka a ina kika san wannan? Who told you that sex is sweet? And ki faɗa mun gaskiya waye ya faɗa maki dik waɗan nan abubuwa?”……. Tana girgiza kai, da kyar ta iya cewa. “Daddy a wannan video kawai na gani”. Da ɗayan hannunsa ya yi amfani wajen ɗauke mata fuska da wani gigitaccen marin da ya sanyata daina jin sautin komai na ɗan lokaci, jifa ya yi da ita a saman bed, hannu ya ɗaura a waist ɗinsa da nufin ya kwance belt ɗinsa sai ya ga ashe pj’s ce a jikinsa babu belt, ai wani irin takaici ne ya kama shi, babban tashin hankalinsa ɗaya shi ne ya san sun taɓa aikatawa ne ko basu taɓa ba? Zuciyarsa har rawa take a kan hakan, yana jin tamkar zuciyan nasa zai fasa kirjinsa ya fito waje.Zabura ta yi tana ƙoƙarin miƙewa bayan ta dawo hayyacinta daga marin da ta sha, fuskarta ya yi jajir, hannunsa sun fito ɓaro-ɓaro kwance a face ɗinta, wajen har kumbura ya yi. Ai tsabar azaba da tashin hankali hawayenta yaki fitowa, ita tashin hankali ganinsa a cikin wannan yanayi ma ya fi komai gigitata, yau ya koma face ɗin IRON FIST ɗinsa, no mutunci no tausayi, dan ji yake yi zai iya sanya kafa ya tattaketa sai ta daina motsi, kun san zuciya shegen abu ne, yau ba soyayya. Tana miƙewa a saman bed ɗin cikin zafin nama ya damki gashin kanta, janta baya ya yi tamkar zai kwantar da ita, hakan yasa ta ɗaga kai sama, sai ya sanya ɗayan hannun nasa ya damko wuyanta, ya shaƙeta da karfi tare da sake tambayarta a ina ta san waɗan nan abubuwa ba tare da ya saki wuyanta ba, yarinya na ƙoƙarin sume mashi. Ai gagara iya magana ta yi, saboda tashin hankali.”Who told you all this?!”. In a harsh way ya faɗa still bai saki wuyanta ba. Har yanzu ta gagara yin magana, kuma karya take yi, ba iya videon can bane kawai, da yake ya razanata ne yasa ta fahimci abin ba mai kyau bane shiyasa taki faɗa mashi ainahin yadda komai ya faru, yanzu ma daga labari yana neman kaita lahira ina ga kuma ya ji cewa koya mata ake yi? Ai tana ganin yau mutuwa zata yi ta bi mammy ɗinta. Ganin yadda ta razana ta gagara yin magana ne yasa ya saki wuyan nata, ransa a matuƙar ɓace ya ɗauko school bag ɗinta, zuge zip ɗin ya yi, gabaɗaya ya zazzage abin dake ciki a tsakiyar room ɗin. Ai tana ganin haka ta watsa da gudu zata yi waje, dan tasan tin da ya ɗauko jakarta shikenan ya gama ganin komai, asirinta ya tonu, kasheta kawai zai yi ta sani. Sai da kuwa tana zuwa wajen door ta samu kofar a rufe, ta yi matuƙar mamakin ganin hakan, saboda a lokacin da ya shigo ai bata ga ya rufe kofa ba, to ta ya aka yi kofar ta rufu? Ta manta da cewa gidansa ne, kuma ta manta da cewa gabaɗaya doors na gidan automated doors ne wanda da app ɗinsu na wayarsa ma kawai zai iya rufe door ɗin ba sai ya kunna computer ba ko ya je wajen control na jikin door ɗin ba, tin da yai mata tambayar farko bata amsa ba ya rufe dikka kofofin gidan, har da kofar ɗakin Madam ya rufe dan ma kada ta ce zata zo ta shiga tsakaninsu, saboda ya sha alwashin yi mata mugun duka in har bata bashi amsa ba.Hankalinta idan ya yi dubu yau ya tashi, hannu tasa ta toshe bakinta tana faman girgiza kai irin shikenan ta gama yawo yau. Shi kuwa wasu books guda biyar ciff ya zaro daga cikin littafanta da ya gama watsawa, gabaɗaya jikin covers na littafan babu kyan gani, daga lesbian book, sai sex and romance. Wanda aka rubuta how to have a nice sweet sex ya zaro daga cikin biyar ɗin. Buɗe cover ya yi, ai yana sauke kallonsa a kan page na farko bai san time ɗin da ya ɗago ya kalleta ba. Wani irin razanannen ihu ta zunduma haɗe da cewa yau ta shiga uku. A ransa ya ce daga ke har Madam yau sai na lahira ya fi ku jin daɗi, domin kuwa ita ce malamarki ta farko a gidan nan kafin school! Shi kansa school ɗin naku ba barinsa zan yi ba!.Innalillahi wa inna ilaihir rajiun ya furta a lokacin da ya fara karanta rubutun da yake farkon shafin, bayan wani hoto da mace and namiji suke kwance sirara akwai dogon note a wajen na bayani dallah-dallah yadda mace zata gamsar da namiji, irin jima’in da namiji ya fiso, yadda zasu yi dan su ji daɗi da sauransu.Tin da yake a rayuwansa, yau yana da shekaru 33 zuwa 34 a duniya bai taɓa sanin dikka wannan karatun ba, ya dai san abin da musulunci ya koyar, amma wannan kafurin tsiraran karatu bai taɓa ji ba, shi kansa sai da kwakwalwarsa ta wani irin bugawa ya ɗan ɗauke wuta, karatun tafi karfinsa wlh, dan a tsiraranta aka yi ta.Ya ilahi, wani irin tsumar da jikinsa take yi ne yasa ya yi jifa da takardun, cikin zafin nama ya nufeta yana faɗin ta faɗa mashi daga ina ta samu waɗan nan takardun dikka? Waye ya koya masu wanan mummunar aiki? Ta taɓa yi ko bata taɓa yi ba?”