Hausa novels

Kanwar Maza Page 58 Complete Novel By Ayshercool

 

Page 58

 

Sororo ta yi tana kallon sa, sam ba ta fuskanci in da ya dosa ba, abun da ta iya ganewa kawai shine ƙwaila, wato wadda ba ta da nono.

 

“Am talking to you kin tsaya kina kallona”

Cikin tsuke fuska ta ƙarasa gaban booth ɗin, manyan ledoji ne a ciki.

Ya dubeta ya ce “Gasu nan, iman ta ce yadin wanda zaki rabawa ƙawayenki, sauran bayanin ban riƙe ba, idan kun yi waya ta yi miki.

Akwai invitations da wurin da za ayi events, sai kayan sawarki”.

 

Maimakon ta ce Ta gode, sai cewa ta yi “Ni ta yaya zan iya ɗaukar wannan kayan masu nauyi, kuma fa an sai mini kaya a gida, nifa kar ka zo daga baya ka din ga yi mini gori, idan ka san ba da zuciya ɗaya ka bani ba, ka riƙe abunka, ƙawayena za su saka abun da suke da shi” ɗagowa yayi ya kalli rumaisa, sai dai maimakon ya ji haushin abun da ta faɗa, sai ma ya yaba da yadda take taka tsan-tsan, ita dai kar ayi mata gori, tana da gudun abun wani.

 

Amma a zahiri, sauke mata kayan ya yi a ƙasa, ya rufe booth ɗin motarsa, ya saka hannu ya ɗauko wata babbar ledar a motarsa, ɗora mata a kan kayanta ya ce “Idan da wani abun ki saka Aliyu ya kirani” daga haka ya shiga mota ya ja ya tafi.

 

Gida ta shige ta ce wa su Huzaifa su je waje su kwaso kaya, idan ba haka ba a sace. Sun zata da wasa take yi, ashe da gaske take.

Gwaggo tuni ta zo kano, ita da lawisa, da zaliha, aka baje kayan da takawa ya kawo wa rumaisa.

 

Iya leshin da zata saka na dinner, ka san ba ƙarami bane ba, an ɗinka shi da jakarsa da takalmi da komai, an haɗo mata kayan fitar biki, ga kuma invitations, rumaisa ta yi ta kallon invitation ɗin tana mamakin wai sunanta ne a jiki.

 

Ledar nan da ya bata kuwa, babbar envelope ce a ciki wata dubu ɗari biyar ɗin ce a ciki.

 

Mama ta kalleta ta ce “Rumaisa tambayarsa ki ka yi?”

 

“Haba mama, to ni ce masa ma na yi, idan ya san zai yi mini gori wataran, ya ɗauki kayansa, ni za a sai mini a gida”.

Gwaggo ta yi salati ta ce “Shi mijin naki ki ka gayawa hakan?”

 

Rumaisa ta ce “Mijina kuma taɓ”.

 

Usman ya ce “Ke fa banza ce, yanzu ya kawo miki wannan uban kayan ki kasa yi masa godiya, saboda ke dai baki da alƙibla?”

 

Ta yi shiru tana muzurai. “Bari Aliyu ya dawo, ya kira shi a waya, ki yi masa godiya tun da ba ke ki ka nema masa kuɗin ba”

 

Haɗe rai ta yi, saboda zuwa yanzu yaya usy yana takura mata a kan mutumin fiye da kima.

 

Can kuma ta hau murna, tana lissafin ƙawayenta da zata bawa ankon da zasu ɗinka, ga uban kuɗi kuma tana gani.

 

Mama dai shiru tayi tana bin kayan da kuɗin da kallo, ita ba tarin kayan alatun ba, fatan ta Allah ya sa rumaisa ta shiga a sa’a ya sanya mata albarka.

 

***

Bin invitations ɗin yake da kallo, yana tuna lokacin da yayi auren fari, tun saura wata guda biki ya fara ɗoki, yana murna yana rabon invitation card, a wannan karon da shi da amaryar bai san wanda ya fi wani anti serious ba.

