Kannywood

Innalillahi: Shahararriyar Jarumar KannyWood Maryam KK. Tayi Yunqurin Barin Addinin Musulunci Bisa Wani Hali Data Tsinci Kanta.

Shahararriyar Jarumar KannyWood Maryam KK. Tayi Yunqurin Barin Addinin Musulunci Bisa Wani Hali Data Tsinci Kanta.
Jarumar Dai Ta Tsinci Kanta Cikin Wami Mawuyacin Hali Tunda Wasu Abubuwa Su Dinga Faruwa Da Ita Cikin Dan Lokaci Qalilan. Hakan Yasa Ta Dau Fushi Ta Fito Tayi Rubutun Data Bayyana Cewa Ita Zata lya Barin Addinin Ma.
Jarumar ta bayyana hakan ne a shafinta na sada zumunta inda ta rubuta cewa:
“Kullum burin wasu musulmai su tozarta yan uwan su musulmai toh ya ishe ni haka na gaji gaskiya sai na hakura da addinin maybe ku kyale
idan aka ce ba musulma bace ni abun naku ya zama rainin wayo maula ko hauka bace wanda kuke so burge ma su gaji sun fita harka ta, amma ku saboda mutuwar zuciya sai matsa mun kuke to nagaji.
Kun saka na fada tsananin rayuwa da kunci na wata biyar 5 na fita da kyar na canza rayuwa ta na chanza komai na yanzu kun hada tsofaffin
video dina da wani abu da azumin nan kuna ta jawo mun tsinuwa bansan meye matsalar ku dani ba, to koh dai na bar muku addinin naku
neh”- inji Maryam kk
Mufida rashid wata mai amfani da kafar sada zumunta kuma S.A ta mai girma gwamna abba Kabir Yusuf akan kafafafen sada zumunta ta yi kiran gaggawa ga mahukunta harka shirya fina finai Abba elmustapha da MD Ali Nuhu domin kawo dauki idan take cewa.
“Budadiyar wasika zuwa ga @abbaelmustapha1 @realalinuhu Jaruma Maryam kk wacce aka fi sani da autar 1313 bayan hidimar data dibgawa kungiyar karshe suka zo suka kore ta.
Jim kadan bayan korar daga 13 13 kuma se wani video ya fito inda jarumar ta rungumi hassan makeup.
Har ya kai ga hukumar tace finafinai ta dakatar da ita Wwanda sukai mata alfarma bata tare da sun fada a media ba ganin maryam kk na daya daga cikin wanda sukai register lokacin da hukumar tace finanai tayi dokar sabunta register suka kirata suka dakatar da ita batare da media tasan halin da ake ciki ba aka bata umarni data fito tayi video tace ta fita daga harkar kannywood.
Bayan tayi haka ta koma yin tallah da yin live session a tiktok dan samun kudi.
Bana goyan bayan wannan post din da maryam tayi tabbas akwai karancin ilimia tare da ita Idan kuka duba yanayi yadda take abubuwan ta Maryam ta shiga harkar film da karancin shekaru kuma babu abinda ta sani sama da harkar Inna kira ga @abbaelmustapha1 da @realalinuhu dasu duba lamarin yarinyar nan sannan suyi mata alfarma irin wacce sukai wa jaruma khadija me numfashi wacce taje Nijar tayi wasa har wani namiji ya kwanta jikinta.
Suyi mata alfarman irin wacce sukai wa jarumar tiktok asmee wakili
Wacce tayi video a tiktok tana rungumar wani dan girnman Allah
Inna kira ga @maryamkk_ hakan yazama izna a gareki ba kowani video ake sakawa a social media ba duk lokacin da zaki postin ki duba ki gani a matsayinki na musulma.
Wani alfanu vide০ ze amnfana miki.
Yours faithfully (@yarkasa_ me abun mamaki Depression is real”.

 

 

Back to top button