Haihuwa Da Hanji Page 46 Hausa Novel
Kwanakin da suka biyo baya sun zo mishi da tarin ayyuka haɗe da zirga-zirga ta yadda ma wani daji suka koma suka yi camping don dai ganin an ceto su Aisha a hannun waennan Ƴan garkuwa da mutane, inda yake ko service babu hakan ya sa ya manta rabon da su yi waya ko da Abeeha ce kuwa bare Afeefah da sau biyu ya taɓa kiranta gashi har an ci tsawon sati uku suna abu ɗaya ba su ƙare ba, sun yi namijin kokari duka team ɗin wanda suka hada har da taimakon wasu airforce, polisawa da ‘yan sa kai da ake cewa Hunters a cikin sati na huɗun suka samu gagarumar nasara bayan kubutar dasu sun kubutar da dayawa daga cikin waenda abin ya ritsa dasu kuma sun samu nasarar hallaka dayawa daga cikin miyagun.A yau da ya kasance Juma’a suka iso cikin garin Fombina zuwa masarauta, kai tsaye aka musu iso don an san da isowarsu kuma an shirya musu tarba na musamman, ko bai nuna ya san Aishan ba ma itama daga ita har Zara da yake a tsorace suke har lokacin ba tantance kowa suke yi ba sai da suka gansu tsakiyar masarauta kai tsaye sashen Uwar ɗakinsu Fulani Adama aka yi dasu ta fito ta rungumesu tana hamdala nan suka saki kukan da ya gama cin su a rai.Shi kam Rayyan na cikin baƙin fada inda sarki ya nemi da su koma masaukinsu su huta kafin ya gana da su ko zuwa dare don yanzu yana ta samun baƙin taya murna daga kananan hukumominshi da na shuwagabannin rugagen dake kewaye da Daular fombina, Rayyan ya tashi zai bi bayansu Laamiɗo yayi gyaran murya ya furta “Ciroma!”Chak ya tsaya, ya dawo da baya ya koma zaune”Allah ya baka yawan rai!””Bisa tsarin umurnin da na yanke, ka shigo kenan Sarkin gida zai maka rakiya zuwa sashenka an tanadar maka duk wani abin da zaka buƙata ka je ka huta iyayenka na bukatar ganawa da kai.”Da wani irin hanzari ya ɗago ya kalli mai martaba sai kuma ya mayar da idanun ƙasa ganin duk idanun manyan fada na a kanshi, Miƙewa yayi”Na barku lafiya!”Daga haka ya fice sarkin gida yayi saurin mara mishi baya, a wajen ma dogarai shidda ya gani sun rufa mishi baya kuma ya san sune aka yi assigning don kare lafiyarshi haka kawai yaji kaman an takura shi.Sashe ne na musamman tsararre ya ji furnitures da komai da komai masu tsada da ɗaukar ido amma shi bai wani burgeshi ba tunda ba tatse ɗin shi bane, ɗakuna huɗu ne a sashen ya nufi wanda sarkin gida ya nuna mishi shine nashi ya shige ba tare da ya ce mishi komai ba yayinda sauran dogaran suka kafe a bakin mashigar sashen.Komai kuwa akwai ko da ya buɗe wardrobe kaya ne kala kala kawai gasu nan, manya da kananu Dukda ya san idan ba a cikin sashenshi ba a yanzu saka kananun kaya ma yayi yawo da su a cikin masarautar ya haramta mishi, kayan jikinshi ya zame ya shiga wanka ya jima sossai kan ya fito ya shirya cikin karamin three quater baka da wata karamar riga fara ta kama shi ta fitar da surarshi na cikakke kuma karfaffen namiji, wayanshi ya zara ya fito parlor sai ya samu an cika dining ɗin da kuloli na alfarma wanda ya san abinci ne ciki.Gyaran murya yayi da hanzari dogarin dake dab kofa ya faɗo ciki ya zube ƙasa “Allah ya ja da zamanin Ciroman fombina, Allah ya kare gabanka da bayanka ubangidana, gaba salamun baya salamun naka faɗa ne namu cikawa….”Hannu ya ɗaga mishi”Daga ina aka kawo wannan?”Ya jefa tambayar yana ɗora