Halysaah Page 207 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 207…Suna sauka Airport din Abuja suka tarar motar da zai tafi da su Makurdi na jiran su a airport din, Ajay na zaune kusa da Khaleesat a baggage claim area yana kallonta don idanuwanta a lumshe suke, tun da suka shigo Arrival hall din ta nemi waje ta zauna, and they’ve been sitting there for a while now Jay dai tuni ya fita zuwa gun motar da ke jiransu da hand luggage, wai ɗan tafiyar da tayi daga bakin jirgi zuwa hall din shine take ji kamar tayi tafiyar awa daya a kafa, after some more minutes Ajay yayi kasa da murya yace “Jeeddah” jin bata amsa ba ya fahimci she is sleeping ne haka, mamaki ya sa ya dinga kallonta babu ko kiftawa, Jay ya gaji da tsayuwa a waje ganin basu fito ba kuma su ba kaya suke jira ba ya doka ma Ajay kira, vibration din wayar ne ya tashi Khaleesat ta bude ido, Ajay ya ciro wayar ya daga ya kai kunne, daga daya bangaren Jay yace “Wai Ajay dama ka san baka shirya tafiyar nan ba ka sa muka kamo hanya?” Ajay yace “Not at all, she is having a little nap” Takaici yasa Jay ya rasa ma me zai ce masa, kawai ya katse wayarsa ya mayar aljihu, Khaleesat ta hade rai tana kallon Ajay tace “Me ya ce?” Ajay yace “A’a cewa yayi Driver na waje yana jiran mu” Tace “To naga kamar baya son in bi ku, ya mance wancan lokacin haka ku ka tafi ya dawo shi kadai….” cikin sanyin murya ta kare maganar, Ajay ya ɗan yi murmushi yana kallonta, after some seconds yayi kasa da murya yace “Yanxu dai as my security zaki bi mu kenan wife?” A hankali tace “Eh mana” Yana murmushi yace “To tashi mu je…” Hannu ta mika masa alamar ya dagota, ya dagota suka nufi hanyar fita daga arrival din, a hankali tace “Ina jin kamar kaina yana min ciwo….” Ajay ya juya ya kalleta yace “To bari mu fita outside of the airport a siya maki magani” Ta gyada masa kai, a haka suka isa inda driver yayi parking, Jay na tsaye jikin mota ya rungume hannunsa fuskarsa babu yabo babu fallasa, Ajay ya bude ma Khaleesat back seat yana amsa gaisuwan driver, Jay bai ko kallesa ba ya bude front seat ya shiga, Ajay ya shiga bayan motar ya zauna kusa da Khaleesat yana kallonta, a haka suka fita daga cikin airport din, bayan sun dau hanya Ajay na kallon driver yace “Nearest pharmacy zaka fara kai mu sulaiman” Drivern yace “To ranka shi dade” Suna isa wani babban pharmacy drivern yayi parking, Ajay na kallon Khaleesat yace “Let me get you the medicine” Ta gyada masa kai ya bude motar ya sauka, Jay ma ya sauka daga motar, Khaleesat ta bi sa da kallo, a tare suka nufi cikin pharmacy din, Jay na kallon Ajay bayan sun yi nisa don baya son magana gaban Khaleesat yace “Ajay idan kana son muyi tafiya irin na matafiya masu hankali to ka nemi inda zaka bar Halysaah har mu je mu dawo, ban ga ta yanda za mu yi tafiyar nan da ita tana langwabewa kamar lagwani a haka har zuwa Makurdi ba, gaskiya i am not ready to be stressed Ajay, da ma stress din iya kai kadai zai tsaya da sauki, but in dai tafiya za mu yi cikin tsari it’s better you leave ur wife behind mu yi dropping dinta gidan Ammi” Ajay dai jin sa kawai yake yana tafiya, Jay yace “Kawai duk ka sa yarinya ta dawo wata irin fitinanniya” Sai a sannan Ajay yace “A’a dama tun asali haka take, a haka ka bar min ita don rainon ka ce ai” Jay ya jefa masa wani kallo kamar bazai ce komai ba yace “Cikin dai da ka dirka mata ya maidata haka….” Ajay yayi er dariya yace “Yanxu dai idan mun koma mota sai kayi mata duk bayanin nan da kayi yanxu na cewa mu bar ta a Abuja” Jay yace “Ka tafi gaba da Makurdi da ita ma mana ina ruwana” Ajay na murmushi yace “She is been insecure akan tafiyar ne, and I sense she is afraid to let