Ruwan Zuma Page 37 Hausa Novel
(37) “Yanzu kam kin daina zuwa shago ko?�? Ammi ta tambayi Laila wacce ke zaune a gefenta tana mata yankan alayyaho. Laila ta dakata da abunda take yi na wasu sakanni sannan ta murmusa tace, “Ina buk’atar hutu ne shiyasa na barwa Sabrin kula da gurin. Na fara damunki ko Ammi?�? Ta k’arishe maganan cikin zolaya. Ammi ta dara tace, “Ni bance ba, naga yau kwana hud’u kenan a nan kike yini tun safe sai dare zaki koma gidanki. Ai bazan k’i abokin hira ba tunda kin d’auke mini Ali.�? A kunyace Laila ta sunkuyar da kanta tana murmushi amma bata yi magana ba. Ko da Ammi ta lura da hakan sai ta canja musu hiran tana cewa, “Yanzu kam ya kamata in ziyarci mahaifiyarki mu gaisa, yoo in ba don zamani ya kawomu irin wannan lokacin ba ya za’a yi ace bamu ta6a had’uwa ba alhali ‘yayanmu na auren juna? Na fad’awa Ali ya kaini tun aurenku baiyi sati biyu ba amma kullum sai yace mini sai ya shirya. Inaga kawai gobe ki rakani mu je tunda shi bai san yakamata ba.�? “Ammi nace wai da kin bari sai ya dawo d’in kawai. Kinga kar yace munyi abu ba tare da sanin shi ba. Watak’ila akwai abunda yake son aiwatarwa ne kafin nan.�? Fad’in Laila cikin sauri domin bata son k’ara aikata wani abu da zai tunzura Haydar. “Ke d’in ma biye mishi zaki yi? Shikenan sai muyi ta zama haka har sai lokacin da kuka ga dama.�? “Ammi ba haka bane wallahi, Ummii ma tana son zuwa gurin naki to ita ba lafiya ne ya isheta ba shiyasa aka hanata fita unguwa. Amma da zarar ya dawo zan tuna masa in nuna masa ya dace ku gana d’in. Kiyi hak’uri.�? “Babu komai, Allah ya dawo dashi dai lafiya.�? “Ameen.�? Laila ta amsa kana tabi wayar Ammi da ido wacce ke ruri. Ammi ta d’aga wayar ta kara a kunnenta bakinta d’auke da sallama. Laila na ganin yanda fuskar Ammi ta washe ta tabbatar Haydar ne ya kirata domin kullum sai ya kirata, a gabanta zasu gama hiransu ya kashe. Idan Ammi ta masa magana cewa ga Laila a gidanta sai yace zai kirata da dare lokacin da suke waya, alhali bai ta6a kiranta ko sau d’aya ba. Bayan sun gama wayar Ammi ta dubi Laila tana fara’a tace, “Kinji wai gobe zasu dawo ko?�? Laila da taji maganar a bazata sai ta maske tace, “Haka dai yake fad’a mini.�? “Me tsakaninku da Ali ne Hajiya Laila? Dukkanku na lura akwai wani abu da kuke 6oye mini.�? Daburcewa Laila tayi domin bata yi tsammanin Ammi ta gane akwai matsala tsakaninsu ba. Kararen alayyahon data gama yankawa ta fara tattarawa tana turasu cikin leda amma zuciyarta bugawa take yi had’e da jin kunyar Ammi wacce ke kallonta tsam. “Ammi ba wani abun tashin hankali bane, rashin fahimta ce amma Insha Allah zamu gyara.�? Ta fad’a ba tare data bari sun had’a ido ba. Girgiza kai Ammi tayi tace, “Na sani wani lokaci Ali yana da zuciya, don haka ke sai kiyi amfani da naki hak’urin da aka san babba yana dashi. Wallahi bana son ko sau d’aya naji wani abu ya faru tsakaninku, burina ku dauwama cikin farin ciki da walwala. Duk da bansan laifin waye bane kuma bana son ji zan mishi fad’a dole, bana son yawan fushinsa yayi yawa.�? “Ammi ba tarar numfashinki nayi ba amma daa kin bari kar kiyi masa magana, domin zai gani kamar k’ararsa na kawo.