Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 47 Hausa Novel

“Yaya Rayyan mijinki nake magana a kai girlll wlh da gaske nake miki yanzun nan Baba Musa ya ƙira ni yake cewa za mu shirya tafiya Fombina gobe sun sayi tickets already, ya ce mu shirya kaya kuma mu kintsa komai don za mu iya ɗan jimawa bamu zo kd ba.”Bata san me ta ji ba a lokacin mamaki ko tsananin farin ciki, tayi matukar taya shi murnar reconsiling da iyayenshi don dole su ɗin su ne dolenshi ko ba jima ko ba dade, ashe yana da alaƙa da sarauta? Fuskarta cike da murmushi tace “Alhamdulillah Allah mun gode maka”Wani sashe na zuciyarta kuma tsoron tafiyar take don bata san me kuma zata tarar ba, hakika ta fi jin natsuwa da kwanciyar hankali a gidan na Mammi, sai ta fara tunanin idan basu karɓeta ba fa? Dama gashi ba sonta yake ba kila suna ce mishi ya rabu da ita zai rabu da ita a yadda ta san tsarin gidan sarauta.Abeeha ta wuce ta shige sashensu zuwa ɗakinta ta samu bakin gado ta zauna “Allah mai girma annabi mai dumbin daraja! Yanzu ni ce Afeefah ke da matsayin matar ɗan sarki mai daraja a wannan ƙasar? Anya? This is too good to be true… Hankali ba zai kama ba ni Afeefah dai ta Dutsen-wai annoba Mayya ajalin duk wanda ya raɓe ki!”Bata san adadin lokutan da ta dauka zaune a wurin ba har lokacin sanye da uniform don ba sallah take ba bare tayi tunanin azahar da aka idar a wasu masallatan, tana nan zaune sai ga Abeeha ta shigo da sauri bayanta jannah tana cewa “Zo ki ga wani abu Khaihh Ya Rayyan duniya ne! Sarakin Maammi ne a gasken gaske an tashi kaina!”****Yana fita daga sashen Laamiɗo Saleem ya ƙira yana tafiya a hankali suna magana sun jima sossai suna wayan Saleem ya san komai a kanshi ya kuma taya shi murna kwarai shima kuma yana cikin masu tahowa gobe ɗin, idanun Rayyan ne suka sauƙa akan Fulani Adama dake tahowa hanyar sashen mai martaban, bai wuce ba sai ya tsaya yana cigaba da wayan idanunshi na a kanta yadda take tafiya cike da izza da takama bayi da kuyangi na zube mata ko kallo basu isheta ba ɗauke ido yayi ya cewa Saleem”Zan saka maka wani abu ka sallami duk ma’aikatan gidan ka kuma ba su haƙuri na barin aikin ba tare da an sanar da su da wuri ba, za’a basu abin da zai ishe su jarin wata sana’ar in shaa Allah. Please a rufe komai yadda ya kamata don zan dawo ba na zo kenan ba!”Kalamanshi na karshen karab a kunnenta, idanu ta zuba masa Dukda kaɗuwar da tayi na namijin da ta gani a gabanta ta wani sashen ta ɗan ji sanyin kalaman nashi har hakan bai ɓuya a kan fuskarta ba sai da tayi murmushi ya sake kawar da idanu a kanta yace “Na gode Saleem za mu yi magana please ka sanarws Sulaiman kafin na ƙira shi, Sai na ganku a gobe ɗin…”Yana sauƙe wayan ya kalleta “Barka da wannan lokaci Mama..!”Ya faɗa da ɗan murmushi mai dauke da dumbin ma’anoni.”Ashe rai kan ga rai Sameer? Ko da shi ke na zaci ka manta da mu gabaɗaya ai shiyasa ban ga ka kawo gaisuwa ba…”Har lokacin yana dan murmushi yace “Wani abin ake mantawa amma wani ya fi ƙarfin mantuwa Mama, zan zo in shaa Allahu ban gama warware gajiyar aiki bane. Na bar ki lafiya”Yana kai nan ya wuce ta Gaabɗo ya bishi da sauri.Da kallo ta bi bayanshi sama da mintuna biyu kan ta juya ta nufi sashen na mai martaba.