.Da gudu ta watsa ta nufi wajen curtains tana ihu tana faɗin. “Daddy please for give me, ba zan sake ba”……. Yana zuwa ya sa hannu zai damkota ta gudu ya damki curtain na view. Ai tsabar takaici fisgo curtain ɗin ya yi ya ɓaɓakosa daga jikinsa bango ya yi jifa da shi. Da gudu ta shiga toilet tana bashi hakuri, ta rufo kofa har da sanya key, har yanzu kuka yaki zuwa mata saboda tsananin firgita. Ai yana zuwa dukan takaici ɗaya ya yi wa toilet door ɗin, take kofar ta ruguje. Tamkar mahaukacin zaki ya zama yau. Ciki ya shiga, da gashin kanta ya damkota, ya jata har zuwa tsakiyar room ɗin. A fusace ya damki wayar tv na ɗakin, da karfi ya fisgo shi ya tsinka. Ja da baya ta fara yi zube a ƙasa tana girgiza mashi kai.Ai yana zuwa yasa kafansa ɗaya ya take kafafunta dikka biyu. Baya ji baya gani ya fara zaneta tamkar wanda aka saukewa wahayin duka. Tin tana ihu da karfi har ta fara yi a hankali alamar ta jigata, tin da yake bai taɓa dukan mace ba, sai yau a kanta ya fara, basa dukar halitta mai rauni, amma yau ta kuresa ne, dole ya daketa.Sai da ya ga ta daina motsi, wayar tvn gabaɗaya ya tsisstsinke a jikinta, ya farfasa mata jiki sosai har da jini, ga shi irin dukan haukar nan ya yi mata, bai san in da yake duka ba, zuciya ta ɗebesa kawai dukan yake yi, har a kirji sai da ya daketa, wuya da baya dik, hannunta da tasa ta kare fuskarta dik ya fasa mata. Ko da ta daina motsi ba wai ya hakura bane, jefa ya yi da ragowar wayar hannunsa, ya tsugguna a gabanta, yana wani irin huci ya fara faɗin. “Faɗa mun kin taɓa aikata ɗaya daga cikin abin da kika kirga? Waye kuma ya baki littafan nan? Waye yake koya maku dikka wannan lalata? Da wani classmates ɗin naku kuke fita yawo? Ina kuma kuke zuwa?”. Sai dai ina, bata motsi, hannu yasa ya ɗan jijjigata, nan ya fahimci suma ta yi, wani irin takaici ne ya kara turnuƙe shi. Cikin zafa ya miƙe ya nufi door, wayarsa ya fitar ya buɗe kofar, yana fita ya sake rufe kofofin gidan, kai tsaye ƙasa ya sauƙo.Motarsa ya ɗauka ya nufi gidansu. Yana zuwa bai gamasa parking da kyau ba ya fito cikin zafa. Dik wanda ya gansa yau hanya yake bashi a miliyan. Elevator ya nufa kai tsaye ya nufi cikin gidansu.Elevator na tsayawa ya fita, babu ko sallama ya faɗo cikin main parlo ɗinsu. Nan ya isko Abba, Ammie, Faryan, Hareeln sai Rimsha dake kwance jikin Abba ta tada kai da cinyansa tana danna waya. Dikkansu babu wanda bai razana da ganinsa ba, musamman Harleen da ya riga kowa ɗago ido a kansa.Cikin hanzari Rimsha ta miƙe zata gudu sama dan in baku manta ba bata zama a in da yake. Ai wani irin damka ya yi wa gashin kanta. Yana wuci ya kwashe kafafunta ta faɗi ƙasa. Kusan a tare su Abba dik suka miƙe, saboda sun san Aryan baya dukan mata, dik tsanar Rimsha da ya yi sai dai tsawa da kora ne yake shiga tsakaninsu ban da batun duka, ko su Faryan dake maza baya dukansu bare mace.Tana faɗuwa ƙasa yasa kafa ya fara tattaketa. Ihu ta fara yi tana faɗin. “Uncle ka yi hakuri”. Baiwar ALLAH dik da bata san laifin da ta yi ba, tana bashi hakuri. Dik cikin parlon babu wanda ya yi gigin nufarsa bare ya dakatar da shi, sai Abba ne ya yi ta mazan cewa. “Aryan lafiyarka kuwa yau? Ko ka fara shaye-shaye ne?”. Ai ina bai kula kowa ba, kai tsaye ya nufi wajen robar wayar da ta haɗa da switch da ya yi connecting light. Ɓanɓako robar ya yi, da karfi ya fincikosa, ya sanya karfi ya zaro wayar dake ciki, ya tsinkota ya nufo Rimsha. Ai tana ganin ya nufota ta kurma ihu tare da miƙewa, ta watsa da gudu ta yi sama. Ai da gudun gaske ya bi bayanta, room ɗinta ta shiga har da sanya key. Aikuwa yana zuwa duka ɗaya ya yi wa kofar ya rugujeta. Da gudu ta ruga zata nufi toilet, taku ɗaya ya yi ya damki gashin kanta. Janta ƙasa ya yi, ya take kafafunta yadda ya yiwa Seraphina, tsakaninsa da ALLAH ya fara zuba mata wannan wayar wutan, yadda yake dukanta ma ya ninka na Seraphina sau biyu.Ba komai yasa ya yi hakan ba kuma face ita Rimsha ai musulma ce, me bata sani ba? Bata san lesbian haramun bane? Bugu da kari ta fi Seraphina shekaru, yakamata ace idan Seraph tana yi ta tsawatar