Uncategorized

Abban Sojoji Page 55 Book 2 Complete Novel

 

“`The father Of Soldiers“`

Story &  Written 

       By 

      Hafsat Bature

 

_💋Boss Bature💋_

 

 

father of soldiers💫

 

part 2

 

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💘💋💖🤍

 

حفصة باتور محمد story by

 

Tun bayan da sehrish ta koma bedroom ɗinta a wani irin yanayi na kasala ta faɗa saman gadonta tare da kai hannu ta janyo pillow a ƙirjinta tayi hugging ɗinshi sosai,ta jima tana tariyo abunda ya faru tsakaninta da Sgr har lokacin jikinta bai bar kerma ba,duk wani juyi da zatayi sai ta dinga jin tamkar yana a jikinta ne,musamman data rungume filon nan sai taji tamkar shine ta rungumo ajikinta kamar yarda ya faru a bedroom ɗin shi,wani irin tsananin son shi ne da ƙaunarshi da kuma sha’awarshi duka suka mamaye ko’ina na sassan jikinta wannan yanayin ne ya haifar mata da jin matsanancin Sanyi,cikin sauri takai hannu tare da jan bargonta ta lullu6e jikinta duka dashi,daƙyar ta samu tayi addu’ar bacci kuma cikin sa’a baccin ya ɗauketa❤

 

A 6angaren su Hosana da jahad kuwa ƙin bacci su kayi saboda jiran zuwan Ya Omar ɗinsu sun sa ran zaizo,amma har dare ya ritsa baizo ba,hakan yasa suka fidda rai da zuwan nashi,tuni bacci yayi awon gaba dasu asaman gadon nasu,kowannansu na sanye da sleeping dress,hossana na rungume da pillow yayin da jahad ke manne da drawing book ɗinta asaman chest ɗinta,sai faman sharar bacci suke yi hankalinsu kwance,Rainon Omar,

Wuraren ƙarfe ɗaya da rabi,jahad ta farka daga baccin da take yi,a hankali ta buɗe kyawawan idanunta tana kallon ceiling,bakomai ne ya faɗo mata aranta ba fa ce,addu’ar da tayi promising ɗin cewa zata dinga tashi tsakar dare tana taya ya omar ɗinsu da kuma ahalinshi addu’a kyauta saboda kyautatawar da yake yi masu,hakan yasa take so ta saka mashi ta wannan 6angaren,

Tuna wannan yasa jahad miƙewa zaune daga kwancen da take hannunta na dafe da zanen fuskar junaid,ɗago da littafin tayi tare da aza idonta akan fuskar tashi murmushi ta ɗanyi tare da cewa”bansan kowanene kai ba,amma ka kwantamin araina,idan na kalli wannan murmushin kashe zuciyar naka sai inji wani irin sanyi ya ratsa zuciyata,insha Allah kaima zan sanyaka acikin addu’ata,da kowa ma,”

ta ƙarasa maganar tare da ajiye drawing book ɗin asaman bedmattress ɗin,sannan ta zuro da ƙafafunta ƙasa tare da miƙewa ta sauko daga saman gadon,

Riga da wando ne ash colour,sai hula data rufe kanta da ita,takawa tayi izuwa cikin toilet,after some minutes sai gata tafito tana yarfe ruwan dake a fuskarta da hannunta,

Wuce wa tayi wurin closet ɗinsu,Hijab ta ɗauko aciki tare da darduma,bayan ta shimfiɗe darduma,ta zura hijabin ajikinta sannan ta kabbara sallah da wannan kyakkyawar niyyar tata,cikin natsuwa ta shiga yin sallar,ba ƙaramin ƙoƙari jahad tayi ba,don sai da ta raba dare tana yin nafilfilin nan,har sai da ƙafafunta suka soma yi mata zogi sannan ta tsagaita tare da sallame sallar,hannayenta ta ɗaga sama ta shiga jera addu’o’i cikin harshen larabci tashiga karantosu ba adadi,

daga cikin waɗanda ta sadaukarwa wannan addu’oin nata harda Sehrish da kuma ya omar ɗinsu tare da ahalinsa da kuma sauran al’ummar musulmai baki ɗaya,ta jima tanayi ƙarshe ma asaman dardumar ta kwanta,kuma ahaka bacci ya ɗauketa,

 

Wuraren sallar Asubahi,Abbansu ya fito daga cikin toilet jikinshi sanye da jallabiya da alama alwala yayi,wucewa yayi wurin gadonshi domin ya tashi junaid su wuce masallaci,

Zama yayi daga gefen gadon yana kallonshi sai faman sharar bacci yake yi,hannu yasa tare da ɗan bugun bayanshi tare da cewa”babyn abbansa baccin ya isa haka,ka tashi muje muyi sallah kada time ya ƙure mana,”ko motsi junaid baiyi ba,hannu abban nasu ya kuma kaiwa ya ƙara ɗan bugun bayanshi Yace”junaid ka tashi mana,”

tun abbansu nayin maganar hankalin shi kwance harya fara shan jinin jikinshi,sosai ya shiga bugun bayan junaid don ya farka amma ko motsi wannan baiyi ba,cikin tashin hankali abban yakai kunnan shi a saitin hancin junaid don yaji ko yana numfashi amma sam babu wata iska dake fita a wurin,da hanzarin gaske ya juyar dashi yana fuskantar ceilling,sannan ya kuma kai kunnan shi saman ƙirjinshi saitin zuciyarshi sam zuciyar junaid ta tsaya da bugu,

Cikin ruɗu Abbansu ya shiga furta”innallahi wa’inna ilaihirraji’un!junaid pls ka tashi!in ma wasa kake mun kadaina,bana son irin wannan wasan junaid,

gaba daya duk yabi ya rikice,hannu ya miƙa tare da ruko bottle watern dake ajiye a bedside drawer wanda suke ajiyewa in case ko wani zai buƙata yasha acikinsu,

Yatsun hannunshi har kerma suke yi wurin buɗe murfin robar,ɗebo ruwan yayi a hannunshi sannan ya shiga yayyafa ma junaid a fuskarshi,ko gizau junaid baiyi ba tamkar ba ruwa ake yayyafa mashi ba,hankali tashe Abban nasu ya ajiye robar ruwan asaman drawer dinsa,jiki na rawa ya tashi daga saman gadon,ya fito daga ɗakin,sai faman sauri yake yi duk yabi ya rikice,kai tsaye upstairs ya wuce,yama rasa wurinwa zai fara zuwa ya sanarma halin da ake ciki,

da hanzari ya tunkari corridor din sashen Omar da Sgr kamar zaiyi tuntube haka yake ta faman sauri,

“Abba”! Muryar Marshal Omar ce ta katse mashi hanzarin shi,saboda tsabar ruɗu har abbansu ya wuce shi bai sani ba,

Yana juyowa yaga Omar nan fa ya tunkare shi hankali atashe yace”Omar dan Allah kaje bedroom ɗina,junaid baya numfashi zuciyarshi bata bugawa bansan meke faruwa dashi ba….”

Hankalin Omar ba ƙaramin tashi yayi ba,ko ƙarasa sauraron Abban nasu baiyi ba ya wuce da saurin gaske ya sauka downstairs direct ya nufi ɗakin abban nasu,

Akan hanyar zuwan shi bedroom ɗin na Abban nasu ya haɗu dasu Twins tare da fawan da kuma kanal yousouf da sauransu,tunda ya sanar dasu abunda abbansu ya faɗa mashi game da halin da junaid ke ciki,nan fa suka ɗunguma gaba ɗayansu izuwa ɗakin nashi atare,

Shi kuwa Abban nasu part ɗin babban yayansu ya nufa don ya sanar mashi halin da ake ciki,adaidai lokacin daya shiga bedroom ɗin nashi,a lokacin shi kuma ya fito daga cikin toilet jikinshi sanye da jallabiya,bai jima da tashi daga bacci ba yashiga toilet don tsarkake jikinshi tare da ɗauro alwala,ganin yarda abban nasu ya faɗo cikin ɗakin nashi batare da sallama ba yasa shi cewa”Abba lafiya”?

Fuskarshi cike da damuwa yace”ina fa lafiya?junaid na can araye ko amace na rasa ganewa,dan Allah kaje ka duba shi bansan meke shirin faruwa dani ne………..’

 

A ruɗe Sgr yace”bana fahimtarka abba!me ya faru da junaid ne”?

