Karfe A Wuta Chapter 110 By Ayshercool
110Kunaneman group din dazakuringa sarin kayan kitchen afarashin sari yanda duyanda zaku karade kasuwa bazakusamu kasa d farashinmuba!!! Kuyi joining a mai nono kitchen utensils and household domin siyan dai dai ko sari dukkanin kayanmu available ne kuma farashi daidai aljihunku siyan nagari….maida kudi gida…gaskiya d amana sune takenmu!!!Ɓoye hodar ya yi, gabansa na tsananta faɗuwa ya nufi ƙofar ɗakin, yana tambayar waye?. Shiru ba a bashi amsa ba, aka ci gaba da bubbuga ƙofar.Ya buɗe ƙofar, yana buɗewa aka hankaɗo ƙofar, jami’an tsaro suka shigo cikin ɗakin, aka hau caje ɗakin.Ba ma wadda ya buɗe suka gano ba, wata jaka suka ɗaukko, ana zazzageta sai ga miyagun ƙwayoyi da hodar iblis a ciki.Rantse rantse indabo ya fara, cikin matsanancin tashin hankali, ya rasa ma me zai ce, suka saka masa ankwa, suka ingiza ƙeyarsa suka tafi da shi.****Nabila na ta rawar ƙafar shirin bikin Sumayya, sai dai jikinta gaba ɗaya babu daɗi, wani irin nauyi jikinta yake yi mata ga kasala.Shahara da ɗaukakar da ta yi, ya sanya take samun manya manyan case, amma yanayin ɗawainiyar aure, ya sanya ta fara sarewa, gaba ɗaya jin ta take ba a dai-dai ba.Suka shirya ita da Viper ta kai shi gidan ramma, ta ji daɗi sosai da sosai da zuwansu, dan ranar Abdul ma bai fita ba, da ta gaya masa za su zo.Abincin da ramma ta yi, Nabila ta ce ba ta ci, wai ta dafa mata indomie ta cika attaruhu ta bata.Ramma ta yi murmushi, ta ce mata to, ta dafa ta bata, ta ji daɗin indomien sosai da sosai, dan a gida ba ta iya cin abinci.A hanyar komawa gida, ta saka Viper ya saya mata ƙosai, suka je gida ta dirarwa ƙosan nan, ta din ga ci da yaji tana suɗar baki.Ya dawo daga sallar isha’i, ya tarar ta kashingiɗa, tana ta lasar lemon tsami.”Abla, idan ki ka ce mini cikin ki yana ciwo, ko kuma ulcer, ko saurararki ba zan yi ba, kalli yadda ki ke azabtar da kanki da yaji, ina kallonki har da barbaɗa yaji a kam man ƙosai kina lasa, yanzu kuma kina shan lemon tsami ko?””Vi dan Allah kar ka yi mini baki mana””Ni dai na gaya miki ne”Aikuwa hakan ce ta faru, kwana ta yi tana yawon banɗaki, atini ya sakota a gaba, ga amai. Yana kallonta ya yi mata banza ya sha baccinsa da daddare.Da safe ma da kyar ta yi masa breakfast, almajirinta ta aika chemist ya sayo mata ruwan gishiri da suga ta haɗa tana sha. Gaɓoɓinta duk suka sage, wunin ranar ta kasa cin komai, indomien da ramma ta ba ta ce kawai take dawo mata.Cikin dare yana jin motsinta, tana ta sintirin toilet, har ya basar sai ta bashi tausayi, yadda gari yayi tsit sai kakarin amanta kamar zata amayar da kayan cikinta.Ya je ya sameta a zaune dirshen a banɗaki, duk ta fita hayyacinta. Dolensa ya fita ya bugawa maƙwabcinsa ƙofa yana da abin hawa suka tafi da Nabila Asibiti.Kwantar da ita aka yi, fatarta duk ta bushe ta zama dehydrated, leɓenta ma ya bushe sosai.Abinka da farin mutum, sai tayi busu-busu kamar korarriya.Ga tausayinta ga dariya ta bashi, iya sintirin banɗakin da ta sha ma, ya isheta punishment.”Abla ko a sayo ƙosan ne?” Murguɗa masa baki ta yi, ta lumshe idanunta, saboda har a lokacin cikinta hautsunawa yake yi.Da safe Abdul ya shigo, yana ward round kawai ya ga su Viper.Ya ce “Ya aka yi ba a kirawo ni ba? Daga tafiyarku shekranjiya har jikinta yayi haka?”Viper ya ce “Eh, likitan da muka tarar yayi mata