Haihuwa Da Hanji Page 8 Hausa Novel
“Karen hauka ne ya cije ki? Ko stupid lunatic brain naki hauka yake karanto miki?? Are you stupid?? Ki kashe kan naki oya take this…”Muryarshi mai cike da fushi haɗe da zafi ya cigaba da sauƙa wane aradu bisa kan su ba ita kaɗai ba hatta nurses da suka san shi sai da suka sha jinin jikinsu a take, wani irin shiru ne ya ratsa ɗakin kan takun sawayenshi suka amsa ya isa ganganta riƙe da scapel (aska irin ta likitoci) ya damƙa mata a hannu ya fusgo ɗayan da karfi har canular ɗinta na fita daidai jijiyar Wrist ɗinta ya sa yatsarshi babba.”Nan! Nan kawai za ki katse ki mutu idan sha’awar wutan Jahannama ne yake ɗibarki, ba mutuwa kike ƙaunar yi kafura ki tabbata cikin azabar Allah ba? Oya yanke mana!!!”A zaune take amma sai da tayi wani tsallen tsoro saboda tsawar da ya daka mata sai da ya kaɗa ‘yar hanjin ta.”Haba Rayyan, yarinya ce don Allah ka bita a hankali mana ka ga yadda duk ka firgitata?”A zafafe yace “Za ta ci kashi ne salim? Muddin ba za ta ci kashi ba to tabbas babu zancen yaranta a lamarin ta sai tsagwaron iskanci da ƙarancin ilimin addini… Tana tunanin da kashe kai shi ne hukunci mafi sauƙi ga bawa a duk sadda ƙaddara ta ruro wutarta za ta samu miliyoyin mutane a raye ne?”Ita dai bata san a wace duniyar take ba don tsabar yadda take kaɗuwa bata sani ba a farke take ko a sume ya juyo da figitattun idanunsa da basu yi mata kala da na mutane ba ya zura mata”To bari ki ji, idan ma ba ki sani ba ki sani idan ma kin sani danne sanin kika yi to gidahumar kwakwalwarki ta tuna kuma ta yi hadda wutar Allah ya fi gaban wasa, kar ki zaci wannan wuta da kuke girki da shi duk zafi da raɗaɗin na wannan duniyar, duk irin hatsarinshi da in ya ɗan taɓa ki za ki ihu sai da aka wanke shi sau dubu saba’in kan aka jefo mana”Kanshi ya dafa yana wani jan tsaki mai tsawo saboda rabon da yayi magana haka ya manta, amma dole ya ƙarasa don zuciyarshi a tunzure take ji yake kaman ya faffalla mata maruka wa ta fi shiga cikin damuwa da zata kashe kanta? “Tabbas duk wanda yana musulmi ya kashe kanshi da gangan ya fita daga musulunci kuma zai mutu ya kuma tashi ranar gobe a kafiri… Ƙarbar kaddara mai kyau ko marar kyau na ɗaya daga biyar ɗin cikacikan musulunci. Ki yi gaggawar tuba domin a yanzu haka kin nunawa ubangiji ba ki da cikakkiyar imani ki kuma gode Allah we were there on time Nonsense…!Wani irin rawa da jikinta yake ya sa tuni askar ya zame ya faɗi ƙasa yana ba da sautin kwankwataraaaan, yadda kalamanshi suke fita a hautsine cike da zafi da ɗaci mai tarin zallar gaskiya haka su ke hautsina mata ‘yar hanji suna kaɗa hantarta kuma suna shiganta ba da wasa ba. Tun da idanunta suka sauƙa cikin nashi a karon farko ta yi saurin sadda nata ƙasa don ba za ta iya ko da gangancin jurar ganin cikinsu ba, ganin tana shirin zubewa a sume ya sa salim damke hannun Rayyan da har kaman zai rufeta da duka at any moment ya ce”Calm down please dude”Ya maimaita kusan sau uku don ya san hayaƙin kan rayyan ba kowa ne ke iyawa dashi ba, hatta shi karan kanshi wani lokacin shakkar shi yake saboda wani irin kwarjini da Allah ya zuba masa na ban mamaki, bare wannan yarinya da rubdugun rayuwa yayi mata ƙatutu.”Sister ku taimaka mata ko da allurar bacci ne samu ta huta ta kuma samu natsuwa please”Salim ɗin yayi directing kalaman to nurses ɗin, da sauri suka shiga ƙoƙarin aiwatarwa don babu wadda bai san Zafin kan Surgeon General Ryan Moh’d Khamis ba, a