****Saleem na sauke waya ya kalli Mommy dake zaune cikin kujera a sabon gidansu da suka dawo komai na ciki sabo ne kuma a tsare gwanin kyau da ɗaukar ido yace “Mommy kin ji ikon Allah ko?”Duk su Sameera idanu suka mayar kanshi mommy tace “Me ya faru?””Mommy ashe Rayyan jinin sarauta ne, mahaifinshi shine Laamiɗon Fombina.””Da gaske kake ko wasa?”Cike da dumbin mamaki mommyn ta jefa mishi tambayar “Wallahi da gaske mommy yanzu haka yana masarautar su ashe ƙanwar shi ce aka yi kidnapping suka je suka samu sa’ar tseratar dasu, gobe duk su Afeefah za su tafi chan nima yanzu zan sayi ticket””ikon Allah ikon gaske, wato a wannan duniya ka kalli mutum ne kawai baka san waye shi ba, No wonder yake da ɗabi’ar sarautar… Ikon Allah wannan abin mamaki dayawa yake”Sadiqa tace “Oh wa zai tuna Afeefah za ta iya sa’ar zama matar irin wannan mutumi? Yanzu mu fa ko kallonshi sai da hanya…waye bai san irin tarin dukiyarsu, karfin mulkinsu da izzarsu ba!”Samha tace “Gaskiya tayi dace kam tsuntsu daga sama… Mun mata murna Allah ya cigaba da basu zaman lafiya haɗe da zuri’a dayyaba”Duk suka amsa da Ameen amma mamaki da tsoron Allah na sake rufe su rufff.Saleem ya miƙe ya fice daga gidan.****Kitchen ya shiga kai tsaye bayan shigarshi sashen ya dafa indomie don babu abinda babu na girki cikin babban kitchen ɗin komai na zamani komai kuma fess kaman ka lashe don walwali, a plate ya juyo ya dawo parlor hannunshi ɗaya rike da ruwa yana gama ci ya mayar da kwanonin ya wuce ɗaki bai samu ya Kira Abeeha da ya ga missed call nata ba saboda lokacin masallaci dake kokarin ƙurewa ya sauya kaya zuwa wasu Fararen jumpha hadadden ɗinki ‘yar ciki da babbar riga ya fita yayi kyau ainun daga ka ganshi zaka san yaro da kuɗi ne abokin tafiyar manyan, ga sarautar amma ya tafi da tsantsar wayewa, ilimi da sanin kan tsarin shiga.Hula da takalmin da ya saka duka farare fatarshi sai shining yake Dukda ma ya ɗan yi duhu kaɗan saboda zaman da suka yi daji amma fess yake ba ma zaka gane ba idan ba ka san shi ba, turare ya feshe jikinshi da su kala daban daban kan ya zari wayanshi ya fito tuni duk suka miƙe dogaran suka fara zabga mishi kirari ya ɗaga musu hannu don bai cika so ba yayi gaba suka rufa mishi baya har mota, Dukda masallacin ma a cikin masarautar yake sai dai akwai ‘yar nisa don haka dole mota ya shiga suka yi har motoci uku da dogaran suka nufi masallaci.Mai martaba na shiga shima ya iso ya shiga nan aka fara huduba bayan an gama tsaf aka gabatar da sallah kaman yadda addini ya tanada aka yi adu’o’i kan aka shiga watsewa a hankali, daga nan fada suka nufa don sarki na son ganinshi yana isa gaban manya jagoran addini da al’ada na fulani wato Laamiɗo ya gabatar dashi a matsayin Ciroman