A ƙagare abban yace”kaje ka ganshi kawai!sam baya motsi kamar matacce..  ”

tunkan yakai ƙarshen tashi maganar tashi,sgr yayi hanzarin kama hanya ya fuce daga ɗakin,shima Abban nasu yabi bayanshi cikin sauri,

 

Marshal Omar ne zaune agefen gadon su kuma su fawan suna daga tsaye cikin yanayi na damuwa,sun tashe shi yafi a ƙirga har ruwa suka ƙara yayyafa mashi amma ko motsi babu,hakan yasa duk suka sha jinin jikinsu,

Shigowar babban yayan nasu ne tare da Abbansu yasa suka juya atare suna kallonsu,ganin sgr yasa suka matsa tare da bashi wuri ya wuce,kai tsaye ya hau saman gadon ya ƙarasa har inda junaid yake kwance fuskarshi na fuskantar ceilling,

Hannu yasa tare da shafa gefen fuskarshi da kuma wuyanshi kafin daga bisani ya janye hannun nashi izuwa saitin zuciyar shi,yana aza hannunshi asaman wurin nan take zuciyar junaid tashiga harbawa da sauri da sauri,

gaba ɗaya duk sunyi zuru suna jiran jin me zaice tsoransu kar ace junaid ya mutu sai faman addu’o’i suke yi acikin zuciyoyinsu akan Allah karya tabbatar da hakan don bazasu juri rashin shi ba,

ɗan ƙayataccen murmushi sgr yayi shi kanshi ba ƙaramin kwanciyar hankali yasamu jin zuciyar junaid na bugawa duk da yayi mamakin abunda Abban nasu ya sanar dashi nacewa zuciyar ta tsaya da harbawa,bayan shi kuma da yazo yasanya hannunshi a wurin zuciyar tashi tana harbawa,

Jin yayi shiru baice komai ba yasa Abban nasu cewa”Son meya faru?junaid yana raye kuwa”?  A ɗan tsorace yayi maganar saboda tsoran Amsar da zata biyo baya,

Cike da tabbaci sgr yace”junaid fa ba mutuwa yayi ba,he’s still breathing,yanzu haka ma bacci yake yi”

wata irin ajiyar zuciya Abban nasu ya sauke tare da fadin “Alhamdulillah” bashi kaɗai ba hatta sauran ma,

A hankali sgr ya sanya tafin hannun shi tare da ɗan bubbuga bayan junaid ya ambaci sunan shi”junaid!junaid,”

Kai tsaye kiran yashiga cikin kunnan shi,aikuwa ashagwa6e yace”pls Abba leave me alone,ni baccin bai isheni ba,tun ɗazu ka takuramin natashi nayi sal…….’bai ƙarasa maganar ba saboda buge mashi baki da Sgr yayi,hakan yasa ya ware idanunshi dake ɗauke da bacci yana kallonsu biji biji,ganin yarda sukayi mashi ƙawanya sun zuzzuba mashi ido,yasa ya miƙe zaune yana faman murza idanunshi don ya shaida su wanene haka,

Sam bakin abban nasu yaƙi rufuwa saboda tsabar farin ciki,gaza jurewa yayi don haka cikin sauri ya ƙarasa daga gefen gadon ya ɗan russina tare da rungumo shi ajikinshi yana cewa”junaid nashiga tashin hankali sosai saboda halin da ka shiga,ba ƙaramin daɗi naji ba daka farka, da bansan wani hali zan tsinci kaina ba,”ya ƙarasa maganar tare da ɗan janye jikinshi daga na junaid ɗin yace”faɗamun menene ke damunka shalelena,”?

turo baki junaid yayi tare da cewa”Abba su wanene waɗannan nifa bangane su ba,kuma kana gani wani ya bugar mun baki bakace komai ba,”

hannu Sgr yasa tare da ƙara make bakinsa,aikuwa rai a6ace junaid yasa musu kukan shagwa6a yana bubbuga ƙafafun shi,hakan ba ƙaramin nishaɗi yasa su ba,

Cikin shessheƙar kuka yace”wlh bazan yarda ba,duk wanda ya ƙara bugarmin bakina saina rama,”

Hannu Sgr ya ƙara sawa tare da ɗan bugun bakinshi,a fusace junaid ya ɗaga hannu zai rama,tsayawa sgr yayi yana kallon ikon Allah,

Junaid kuwa tuni idanunshi sun washe ganin babban yayansu yasa yayi saurin janye hannunshi,sai lokacin ya gane cewa ashe duk sune,

Cikin sanyin murya ya ambaci sunan shi”babban yaya,”sannan ya juya tare da kallom Omar dake daga zaune agafen gadon yace”ya Omar,” binsu yayi ɗaya bayan ɗaya yana kiran sunayensu a ƙarshe yace”meya faru ne nagan ku anan?Abba kodai idona ne ke nuna min badai dai ba,”

Omar ne yace”junaid mun sameka awani yanayi ne shiyasa ka ganmu anan dukan mu,amma Yanzu Alhamdllh tunda ka farfaɗo,ka hanzarta tashi mu tafi masallaci muyi sallah duk da time ya wuce,”

kallonsu fawan Omar yayi tare da cewa”kuyi gaba,zamu zo tare da shi,”

amsa mashi su kayi da toh sannan suka fuce daga ɗakin,

Su kuma sai da suka jira junaid yashiga toilet ya ɗaura alwala sannan suka fito tare dashi,

Don tsabar gatanci ma Omar ya goya shi abayan shi kamar wani ƙaramin yaro ahaka suka tafi dashi,duk wannan budurin da akasha Haroon na la6e yana sauraronsu babu wanda yasan dashi daga shi sai short ajikinshi,murmushin takaici yayi tare da cewa”kun makaro,aikin gama ya gama,dole ku rasa junaid,”

 

***************washe gari**********

Sehrish

A washe gari da wannan yanayin data kwanta dashi ta farka,daƙyar ta iya nufar toilet tayi wanka tare da fitowa ɗaure da towel,shaf shaf batare da 6ata lokaci ba ta kammala shirya kanta cikin school uniform ɗinta riga da wando bayan ta kammala shafe jikinta da body oil ɗinta,bin ko’ina tayi na jikinta tana feshe shi da turare gaba ɗaya hankalinta na akan Sgr,abunda ya faru jiya tsakaninsu,har yanzu ji take kamar mafarkine abun nan daya faru,yarda 6awon ayaba ya ja shi ya sul6e zai faɗi ta taro shi suka faɗa saman gadon,murmushi ta ɗanyi tare da cewa”wani ikon Allah,tunda nake kai mashi fruits ban ta6a kai mashi ayaba ba batare da na 6areta ba na yanka mashi ita ba,kamar yarda nake yanka sauran kayan marmarin amma jiya rabon ayi saina manta na kai mashi ita a haka,lallai 6awon ayaban nan ba ƙaramin aiki yaso yayi ba,da ace ya faɗi bansan wani irin buguwa zaiyi ba,”

tsayawa tayi da tunanin nata na wani lokaci,ɗago da idanunta tayi acikin mirror ɗin tare da sakin wani irin ƙayataccen murmushi tace”ɗaya daga cikin amfanin 6awon ayaba kenan wanda mutane basu son dashi ba,wato ƙulla allaƙar soyayya,”

Ƙarasa maganar tayi tare da fashewa da dariya,mayar da flower bomb ɗin tayi ta ajiye shi asaman mirror ɗin,sannan ta ƙarasa saman gadonta inda ta ajiye short hijab ɗinta tare da ɗaukar shi ta zura ajikinta,bata dauki school bag ɗinta ba saboda tana son zuwa kai mashi breakfast ɗinshi before ta wuce school,

Slippers ta zura a ƙafarta sannan ta buɗe ƙopar tare da ficewa izuwa cikin kitchen ɗin,tunkan ta ƙarasa ta hangi Hayaam acikin kitchen ɗin tana taya Azmee girki,nan take taji gabanta ya faɗi,ɗaurewa kawai tayi tare da sa kai cikin kitchen ɗin bakinta ɗauke da sallama,

Juyawa Azmee tayi daga tsayen da take agaban gass tana kallonta fuskarta ɗauke da murmushi,cikin sauri sehrish ta gaishe ta”ina kwana aunty azmee fatan an tashi lafiya,”

“Lafiya lou,Alhmdllh yau kinsha bacci ko leƙowa kitchen bakiyi ba,har nayi tunanin cewa ko baki jin daɗine,shiyasa ban tashe ki ba,”

Sunnar da kai sehrish tayi tare da cewa”Aunty azmee nikaina bansan ya akai nayi bacci dayawa har haka ba,naso ace nashigo kitchen ɗin da wuri don na tayaki aiki,”daƙyar sehrish ta kai ƙarshen maganar tata,ganin yarda hayaam ta zuba mata ido kamar zata haɗiyeta,tana a tsaye gaban choppping board tana yanka vegetables din da zasu yi amfani dashi,

“Yanzu junaid kike jira ya kai ki school ɗin kenan?naga har yanzu ma bai fito daga bedroom ɗin nashi ba,’

Kafin sehrish tace wani abu,Hayaam tayi karaf ta amshe da cewa”Junaid kuma?shine drivernta kenan?school ɗinsu babu bus ne”?ta jefa ma azmee tambaya,

Shiru sehrish tayi batace komai ba don batasan amsar da zata bata ba,

Azmee ce tace”ae da yake bata jima da fara zuwa school ɗinba,har yanzu bata saba da wasu abubuwan ba,amma nan bada jimawa ba,zata fara hawa bus ɗinne,”

Yatsina fuska hayaam tayi tare da mayar da idonta akan kayan lambun da take yankawa,

ganin yarda Sehrish tasha jinin jikinta yasa Azmee cewa”ba zakiyi breakfast bane?

cikin sanyin murya tace”A’a Aunty azmee bana jin yunwa,in naje school zanci acan,amma inaso kafin na tafi in kaima Babban yaya nashi breakfast ɗin in akwai abunda kuka kammala…..’