�? Fad’in Laila cikin magiya domin bata son koda wasa Ammi ta san dalilin fad’ansu domin bazata ta6a goyon bayanta ba, saboda ita uwarsa ce kuma itama tana da burin ganin jikokinta. Kai duk wand’anda ma ta sani baza su bata gaskiya ba, dalilin ba lallai su gane halin da take ciki ba. “Na bari. Allah ya daidaita tsakaninku amma don Allah ku dinga hak’uri kuna kai zuciya nesa.�? “Ameen Ammi. Kuma Insha Allah zan gyara.�? Suna idar da sallar la’asar Laila ta tattari kayanta tace zata tafi gida, Ammi ta rakota har bakin k’ofa suka yi sallama. Wani irin d’okin ganin Haydar Laila take yi, sai take ganin kamar goben ya mata nisa. Ko data koma gidan kasa aikata komai tayi domin gidanta a gyare yake, girkin da zata tareshi dashi kuma dole zai gobe zata yi. Haka kawai taji tana son burgeshi idan ya dawo don haka ta nemi ganyen zogale ta markad’ashi da wani ajiyayyen nonon rak’umi, tasha tana toshe hanci tana tsayawa. Bata jima da sha ba taji danshi-danshi a jikinta amma ba wanda take muradi ba, cikin sauri ta shiga band’aki ta duba jikinta taga al’adarta ce ta dawo kenan wannan watan ma ta tsallake rijiya da baya ruwan gishiri yayi amfaninsa. Duk da cewa taji dad’in hakan amma ta wani guri bata so hakan ba wanda ya sakata cizon yatsa. Washe gari tun da safe masu aikinta suka gama mata sharan gidan, itama ta shiga side d’insa ta share masa had’e da canja masa bedsheets. Kafin azahar ta gama duk abunda zata yi na tar6an mijinta Ruwan Zumanta sai jiran isowarsa kad’ai take yi. Kwalliya da shigar da tayi har ita kanta sai data yaba. Tana zaune tana jin nishad’i ta tuna rana irin haka da take jiran Aliyu ya dawo gareta amma sai sak’on mutuwarsa aka kawo mata. “Allah kaji k’aina kar ka jarabceni da mutuwar miji again, Allah ka kareshi mini shi a duk inda yake.�? Ta fad’i hakan a bayyane tana d’aga hannunta sama. Tun tana zaune zaman gayu har ta kishingid’a dalilin gajiyar da tayi da zaman jiranshi, ya kamata ace daga Abuja zuwa Kano ya iso ko da kuwa basu taso da wuri ba. Farkawa tayi daga baccin daya d’auketa jin ana buga k’ofar falonta. Yaushe bacci ya d’auketa? Shine bata sani ba. Rigar Haydar dake kan cinyarta ta 6oye bayan throw pillow dake kan kujeran kana ta gyara kallabinta da zaman rigarta ta tashi ta bud’e k’ofar da murmushi a fuskarta sanin cewa Haydar ne tunda ta bar key a jikin falonsa ta ciki yanda bazai iya bud’ewa ta waje ba. Annurin fuskarta ne ya d’auke ganin Mas’ud tsaye a bakin k’ofar wanda daga ganinshi kamar a birkice yake. Apology letter data rubutawa Haydar wanda zata bashi ta jefar a k’asa kana ta rufe bakinta da tafukan hannayenta tana zare idanu wanda nan take suka cika da hawaye. “Kalti lafiyanki?�? Fad’in Mas’ud cikin sauri ya nufota yana kama hannunta d’aya. “Shima ya mutu ko?�? Tayi saurin tambayarsa tana kwace hannunta daga nashi. “Waye ya mutu? Wai lafiyanki kuwa? Me yake faruwa?�? Ya tambayeta cikin d’aga murya domin abun nata ya fara d’aga mishi hankali. “Haydar, Haydar d’ina. Ina yake?�? Sai a lokacin ya gane me take nufi yayi ajiyar zuciya yace, “Kalti babu abunda ya samu Haydar, asalima yana nan lafiya a Abuja. Ki daina kawo irin haka a zuciyarki.