Fombina kuma Yarima Fuunange na ƙasar Fombina (Yariman Matasa) a take aka mishi rawani fari ƙal mai kamshi wow ya fita kaman ka sace shi ciki, kasancewar wurin akwai yan jarida kala kala tuni ya fara zagaya duniya.Turaki ne ya karɓi abin magana ya gabatar da kanshi kan ya ce “Ciroma alhakina ne da in sanar maka aikin matsayinka, na san ka riga ka san Ciroma shine wanda aka ɗauka matsayin ɗan gado ko mai jiran gado. Yarima Fuunange wato Yariman Matasa kuwa mun bar maka goben matasan mu ne a hannunka, kai ne shugabansu wurin ganin sun cimma al’adar mu na fulani bisa kan daidai wato: • Koyon Pulaaku (hakuri, ladabi, kunya, jarumta).• Koyon sana’a ko aikin iyaye (kiwo, noma, ko fatauci).• Haskawa a cikin al’umma ta hanyar waka, rawa, da wasan al’adu da gargajiya.Muna yi maka Fatan alkhairi da Fatan Allah ya baka ikon sauke wannan nauyi da aka ɗora maka”Tuni sarkin busa ya fara busa algaita mai daaɗin sauraro dogarai suka shiga jefo kirari daban daban, ya miƙe tsaye ya isa gaban mahaifinshi yayi godiya ya juya aka yi mishi rakiya da wannan busa da sarewa”Taaakawarka lafiya ɗan sarki jikan sarki kuma uban sarkin gobe, kaaaareka Ciroman duk duniya Yariman Matasa gaba saalaamun baya salaaamun, maƙiyanka fadawarka ɗaawisu sarkin ado… Kyaun ɗa shi ne ya gaji mahaifi kaareka Ciroma”Abin da ake ta nanatawa kenan busa da sarewa na tashi har parlorn baƙin shi na sashenshi inda anan zai gana da ‘yan jaridar da suke jiran shi kan aikinsu.Zama yayi ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya yana dan lumshe ido ya buɗe saboda gajiyar da yayi ga chan ƙasan ranshi wani abu na mintsininshi na kewar abin da zuciyarshi ke mararin ko da sauraron muryarta ne bai samu dama ba.”Ranka ya daɗe Dukda abin da ya ajiye mu anan daban sai dai za mu fara ne da taya ka murnan shigowa cikin ahalinka lafiya, shin me za ka iya cewa akan farin cikin da kake ciki a yanzu? Menene kuma ya zama babban mukamin bayyanarka a wannan lokaci?”Murya ya ɗan gyara bayan yayi sallama da Fatan alkhairi kan ya furta”Komai lokaci ne na yarda da wannan, sannan bafulatani yace Munyal deefan hayre, ko va’i fu jippan”(mai haƙuri kan dafa dutse kuma duk nisan jifa ƙasa zai dawo)”Amsar kenan da ya bayar, dan jaridar ya zaci zai kara wani abu amma sai ya ji shiru sai yace “Masha Allah, Toh bari mu koma abin da ya ajiye mu anan shin menene ya faru? Ta ya aka yi taron al’umma suna jiran ganin waennan miyagu sun kasance Fulani kaman yadda aka jima ana yi wa Fulani kuɗin goro sai kuma aka haihu a ragaya?””Dama chan kulba ta jima tana ɓarna ana cewa jaɓa ce, bana manta ina da wani shugaba a baya da sanadiyar kudin goro da ya mana ban taɓa furta mishi ni bafulatani bane amma ya kafa min karar zuka ban ci mishi ba ban sha mishi ba, hakika wannan irin zato na duk bafulatani ɗan ta’adda ne ya jima yana ciwa dayawa tuwo a ƙwarya.Ba a tuna baya in ji masu iya magana wai gyartai ya ci sarauta, a lokacin da duniya ke kwance kabilu mabanbanta kan shiga