mata ne ma ba ace tare suka san komai ba! Seraph ba musulma bace, amma idan baku manta ba na ce maku Dr Hushaima banbancinta da musulmai rashin sallanta ne kawai, so haka ita ma Seraph, ta iya addu’a, ta iya karanta wasu surorin na Alqur’ani mai girma dik da bata san ma’anarsu ba, kuma tana tsananin kaunar Annabi Muhammad, musamman da mammynta ta faɗa mata cewa Muhammad sunan kakanta ne, ta kara son sunan sosai, kullum tana cewa tana son ganin fiyayyen halitta, saboda mammy ta ce mata sai mutanen kirki masu daraja ne suke ganinsa.Dan haka Rimsha ta fi Seraphina sanin komai, bai kamata ace ita ta yi wannan abin ba, musamman ita da ta samu tarbiyar uwa watau Ammie, gidan Abba ai gidan tarbiya ce, amma ace ta aikata haka, ai dole ta daku sosai. Baya ji baya gani dukanta kawai yake yi, unexpected daga bayansa ya ji an rikesa, yau dik rashin imanin Harleen da tsanar da yake yi wa Rimsha sai da ya tausaya mata ya tinkari yayan nasa zai karɓeta, dan shi da yake namiji ma ba iya jure dukan Aryan zai yi ba, suna yara sau ɗaya ya taɓa dukansa har suma ya yi.Kankame shi Harleen ya yi yana rokonsa da ya kyaleta haka nan ya isa. Ai cikin fushi ya hankaɗe Harleen ya yi baya-baya ya bugu da Abba suka yi baya zasu faɗi Faryan ya tari Abba. A fusace Aryan ya ce. “Dik wanda ya sake matsowa nan sai na kashe shi!”. Yana wani irin huci ya faɗa. Ihu Rimsha take yi tamkar maƙoshinta zai fashe, ta daku iya dakuwa ba tare da tasan shin a kan me ma ake jibgarta ba. Daga bayansa aka rike wayar wutar, a fusace ya juya da sufin kaiwa wanda ya rike ɗin duka. 4 eyes suka yi da Ammie, bata bari ya yi wani motsi ba ta ɗaukesa da wani gigitaccen marin da ya sanya shi ɗan ɗauke wuta……. “Ka haukace ne? Ko wani kwayan kasha? Kasheta zaka yi ne?!”……. Cikin tsawa ta faɗa alamar ranta ya kai kolokuwar ɓaci. Sake mata wayar ya yi tare da juyawa, cikin fushi ya nufi door, a lokacin Faryan da Harleen sun fita da Abban da numfashinsa yake ƙoƙarin ɗaukewa, su dik a tinaninsu tsanar da Aryan ya yi wa Rimsha yasa yake yi mata wannan duka, shiyasa dik suka tashi hankulansu.Waje ya fito da sauri har yana haɗawa da gudu tamkar zai tashi sama. Ƙasa ya sauƙo, motarsa ya shiga, da gudu ya tada ya bar gidan, dan in ya tsaya billahil lazi zai iya haɗawa da Ammie ɗin ma. Kan Rimsha Ammie ta yi, dik ta yi laushi, ko motsin kirki bata yi baiwar ALLAH. Ɗagota Ammie ta yi ta rungume a jikinta, ita ma dik ya farfashe mata jiki da bulala har da jini kamar Seraph. Faryan Ammie ta kira tare da bashi umarnin ya ɗauketa sai hospital da gaggawa. Ai da sauri ya ɗauketa babu ɓata lokaci, dan numfashinta ɗaukewa yake yi ya sake dawowa. Kai tsaye CPH ya wuce da ita dan a cetota. Ammie kuma ta nufi room ɗin Abba dan su tattauna wannan matsala. E kam akwai matsala sosai fa. To mu je wajen team DOL, watakila kafin mu dawo su Rimsha sun samu farfaɗowa, ko ita Seraph waye zai kaita asibitin? Ga shi ya rufeta a ɗaki! Ya kuma fita cikin fushi saboda marin da Ammie tai mashi, ko ina ya nufa? Fatana ma kada ya je ya yi haɗari a irin wannan yanayi. —————————–🔥DOL.Wasa-wasa kwanaki uku suka shuɗe babu su Lion babu labarinsu, domin kuwa bluetooth da suka sanya ma dan samun infamation ma ya yi disconnected, su Arya sun daina jiyo motsinsu, hakan ba karamin gigitasu ya yi ba, dikkansu sun shiga damuwa, V har da kuka, ita kuwa Arya a fili zaku ga tamkar bata damu ba, amma a cikin zuciyarta da sunan wannan my sterious ɗin nata take wuni take kwana, dik ta damu, ko abinci bata ci, ga wayoginsu a sansanin basu tafi da shi ba.Arya ce ta fito daga cikin tantinsu sanye cikin uniform ɗinta, fuskarta har ya ɗan rame, bata cin abinci sosai, bata da natsuwa, da daddare kwana take yi manne da laptop ɗinta a kusa da ita, komai ƙanƙantar ƙara ta ji sai ta duba ta ga ko su Leo ne, ga shi a garin musayar wuta sun harbe drone ɗin da ta tura masu. Ta yi ƙoƙarin tura wani amma ta gagara kama ainahin saitin in da suke, yanzu kwanaki uku kenan basu san a wani hali suke a ciki ba.Dik suna zaune jigum-jigum, Angelina dai ta sanya bluetooth a kunne tana sauraran kiɗa, wani lokaci ta taka rawa, idan ta gaji ta zauna. Gajiya da zama a cikin ɗaki Arya ta yi, dan tana kara shiga tashin hankali da damuwa ne. Waje ta fito bayan ta ɗauki ɗan karamin pistol da aka basu dan kare kansu. Kai tsaye wajen kogin ranar ta nufa, tana