Hausa novels

Matar Damisa Book 1 Chapter 28 Complete Novel

typing📲

🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)

*written* *and* *story* *by*
*Asma’u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)

*WhatsApp me 09065443871*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK ONE*
🅿️ ——-> 77 & 78 <——-

💫💫✨ Ayush tana zaune a cikin motor tare da mutumin da ake kira da Malam Lawan, tana zubda hawaye kai a sunkuye tace “malam wallahi banzo gidan nan don nayi musu leƙen asiri ba, ni da farko ban san su ba, dan Allah ka rufa mun asiri…”

Dariya Malam yayi da farin gemunsa yace “Ayshert kenam! inda ace zan tona miki asiri ai da tun farkon zuwanki gidan nan na tona, saboda har aka kaiki asibiti daga nan Hajia Fateema take riƙe da ke, nasan da alkhairi kika zo gidan nan, sannan zoben dake jikin cibiyarki sanan shine maganin ciwon Junaid,
ki temaka ki ceto Junaid ke kaɗai ce zaki iya magance masa matsalarsa Ayshert, insha Allahu baza ki mutu ba…

Ayush tana kuka tace “malam ina tausayawa Junaid a halin da yake ciki, shi ɗin rayuwata ce kuma farin ciki na, ko zan mutu zan cire zoben a jikin cibiyata…” ta fashe da kuka ta kuma cewa “duk laifin mahaifi nane da kuma mahaifiyata ina zasu kai alhakin Junaid da suka ɗauka…”
malam yace “mahaifiyarki bata da laifi domin itama ana amfani da itane ta hanyar tsafi, mahaifinki shine babban mai laifi domin a rayuwarsa ba abunda ban saniba, hatta mahaifiyarki bata san abunda na sani akan mahaifinki sarki Raamud ba, da ƙwacen mulkin da yayi wa mahaifin Junaid…”
Ayush tana kuka idanuwan ta sunyi jawur ga leɓen bakinta ya bushe domin rabon da ta ci abinci tin shekaran jiya, ruwa kuma banda ruwan da aka ɗaura mata bata sa ruwa a bakinta ba, duk ta rarrame ƙashin wuyanta sun fiffito, damuwa ne ƙarara a saman fuskarta bakinta na kakkarwa tace “ba komai Junaid zai samu lafiya, amma dan Allah Malam inaso kamun wani alfarma..”

malam yace “inajinki ƴata..”
tace “kamun alkawarin kar kowa yasan wannan batun, kar ka sanar musu cewa inada alaƙa da maƙiyansu wato iyaye na, koda na mutu kar ka sanar musu cewa ata sanadiyata Junaid ya samu lafiya dan Allah malam..”

Malam ya dube ta dakyau sannan yace “Ayshert ya za’ayi kiyi sadaukarwa sannan ace bazasu sani ba? wannan fa wasa da rai zakiyi..”
“Eh malam duk da hakan inaso ya zama sirri..” kuka ne yaci ranta da sauri ta buɗe murfin motar ta yi ficewar ta,
a falo ta tarar da Mommy tana zaune akan sofa tayi tagumi sai hawayen da ke kwance saman fuskar ta,
Ayush haura wa upstairs tayi domin bazata iya ganin mommy a cikin damuwa ba, direct ɗakinta ta wuce…

malam ne ya shugo falon ya tarar da mommy shima zama yayi yana faɗin “kin kusa ki kashe kanki indai bazaki daina shiga damuwa haka ba, karfa ki manta ciwon zuciya gareki, kuma bugu biyu yake yi yayi bugun farko sauran na biyu wannan kuma zaki rasa rayuwarki ne….”

mommy ta ɗago tana hawaye tace “to ya zanyi malam wannan al’amarin yana shirin fin ƙarfi na, bazan iya juran ganin yarona a cikin wannan matsalar ba, shi kaɗai Allah ya bani, wani irin ciwo ne haka an rasa maganinsa….” kuka ne yaci ranta sosai take kukan,

Ajiyar zuciya malam yayi sannan yace “Addu’a shine mafita kuma shine maganin ciwon Junaid idan kin dage da yinsa, shiga damuwan nan bashi zaisa Junaid ya warke ba, ki yawaita tashin dare kina salloli kina kaiwa Allah kukan ki, ai ba abunda ya gagari Allah…”

