Karfe A Wuta Chapter 78 By Ayshercool
Cak Viper ya tsaya yana bin kankarofi da kallo, zuwa kan ɗan mama da yake ta zazzaro idanu.Kankarofi ya haɗiye wani abu mai ɗaci, saura ƙiris ya yi loosing control ɗin sa, saboda yanayin da ya ga Viper da Nabila.Viper ya a janye hannunsa a hankali, ya tsaya a tsakiyar ɗakin, su kankarofi suka shigo.”Meya kawo ka in da nake?” Yayi maganar a kausashe.”Haba ƙanina, mayar da wuƙar mana, abun rabo ya ƙare, miƙa hannu na menene, bai kamata ace zuwa yanzu muna cigaba da wannan abubuwan ba, ko da ran jauhar, ko babu mallakinka ce, matarka ce dan haka ba zan din ga bibiyarta ba, balle yanzu da babu ranta, ka sassauta wannan kishin dan Allah. Ga Anas, wato ɗan mama yaronka na hannun damanka, da duk wani nasarar aiki da muka yi a kanka, ya faru ne saboda ƙoƙarin sa, sai dai kan mu kai ga bayyana maka komai, ashe ka gano shi, ya gudo wurina hankali a tashe, ya ce na taimake shi, ba zai iya jure hukuncin da zaka yi masa ba, na zo on his behalf, na bayar da haƙuri kuma nayi maka bayanin komai”Viper ya bi ɗan mama da wani irin kallo, ɗan mama ya ce “Na shiga uku, dan girman Allah Oga Viper kayi haƙuri, tursasa mini aka yi, wallahi bani da niyyar cin amanarka, ban taɓa cutar da kai ba, ka san ina yinka, kamar yadda ka ke yi na, kayi mini rai saboda Allah”Alhaji mu’azzam ya ce “Ya isa haka Anas, ni yakamata na wanke ka” duk maganar nan, Viper idonsa na kan ɗan mama, ɗan mama ya sake maƙalewa a bayan Kankarofi ya ce “Gaskiya daga nan kayana zan tattara na gudu Cadi, kallon nan da yake yi mini, tsoro yake bani, bana tunanin zai yafe mini, da ƙyar idan bai saka na gana da Russia ba”Kankarofi ya riƙo hannun ɗan mama, suka ƙarasa gaban Viper, ya numfasa sannan ya ce “Lokacin da uban gidanka yana raye, Dodo, ka fi ni sanin waye shi, ka fini sanin hatsarinsa da imaninsa. Babu wanda ya bawa damar sanin sirrikan da yake da su, kuma ya sani sai kai.Duk da shi ma mai aikata laifi ne, amma yana yi wa hukumomi amfani sosai wurin kama masu laifi, daban-daban.Ya baka horo na musamman, ta yadda yake gane masu laifi, komai kamalarsu, yadda yake iya gane idan akwai kayan laifi a wuri, bai tsaya nan ba ya saka aka baka horo na musamman, a kan fasahar na’ura mai ƙwaƙwalwa.Manyan ƙasar nan na mu’amala da shi sosai da sosai, dan ya san duk wasu hanyoyi da za a iya shiga da fitar da kayan laifi, ciki da wajen ƙasar nan, ba tare da ta an kama kaya ba, sukan haɗa kai da shi, su bashi dukiyoyin su, ya yi musu kasuwancin ƙwayoyi da sauran kayan laifi, ya ruɓanya musu riba a shekara”.Viper ya ce “Duk meye amfanin dawo da abin da ya riga ya wuce, abin da na riga na sani, kar ka aibata gawar uban gidana”Kankarofi ya ce “Ba aibata shi nake yi ba, kayi haƙuri na sadaka da gaɓar da nake son na kai ka. Dodo yayi shirin yin murabus, bayan ya koyar da kai manyan abubuwa, da ka iya zama makamin rusa wasu daga cikin manyan hanyoyin aikata laifuka da ba kowa ya sani ba.Daf da zai mutu, ya danƙa amanarka ga manyan mutane da ya yarda da su, ciki har da shugaban hukumar NIA na wancan lokacin, ya basu tabbacin zaka iya basu gudunmawa ta kowane ɓangare, sukaɗai ne hukumar da ya yarda ya damƙa amanarka