Rumaisa Mahmud, ya din ga kallon sunan nata, da kuma nasa Adam Sharif Galadima.

 

Bashir ne yayi sallama a falon, Adam ya amsa masa, ya ƙarasa suka gaisa sannan ya zauna ya kalli Adam ya ce “An kammala komai na gidan, zasu iya kai kaya a kowane lokaci”.

 

Adam ya ce “Masha Allah, that’s good ina godiya sosai, ina sidi?”

 

“Na ajiye shi, shima ya sha aiki ya gaji”

 

“Na gode sosai bashir, zan shiga na je na gani, daga nan sai na ɗauki ko mutum biyu a yayyenta, mu je su ga gidan”.

 

Bashir ya ce “Hakan yayi, Allah ya sanya albarka, amma haryanzu fa ba ka fara rabon invitation ba, ko a social media ba a saka ba”.

 

Adam ya ɗan yi jimm sannan ya ce “Wallahi Bashir sam bana ɗokin auren nan, bana son duniya ma ta san zan yi shi, ni da za a shafa fatiha ma ba wannan events ɗin da na so hakan, rainon yarinya kawai za a kawo mini”

 

Bashir ya yi murmushi ya ce “Ka yi haƙuri, ammi ba zata zaɓa maka abun da zai cutar da kai ba. Sannan ba zai yiwu ka ɓoyewa duniya zaka yi aure ba, idan ta fasu aka sani, za a iya yi maka wani sharrin”

 

“Haka ne, haka zalika idan aka ga Yarinyar da zan aura, shi ma ba zan tsira ba, mussaman idan aka san ita ta zo da ɗa na daga hannun ƴan bindiga”.

 

Bashir ya ce “Mafita ɗaya ce, duk yadda zaka yi ka ɓoye wa duniya cewar ba son auren ka ke yi ba, dole a ga farinciki da ɗoki a fuskarka”.

 

Adam ya yi murmushi ya ce “Yadda za a ji daɗin cewa, saboda na auri yarinya ƙarama na kashe matata ko?”

 

“Ai dama dole sai an faɗi wani abu, amma yafi ace ka yi amfani da ƙaramar yarinya ka ɓoye wa duniya laifinka, na kai kashe matarka, ka turasasata ta aureka, dan kar a cigaba da surutu da zargin ya za ayi yarinya ƙarama kamarta ta kuɓuta da jariri a hannun ‘yan bindiga”

 

Adam ya yi ajiyar zuciya, ya ɗan murza goshinsa ya ce “Duniya gidan rikici, Allah ya iya mana”.

 

“Amin ya Allah”

 

Wayar takawa ce ta fara ringing, ya ɗauka ya duba ya ga sunan Aliyu.

 

Ya ɗaga ya saka a kunnensa tare da yin sallama, Aliyu ya amsa ya ce “Barka da wannan lokaci, ya hidima?”.

 

“Alhamdilillah, ya taku hidimar?”

 

“Mun gode Allah, dama rumaisa ce za ta yi magana da kai”

 

Adam ya ce “Ok, ba ta”.

 

Rumaisa ta karɓi wayar, Usman ya sakata a gaba ya tsareta da ido.

 

Ta karɓi wayar ta saka a kunneta, amma ta tsaya tana kallon Usman, ta kasa magana.

 

Ya daki ƙafarta ya ce “Ba zaki gaishe shi ba?”

 

“Ina wuni?”

 

Maimakon ya amsa ya ce “Ya aka yi?”

 

“Gaisheka fa na yi” ta yi maganar a ƙule.

 

“Ba a yi wa basarake irin wannan gaisuwar, babu ladabi a gaisuwarki, dan haka ko sau nawa zaki yi ba zan amsa ba, riƙe kayarki, ina jin ki”

 

Rumaisa ji ta yi kamar ta yi zagi, meye aibun gaisuwar ta, idan ba neman bala’i ba.