duk abin da ya kamata ai, ba ta ji ne, ka ga gobe ba ta kuma ba, ba zata ci abinci ba, sai ta zabga yaji, abincinma sai ta gama zaɓe-zaɓe, ko ba komai ai ta hanamu bacci, in da na ji daɗi ta ji a jikinta ai, nan ɗin ne yafi mana kusa shiyasa kawai muka yo nan”Abdul ya yi murmushi ya ce “Gaskiya yakamata a tausaya mata, wataƙila baby ne ya saka take hakan, bari na yi reviewing ɗin ta” ita dai ba ta san me ake yi ba, bacci ya sake ɗaukar ta.Gwajin farko ya tabattar da Nabila na ɗauke da juna biyu, dama Viper jikinsa ya bashi, sai dai bai tabattar ba ya bar abin a zuciyarsa.Abdul ya ce “Ka ga babynka ne ya sakata cin yaji, ka ke mata dariya”.Cikin farinciki Viper ya ce “Har da rigimarta, da kafirin kwaɗayinta”Ya rasa in da zai saka kansa dan murna, shi yana ta farinciki, Nabila na fama da kanta, atini ya tsaya amma jiki babu ƙwari.Sai yamma aka sallame su, Abdul ya ɗauke su a mota zai kai su gida.Duk in da aka tsaya sai ta ce Viper ya saya mata abu, duk sai dai ya kashe kuɗin jikinsa.Tun da suka koma gida kuma, Nabila ta kwanta laulayi sosai da sosai, ba ta cin komai, amai ya sakata a gaba, ga zazzaɓin dare. Jauhar ta yi laulayi ita ma, amma Nabila ta fita laulayi nesa ba kusa ba, ko fita ta daina yi, sai lokaci lokaci.Viper ne yake ta kula da ita, yana roƙon Allah ya kare masa ita da abin da yake cikinta su rabu lafiya.Ya sanya yana da rabon ganin ɗan sa a duniya.Sosai Viper yake ba ta mamaki, mutum ne mai tausayi, sai lallaɓata yake yi.Ranar wata juma’a, aka ɗaura auren Abbu da maman ramma, hakan ya yi wa Viper daɗi sosai da sosai, su Major, Baba duk sun halarta, a wurin ɗaurin auren Major ya haɗu da mahaifin liti.Classmates ɗin sa ne, tare suka yi karatu, tun lokacin secondary school, sun yi zaman mutunci, ɗakinsu ɗaya kuma kwanarsu ɗaya, tare suke komai.Rashin wayar hannu a wancan lokacin ya sanya zumuncin na su bai ɗore ba, nan hira ta wanzu tsakaninsu, hirar yaushe rabo, da hirar ƙalubale da kuma nasarorin da suka samu a rayuwa.Rahila tana ji tana gani, aka ajiyeta a gidan masu rangwamen hankali, Abbu kuma ya yi aurensa.’yan kwanakin nan, kusan kullum idan Zakiyya ta kwanta bacci, sai ta yi mafarki da Chubaɗo, hannunta rungume da jarirai guda biyu, ɗanyen haihuwa, ƙafafuwanta duk jini, tana kallonta tana kuka.Tun da ta rasu, ba ta taɓa mafarki da ita ba sai a wannan lokacin, da fari ta maze ta basar da mafarkin, amma kuma ta ci gaba da yin sa a kai a kai, har ya zamana tana yi mata gizo a zahiri.Abu kamar wasa, ba iya ita take gani ba, wasu lokutan har da jauhar, idan ta hange su, su na zaune su na cin abinci, da sun hangota sai su nufota.Kafin wani lokaci, ta yi wata irin rama, abin duniya ya isheta, ta kasa gaya wa kowa halin da take ciki, ba ta iya cin abinci, ga wata irin fargaba da faɗuwar gaba, sai ta din ga ganin kamar ita ma mutuwa za ta yi a kowane lokaci.Gaba ɗaya ta ji duniya tayi mata zafi, ba ta son komai, ba ta jin daɗin komai, ta tsangwami kanta kuma ta kasa gaya wa kowa halin da ake ciki, gashi tana murna yanzu miji ya zama nata, tun da mama na kwance tana jinya, amma ita ma ta kasa jin daɗin rayuwar gaba ɗaya.Kafin Viper ya auri Nabila, kallon mace mai son jiki yake yi mata, kai ba ka ce ta iya wani abu ba, saboda yadda take a sangarce, amma sai ya ga abin da ba haka ba, sam ba ta son ƙazanta, idan ya rage mata aikin gida