�? Minti biyu da haka ta dawo cikin hayyacinta bayan Mas’ud ya fad’a mata cewa yanzu suka gama waya da Haydar wanda shine ma ya aikoshi. “Ban gane ya aikoka ba. Shi d’in ina yake? Yau yace zai dawo fa.�? Ta fad’i hakan tana yarfe hannu domin ta daina gane komai. “Kud’i ya turo mini yace in kawo miki kuma in kaiwa mamanshi domin zai k’ara kwana biyu ko uku kafin ya dawo. Ina bacci ya tasheni wallahi ko abincin rana ban ci ba yau ina hutawa a gida.�? Laila bata k’ar6i kud’in ba illah tashi da tayi ta nufi d’akinta tana jin zafi a ranta, kenan duk shirin da tayi ya tashi a banza? Meyasa ba zai kirata yace ya fasa dawowa ba? Kuma yaushe ta fad’a masa cewa tana buk’atar kud’i? Shi take so take kuma buk’ata ba kud’i ba. “Kalti yaya dai?�? Mas’ud ya tambayeta yana tashi tsaye shima yabi bayanta. A bakin gado ya sameta ta d’auki wayarta tana dannawa can kuma ta kara a kunnenta. Abu aka fara fad’a ta cikin wayar tayi saurin ajiyeshi a gefenta tana dafe kanta. “Kalti Meya sameki kuma wai me yake faruwa ne? Me haka?�? “Kawai zuwan naka ne triggered some memory.�? “Shi ya matsa mini in kawo miki kamar wacce kika ce baki da ko sisi a hannunki. I’m sorry.�? “It’s ok ba laifinka bane. Nima lokaci yayi da zan cire wancan abun a zuciyata.�? “Amma akwai wani matsala bayan nan ko?�? Girgiza kanta tayi tana d’age hannunta daga fuskarta. “Tell me Kalti. Ina gane yanayin ki. Wa kike dashi wanda zaki fad’awa damuwarki sama dani? I’ll always be your best friend, so tell me.�? “Haydar haihuwa yake so ni kuma bana so shine ina taking birth control ya ganni yayi fushi.�? Ta fad’i hakan cikin sauri kuma cikin numfashi d’aya tamkar wacce aka shak’eta ta fad’a. “Kina nufin ba yanzu kike son haihuwan ba kenan?�? “I mean not ever.�? Ta fahimtar dashi. “Wasa kike yi ko?�? Ya tambayeta yana murmushi. Kallonsa tayi fuskarta babu alamun wasa tace, “Babu maganar wasa Mas’ud.�? Murmushin dake fuskarsa ce ta gudu nan take, ya gyara tsayuwarshi yace, “Saboda meyasa kenan? Baki da lafiya ne?�? “Lafiyata kalau, amma Mas’ud ko kaine zaka bani shawarar k’in haihuwan dalilin na girma, gashi na aurar da ‘yata wacce itama kwanan nan zaka ji ance tana da ciki. Sannan ga matsalolin dake gabana da yawa bana son k’arawa kaina wani abun.�? Mas’ud ya hard’e hannayensa kan k’irjinsa ya zuba mata ido ba tare da yace uffan ba. Ganin haka yasa Laila taji ta tsargu ta kawar da kanta gefe tana cewa, “Kayi shiru baka ce komai ba ka tsura mini ido.�? “Ina tuna yaushe kika zama irin haka ne.�? “Irin haka…. kamar yaya kenan?�? “Mutum mai son kansa.�? “Dama nasan ba dole ku goyi bayana ba saboda babu wanda yasan me nake fuskanta kullum idan na fita cikin jama’a. Kowa kanshi ya sani.�? “Maganar jama’a yana kan kowa har da su jama’ar masu yi basu tsira ba, kenan idan kika biye musu numfashi wannan sai kin daina domin wani cewa zaiyi kin fi kowa shak’ar iskan. Ban san ko kina da wata hujja ba amma wanda kika fad’a mini ban d’aukeshi a matsayin hujja ba.�? Bata k’ara cewa komai ba har ya gama tsayuwarsa yace mata zai tafi. “Ka gaishe da Naana.