 

“Idan kin shirya yin magana, sai ki sake kirana”.

 

“Su yaya ne suka ce dole sai na kiraka na yi maka godiya, na gode, kuma wai kuɗin da ka bani sun yi yawa, sannan……”

 

“Lokacin da ki ka san abu yakamata, ba sai wani ya saka ki ba, sai ki neme ni, yayyenki na ƙoƙari wurin baki tarbiyya, Allah ya biya su, kuɗi kuma ki zubar” ya kashe wayarsa.

 

Dungurar da wayar ta yi a ƙufule, ta ce “Yaya usy kalli abun da ka janyo mini”

 

Dungure mata kai yayi ya ce “Ki ka jawa kanki dai, ke a rayuwar duniya baki iya siyasa ba? Ji yadda ki ke gantsara masa magana, kamar kashi ba tausasa lafazi, ba ɗan karya murya, wai ke ma namiji ce irinmu ne? to ko mu muna kashe murya, ranar da na kama malam habu yana waya, kamar ma nutse dan kunya, amma ke kina ta wani shirme.

Ke, tashi mu je ɗaki, na yi miki bayanin me auren ya ƙunsa, in fayyace miki komai in gaya miki, na ga mama ba ta da niyyar gaya miki, daga ita har su gwaggon.

 

Aliyu ya ce “Kai fa wasu lokutan baka da kamun kai, uban me zaka gaya mata?”.

 

“Komai ma gaya mata zan yi, yo haka za ta je ta zauna masa a gida kamar gardi, idan ka ga tana tausa murya to wani abun take nema, tashi mu je na fayyace biri har wutsiya”.

 

Aliyu da dariya ta ƙwace masa ya ce “Mama, wallahi usman ya zama abun da ya zama, zai juyawa yarinya tunani, saboda bashi da kamun kai”.

 

Usman ya ce “Eh, bani da kamun kan, ni ina ma ni za ayi wa auren nan, wai muna zaune ƴar da aka haifa a gabanmu za ta rigamu girma Allahu Akbar wata shekarar sai ta fara ƴa ƴa kuma”.

 

Aliyu ya ce “Wani irin ta fara ƴaƴa wata shekarar, kamar wata bishiyar lemo, wannan yarinyar ko nan da shekara biyar albarka”

 

Wani irin kallo Usman ya yi masa ya ce “Haba, a banza za ku kaita ya din ga bata abinci, yana biya mata kuɗin makaranta ko? You don’t get sense. Ko kaza dan a cinyeta ake killace ta a  sai mata dusa, kar ka yaudari kan ka”.

 

Aliyu ya ce “kai haba, she’s too young for it, and the man is very decent and calm, bana tunanin haka”.

 

Usman ya yi dariya ya ce “Uban calm da decent ɗin, that thing don’t get sense, don’t fool yourself, if not ku fasa aurar da ita, hauka ake mutum zai kashe kuɗi ya auri ƴa ya sakata a gaba yana kallonta, Allah ya sa jaririya ce”

 

Aliyu ya yi tsaki ya ce “Zaka ɓata mini rai ”

Rumaisa da ba gane kan hirar take ba, ta din ga bin su da kallo, Usman ya ce  “To Algume, sai kallon bakinmu ki ke, ƙila kin san komai, ki ka yi wani kasaƙe da kai”.

Kanwar Maza Complete Novel Document Txt

Aliyu ya ce “A hakan ta san komai? Tana wannan gidadancin”.

 

Usman ya ce “Kuma fa haka ne, to jeki na fasa gaya miki komai, duniya zata gaya miki, Allah ya shiryeki”.

 

“Nuraini, Allah ya baka abun yi na aurara da kai, ina ga daga rumaisa kuma sai kai, tun baka wuce in da nake tunani ba” a guje Usman ya faɗa ɗakinsu, dan sam bai san mama ta ji hirarsu ba.

