Halysaah Page 71 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 71…Wajen karfe tara Khaleesat ta sauko downstairs bayan tayi shirin tafiya makaranta, zaunawa tayi kan kujera ta jinginar da kanta jikin kujeran tana jin kanta na mata ciwo, banda suna da test da baza ma taje schl din ba don har a lkcn she was still stunned at what happen yesterday, gaba daya a dar dar take cikin gidan, ko appetite din yin breakfast bata da shi, ganin it’s almost 10am ta ciro wayarta a jaka tayi ordering Uber da zai kai ta school din, bayan ya iso ta mike ta dau jakarta ta nufi kofa, tana isa school taga Safiyyah bata iso ba, kiranta ta fara yi a waya amma baya shiga, dab da za su fara test din sai ga Safiyyah, bayan sun fito Safiyyah ta sauke wani ajiyar zuciya tace “Kawai daga na ɗan sake ma yaro fuska uwarsa bata da lafiya shine ya kai ni ya baro Khaleesat” Khaleesat ta kalleta amma bata ce komai ba, Safiyyah ta gyara zama tace “Gaba daya ya lalata min jakunkuna da jambakin uwarsa, duk ya goggoga, daga in shiga wanka in fito, ai ko ni dai na dokesa in ma uban ya kullace ni shi ya jiyo, jakunkuna na masu shegun tsada sai kace uwarsa ce ta siya min” Khaleesat dai ta ɗan yi murmushi kawai without saying anything, Safiyyah na kallonta da kyau tace “Me kuma ya faru na gan ki haka?” Khaleesat ta bude jakarta ta ciro zoben da Housemate ya bata ta mika mata, Safiyyah ta amshi box din ta bude, zaro ido tayi with awe tace “Oh my God, who got u this Khaleesat? diamond ne fa, don Allah wa ya baki, kamfanin Forevermark fa….” Ganin Khaleesat taki bata amsa Safiyyah ta hade rai tace “Don Allah ki min magana, where did u get this from?” A hankali Khaleesat tace “My Housemate gave me” Mikewa Safiyyah tayi baki bude tana zaro ido tace “Don’t tell me he proposed to you?” Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba tace “Ko ba propose ba, he just gave me as a gift Sophie” Safiyyah tayi wani ƙara tace “Omg, wallahi proposing yayi maki amma saboda sense is far from you kinga ai baki gane ba, ya salam luxury brand ne fa Forevermark, to da ya baki me kika ce masa? Kuma ta yaya ya baki, kuna zaune ne ko kuna tsaye sanda ya baki?” Safiyyah ta koma ta zauna kusa da Khaleesat looking so excited tace “Don Allah how did u react da ya baki?” Khaleesat tace “Bai ma jira nayi masa godiya ba kawai ya wuce” Safiyyah tace “A apartment din ki ya baki?” Khaleesat tace “A’a, he took me out for dinner yesternight, bayan da muka dawo shi ne ya bani a mota” Safiyyah ta kyalkyale da wani shegen dariya tace “Yanxu fa sai kice har yanzu baki gane Housemate dinki is in love with you ba ko? Duk sai kice he is just being kind ko?” Khaleesat ta wani kalleta, Safiyyah na dariya tace “Ae ba abun mamaki bane kice baki gane yana sonki ba har yanxu, amma wallahi Housemate dinki na bala’i son ki kawata, don wannan care din is extra ordinary, ko kanwarsa da suka fito ciki daya bazai dinga yi mata irin wannan hidimar da yake maki ba, kai budurwar da saurayinta zai mata haka ma ba karamin musulmin sonta yake ba, yan mata nawa ne yanxu ko Naira biyar baya hadasu da samarinsu kuma a haka wai aurensu za ayi, ke dai wallahi you are very lucky om earth, Allah ya kashe ya