a hannunsu, duk da kasancewar baka ji, amma kai babban makami ne, ka san manyan sirrukan da bayan shi babu wanda ya sani.Bayan mutuwar dodo, sun buƙaci kaje su baka horo, kayi aiki da su, amma ka ƙi, saboda zuciyarka da tunaninka na kan ɗaukar fansa a kan madaki, kuma rashin yadda ya sanya ka sake cewa ba zaka je ba, dan baka da tabbacin ta wace hanya zasu yi amfani da kai.Bayan aurenka da jauhar, bayan na shiga damuwar rashinta, wataran muna hira da cousin ɗina, wanda shi ne aka danƙa amanarka a wurinsa, muna hira, yake bani labarinka, a nan na gano cewa lallai kai ne ake magana a kai, na cigaba da matsa masa, a kan lallai suyi ƙoƙarin su ga sun ɗauke ka, zaka yi musu amfani sosai, a lokacin ina fatan silar aikin, ka daina wani abun, kuma ka samu hanyar kula da Matarka.Har bincike na saka aka kuma yi mini sosai a kanka, a nan na gano kana aiki da Indabo, abin ya ɗaure mini kai ya bani mamaki. Bayan wani lokaci, ban san meyafaru ba, na samu labarin ka je ka basu haɗin kai, an kama ɗan gidan indabo a Mexico, da laifin safarar cocaine, duk da babu wanda ya sani, amma ni ina da hanyar samun bayanai na a kanka.Na cigaba da fatan Allah yasa daga haka su hilace ka, ka amince da aikin nan, amma sam baka da intrest a kan haka.Wasu lokutan Hafsa kan bani labarin, irin soyayya da ƙaunar da ka ke yi wa jauhar. Kwatsam na samu labarin mutuwar ta, wai ka sha miyagun ƙwayoyi ka kasheta, sai dai sam ban ji na yarda ba.Daga yadda na bibiyi case ɗin silently, naga sam babu adalci, a yadda aka gudanar da binciken da gurfanar da kai ɗin ma a gaban kotu, kuma na samu labarin abokin gabarka, Madaki shi ya maye gurbin aikinka, a wurin Indabo.Ni na saka aka kamo Anas ɗan mama, aka matsa mini shi, yadda yakamata kasancewar sa, yana cikin tsagerun dabar Madaki.Shi ya tabattar mana da Madaki ne ya karɓi kwangilar kasheka a wurin Indabo, amma azal ɗin ta hau kan matarka.A lokacin shugaban ƙasa ya samu nasara a tenure farko, kuma yayi mini S.A ɗin sa na fannin tsaro, haka zalika ya tafi da ɗan uwana a matsayin shugaban hukumar NIA.Sosai nake biyan ɗan mama, ya koma wurin su Walid, tun suna korarsa, suna hantararsa, har suka saki jiki da shi a dabar su, duk da kasancewarsa yaron madaki, suka bashi cikakkiyar kariya daga Madaki, yana reporting duk wani motsinka a gareni, da kuma hukumar NIA, hakazalika ni ne nake tura maka saƙonni. Tabbas nayi amfani da kai dan cimma nawa muradin a kan indabo, kuma taimakonka nayi, sauran abin da ya faru ka sani, ni nake sanya a goge duk wani sahun laifi daka aikata, ta hanyar amfani da jami’an Civil defense, kan daga baya, hukumarku ta karɓi ragamar cigaba da kula da kai, tare da turo maka gayattar dawowa ka cigaba da aiki da su ta hanyar ɗan mama, da yake ajiye maka rigunan aiki, ina nema masa afuwa, shi ma umarni aka ba shi da dole ya bi”Viper ya din ga haɗiyar wani yawu mai zafi, yana son yayi magana, Nabila ta dafe kanta ta ce “Wannan wane irin abu ne wai, gaba ɗaya sai juya mini kaina ake yi, na kasa gane komai, wai menene haka” tayi maganar cikin ɗaga murya, tana dafe kanta. Viper ya juya ya koma in da take, ya durƙusa ya ɗauki hoton Jauhar da yake ƙasa, kawai