 

***

Jabir ya din ga juya invitation ɗin, sannan ya kalli Adam ya ce ” da gaske Adam saura kwanaki a ɗaura maka aure, amma ban sani ba?”

 

“Am sorry, abun ne ya zo cikin gahgawar gaske fiye da yadda na yi zato, sai haƙuri”.

 

Jabir ya sake kallon invitation ɗin, sannan ya ce “To ita kuma wacece, a ina take? Kamar na san sunan nan”.

 

Adam ya ce “Zaka ganta very soon”.

 

“Da jamil ya gaya mini maganar auren nan, na zaci da wasa yake yi, ashe da gaske ne, Allah sarki samha ina tausayin yarinyar nan sosai”.

 

Adam ya ce “Please, don’t raise that issue here, ku daina ganin laifina, ƙaddara ce ta zo a haka”.

 

Jabir ya ce “Na yadda, ban ce wani abu ba, kawai dai ina jin tausayinta ne, sai dai na yi mamakin yadda har ka nemi aure, har ka samu ban sani ba, yaushe muka fara haka da kai”.

 

“Jabir, this is an arranged marriage, ku yi mini uzuri”.

 

Jabir ya ce “Arranged marriage, to Allah ya sanya alkhairi ya sa za ayi da mu”.

 

“Amin, addu’arku nake buƙata dama, yanzu ka tashi mu je gidan mai girma turaki, zan kai masa nasa katin, da zai bawa mutanensa, da na jamil da gidan gaba ɗaya”.

 

Jabir ya ce “Ok, ba damuwa bari mu yi salla tukuna”

 

Bayan sun idar da salla, suka tafi gidan turaki, kai tsaye sashinsa suka shiga, bayan sun tarar da babu kowa a falon.

 

Yayi murna sosai yayi addu’a da fatan alkhairi, sannan ya yi wa adam nasiha sosai mai shiga jiki. Sai dai kamar haɗin baki suka tarar da mama da Samha, har ma da zainab a falo.

Samha jikinta har tsuma yake da ta ga Adam, ga soyayya ga kuma kishi, ya gaida mama ta amsa masa sama-sama, ta saki jiki ta amsa gaisuwar Jabir.

 

Su Samha suka gaishe shi ya amsa, ya ajiye wa mama katuna, ya ce “Gashi nan, ammi ce ta ce in kawo miki, na taron wunin da za ta yi, na bawa mai girma turaki nasa”.

 

Da ƙarfi Samha ta ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, Adam wai dama da gaske ne, ta tabatta aure zaka yi?” Ya ɗaga kai ya kalli Samha da tsoro da kishi ya bayyana a fuskarta, ya jinjina mata kai a hankali cikin tausayawa.

 

“Shikenan, bakomai na gode ” ta tashi ta bar falon. Jikin Adam ya yi sanyi, mama kawa jan tsaki ta yi ita ma, Zainab kuwa cewa ta yi Allah ya sanya alkhairi.

 

Ɓangaren ammi ma, da ta bawa mummy katin gayyata, masifa mummyn ta din ga yi, wai har ace adam zai yi aure, amma a kasa sakata a cikin lamarin bikin, sai dai ta zo a ƴan gayya, saboda ba a mayar da ita a bakin komai ba.

 

A gidansu rumaisa ma, shirye shirye sun yi nisa. Mai sunan baba ya buga wani invitation ɗin na ɗaurin aure, aka rubuta sunan Adam sharif, ba tare da sanya cikakken sunan Adam ba. Ba ƙaramin mamaki ƴan unguwar su rumaisa suka yi ba, jin za ayi mata aure, wasu suka din ga surutu suna cewa sai ka ce a ƙauye, wasu kuma suka ce ta tabbata rumaisa ta yi cikin shege ne, ake son a liƙawa wani, kuma aka kasa gane wanene mijin, sai dai hatta wurin da aka rubuta za ayi bukukuwan a wurin ba ƙananan wuri ba ne, nan ma aka yi ta surutun ina suka samu kuɗin kama wannan wurare.