Wani irin kallo hayaam ta watsa mata wanda hakan yasa ta ƙarasa maganar adabarbarce,

“Babu buƙatar ki kaimashi breakfast ɗinshi,ke da zaki school salon kawai shiririta don kiyi late ko?to ki tafi kawai ni zan kai mashi breakfast ɗin nashi,” cike da isa hayaam ke magana batare da jin wani ɗar azuciyarta ba,

Ba sehrish ba hatta azmee tayi mamakin yarda hayaam ke magana a gadarance,duka duka jiyan nan tazo gidan amma zaƙewarta harta fara yawa,

jiki asanyaye sehrish tace”shikenan,Aunty azmee ni zan wuce,”

azmee bata ji daɗin abunda ya faru ba saboda tasan yarda sehrish ke kwallafa rai akan son kai ma Sgr abincin shi,

gyaɗa kai kawai tayi tare da cewa”Adawo lafiya,”

juyawa sehrish tayi kamar wadda aka zare ma laka,

Shu’umin murmushi hayaam ta saki tare da cewa”kaɗan kika fara gani,gayyar soɗi kawai,” ƙasa ƙasa tayi maganar don kada azmee taji,

 

Bayan sehrish ta fito daga kitchen ɗin tsayawa tayi a main palour ɗin tana jiran ganin ko junaid zai fito,ita kanta tayi mamakin rashin fitowarshi da wuri saboda har zumuɗi yake yi nasan kaita school,babbar damuwarta shine batasan inda zata samu school bus ɗinsu ba saboda wurin ƙarfe 8:00am take kammala daukar student a areas ɗinsu,yanzu kuma har da rabi ta buga already bus ɗin ta kammala kwasar ɗaliban,bazata same ta ba,

jin shiru bai fito ba yasa ta juya tare da komawa cikin bedroom ɗinta,kusan minti 5 ta fito hannunta ɗauke da school bag ɗinta,ta kuma sanya sandals ɗinta,

 

tafiya take tana waiwayon twin stairs ɗin wai ko zata ganshi ya fito amma babu alamar shi,aranta tace kodai yana a bedroom ɗin Abbansu ne?amma kuma ae da asuba yake komawa ɗakin shi don ya shirya in zai kaini school,”

tana cikin wannan tunanin sai ga junaid yana saukowa down stairs fuskar nan tashi ɗauke da ƙayataccen murmushin nan,wankan pakistani ya ɗauka ajikinshi farare sai ya fito wani handsome dashi yayi fresh ga wani haske daya ƙara,

washe baki sehrish ta shiga yi kamar taje ta rungumo shi saboda tsabar farin ciki,dama abunda take zullumi kenan wazai kaita school in ba junaid,gashi ko sisi bata dasu balle tace zata tsaida taxi takaita,

Hannunshi na ruke da key ɗin motar shi,yana ƙarasowa batare da 6ata lokaci ba ya ruƙo hannunta acikin nashi suka fuce daga cikin gidan,

Ran hayaam ba ƙaramin 6aci yayi ba saboda ta hangi junaid tare da wannan yarinyar da ta tsone mata ido,ta wani 6angaren kuma tayi mamakin girman junaid ba ƙaramin kyau yayi mata ba,

 

Bayan sun shiga motar a hankali ya tashi motar tare da fito da ita yajata da gudun gaske saboda time dayaga yana ƙurewa,

Satar kallon gefen fuskarshi tayi tare da cewa”ko kasan cewa kyau kake ƙarawa”?

Murmushi junaid yayi hankalinshi na akan driving ɗin da yake yi yace”dame dame kenan na ƙara”?

Lissafa mashi tashiga yi”ka ƙara haske sosai,ka ƙara tsayi ka ƙara komai dae hada ak47 ma duk ka ƙara……’ bata ƙarasa maganarba saboda jin yarda junaid yaja burkin motar,kallonta yayi a ruɗe yace”rishi kinsan menene ak47 kuwa”?

murmushi sehrish tayi tare da cewa”a’a nima bansani ba,naji kwanakin baya da jimawa,su fawan na jan ka faɗa suna ambaton sunanta shine nace nima bari naja ka faɗa da ita,”

Ajiyar zuciya junaid ya sauke jin abunda tace,dama sai da ranshi ya bashi cewa batasan menene ainihin ma’anar abunda suke nufi ba shiyasa ta furta mashi kalmar,

Tambayarshi ta shiga yi me take nufi ne,aikuwa nan yashiga tiƙar dariya batare da ya bata amsar ba ya tashi motar suka nufi hanyar school ɗin,

 

**************

“Hossana wai bazaki fito mu tafi ba!?ya osman fa yana waje yana jiran mu,”jahad ce ke ta faman tunatar da hossana dake zaune asaman dining table wanda ke shake da kayan breakfast ɗinsu,tun dazu jahad tabarta tana ta faman cusa abinci a cikinta sam bata ƙoshi,ta haɗa wancan ta kwa6a wancan ta tura abaki,

ran jahad ba ƙaramin 6aci yayi ba lokacin data fito ta samu hossana ko motsi batayi ba gashi ko uniform bata sanya ajikinta ba,iya kayan baccin jiya ne ajikinta,ita kuwa har ta jima ta kimtsa kanta acikin unform ɗinta hatta hijabi ta zura a jikinta,hannunta na ruƙe da shool bag ɗinta,

a tsiwace tace”Hossana!ki ajiye wannan abincin ki tashi mu tafi school!”

Batare da ta ɗago ta kalleta ba tace”dan Allah jahad ki bari na ƙarasa shanye wannan madarar dana haɗa da zuma,”

Tsoki jahad taja tare da wuce wa tana cewa”bazan bari kijamin ba,ni kinga tafiyata,”

“Dan Allah ki jira ni ukuty,kada ku tafi ku barni,”ta ƙarasa maganar tare da tashi cikin sauri ta wuce cikin bedroom ɗinsu don ta sanya uniform ɗinta,”

Fitowa jahad tayi a farfajiyar gidan ta samu Motar Osman yana jiransu,cikin sauri ta ƙarasa tare da buɗe back seat na motar tashiga daga ciki tana gaishe shi ”

Amsa mata yayi sannan yace”ina ɗayar take ne”?

“Nabarta aciki,idan zata 6ata mana lokaci mu tafi kawai,”acewar jahad,

Suna cikin maganar saiga hossana tafito da saurin gaske harta kammala shiryawa cikin nata uniform ɗin,hannunta na ruƙe da school bag ɗinta,

Tana ƙarasowa ta wuce front seat ta buɗe tare da shigewa ciki ta zauna,

Murmushi osman ya ɗan saki tare da kallonta yace”ta gaban mota,yau ba gaisuwa ne,”

ɗaure fuska tayi tare da cewa”banason magana ni,ko ƙoshi banyi ba an taso ni,makaranta makaranta kamar in nayi aljanna za’a sani,”ta ƙarasa maganar tare da jan guntun tsoki,

dariya suka sa gaba dayansu hakan ya ƙara tunzurata,

Jan motar Osman yayi tare da fucewa dasu daga cikin gate ɗin gidan,

Abu kamar wasa suna cacar baki da jahad,sai ga hossana ta dawo back seat wurinta,harara jahad ta watsa mata tare da cewa”shiyasa nace ke zararriya ce in ba haka ba,taya zaki dawo daga gaban mota zuwa inda nake salon jan faɗa ko,”

Jin wannan maganar yasa hossana ta cakumi wuyan hijabin jahad,nan fa suka shiga dambatawa acikin motar,duk yarda osman yaso ya dakatar dasu abun ya faskara,sun cika motar da tsiwa sai faman kokoyi sukeyi,

A haka ya samu ya ƙarasa dasu cikin makarantar,tsayar da motar yayi tare da fitowa ya bude masu ƙopa,kowacce daga cikinsu sai faman huci takeyi,rai a6ace hossana ta sungumi school bag ɗinta tare da wuce wa fuuuu tabarsu a motar,

cikin sanyin murya osman yace”ke ma meyasa kike biye mata?ina ganinki mai hankali bai kamata ace kina biye ma hossana ba,itafa yanzu tamkar kanwarki take saboda ta6in hankalin da ke gare ta,”

tuni idon jahad sun cicciko da kwalla saboda tsananin 6acin ran yarda Hossana ta cakumi hijabin jikinta duk tayi uban squeezing kamar batayi guga ba,jiki asanyaye takai hannu tare da ɗaukar school bag ɗinta sannan tasa ƙafa ta fito daga cikin motar tafiya ta soma yi tana matse kwallar idonta,

Sam osman baiji daɗin hakan ba,dama kusan kullum in zai kawosu school sai sunyi faɗa acikin motar kuma duk Hossana ce sila,sam batasan zaman lafiya kamar ƴar dambe haka take,

Shiga cikin motar yayi tare da janta yabar cikin makarantar,

“Madam kin yada ribbom ɗinki,”wata irin sanyayyiyar murya ce ta ratsa kunnanta,dakatawa jahad tayi da tafiyar sannan cikin sauri ta juyo don taga wanene,

Waro ido waje tayi tana kallonshi saboda tsabar mamaki abun kamar a mafarki take ganin shi,

zuƙunnawa junaid yayi tare da kai hannu ya ɗauki ribbom ɗin jahad dake yashe ƙasa,ɗagowa dashi yayi a hannunshi fuskar nan tashi ɗauke davwannan ƙayataccen murmushin nashi ya miƙa mata shi tare da cewa”basai kin gode mun ba,nayi ne don Allah,”har lokacin bai ɗago da idonshi ba ya kalleta,la66an jahad har kerma sukeyi wurin son ta buɗe baki tayi mashi magana amma sam tagaza,gaba daya ta sandare a tsaye tana kallon kyakkyawar fuskar junaid,

Ganin taƙi yin motsi bare ta kar6i ribbom ɗin nata,hakan yasa yakai hannunshi tare da ruƙo yatsun hannun jahad,bude tafin hannun yayi tare da sanya mata ribbom ɗin aciki,

Sannan cikin sauri ya juya tare da tunkarar motar shi ya buɗe ya shige ciki,sannan yayi mata key tare da janta ya karya kwana tare da fucewa daga babban gate din makarantar,

Sai lokacin jahad ta sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya,tunani tashiga yi anya ba gizau yayi mata ba kuwa?taya zata ga mutumin data zana a zahiri kuma a kusa da ita yanayi mata magana”?gaba daya tayi confusing ɗin kanta,daƙyar ta iya jan ƙafarta tare da nufar hanyar class ɗinsu,

 