ya fita, idan ya dawo a hakan zai tarar ta lallaɓa jikinta, ta gyara ko ina, har ma ta yi girki.Kayansa za ta saka a inji ta wanke ta shanya, su bushe ta bayar a goge masa.Sosai yake jin tausayinta, gashi lokacin komawarsa bakin aiki yayi.Cikin kulawa ya ce “Abla ko dai tare zamu tafi ne, ko na tafi hankalina ba zai kwanta ba saboda yanayin jikin nan naki””Komawa zaka yi, babu wani abu da zai faru in sha Allah””Yanzu ko a gidanku, babu wani wanda za a baki, ya zo ya tayaki zama?”Tayi murmushi ta ce “Maraicin kenan Vi, ba sai na gayyaci kowa ba, na san ba bani za su yi ba, Sumayya ce dai ta ce mini za ta zo idan ka tafi, kar ka damu zan iya zamana”Cikin kulawa ta ce “Abla ba kya cin abinci ai, duk kin yi wani iri” yayi maganar yana shafa wuyanta. Langaɓe masa ta sake yi, daurewa kawai take yi ne, dan kar ya ƙara shiga damuwa, dan kuwa har kuka take ɓuya tayi, ganin yadda ba ta iya cin abinci, kullum cikin amai take.Shi kansa Viper sai da ya tambayi Abdul, ko akwai maganin da za a bata ta daina aman nan, ya ce masa sai dai ayi haƙuri, lokaci ne zata daina.Lokaci lokaci, ramma sai ta yi girki, ta ba wa Abdul ya biya ya kai wa Nabila. Har Viper ya tafi, hankalinsa yana kan Nabila da ya bari, Sumayya ta kan zo ta ɗan tayata zama ta kwanar mata biyu, ita kanta tana jin tausayin Nabila dan wani irin wahalallen laulayi take yi.Sai dai duk da halin da take ciki, kasancewar ‘yar dagiya ce, bai hanata kasawa tare da tsarewa ba, a duk lokacin da za a gabatar da shari’ar Naja’atu Bunkure ba.Dan ranar farko da Bunkure ta ga Nabila, sai da haɗuwarsu ta farko ta dawo mata, bayan gama saurara Shari’a sai da Nabilan ta bita, ta ce “Allon kwaikwayona, ina fatan a yanzu kin tabattar da Allah ne mai yi, babu ruwansa lokacin da ya so, zai iya ɗaukko na can ƙasan da ba a iya hango shi, ya ɗaukaka shi sai kowa ya ji shi, hakazalika ya ɗaukko na can saman ya kai shi ƙasa, sai kowa ya manta da shi.Ba zan ci gaba da bibiyar shari’arki dan fatan na ga bayanki ba, sam, na gama nawa tun da na kai ki ƙasa, na bayyana wa duniya wacece ke, zan bibiya ne saboda hakkin mutane da kuma jinin ‘yar uwata da ki ka ce ya tafi a banza” Bunkure ba ta iya mayar da martani ba, aka zunkuɗata cikin motar masu laifi, aka tafi da ita.*****Duk ƙumbiya-ƙumbiyar da ake yi, da ƙoƙarin rufe abin da ya faru, sai da abun ɓoye ya bayyana na kama Indabo da miyagun ƙwayoyi a ƙasa mai tsarki.Ramma tana zaune a falo, tana assignment, Abdul ya shigo babu ko sallama, ya wuce ɗaki.Ta bi bayansa tana faɗin “Yau kuma waye ya taɓo mini bokan turai” idanunsa ne suka tabbatar mata akwai damuwa gagaruma.”Doctor meyafaru kuma? Wani abin ne ya faru?”Ya haɗiye wani abu mai ɗaci, ya dubeta ya ce “Daddy aka kama a Saudiyya”Ramma ta ce “Subhanallah, me ya yi aka kama shi?””Da miyagun ƙwayoyi aka kama shi, abin takaici wai a ƙasa mai tsarki”Ramma ta ce “Subhanallah, abin bai yi daɗi ba. Addu’a ce yanzu ya kamata ayi, Ubangiji Allah ya fitar da shi”Ya kalli ramma idonsa fal hawaye ya ce “Allah ya fitar da shi how? Saudiyya ba fa Nigeria ba ce ba, duk laifukan da yake aikatawa ba su isa ba, sai ya tsallaka ƙasa mai tsarki?. Har tsoro nake ji, ko idan ya koma ga Allah idan na roƙa masa rahama Allah zai karɓa? Tarin mutanen da zalunta saboda kujerar nam, a ina zai gansu ya nemi afuwarsu? Ni iyayena ne jarrabawata, da ina