Hausa novels

Ajiya A Duhu Book 1 Page 9 Complete Novel

*_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU….💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_**_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._*_My TikTok account 👇_*https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1*_Instagram👇🏻_*https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv*_Arewabooks_*Read My Book “AJIYA A DUHU” on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_🅿️➖0️⃣9️⃣______________Lady’s collection and more Zumar kibaZumar breast Zumar hips Zumar infection Zumar sliming Zumar sabon budurci Back to virgin Abayas Atamfa LessHijabs Supplements Kitchen items and more Muna maraba da masu siyan Daya ko 08169307477Address bayan gidan drugs katsina State. Kayanmu nada inganci da zasu birge mai saye fiye da yanda yake zato. Maza ku garzayo kada ayi babu ku._______________………Tunda suka fito ya zuba mata ido daga inda yake tsaye jikin mota. Itakam sam bata lura da shi ba tana ta ƙoƙarin gyara kayan data zubo a handbag ɗinta dataƙi rufuwa. Sai da suka iso gab da shi ta tsinkayi muryarsa yana gaida Ammie. Yayinda Amrah ta taɓota itama tana gaida Ammien. Ɗagowa tai ta dubi Amrah ɗin, suka sakarma juna murmushi, harta maida kanta sai kuma ta ɗan ɗago dan sai yanzu hankalinta ya kai garesa sosai. A take ta shanye murmushin saman fuskarta ziciyarta na takurewa waje ɗaya a ƙirjinta. Tabbas da tasan tafiyar nan tare zata kasance musu ALLAH duk yanda zatai da sai tayi ta zame kanta a masu yinta. Amma yanzu babu yanda ta iya dole ta dake. Ganin su Ammie sun shige itama ta fara ƙoƙarin shiga kusa da su amma sai Amrah tai saurin rufe murfin tana faɗin, “Kije wajen Yaya mana gashi can ya buɗe miki”. Tsaye tai kawai tama gagara cewa komai, koda ta saci kallon Ammie sai taga ta ɗan harareta, dole ta shiga kusa da shi ɗin tana faman sauke ajiyar zuciya. Ɗan karkatowa yay inda take kaɗan kamar zai ɗauka abu a ƙasan ƙafafunsu. Cikin raɗa ya furta, “You look so good dear”. Kasa cemasa komai tayi, sai ma takurewa data ɗanyi jikin kujerar, yayinda shi kuma ya ɗaga yana gyara zamansa tamkar bashi yay maganar ba dan fuskarsa sam babu wani walwalan kirki. Sun fara tafiya shiru motar babu mai magana. Sai da suna gab da barin titin anguwar gaba ɗaya kamar ance ta kalla hannunta idanunta suka sauka akan agogon da Didi Shahidah ta ɗaura mata. Ba ƙaramin bugawa ƙirjinta yay ba har kana iya ganin yanda maƙoshinta ke kaiwa da komawa a wuyanta. Ta ƙurama agogon ido wani abu mai shegen nauyi na sake saukar mata a dukkan illahirin jikinta. Bata masan wani ƙarfi yazo mata ba tasa ɗayan hannunta ta fincike agogon, kamar zatai wurgi da shi waje sai kuma ta daure ta ɓalle bag ɗinta ta jefashi ciki batare data zuge zip ɗin ba ta maida kanta ta nannaɗe cikin ƙafafunta data ɗage gaba ɗaya zuwa saman kujerar. A take wasu hawaye masu zafin gaske da raɗaɗi suka fara zirara mata. Yanda tayi ɗin sai sukai tunanin ko barci take, musamman Ammie da tasan bawani barcin kirki ta samu ba a safiyar yau dama daren. Shima Yazeed daya ɗauka barcin tayi sai kawai ya farama Ammie hira. A haka har suka iso Zaria kasancewar tafiyar ba wata mai yawa bace ba. Da yake Yazeed yasan hanya basu wani sha wahala ba nan ma suka iso. Sun sami anguwar kanta da mutane sosai balle ƙofar gidan daya kasance masha ALLAH dan har Ammie na faɗin, “Anya Yazeed zamu iya keta mutanen nan zuwa cikin gidan kuwa?”