Nabila ta tafi zata faɗi, idanunta a lumshe, ya riƙe ta, amma ya kasa magana,a hankali ya ja ta, ya mayar da ita kan gadonta.Ta ce “Bana gani, duhu nake gani, kaina zai fashe” kankarofi ya nufo gadon, amma Viper ya ɗaga masa hannu, ya ce “Excuse us please”Kankarofi ya tsaya yana kallon Viper, Viper ma ya ƙura masa ido.Barrister Habib ya ce “Ina son zan yi magana da ita”Viper ya ce “Ka jira tukuna” Kankarofi yayi musu alama, da su fita, haka duk suka fice.Nabila ta dafe kanta, ta cigaba da kuka, ya ce “Wai kukan me ki ke yi haka?””Ni ka rabu da ni dan Allah, ka ƙyale ni, so ka ke na haukace, gaba ɗaya kun ruɗa mini kai, sai ƙara bijiro da wasu abubuwa ku ke yi da ban san da su ba, ni ka rabu da ni”.”Ki tsaya ki saurare ni””Ba zan saurareka ɗin ba, ba na son jin komai, ni ka rabu da ni””Am talking and you are misbehaving” yayi maganar cikin tsawa.A razane ta dafe kanta, ta faɗo daga kan gadon, ta takure a wuri guda tana kuka.Ya tashi ya sake dawowa gabanta, amma ta hau jifansa, da abun da duk ta samu a kusa da ita. Shiru yayi yana kallonta, yana tuna lokacin da jauhar ta burkice masa, da yayi mata laifi, ta din ga jifansa da kwanuka, yayi ajiyar zuciya ya kira wayar Asibiti. Mintuna kaɗan likita ya shigo, ya tarar da Nabila kamar mai shirin zarewa, ya yi mata magana, amma tayi masa shiru.Ya fita ya dawo da allura, ya kama damtsenta zai yi mata, taƙi tsayawa, sai da Viper ya riƙeta aka yi mata, sannan jikinta ya saki ta hau lumshe ido.”Viper, garin yaya ta zama haka lokaci guda? Ba ta fara samun sauƙi ba?”Viper ya ce “Ta ɗan samu damuwa ne, idan ta farfaɗo ta samu sauƙi, kawai a sallame mu”Likitan da yake sanye da wandon sojoji ya ce “Viper, discharge kuma? Why? Ba haka aka shirya ba, tana ƙarƙashin kulawar hukuma, kai fa shegen taurin kai ne da kai, sai ka janyo wata matsalar tukuna?”Viper ya ce “She’s not safe here, zamu bar wurin nan””Zuwa ina kuma? Akwai wanda zai shigo cikin barrack, ya zo asibiti yayi mata wani abu ne?””John, i want her to be discharged”John ya ce “Ko nayi discharging ɗin ta, ka san ba zata bar wurin nan ba, sai an bamu izinin hakan. Let me help you put her to bed, she’s already sleeping on the floor” wani irin mugun kallo Viper ya yi masa, ya ce “Ohh sorry” ya juya ya fice.Viper ya sunkuya yana kallonta, fuskarta ta koma ja, sai tsatstsafar da gumi take yi, da gani baccin na dole ne kawai saboda allurar da aka yi mata.Zai iya cewa ya bai taɓa ganin mace mai naci, da tsantsar jarumta, kamar Nabila ba.Duk da baya son taɓa ta da yake yi, amma dolensa ya ɗagata ya mayar da ita kan gadon, ya gyara mata kan gadon, ya juya ya fito.A waje ya tarar da Alhaji mu’zzam da barrister Habib, da ɗan mama a zazzaune.Ya taka ya ƙarasa gaban Alhaji mu’azzam, ya ce “Meyasa ka zaɓi irin wannan lokacin, ka gaya mini wannan maganganun a gabanta? Na gaya maka ni zan kawo ƙarshen wannan lamarin, tun da ni ya shafa, abu ne mai nauyin gaske da ɗaukarsa ba lallai ya zama abu mai sauƙi a gareta ba. Dan haka bana buƙatar ka a cikin abin da ya shafeni ya shafi abin da ya shafe ni. Wadda ta haɗa ba rabonka ba ce ba, ban san dalilin da zai sanya ka din ga bibiyar rayuwata ba kamar kana bi