***********************

bayan sun kammala aiki acikin kitchen ɗin Hayaam ce ta shiga kai abincin tana jerawa asaman d table,bayan ta kammala jera musu ta koma cikin ɗakinta,bata jima da shiga ba sai ga kiran sofwan ya shigo acikin wayarta dake ajiye saman pillow ɗinta cikin sauri takai hannu tare da ɗaukar wayar takara a kunnanta ko sallama bata yi mashi ba kuma bata jira yayi mata ba tace”sofwan ina trolley ɗin kayana yake?jiya nabarshi acikin boot ɗin motarka,inaso ka kawomin shi yau ɗin nan ina jiranka,”tana faɗin hakan tayi rejecting kiran tare da mayar da wayar ta ajiyeta asaman pillown,

murmushi tashiga saki tunawa da abun harinta Sgr,cike da zumuɗi tashiga toilet donta gyara jikinta saboda takai mashi breakfast ɗinshi,

Sai da ta fito daga cikin toilet ɗin sannan ta tuna cewa babu fa kayan da zatayi gayu dasu hatta kayan kwalliyarta duk suna acikin trolley ɗin nan data baro a boot ɗin motar Sofwan,tsoki taja tunawa da wannan,tunani tashiga yi yanzu ya zatayi taje wurin shi,gashi wannan short gown ɗince ajikinta,murmushi ta saki tunawa da hijabin data zo dashi,don haka cikin sauri ta buɗe wardrobe ɗin dake a ɗakin don anan ta ajiyeta jiya,

ɗaukowa tayi tare da zura hijabin ajikinta sannan ta kama hanya ta fito daga cikin ɗakin tana tafiya anatse kamar wata kamila,

lokacin data fito daga cikin corridor ɗin anan tasamu mutanen gidan sun hallara a saman dining chairs sunayin breakfast,

Jin takun tafiyarta ne yasa suka ɗago gaba ɗayansu suna kallonta,hakan yasa hayaam duk tabi ta dabarbace tashiga ƴan kame kame,

“Azmee wacece wannan ko bakuwa mu kayi ne”? Abbansu ne yayi wannan tambayar saboda bai gane fuskarta ba,

Fawan yace”kamar ƙanwar Amani naga suna ɗan yanayi ,”

Kowa da hasashen shi akanta,amma basu ganeta ba kai tsaye,

Murmushi azmee tayi tare da cewa”wannan Hayaam ke nan,kanwar su Amani,jiya tazo gidan nan alokacin duk bakunan kun fita,”

fuska a sake Abbansu yace”Masha Allah,shine tayi mana zuwan bazata batare da ta sanar damu ba”?jin yarda abbansu yayi maganar fuskarshi ɗauke da farin ciki hakan yasa hayaam ta ƙarasa wurinsu tana faman sakin murmushi,gaishe da abbansu ta shiga yi,

ɗan ɗaure fuska yayi cike da zolaya yace”gaskiya fushi muke dake,saboda bakyason zumunci,gashi nan har mun fara mantawa da kamannin fuskarki,meyasa baki leƙo mu”?

Sunnar dakai tashiga yi tana cewa”ayimun afuwa Abba,abubuwane sunyi mun yawa shiyasa bansamu lokaci nazo ba,Amman kuna araina shiyasa nazo wannan karon don na goge laifina,”

Kallon juna Ayaan da jahan su kayi bakinsu kumshe da dariya,dama su ba’ayi masu gwaninta,su dai su jabeer basu ce komai ba,binta kawai sukeyi da kallo,kanal yousouf kuwa hankalinshi na akan abincin da yake ci,amma yana sauraronsu,

Murmushi Abba yayi tare da cewa”koke fa,yanzu naji magana,ina fata dae azmee tayi maki tarba mai kyau ko”?

ɗaga kai tayi alamar eh tace”Aunty azmee ta karramani sosai,”ta ƙarasa maganar tare da kallon fawan tace”Ya jikin naka fawan?naji abunda ya faru dakai fawan nashiga damuwa sosai lokacin naso nazo na dubaka,amma bansamu halin zuwa ba,shiyasa nayi wannan zuwan na musamman saboda kai,”

baki asake fawan ke kallonta irin kallon rainin wayon nan,can kuma sai ya ɗan waske tare da sakin murmushi yace”nagode sosai da wannan kulawar taki,kuma jiki Alhamdulillah naji sauƙi sosai,”

Jahan yace”ae fawan ya riga daya warke,da kinsani kinyi zaman ki agida,ko waya kin bugo kiyi mashi ya jiki,basai kinsha wahalar takowa kinzo ba,”

“Wannan haka yake Jahan,”acewar Ayaan,

Nan da nan jikin hayaam yayi sanyi tashiga zazzare ido tana mazurai don bataji daɗin abunda suka ce ba,

 

Abbansu kuwa ba ƙaramin daɗi yaji ba,jin yarda ta nuna damuwarta akan jinin shi,kuma har ta tako tazo donta duba shi,

Yace”Gaskiya naji daɗin jin maganar nan taki sosai,fawan yaji sauƙi sosai,ga alama nan ma kin gani,”yayi maganar yana nuna Fawan dake tura wainar kwai abakinshi,

Murmushi suka saki atare ita da Azmee,

“Amma dae ina fata zaki zauna mana ko?don banason wannan zuwan naku shaf shaf azo atafi kamar ana korar mutum,”

ƴar dariya hayaam tayi tare da cewa”a’a abba insha Allah wannan karon har sai kun gaji dani,”

Jin wannan maganar ta hayaam,yasa su twins sakin cokulan dake a hannunsu atare cikin plate suka bada wani sauti wanda yaja hankalin kowa kansu,kumshe dariya su irfan su kayi saboda sun gane dalilin dayasa su twins suka saki cokulan hannunsu,

Tuni hayaam taji ta muzanta duk tabi ta turniƙe fuska tana ɗan tsuke baki,

Sai lokacin kanal yousouf yace”muna maki barka da zuwa baƙuwarmu,koda yake ke fa ba baƙuwa bace ƴar gida ce,”ya ƙarasa maganar da murmushi a fuskarshi,

Ba ƙaramin sanyi hayaam taji ba jin abunda yousouf yace mata,nan tashiga sakin murmushi tana cewa”ngde sosai yaya yousouf da tarbar dana samu a wurinka,”

ta jima tana gaisawa dasu kafin daga bisani ta wuce kitchen don ta shiryama sgr breakfast ɗinshi,

Bayan tafiyarta marshal omar ya sauko downstairs ɗin ya shirya tsaf acikin jean da t -shirt,ƙarasawa yayi wurinsu tare da samun wuri ya zauna shima,gaishe da abbansu yayi, da fara’a a fuskarshi ya amsa mashi,sannan su kuma su Yousouf suka shiga gaishe dashi,amsa masu ya shiga yi kafin daga bisani yace”Ya muka ji da abunda ya faru da suba”?

murmushi su kayi gaba ɗayansu kanal yousouf yace”gaskiya ba ƙaramin tashin hankali muka shiga ba,especially Abbanmu don nasan ƙiris ya rage zuciyarshi ta buga,saboda babynshi,”

Dariya suka kuma yi,girgiza kai Abbansu yayi tare da cewa”oh nazama abun tsokana ko?ae bani kaɗae naji jiki ba,kowa acikin ku sai da hankalinshi ya tashi akan halin da junaid ya shiga,’

Fawan yace”wai ina ma junaid ɗin yake ne”? Ya tambaya yana kallon abban nasu,

gaban azmee ne ya faɗi rass saboda tasan cewa duk basu son cewa shi ke kai sehrish school ba,

Kafin tace wani abu muryar abbansu ta katseta da cewa”tunda asuba yabar bedroom ɗina,ina tunanin ko yaje kai sister ɗinshi school ne,don naji ran nan yana cewa zai kaita school ne a motarshi,

Tunkan ya ƙarasa maganar tashi fawan yace”What!!junaid shike kaita school?for what reason?basu da school bus ne”?ya tambaya yana kallon abban nasu,gaba daya abun ya ɗaure masu kai,

Kanal yousouf ne yace”its enough pls,ku bari muyi breakfast cikin kwanciyar hankali,inyaso daga baya munyi magana akai,”

Jinjina kai kawai sukayi tare da mayar da hankalinsu akan abincin da suke ci,shi dai Marshal Omar baice komai ba hankalinshi na akan farfesun da azmee ta zuba mashi a plate,

 

*SGR*

 

Anatse yake danna laptop ɗin dake gabanshi,yana zaune acikin palourn shi saman royal sofa mai mazaunin mutun uku,bakomai yake jira ba face breakfast ɗinshi,ba ƙaramin wanka ya dauka ba,wrap shirt ce ajikinshi White colour tare da black trouser wow kyau iya kyau,sai ƙamshi ke tashi ajikinshi ta ko’ina,ga wani gyara da yayi ma sumar kanshi mai matuƙar jan hankali,fuskarshi kuwa kamar wanda yayi makeup saboda kyau,

Ƙarasowa part ɗinshi hayaam tayi fuskar nan washe sai faman ɗokin ganin shi take yi,hannunta na ruƙe da tray mai ɗauke da kayan breakfast ɗinshi da ta haɗo mashi,

Tsayawa tayi daga bakin ƙopar shiga ta kashe murya tare da yi mashi sallama,

amsa mata sallamar yayi da wannan daddaɗar muryar tashi yace”wa’alaikum salam,” har wani lumshe ido hayamm take tana leƙen shi ta ciki,

A hankali ta zura ƙafa tashiga cikin palourn nashi cike da kwarkwasa ta ƙarasa inda yake tare da ajiye mashi tray ɗin asaman table sannan ta matsa mashi da table ɗin a kusa dashi,

tsayawa tayi tana bin shi da kallon ƙurulla kamar wata mayya,ji take kamar ta lashe shi don tsabar sha’awarshi da take ji kamar zata kai mashi attack haka ta dinga yi,

daƙyar tasamu natsuwar cewa”Gm sir,ina fata ka tashi cikin ƙoshin lafiya,”

tun daga kan muryar hayaaam ya gane cewa ba yarinyar nan bace dake kawo mashi abinci ba,

Amsa mata kawai yayi da”Alhmdllh,”