tafiya tana ƴan waige-waige, tana jin kamar alamar motsin wani abin ne a bayanta, tana jin kamar dai ana biyota, idan kuma ta juya sai a ɓuya ne yasa ta fara tafiya slowly. Sai da ta isa dab kogin, da karfi ta juyo tare da ɗaura hannunta a saman pistol gun ɗin nata, ta yi readyn koma menene ta gani zata harbesa ne. Ga manakinta sai bata ga kowa ba. A matsayinta na jami’a sai ta yi amfani da kwakwalwarta, ta motsa tamkar ta juya tare da rungumo hannayenta a kirji. Aikuwa tana motsawa kamar ta juya sai ga mai binta a baya ɗin ta bayyana, daga bayan wata bishiya katuwa ta fito. Ai wani irin razana Arya ta yi ganin yarinyar, na faɗa maku yarinyar kyakkyawa ce sosai, ga idanunta manya-manya fafare tas. To yau gashin kanta a watse yake, ya zubo mata ta gaba har baya, kuma gashin nata yana da mugun tsawo, dan ya wuci mazaunanta sosai, kuma yarinya ce ƙarama sosai.A farko da Arya ta ga motsi a bayan bishiya ana ƙoƙarin fitowa har ta zaro bindigarta, amma ganin yarinyar yasa ta mayar da bindigar bayan ta dawo daidai daga razanar da ta yi. Ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗan kyafta idanunta dan ta tabbatar ba almara bace. Yau yarinyar yadda kuka san aljana ko mahaukaciya haka ta bayyanar mata. Dik da ta ji tsoron yarinyar, amma hakan bai hanata takawa a hankali ta nufi in da yarinyar take ba. Shiru yarinyar ta tsaya bata motsa ba har Arya ta iso in da take.Durkusawa a gabanta ta yi tare da riko hannunta, cikin harshen turanci ta tambayeta yau kuma me take so?. Kwace hannunta ta yi tare da nuna mata alamar yunwa take ji, abinci take son ci. Ajiyar zuciya Arya ta sauke, miƙewa ta yi tare da kama hannunta suka nufi wajen sansaninsu. Ai tana isa da ita wajen da gudu su Angelina suka yi kanta suna faɗin a ina Arya ta samo kyakkyawar yarinya haka? Kamar aljana, V mai kuka tuni ta goge hawayen, a gaban yarinyar ta tsaya, sai kuma ta ce. “Arya wannan yarinyar ta yi kama da commander Nirash, ta wani gefen kuma sai naga kamar Romeo ɗina, kamar suna kama, ko dan ina kewansa ne?”. Angelina ce ta ce. “No da sir Nirash take kama”……. Siririn tsaki Arya ta ja tare da wucewa cikin ɗaki, biscuits da wani ɗan ƙaramin kwalin drink ta ɗauko, bata amsawa kowa ba ta zo ta kama hannun yarinyar, a saman wani dutse da Manassa ta ajiye a wajen kofar tantinsun dan zama ta zauna tare da zaunar da yarinyar a ƙasa. Biscuits ɗin ta buɗe ta miƙa mata, ai da karfi yarinyar ta kwace biscuit ɗin har sai da Arya ta razana, dannawa a baki ta yi har da laidar tana kara zazzare masu idanu. Dikkansu sun tsorata musamman Manassa da dama bata wani yarda da yarinyar ba. Zuba mata ido suka yi suna kallon yadda take danna biscuit ɗin a baki, da alama yunwa yana neman kasheta ne. Ganin zata ci har da ledar ne yasa V ta yi gaggawar sanya hannu zata kwace ledar, ja da baya yarinyar ta yi ta hanata tana cigaba da danna shi a baki, ta cika kumatu tap tana kara zaro dara-daran idanunta masu kalar sanyin nan, ita ma jade eyes gareta. Wani irin damƙa Arya ta kaiwa hannun yarinyar, tana ƙoƙarin kwacewa ta hanata tare da sanya ɗayar hannunta ta zare ledar biscuit ɗin kafin ta saketa. Zabura yarinyar ta yi zata kwace ledar daga hannun Arya, miƙawa V Arya ɗin ta yi tare da cewa ta jefar da shi. Da sauri V ta miƙe da shi ta je ta jefar ta dawo. Yarinyar tana ƙoƙarin zabura ta bi bayan V sai ta kware ta fara tari. Da sauri Arya ta buɗe drink da ta ɗauko mata, a natse ta kai mata saitin bakinta. Da karfi yarinyar ta kwace ta sanya baki, bata ita sha daidai ba, rabi na zuba a ƙasa rabi na bin bakinta. Ƙoƙarin gyara mata Angelina ta yi, sai dai ina, ta ja da baya dan a tinaninta kwacewa zasu yi.Arya da bata iya jurar hakan ne ta damketa, ta matseta ta gyara mata. Ai tin da ta kafa baki sai da ta shanye tas sannan ta cire. Mamaki ne ya kamasu, Arya ta ce. “Mu kara maki?”