Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 6 Hausa Novel

“Uncle, Aunty hamdiyya don Allah ku yi haƙuri, ban zo da niyyar wargaza zaman ku ba, na sani Auntyna ta faɗa miki magana ne saboda irin ƙaunar da take mini amma ni na san gaskiya kika faɗa, don Allah ki koma asibitin ki cigaba da kula da ita da jariran ni zan koma gida zan cigaba da jira har lokacin da ya kamata a ce na ɗauke su ɗin”Cikin wani kalar sanyin murya take maganan, idanunta har lokacin ba su daina zubar da hawaye ba. Uncle ɗin tausayinta ya ji yayinda hamdiyya ta taɓe baki ta ce “Toh ai shikenan, ni ba na yi magana ba ne da wata manufa kawai dai ina kare yaran da yanzu ne muka fara morewa wanzuwar su ba za mu juri dare ɗaya a yi abincin meeting da su ba”Uncle ne ya katse ta”ya isa haka, ki tashi ki koma asibitin. Afeefah tashi mu je in sauƙe ki a babur na”Miƙewa ta yi suka fice daga gidan, har suka iso gidan Auntyn nata magana bai haɗa su ba ta sauƙa ta shige yayinda ya juya ya koma asibitin.Bata bari abin ya cigaba da damunta ba ta kintsa gidan tamkar Auntyn na nan ta ɗora girki marar nauyi ta ci ta zuba saura a kula kan ta ɗan kwanta bacci, har ga Allah ta tsame kanta ne saboda gudun abin da zai je ya dawo sam ba zata so wani ya yi kuka sanadin ta ba bare Auntyn ta don haka tana ganin shawarar da ta yanke shine daidaiSai da Aunty zee ta kara kwana biyu a asibiti saboda postpartum ciwon ciki da ya matsa mata amma duk da haka sai damun uncle usman take akan maganan Afeefar har fushi ta yi ta matsa a sallame ta saboda tunanin ta kar Afeefar ta ji an ware ta ko ta sanyawa kanta damuwa, duk da sun shirya da hamdiyya sai dai har aka yi sallamar hirar arziki bai haɗa su ba don ta matuƙar jin zafin abin da ta yiwa Afeefar.Tana sanya kai cikin gidan ta soma kiran “Afeefah! Afeefah!!”Da gudu Afeefah da ke zaune a parlor tana kallo ta fito ta rungumeta tana murmushin ganinta, Auntyn ta ɗago fuskarta sai ta sauke ajiyar zuciya “Afeefah ni kika yasar a asibiti ko?””A’a Aunty ban isa yasar da ke ba wallahi, na bari ne Aunty hamdiyya ta kula da ku ni kuma sai in kula da gida ba gashi ba gidan ma ya ji daaɗi, da missing ɗin mu da zai yi sai yayi mishi yawa”Dariya Aunty zee ta yi tana girgiza kai, a parlor suka ya da masauki kan a natsa ma maƙota da abokan arziki an fara shigowa barka tuni gidan ya soma ɗinkewa da jama’a nan Afeefah ta shiga jeka ka dawo.Zamanta da hamdiyya na kwanaki shidda ba karamin wahala ta sha ba ta kuma danne zuciyarta, ko Aunty bata bari ta san hamdiyyar tana matukar musguna mata ba ta yadda ko satan kallon yaran ta yi sai ta yaɓa mata baƙar magana, har tsoron kallonsu take Dukda tana jin son su tamkar jini da tsokarta ta sha ɓuya tayi kuka sossai na mummunar shaidar da take dashi don bata tsira ba ranar suna har nuna ta hamdiyya ta saka ake yi saboda kananun maganganu duk Aunty bata sani ba. Auntyn Ta yi matuƙar kyau cikin milk leshin ta yayinda yaran suke sanye cikin kyawawan tufafinsu pink da blue, Afeefah ma cikin leshin da Auntyn ta yi mata musamman na suna maroon