�? “Zata ji. Amma ki zauna ki nitsu kiyi tunanin wannan al’amarin Kalti. Ana aure ne don ibada kuma don a hayayyafa, Haydar da yake matashi kuma wanda bai taso cikin ‘yan uwansa ba zai so ganin ya haihu. Idan kuma kika hanashi haihuwa bana tunanin Allah zai yi farin ciki dake domin ba rashin lafiya mai barazana ga rayuwa ce zata hanaki haihuwa ba illa wani reason d’inki mara ridge. Idan kuma da gaske bakya son haihuwa sai ya k’ara aure ya kawo yarinyar da zata tara masa ‘yaya ke kuma kuci gaba da zama a haka. Amma in hakan bazai yiwu ba to gaskiya kullum zaku rayu ne cikin rashin zaman lafiya da tashin hankali.�? “Yayi duk abunda yake so ni bazan hanashi ba.�? Shine kad’ai abunda ta fad’a cikin zafin rai. Mas’ud yayi mamakin duk zancen daya gama fad’a bata amsa ko d’aya ba sai wanda yace Haydar ya k’ara aure. Murmusawa yayi wanda bai kai zuci ba amma a gaba yana hango draman da za’ayi idan Haydar yayi niyyar k’ara aure. “Halinku duk d’aya; ga can Naana ma tana wata maganar banza wai sai mun shekara kafin ta d’auki ciki wai kafin nan mun k’ara sabawa mun san juna! Can you imagine? Wani irin sabo ne wanda ya wuce mu zama ma’aurata muna sharing shimfid’a d’aya? Na rasa gane me yake damunku da k’in haihuwa alhali mazajenku na so kuma they can take care of the child expenses na rayuwarsa gaba d’aya. Wallahi daa ba don bani da ra’ayin mata biyu ba dana k’ara aure bayan aurenmu da sati d’aya. Banga amfanin k’in haihuwa da wurin ba tunda dama don a hayayyafan akayi auren, ku canja halayenku amma ko nine bazan d’auki wannan zancen ba Kalti. Ke babba ce kin girma kinsan mecece rayuwa, idan har zaki yarda ki bud’e idanunki ki ga gaskiya kema zaki san baki kyauta masa ba, sam baki mishi adalci ba.�? “Idan ka tashi tafiya ka fita da abincin can ka rabawa almajirai.�? Mas’ud yana jin hakan ya fita daga d’akin bayan ya mata sallama don ya lura bata d’auki maganarsa ba sam. Bayan kwana uku, la’asar sakaliya Laila ta dawo daga shago taji kamar muryar Haydar a sashensa, zama tayi akan kujera bayan ta cire hijabinta tana jin zuciyarta na bugu wanda ta rasa dalili. Wani gefe na zuciyarta kuma farin ciki take yi na dawowarshi duk da cewa ya 6ata mata rai bana wasa ba. Yafi sati d’aya da yin tafiya amma ko sau d’aya bai ta6a kiranta yaji yaya take ba, koma me ta mishi ita iyalinshi dolenshi ne ya tabbatar da lafiyanta. Wannan tunanin da tayin ne yasa ta tashi ta shiga falon nashi ta sameshi zaune a kan kujera daga shi sai wandon tracksuit yana waya murmushi shimfid’e a fuskarsa. “Wa ya fad’a miki?�? Yayi yar dariya kana ya maida kanshi ga Laila wacce k’arar bud’en k’ofarta yasa ya gane bashi kad’ai bane a d’akin. “Anya kuwa shi zai fad’a miki haka? Zan kiraki anjima.�? Yana fad’in hakan ya kashe wayarsa ya k’ara duban Laila yace, “Sannunki da dawowa.�? Da waye yake waya? Shine tambaya d’aya dake cikin kwakwalwar Laila wacce ta sakata jin kishi mai zafi da d’aci a cikin zuciyarta. Nitsuwa tayi kana taka zuwa cikin falon ta zauna kan d’aya daga cikin kujeru masu fuskantar Haydar tace, “Sannunka da dawowa. Ina wuni? Ka dawo lafiya?�? Ta gaisheshi ba tare data bari ya gane halin da take ciki ba.“Lafiya kalau Alhamdulillah. Kuna lafiya ko?�? “Bana tunanin kana son sanin hakan.�? Ta bashi amsa tana mai k’ura mishi ido sai taga kamar ya canja dalilin barin gashi da yayi a kanshi. “Meyasa zaki ce haka?