. Amsa ya bata da faɗin, “Ammie zaku iya shiyyasa ma nai parking tanan ganin yafi ƙarancin mutane. Zan bidaku ta baya ne akwai wata ƙofa dana sani Uncle na amfani da ita nasan zata kasance buɗe yau kodan baƙinsa”. Cikin gamsuwa Ammie ta ce, “To Alhamdullah hakan ma yayi”. Sun firfito yayinda a kallo ɗaya Ammie ta fahimci Manaal tayi kuka duk da gilashin dake a idonta. Sai dai ta fassara kukan nata da zaman gaba da aka sakata yi ne dole. Dan haka ta watsar da ita tama haɗe fuska. A wannan yanayin suka shiga gidan ta inda Yazeed ɗin ya faɗa. Aiko sai suka samu sauƙi jama’a anan sai falon Uncle ɗin ne ma da mutane dan akwai takalma kusan ƙafa bakwai a wajen masu ƙyau. Wucewarsu sukai zuwa cikin gida dan itama Ammien ba wannan ne zuwanta na farko ba. Hakama Amrah. Maanal ce dai bata taɓa zuwa ba dama sai yau ɗin. Amma ta ɗan san yaran gidan saboda suna zuwa can gidan nasu lokaci-lokaci… ★———– Babu jimawa da shigewar su Maanal tawagar ango da abokansa suka iso ƙofar gidan. Cikin tsari da nutsuwa tarin motocinsu suka layantu dai-dai inda Yaya Yazeed yay parking motarsa. Firfitowa duk suka shiga yi, kowa ka kalla shar da shi cikin dakakken yadi mai shegen ƙyau da tsada, wasu kuma shaddoji. Sai shima ango dake sanye da shadda fara ƙal tanata maiƙo da ɗaukar idanu. Sun gama firfitowa sai motar dake kusa data Yazeed ce kawai wanda ke ciki baida alamar fitowar, sai da angon ya juya yana ɗan kalle-kalle da faɗin, “Wai Uncle fa?”. Duk motar suka kalla. Kafin wani a cikin abokan yace, “Bai kai ga fitowa ba kamar ma suna magana ne da Uncle Nass”. “Oh ai fa an haɗu. Ni dai suyi su fito kar a fara neman waliyyai aga duk basa kusa. Bara ma na taɓa su Uncle Fawzan suma”. Dariya abokan nasa suka sanya masa da shaƙiyanci. Yayinda yay gefe yana dariya. Wanda dai ya ambata da Uncles basu fito a motar ba sai kusan bayan mintuna talatin, suma ɗin dai ba tsoffi bane, matasane da shekarunsu ya haura talatin kaɗan, ɗaya ma zai iya girman ɗayan. Wanda bai kai shekarun ba dake sanye cikin yadi milk ne ya fito ta sashen da motar Yazeed take. Ɗan jingina yay da motar yana amsa waya kansa a sunkuye ta yanda ko fuskarsa ba’a wani gani da ƙyau. Yaci fin mintuna biyu a haka kafin ya katse wayar yana mai kai wa duƙe ya ɗauki abinda idonsa ya sauka a kai tun fitowarsa dake yashe a ƙasa. Agogo ne silver na mata mai ƙyau sosai, juyawa yay ya kalla motar daya jingina batare da yayima agogon wani kallon tsaf ba. Har ya kai hannu zai aza agogon saman motar da tunanin maybe masu motar ne suka yadda sai kuma ya fasa. Tunanin ajiyewa yay a hannunsa dan maybe su haɗu da masu motar sai ya basu, kada ya ajiye kuma wani ya ɗauka dan a ɗan kallon fisha da yay ma agogon ya fahimci mai daraja ne da za’a iya sayensa da kuɗi masu yawa. Motar da suka fito ya buɗe ya jefa agogon sit ɗin mai zaman banza daya zauna dan ɗayan ne yayo