da iko, da ban zo a tsatsonsa ba”Cikin kulawa ramma ta fara rarrashin da bai kai zuciyarta ba ta ce “Doctor, ba a yanke tsammani da rahamar Allah, kuma shi mai rahama ne, dole a roƙa masa rahama tun da musulmi ne””Amma kin san Allah baya yafe hakkin wani a kan wani ko? Yau ko tuba yayi ya daina laifukan da yake yi, waɗanda ya zalunta fa wasu ba sa duniyar nan, sun bar ta, a wurin wa zai nemi yafiyar? Mutanen da ya dasawa damuwa da baƙin ciki su na da yawa fa.Allah mai rahama ne da jin ƙai, amma sai da ya haramta shi a kan kansa, sannan ya sanya shi abin haramtawa a tsakaninmu, ke ki ka biya mini wannan hadisin, ni babu wani abu da za a gaya mini yanzu na ji sanyi, ina tausaya masa haɗuwarsa da Allah”Jiki a sanyaye ramma ta ce “Ka yi gaskiya, amma yanzu ai ba mutuwar yayi ba”Ya kalleta fuskarsa duk hawaye ya ce “Kin san hukuncin ace an kama mutum da irin abin da aka kama shi da shi a ƙasa mai tsarki? Muddin suka tabattar hukuncin kisa ne” gaba ɗaya sai ta rasa me ma za ta ce. Har ga Allah Abdul ya bata tausayi, amma ita ba ta ji ta damu ba ko kaɗan, albarkacin Abdul ɗin ne ma bai sanya ta ce Allah ya ƙara a zuciyarta ba.****Hafsa ta biyo Alhaji mu’azzam, domin kawo ziyara gida, sai dai ta tsorata da yadda ta ga jikin mama ya ƙara tsananta, ta zama wata irin miskiniya abin tsoro.Sai dai ta tsorata da ganin ita ma tata mahaifiyar ta yi wata irin muguwar rama, gashi duk kauɗinta yanzu ba ta son yin magana.Ga zaman ɗaki, cikin mamaki take tambayarta ko lafiya?Ta fashe da kuka take gaya wa Hafsa abin da yake faruwa.Tayi shiru sannan ta ce “Ikon Allah, kin ga kaɗan daga illar biye-biye anty, yanzu an ce Anty Rahila tana gidan masu rangwamen hankali, ni na fara yin ciwon hauka a sanadin shaye-shaye, ke ma kuma ga alamu”Ta waro ido ta ce “Hauka kuma?””Eh matsalar ƙwaƙwalwa, wannan alamomi ne na depression””Wallahi na yarda da maganarki, wasu lokutan ji nake kamar na fita da gudu ina ihu, duniyar tayi mini zafi, amma ni sai nake tunanin ko matar nan ce duk da tana kwance, ta haɗa kai da yaranta suke banko mini asiri”Hafsa ta katseta ta ce “Mama babu wanda yake banko miki wani asiri, ganin Jauhar da mahaifiyarta da ki ke yawan yi, yana alamta miki, kin tafka mummunan laifi a rayuwarki, da babu lallai sun yafe miki, gashi ba sa duniyar. Shawara ɗaya zan baki, ki din ga yi musu addu’a, sannan ki dage da istigfari kuma ki daure, ki nemi afuwar Baba, sannan ki nemi afuwar ɗan uwanta babansu Nabila, da ita kanta Nabilan, tun da duk su na da alaƙa da su, idan ki na so ki samu nutsuwa. Sai kuma mu dangana da asibiti ki fara ganin likita””Tabɗijan, kawai kuma sai na je ina cewa wani su yafe mini, da na yi musu me? Wallahi ba zani ba”Cikin takaici da mamaki, take bin Antyn da kallo, ta ce “Ba zaki ba Anty, sai abin da ya samu babar su Shahida ya same ki tukuna?””Ya daɗe bai same nin ba, ba zani ba, ni na san asiri kawai ake yi mini, kuma ni dai-dai nake da kowane mara mutunci” Duk yadda hafsa ta so ganar da ita, ta rufe idonta taƙi ganewa.”To mu je asibiti, tun da nima kin ga da haka na warke, da aka din ga kai ni Asibiti””Ba zani ba shi ma, ni na san maganin matsalata” haka Hafsa ta ƙyaleta, dan babu yadda ta iya da ita”.Washegarin zuwanta ta tafi gidan Nabila, tayi sa’a Sumayya ma tana can, haɗuwar ta su ta yi musu daɗi, sai dai a kallon farko ta ga Nabila ta rame sosai, ba ta yi magana ba, Nabila nata nuƙu-nuƙu da hijjabi, amma sai da Hafsa ta gano ta.”Abla, wai me ki ke ɓoyewa ne? Duk ɓoyonki ana gani ai”Kunya ta kama Nabila ta ce “Ake gane me?””