ta shirya ta yi mugun kyau Aunty zee har ajiye ta tayi ta zana mata liner a baki ta saka ta saka kwalli ta shafa mata powder sai tayi kaman ka sace ta ka gudu, masu hidima da kitchen ita suke kira tana miƙawa mutane abinci daidai ta zo miƙawa wasu mata kenan da yake ta bayansu ta zo ta ji ɗayar tana cewa “Ni kam dai ina tausayawa Zainabu saboda fa da gaske yarinyar da take riƙo rikakkiyar Mayya ce kuma fa an ce Mayu sun fi zaluntar wanda ya ji tausayin su”Ɗayar ta ce “Ni fa ban san yarinyar ba amma kuma ina da labarin tun tana ciki take cin maita, uban ta ma bai tsira ba haka uwar da ta haife ta, aiko Allah raba mu da irin wannan iri. Haihuwa bata yi rana ba”Wani irin abu mai nauyi ne ya taso ya tsayawa Afeefah a kirji tana ji na ukunsu na furta “za ki gane ta mana wata baƙa marar kiba ta saka leshi maroon, ai daga kallon idanunta da suke manya kaman kwai kin san za’a ga kurwa da kyau… Allah dai ya hana farin ciki komawa baƙin ciki”Gabansu ta zagayo suka ɗan sha jinin jikinsu ganin fuskarta babu ɗigon walwala idanunta da suka surke zuwa ja ta ɗan zuba musu kan ta ajiye abincin ta juya ta bar wurin.A karshe dai ba’a tashi suna lafiya ba don wata wai aljannunta sun tashi ai sai ta kashe Afeefah Mayya ce! nan fa gidan suna ya kachame dayawa suka shiga kururuwa su ma, da ƙyar aka fita da ita a gidan zuwa maƙota ban da kuka babu abin da take, bata san wani irin tunani zata yi ba duk ta ji kaman ta sallamarwa duniya farin ciki da rayuwarta sai ta tuna Aunty zee da ta yarda da ita take kuma bata kariya don yanzu ma ita ce ta nuna jan ido ta sallami kowa da abin da za’a yi sai ya fi haka, chan kuryar maƙociyarsu ta takure tana kuka sossai bata ji Shigowar Aunty zee ba amma ta ji hannu ya taɓa ta firgita ta yi ta miƙe tsaye tana girgiza kai”Wallahi ni ba Mayya ba ce! Ban san ya ake yi ba don Allah ku yi haƙuri ban taɓa cin naman mutum ba wallahi..!”A rikice take maimaitawa da sauri Aunty zee ta rungumeta tana hawayen tausayinta “Ya isa Afeefah! Ni ce! Auntynki ce, na sani wallahi na sani ke ba Mayya ba ce na yarda da ke”Kuka kawai ta saki mai tsuma zuciya tana yin luff a jikin Aunty zee ɗin.Jiki a sanyaye duk suka dawo gidan, yayinda abin da ya faru a sunan ya tsayawa Afeefar ta yadda ko kuzarin taɓa yaran bata da shi, tsoro take ji kar ta taɓa su abu ya faru haka Aunty zee ta sa uncle usman a gaba tana kuka sossai “Duk laifin matar ka ne usman da bata fara ba da hakan bai faru ba, yaran nan fa kannen Afeefah ne amma ka ga yadda take baya baya da su ko taɓa su sai na yi da gaske take yi! Haba mana ko bata duba komai ba ta duba maraicinta mana wallahi ta ɗauki alhakinta dayawa kuma ni kam ta daina burgeni sam”Shiru yayi chan ya ce “Ki yi haƙuri zan yi mata magana, amma ki dinga dubawa itama hamdiyyar ba don tsanar Afeefah bane ya sa take hakan saboda kare yaran nan ne ganin tsawon lokacin da muka ɗauka kafin Allah ya ba mu””Wallahi na fi ƙaunarta a kan su, ta cigaba da rayuwa da wannan tsangwamar rayuwarta na cikin haɗari don Allah zan roƙe ka Alfarma don girman