Kura A Rumbu Complete Novel
“Malam idan kaje ƊAN ALJANNAH zan sauka” na faɗa ina nunowa me Adaidaitan da muke ciki saitin in da ze ajiye ni, bayan daya gama daidaita parking na sauka ba tareda na kalli Hansa’u data kalli ɗaya ɓangaren ba nace”Da ace kuturwa Allah yayi ni se inji haushi dan kince ba zaki tayani aiki ba, dake ko babu ke bazan rasa wanda zasu rufamun asiri ba” na faɗa ina miƙawa me Adaidaita ɗari biyar. Bata tankamun ba na juya ba tareda na amsa tambayar da me mashin ɗin yake mun ba akan iya kuɗi na ze ɗauka ko na mu biyun na shige kantin. Na rigada na rubuta list ɗin abubuwan da zan siya dan haka kai tsaye na shiga ɗauka cikin abinda be wuce minti sha biyar ba na gama dan ma na tarar da layi gurin biyan kuɗi. Wani Adaidaitan na tare ya ƙarasa dani kofar Nasarawa gidan Anty Labiba. Munir na ƙofar gida da abokinsa ina hango su naji raina ya sake ɓaci dan nasan ƙarshe yanzu Anty Labiba se ta tado da zancen da bana so amma ganin ya riga da ya ganni in na ce mu juya ma ze ga ai saboda shi ne yasa nacewa me Adaidaitan ya faka na sauka ina cin magani na biyashi kuɗin sa.
“Barka da zuwa Hajiya Halima” Abokin nasa wanda seda na sauka na gane Yahuza ne ya faɗa yana mun murmushi, na ɗauke kai sama ciki ciki nace “yawwa”. Kafin na miƙawa me Adaidaita kuɗin sa Munir daya iso kusada dani ya rigani, ɗari biyar ya bashi sannan ya duƙa ya shiga ɗaukar ledojin siyayyar dana zube a ƙasa. Murmushin sa me kyau yayi kafin yace”Ashe kece zaki zo shiyasa na kasa tafiya”. Na wuce cikin gidan ba tare da na tankashi ba ina ji ya biyo bayana. Anty Labiba na zaune kan tudun gurin wanke wanke tana cire hancin kayan miya ta ɗago tana amsa sallamar mu. “Aa, Munir. Ashe baku tafi ba?” Ta faɗa tana tsame hannunta daga abinda takeyi, a ƙasa ya aje kayan yana cewa
“Eh wlh, haka nan fa muka tsaya ashe rabon na ganta ne yasa” ya faɗa yana nuna ni. Na tura baki gaba ina wucewa falon Antyn ina jiyo ta tana cewa”Billahillazi dai Munir se in ce baka da zuciya, yanzu saboda Allah ba zaka bar yarinyar nan ga mata nan fululu a gari masu sonka kamar suyi me ba? Wlh idan nice kai inuwar Halima bazan sake kallo ba balle har maganar arziƙi ta haɗa mu”.
Ya shafa kansa yace”Ba zaki gane ba Anty” se tayi saurin tare shi tace “dama ta ina zan gane? To dai tun wuri gara kawa kanka faɗa ka nemi wata dan nan kusa banga Halima nada rabon gane wautar data tafka ko in ce take shirin tafkawa ba. Ita tayi asara wlh samun saurayi nagartacce kamarka me abinyi a zamanin nan” .”Bari na wuce, adai cigaba da taya mu da addu’a a kuma sake tayani rarrashinta Anty” ya faɗa jin zata ɓaro wani zancen sannan ya juya ya fita nan kuwa Anty Labiba ta dasa mitar da bata gajiya dayi tunda na watsa mata ƙasa a ido nace bana son ƙanin mijinta kuma ɗan ɗakinta. Seda na jiyo ƙarar tashin mota alamar sun tafi kafin na aje mayafina na, kujera na aje kusada inda ya zube mun kayan na shiga gaida Anty Labiba ta wani amsa mun a ɗage ni se ta bani dariya ma irin wannan ɗaukar dumar magaji da nishi. Shikenan kuma se akace dan ya mata dole nima ya mun in so shi? Kowa fa da ra’ayinsa a rayuwar nan, ni da wanda nake so shima rashin zuciya yasa har ya bari maganar ta fito bayan tun ni dashi daya furta mun na sanar masa ina da wanda nake so ba kuma na ra’ayinsa.