baki kawai, ni kuma zan baki shawara kar kiyi misusing privilege din nan, cause it’s a privilege to you wallahi, bai duba wai kin taɓa aure ba kawai shi tsakani da Allah yake son ki a zuciyarsa, come to think of who he is, daga gidan sarauta fa ya fito, in zaki ajiye kunya ki nuna masa kema kina sonsa to zai dai fi maki, you are not a kid Khaleesat, kinsan sonki Jawwad yake, so me tsanani kuwa” Khaleesat ta sauke idonta kamar bazata ce komai ba, sai kuma a hankali tace “Kinsan me Sophie?” Safiyyah na kallonta tana washe baki tace “Ina jin ki” After some seconds Khaleesat tace “Abdul came to my apartment yesterday night” Mikewa Safiyyah tayi ba tare da tasan ta yi hakan ba a tsorace, tana kallon Khaleesat with shock all over her face tace “Waye kuma Abdul? Did you have another frnd that is Abdul by name da ban sani ba?” Khaleesat ta daga idanuwanta ta kalleta, cikin sanyin murya tace “Abdul dai guda da kika sani” Safiyyah tace “Na shiga uku na lalace, Abdul tsohon mijin ki wai kike nufi?” Khaleesat ta kasa ce mata komai, Safiyyah ta koma ta zauna tana kallonta da wani expression tace “Ta yaya yasan apartment din ki Khaleesat? Kuma me yaje yi maki a apartment? Don Allah ki min bayani yanda zan gane, i am lost….” Khaleesat ta sauke wani ajiyar zuciya tace “Wallahi ban san ta yaya yasan apartment dina ba Sophie, ni kaina i am still shock up till now, ko breakfast na kasa yi saboda tsoro, yanda kika san an jefo sa” Safiyyah ta maida jakarta gefe tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, ji min shege ɗan iska, to wai uban me yaje maki a apartment din, tell me what happen da yaje, ke kuma da yaje kofa kika bude masa ya shigo?” Khaleesat tace “Bayan Housemate dina yayi dropping dina a gida ya tafi ana ruwa, after like 10 mins sai aka danna bell, to na mance jakana a motar Housemate i was thinking shi ne ya dawo ya kawo min jakar, da na sauka downstairs sai na bude kofa kawai, ashe Abdul ne” Safiyyah da tayi mitsi mitsi da ido tana sauraron Khaleesat tace “Go on, ina jin ki, sai aka yi yaya?” Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace “I was very shock and afraid bayan na bude kofan ya shigo, shi ne na shiga kitchen da gudu dama wayata na hannuna nayi dialing number Ya Junaid, sai gashi ya biyoni kitchen din ya karbe wayar” Buda baki Safiyyah tayi tana kallonta da firgici a fuskarta, cikin sanyin murya Khaleesat ta gaya mata duk abubuwan da Abdul yace mata a kitchen din bayan da ya sameta a ciki, da kuma yanda Ajay ya zo gidan duk bata boye mata komai ba…. Safiyyah na girgiza kai tace “Amma kin bani mamaki Khaleesat, yanxu shi Abdul har wani abun tausayi ne shi da zaki boyesa a apartment dinki? Abdul fa???” A hankali Khaleesat tace “Ce min fa yayi in tuna alkhairansa gare ni Sophie, kuma he look afraid also baya son Ajay ya gansa, shi ne yace in rufa masa asiri” A fusace Safiyyah tace “Wani shegen alkhairin yayi maki da zaki tuna? Harrassing dinki da ya dinga yi ko kuma gorin da yake lafta maki da walakanta ki da yake yi? Nan nan ranan kika bani labarin zaman ukuban da kika yi a gidansa kafin ya sake ki, da yanda ya bar ki da kwalin indomie ko albasa babu balle tarugu, marukan da ya dinga maki