Allah kar ka chanza mata kaman yadda ka fara mata, ka dubi maraicinta ka riƙe ta kamar yadda za ka riƙe suhail da suhaila”.Hannayenta duk biyu ya riƙe “Ban tsani Afeefah ba Zainabu, in shaa Allahu kuma zan cigaba da iya ƙoƙarina a kanta””na gode sossai Baban ‘yan biyu”Ya saki murmushi ita ma ta mayar masa.Duk su biyun sun mayar da hankali kanta ta yadda hatta shi uncle ɗin kan ja Afeefar jiki ko ma ya bata babies ɗin da take matukar so ta riƙe, yau satinsu na biyu kenan a duniya.Tsaki Aunty zee ta ɗan ja kaɗan karo na ba adadi hakan ya saka Afeefah dake jijjiga suhaila yayinda Auntyn ke ba Suhail Mama ta kalleta ganin tana ta yamutsa fuska ya saka Afeefar katse shirun nasu “Aunty lafiya kuwa?”Ta sake jan wani tsakin karo na barkatai kan ta furta “Wlh Afeefah ciwon ciki ne ke ɗan matsa min tun haihuwar nan kullum sai na yi shi kaman ƙa’ida””Sannu Allah ya ba ki lafiya, babu maganin da suka ba ki a asibiti?””Akwai fa ina sha amma kaman bana sha””Sannu”Haka tayi ta jera mata duk ta saka kanta a damuwa domin sam bata so taji wani na ciwo a gidan sai gabanta yayi ta faɗuwa fargaba ya bi ya rufeta har sai an furta mata yayi sauƙi.Shigowar Uncle da karbar babyn da yayi daga hannunta ya sa ta yi musu sai da safe ta shige ta bar su nan parlor. Chan cikin dare sai ta ji kaman ana motsi da ƙarfi, sai kuma ta ji bugun kofar ɗakinta a razane ta farka tana salati jin Muryar uncle ya sa ta dirko da hanzari ta zo ta buɗe kofar “Afeefah ki zauna da yaran nan idan sun yi kuka ki ba su madara zan kai Auntynki asibiti ciwon ciki ya tasar mata sossai”Tuni ta rikice hawaye har sun fara zarya a idanunta.”Toh uncle”Ta faɗa tana bin bayanshi, shi ya riƙo Aunty zee da ke tafiya da kyar Afeefah na ta bin su tana share hawaye har zuwa kan babur ya hau ta kwanta jikinshi suka fice tana ta jera mata sannu da Allah ya bata lafiya. sai da taje ta rufe kofa kan ta dawo kan yaran ta zabga tagumi cike da damuwar ciwon Auntyn.Yaran sam ba su da rikici daman, tun tana tagumi har bacci ya sure ta a kansu ƙiran Sallar farko da kukan suhaila su ne suka farkar da ita, ta tashi ta haɗa musu NAN1 ɗin su da ake basu saboda abinci ya ishe su, ba zallar nono Auntyn ke ba su ba, sai da ta saisaita ya zama da dumi cikin tsafta ta fara ba su don suhailar na koshi sai suhail ma ya tashi bayan ta gama ta fice taje tayi alwala ta zo ta fara sallah sai da ta idar tayi Adu’a ciki har da roƙon Allah ya ba Auntynta lafiya kan ta miƙe ta bar sallayar zuwa tsakar gida.ƙoƙarin ɗora musu breakfast ta fara a natse take aikin Dukda hankalinta rabi na ga su Uncle da suke asibiti rabi na ga ‘yan biyu kar su farka bata ji kukansu ba har ta gama haɗa abinda zata buƙata ta ɗora kan ta shiga sharar tsakar gidan.Ta gama haɗawa tana ƙoƙarin kwashewa kenan ta ji ana bubbuga kofa ba irin bugun hankali ba, jikin kofar ta isa sai ta ji kaman surutai dai ba na mutum ɗaya ba, bata buɗe ba ta shiga tambayar waye ne?”Ki buɗe mana ai za ki gani!”Muryar hamdiyya da ta ji ya sa ta buɗe kofar sai dai me za ta gani…!

Back to top button