Cike da zumuɗi tace”ga breakfast nan na kawo maka,bari na zuba maka,”cikin sauri takai hannu zata ɗauki plate kenan ya dakatar da ita da cewa”dama kece ke kawomin breakfast”?yayi maganar yayin da idonshi ke akan laptop ɗinshi,yana daga ɗan kishingiɗe

Fari da ido hayaam tayi tare da cewa”No bani nace,ita tana a school ne shiyasa na kawo maka,kuma inaso daga yanzu naci gaba da kula dakai…..’tun kafin taƙarasa maganar yace”Why”?

cikin en ina hayaam tace”saboda ita yarinya ce,abubuwa sunyi mata yawa,kuma tana makara a school ne,wannan dalilin ne yasa Aunty azmee tace naci gaba da yin aikinta ina kawo maka abinci kuma ina gyara maka part dinka,’

Kusan minti biyar baice komai har sai da ta gaji da tsayuwa sannan taji yace”Call azmee 4 me!”

dan zaro ido hayaam tayi jin abunda yace murya na rawa tace”aunty azmee nabarta a kitchen ne kuma tace mun zata shiga wanka ne,yanzu haka ma shi take cikin yi,”

Yamutsa fuska sgr yayi sam baya jin daɗin muryarta ta cika hayaniya da alama,

“Its okey,ki tattara kayan abincin nan da kika kawomin ki mayar dasu inda kika ɗauko su,”

hankali tashe Hayaam tace”sir,saboda me”?

Kai tsaye yace”ba’a sharing  aiki na,I just need one person to be doing it,kuma bana son dogon zance,so u ave to leave tun kafin raina ya 6aci,sannan muddin ba ita yarinyar zata kawomin breakfast ba ko wani aiki banason sake ganin wani ya shigo min part ɗina!bana son shashanci,”

Tuni idon Hayaam sun ciko da kwalla don ita bata iya 6oye 6acin rai ba,zuciyarta har wani tafarfasa takeyi saboda tsabar takaici,ba ƙaramin tozarta tayi ba a wurinshi,taji kunya sosai inda ta gode ma Allah ma bai ɗago ya kalli fuskarta ba,

daƙyar take iya haɗiye yawu a maƙogwaronta saboda ɗacin da taji yayi mata,hannu takai rai a6ace ta ɗauki tray ɗin tare da kama hanya ta fuce daga part ɗin nashi,tafiya take tana faman sambatu,yau taji kunyar da bata ta6a ji ba,ranta yayi mugun 6aci kuma taci alwashin cewa sai ta wulakanta sehrish,sai taja mata sharri awurinshi da sauran mutanen gidan,da wannan mummunan ƙudirin nata ta sauko down stairs tare da nufar kitchen,

..yarda take tafiya atsiyace yasa su fawan da suka rage a dining area ɗin dagowa suna kallonta,tunda suka ga hannunta ɗauke da tray ɗin kayan abinci ransu ya basu cewa Babban yayansu ne yace ta maido shi,

dariya sosai fawan yayi tare da cewa”ita waccan batasan cewa ba’ayi mashi shisshigi ba,daga zuwa jiya jiyan nan harta fara zumuɗin kai mashi abinci,dama ni saida raina ya bani cewa wani abu ya kawota gidan nan ba don dubiya tazo ba,”

irfan yace”aiko tayi ta gama indai babban yayanmu ne ko kallo wancan muciyar bata isheshi ba abu tana tafiya kamar zata tashi sama,”

Fashewa sukayi da dariya gaba ɗayansu,

Jahan yace”ae ɗazu baku ga muna kumshe dariya ba,in banda neman kai komene ya kawota gidan hadasu kwanar mana,kuma har tana cewa wai har sai mun gaji da ita…’

tunkan ya ƙarasa maganar Fawan yace”ae kuwa da ƙafafunta zata bar gidan nan!ku zuba ido ku gani,in banda abun kunya taya ƙanwar matar yayanmu zata kwaso ƙafa zata gidanmu hada su zama?bayan tasan cewa duk maza ne acikin gidan?da alama mijin aure tazo nema itama,harda fakewa da tazo dubani” muryarshi ɗauke da dariya ya ƙarasa maganar,

“Shiyasa naga tafara kamun ƙafa wurinsu babban yayanmu tunkan aje ko’ina,da yake hankalin ɗiyar roba gareta,ina laifin ma tafara ta wurin haroon don shine mara Alkibla duk inda ta fadi daidai ne” a cewar Khaleed,cike da nishadi sukeyin firar tasu,hayaam dae taga takanta tun awurin ƴan gida bata samu kar6uwa ba,dama irinsu masu mummunan aniyyar nan basu cika farin jini ba ko a idon jama’a,

Tunda tashigo kitchen ɗin hannunta ɗauke da tray Azmee ke kallonta da mamaki a fuskarta tace”hayaam ya akai naga kindawo da breakfast ɗinne?ko bai cikin part ɗin nasa ne,”

fuska a yamutse tace”yana nan,nakai mashi amma yace shi ba’a sharing aikin sa,in mayar da kayan abincin bazaici ba,indai ba wannan yarinyar bace ta kawo mashi ba,”ta ƙarasa maganar tana hura hanci,

jin wannan maganar yasa hankalin azmee tashi,sarai tasan da maganar bayason ana mashi exchanging mai kula dashi don bai yarda da mutum biyu ba a lokaci ɗaya suna mashi aiki hakan ya sa6awa ƙa’idarshi,lokacin baya azmee ce ke ɗawainiya dashi in yazo nigeria,wannan karon kuma tunda yadawo daga Us sehrish ce ta ɗaura daga inda azmee ta tsaya,tun ranar farko daya dawo daga us,sehrish ce tafara kai mashi abinci wannan dalilin ne yasa ta samu kar6uwa a wurinshi,yanzu indai ba sehrish bace zata kai mashi abinci ba,tofa bai yarda da kowa ba in ba Azmee ba,

ɗan murmushi azmee tayi tare da cewa”kash!wlh namanta ɗazu in sanar dake cewa ki bari takai mashi,saboda Sgr baya son mutum biyu suna ɗawainiya dashi,bai yarda da wannan ba,am really sorry bari ni nakai mashi,ta ƙarasa maganar tare da kai hannu ta kar6i tray ɗin dake a hannun Hayaam sannan ta kama hanya ta fuce daga cikin kitchen ɗin,

tamkar ta aza hannu akai tafasa ihu haka taji,rai a6ace ta fuce daga cikin kitchen din,bedroom ɗinta ta koma tana faman cizon la66a tana zagaye ɗakin yayin da take faman sakin hucin 6acin rai,tunani tashiga yi taya zata kwace wannan matsayin da sehrish ta samu a wurinshi!!!!dole ne ta shirya mata tuggu…………….

 

 

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖

 

 

 

Amalil Islam

 

Kwance take saman gadon asibitin hankalinta kwance sai faman sharar bacci take,tasamu kulawa sosai wurin nurses ɗin nan gaba daya duk wani rauni da taji anyi mata dressing ɗin wurin,a daren jiyan nan har ƙarin ruwa su kayi mata fiye da leda ɗaya don taji jiki,da safe kuwa kyakkyawan breakfast tasamu na kyauta da suke rabawa asibitin,sai da taci tayi hani’an sannan tafara wannan baccin,har farkawa tayi tana neman waɗanda suka kawota asibitin don su kira mata Auntynta kamar yarda ɗaya daga cikinsu yayi mata alƙawarin cewa zai kira mata ita, nurse ɗin dake kula da itace ta sanar da ita cewa basu zo ba,sam hankalinta bai tashi ba,don ita ji take koda basu zo ba,ba inda zataje ita fa tayi gida acikin asibitin don ba ƙaramin daɗinshi take ji ba,

 

Wuraren ƙarfe 12,Motarsu Jahan ta shigo cikin katafaren asibitin,a hankali sukayi mata gurbi a parking space ɗinsu,ɗagowa jahan yayi tare da kallon ayaan dake a gefenshi yace”zan jiraka anan and don’t keep me waiting”

Wurga mashi kallo Ayaan yayi tare da cewa”bro kai fa baka da imani na lura,jiya kaine kayi causing accident ɗin nan,yarinyar ta raunata amma ko zuwa ciki ka leƙata bakayi ba,atlease ya kamata kaje ka dubata yau,”

ɗaure fuska Jahan yayi yace”bani ne Sila ba!yarinyarce ta fado mana agaban moto dinmu all of a sudden,har nagaza cin burki,so am not guilty,’

Cikin lallashi ayaan yace”pls mu shiga atare mana,”yarda yayi maganar da ƴar shagwa6a afuskarshi yasa Jahan cewa”taci albarkacin wannan shagwa6ar da kayimun da ba don haka ba,ba inda zanje,”

Murmushi Ayaan yayi tare dasa hannu ya buɗe motar ya fito waje,shima Jahan ya fito daga cikin motar,atare suka jera tare da nufar interior din asibitin,

Ayaan ne ya fara shiga room ɗin da aka kwantar da Amal sannan jahan yabi bayansa suka shiga ciki atare,

Lokacin da jahan ya aza idonshi akan Amal dake baje saman gadon tana sharar bacci,a wani irin firgice yaja da baya yana faman zare ido,

Kallonshi ayaan yayi tare da cewa”meya faru ne bro?naga kamar ka tsorata da wani abu,

Nuna amal yayi da yatsan shi tare da cewa”Ayaan dama wannan halittar muka kwaso acikin motar mu jiya?shiyasa akace rashin sani yafi dare duhu Ya ilahi da nasan hakane da ban sha wahalar ɗaukota ba Allah,dole ayi mana wankin mota yau,”

baki asake ayaan ke kallonshi,duk wani wulakanci da anzo kan Jahan to an ƙare,don shi kankat ne dama yana ɗaya daga cikin waɗanda suka ɗauko ɗabi’un mahaifiyarsu da halayyarta kaf bai bar komai ba,”

girgiza kai kawai Ayaan yayi tare da wucewa wurin gadon da Amal take,wuri yasamu asaman chair ɗin dake fuskantar gadon nata ya zauna yana kallonta gwanin ban tausayi,