na bashi ba””Muddin za a bayar da labarin jauhar, dole mu’azzam zai fito a ciki, ban cigaba da bibiyarka dan ina neman wani abu a wurinka ba, na bibiyeka na taimake ka ne, domin mu taimakawa juna, daga ni har kai, buƙatata ta biya kaima taka haka, naga bayan indabo, kai kuma ka ɗauki fansar tozarci da zaluncin da aka yi maka. Ban da ƙaddara ta Ubangiji, na rigaka ganin jauhar, kuma aurenta nayi niyyar yi, amma Allah ya nufa matarka ce, na so jauhar so na haƙiƙa, amma na kawar da kai, duk na shiga tashin hankali jin irin mutumin da ta aura, yanayin zamanku daga baya ya sanya na samu kwanciyar hankali, kisanta da abin da aka yi maka ya bani ya sanya na tausaya muku nake bibiyarka.Nabila ma na rigaka ganinta, ni ba a garin kano na fara ganinta ba, tun a Abuja wurin da aka basu rantsuwar zama cikakkun lauyoyi. Sai da na kusa rasa hankalina da tunanina, saboda tsananin tashin hankali da ruɗewa, har sai da na zata ko matsalar ƙwaƙwalwa na samu, saboda damuwar kisan gillan da aka yi wa jauhar.A lokacin ban yi ƙasa a gwiwa ba, na tashi yin bincike a kanta, har zuwa wannan lokaci, nake bibiyarku daga kai har ita. Muddin ba butulci zaka yi mini ba, na taimakeka Aminu, ko nayi maka laifi a wani wurin, wani wurin na taimake ka”. Sai da ya gama tsaf Viper ya ce “Na nemi taimakonka ne? Wane irin taimako ne kayi mini kana yawo da hankalina, ka yi mini shi a munafunce? Ka din ga wasa da hankalina kana ɓoye kanka? Madalla da abin da ka yi, amma ina buƙatar abin da ka ke yi ya tsaya a iya nan, Nabila da abin da ya shafi rayuwar ta hurumina ne, daga nan idan ta farfaɗo zan bar wurin nan da ita””Waye ya baka wannan damar? A ƙarƙashin kulawata take ba taka ba, naje na samu mahaifinta ma, na sanar masa da hakan, sai dai kai ka bar nan wurin, amma Nabila na tare da mu””Don’t cross the boundaries! Ban ƙi ayi mutuwar kasko ba, ba na wasa da duk abin da ya shafi marigayyiya, a kanta ba abin da ba zan aikata ba, idan da na koma na ɗauki wannan rigar ce, zan cireta na ajiye, kar ka sake kusanto in da nake, bana buƙatar taimakonka”Kankarofi ya ce “Jauhar ce mallakinka, Wannan kuma Nabila ce””Na gaya maka Nabila ta haramta ga kowa muddin ina ganin fuskar matata a jikinta” Viper ya yi maganar yana zazzaro ido cikin matsanancin kishi, jijiyoyin kansa suka ɗaɗɗaga.Cikin hanzari ɗan mama ya fito, ya shiga tsakanin Kankarofi da Viper, barrister Habib gefe ya koma, dan gaba ɗaya Viper tsoro yake bashi.Hankalin sojojin wurin ne, ya fara dawowa kansu, suka tattaso suka nufo su, Viper sai huci yake yi.”Easy oga, ka fahimci al’amarin nan dan Allah, wallahi Yallaɓai mai ƙaunarka ne, ba ya nufin cutar da kai, ba ƙaramin taimako ya yi maka b…..”Shut up! Da na ƙyaleka ban ce maka komai ba, ka ke gaya mini maganar banza, ka kuma yi mini magana, sai na tatsule ka a wurin nan, menene na cigaba da bibiyar rayuwata dan na auri wadda ya so ya aura, menene amfanin haka?””Wadda ake yi domin ta, ta bar duniya, ba shi da wata mummunar manufa a kanka, ka fahimci hakan oga dan Allah”Ya nuna ɗan mama da yatsansa, alamar kashedi.”Viper wai me ka ke yi haka ne? Oga ne fa da kansa a wurin nan, ka ke ɗaga masa murya ka ke faɗar maganganu”Viper