driving ɗin. Daga haka ya juya abinsa kawai…. ______________★ Duk da yawan taron jama’a bai hana ai musu tarba ta musamman ba da girmamawa da mutuntawa. Dan can ƙuryar ɗakin amaryar gidan aka kaisu tare da musu sauka ta musamman da abinci da kayan ciye-ciye irin na biki. Sai nan nan Hajiya Majdiya keyi da Ammie dan tuntuni take son su jone su zama ƙawaye Ammien ce dai bata maida hankali ba. Ita kuma ba komai yasa hakan ba sai sanin uwargidanta jone suke da Hajiya Yaya 5&6, ko bikin nan ma dan na yarinyar matar tsakkiya ce shiyyasa Hajiya Yayan bata zo ba saboda suna matuƙar adawa da juna. Ita kuma aminiyar Hajiya Basariyya ce dan ita tun sassafe ma tana nan Zaria ɗin da duka yaranta kuma kwana zasuyi dan har Abuja inda za’akai amarya zasuje ma. Ƙorafin da take tayi yasa Ammie bama su Maanal umarnin cin abincin. Amrah ce ta zuba ma Ammie sannan ta zuba musu. Maanal na cewa ta ƙoshi Hajiya Majdiya tace, “Haba ɗiyata kada kimin haka mana, idan kuma baƙya sonshi na canjo miki wani ko na dafo miki yanzun nan”. Da sauri ta ɗauki spoon ta saka cikin abincin, hakan ya saka Amra kwashewa da dariya. Sunci abincin Ammie da Hajiya Majdiya na hira sai ga wata budurwar yarinya ta shigo ɗakin. Zasu iya zama sa’anni dasu Maanal, tayi ƙyau cikin lass da nake ƙyautata zaton ankonsu kenan dan ƴammata da yawa na dashi a wajen bikin. Tafawa suka ɗan yi da Amrah alamar sun san juna sosai sai kuma ta ɗan zunguri Maanal cike da tsokana ta furta, “Kurman Ammie”. Hararta Maanal ta ɗan yi duk da ba wani sabo sukai ba gaskiya, dan ko gidan sukaje iyakar Maanal ɗin da su gaisuwa ne. Cikin dariyar da suke ta gaida Ammie, yayinda Amrah ke faɗin, “Amma fa sunan nan ya dace da ita sosai, Najwa kin iya saka suna ALLAH”. Dariya Ammie da Hajiya Majdiya suka sake yi. Nan dai suka cigaba da tsokanar Maanal ita da Amrahn. Bayan sun tsagaita ta dubi Maman nata tana faɗin, “Ummy Uncle Rafeeq fa ya iso”. “Oh Masha ALLAH har ya ƙaraso, da’alama gudun nashi na tsiya yayi kenan. Yana ina?”. “Na kaisa ƙaramin falonki wai yunwa yake ji, sai yaci abinci zai fita wajen ɗaurin aure”. Ƴar dariya tai da faɗin, “Acici kenan mala’ikun tauna. Ga key dama na haɗa masa abincin ai. Idan kin ɗauka ki rufe min kitchen ɗin, sai ya gama sai nazo mu gaisa”. Amsa tai tana miƙewa, sai kuma ta kalli su Amrah, “Ku taso muje kunzo kun ƙunshe a nan. Amrah karfa ki bari Maanal ta koya miki halinta”. Da sauri Amra ta ce, “Da naga takaina. Maanal fa ko maijego bazata faɗa mata zaman ɗaki ba, magana kuwa yakan iya sati batayi da kowa ba”. Hararar su Maanal tayi batare data motsa ba ko yin magana. Ganin haka suka fahimci bazanje ba. Dan haka Najma tai saurin kai ƙararta wajen Ammie. “Ammie kinga wai bazata ba”. Kallon Maanal Ammie tayi dole ta miƙe badan taso ba suka fita. Kitchen ɗin ta shiga ta ɗauka basket ɗin da aka shirya kayan abincin sanan suka bi wani ƙofa, roƙonsu take akan suje kai amarya Abuja dan ALLAH. Yayinda Amrah ke bata amsa da basuzo da wasu kaya ba. Dai-dai zasu shiga take cewa baga nata kayan ba tasan zasu musu ai, kokuma idan zasu wuce Abujan su tsaya kd ɗin su ɗauki kayan. Shigarsu tasa babu wanda ya bata