. ….. Bata san me suka ce ba, sai kallonsu kawai take yi. Miƙewa V ta yi ta ɗauko mata wani biscuit ɗin.Yarinyar tana gani ta miƙe ta nufi V zata kwace, ita babu ruwanta da kakin dake jikinsu, bata san wani abu wai soja ba. Riketa Arya ta yi gam tare da cewa V ta fasa mata biscuit ɗin ta zare ledar…….. Wani irin ihu ta kurma saboda rike da Arya ta yi, tana ƙoƙarin kwace kanta, ita dai a barta ta isa ga biscuit ɗin. Arya bata saketa ba sai da V ta fasa mata shi. Ana bata ta hau dannawa a baki. Ganin haka yasa Arya ta ce su ɗauko mata abincin safenta da bata ci ba, da ruwan sha. Angelina ce ta miƙe ta nufi cikin tantin. Su dai sojojin dake gadinsu suna ta faman kallonsu, suna tsaitsaye tamkar saƙaguna. Angelina ta dawo ɗauke da abincin cikin plate. Yarinyar tana gani ta zabura ta miƙe, kamata Arya ta yi zata zaunar, ina ai ƙoƙarin kwacewa ta fara yi, ganin haka sai ta saketa dan ta ga gudun ruwanta. Kwace abincin a hannun Angelina ta yi, a tinaninsu zata zauna ta ci ne, sai suka ga akasin haka, domin kuwa tana kwacewa ta juya da gudun gaske ta kutsa cikin daji ta hanyar da suka bi suka zo. Miƙewa Arya ta yi, da gudu ta rufa mata baya dan ta ga ina zata je, sai dai kuma bata yi taku biyu ba laptop ɗinta dake ɗaki ya fara kara. Ai da gudun gaske ta juyo, su Angelina dik da gudu suka watsa izuwa cikin ɗakin, su kansu sojojin dake tsaronsu da gudu suka nufi cikin ɗakin.ALLAH sarki abin da suke jira ne kwana uku kenan, watau samun location ɗin su Leo. Da gudu ta isa gaban laptop ɗinta, wani irin zubewa a ƙasa ta yi, hannunta har yana rawa wajen tsayar da alert na laptop ɗin kafin ta shiga kan drone ɗin nata. Ai tana shiga kai tsaye video ɗin a kan faskan Leo dake tsaye bayan wata katuwar bishiya yana kokarin canza bullet na bindigarsa ta fara nunawa, ga harbin bullet sai sucewa ta gefensa yake yi, da alama musayar wuta suke yi, ALLAH sarki, kwanaki biyar kenan yau da tafiyarsu, sun yi kwana biyu a hanya kafin su kai in da mutanen suke, da isarsu da kwana ɗaya network na wajen ya jagule saboda musayar wuta, a haka Arya ta rasasu har aka harbi drone ɗinta, yanzu wanda ta sake turawa ne suka yi sa’ar ya kama network ɗin.Ai tsabar farinciki idanun Arya cikowa da kwallah ya yi, su V kuwa rungumar juna da su Angelina suka yi, thank God ba’a kashe masu jami’ai ba dik da basu da tabbaci sauran suna raye ko aa, amma ganin Leo yasa sun ji kamar sauran suna raye. Da sauri ta shiga drone control ɗin, hannunta har yana kerma sosai. V ce ta ce. “Arya ki bibiyi sauran soldiers ɗinmu muga ko suna raye?”. Tamkar zata yi kuka ta faɗa, zuciyarta na harbawa da karfin gaske, tana tsoron wani abu ya sami Noor ɗinta. Arya na kokarin juya akalar drone ɗin izuwa arear wajen dan ta duba sauran sojijinsu sai gani suka yi Noor ya bayyana a gaban drone ɗin, da karfi ya rungumi Leo suka faɗi ƙasa. Suna faɗuwa bullet ta wuce ta kansu, da gefen wuyan Leo bullet ɗin zata fasa Noor ya cecesa, shi hankalinsa yana can yana ƙoƙarin canza bullet ya zuba sabbi daga waɗan da suke waist ɗinsa a ɗaure.Ai wani irin yawu da Arya ta haɗiye sai da sautinsa ya bayyana a fili, dikkansu jikinsu tsuma ya fara yi, suna jin ina ma ace suna wajen. Miƙewa Leo ya yi yana faɗin. “Thank you bro”. Ya faɗa yana yi wa Noor alamar jinjina da hannunsa.Noor dake kwance a ƙasa cikin ciyayin dake wajen ne ya miƙawa Leo hannunsa ɗayar da bata rike da bindigarsa, ya shagwaɓe fuska yana faɗin. “Ɗagani”…….. Hararansa Leo ya yi tare da cigaba da abin da yake yi na zuba ƴaƴan bullet a cikin bututun bindigarsa. Cigaba da kwanciyarsa Noor ya yi, wai ba zai tashi ba sai Leo ya ɗaga sa. Watau Noor yana da iya shege, a filin yakin ma sai ya yi. Shagwaɓa ya fara zubawa Leo yana shi dole a ɗagasa. Leo na ƙoƙarin juyowa zai yi mashi magana sai ganinsa ya yi ya yi wani irin tashi cikin zafa, ya yi tsalle ya taka bishiyar da Leo ke tsaye a jikinta tare da ɗaga hannunsa dake rike da bindiga ya saita ta bayan wuyar Leo ya saki wuta, kan ya faɗi ƙasa ya yi harbi biyar a jere kuma dik sun samu mutanen da ya hara, dan kuwa ƴan ta’adda ne suka ɓuya a cikin ciyayyin wajen, su suka harbo bullet da ya so taɓa Leo Noor ɗin ya cecesa. A tare suka faɗi ƙasa da waɗan da ya harba ɗin. Sake bajewa ya yi a ƙasa yana mayar da numfashi tare da cewa. “Wayyo my dad, my Juliet, i missed you more”. Ya faɗa yana rugumo bindigarsa. Hararansa Leo ya yi tare da cewa. “Tashi mu bar nan dan ba tsaro, mun shiga sansaninsu dayawa”……… Miƙo mashi hannu Noor ya yi yana faɗin. “Ɗagani, karfina ya kare”. A shagwaɓe ya faɗa. “Zaka tashi ne ko sai na ƙara maka nauyi?”