rugagen Fulani ayi wasa tare, a ci abinci tare a sha kindirmo a dalilin haka har zumunci ya ƙullu sai auratayya ta shiga tsakani. Da tafiya tayi tafiya a sannu sannu aka fara kwacewa Fulani shanu da matayensu a rugage kafin komai ya ta’azzara da abin ya fara zuwa gidan gona da kauyuka sai aka yi musu kuɗin goro aka far musu da kisa na kan me uwa da wabi wanda kan iya ɗarsa ɗaukar fansa, dayawa daga cikin Fulanin da suke rayuwa a daji babu ilimin addini ba na zamani, malamai babu ruwansu da kai da’awa, gomanti babu ruwan ta da samar da ingantacciyar ruwa ko makarantun zamani, aka kwace sandunansu na kiwo aka damƙa musu makamai saboda wani ƙudiri kawai na samun duniya a ji daaɗin cin ta da tsinken sakace. A hankali ringingimu suka fara yawa ta yadda zaman lafiya yayi mana ƙaura hakan ya shafi har waenda basu ji ba basu gani ba, shi fa ɗan ta’adda bashi da ƙabila, yare, addini ko jinsi in dai mutum bai da imani ko wanene shi bahaushe, Fulani, kanuri, yoruba ko igbo zai iya kasancewa ɗan ta’adda hasali ma ku sani ba Fulani bane suka aikata mana wannan ta’asar idan ma su ne suka aikata wa wasu daga cikin mu a wannan karon ba su bane don ma turanci ne tsantsa a bakin waennan, makamai da abincin da suke ci be yi yanayi da na bafulatanin ruga ba sai na wayayyen mutum ɗan zamani amma kuma idan zasu yi hausa su kan yi da sigar harshen Fulani Lallai an jima ana ruwa ƙasa na shanyewa.”Ɗan jaridar cike da gamsuwa yace “Barka da Yariman Matasa Ciroman Fombina, hakika gwalagwalan kalamanka sun fi yanayi da na hikima Allah ya sa mu gane. Toh wace hanya kake gani za’a bi wurin dakile wannan al’amari da ya ta’azzari al’umma yake kuma lalata musu Matasa?””Hanyoyin masu sauƙi ne ga al’umma amma masu wuya ga gomnati don zai kawo musu cikas amma idan al’umma suka tashi suka yi aiki a tare za’a iya maganceta cikin sauƙi, hanyoyin za su iya haɗa wa da • Karfafa tsaro da sa ido a kan dazuka dahanyoyi.• Ƙara horo da kayan aiki ga jami’an tsaro.• Bincike da hukunta masu laifi cikin hanzari.• Ƙarfafa al’umma da aikin yi ga matasa.• Ƙarfafa haɗin kai tsakanin al’umma da hukumomi – wato tsaro na gari.• Ƙin biyan kudin fansa – domin rage ribar garkuwa”Yana maganan ne yana ƙirgasu da yatsun shi cikin aji da iya magana.Kanshi duk ya ishe shi da ciwo da kyar ya gama sallama da mutane yayi la’asar ya shiga ya kwanta yana lumshe idanunshi da suke mishi nauyi ainun duk yadda ya washi baccin yamma bai san ya ɗauke shi ba don ya sha magani ga gajiya da ya tarar mishi.***Idanu kawai Afeefah ke Binshi dashi tun sanar da dawowanshi hasko shi da aka yi ana mishi sarautar Yariman Matasa da ma hirar da aka yin don live ne a manyan jaridu har international, Fatan alkhairi da ake Binshi da shi da yabon da yake sha duk suna kallo a ipad ɗin Abeehar, ita dai ta rasa me ke damunta ma hawaye kawai ta fara tsabar feelings ɗin sun zo mata daban daban, ya mata kyau ba ƙarami ba yadda kuma ya mata ta san yayiwa yanmata dayawa, kishi na taso