da zagin cin mutunci ne alkhairin da zaki tuna game da shi? Mutumin da ya ci mutuncinki ya sake ki bayan ya samu abinda yake so a wajenki har shi ne abun tausayi Khaleesat? Yanxu kina nufin kika boye Abdul har washegari a apartment din ki kika bar Ajay da gadin ku? Ikon Allah, Gaskiya baki taɓa bani tsoro irin yau ba Khaleesat, i fear who no fear you, me yake damun ki ne haka?” Khaleesat da duk jikinta yayi sanyi tana kallon Safiyyah tace “Safiyyah kar ki manta this is America, we are not in Nigeria, Ya Junaid na lura temper dinsa a kusa yake, yana da zuciya sosai, what if yaje ya masa wani illa wajen dukansa don nasan definitely bazai kyalesa ba idan ya gansa a gidan, kina tunanin idan yayi masa wani abu za a kyalesa ne a kasar nan? dole doka zai yi aiki a kansa, kuma duk saboda ni sai haka ya faru Sophie??” Safiyyah ta wani kalleta tace “Sannu me hangen nesa, da duk baki san da hakan ba kika doka masa kira? Why did you call him at the first place idan ba don ya zo ya fitar maki da Abdul ba?” Hawaye ya cika idon Khaleesat tace “Ai a sannan ban san da wani Intention ya zo min gida ba, kinga if he just came to harm me wannan daban ne, amma he meant no harm he was even afraid, banda haka ai bazai rokeni kar in gaya masu ya zo gidan ba” Safiyyah tayi wani murmushi tace “Maa sha Allah, kinga shawara daya kawai Abdul ya koma Nigeria ya bada sabon sadaki a kara daura maku aure kije can ku karata, tunda yanxu kam ya tuba kuma har kin yarda da tubansa kina mugun tausayinsa a rai, Allah ya baku zaman lafiya da zuri’a masu yawa” Khaleesat ta hade rai tace “Come off it Safiyyah, ni nace maki i am ready to accept his repentance? Ko sake daura min aure aka yi da shi ba sai dai a kai gawata gidan ba, how will I forget what i went through so soon Safiyyah, wallahi kawai kalman alkhairi da ya furta ne da kuma irin sigar da naga ya zo min yasa na rufa masa asiri, ni ba butulu bace bazan ce Abdul bai min abubuwan Alkhairi ba a rayuwata, in ba don shi ba yaushe har ma zan zo kasar nan in hadu da su Housemate dina? I lacked nothing tun da Abdul ya kawo ni kasar nan karatu, don har nafi wasu da iyayen nasu ke daukar nauyinsu, kinga bazan ce Abdul bai min wani abun alkhairi ba, kuma bazan taɓa iya biyansa abinda yayi min ba, ki fahimce ni plss Sophie, ba wai nace ya kamata in sake kulasa bane, don wallahi ko ganinsa bana son yi don hakan na fama min ciwon dake zuciyata…” Safiyyah ta tabe baki tace “Tun da kin rufa masa asiri kin ga yau ma nasan yana can bakin apartment din naki yana jiran ki, hauka ake zan rufa ma Abdul asiri idan ni ne a shoe din ki? Abdul fa? Ai ko duk alkhairan duniya yayi min wallahi bazan rufa masa asiri ba sai dai Allah ya yafe min kawai, Monster in form of human ne fa Abdul, gaskiya kin ci amanar Junaid, kin cuce sa, kuma da ya kuskura yasan abinda kike boyewa a gidan nasan ko ciki daya ku ka fito da shi bazai sake barin wata alaƙa ta hada ku ba har abada, kuma bazai taɓa yafe maki ba, in kina tsoron kar Ajay ya masa illa me ya hanaki kiran 911?” Khaleesat dai tayi shiru tana bin inda suke zaune da ido, Kawai ganinsa suka yi a gabansu, ta rike numfashi tsabar yanda tayi shock tana kallonsa babu ko