ya ce “Bana buƙatar sa a rayuwata, ya bar wurin nan, ko kuma ni yanzu na bari”Ɗan mama ya koma wurin kankarofi ya ce “Dan girman Allah sir kayi haƙuri, wallahi Viper yana da kirki, kar ka ce zaka cire hannunka, tsabar kishi ne kawai, kar ka ce sai ka na son Nabila sai ka aureta”Kankarofi ya ce “Yaron ba shi da kunya, ba kuma shi da ɗa’a, ban yi zaton haka daga gare shi ba”Ɗan mama ya ce “Wallahi Viper yana da ɗa’a da biyayya, kawai ka san soyyaya ba ta da gwani ko jarumi, na san dai yana da taurin kai da azabar fushi, amma wallahi duk faɗansa yana da kirki, kar ka manta, da shi nake kwana nake tashi muke rayuwa. Amma ba haka yake ba, dan Allah kar ka cire hannunka a kansa, zan yi maka proving abin da na gaya maka, ai na san maganinsa, zai nustu bari ya gama hargowar”.Ana ta fama da Viper, ya ce sai ya bar Asibitin da Nabila.Liti ne ya ɗaga wayar Walid, ganin kiran ɗan mama ne ya ce “Kai dan ubanka, ina ka shiga kwana biyu baka nan, baka sanar mana ina ka tafi ba, Viper duk ya addabe mu, ko wani rashin gaskiya ka fara ne?”Ɗan mama ya ce “A’a oga liti, akwai matsala ne, ina oga walid?””Yana banɗaki matsalar me? Tsokana ka yi ko me? Kana ina ne?””Ina cikin barikin sojoji”Liti ya ce “Iyee, ba wurin yan sanda ba sojoji? Ɗan mama me da me ka ke sha ne? Sojoji fa ka ce? Me ka yi musu?””Dan Allah ku zo, da kai da Oga walid, ku kaɗai ne zaku yi solving case ɗin nan”Liti ya ce “Kai, duk iskancina, ban taɓa tsokanar wannan mutanen ba, da babu Allah a ransu, haka kurum su tumurmusa ni a banza, su sauya mini kamanni, Allah ya ƙwatoka, bari Walid ya fito ko zai iya ƙwatoka, dama ya fi ni imani da tausayi, ko shi ko Viper, dama shi ya saba da jure wahala. Dukanka suka yi ko kuma karairayaka suka yi?”Ɗan mama ya ce “Ba ɗaya, matsala aka samu ne””To Allah ya yi maka maganinta, ya tsayar iya kanka, Allah ya sa idan su Walid ɗin sun zo su ganeka, ba su sauya maka fasali ba, su mayar da kai gorilla ko wata halittar ba”Walid ya ƙaraso, ya karɓi wayar daga hannun liti cikin tashin hankali ya ce “Ɗan mama, kana ina ne? Meyafaru meya kai ka wurin sojoji ne?””Oga walid, lafiya ƙalau fa, wani case ake yi, ina tare da oga Viper, ku yi sauri ku zo dan Allah, kar ya aikata wata ɓarnar, ku kaɗai ne zaku iya shawo kansa”Walid ya ce “Kai da Viper kuma a cikin barikin Sojoji? Garin yaya?”Liti ya miƙe ya ce “Viper kuma? Ka gani ko? Viper wasu lokutan baya lissafi ko shawara, kawai ya ɗibi jiki ya tafi, Allah kaɗai ya san me ɗan maman yayi musu, ya janyo an kama shi”Walid ya katse wayar ya ce “Muje dai mu ji menene, ka san babu yadda za ayi Viper ya bar ɗan mama ko wa ya tsokana kuwa”Liti ya ce “Ai da yake ba mutunci ne da shi ba, kwana nawa muna nemansa, da ya tafka tsiyarsa kai tsaye kuma sai ya nemi Viper ba mu ba” haka suka tafi, liti yana ta masifa.Al’amin na ɗakin da Nabila take, shikaɗai ya kasa ya tsare, ya zuba mata ido, tana ta bacci. Tun da aka yi wannan dambarwar yaƙi fita, gani yake yana matsawa zasu ɗauke Nabila.Ji yayi an buɗe ƙofa, ya waiwaya.Wasu manyan sojoji suka shigo, ɗaya ya ce “Viper, taso muje ko””Muje ina? Am not going anywhere””Meyasa ka ke haka ne, kar ka saka mu yi faɗa da kai