. Leo ya faɗa on a serious note. Shagwaɓe fuska ya yi yana turo baki, ya ce sam shi sai dai a ɗagasa bashi da karfi. Leo zai yi magana suka ji motsin a kewayen nasu. Kallon juna suka yi. V da Arya sun gama haukacewa a zaune gaban laptop ɗin, Arya da yake bata son wasa a wajen aiki sai take jin tamkar ta shaƙo Noor, yana ɓata masu lokaci, a cikin ranta tana cewa in dai wani abin ya samu my sterious to kai ne sila, kuma ba zan barka ba. Ita kuwa V kome Noor zai yi burgeta yake yi, salon yaƙinsu ya gama tsumata, har wani nishaɗi suke bata. Gera guda Leo ya ɗagawa Noor kafin ya miƙa mashi hannu. Kama hannun nasa Noor ya yi tamkar zai miƙe, Leo ya gama sakin jiki Noor zai miƙe sai ya ji Noor ɗin ya fisgisa da karfin gaske ya tafi gabaɗaya ya faɗo kansa. Take bullet ta wucesu fiw. Dunkule hannun Leo ya yi ya daki Noor a shoulder, alama ce ta jinjina da sojoji ke wa junansu. A wannan karon a tare suka miƙe cikin zafa, jingina bayansu da jikin juna suka yi, Leo na fuskantar gabas Noor na fuskantar Yamma. Kafin su yi wani yunkuri sai gani suka yi ƴan ta’adda sama da 100 sun yi wa wajen zobe a cikin ciyayyin, kuma kusan dikkansu suna rike da bindigu. Leo ne ya ce. “Bullet nawa ce a bindigarka?”. Can ƙasa ya faɗa yadda babu wanda zai ji. “Jaka ɗaya”. Ya bashi amsa. Yana nufin bindigar a cike da bullet ya zo da ita, wanda ya harba guda biyar ɗin nan ne kawai suka fita, dama ya gama sanya bullet ne ya zo wajen. Shi ma Leo kunga yanzu ya zuba sabbin bullet..”What next?”. Noor ya faɗa a hankali. “Fire!!”. Leo ya amsa mashi da shi. Haba yana rufe baki suka fara ɓarin wuta, take miyagun suka fara mayar masu da martani, hakan yasa suka rabu suka nemi mafaka, Noor ya ɓuya a bayan wata ƙatuwar bishiyar ɓaure, shi kuma Leo ya kutsa cikin daji. Ɓarin wuta suke babu kama hannun yaro.Daga bayansa Noor ya ji an saka mashi bindiga a kai, wani ɗan ta’adda ne da fuskansa yake rufe da rawani, ɗana kunamar bindigar ya yi, babu imani ya nufi fasa kan Noor. Sai dai kafin ya harba Leo ya rigasa, wani irin wawan harbi Leo yai mashi a gaban goshi, farat ɗaya tafiya ɗaya kenan. Shege take ya zama mushe. Ɗago kai Noor ya yi, suka haɗa ido da Leo dake tsaye a bayan wata bishiya da Noor ɗin yake fuskanta. Sara mashi Noor ya yi kafin ya juya suka cigaba da ɓarin wuta. A lokaci guda bullet na bindigarsu ta kare ga ƴan taaddar basu kare ba. Kallon juna suka yi, da ido suka sanarwa da juna bullets ɗinsu ta kare. Ai su Arya na ganin maganar da suka yi da ido na cewa bullets ɗinsu ya kare dik suka ɗauke wuta, musamman V da ta fashe da kuka ne ma. Ita kuwa Arya dafe saitin kirjinta dake barazanar tarwatsewa ta yi. Ƙoƙarin sanya bullets a bindigar nasu suka yi, sai dai kafin su motsa miyagun sun yi masu zobe, dama sun shigo cikin sansaninsu sosai ne, kwana biyu da suka wuce a waje-waje suke musayar wuta, yau Leo ya ce sai ya matsa gaba, shi ne ya shigo.Saitasu da bindigu suka yi suna faɗin kada su motsa, sun kewayesu ta ko’ina ba hanyar tsira. Basu da zaɓin da ya wuce dole su ɗaga hannu, kallon juna suka yi, da ido Leo yai wa Noor magana kan ya miƙa kansa. Da farko Noor ya so yin gardama, amma da ya tuna cewa Leo baya abu haka kawai sai ya yarda suka miƙa kansu, suka yi surendar. Matsawa ƴan ta’addan suka yi, mutum biyu suka kwace bindigun hannun su Leo, sannan suka kwace bullets dake waist ɗinsu, suka haɗesu suka tasa ƙeyarsu kan su wuce izuwa cikin ainahin sansaninsu, sai murna ƴan ta’addan suke yi kan sun kama sojoji, zasu kashesu su ɗauki videon yadda suke kashesu su turawa ƙasa dan a kara tsoronsu. Arya da V tamkar zasu haɗiyi zuciya, kuka V ta fashe da shi, ita kuwa Arya jikinta har kerma yake yi, idanunta sun kara ciccikowa da kwallah, da sauri ta bar gaban laptop ɗin ta fito waje cikin tsananin tashin hankali. Manassa ce ta biyo bayanta, V kuma ta juya ta faɗo jikin Angelina tare da fashewa da kuka mai tsuna zuciya, tana faɗin shikenan mutuwa zata yi idan aka kashe Romeo ɗinta. Su kansu sauran sojijin dake wajen suke tsaronsu sun girgiza na ganin an kama su Noor, han kulansu ya tashi. Waje suka yo suma. Ita kuma Angelina ta yi ƙoƙarin control na drone na Arya dan ta duba ina su Zash suke ta ankarar da su an kama su Leo idan hakan zai yiwu, tana rungume da V tana rarrashinta. ———————-🔥WS-H.Dr Kamal ne ya yi wani irin shu’umin murmushi kafin ya ce. “To amma ai in baka son Lazy kana son Zinta kam ko? Kuma nasan kasan tana sonka tin ba yau ba!”……… Wani irin shu’umin one side smilling ya saki kafin ya ce. “Kwarai, shiyasa nike son dawo da ita karkashin office ɗina”…….. “Kana son haɗa jini da Muhammad kenan?”