kiftawa, Safiyyah da ita ma ta gwalo ido tana kallonsa da mugun mamaki ta mike tana huci tace “Kai bawan Allah lafiya muna zaune zaka tsaya mana a kai, ko dai batan hanya kayi ne?” Sau daya ya kalli Safiyyah sannan ya mika ma Khaleesat wayoyin dake hannunsa guda biyu yana kallonta, daya na Jay daya na Ajay, Khaleesat ta wani hade rai tace “Abdul kaga bana son muyi creating scene a nan, kindly stay away from me, are you even okay? Meye zaka dinga bibiyata?” Safiyyah ta figi jakarta tana kokarin ciro wayarta tace “Idan ban kira maka 911 ba Allah ya tsine min albarka….” Tana ciro wayar ya fixge daga hannunta yana kallonta da kyau yace “Wajen ki na zo da zaki kira min 911 Malama?” Safiyyah ta kundumo wani zagi tana kallon Khaleesat tace “Kin dai ga crook din da kika ji tausayi har kika boye a apartment din ki kar Ajay ya gansa ya jibgesa ko, kin taɓa ganin inda shedan ya tuba dama? Shey u can see the useless monster you are pitying har da boyesa kar a dokesa?” Abdul na mata wani kallo yace “Hey watch your tongue, idan ba haka ba i will teach you a bitter lesson Billah, Ajay kika kirasa ko? To ya zo ya dokeni tunda ni statue ne, ina ga shi ko gidan dambe bai taɓa zuwa ba, ki je ki tambayi wanene ni a Lagos…” Khaleesat ta maida box din zobenta cikin jaka sannan ta mike ta amshe wayar Safiyyah dake hannunsa, ta dau jakar Safiyyah da nata ta fara janta su bar wajen, banda zagi babu abinda Safiyyah ke kunduma ma Abdul idonta rufe tana cewa “Munafuki kawai algungumi, wato saboda ka san tana da tausayi shi ne ka dawo sumui sumui da kai kamar na Allah zaka kara yaudaranta ka cuceta, har kana cewa ta rufa maka asiri, to kuwa sai na tona asirin nan naka wallahi, shegen duka za ayi maka da zai sumar da kai, in ka farfado ka siya ticket ko koma gida kayi jinya, tsabar baka samu daman ci gaba da musguna ma kawata ba har da rama sai da kayi kamar me ciwon Aids, to wallahi in baka fita harkar Khaleesat ba sai nayi maka abinda har ka koma ga Allah bazaka manta ba, mugu azzalumi kawai” Gaba daya attention din mutane ya dawo kansu a wajen, Abdul yayi wani murmushi yace “Sai kinyi regretting duk kalaman nan naki wallahi, sai na sa an lalata maki rayuwa i promise you this….” Khaleesat dai ta samu ta ja Safiyyah suka bar wajen gaba daya, banda rawa babu abinda jikinta yake yi don tsoro, Safiyyah ta warce hannunta tana kallonta a fusace tace “Kin dai ga ɗan iskan da kike tausayi ko? ashe da sabon salo kawai ya dawo don ya samu attention din ki, ke kuma ga sarkin masu tausayi, to kuwa rabon a karyasa yasa ya dawo Amurka don wallahi Ajay karyasa kawai zai yi” Khaleesat ta zauna ta rufe fuskarta da hannunta tana kuka a hankali, gaba daya ta gama tsorata, ta ma rasa wani irin tunani zata yi, zaman apartment din nata ita kadai ya fara bata tsoro kuma, can ta kalli Safiyyah dake ta bambami cikin rawan murya tace “Sophie ko dai in ma Ya Musty magana da kaina ki dawo apartment dina da zama tunda exams za mu fara? Wallahi bazan iya zama ni kadai ba kuma a gidan nan Sophie, i am afraid…” A fusace Safiyya tace “Ai baki zama afraid ba tunda har kika iya boye kasungumin ɗan daba a gidanki ya kwana, Abdul har abun yarda ne bayan duk mun san ɗan iska ne shi? Wani