lokacin da suka roƙi ta kwanta ko uhmm bata yi ba ta miƙe flat zuciyarta har a lokacin tana jin shi a tsaye kyamm tsabar tsoro.Jan Rayyan da ke tsaye ya zubawa gini idanu yayi suka fice, haɗadɗen office ne mai cike da ƙawa tamkar ba asibiti ba suka shiga, fasalta kyau da tsaruwar office ɗin bata lokaci ne sai wani masifaffen ƙamshi yake fitarwa tare da sanyin Ac mai ratsa jiki. A doguwar kujera Brown mai cin mutum uku salim ya mishi masauki, ya nufi chan dungu wurin wani tsararren frigde ya buɗe ya ɗauko mishi ruwa masu sanyi ya taho ya miƙa mishi bayan ya ɓalle murfin ba tare da yayi magana ba ya karɓa kaman faɗa ya kafa kai, sai da ya shanye tasss kan yayi wurgi da goran”I need some space Salim”Maganan ya fito daga chan ƙasan maƙogoronshi in ba ma salim ɗin hankalinshi na kanshi ba ba zai taɓa cewa shine yayi maganan ba, dama kuma ya san za’a yi hakan dole ya fice ya barshi nan yana zamewa kwance cikin kujerar Dukda tsawon shi ya zartawa kujeran nesa ba kusa ba.Salim na fita ɗakin ya koma ya janyo kujera ya zauna tare da tsura mata idanu, duk da ba zai ƙira ta kyakyawa ajin farko ba sai dai tana da nata qualities ɗin na daban da ba kowa ke da shi ba kuma da matuƙar wuya a same su wurin wata macen, baƙa ce amma baƙin mai haske tana da doguwar tsiririn fuska da dogon hanci duk da idanunta ya musu kallo ne na tausayi don a rine suke a kuma firgice zai iya ƙiransu manya kuma farare, girarta kaman ita ta zana yanayin tsawon gashin idanunta da ma masu sheƙi irin na baƙaken Fulani dake kwance lublub bisa goshinta za su tabbatar maka da cewa tana da tarin suman kai, bakinta kalar peach da ya ƙara haskaka kalar skin ɗinta ya amshi fuskartata.Ta yi mishi yarinya kwarai da tunanin kisan kai, kuma ya tabbatar duk abin da zai saka mutum tunanin kashe kan shi ba ƙarami ba, ba zai ce ga iya adadin lokutan da ya ɗauka yana gwamutsa biyar da goma ba a kan matsalar yarinyar sai motsin ta ya ji, da ɗan hanzari ya mayar da hankalinshi kanta don dama tuntuni kallonshi na a gareta.”Sannu ‘yanmata kin farka?”Tsura mishi idanu ta yi tana tariyo abin da ya faru a ɗazu da sauri ta shiga dube dube tana jin gudun zuciyarta na wani irin ƙaruwa ganin firgici a idanunta ya sa ya miƙe ya isa gangarta yana furta”Natsu ‘yanmata dodon ɗazu ba ya nan, da ma matuƙar wuya ki sake ganinshi a gangarki.”Numfashi mai nauyi ta sauƙe duk da tarin tsoron da take ciki hakan bai hana kalamanshi na ɗazu na sake bijiro mata ba, wani irin sanyin jiki da tsoron Allah na lulluɓeta a take ta fara tuba hawayenta na ɓallewa take furta”Allah na tuba ya Allah! Wallahi na yi nadama Allah na san kana sane dani da kuma halin da nake ciki ya Allah ka sassauta min, Allah ka ba ni ikon ƙarbar kaddara ta a yadda ta zo min Allah ka yafe min…”Sossai take kuka har tana shiɗewa, bai hana ta ba ya barta tayi kukan sossai har tana ajiyar zuciya kan ya ɗauki ruwa ya miƙa mata, sai da ta jima tana kallon hannun nashi kan ta sanya hannu ta karɓa ta sha sossai kan ta sauƙar tare da gintsewa cikin hannunta tana sauƙe numfashi ta sake ƙura wa bango idanu.”Ya Sunanki?”Ta ji tambayar ya zo mata, kallonshi ta yi yana da tausayi haka yana da sanyin hali duk da khakin sojojin da ta ganshi da shi ba irin wanchan ɗayan ba da ko a mafarki bata fata ta sake ganinshi don kila sai ta sume.”Afeefah”Ta furta a hankali”kina da suna mai daaɗi Afeefah”.Shiru ta yi.”Ko za ki kwanta ki huta? Ko in samo miki abin da za ki ci?”Nan