“Shikenam malam insha Allahu zan rage shiga damuwan, sannan zan cigaba da yin Addu’a, banaso na rasa ɗana kamar yanda na rasa mijina…”

kawar da kai malam yayi yana murmushi sannan ya girgiza kai yace “ina mai miki albishir da cewa Junaid zai samu sauƙi, ki zuba ido daga nan zuwa gobe,
Ki kasance cikin Aminci Hajia Fateemah, na barki lafiya..”
daga nan ya tashi yayi mata sallama sannan ya tafi..
Maganganun malam ba ƙaramin tasiri yayi wa mommy ba, domin lokaci guda taji wani sanyi a ranta, tashi tayi itama ta nufi ɗakinta…

Bayan Ayush ta shige ɗakinta tsaya wa tayi a gaban mirrow ta ɗaga rigar ta sama tana ƙoƙarin cire zoben,
zafi take ji bana wasa ba, ga kuma tana ji kamar wata jijiya zata tsinke a cikin cikinta,
abun bazai fita da daɗin rai ba jin zafin yayi yawa yasa tayi ƙara ta sake zoben jikinta yana wani kakkarwa, har cibiyar yayi jawur hatta idanuwan ta ma sun kaɗa sunyi jaa, wani irin zazzaɓi ne ya rufe ta,
duk da hakan bata daina fisgar zoben ba,
ganin bazata iya cire wa ba yasa ta daina jan zoben ga kuma raɗaɗin da take jii,
zama tayi a bakin gado tana kuka, ga ciwon kai daya dameta,
idonta ya faɗaa kamar majinyaciya daƙer ta tashi tana jan ƙafa ta fice a ɗakinta ta nufi ɗakin Junaid ga hajijiyan da yake ɗiban ta da haka ta shige ɗakiin,

shi kuwa Junaid yana kwance a saman gadonsa yana fuskartar ceiling ido a rufe, da alamun bacci yake yi.
zama Ayush tayi daf da shi ta ƙwantar da kanta saman ƙirjinsa tana kuka mai cin rai,
ta ɗago tana kallonsa hannunta a kan fuskarsa tana shafar sajensa,
Junaid ya rame sosai shima fuskar ya yi fiyau, ga yayi wani irin fari lips ɗinsa kamar wanda aka shafa cream sai sheƙi yake tayi..

ƙara fashe wa tayi da kuka tana faɗin “Yaya Junaid na kasa wallahi, bazan iya cirewa ba, inajin raɗaɗi sosai, ina matuƙar ƙaunarka Yayana….”

*WASHE GARI*
Ayush tana zaune a bakin gadon Junaid tana ɗiban milk a spoon tana bashi a baki,
shi kuwa yana zaune yana motsa bakinsa a hankali, ko motsa yatsansa baya iya yi,
zama ma saida mommy da Ayush suka zaunar dashi,
cikin kulawa Ayush take feeding ɗinsa,
idonsa kuwa akanta ko ƙibtawa baya yi.
suna cikin wannan halin
aka turo ƙofar ɗakin da sallama aka shugo, waiwaya wa Ayush tayi tare da amsa sallama tana binsu da kallo!
Doctor Hasheem ne ya shugo shi da ƙanwarsa Laila sunzo duba jikin Junaid.