fa”Viper ya ce “Wace azaba ce ni ba a gana mini ba, ba zan je ko ina ba, ban san me kuka haɗa kai da mutumin nan, ku yi mana ba” da ƙyar suka lallaɓa shi, suka fita zuwa wani sashe na barrack ɗin.Suna shiga wurin, ya ga liti da Walid, sai dai still ya ga kankarofi, take ransa ya kuma ɓaci, yana mamakin taurin kai da rashin zuciya irin na kankarofi.”Me kuma zan yi maka? Me kake so kuma yanzu?”Walid ya miƙe ya ce “Mai zamani”Viper ya ɗaga masa hannu ya ce “Mai laya”Walid ya ƙarasa gaban Viper ya ce “Mai zamani, easy mana cool your temper” yayi maganar yana ɗan dukan ƙirjin Viper.”Meyasa yake bibiyata, dan na auri matar da ya so aura?” Yayi maganar cikin damuwa.”Ta rasu fa yake bibiyarka, da tana raye ya bibiyeka ne?” Viper ya yi shiru.Walid ya ce “Kishi ne yake damunka, an fara yi mana bayani, bawan Allah nan, ya taimaki rayuwar ka ta fuskoki daban-daban, ka nutsu ka kwantar da hankalinka, mu taimaki rayuwar Nabila. Ba zai yiwu ta cigaba da zama a nan ba, tun da Asibiti ne, kayi haƙuri a samu kauwammanen wuri a ajiye ta, idan ya so kaima ya zamana kana tare da ita. Wancan abokin aikinta ne, kuna buƙatar ƙawarta ‘yar jarida, da sauran su, kai a tunaninka effort ɗin ta kawai ya isa ya sanya ku yi Wannan nasarar? A Nigeria fa muke, dole sai da wa ka sani wa ya sanka, ka danne koma me kake ji, mu fuskanci gaskiya.Butulci da manta alkhairi ba halinka bane mutumina, ka ajiye kishi a gefe, muna buƙatar a bi mana hakkin jauhar, muna buƙatar yi wa Nabila tukuici da abu mai muhimmanci, idan ka ɓata aikin nan saboda taurin kai, ba ka yi musu adalci ba, ciki har da ita da mu kanmu da muke tare da kai” Viper ya ja jiki ya zauna a hankali.Liti ya ce “Ɗan mama duk zaman da muka yi da kai, ashe aikin munafunci ka ke yi, amma kuwa ka yi asara dan wannan ba aikin yi bane ba, kuma saboda tsabar ƙwarewa, ko da wasa baka taɓa gaya mana ba. Ni dama na daɗe ina zargin baka da gaskiya”****Miƙa tayi sosai tana addu’a, ta ji kamar gadon da take kai, ya sha bamban da wanda ta kwanta a kai, ta tashi zaune a hankali, ta ganta a cikin wani katafaren bedroom, bisa wani ƙaton gado.Tayi tsuru da ido, tana tunanin ko mutuwa tayi.Wata mata ce tayi sallama, ta ce “Kin tashi? Ga banɗaki nan idan zaki yi alwala ki yi wanka ki rama sallolin da ake binki”.Nabila ta ce “Ina ne nan baiwar Allah? Ko mutuwa nayi ne?”Matar ta ce “A’a, wanda suka kawo ki, zasu zo su yi miki bayani, ga kaya nan ko zaki canza”.Ta tashi a hankali tana addu’a, ta shiga banɗakin, ta yi wanka, ta yi alwala, ta fito ta din ga salloli, daga iya abin da ta iya tunawa, ga wata irin yunwa tana ji, gaba ɗaya ta kasa tantance meyake faruwa gaba ɗaya.Matar ta dawo, ta kawo mata abinci, amma Nabila ba ta taɓa ba, ta takure a gefe.Viper ne ya shigo, ta ɗago kai ta ƙura masa ido, har ya ƙarasa gabanta, ya zauna ya ce “Sannu, ya jikin?”Ta ɗan yi shiru sannan ta ce “Kamar nayi kuskuren yinƙurin taimaka wa rayuwarka, kana ƙoƙarin rusa tawa, ta hanyar ganin ka haukata ni, me nayi maka haka? Kuma ina ka kawo ni nan?””Ba ki yi kuskure ba, domin kuwa kin yi sara ne a kan gaɓa, kuma zaki alfahari da ƙaddarar da ta haɗa ni da ke””In yi alfahari bayan na haukace