kafa ɗaya kan ɗaya a lokaci daya yana dan karkaɗawa idanunshi zube a kan screen ɗin wayanshi “kuyangin Uwar magajin sarki ne suka shigo dashi ranka ya dade….””Ku tattara ku fitar min, daga yanzu ban amince a shigo min da abincin ko wani sashe ba don ba na buƙata!”Cikin ba da umarni yayi magana hakan ya sa dogarin sake zubewa “An gama sadaukin maza..!”Da wuri yaje ya fara tattare wa shi kam yana zaune shiru don ya gwada Layin Afeefah bai shiga ba na Abeeha kira daya ya mata bata ɗaga ba kuma bai sake kiran ba.Damuwar shi yadda mai martaba ya ba da umarnin dawowanshi kenan ya san ba zai taba amincewa ya tafi ba amma kuma idan ya zauna kaman bai yi adalci ba, bai kamata kawai su Uncle Musa su ji cewa ya dawo gida ba dole yana bukatar komawa da su su san asalinshi ya tattauna da su da tsara yadda za’a tafiyar da rayuwar su Abeeha da yake jin banda aure babu wanda ya isa ya ce zai karbi riƙon Abeehar don kawai ya dawo gida har yanzu shi a jinin Maami yake kallon kanshi kuma a hakan yake so ya tabbata don haka dole ne ma ya ga sarki.Time ya kalla karfe tara ne kwata kwata da mintuna ashirin, Dukda baccin da ya tarar mishi dole yaje ya ga sarki ya san karfe goma zai koma turakarshi don fara shirin tafiya masallaci, Miƙewa ya yi ya koma ɗaki ya shirya cikin wasu navy blue kaftan da ya sha ɗinki irin na sarauta, ya saka hular da ta dace da kayan ya zura takalmi ya fito hannshi riƙe da waya amma sai ya tattaresu ya goya a baya ya fice daga sashen dogaran na ganinshi suka rufu za su bi shi ya juyo ya kalli shugabansu.”Sunanka?””Gaabɗo ranka ya dade” (Joy yake nufi)”sauran su zauna kai ka biyo ni”Yana kai nan ya juya da sauri Gaabɗo ya bishi har turakar mai martaba duk inda ya ratsa hadimai za su zube suna kwasar gaisuwa kai kawai yake ɗaga musu, sai da aka sanar da isowarshi kan ya shiga, ya ci sa’a mai martabar ma na son ganinshi da kallo yake ta Binshi har ya zauna a ƙasa kaman yadda me martaba ke zaune cikin shimfida na alfarma ya kishingida da tun tun.”Abeey barka da wannan lokaci””Barka dai Ciroma, na san ka ji hukunci na kuma kana tunanin bai maka daaɗi ba amma abin da zan iya cewa kenan Sameer ba zan bari ko kusa ka sake subuce min ba, Kukan BOƊEJO da ma sautin kalangun gado sun isa su tabbatar maka da cewa kai ne mai jiran gado”Numfashi ya ɗan sauƙe yace a hankali “Abeey ka yi haƙuri da abin da zan faɗa ba zan saɓa umarninka bane amma zuri’ar da na ajiye a chan sun fi karfin na sanar da su cewa na dawo nan a waya, ɗiyar su ta zame min uwa da uban da na rasa a rayuwata tsawon shekaru ashirin da shidda bata taɓa gajiyawa da hidimata ba, bata taɓa min kallon banza ko Harara da sunan tsana ko kyara ba, ta gatanta ni ta fifitani fiye da komai da ta mallaka a duniya ciki har da miji da ‘ya’yan cikinta, Abeey duk yadda zan fasalta maka irin son da Mammi tayi min ɓata baki ne duk kuma ta yi bata san ni waye ba har sai da take kwance a gadon mutuwarta a haka roƙona tayi da in dawo in samu farin cikin da na rasa, in dawo in ji uzurin….” Sai bai ce komai ba ya duƙar da kai.Hadiye abin da ya taso mishi yayi kan ya cigaba”Ban shirya dawowan ba na riski labarin ɓatan Aisha bayan ma ƙiran da shugabanmu yayi min na ina cikin team da aka yi assigning wannan aiki na taho ne ba da shirin dawowa b..””Muhammad