Ɗan baban mana”Sumayya ta kwashe da dariya ta ce “Ai na gaya mata ana gani, taƙi yadda, mai cewa sai ta yi good 2yrs a gidan miji, kafin ta ɗau ciki, amma farawa da bisimillah”Hafsa ta kwashe da dariya ta ce “Ai kura ta san gidan mai babban sanda, ai ita ta san in da za ta iya cewa, sai ta shekara biyun ba ta haihu ba, ba dai a gidan Viper ba”Nabila ta ce “Baku da aikin yi ne, ulcer ce ta kumbura mini ciki””Viper dai yayi ajiya, shi ya kumbura miki cikin” Hafsa tayi maganar tana dariya.”Ku da Allah, kuna munafuncin mijina a gabana, wanda idan yana nan, ko tarin kirki ba zaku iya ba, a ƙyale mini shi kar a saka ya ƙware, yana can yana aiki, kuna nan ku na gulmarsa”Hafsa ta ce “Ke abin alkhairi ne ai, Ubangiji Allah ya inganta miki ƙanwata, ya rabaku lafiya””Amin Anty hafsyna”Sumayya ta ce “Shahida ma na ga kamar an gamu”Hafsa ta ce “Nima ma gani, ai na je gidanta”Nabila tayi dariya ta ce “Mijinta ce mini yayi baya son saka ido mura take yi” suka yi ta hirarsu gwanin sha’awa, hafsa ta ce “Dan Allah ku tayani da addu’a, nima Ubangiji Allah ya sa ina da rabon ganin jinina a duniya, ni haryanzu shiru” suka yi ta kwantar mata da hankali da yi mata fatan alkhairi.Aka koma maganar bikin Sumayya, Hafsa na ta ƙara nanata mata, kar ta kuskura ta je ta sha wani abu da ba ta san menene ba, alhalin ga likitar mata.Nabila ta ce “In dai ki na son daga shiga kema ki ɗaukko magana, ki riƙe wa kayan likitar mata wuta, zaki gane baki da wayo, laulayi is not your mate “Hafsa ta ce “Rabu da ita, ta ji da assignment ɗin da Viper ya bata”Nabila na daga kwance a kan cinyar Sumayya ta ce “Wuta balbal idan aka ƙira sunan mijina””An faɗa Aminu Viper, mai zamani””Ku da Allah” Nabila ta dage ta din ga lallaɓa hafsa, sai da ta kira Alhaji mu’azzam, suka kwana a gidan.Ita dai kaf ‘ya’yan babansu, da aka nuna mata, babu wanda take jin tana so, kamar hafsa, ita dai tana ƙaunarta sosai.Sai kuma suka koma hirar ƙalubalen rayuwar gidan auren, tare da ba wa junansu shawarwarin da za su fishshe su.Kwana biyun da suka yi mata ta ji daɗi sosai, bayan tafiyarsu zaman kaɗaicin ya ci gaba da damunta.Babu tsammani taga Viper ya dawo, aikuwa ta ji daɗin hakan.”Vi ya na ganka ka dawo yau?””Shi ne lokacin da aka ce ki fara zuwa awo, ina lissafe ni ai”Tun daga Abuja ya taho mata da amala, saboda ya san tana sonta, aikuwa ta ji daɗin amalar nan.Ta ci kaɗan ta ga tayi awa biyu ba ta yi amanta ba, aikuwa ta rufar mata, ta cinye tas.Kwana tayi amai, ba ta yi baccin kirki ba.Da safe ya buga wa Abdul waya, ya ce masa zai kawo Nabila asibiti, ya ce masa to.Abdul ya yi mamki, ganin cikin Nabila wata huɗu, amma ya ɗago sosai.Suka gaggaisa, ya yi mata sannu.Viper ya ce “Ya ƙanwata?””Tana gida sun yi hutu, ga saƙo ma ta bani, wai na kawowa yayarta” yayi maganar yana nuna musu fulas ɗin abinci.”Ko menene a ciki, in dai yaji yayi yawa ba zaki ci ba, bar rawar jiki” yayi maganar yana harar Nabila.Tashi Nabila ta yi, ta buɗe flask ɗin, ƙamshin miyar jajjage ya daki hancint, tayi maza ta rufe dan da alama miyar mai yaji ce.Abdul ya ce “Ina ce mata zaku zo, ta zaunar da ni sai na taho miki da abinci”Viper ya ce “Duk in da muka je, har rawar jiki take ace mata ga abinci, kamar ba na ba ta abinci a gida””Bana ƙoshi ne” tayi maganar tana dariya.Abdul ya ce “Maybe na gidanta ba ta iya ci, idan suna irin wannan halin sai haƙuri ai”Viper ya ce “Haka ne, amma ya na ganka wani iri, ko baka da lafiya ne?”Bai ɓoyewa Viper ba, ya gaya masa komai, Viper ya ce “Irin haka sai haƙuri, kuma ka ci gaba da addu’a, kuma kai ka kiyaye aikata makamantan laifukan da ya aikata”Kalaman Viper dai babu tausayawa ga Indabo, amma rarrashi ne ga Abdul.Ɗakin scanic suka tafi, bayan an yi wa Nabila gwaje-gwajen masu ciki.Viper yana tsaye a kan Nabila, yana riƙe da hannunta.Abdul yake gaya wa Viper, doctor Muktar ya tafi ƙaro karatu malesia.Abdul yana cikin maganar ya yi murmushi, ya kalli Viper ya ce “Congratulations bani goron Albishir””Albishir ɗin me? Bayan dama can na san da akwai cikin?”Abdul ya ce “Ba zan faɗa ba ne, sai ka bani tukuici”Viper ya ce “Faɗi sai a baka””Naƙi wayon, kawo kawai”Viper ya yi murmushi ya zaro dubu ɗaya ya ajiye masa ya ce “Faɗi idan yayi mini sai na ƙara maka”Abdul ya ce “Ai kai ne mayar da tukuicin, ai albishir ɗin namu ne gaba ɗaya. Twins ce dama ita ai ko?” Viper ya jinjina masa kai.”So congratulations, babynta biyu ne a cikinta, twins ne yaran”Waro ido Viper ya yi yana kallon screen ɗin injin scanic ɗin, tamkar zai gane menene a jiki.Jikinsa ya hau wata irin tsuma ya ce “Dan Allah da gaske ka ke ko da wasa?””Yaya zan yi maka wasa da abu mai muhimmanci har haka? Wallahi da gaske nake, twins ne, kuma duk su na cikin ƙoshin lafiya”Viper ya miƙe ya yi sujudar godiya ga Allah, ya miƙe ya rasa me ma zai yi ko ya ce.Ya kwance agogon hannunsa, ya ajiyewa Abdul, ya zaro ɗaya daga zobensa na azurfa shi ma ya ajiye masa.Ya fara laluba aljihunsa, Abdul ya ce “Haba Viper, yanzu mun zama ɗaya sirikina ne fa kai, ina tayaka murna, Allah ya inganta ya raba lafiya, amma ku yi shiru kar wanda aka gaya wa biyu ne. Ga agogonka da zobenka ba zan karɓa ba”Viper ya yi ajiyar zuciya ya ce “Kar mu yi haka da kai, yarana biyu na rasa, ɗaya aka yi ɓarinsa, ɗaya kuma bai ma zo duniyar ba, yanzu Allah ya haɗa mini biyu. Na ma rasa wane irin farinciki zan yi ne, ba kai ka bani ba, saƙon kawai ka gaya mini, amma ba ka ji zuciyata ba, Alhamdilillah ala kulli halin.Na rasa jauhar, ga Nabila, na rasa yarana ya bani biyu Allah Alhamdilillah. Yayi maganar yana goge ƙwalla.Jikin Abdul ya yi sanyi, da ya tuna babansa ne silar ajalin matar Viper.Ya tuna lokacin da yake yi wa Viper kallon ɗan jagaliya, ɗan maula ƙasƙantaccen mutum da yake zuwa maula wurin mahaifinsa, yau gashi Allah ya canza komai, ya nutsu ya zama mai bayar da gudummawa ga al’umma.Ya ƙarasa ya ɗago Nabila, yana mata sannu.”Abincina” tayi maganar kamar ƙaramar yarinya tana kallonsa.”Ai dole ma a ɗaukko abincin nan Abla””Kuma ka gaya musu su daina damuna, ko in ƙi haifarsu”Cikin murmushinsa da yake ƙara masa kyau ya ce “Za su daina in sha Allah”Abdul ya ci gaba da yi musu fatan alkhairi, da taya su murna.Tun da suka koma gida, duk in da Nabila ta yi sai ya bi ta da kallo, yana tunanin yara biyu ne a cikinta.Addu’a ya din ga yi, Allah ya sa yana rabon da ganin yaran, tare da yi musu fatan shiriya tun kafin su zo duniya, da fatan Allah ya sa kar laifukan da ya aikata su shafi yaransa.Nabila tunani ta din ga yi, na abin