Jahan kuwa koda ya matso wurin bed din nata,goya hannun shi yayi asaman ƙirjin shi yana binta da kallo a ƙyamace yace”Anya Ayaan yarinyar nan ma tana numfashi kuwa?karfa mu ƙarasa gawar da ba tamu ba”

Murmushi kawai Ayaan yayi tare da kai hannu ya dan bubbugi pillown da Amal ta kwantar da kanta sama,

Firgigit ta ware idanunta tana faman binsu da kallo ganin mutum biyu iri ɗaya,hannu tasa tare da ɗan murza idanunta tana ƙare masu kallo, lokaci guda ta gane cewa identical twins ne,

“Barka da safiya,ya jikin naki,”?ayaan ne ke tambayarta fuskarshi asake,hakan ne yasa ta gane cewa shine na jiyan nan da yayi mata alƙawarin kiran Auntynta,

Ƙoƙarin tashi Amal tashiga yi,cikin sauri Ayaan ya taimaka mata ta zauna tare da dan tada bayanta a jikin pillown,

Cikin sanyin murya tace”Alhmdllh,naji sauƙi sosai,”

“Kinyi breakfast”? Ya kuma tambayarta,ɗaga mashi kai tayi alamar eh,

Lumshe idonshi yayi tare da cewa”Masha Allah,so now tell me, how can i help u? Zuba mashi ido tayi tana kallonshi,hakan ya tabbatar mashi da cewa bata gane me yake nufi ba,don haka yace”ina nufin taya zan iya taimaka maki ne?wurin haɗuwa da Auntyn naki”?

Cikin sauri tace”ina da numbarta akaina,”

Amsa mata yayi da okey,sannan ya zura hannunshi acikin trouser pocket dinshi ya ciro wayarshi,karanto mashi numbar Amal tashiga yi shi kuma yana dialling numbers ɗin acikin wayarshi,bayan ya kammala rubuta numbar ya buga call ɗin nan take Sunan Matar yaya ya bayyana akan wayarshi,tsananin mamaki ne ya kama shi aranshi yace wannan ae numbar Amani ne matar Yaya Abbas,kanshi ya gama ɗaurewa a lamarin,har kiran ya katse amani bata ɗaga ba,almost 6 times yana kiran numbarta amma ba’a daga ba,hakan yasa ya ɗan dakata tare da kallon Amal yace”idan ba damuwa inason jin yaya kuke da Auntyn nan taki da kika ban numbarta….’tunkan ayaan ya ƙarasa maganar jahan ya buga tsoki tare da cewa”Ayaan am tired ka tashi kawai mu tafi,bansan menene amfanin tambayarta ba,

mayar da idonshi yayi akan na Jahan yace”pls ka bani time,zan faɗa ma dalilin dayasa nake tambayarta,”

tsuke fuska jahan yayi yana faman hura hanci,

“Ina sauraronki,” muryar ayaan ce ta katse mata tunanin data tafi,

Murya asanyaye tace”ƴar uwatace ita,na jima ina nemanta bamu ta6a haɗuwa da ita ba,ita ma kuma nema na takeyi,tunda tayi aure na rabu da ita,shine yanzu nasamu sunan garin da take nazo,amma bansan a ina zan sameta ba,abu ɗaya kawai nake dashi numbar wayarta,drivern daya kawoni ya kirata a waya ya sanar da ita cewa tazo ta ɗauke ni,batazo ba shine wasu mutane suka biyoni acikin tashar,wannan ne dalilin dayasa nayi gudu harna faɗa saman titi Motarku ta buge ni………’

jinjina kai Ayaan yayi tare da cewa”Yanzu idan na kaiki gidan Auntynki,Ni kuma wani tukuici zaki bani,”

cike da mamaki tace”kasan inda take ne”?

Lumshe idonshi yayi tare da cewa”a’a bansan inda take ba,amma inaso zan kaiki wani wuri in ba damuwa,bari nasa doctor ya sallame ki,sai mu tafi atare,Zaki bini?

shiru ta danyi tana tunanin karfa tayi gangancin binsu wani abu ya faru da ita,tunda ita dae batasan ko su wanene ba,amma ta wani 6angaren taji cewar zata iya binsu saboda ta yarda dashi sosai,ba don komai ba sai don yarda yake yi mata magana cikin lallami,”

amsa mashi tayi da eh,miƙewa ayaan yayi daga saman chair din,ruƙo hannun jahan yayi tare da janshi gefe guda yace”ko kasan cewa numbar da yarinyar can ta bani na kira mata auntynta,ta matar Ya Abbas ce Amani!”

Fuska ɗauke da mamaki Jahan yace”Really?kenan ƙanwarta ce ita,amma indai hakane ya akai ita yarinyar ta kasance haka?

Ayaan yace”abunda nake tunani kenan nima,”

jahan yace”Ba shakka,dama na jima ina tunanin taya akai Ya ishaq da Ya Abbas suka auri waɗannan matayan nasu,Nidae raina ya jima yana bani cewa matsiyatan talakawa ne,saboda koda mu kaje ɗaurin aure fa a maid,bakaga tsohonsu ba wani zararre dashi,yadin jikinshi duk ya koɗe,zariyar wandonshi fa har ƙasa take ja,abun kunya…’

Rufe mashi baki Ayaan yayi cikin sauri saboda yarda yake magana yana ɗaga Voice ɗinshi,yarinyar zata iya ji,

“Pls jahan its okey,mubar wannan zancen nidae yanzu so nake mu ɗauki yarinyar mukaita gidan Auntyn nata…’tunkan Ayaan ya ƙarasa maganar Jahan yace”Wai a motar wa kake nufin za’a kaita?ae wlh waccan sauran  ramin bazata ƙara zauna mana a motar mu ba,sai dai ka tsaida taxi ta kai ku atare,ni kaga tafiyata”yana kai ƙarshen maganar tashi ya juya tare da fucewa daga cikin room ɗin,

girgiza kai kawai Ayaan yayi tare da cewa”sai yanzu nasan da wa nake tare,Jahan sam baka da mutunci,haihuwarmu kawai akai atare amma zuciyoyinmu ba iri ɗaya bane,ni ta 6angaren Abba nake kai kuma ta 6angaren Mommynmu kake da kuma Ammi dama sune masu zafi,’

 

Batare da 6ata lokaci ba,Ayaan yasa aka sallami Amal ba don komai ba sai don yayi suprising ɗinta,kamar yarda jahan yace sai dai su hau taxi hakan ce tafaru,a bakin Hospital ya tsayar masu da taxi suka shiga ciki atare,

 

**********************Reeshi

 

Zaune suke acikin class sun natsu suna sauraron karatun da akeyi masu,malaminsu ne mai koyar dasu islamic studies,tun da ya fara karatun ya lura da yarinyar dake kwance tana yi mashi bacci acikin class,shiru kawai yayi baice komai ba,sai da ya kammala karatun sannan yace”wacece waccan yarinyar dake yi mun bacci acikin class”?ya tambaya yana nuna sehrish da maker ɗin hannunshi,

kamar jira ƴan class ɗin sukeyi ya tambayesu nan fa kowa yashiga bada bayani,

“Uncle ae wannan yarinyar da kake gani sleeping sickness gare ta,ba’a ta6a yin darasi ba idonta biyu,kullum cikin bacci take kamar mai tsohon ciki,” fashewa da dariya ƴan class din sukayi,

Wani kuma yace”sir,da zarar tearcher ya shigo cikin class shikenan zaka ga ta fara hamma,daga nan sai bacci,”

Bayan ya gama sauraron bayanansu,ya taka ya ƙarasa inda seat din sehrish yake,hannu yasa tare da ɗan bugun desk din,a firgice sehrish tafarka tare da ɗago da kanta daga saman desk ɗin tana kallonshi,

jallabiya ce ajikinshi fara,ya tara dogon gemu,kana ganinshi zaka san cewa ba ƙaramin malamin addini bane,fuskarshi na manne da farin glass yayin da kanshi ke anaɗe da rawani,

hankali tashe sehrish ke kallonshi tayi wuƙi wuƙi da ido saboda tsoran karya hukunta ta akan baccin da take yi mashi a class,

Cikin harshen larabci yace mata ta miƙe tsaye,jiki na rawa sehrish ta miƙe tana faman zazzare ido,

“Kalli cikin idona,”ya bata umarni,sunnar dakai sehrish tayi tana faman jin wani irin bugun zuciya,maimaita mata ya sake yi da cewa”bakiji me nace ba!ki kalli cikin idona!”

ƙin ɗagowa tayi da idonta ta kalleshi,kuma nan take jikinta ya shiga yin kerma,

Ƴan class ɗin duk sun zuba ido suna kallonsu,musamman amrish da tashiga damuwa ganin kamar malamin nason takurawa ƙawarta,

Cikin sauri tace”pls uncle ayi mata afwa,bazata ƙara ba,’

Batare da ya kalleta ba yace”Amrish ba laifi tayi mun ba,in fact nikeson taimakonta,shin wannan yarinyar ƴar wani gida ce”?ya tambaya yana jiran amsarsu,har lokacin sehrish na tsaye kanta na kallon kasa a matuƙar tsorace take,

amsa mashi su kayi da cewa”bamu san a wani gida take ba,lokacin da aka kawota class ɗinnan tayi introducing ɗin kanta amman bata faɗa mana family status ɗinta ba,,’

Amrish tace”nima bansan taƙamaimai daga inda take ba,amma akwai wani elder bro dinta dana sani sunan Shi Junaid romeo,muna shiri sosai dashi,’

mayar da idonshi yayi kan fuskar sehrish yace”Ke!a wani gida kike?su wanene iyayenki?

murya na rawa tace”Ni….ni..daga family din SALAHUDDEEN HUSSEIN nake Abban sojoji….’tunkan ta ƙarasa maganar malamin ya waro ido waje yana kallonta,bama shi ba hatta sauran student ɗin cike da mamaki suke kallonta,sun jinjinawa gidan da tafito bakomai yafi ɗaure masu kai ba face yarda ta kasance ba ruwanta da kowa haka,bayan duniya tasan da zamansu,

“Kina nufin ke ƙanwar Surgeon genaral rafayet ce!da marshal Omar!”?