Sameer”Laamiɗo ya kirashi runtse ido yayi don ya san bai amince bane.”Ka ba ni labarin abinda ya faru daga barinku gidan nan da mahaifiyarka, na dai san ta nemi izinin tafiya chan mambila wurin dangin mahaifiyarta kuma na bata izini da driver da kuma amintacciyar Kuyangarta sai labari marar daaɗi aka dawo min dashi da sunan ka ɓace a tsaunukan mambila an neme ka an rasa na kwashe tsawon shekaru ban bar kowani hukuma sun huta ba da neman ka har wasu suka zartar da cewa ka mutu ni ban yarda ba hakan ya sa a kullum nake Adu’a duk juma’a nake sadaka duk goman karshe na kan manta kaina ina rokar maka kariya da nasara a duk inda kake da Fatan Allah ya bayyana min kai ya tsare maka imaninka me ya faru? Meyasa daga kalamanka na yarda Ammienka na da hannu dumu dumu akan abin da ya faru?”Kanshi na a ƙasa ya shiga magana kana jin ɗaci a saman harshenshi a kuma hankali yake maganan”Abeey bayan mun yi muku sallama mun bar nan tafiya ne mai nisan gaske muka dauka ba tare da na san inda muka nufa ba, na taɓa zuwa mambila sau ɗaya don haka inda muka nufa bai min kama da hanyar ba, idan nayi bacci na gaji na farka na tambayi Ammie har yanzu bamu isa ba sai ta mayar da ni jikinta ta rungume tace har yanzu da saura ban sani ba ashe nesanta ni take da asalina, nesanta ni take da inda na fi wayo da kuma farin cikina duk ku biyu, yamma ne sossai muka isa inda ban sani ba hatta yaren su kaɗan kaɗan nake ji shima saboda akwai wasu kuyangai dake yi anan ina sha’awar iya yaruka na saka su a gaba ina koyo, ko da ta saka driver tsayawa kuka take yi ta bani ƙullin kayan marmari da abinci waenda basa lalacewa da wuri cikin guzurinmu tace in riƙe, muka sauka muka bar driver da Kuyangarta Kande a mota mun yi tafiya sossai har muka kawo gefen wani juji da babu hada hadar mutane sossai ta kalleni.”Ka yi haƙuri ɗana ina sonka amma dole ta sa zan rabu da kai babu yadda na iya!”A karye na ce mata “Ammie Meyasa tunda muka fito kike kuka? Meyasa za mu rabu? Me muke yi anan?”Ta ja numfashi tana share hawayen dake kara gangara tace mini”Nan shine inda na ji ya kwanta min ka cigaba da rayuwa, ka yi aiki kaman na jaruman maza ka nema da kanka ka samu har ka tsaya da kafafunka, idan da rabon mu gana watarana za mu gana amma a yanzu ka cire cewa kai ɗan sarki ne jikan sarki, ka jingine ka taɓa sanina ko mahaifinka, ka manta ka taɓa ko da amsa suna Ciroma Sameer ka samu sabuwar rayuwa zan maka sdu’a ba zan gaji ba amma daga yau ka gama zaman masarauta…”Hankalina ya tashi da kalaman ta na rikice ina tambayarta “Meyasa Ammie? Me yasa zan manta ku? Meyasa zan manta Abeey?””Saboda Dole ne Sameer!”Ta daka min tsawar da bata taba min irinshi ba Dukda na razana kuma kuka ba ya daga cikin al’amarina ban san na fashe da kuka ba na riƙo hannayenta ina roƙonta kar ta bar ni anan ban san kowa ba, kar ta bar ni anan ba zan iya rayuwa ba Ammie ta zame hannunta ta tureni har na faɗi na rarrafa ba tare da na damu ba na rike kafarta ina kuka sossai da roƙonta ta tafi da ni amma ce min tayi “Ko a mafarki ka biyo baya na ba zan taɓa yafe maka ba Sameer!”Baya baya nayi na zube a ƙasa a zaune ina kallonta har ta ɓace min, na ji na tsani duniyar na ji na tsani kowa da komai kuma a lokacin zuciyata ta kafe Abeey na ji ba zan iya sake yi mata kuka ba tunda