. Dr Mark ya faɗa.”Hmmmm”. Dr James ya faɗa, like shi kaɗai yasan me yake ransa. Jama’a bari in ɗan baku ƙaramin surprise a nan kafin mu wuce. Wani abin da baku sani ba a nan shi ne, da Maya da Zinta dik an kyankyashesu ne daga sperm na daddyn Lion, su Dr James suna da sperm ɗinsa da suka mashi tiyata suka ɗeba, kun san ana iya yi wa namiji tiyata a ɗebi sperm ɗinsa ai.Ana mashi ƙaramar tiyasa a shiga percutaneous epididymal sperm aspiration ɗinsa a ɗebi sperm ɗin. To su Dr James sai da suka san yadda suka yi suka ciro sperm ɗinsa, yanzu haka suna da ragowa sun mashi babban killacewa da matakan tsaro, a cewar Dr James zai kyankyashi matar da zai aura da wannan sperm ɗin, sannan idan ya mallaki matar zai yi mata dashen wannan sperm ɗin da kwayayen haihuwarta domin ta haifo mashi magaji mai kaifin kwakwalwar daddyn Lion wanda zai iya irin aikin da yake yi, shiyasa ya kyankyashi sister Maya and sister Zinta, a cewarsa Zinta matarsa, Maya ma’aikaciyarsa, nan gaba kaɗan zai sauke Lazy, da Maya zai maye gurbinta saboda shi masu basira kawai yake so a kusa da shi. Bai son daƙiƙu!.Baku yi manakin yadda Maya da Zinta suke da tausayi ba? To daddyn Lion shi ne ubansu, uwarsu kuma sai ALLAH ne kaɗai ya san daga gidan uwar wa Dr James ya kwaso kwayayenta ya haɗa ya kyankyashesu, amma dai koma kwayayen wace mace ya ɗauko ya haɗa da sperm na daddyn Lion tabbas kwayayyen sun kasance special ne, dan tin da ya ce zai kyankyasawa kansa mata da magaji ai kunsan ba zai sanya ordinary eggs ba, dole special zai sanya.A takaice dai plan na shirta mai karfi yadda zai mallaki Zinta, ya kuma dasa mata sperm na ubanta da eggs ɗinta ta haifa mashi magaji mai basirar daddyn Lion, amma wanna plan ɗin ya ɓoye ko su Dr Mark bai faɗa masu shirinsa ba, ya dai fake masu da cewa zai auri Zinta ne kawai dan tana da kyau, saboda daddyn su Lion kyakkyawa ne, so Zinta da Maya sun fi kiwa kyau a hospital ɗin, bai faɗa masu zai ɗebi sperm daga cikin na daddyn Lion da suka killace ya dasawa matar tasa idan ya aureta ba. Kai na ce akwai cakwakiya babba, dik mommynsu Lion ce silar komai, da bata karɓi kuɗi ta masu hanya sun kama daddyn Lion ba, da ba’a ɗebi sperm ɗinsa an ajiye ba.Yanzu dai a taƙaice Zinta da Maya kannen Lion ne daga kyankyasar kwalba, sun haɗa uba, uwar ce dai ba’a san daga in da aka samo eggs ɗinta ba. Kai Dr James ya zarce shaiɗani wlh, wannan irin kaifin ƙwaƙwalwa da ɗan banza basirar, kuna ga wata plan na ban mamaki!. ALLAH sarki shiyasa Maya da Zinta suke son junansu sosai, ashe ubansu ɗaya, uwar ce dai bamu sani ba ko eggs ɗin mace guda ne ko kuwa kowacce da uwarta!”Ku daina yi mana maganar Muhammad a nan”. Dr Mark ya faɗa tare da miƙewa, ya nufi hanyar fita yana faɗin zaman ya kare tin da za’a tuna baya, daga haka ya fice zuwa office ɗinsa. Su ma su Dr James ɗin fita suka yi kowannensu ya nufi office ɗinsa.After some days da faruwar wannan abin. Sister Zinta and sister Maya ne zaune a ɗakin da suke haɗa Chemicals ɗin nasu, abin duniya dik ya ishesu, waɗan nan chemicals da sune haɗawa ya yi mugun tsaya masu a rai, sun gagara tursasa zuƙatansu su cigaba da aikin, sun kuma rasa ya zasu yi, dan basu isa su ce ba zasu yi wannan aik ba, ba mai ja da 3D, sannan ita Zinta zuciyarta ta mace a kan soyayyar Dr James, ba zata iya kin yin aiki idan ya sanyata ba. Dik da basu san ne za’ayi da chemicals ɗin ba amma zuƙatansu sun yi muguwar karaya da tsorata, musamman sister Maya da ta fi Zinta rauni, wani lokaci ma idan tana aiki kuka sosai take yi, saboda haɗarurrukan chemicals ɗin sun zarce yadda kuke tinani, sai ta yi ta kuka tana jin kamar wasu za’a cutar, kamar abin sharri ne, ta rasa dai gane dalilin da yasa take kuka idan tana haɗawa. Yanzu haka kuka take yi hawaye bibbiyu tana tace sabbin chemicals da aka shigo da su yanzu, masu haɗarin da suka fi na baya. Haka ta tacesu, ta cire masu karfin ciki, ta zare matattun ciki, sannan ta je ta haɗa cikin waɗan can chemicals da suka haɗa a cikin wani katon drom mai zurfi, ta zuba a ciki. Tsayawa ta yi a kusa da drom ɗin tana kallon yadda miyagun chemicals ɗin suke juyawa a cikin drom ɗin suna haɗewa da juna. Sister Zinta ce ta matsa wajen, nata chemicals ɗin da ta gama haɗawa ta juye a ciki, sannan ta ce. “Sister Maya lafiya?”