 

Zaman Gwaggo a gidan, ta din ga yi wa rumaisa faɗa, tare da nasiha a kan aure, da yadda za ta kula da miji, sai dai sam rumaisan ba ganewa take yi ba, yadda aka sakata a gaba ana sake koya mata girki ya fi komai ci mata rai, a ganinta ana hanata hutawa, girkin nan da karambani ta iya shi, dan tun shekara tara take gwadawa, tun mama tana hanata har ta haƙura ta rabu da ita.

 

Samha ta yi kuka kamar zata yi hauka, gaba ɗaya ji take komai ya fita daga ranta, ko abincin kirki ba ta iya ci, sabuwar soyayyar adam ta dawo mata sabuwa fil, sai dai ta yi alwashin yadda ta zubar da hawayenta a kan sa karo na biyu, daga shi har matar ta sa sai sun ɗanɗana kuɗarsu.

Fauziyya ta din ga zigata a kan ta san duk yadda za ta yi, ta cuzgunawa matar da adam zai aura, har da ba ta tabbacin cewa, ta ji an ce auren haɗi  ne ba son ta yake yi ba.

 

Ana gobe za a yi wa rumaisa jeren kaya, Adam ya ɗauki Aliyu da Abdallah, zuwa gidan rumaisa, dan su gani daga nan ya basu mukulli.

Sai dai da suka je, Aliyu ya raina kayan da suka saya, da suna ta murna sun yi wa rumaisa kaya masu kyau da yawa, sai dai gidan babba ne sosai.

Sama da ƙasa ne, ƙasan akwai babban falo, da ɗakuna biyu, da kitchen da store, saman bene kuma falo biyu, bedroom uku, da kitchen da dining, kowane ɗaki da toilet.

Gidan ya tsaru yayi kyau, dan an kashe kuɗi wurin yin sa sosai.

 

Aliyu suka yi ta santin gida, suna yi wa Adam godiya. Sai dai tun da suka koma gida suka sanar da mama, gidan yafi ƙarfin abun da za a kai, jikinta yayi sanyi, dan ba dan kar ta nuna halin ƙaranta ba, cewa za ta yi idan da ƙarami a saka rumaisa a ciki.

 

Kaf ƴan unguwa ba wanda mama ta ce su je yi wa rumaisa jere, ƴan uwanta da ƴan uwan mahaifinsu rumaisa, sai yayyenta ne suke je suka jera mata abun da ya samu a saman benen.

Gado biyu aka yi mata, dangin babansa suka yi mata ƴan waje guda ɗaya, yayyenta suka yi mata ƴan gida, masu matuƙar kyau.

 

Kitchen ɗin ta ma babu laifi, a dai ƴar talaka, iyayen rumaisa sun taka rawar gani sosai da sosai, ga kujerunta da labulaye, ga dininga komai dai-dai gwargwado.

 

Ƴan uwa suka dawo, suka din ga santin gida, suna yi wa mama barka da arziki, rumaisa ta je gidan hutu.

 

Da daddare Adam ya je gida da shi da su ammi, suka ga jeren da aka yi, ammi ta jinjinawa ƙoƙarin iyayen rumaisa, ba ita ba shi kansa adam, abun ya bashi mamaki, aka jere mata akwatunanta goma sha biyar a bedroom.

Washegari Adam ya saka aka kawo abubuwan da babu, wanda basu ƙarasa ba.

 

Rumaisa ba ta yadda aurenta za ayi ba sai da satin biki ya kama, dama Aliyu sun shirya football match, a nan cikin unguwa.

Tun da rumaisa ta tabattar da idan aka yi auren barin gidan za ta yi, ta fara koke-koke tana fasa.

 

Ranar da za ayi bridal shower, daga gidan su adam, aka aiko da mota, aka ɗauki rumaisa zuwa gidan kwalliya, ita da ƙawayenta, babu ko sisinsu, aka yi musu kwalliya aka wuce da ita wurin biki.