bata so na ta tsaneni, babu abin da yafi kona min rai irin bolar dake gangana nan uwata tace min in ci gaba da rayuwa, nan fa ta zaɓa min. A inda ta barni anan na zauna har dare ban motsa ba dare da naga karnuka na zuwa wurin cin abinci na bar musu duk abinda ta bani don ba zan iya amfani dasu ba na koma wani gini da ba’a ƙarasa ba na zauna daga ranar na rasa bacci na Abeeyy daga na rufe idanu kalaman ta su ke farautar numfashina….A ranar Ammie ba rabuwa da ni kawai tayi ba ta kashe ruhi da zuciyata kisa mafi muni na yi kwana biyu ban iya cin komai ba sai ruwa kan wani almajiri ya ja ni muka fara sana’ar wanke gilasan mota Dukda ban taɓa mishi magana ba amma shi yana min surutu sossai, kayan aikin nashi ne idan ya gaji zai bani in yi ko kwanaki goma ba’a yi ba garin wanke gilasai mota ta kaɗe shi ya rasu, kayan aikin nashi na cigaba da amfani da su har Allah ya haɗa ni da Mammi..”Nan ya cigaba da bashi labarin komai da komai mai martaba banda hawaye babu abinda yake, a lokacin da ya zo rasuwar Mammi sai da hawaye ya ziraro mishi ya sa hannu ya ɗauke jijiyoyin kanshi duk sun tashi raɗa raɗa idanunshi sun yi ja sossai da sossai.Shiruuu ne ya ratsa parlorn fiye da mintuna biyar Abeey a hankali ya ce “Mahaifiyarka ta cuce ni ta ci amanata Sameer! Ban san me zan yi na huce wannan zafi da raɗaɗin da nake ji ba… Bata da uzurin bani na wannan laifi da ta aikata. Hakika na so Mammin ka tana raye in ganta ido da ido in yi mata tarin godiya marar adadi akan kaunar da ta nuna maka sai dai kash! Allah bai taɓa barin wani don wani yaji daaɗi ba idan ajali ya zo babu mai ƙara ko da second guda ne sai an tafi, a yanzu ma bata ɓaci ba za mu tabbatar mun yi tarin abubuwan alkhairi masu yawa da sunanta don ladar ya je mata a makwancinta. Allah ya musu rahama ita da mai gidanta ya sada su da annabin rahama”Ya amsa da ameen “Ɗauki ipad ɗin chan ka kira min Mahaifinta video call za mu yi magana”Ipad ɗin ya dauka ya saka numbern uncle Musa ya kira aka taki sa’a yana online ya ɗaga zaune yake da Uncle sanusi da Uncle Mansur suna tattaunawa ganin fuskar Rayyan ya sa suka yalwatu da fara’a ya shiga gaishe su yadda ya saba suka amsa kan ya mayar da fuskar kan fuskar Abeey ba tare da ya ce komai ba.”Assalamu Alaikum warahmatullah…”Amsawa suka yi suna ta kallonshi kan Uncle Mansur ya zare idanu “Laamiɗon Fombina mai girma Muhammadu Modibbo Aliyu..”Duk sai lokacin suka ɗago suka shiga gaishe shi da girmamawa don shima ba ƙarami bane idan bai girmi uncle Musa ba za su yi sa’anni. Sannan ko babu girman shekaru akwai na mulki da sarauta mai girma.”Na yi muku laifi ina Fatan za ku yi haƙuri ku yafe min kuma ku dubi uzurina, kaman yadda kuka sani sunana Muhammadu Modibbo Laamiɗon daular kudu maso arewacin Kasar nan, a cikin tarihina ina da ɗa namiji tilo da ya ɓace da kananun shekaru inda an yi neman duniya an rasa shi sai satuttuka da suka wuce Allah ya bayyana min shi. Wannan yaro ba kowa bane face ɗan ƴar wurin ku mai rasuwa wato Rayyan a chan anan kuma Muhammadu Sameer””Allahu Akbar kabiran! Allah mai girma! Allah mai yadda ya so iko sai Allah ashe dama Rayyan ɗanka ne? Kai Alhamdulillah wannan abu na farin ciki ne Alhamdulillah ina ma Mamanshi na raye ta ga wannan rana…”Uncle Musa ke fada cikin tsananin farin ciki