……. “Sister Zintata hankalina ya gagara kwanciya a kan wannan aiki, ina jin tamkar sharri ne”. Dafata Zinta ta yi, juyowa Maya ta yi suka rungumi juna, Zinta ta ce. “Babu wani abu, yanzu bari in je office na Dr James in bashi report na yau sai in zo mu koma SECTION A mu tattauna a can ko?”………. Kai kawai Maya ta iya gyaɗa mata……. “Je ki kaiwa Dr Kamal naki rahoton kin ji? Mu haɗu a gate na SECTION A”. Nan ma kai kawai Maya ta gyaɗa mata. Raba jikinsu ta yi tare da wucewa ta ɗauki result na aikin yau, ta nufi waje cike da zumuɗin zata ga Dr James, yarinyar nan ta haukace a kansa sosai, ita ko iya ganin face ɗinsa ta yi ba ƙaramin daɗi take ji ba, bare ace ya yi mata magana, ooooo, kwanar farinciki take yi. Hannunta rike da file ɗin ta shigo arear 3D office. Tin daga nesa sister Lazy ta hangota, da sauri ta mike ta tareta bata bari ta kariso kusa da office ɗin nasa ba. A gabanta ta tsaya tare da miƙa mata hannu tana faɗin. “Bani rahoton in kai mashi!”. Babu wasa a tattare da ita ta faɗa. Tsoronta yasa Zinta ta miƙa mata hannayenta suna ƴan kerma. Fisga ta yi da karfi tare da juyawa tana cokala wannan takalmin nata mai uban tsawo ta nufi office ɗin nasa. Idanun sister Zinta ne ya cicciko tab da kwallah, ta ɗan turo baki kafin ta juya cike da takaicin yau bata kallesa ba, ɗazun da safe ma da zata kai mashi rahoton wani chemicals cikin wanda suka kawo ya faɗi kwalbar ta fashe ya zube su sake kawo irinsa Lazy ta hanata shiga, sai dai ta karɓi rahoton da ta rubutan ta shigar mata da shi, ta kuma karɓo amsar ta dawo mata da shi, abin ya yi mugun bata takaici. Tsaye sister Lazy ta isko Dr James a tsakiyar office ɗinsa yana kokarin haɗe takardun dake kan table ɗinsa, sun tashi kenan, yana tattare rahotonni masu muhimmanci saboda in ya natsu a gidansa cikin dare ya dubasu. Cikin wani irin karuwan yanga da yauni tana wani kwas-kwas ta shigo office ɗin. A gabansa ta tsaya tare da miƙa mashi result ɗin, tana wani karairaya ta ce. “Should I escort you?”……. Shiru bai yi mata magana ba, bai ma ɗago ya kalleta ba, sai da ya gama shan kamshinsa kafin yasa hannu ya karɓi takardan hannun nata. Ɗan duba takardan ya yi, a natse ya ce. “Ina mai wannan aiki ɗin da ba zata kawo rahotonta da kanta ba?”.Ɗan tsuke fuska ta yi, sai kuma ta ce. “Ban san meyasa bata son shigowa office ɗinka ba, amma ranar na ji tana cewa da ta shiga office ɗinka gara ta shiga cikin wuta, shiyasa idan ta zo take bani result ɗin ta ce in miƙa maka, ni dik tinanina ma kai kake cewa ta bani in baka ai”. ……… Shiru ya yi bai sake yin magana ba, sai dai ya miƙo mata result ɗin alamar ba zai karɓa ba, idan kuma bai karɓa ya sanya hannu ba to fa aikin sister Zinta na yau an yi cancel ɗinsa, idan dama aikin 30 days zata yi to sai ta kara maimaita wannan aiki da aka yi cancel ya zamana kenan 31 days zata yi. Abin ya yi mugun yi wa sister Lazy daɗi na yadda ta ga ta lalata mata aikinta na yau, cike da yanga ta juya ta fita. Kai tsaye room na su sister Zinta ta nufa, tana wani irin makirin murmushi. Tana zuwa ta iskosu a ɗaki, isowarsu kenan suna ƙoƙarin cire kaya zasu shiga wanka. Jefawa sister Zinta file ɗin a kan fuskanta ta yi tare da cewa. “Ya soke aikin yau! Kuma ya ce dik in kika zo kawo mashi rahoto ki ajiye a PA office”. (Office na PA office ɗinta kenan, kunga ta samu damar kullum ta dinga ɓata mata aiki, tana shirga mata karya a wajen Dr James har ya fusata ya fara hukuntata. Cike da tashin hankali ta ɗauki file ɗin, tamkar zata yi kuka ta ce. “Meyasa ya soke aikin? Akwai in da na yi mistake ne? Ko dai akwai abin da yakamata in saka wanda ban saka bane? Aunty Lazy please help ki basa hakuri, zan sake duba komai in gyara”. Dogon tsaki Lazy ta ja tare da juyawa ta fita, tana fita Zinta tasa kuka tana faɗin ta shiga uku, dan tasan idan ya soke aiki fa mutum ya shiga uku, bayan sake aikin sai ya bashi hukunci mai tsanani. Jikinta na rawa ta ce. “Sister Maya me abin yi?”…….. Maya da gabaɗaya jikinta ya yi mangaribar jemage ne ta amsa da. “Ina ganin mu yi wanka sai mu je gidansa ki bashi hakuri, ki ƙara gyara rahoton, ki duba da kyau ko akwai in da baki yi daidai ba”. Na’am ta yi da wannan shawara, cikin rawar jiki ta buɗe file ɗin ta zaro paper, a gefen gadonsu ta zauna ta hau dubawa a natse. Ita kuma Maya ta wuce cikin toilet dan yin wanka.Me kuke tinanin zai faru? Cakwakiyar asibitin nan dayawa take!.