�? Ya tambayeta fuskarsa babu yabo babu fallasa amma idanunshi na cikin nata ya kasa d’aukesu gefe. “Haydar kenan, tafiya kayi amma ko sau d’aya baka ta6a kira ka tambayi lafiyata ba, hasalima kashe wayarka kayi yanda bazan sameka ba.�? “Shine hujjarki?�? Ya tambayeta ta gyad’a masa kai. “Wannan ba hujja bace Hajiya Laila.�? Yana fad’in hakan ya tashi ya nufi d’akinsa ya barta a gurin. Ta jima zaune tana jiran dawowarshi domin ta d’auka wani abun zai je yayi, sai dai ganin har minti biyar ya wuce bai dawo ba sai taji babu dad’i, kenan tafiya yayi ya barta baya ma d’okin ganinta da son kasancewa kusa da ita? Me yake nufi sannan wani sabon hali ne wannan? Tashi tayi ta bud’e d’akin nashi ta samu yana kwance yayi rigingine yana kallon ceiling kamar mai tunani. “Kwanciya kayi kenan?�? Ta tambayeshi. “Ehh, na gaji ne.�? Ya bata amsa. “Me zaka ci a dafa maka?�? “Bana jin yunwa na bi restaurant naci abinci kafin na iso gida.�? “Me kake nufi dani ne Haydar? Ban gane wani irin zama muke yi ba.�? Ta fad’i hakan tana yarfe hannunta domin ko a aurenta na baya bata saba rashin kula miji ba. Da zarar sun sami sa6ani tayi fushi to Aliyu koda shine da gaskiya shi da kanshi zai zo suyi sulhu domin shi mutum ne mara son tashin hankali, amma ta lura Haydar ba haka yake ba. “Kamar yaya kenan? Wani abu na miki?�? “Ka sani sarai me nake magana akai Haydar. Ka raba mana makwanci ka daina cin abincina, sannan ka nesanta kanka dani yanda duk inda na zauna sai ka tashi a gurin. Me kake nufi dani? Wani irin zaman aure muke yi haka?�? Shiru yayi yana kallonta kamar wanda bashi da wata damuwa a duniya, bakinta kawai yake bi da kallo wanda ke furta duk wad’annan kalmomin. “Haydar ka daina kallona ka mini magana. Wannan abun da kake yi yarinta ne, idan akwai laifin dana maka sai ka zaunar dani ba wai kayi ta throwing tantrums ba.�? “Zaki koya mini yanda zan yi zaman aure da matata ne Laila? Kuma yau nine nake yarintar?�? Ya tambayeta yana mai tashi zaune. Dubanshi tayi taga alamar maganarta bai mishi dad’i ba, amma dole ta fad’a mishi gaskiya ko da kuwa ranshi zai 6aci. “Maganar gaskiya kenan Haydar, komai d’an a zauna a tattauna ne ba wai ayi fushi a daina kula juna ba. Ka duba maganata da kyau.�? “Kin hak’ura zaki haihu dani ko har yanzu kina kan bakanki?�? “Na fad’a maka dalilaina…�? Bata k’arasa ba ya dakatar da ita ta hanyar d’aga mata hannu. “Kin hak’ura? Yes or No Laila?�? “No.�? “Ina buk’atar lokaci Laila. Baki san ya nake ji ba idan na tuna yanda kike kyamatar had’a zuriya dani. I can’t continue wasting my sperm a inda ake flushing d’insu da gangan don kar su zama ‘yayan halak kamar kowa. Kije kiyi bincike akan rejection zaki gane me nake ji ba tare da kin jefeni da kalmar yarinta ba. Ni ba yaro bane Laila kuma kin fi kowa sanin hakan. Sannan kece mai throwing tantrum kina k’okarin hana ikon ubangiji. Duk ranar da kika shirya d’aukan cikin Haydar kin san inda zaki sameshi.�? Bata tsaya kara sauraranshi ba ta fita daga d’akin cikin d’aurewar kai game da wannan kafiya irin ta Haydar. Bata ta6a tsammanin zai yi haka akan haihuwarta ba da tuni sun yi maganan kafin abun ya kaisu ga haka. Idan haka ya za6a fine, tayi shekara ashirin babu miji babu abunda ya sameta.
Mum Fateey 👌