suka shiga taya su murnar saduwa da juna. Bayan gama barka da jaje Mai martaba ya ɗora “Laifin da na muku shine na sanar da ku a waya, shi Ciroman ya so ya je ne don martabarku ya shallake haka a gareshi amma ban ba da goyon bayan hakan a yanzu ba, zai iya zuwa ziyara ko wasu kananun al’amura da bai kamallah ba amma sai ya gama blending da dangi ina fata hakan bai ɓata muku ba, in shaa Allah zan yi tattaki na zo da kaina na kawo ku kuga inda yake”Uncle Musa ya ji daaɗin martaba da ƙimar da aka basu yace “Ba sai ka zo ba ranka ya dade da kanmu za mu zo har nan mu taya ku murna in shaa Allahu””Sai abu na ƙarshe ban san ko za’a yi min wannan alfarma ma””Alfarmar ka ya wuce ka roƙa mai martaba sai dai umurni”Uncle sanusi ya faɗa don basu taba zaton sarkin haka yake da saukin kai da iya mu’amala ba Dukda tarin dukiya da irin rigar mulkin da yake ciki hakan bai hana shi yi musu magana cikin girmamawa da fahimta ba.”Idan za ku taho ɗin ba matarshi kawai za ku taho da ita ba, za ku taho min da ‘ya’yana Jannah Da Abeeha ita jannah za ta koma ne kawai saboda auren dake kanta Abeeha kuwa ta zama tawa aure ne zai fitar da ita daga wannan gida bi’izinillahi”Sun gamsu suka yi godiya don martabarsu ne Dukda suna da dukiyar da zasu iya rike Abeeha amma Mammi Rayyan ta barwa shi kuma duk inda Rayyan yake dole ta zauna dashi… Bayan sun ajiye kan sadarwan Mai martaba Laamiɗo ya dubi Ciroma “Alhamdulillah! Yanzu ka je kayi shirin juma’a idan an sauƙo akwai media team da suke son ganawa da rundunarku da kuka ceto su Aissatou to amma su sun tafi bayan na sallamesu don komawa ga iyalan su bayan sun bar nan shugabanku ya kira ni akan ba za su iya zama har Washegari ba dole na wakilta Galadima ya je ya min godiya ya kuma sallamesu kai za ka gabatar da shirin madadin ku gabaɗaya”Bai so ba amma ya ya iya dole ya amsa ya yi godiya ya miƙe ya fice.Yau suka yi finals jiya garin gigin baccinta an dauke musu wuta kuma ba’a yi rana ba don ruwa suka samu basu samu chargy a solar ba kan a kunna gen ta tafi fitsari ta jefar da wayanta a ruwa, ta ji haushi saboda bata da wayan kallonshi tunda ba ya kira yanzu, sossai take jin kewanshi kaman sun wani saba sukuku ta shigo parlorn abin da ya kamata tana murnar kamallah secondary da aka yi da kyar amma damuwar da zuciyarta ke ciki ya hana ta.A babban parlor ta samu Abeeha na kai da komo wa tamkar ruwan cikin kwano ta kasa zaune ta kasa tsaye ganin Afeefah yasa ta daka tsalle ta riƙo hannayenta “Afeefah mun warke… Innalillahi wainna ilaihi rajiun khaihhh farin ciki zai kashe ni…! Afeefah Albishirrinki..”Cike da zumuɗi take maganan har jikinta na rawa “Goro..”Ta faɗa cike da mamakin me ya saka Abeehar farin ciki haka “Afeefah kin zama Gimbiya matar yarima ko in ce Sarauniyar gobe matar Saraki… Ashe Saraki da Mammi ke kiran Ya Rayyan ba’a banza ba? Afeefah mijinki ashe ɗan babban sarki ne mai tarin daraja da tushe me kyakyawar asali? Ashe ya Rayyan jinin sarauta ne ke yawo cikin jikinshi? Kaii amma Allah ya isa wa mahaifin yarinyar nan da ya kalleshi yace kila ba tsatso mai kyau aka samo shi ba ya ci mutuncin sarauta..”Afeefah dai ta kafe a tsaye tana ta kallon Abeeha na zuba chan tace “Anya Adda Abeeha lafiyarka kuwa? Wani irin magana kike tayi ba kan gado…? Wani yaya Sarakin?”



