Uncategorized

Yadda Za’a Yi Amfani Da Kanumfar Wajen Neman Lafiya Musamman Mata Masu Ciwon Sanyi


CIWON KAI

Yana maganin ciwon kai. A shafa man kanimfari a goshi, Yana taimakawa
wajen ciwon kai wanda ke faruwa sanadiyar mura.

Idan kuma ciwon kan bana Mura bane, za’a iya samun Kanumfari guda biyar a saka a cikin ruwa kofi guda, a saka a wuta su tafasa sosai sai a saka Suger kamar Rabin cokali a ciki idan ya dan huce sai a sha ayi haka sau 2 a yini In shaa Allahu kan zai daina ciwo koda kuwa baya jin Magani ne.

Karanta>>> Ingantaccen Matsi Da Bashi Da Illah Ga Mata.

CIWON HAKORI

Yana maganin ciwon hakori. Zaka iya amfani da man-kanimfari (Clove oil) ga hakori mai-ciwo ko kuma kanimfarin
(dakakke), a jikashi kadan da ruwa a lika wajen hakori mai-ciwo. Idan mai (Clove oil) kake amfani dashi sai asamu auduga a zuba man kadan a lika wajen hakori mai-ciwo (ka danne da hakora).

Karanta>>> Dalilan Dake Kawo Tusar Gaba Da kuma Hanyar Maganceta.


WARIN BAKI


Za’a iya amfani dashi a matsayin abun wanke baki. Yana maganin warin baki (a tafashi a yawaita wanke baki dashi sau 3 a rana).


MAGANIN AMAI

 

Domin Tsayawar amai ga Mata masu ciki, a daka kanunfari biyu a sa babban cokali daya na zuma a sha yana maganin Amai ga macce mai ciki.

Don magance amai baga mai juna biyu ba kuwa, a saka kanumfari 4 a cikin ruwa kofi daya a tafasa idan ya tafasa a saka sugar cokali daya a sha.

Karanta>>> Yadda Zaku Kula Da Jikin Ku Lokacin Sanyi Kada Ya Lalace.


TYPHOID


A samu ruwa littr biyu sai a saka kanumfari kamar guda 5 a cikin ruwan a tafasa ruwan kada a sauke sai ruwan sun koma sauran littr daya sai a sauke idan suka huce sai a riqa sha Wannan yana Maganin typhoid.


CIWON KUNNE


A hada Man kanun fari da Man Ridi diga a kunne mai ciwo duk lokacin da za’a kwanta wannan yana maganin ciwon kunne.

Karanta>>> Sirrin Gyaran Nono Kashi Na Daya.

MAGANIN MURA


Ga masu su mura A tafasashi da citta/jinja (ginger) a sha a shayi.MAGANCE MAKERO/KYANDA


Ana goga Man kanumfari a wurin da matsalar tace wannan yana maganin Makero.


Karanta>>> Yadda Zaku Kula Da Fatar Jikinku A Lokacin Sanyin Nan

GIRMAN MAZAKUTA


Asamu nikakken kanumfari ko adakasa sai ajikasa da mansa ahada da man zaitun, sai ajika “gaba” dashi,idan za’a kwanta,da rana kuwa duk bayan anyi
wanka sai ashafa, wannan yana sa girman Azzakari.

KARFIN MAZAKUTA

A samu Man kanumfari duk za’a yi saduwar aure awa daya kafin a fara a shafe gaba da shi.


KURAJEN HARSHE

Don Magance Kurajen Harshe, daka Kanumfari a saka a harshen a barshi zawon wani lokaci, ko kuma idan za’a kwanta a saka in shaa Allahu kafin safe zasuyi dama.


Back to top button