amsa. Falone ƙarami amma yayi ƙyau sosai cikin tsari. “I’m sorry Uncle na barka kana jira”. Ta faɗa dai-dai tana ƙarasawa gaban mutumin dake zaune ya ɗan juya ma ƙofa baya ta yanda basa ganin fuskarsa da ƙyau. Juyowa yay ya kallo ta inda suke cikin sigar harara, sai idanunsa cikin na Maanal. Cak kuwa ta tsaya kamar wadda aka buge mata ƙafafu da sanda, hakama numfashinta sai da yay rawa. Shima ɗin da wani kalar mamaki ya zuba mata idanunsa har yana ɗan warosu waje na kasa ɓoye mamaki. Sai yanda yay ɗin ya saka su Amrah kallon Maanal ɗin suma cike da tambayoyi. Lips ɗinsa ne suka ɗan motsa a hankali ya faɗi abinda ita da su duk basu ji ba. Yayinda Najma ta furta, “Uncle ko ka sansu ne?”. Maimakon amsa mata sai ya saki wani ƙayataccen murmushi kawai da kai hannu ya ɗan shafo sajensa siriri yana lumshe idanu da kauda kansa gefe. Itama Maanal janye nata idanun tayi a hankali daga garesa, sai kuma ta juya da nufin fita. Najma ce ta riƙota da sauri tana faɗin, “Kimma isa madam. Dawo ku gaisa. Ai mu wannan abin farin ciki ne agaremu Uncle Rafeeq da budurwa a yau”. Da sauri Maanal ta harareta da faɗin, “Aka faɗa miki”. “Basai an faɗa mana ba komai ya bayyana kansa ko Amrah?”. Tai maganar da kallon Amrah da jikinta duk yay sanyi. Murmushin yaƙe ta mata da faɗin, “Ai kam dai gara mu sani”. Maanal zatayi magana suka ja hannunta suka ƙarasa cikin falon dole badan taso ba. Zama sukayi ita da Amrah, yayinda Najma ta duƙa gabansa tana haɗa masa abincin. Shiko ya zuba ma Maanal ido ko ƙyaftawa baiyi. Ita kuma data ɗago taga ita ɗin yake kallo sai ta ɗan hararesa, shi kuma ya sakar mata murmushi. A haka Amrah ta gaishesa. Ya amsa mata cike da basarwa kafin ya maida dubansa ga Najma, cikin sigar tambaya yay mata nuni da Maanal. Juyawa tai ta kalleta itama da ƴar dariya a fuskarta ta ce, Ƙawayena ne kuma ƴan uwana.” “Uhm yayi ƙyau” ya faɗa yana maido kallonsa kan Maanal dai. Hakan yasa cikin dauriya da sake tsuke fuska ta ce masa “Ina yini”. Kansa tsaye ya amsa da, “Ya gajiyar tafiya? Da ƙin amsa min waya?”. Jitai kamar ta ja abu ta wulwula masa bisa kai amma dai ta daure kodan su Najma, batare data kallesa ba ta ce, “Hummm”. Shima Humm ɗin ya faɗa yana ɗaukar spoon ya fara cin abincinsa. “Oh oh mukam an sakamu a duhu, Uncle Please ka mana bayani”. “To uwar gulma anƙi ɗin. Ga ƙofa maza kama gabanki idan na gama zan nemoki. Auntyn ma kice ta hutar da kanta ma gaisa bayan an ɗaura auren”. “Oyooooo!! Korarmu ma ake, kinga Amrah taso mu ware to”. Tai maganar tana kama hannun Amrah suka nufi ƙofa. Miƙewa itama Maanal tayi dan bazata yarda a barsu su biyu ba, sai taga shima ya miƙe idanunsa a kanta kamar zai cinyenta da su………✍️✨ZAFAFAN DAI ✨1 ƘALBIM (Mamu gee)2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)3 DUNIYAR MU (Huguma)4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)Book 1:-500Book 2:-1000Book 3:-1500Book 4:-20000022419171Access bankMaryam Sani GumiShaida:- 09033181070Kati MTN:- 09032345899Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF89825722Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Ajiya A Duhu Complete Novel Document Txt

Back to top button