da za ta yi, da zai wayar wa da al’umma kai, a kan muhimmancin neman ‘yancinsu, da ƙirƙiro abubuwan da za su taimaka wurin ƴaƙi da harkar daba da shaye-shaye da kuma bangar siyasa.Yanayin shirin bikin Sumayya da suke yi, ya hanata zama su tattauna yadda yakamata, ta na son ta yi magana da Viper ma, domin za ta so goyon bayansa ɗari bisa ɗari a kan abin da take ƙudurin yi ɗin.Aka yi taron bikin sumayya lafiya, aka gama lafiya, ita ma mijinta mutum ne mai rufin asiri, ya na da mace ɗaya da yara uku, cousin ɗin Alhaji mu’azzam ne, shi ne ya haɗa shi da ita ma.Major yana ta mitar Nabila kwana biyu ba ta zuwa gaishe shi, ya kirata ya ce mata shi zai zo ya ganta, amma ta ce masa ba ta nan, sai dare zata dawo.Bayan sallar isha’i kuwa sai gashi shi da Anty, tun da suka zo ta manne a wuri ɗaya ta ƙi tashi.Viper ya yi wa Major zancen rabon gadon Jauhar, za a sayar da kayanta, Nabila ta ce ba ta son kaya.Abba ya ce “Ni idan an yi wa kayan kuɗi a bani na saya, sai mu bayar sadaka Allah ya kai mata ladan”.Viper ya ce “Ita ma ta ce kuɗin, ayi wani abu da su, Allah ya kai ladan kabarin Jauhar”Major ya ce “Hakan ma yayi kyau, amma a ajiye wani abu da za a din ga tunawa da ita dai””Eh in sha Allah, ko ma muje gidan tare, sai na yi wa Baba magana muje a duba”Major ya ce “Duk yadda ka yi yayi, Allah ya saka maka da alkhairi kai ma, Allah kuma ya ƙara bamu haƙurin rashin Jauhar da mahaifiyarta”Har suka gama abin da za su yi, Nabila taƙi yi musu rakiya, sai Viper ne ya raka su, suna tafe a hanya Major yake mitar Nabila duk ta zama so silent, ko dai akwai wani ne da take ɓoyewa.Anty ta ce “Ciki ne fa da ita, take ta wannan nuƙu-nuƙun””Kaii ciki, tun yanzu?”Anty ta ce “Ahh ikon Allah, wata nawa da yin auren?””Lallai Major, wato Arfa ce ‘ya, mu a shekara nawa muka haihu?”Ya ce “Ai ku tun zamanin baya ne, ita kuwa kamar yayi wuri, haryanzu ƙanƙantarta nake gani””Shekara ashirin da shida?””Eh mana, rainon ciki akwai wahala, kin ga ita ga ba uwa, ku ba tayi sakewar da za ta tunkaroku da wannan maganar ba, balle ma idan wani abin ne ku taimaka mata ba, bari na koma gida, zan kirata a waya, ko da wani abu da take buƙata”Waro ido ta yi ta ce “Sai ka tambayeta a kan cikin?””To shi ne me? Ni uwar ni ne uban, ai cikin halak ne, mijinta ba mazauni ba ne ba, cikin fari ba ta san kan komai ba””Amma ai ka bari mu mu tambayeta ko””Tsakaninki da Allah yaushe rabonki da ita, ban da yau da na ce ki zo ki rako ni wurinta? Ni ba abin kunya ne a wurina ba, idan ta kama na dawo da ita gida, gani gata magajiya ta din ga kula mini da ita, ba ruwanku” Anty ta ja bakinta ta tsuke, dan ba ta ga tsari a hakan ba.Aikuwa kamar yadda ya faɗa, hakan aka yi, bayan ya koma gida ya kira Nabila yake tambayarta. Kasa ba shi amsa tayi, ta ji tamkar ta nutse a wurin, saboda kunya.”Idan kin san akwai matsala, ni sai na yi wa mijin naki magana, idan baya gari ki taho gida, ko na turo miki magajiya, ta din ga kula da ke””Abba yana kula da ni, baba Magajiya kuma yakamata ace zuwa yanzu ta huta ita ma, ina iya yin komai ma””Kin tabatta?””Eh Abba””Arfa ba na son kawaicin nan naki, Ni babu kunya a tsakanina da ke, baki da uwa a raye, kar ki bari wani abu ya shige miki duhu, idan ba zaki iya kirana a waya ba, ki yi mini message kin ji ko?””To Abba””Allah ne mai komai, amma ba zan so ki sha wahalar da mahaifiyarki