dadin baki zai maki har ki yarda da shi? Kin dai ga abinda yayi min ai yanxu, dama kuma me hali baya taɓa fasa halinsa” A hankali Khaleesat tace “To ko dai in yi ma Ajay bayanin abinda ya faru jiya kar ya zo ya gano yaji haushina? Wallahi i am so confuse Sophie” Safiyyah tace “To nima naji haushin ki balle Ajay da yayi gadin ke da Abdul ku ka sharbi baccin ku? ai wallahi kin cuce Ajay kuma sai Allah yayi masa sakayya” Khaleesat ta goge hawayen gefen idonta tace “To amma sai dai inje can gidan nasu in masa magana ko? Don kar yaje yayi misinterpreting dina ta waya idan na kirasa, i want to explain to him ta yanda zai gane” Safiyyah tace “Dama ai gwara ki samesa face to face kiyi masa bayani, sannan kar ki kuskura ki ce masa a gidan Abdul ya kwana don daga nan zai fatattake ki ya kora ki, ko ya hadaki da karensa ya kora ki, inda Ajay ke burgeni kenan wallahi, no nonsense Man kike ji, sam baya daukan wargi, tsayayyen namiji kenan, kawai ce masa zaki yi kin shiga kitchen zaki zuba abinci sai kika ga kamar Abdul a jikin window din kitchen dinki yana kallonki, shi ne duk kika rude kika kirasa jiya da daddare, daga baya kuma kika ga wajen wayam ba kowa, amma da ya zo sai baki gaya masa hakan ba tunda baki tabbatar ba kin zata hallucination kawai ki ke yi don dama kanki na ciwo jiyan, sai ki ce masa yau kina department muna zaune ni da ke kawai sai ga katon a gabanmu, ashe jiya shi din dai kika gani a jikin window, kinga ai maganata tayi making sense akan ki ce masa ai boyesa kika yi a daki jiya….” A hankali Khaleesat tace “To bari inyi order din Uber zuwa gidan” Safiyyah tace “Sannan idan kin je gidan ki fara masa godiyan gadin ki da yayi jiya ya hana kansa bacci, don nasan ba hankali gare ki ba kina iya zuwa ki fara maganar da ya kai ki kanki tsaye….” Khaleesat ta ciro wayarta za tayi order din Uber da zai kai ta gidansu Ajay, kafin tayi order din ta kalli Safiyyah tace “Ko zaki rakani mu je mu biyu?” Safiyyah ta rike haɓa tace “Wa?? Ni? Salon inje ya koro ni mutumin da ba kirki ne da shi ba, a’a wallahi bazan je ba, ko kadan bai taɓa burgeni ba dama ni, tun farko tamu bai zo daya da shi ba don na tsani mutum fitinanne, da dai Housemate ne sai in bi ki mu je, kuma banda ma yafi Housemate zafi me zai sa ma a sako sa cikin wannan case din, to tsorona muna iya sako Housemate yaje ya fara ba Abdul din hakuri kinga ai lamari ya lalace kenan, babu dai yanda muka iya Ajayn zaki je ki sama duk da mugun halinsa, ayi mutum ace bai son mutane kullum yayi ta daure fuska yana fushi shi kadai” Khaleesat na kallon Safiyyah cikin sanyin murya tace “Ko dai kawai in gaya ma Housemate in kyale Ya Junaid din?” Safiyyah ta wani hade rai tace “Wani Housemate, hakuri kike son ya tafi ya ba Abdul din kenan yanda zai ji dadin ci gaba da iskancinsa, ai karki kuskura ki gaya ma Housemate he won’t help matters at all, gwara Ajay no nonsense, tsaf zai mana maganin Abdul, amma Housemate ai har durkusawa sai ya iya yi ya ba Abdul din hakuri yanda suka yi ma Aymaan shi da Ya Musty, Ajay ai shi ne namiji” Khaleesat dai bata ce mata komai ba tayi order din ride din, Safiyyah ta zaro ido tana kallon hannun Khaleesat tace “Ina zoben naki? Mun shiga