Laila ganin Ayush tana feeding ɗin Junaid ta dafa ƙirjinta tana faɗin “na shiga uku,”
Doctor Hasheem ne ya dube ta yace “lafiya kuwa?”
tayo kan Ayush tana faɗin “wacece ke? daga ina kike? meye alaƙarki da Oga Junaid?..” ta ƙarasa maganar tana zazzaro ido waje.
Ayush murmushi kawai tayi ta cigaba da bawa Junaid madara a baki,
Laila ce ta zuciyo tace “ke magana fa nake miki kodai keɗin kurmiya ce..”
Ayush sake yin murmushin tayi ga dimple yanda yake ta lotsewa, ta ɗago da manya-manyan eyes ɗinta tana kallon Lailah, murya a sanyaye tace “me kike son sani…?”
Laila tana ɗaga murya sama tace “alaƙar dake tsakaninku nake son sani..”
Ayush lumshe ido tayi ta sake buɗesu kamar mai jin bacci tace “sanar miki bashi da wani amfani,”
Laila tace “oh hakane ko! to kawo madarar ni ya dace na bashi ba ke baa…”
Ba takuri Ayush ta miƙawa Laila madarar tana faɗin “gashi nan duk ba wani abun damuwa bane, akan namiji bai kamata kina tada jijiyoyin wuya ba, gaki ga oga Junaid ɗinki…” tashi Ayush tayi ta bata wuri ita kuma ta zauna a wajen da Ayush ta zauna tana hararar Ayush,
Ita kuma Ayush martanin murmushi take jifarta dashi, Ayush tana da kishi sosai amma sai dai kishinta bana hauka bane sannan bata bayyana kishinta, abunda Laila tayi mata ya sosa mata rai sai dai bata nuna ta damu ba…

( *masu suna Aishat kenam, duniyan kishi da kuma sani yakamata*)..

Ayush kallon Doctor Hasheem tayi taga itama kallonta yake yi, abunda ya sanar mata ne a asibiti ya faɗo mata a rai cewa yana sonta..
murmushi ya sau mata itama martani ta mayar masa.

Laila ce ta ɗebi madarar a spoon ta kai saitin bakin Junaid da sauri ya kawar da kansa gefe ganin ba Ayush ba ce, tayi akan ta bashi madaran nan amma Junaid yaƙi buɗe bakin,
ƙololuwar baƙin ciki ne ya ishi Laila kamar zata rausa ihu haka ta ajiye cup madarar a saman gado ta tashi, sai data taka ƙafar Ayush kafin ta wuce ta zauna akan kujerar ɗakin,
girgiza kai kawai Ayush tayi ta koma ta zauna ɗaukar cup tayi ta cigaba da bawa Junaid madarar yana buɗe bakin a hankali yake motsi da bakin, da zarar madarar ya ɓata masa bakin sai ta sa handkerchief ta goge masa,
Laila da Doctor takaici kamar ya hallaka su da kuma kishi, duk babu wanda yayi magana a wani har sai da mommy ta shugo tana faɗin “ha’a Laila Autar mu yau kece a gidan namun..? shuru Laila bata kulata ba tanata turo baki, sai da Dr yayi ƙarfin hali yace “wallahi kuwa mommy munzo duba jikin ogah Junaid ne”
mommy tace “ayyah ai kuwa kun kyauta ga Junaid jiki da sauƙi”
ta kalli Ayush tace “Ayushert kije ki ɗebi abinci kici kina zaune da yunwa a jikinki, kawo madarar zanyi feeding ɗinsa”
miƙe wa Ayush tayi ta fice daga ɗakin, itama Laila tsabar neman masifa tashi tayi tana cewa “nima yunwa nake ji bari naje naci…”
tazo fita kenam Dr ya riƙe hannunta yana girgiza mata kai, cikin zafin rai ta finciki hannunta tana gunaguni ta fice a ɗakin…

samun Ayush tayi a kitchen tana faɗin “ƴar matsiyata an samu guri, Yayana ya sanar mun cewa Mommy ce ta temake ki bakida kowa baki da komai, daman daga gani ke ƴer matalauta ne..”

Juyo wa Ayush tayi da murmushi saman face ɗinta tana fuskantar Laila tace “ok kinyi ƙoƙari fah, na gaishe ki..” tana kaiwa haka ta juya ta cigaba da yin haɗin kayan abincin da take son ci..
ran Laila ne yayi matuƙar ɓaci tace “ke matsiyaciya banda ƙaddara mai Yayana zaiyi dake ma har yake wani nace miki, idan kinga budurwarsa haɗaɗɗiyar balarabiya sai kin kama baki saboda ta fiki komai, kuma nazo naga kinata shishshigi wa Oga Junaid, toh wai ke banda ƙwacen samarin mata ba abunda kika iya ne? kin ƙwace wa Maimoon Doctor Hasheem sannan nima kina shirin ƙwace mun Junaid to ina zaki kai su….”