mata sai kuma ta shiga damuwar anya ma a mace ya dauƙeta? Don ko ta wani ɓangare tana ganin ita ɗin ba tsararshi ba ce, tun daga tsatso, asali, ilimi, dukiya da kuma mulki ba ta inda tayi matching da shi kenan ‘yan uwanshi za su iya ware ta yadda take jin labarin gidan sarauta? Meyasa be neme ta ba? Sukuku haka su Abeeha suka taya ta haɗa kayanta akwati biyu suna ta surutu bata ce musu komai don faɗuwar gaban da take fama dashi kaɗai ya ishe ta, ko da suka bar ɗakin kifewa kawai tayi ta saki kukan da bata san na menene ba, ko abinci bata ci ba tayi kuka ta koshi har bacci ya ɗauketa a haka wuraren bakwai na dare.****Shafa fuskar ipad ɗin take da ake nuno hiran tana kuka, tana ganin yadda yaronta ya girma ya zama mutum, tana ganin tarin baiwa da nasaba da Allah yayi mishi tana jin guilt na tauye mishi wannan hakki tun daga yaranta, tana tuna yadda ta zame kafafunta daga cikin hannunshi tana tafiya ta barshi a bakon wurin da bai san kowa ba…. Bata ga laifinshi ba don bai zo inda take ba itama kunyar fuskantar shi take ji kaman ta nitse. Turo kofan aka yi aka shigo, ta ɗaga kai ta kalli Aisha, Matashiyar kyakyawar yarinyar da ke tsananin kama da Rayyan ɗin ta iso gangarta “Ammi Meyasa kike son sakawa kanki damuwa har haka? Baya nan kullum kuka da tunani ba ki samu cikakken farin ciki ba ya dawo ma baki huta ba? Gashi shi ko ya damu dake tunda bai tako kafarsa ya zo inda kike ba?””Aisha bashi da laifi don bai zo ba, baki san me na aikata mishi bane””ko me kika aikata mishi uwa fa uwa ce Ammi don Allah tunda ya bayyana cikin koshin lafiya yana ci yana sha kuma babu abinda ke damunshi ki bar wannan kuka haka ki nemi natsuwar ki”Da lallami tayi maganan, Ammie tayi murmushi mai ciwo sati uku kenan ko kallonta mai martaba bai sake yi ba bare har yayi magana da ita, ta san tayi kuskure amma su saurare ta kan su yanke kowani irin hukunci, tana kuma ganin Aishan bata san zafin dake cikin Abandoning bane ta tashi gaban iyayenta da gatanta shiyasa take wannan magana amma ita ta san dole sai an dauki lokaci Sameer zai sauƙo.Karfe shidda ya tashi ya watsa ruwa yayi sallah kan ya kira Abeeha ta ɗauka suka gaisa kan yace “Me kaman Muryar jannah nake ji?””Eh Yaya ta zo ne da shirin tafiya akan gobe kawai sai mu wuce airport daga nan””Me zai faru idan goben kuka haɗu airport da ita? Mijin yarinyar nan na sakacin barin matarshi sakaka tana yadda take so fa… Ina Afeefahh?”Miƙewa tayi “Bari na kai mata tana ɓangarenku””Wayanta fa me ya same shi?””Ruwa ne ya shiga sai ya ɗauke Yaya”Bai ce komai ba chan kuma ya fara ja mata kunne akan su tabbatar basu bar komai da zai iya lalacewa a gidan ba tana amsawa har ta tura ɗakin Afeefah da sallama.”Yaya ta yi bacci fa in tashe ta?”Ya ɗan yi shiru yana jin ba daaɗi kaman ya ce eh sai kuma yace “Kyaleta..amma sallah fa?”Sai tayi shiru ya fahimta don haka yace “Shikenan! Da safe za mu yi magana”Ta mishi sallama ya katse wayan ita kuma ta fice daga dakin.

Back to top button