uku ko dai Abdul din ya kwace?” Khaleesat bata san sanda tayi dariya ba tace “Ga fa shi nan a jaka” Safiyya tace “Atoh, don ni yanda na gansa wujiga wujiga anya karayar arziki bai fada masu ba kuwa, kamar wanda yake yunwa duk ya rame sai idanuwa da hanci, da kyar idan ba talauci a tattare da shi” Khaleesat dai bata tanka Safiyyah ba, Safiyyah tace “To ki saka zoben mana, ko jere zaki yi da shi a gaban madubi?” Khaleesat ta bude ido sosai tace “Ina zan je da zan saka zobe Sophie?” Safiyyah tace “Ke dai kin ki wayewa a rayuwarki Khaleesat, ba don gayu ya siya maki ba dama?” Warce jakar tayi ta ciro box din zoben tace “Dalla ki saka” Khaleesat tayi murmushi ta amshi zoben ta saka tana kallonsa admiringly, cif ya zauna mata ta kalli Safiyyah dake ta murmushi ita ma kamar bakinta zai yage tace “It’s sooo cute, gaskiya Housemate is so romantic, har na hango kun yi aure, wallahi kashe ki zai yi kawai da soyayya, in soyayya ne a bar ma Housemate kawai, in kuma kwato hakki ne a bar ma Ajay” Dariya sosai ta ba Khaleesat, kawai ta mike bayan ta maida wayarta da empty box din zoben cikin jaka, Safiyyah ta rakata har zuwa inda Lyft dinta ke jira, ta bude motar ta shiga, hannu ta daga ma Safiyyah dake ta murmushi tana kallon zoben yatsanta dake ta kyalli, a haka Lyft din ya bar wajen, tun da suka kama hanya Khaleesat ke ta waige waige to be sure babu motar dake bin su a baya, don ita kam yanxu duk a tsorace take, tunda har Abdul ya iya gano apartment dinta to babu kuma abinda bazai iya yi ba, har dai suka isa bata ga alamar ko wani mota dake biye da su a baya ba, ta sauka daga lyft din tana tafiya a hankali ta shiga compound din, it’s almost 4pm na yamma, motar Ajay ta fara gani a parking space din gidan, sannan ta ga motar Jay ma alamar duk suna gidan, walking slowly ta karasa har entrance din parlon dai dai sanda aka bude kofar parlon, ta ɗan koma baya tana kallon Housemate dinta dake kallonta da mamaki, cikin dubara ta boye zoben finger dinta da veil dinta kar ya gani, tana kirkiran murmushi a hankali tace “Good evening” Yace “Evening Housemate, come in” Ta sauke kanta kasa ta bi bayansa har zuwa cikin parlon, ta zauna kan kujera shi ma ya zauna yana kallonta hoping all is well don sai yaji gaba daya hankalinsa ya tashi ganinta a gidansu, jin tayi shiru yana kallonta yace “Hope all is well Housemate?” Tana murmushi tace “Alhamdulillah, babu komai, Ya Junaid yana nan? I came to greet him” Jay yayi shiru yana kallonta, after some seconds yace “Yeah, he is upstairs” Ta sunkuyar da kanta a hankali tace “Ohk, i want to meet him” Jay ya gyada mata kai yace “He is at the parlor upstairs, ki samesa a can” A hankali tace “Sai na je sama?” Jay ya mike yace “He is there, ni zan fita yanxu….” Khaleesat tayi shiru tana kallonsa, ya ɗan yi murmushi ya nufi kofar fita parlon ta bi sa da kallo har ya fita, bayan fitarsa da kusan minti goma Khaleesat ta mike, walking slowly ta tafi sama, tsaye tayi ɗan nesa da parlon dake sama tana kallon Ajay dake kallon kwallo a Tv, ga grapes a gefensa yana sha, ko lura da ita bai yi ba, he was so engrossed in the football match he was watching…..*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