ta sha ba””In sha Allah”Ya ce “Yauwwa, sai da safe, ki gaida mijin naki, Allah ya yi muku albarka gaba ɗaya””Amin mun gode, ayi wa Anty ya ta je gida” ta kashe wayar, Viper ya na kusa da ita, ya na saurarenta.”Abla” ta waiwayo ta ce “Na’am””Kowane dangi, idan aka samu irin Abba ko guda ɗaya ne, mai jajircewa a kan zumunci, ba tare da kallon ɗora wa kansa ɗawainiya ne ba, da an rage wani abin. Mutum ne mai zafi, amma jajirtacce ya san abin da yake yi. Ke kaɗai sadaƙatul jariya ce a gare shi ko bayan ransa. Banda ladan zumunci hatta taimakon da ki ke yi wa al’umma yana da lada. Kin tsayawa dattijon nan babu ko sisi, kin tsaya wa rahama, kin tsaya mini duk babu ko sisi, kin siffantu da wasu daga cikin kyawawan ɗabi’unsa, da shi da Alhaji mu’zzam, da Walid da liti, mutane ne da al’umma ke buƙatar irin su.”Nabila ta ɓata fuska ta ce “Ban da liti dai””Haba masoyiyya, ya fa baki haƙuri. Wallahi Abdallah mutumin kirki ne fiye da yadda ki ke zato, kawai dai mutum ne da babu ruwansa da kara, zai yi abin da yake so ne, ko yayi maka daɗi ko ya kashe ka, bai damu ba””Ai na ga alama, ni fa ban taɓa zaton ya na barkwanci ba, ranar da na fara ganinsa, a tal’udu wurin da yake sayar da katin waya, amma kayan maye yake sayarwa, sai da na tsorata.Babu alamar ɗigon imani a tattare da shi, sai fa da ya ce sai ya kashe ni, idan na sake zuwa””Wallahi ba haka yake ba, sharrin ƙwaya ne kawai da kayan maye, Allah dai ya ƙara shirya mu, rayuwa duk ta fi yi mana daɗi a yanzu. Mutane kowa yana sonmu, yana son haɗa alaƙa da mu, har ana ɗora mana wasu nauye-nauye.Duk a baya, mu kanmu bamu jin cewa, a duniyar da mutane suke muke, hango duniyarmu muke yi daban, saboda kowa kallon mutane marasa amfani yake yi mana. Marigayiyya ce ta fara ƙoƙarin ankarar da mu, muhimmancinmu a cikin al’umma.”Nabila ta jinjina kai ta ce”Jauhar ta yi namijin ƙoƙari ƙwarai da gaske, kuma in sha Allah, yana daga cikin abin da na ƙudurce a zuciyata, ci gaba da yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, ta hanyar nuna wa wanda suka tsinci kansu a harkar, su ma ‘ya’ya ne, kuma akwai amfanin da za su yi wa al’umma.Ina son da ni da kai, sa sumayya, barrister Habib, da wanda suka kamata, mu ga abin yi, idan ta kama ko ƙungiya ce mu kafa, ko mutane goma ne suka shiryu a sanadinmu, mun yi nasara””Duk a bar wannan maganar, sai Allah ya saka kin sauka lafiya, sai ayi ta, tunani mai kyau sosai da sosai. Sumayyan nan taki ma ‘yar aljanna ce da yardar Allah, na ga tana yinki saboda Allah””Ko ba Sumayya ba, ba ka ga Abba ne yayi waliccin aurenta ba ma, ƙawar amana kenan, ina alfahari da ita”Haka Viper suka ci gaba da tattaunawa da shi da abar ƙaunarsa.Kwanci tashi asarar mai rai, cikin Nabila ya yi watanni shida, amma kamar zata haihu a lokacin, saboda girma, hakan ya saka ta daina fita gaba ɗaya, saboda nauyin cikin.Shahida kuwa matar Walid, ta fita nauyi, dan ita nata ya kusa shiga watan haihuwa.Ramma na gida ta dawo daga makaranta, tana ta sauri ta gama abin da take yi, ta san Abdul ko ya dawo, ko ya aiko a ɗaukar masa abinci.Kiran waya ta gani, da baƙuwar lamba, ta ɗaga tare da yin sallama.”Matar doctor Abdul ce?””Eh nice””Ok, dan Allah maza ki taho Asibiti, Doctor ne ya yanke jiki ya faɗi””Innalillahi wa Innalillahi raji’un” ta furta jikinta yayi wani irin sanyi.
Ayshercool 08081012143