Amsa mashi tayi da cewa”eh,”kuma har lokacin bata ɗago da ido ta kalleshi ba,

Jinjina kanshi yayi yana tuna wani abu daya ta6a faruwa dashi wanda ke da alaƙa da gidan,”

gajiya da tsayuwa sehrish tayi nan take idonta suka soma shararo da kwalla,don bata da juriyar wahala irin hakan,tun lokacin data fara rayuwar hutu da jin daɗi,

“Insha Allah bazan fasa ba,kamar yarda nayi kyakkyawar niyyar taimakawa tun a lokacin baya,don haka zan taimaka maki tunda Allah ya haɗani dake,” malamin ne yayi wannan maganar,sannan ya mayar da idonshi kan amrish dake zaune a seat ɗinta tana kallonsu yace”Amrish idan na kammala yi maku karatu ki same ni a office ɗina zan baki ruwan addu’a kiba wannan yarinyar tayi amfani dashi,”

Amsa mashi tayi da toh sir,sannan yaja da baya tare da juyawa ya koma wurin board,

Jiki asanyaye sehrish ta koma tare da zaunawa tana faman sauke ajiyar zuciya,aranta tana mamakin ruwan addu’ar mi zai bama amrish ta bata,gaskiya ni bazanyi amfani dashi ba,lafiya ta lou,koya ban zubarwa zanyi…….’

Sai faman sambatu takeyi ƙasa ƙasa sam takasa samun natsuwa har sai da Malamin yabar Class ɗin,tashi amrish tayi tare da binshi don ta amso mata ruwan addu’ar dayace zai bata.

 

bayan mai taxi ɗin ya sauke su,hannunshi ruke dana Amal suka shiga cikin gidan,gaba ɗaya duk tabi ta susuce tana kallon katafaren gidan duk a tunaninta kodai gidansu ne ya kawo ta? Lokacin da suka shiga katafaren palourn babu kowa acikin shi,tsayawa yayi tare da ita atsaye yana jiran ganin ko wani zai fito,ita kuwa Amal wuyanta kamar zai tsinke saboda kalle kalle muryar Ayaan ce ta katse ta da cewa”har yanzu ciwon na maki zafi?girgiza kai tayi tare da cewa”a’a babu zafi ina lafiya,”

“Okey,ki ɗan ƙara jira nasan matar gidan zata fito ne,bari na sake kiran layinta,”

Hannu yasa tare da ciro wayarsa yana ƙoƙarin danna ma Amani kira,kunnan shi suka jiyo mashi takun takalmanta kwas kwas,ɗagowa su kayi gaba ɗaya suna kallonta,hannunta na ɗauke da tray da alama kayan breakfast ɗinsu da suka ci na safen nan ta fito dashi daga bedroom ɗinta dake a upstairs,jallabiya ce fara ajikinta ta yafa mayafin akanta,

A hankali take saukowa down stairs sam bata lura da mutane ba,ƙura ido Amal tayi tana kallonta sam takasa gane wacece,juyawa ta danyi tare da kallon Ayaan tana neman ƙarin bayani,a lokacin shima idonshi na akanta yace”baki gane ta ba ko”?

ɗaga mashi kai tayi alamar eh,murmushi yayi tare da cewa”Bari ta matso kusa,”

Gyaran murya Ayaan yayi wanda hakan yasa Amani tayi firgit tana kallonsu,murmushi ta saki ganin Ayaan cikin sauri taƙarasa saukowa daga saman stairs ɗin ta tunkaresu,zuba mata ido Amal tayi tana kallonta tabbas taso ta shaidata amma abunda yayi confusing ɗinta shine,taya zata kasance wadda take tunani tunda saurayin ya kawota gidan tafi tunanin ko Auntynshi ce,

Tunkan Amani ta ƙarasa inda suke,hankalinta yakai ga Amal binta da kallo ta dinga yi cike da mamakin ina Ayaan ya samo wannan yarinyar haka,duk taji jiki kodai ya fara taimakon marayu ne,

tsayawa tayi kusa dasu idonta na akan Amal ita ma kallonta takeyi,ji tayi gabanta na faɗuwa rasss rassss,cikin sauri ta mayar da idonta akan Ayaan murya na rawa tace”who…who is she pls?

Murmushi ayaan yayi yace”i don’t even know,ni dai ta bani numbar auntynta ne tace na kira mata ita,shine dana sa numbar Auntyn nata sai sunanki ya bayyana akai,that’s why nayi deciding kawota wurinki,maybe adace………’tunkan ya ƙarasa maganar a firgice Amani ta saki tray ɗin hannunta ya tarwatse ƙasa,zube wa tayi saman guiwowinta kusa da Amal ɗin ta ruƙo hannunta tana cewa”Amal kece dagaske nake gani,ko idona ne Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un,”!!!

Tuni hawaye sun cicciko acikin idonta,

Itama Amal ɗin tuni ta fara shararo hawaye saboda ta ganeta yanzu musamman data ambaci sunanta,

Cikin shessheƙar kuka tace”Ni…Ni ce aunty Amani,ashe dama zan sake ganinki arayuwata………’kukane yaci ƙarfinta hakan ne yasa takasa ƙarasa maganar,atare suka fashe da kuka suna yi kamar kamar me,

Muryar Ayaan ce ta katse su da cewa”pls Aunty amani,ki lallasheta akwai wounds ajikinta idan tana kuka hakan zai ƙara mata raɗaɗin ciwon,”dakyar Amani ta tsagaita da kukan nata kallon fuskarta har izuwa jikinta,tayi matuƙar tsorata da ganin yarda yarinyar ta tsotse ta rame ta ƙanjame kamar kwarangwal,ƙashin wuyanta kamar zai ballo waje,komai na yarinyar da zai nuna cewa ita macece babu shi,sai dai ta hanyar shigarta ta mata da kuma muryarta,

Janyota tayi ajikinta tare da rungumeta sosai tana ci gaba da ambaton sunanta”Amal amal ɗita ce ta koma haka?meya faru dake Amal ya akai kika 6ata,ki ka tafi kika barni inata nemanki Amal,”

Ganin halin da suka shiga yasa Ayaan yanke shawarar tafiya yabarsu,juyawa yayi kawai tare da kama hanya ya fuce daga falon dama jahan sai doko mashi calling yake,

 

Anan ƙasa Amani da Amal suka zauna atare suna fuskantar juna,

“Amal kina jin yunwa”? Jin wannan tambayar yasa hawaye suka ƙara cika mata ido,yaushe rabon da wani ya tambayeta tana jin yunwa harta manta Allah sarki ɗan uwa mai ɗaɗi,musamman in ya kasance shaƙiƙin kane kuma kuna son junanku,

Murya asanyaye tace”bana jin yunwa naci abinci a asibiti,”

Jinjina kai Amani tayi tare da cewa”inason jin Ya akai kika 6ata Amal kika barni?mammy ta sanar dani cewa bakyajin magana wai kina zuwa yawo sun hanaki kin ƙiya shine kika 6ace aka neme ki aka rasa….’

Girgiza kai tashiga yi yayin da hawaye ke cigaba da sharara a idonta tace”Aunty amani wannan duk ƙaryace suke yi maki!nagode ma Allah da ya haɗani dake,a yau inaso zan sanar dake komai game da irin cin zalin dasu Mammy sukayimun na raba ni dake,

Hankali tashe Amani ke kallonta murya na kerma tace”faɗamun meya faru dake!wani irin cin zalin su kayi maki,”

Batare da 6ata lokaci ba,Amal ta zayyana mata duk irin ƙarairayin da sukeyi mata akan cewa ta 6ace,da kuma irin wahalar da takesha a hannunsu da kuma kaita da sukeyi gidan makwabtansu ana kulleta,babu abunda Amal ta 6oye mata kaf takwashe ta sanar da ita,

A kiɗime Amani ta miƙe tsaye cikin tsananin 6acin rai,jikinta har kerma yake yi,wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga shararowa a idonta,

Sai faman cizon yatsa take yi tana danasani,kai aƙarshe data rasa abunyi sai ta sake fashewa da wani matsanancin kukan tana girgiza kai tana cewa”Wlh bazan ta6a raga masu ba!mugaye azzalumai kawai,banta6a ganin mutane masu zuciyar kafirai ba irin tasu,Sun cutar dake Amal kuma sun cutar dani sun yaudareni sunyi mun ƙarya suna samun kuɗi awurina na cewa za’a ba malamai suyi addu’ar neman sa’a akanki ashe duk ƙarya ne!!!!basu tsaya a iya kanmu ba sun cutar da mahaifiyarmu har saida tabar duniya ga mahaifinmu da suke ta gana ma azaba,nayi tunanin soyyaya suke nuna min ta ƴan uwantaka shiyasa na saki jiki dasu har nake ƙoƙarin taimaka musu wurin cimma wannan mummunan ƙudirin nasu,ashe cutata suke suna can suna gana ma ƙanwata azaba,na cuci kaina!tun yanzu Allah ya fara nunamin irin kuskuren da nake ƙoƙarin yi na taimakama waɗancan bijimayen…….’tsagaitawa tayi da maganar tana faman shessheƙar kuka,daga bisani ta ɗaura da cewa”wlh saina tarwatsa duk wani plan ɗinsu uban kowa ya rasa don bazan kyalesu ba,muddin ina numfashi hayaam ko abra ɗaya daga cikinsu bazai ta6a auran jinin salahuddeen hussein ba!!!!,

abun ba ƙaramin ƙona ma Amani rai yayi ba,ta fusata ainin zuciyarta har wani tafarfasa take yi saboda 6acin rai,