 

Su Iman tuni suna can, sun sha kwalliya iman kamar balarabiya, da ita da wasu daga cikin famylinsu, da su ƙawayenta.

 

Rumaisa gaba ɗaya ta kasa sakin jikinta, mussaman yadda ake kallonta, wasu suna jinjina wannan ƴar yarinyar takawa zai aura?.

 

Su hauwwaliya kuwa, sai iyayi ake da rawar kai, su gasu ƙawayen amarya.

 

Babu zato babu tsammani, sai ga ƴan mazan mama sun dira a wurin, da shigar ƙananan kaya, rigunansu mai kalar kayan da rumaisa ta saka maroon.

 

Washe baki ta yi, ta nufesu da gudu tana dariya, suka rungumeta suna juyata.

Yasir ya ce “Taɓ, kin ga fuskarki kamar sarauniyar aljanu?”

 

Ta ɗan kwaɓe fuska ta ce “Na sani nima, fuskata sai ƙaiƙayi take yi, kuma an ce idan na sosa zan ɓata kwalliyar”

 

Abdallah ya ce “Ai abun ka da ba a saba bane ba, kuma fa kin yi kyau”

 

Mamaki ne ya kama ƴan wurin, me ya kawo maza wurin bridal shower, har da anko?.

 

Iman ce ya fara ganinsa ya shigo wurin, sai da hankalin da yawa daga cikin ‘yan matan ya koma wurinsa, ciki har da iman, da take ta ƙara gyara cake ɗin da yake kan table.

 

Rumaisa ba ta taɓa tunanin mai sunan baba zai zo ba, zuwansa ya sanya suka cika su bakwai samarin gidan su kowa ya zo.

 

Gaban table ɗin ya ƙarasa, kusa da iman ya ɗauki ƴar ƙaramar wuƙar yanka cake ɗin, ya yanko cake, ya kalli rumaisa ya yi mata alama da ta buɗe bakinta, ta buɗe kaɗan ya saka mata a baki sannan ya ce “Happy marriage life ƙanwar maza, Allah ya sanya albarka” tafi aka hau yi ana shewa, rumaisa ta kasa tauna cake ɗin idonta ya cika da ƙwalla.

 

Ya girgiza mata kai, ya nuna mata mai hoto, ya ce “Smile, amarya ba ta haɗe rai ranar aurenta”

 

Kasancewar yayyenta a wurin ne, ya sanya ta saki jikinta, suka din ga ƙoƙarin yin abun da zai kwantar mata da hankali.

 

Sai dai mai sunan baba, ya rasa dalilin da ya sanya shi, son satar kallon iman, gaba ɗaya kamar ba bahaushiya ba, ta yi kyau sosai da sosai, a ɓangaren iman kuma, zuwansa wurin ya sanya duk ta takura, da ta motsa sai su haɗa ido, gabanta ya faɗi.

 

Ƙarshe dai da su aka gama partyn, suka ɗauki ƙanwarsu suka yi gida.

 

Mai sunan baba ne ya rage, zai tafi ya fito harabar wurin, in da zasu tafi shi da abokinsa, kasancewar abokin nasa yana da abun hawa.

 

Iman ya gani a tsaye, wani matashin sauryi ya tsareta, yana ta zuba mata surutu ita kuma da alama akwai abun da take jira.

 

Haka kurum ya tsinci kansa da tsareta da ido, wanda hakan ya sanya ta ji kamar ta fasa ihu, jikinta har rawa yake, gani take kamar ta aikata wani zunubi da bai kamata ba.

 

“Me ki ke jira baki tafi gida ba?”

 

A tsorace ta ce “Motocin ne suka cika, shi ne na ce su tafi zan taho”.

 

“Wuce mu tafi” yayi maganar cikin command.

 

Babu musu ta wuce, ya sakata a gaba, zuwa motar da zasu tafi.

 

READ ƘANWAR MAZA PAGE 59 HERE


Proceed with your download by clicking the below button

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button