ko?”Viper ya girgiza kai ya ce “Ba zaki haukace ba, tambayoyin da nayi miki, haryanzu nima ina buƙatar samun amsarki, sai dai bani da tabbacin samun amsarsu duka.Amma bari mu gani, ko a cikin abin da zan gaya miki zamu gano bakin zaren, rayuwata kamar ƙwallon ƙafa take, daga wannan ƙafa zuwa wancan, daga wannan tudu zuwa wancan rami.A haƙiƙanin gaskiya, ban yi shekaru biyar a gidan yari ba”. Nabila ta waro ido tana kallonsa.”Nayi zaman gidan yari, cikin tsananin razani, cikin matsananciyar damuwa da ƙuncin zuciya, tare da fatan Allah ya sa da an mayar da ni kotu, a yanke mini hukuncin kisa, na huta, amma ranar da aka saka a cigaba da shari’ar ta wuce ba a cigaba ba.Azaba da wahalar da nake sha a gidan, bai ɗaga mini hankali ba, kamar yadda halin da nake ciki, bai hana wasu din ga ƙoƙarin nemana da mummunar ɗabi’a ta neman maza ba, ciki har da ma’aikatan wurin.Abin da su madaki suka yi amfani da shi suka shaƙa mini, ya cigaba da affecting ɗina.Azaba da takura, ya sa na zame musu mahaukaci, na danne wanda suke cewa sarkin gida, na kusa janyo maƙogwaronsa waje, nayi masa dukan mutuwa, saboda sun zata dolo ne ni, duk da sun san labarin waye ni, prsion ɗin ta sha banban da wadda ake kaini.Suka ajiyeni a wani wuri, suka din ga gana mini azaba, wai nayi yinƙurin yin kisan kai, ba wanda ya duba abin da ya neme ni da shi. Aka ajiyeni, babu wanka, babu wanki, babu ci babu sha, sai azabar duka. Wurin ga ƙazanta da rashin tsabta, a haka kuma a kan fito da ni, ace za a saka ni aikin wahala.A halin da nake ciki, na tsinci wani ɗan ƙarfe, da zai iya zama makami, na farwa wani, dan fuskar madaki na gani, sai da aka ƙwace shi da kyar, na huda masa wuya, sannan naga ashe ba shi bane ba, ƙwaƙwalwa ta ce ta fara samun matsala, banda kururuwar da nake yi wasu lokutan, ina kiran matata da ɗa na, tare da alwashin kashe madaki. Aka rabani da sauran fursunoni, aka ce na haukace.Watarana, cikin dare ina kwance, na san idona biyu, amma bakomai nake ganewa ba, fatana na farka daga baccin da nake yi, na ganni tare da matata.Kawai wani mutum ya saka mukulli ya buɗe in da nake, ya fara lalubena, duk a galabaice nake, kwana uku ba abin da aka bani na ci, sai na tsaya naga me zai yi mini, kar nayi masa wani abun, na je ƙwaƙwalwata ce take gaya mini shirme, kamar yadda ta saba. Sai na ji bai nufi yi mini lalata ba, kawai ya soka mini wani abu, kamar allura a cinyata, ya fara zuba mini wani abu mai tsananin zafi a jikina, ruwan allurar na shiga, ina jin kamar ana fizgar naman jikina, a take na kurma ihu, na tashi na shaƙe shi, ina dukansa, ina cewa shi ya kashe jauhar, sai na kashe shi. Ina dukansa jikina yana ƙara sanyi, kamar ana zare mini laka.Aka zo aka raba ni da shi, nayi masa jina-jina, ni kuma na faɗi a wurin, basu bi ta kaina ba, suka fice da wancan. Ina kwance na ji wani abu mai sanyi na bin hancina, a taƙaice dai, kasheni yayi yinƙurin yi mutumin.Washegari ina kwance kamar gawa, ina jin duk abin da ake yi, amma ba zan iya motsi ko magana ba, aka ɗauke ni, aka ce za a kai ni Asibiti, ayi mini magani, ashe wasa farin girki, maimakon a kaini asibiti, sai aka yi wani wurin da ni…….
Ayshercool 08081012143