Hannu tasa tare da matse kwallarta sannan ta juya tare da takawa takai hannu ta ruƙo hannun Amal ta miƙar da ita tsaye,sannan ta wuce da ita cikin bedroom ɗinta gado ta nuna mata tare da cewa”Amal ki kwanta ki huta kin raunata sosai,amma karki samu damuwa tunda Allah ya haɗaki dani ƙarshen wahalar ki tazo insha Allah,zakiyi rayuwa tare da Auntynki zan baki kyakkyawar kulawa,kuma zan kira doctor domin ya ƙara dubamin lafiyarki da kyau har kiji sauƙi,

Ba ƙaramin daɗi Amal taji ba farin ciki har bakinta ya gaza rufuwa,sai da amani ta tabbatar cewa Amal ta kwanta sosae saman gadon sannan ta zauna daga gefen gadon tana kallonta har bacci yayi awon gaba da ita,amani bata bar wurin ba,kallonta take hawaye na zuba a idonta haƙiƙa su Mammy da Aunty babba ba ƙaramin cutarta su kayi ba,

Jinjina kai tayi tare da cewa”rama cuta ga macuci ibada ne,Aunty laila kin shiga uku dani,zanbi duk hanyar da zanbi don ganin na tarwatsa plan ɗinki,dama ke jani talau ce sai yarda akai dake sannan kike bi,zanyi amfani da wannan damar wurin lalata shirinki”

Haka Amani ta dinga tufka da warwara a ƙarshe ta shirya nata plan ɗin.

****************

Hayaam na zaune saman gadonta hannunta ruƙe da wayarta tana jiran shigowar kiran Sofwan,harta fidda rai da zai kawo mata trolley ɗin sai ga message ɗinshi ya shigo wayarta,cikin sauri ta buɗe tana karantawa,

_hi beb ya kike ya kwanan gidan surukai ina fata kina lfy,nafa zo gidan ki turo wani ya amsar maki trolley ɗin kayan,don bazasu bar ni nashigo ba_

Jin hakan yasa tayi saurin saukowa daga saman gadon tare da ɗaukar dogon hijabinta dake ajiye saman gadon,zurawa tayi ajikinta sannan tafito daga cikin bedroom ɗin,kama hanya tayi ta fito main palour ɗin tana wurga ido don tasamu wanda zai kar6ar mata kayanta,tana cikin wannan tunanin sai ga Fawan ya fito daga part ɗinsu,

kwala mashi kira tayi cike da kisisina tace”Fawan”!

ɗagowa yayi yana kallonta da wannan kallon nashi na rainin wayau,

cikin sauri hayaam ta nufe shi sai da tazo kusa dashi sannan tace”dan Allah taimako nakeso kayimun,wani brother ɗina ne ya kawo mun trolley ɗin kayana,an hanashi shigowa ciki shine nace ko zaka taimaka ka amso mun,”

Yatsina fuska fawan yayi tare da cewa”Am sorry ni bazan iya wannan wahalar ba,zan dai kira ɗaya daga cikin security guards ɗin na basu umarnin su barshi ya shigo abokina ne inyaso sai kije ki kar6o kayanki,”

washe baki hayaam tashiga yi tana cewa”thank u so much fawan,kana da mutunci sosai naji daɗin taimakonnan da kayimun,’ ɗan ta6e baki fawan yayi tare da kai hannu ya ciro wayarshi a aljihun rigarshi,call ya buga tare da kara wayar a kunnanshi,ɗaga kiran akayi sannan ya sanar dasu cewa subarshi ya shigo abokinshi ne,amsa mashi sukayi sannan ya kashe kiran,

batare da ya kalleta ba yace”kije ki amso kayanki,”

da hanzari Hayaam ta juya tare da kama hanyar fucewa daga falon sai faman sauri take yi kamar zata tashi sama,

Ruƙe ƙugu fawan yayi tare da cewa”Ikon Allah,nifa bangane ma Yarinyar can ba,Naji tana cewa zata amshi trolley ɗin kayanta me hakan ke nufi”?ya jefa ma kanshi tambaya,cizon la66ansa yayi tare da cewa”zaki gane kuranki ne,”yana faɗin hakan ya kama gabansa

 

*💋Boss Bature💋*

 

Wuraren ƙarfe 1:30 junaid ya ɗauko sehrish daga school,tun acikin mota ya lura da yanayinta duk a yamutse babu natsuwa a tattare da ita,har tambayarta yayi ko bata jin daɗine,sai ta sanar dashi cewa bacci ne kawai take ji,jin haka yasa ya ƙara gudun motar har suka ƙaraso cikin gidan,

Fitowa tayi daga cikin motar tare da komawa ta buɗe back seat ɗin ta curo school bag ɗinta sannan ta wuce cikin gidan da sauri,

Abun ya ɗaure ma junaid kai,ganin ta tafi batare da ta jirashi ba kamar yarda suka saba shiga cikin gidan hannunsu ruƙe dana juna,

hannu yakai tare da buɗe motar ya fito bayan ya rufeta,ya kama hanyar shiga interior ɗin gidan,koda ya shiga main palour ɗin kai tsaye ya wuce upstairs bedroom ɗinshi don shima a gajiye yake,

wani irin zazza6ine ya rufar mata,dama tun lokacin da suka haɗa ido da wannan malamin taji gaba ɗaya yanayinta ya sauya,tana shiga bedroom ɗinta tayi wurgi da school bag ɗin ƙasa,sannan ta faɗa saman gadonta tare da kwantawa tana faman juyi asaman shi,

A wannan yanayin bacci yayi awon gaba da ita,

Turo ƙopar bedroom ɗin nata junaid yayi anan ya same ta tana ta faman sharar bacci ajiyar zuciya ya sauke tare da juyawa zai fuce daga ɗakin karaf idonshi suka sauka akan Bottle water ɗin da malamin nan yaba Amrish takai mata,ashe lokacin da ta shigo ɗakin tayi wurgi da jakar nan take robar ruwan ta gangaro daga cikin jakar,saboda ta manta bata rufe zeep ɗin wurin data sanyata ba,

Murmushi junaid yayi yace”Oh ni reeshi kamar wata ƙaramar yarinya,wai yawo da robar ruwa acikin school bag hmmm,”yayi maganar tare da ƙarasawa yakai hannu ya sungumi robar ruwan,

Jin salaf babu sanyi ajikin robar ruwan yasa shi cewa”bari naje na sanya mata shi a fridge,zai fi daɗin sha,”

Yana ƙarasa maganar ya juya tare da fucewa daga ɗakin nata,kai tsaye ya wuce wurin fridge ɗinsu,hannu yakai tare da buɗewa ya sanya robar ruwan aciki,sannan ya mayar ya rufe ya kama hanya yabar wurin,

 

After some minutes sai ga su twins sun faɗo cikin main palour ɗin dawowarsu kenan daga masallaci,raba hanya su kayi Jahan ya wuce bedroom ɗinsu,shi kuma Ayaan ya wuce wurin fridge saboda wani irin ƙishin ruwa da ta zo mashi,hannu yasa tare da buɗe fridge ɗin,ya ɗauko bottle water ɗin da Junaid ya ajiye,

Buɗe murfin yayi tare da kafawa abakinshi ya shiga ɗaɗɗakar ruwan,sai da yayi rabin robar ruwan sannan ya mayar da ita cikin fridge ɗin ya ajiye,

Shafa ƙirjinshi yayi tare da cewa”Alhamdulillalh yanzu naji wani sanyi ya ratsa maƙoshi na,”

Yana faɗin hakan ya nufi bedroom ɗinsu,lokacin daya shiga samun Jahan yayi kwance yana jiranshi ya ƙaraso,

ɗaga kafar da zaiyi kenan yaji gaba ɗaya jikinshi ya shiga jijjiga ta ko’ina,ganin hakan yasa jahan tashi daga zaune yana cewa”lafiya Ayaan meke faruwa ne!!

A wani irin galabaice Ayaan ya zube saman guiwowinshi yana ambaton sunan Allah abakinshi,kafin Jahan yayi wani yunƙurin durowa daga saman gadon tuni ayaan ya yanke jiki ya faɗi kasa abaje idonshi na kallon ceilling yayin da launin idanunshi suka 6ace 6aat sai farar kwayar idon,

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un,” jahan ne ya ambaci hakan a lokacin da ya ƙarasa durowa daga saman gadon ya ƙaraso a hanzarce inda Ayaan yake,

ya zube saman guiwowinsa agabanshi,hankali atashe yake ambaton sunan shi

“Ayyaaan!!!Ayaan dan Allah ka tashi!meke faruwa dakai ne rabin raina!!.,….’

ganin bai da wata mafita yasa ya miƙe da gudun gaske ya fuce daga ɗakin nasu don yaje ya sanar ma wani,

Fitar Jahan ke da wuya,wani siririn hayaƙi baƙi wulik ya dinga fitowa daga ƙofofin hancinshi da kuma bakin shi,da yawan gaske hayaƙin ke kurɗaɗowa ya mamaye ko ina,kafin wani lokaci ya disashe tare da 6ace wa 😳😳😳

Domin Sauke Littafin book 3 Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Back to top button