ma shiru tayi, a hankali kuma ko me ta tuna tace “Eh””Eh wa wanne kenan? Kwanciya ko abinci?”Da wasa yayi maganan hakan ya sa ta sake kallonshi kan tace “kwanciya””duk biyu dai Afeefah, yanzu kwanta ki na hutawa ni kuma zan je in samo miki abincin kin ga ina dawowa ke kuma kin gama hutawa sai cin abinci ko?”Ta gyaɗa kai “yauwa Afeefah”Kwanciya tayi shi kuma ya fice.Ya fi awa ɗaya da fita kan ya dawo, ya samu wani baccin ya ɗauke ta yadda kuma fuskanta da idanunta suka sake suntuma suka tabbatar mishi da ta sake wani kukan fiye ma da na ɗazu.Sossai ta bashi tausayi adu’ar samun sauƙi a ko ma menene dake damunta ya yi mata kan ya ajiye babbar ledan da ke hannunshi ya fice, office na Ryan ya koma sai dai ya samu a rufe girgiza kai yayi kan ya juya ya koma nurses station inda ya roki a duba mishi Drn da Ryan yayi referring ɗinta to don ya san ko mutuwa za tayi ba zai sake duba ta ba. Ganin Dr Sulaiman ya sa ya nufi office ɗin nashi.Dukda Captain Saleem zallar soja ne na ƙasa wato land army sai dai tarensu da Ryan ya sa kusan duk wadda ya san Surgeon General Ryan Moh’d Khamis ya san Salim, Salim shi ne ƙwallin abokin Ryan don shi kaɗai ke iya tolerating murɗaɗɗiyar halinshi da zafin Ranshi sam Ryan ba shi da hayaniya kuma ba ya shiri da mai hayaniya, ba ya dogon magana kuma ko da ido yana so idan yayi magana ka fahimce shi bare kuma in ya buɗe baki ya furta ko za ka mutu ba zai maimaita ba, yana da saurin fushi kullum a hasale yake ga ko in kula a koma menene matukar ba shi ya so yin abu ba babu mai mishi dole, sarauta da ƙasaitarshi wane sarki don har wasu kan tambayi ko shi ɗin jinin sarauta ne?A kofan office ɗin yayi knocking aka bashi izinin shiga ya sanya kai, Dr Sulaiman ya miƙe ya bashi hannu suka gaisa kan ya zauna yana dubanshi yace “Dr. Ka san yanayin aikin namu tafiya ce ta kama ni babu zato, zan tafi Kano kuma zan kwana biyu ban san ko za ka iya sallamar ta a yau ba samu in mayar da ita kar in tafi kuma aiki ya riƙeni in kasa dawowa da wuri”.Dr Sulaiman ya buɗe file ɗinta ya sake dubawa sossai kan ya ɗago yana kallon Salim ya shiga cewa “A gaskiya cap. Sallama ba zai yiwu yau ba yarinyar jininta yayi ƙasa sossai matuƙa kuma ka san hatsarin hakan, ga damuwa dake dukar zuciyarta shiyasa take ta complain ciwon kai da kirjin dole tana buƙatar kulawar likita atleast na kwana uku zuwa huɗu”.Ajiyar zuciya salim ya saki.”Dr Sulaiman ko za ka taimakeni don Allah ka kula da ita har na dawo?”Murmushi Dr Sulaiman yayi “Kar ka samu matsala In shaa Allah zan kula muku da ita, akwai wata tsohuwa dake mana aiki gida zan ɗauko ta ta zauna muku da ita har ku dawo”Godiya sossai salim ya mishi kan ya fice.Ko da ya koma ɗakin ya samu ta farka abinci ya sa ta ci yana ɗan janta da wasa yana mata hira har ta ce mishi ya isheta bayani yayi mata a kan bayan Magrib zai bar garin akwai mai zuwa ta zauna da ita har ya dawo in shaa Allah yana fata kan ya dawo ya samu ta yi sauƙi samu ya mayar da ita gida Fatan hakan ba zai haifar mata da matsala ba?Ta amsa da “uhmm” a ranta take raya a yanzu ko ɓata ta yi ɓat a duniya babu mai neman ta bare ya damu da wanzuwar ta ko akasin hakan, yanzu haka aka tambayeta ina za’a kaita bata sani ba don ko giyar wake ta sha ba za ta tunkari wurin uncle ba dolenta dai shi ne kawu, Nan ma kuma bata san abin da za ta iya riska ba Shikenan ta koma Square Zero?Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga zubo mata. “Afeefah!”