Ayush juyo wa tayi tana dariya,
dariya sosai take yi har da kama ciki,
kuma darinyan yayi matuƙar mata kyau tinda take bata taɓa yin dariya irin ta yau ba duk da damuwar da take ƙunshe dashi haka ta cigaba da yin dariyan tana nuna Laila da yatsa, da ƙer ta iya dakatar da dariyan ta kama kugu tana juyawa cikin salo kamar wacce take gaban namiji tace “toh ya kika ganni! shin akwai mata macen data fini komai? gaskiya bana tunanin haka domin inda ace yarinyar can ta fini komai da Doctor Hasheem bai gujeta ya koma kaina ba, kodai farin jini nane yayi yawa haka, wow gashi inata rikirkita mazan mutane wasu suna barin ƴan matan su suna dawowa kaina wooo ni Gimbiya Mayushert Ɓingel Abbanta ta ƙarasa maganar tana ƙwashe wa da dariya..”

Baƙin ciki duk yabi ya ishi Laila ji take kamar ta shaƙeta , ta ja dogon tsuka tana faɗin “da ba’a san asalin ƙarago ba sai ya ce shi ɗan kamfani ne, meye haɗinki da masarauta har kina ƙiran kanki da wani Gimbiya matsiyaciyar banza, to inaso ki sani Oga Junaid yafi ƙarfin ki, gwara ma ki kama Doctor shima manage zaiyi da ke wannan kuma ki kiyayi haɗuwar ki da Maimoon domin kararayaki zata yi, munafukar banza son maso wani ƙoshin wahala…”

Ayush murmushi tayi sannan tace “eh naga alama Yaya Junaid yana matuƙar ƙaunar ki tinda har kika bashi abinci a baki yaƙi ci ya kawar da kansa gefe idonsa kuwa akaina..”

Kawar da kai Laila tayi gefe cikin takaici ta nufi gurin electric gas ta tsaya sannan ta kunna! idonta yayi jawur ga hawayen dake tsiyaya daga cikin eyes ɗinta tace “idan kina son ranki da lafiyarki ki rabu da Oga Junaid domin shiɗin nawa ne….”
ita ma Ayush matsowa daf da Laila tayi ta zazzaro manya-manyan eyes ɗinta sannan tace “idan kuma naƙi fah?…”
Laila ce ta hura iskar bakin ta sannan ta juyo a wahalce ta cafki hannun Ayush ta ɗora akan electric gas wanda ya yi jaaa kunnawan da tayi,
wani irin ƙara Ayush tayi sai da Mommy da Doctor suka razana da gudu suka sauƙo downstairs kai tsaye kitchen suka nufa,
banda Junaid wanda aka barshi a zaune saman gado, shima saida ƙirjinsa ya buga jin ihun Ayush gashi ba halin tashi balle yaje yaga abunda yake faruwa ba kuma magana sai hawayen da ke zuba daga cikin ƙwayar idanuwansa,

shigar su kitchen suka tarar da Laila ta danna hannun Ayush kan electric taƙi ɗaga hannun,
ita kuwa Ayush har ta fara shiɗe wa da ƙer Doctor ya finciki Laila ya zabga mata mari har sau uku ya jefar da ita ƙasi, bakin ta kuwa ya gagara mutuwa sai cewa take “sai dai ka kashe ni wallahi indai akan Oga Junaid ne, sai na hallaka ta! akan wannan matsiyaciyar zaka dake ni…..” ta fashe da kuka.

Mommy kuma rungumar Ayush tayi sosai tana riƙe da hannunta duk fatar hannun ya ƙoƙƙone, sai naman hannun kake gani ta gagara yin kukan ma sai shiɗewar da take yi, ta kwantar da kanta saman kafaɗar mommy….

miƙewa Laila tayi tana faɗin “wannan raɗaɗin da kike ji a hannunki haka nima nake ji a cikin zuciyata da zarar an kusanci Oga Junaid, tana kaiwa haka tayi ficewar ta daga cikin kitchen….

 

Domin sauke CikakkenLittafin Sai Ku Danna bulun Rubutun dake kasa 👇👇

Matar Damisa Book 1 Complete Novel Document 

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*

Back to top button