me go alone, she doesn’t want history to repeat it self again” Jay dai kallonsa kawai yake jin abinda yace, ya sauke idonsa bayan shi ma memories din sun dawo masa, shi fa tun da ya sa a ransa bazai dinga tuna abubuwan da suka faru a baya ba to kwata kwata baya barin zuciyarsa ya tuna da past, abinda ya saka ka shiga damuwar da baka taɓa shiga irinsa ba duk tsawon rayuwar ka ai ba abu bane da zaka so ka dinga tunawa, after some seconds ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace “But the journey isn’t safe for her duba da yanayin da take ciki, kai baka san yanda zaka lallabata ta hakura da tafiyar ba ne, it won’t be good ace abu ya samu cikin jikinta….” Ajay yayi shiru cause he also reason with what Jay is saying but who will bell the cat? tun da suka nufo mota bayan sun fito daga cikin pharmacy Khaleesat ta hade rai tana kallonsu, kawai ranta ya bata Jay cewa Ajay yayi kar a tafi da ita shi yasa ya fita daga motar ya bi sa, Ajay na shiga back seat ganin yanda ta sha kunu kamar warce ke jiran kiris ta fashe bai samu courage din ce mata ta zauna a Abuja har su dawo ba, Jay kuwa tun da ya kalleta sau daya bai sake kallonta ba cause ya ga alamar kiris take jira tayi masu kuka. The journey to Makurdi was so stressful and not fast saboda tsaye tsayen da suka dinga yi a hanya duk dalilin Khaleesat, bini bini tace amai kuma idan an tsaya sai ta kasa yin aman, duk inda ta kyallara ido taga alamar gari sai tace a tsaya a huta don sosai ta gaji da tafiyar, gaba daya ta rasa inda zata saka kanta ta ji dadi, idan taji zaman ya isheta sai ta kwanta a kafar Ajay, gashi in driver yayi gudu sai tace ma Ajay ya gaya masa ya rage gudu tana jin jiri, Jay dama toshe kunnensa yayi da earpod yana sauraron wa’azi wani lokacin idan yaga driver yayi parking baya ma sanin dalilin parking din don kunnensa a toshe yake kar ma ransa yayi ta ɓaci, cikin garin Makurdi suka nufa direct cause it’s late evening time suka iso Benue, kuma baza su tsallaka ruwa by that time ba, Jay ya biya masu hotel da suka yi lodging a Makurdi, yayi wucewarsa nasa room din ya bar mata da miji a reception, ya dade bai yi tafiya me cike da haushi irin wanda yayi yau ba, kawai sun yi tafiya ne kamar wasu gantalallu, da kyar Khaleesat tayi wanka tayi sallah bayan sun tafi nasu dakin, ko abinci ta kasa ci sai tea da ta sha sannan ta sha magungunan da Ajay ya siya mata ta kwanta, Ajay dai na zaune gefenta yana kallonta, har ransa yake tausaya mata saboda yanayin da ta shiga, she was more than stressed yau, ya kai hannu forehead dinta yaji zafin jikinta babu yawa, a hankali ta bude ido tana kallonsa, yayi kasa da murya yace “Ina yake maki ciwo?” Mikewa tayi ta shige jikinsa ya rungumeta, cikin sanyin murya tace “Kawai na gaji ne” Patting din bayanta ya dinga yi a hankali tana jikinsa, ba a dau lokaci ba bacci ya dauketa, ya jingina da gado making her to relax fully a jikinsa ta yanda zata zama comfortable, shi ma a haka yayi baccin ko abinci bai ci ba. Washegari basu suka bar hotel din ba sai wajen karfe biyu na rana, Ajay gave Khaleesat enough time to rest, tayi bacci sosai ba kadan ba, kawai abinci ne taji bata son ci sai lemon kwali take sha kadai, kiris ya rage patient din Jay ya kare a hotel din, bai yi tunanin za su kai har rana suna hotel din ba don ma payment din kwana biyu yayi masu, Ajay ya ba Khaleesat Jacket dinsa ta saka don ita kadai ce bata taho da Jacket ba, ko da suka bar hotel din khaleesat taji ta samu karfin jikinta babu sauran stress a tattare da ita, amma suna isa inda za su shiga local paddle canoe din da zai kai su riverine area din da za su je Khaleesat taji kanta ya fara juya mata saboda ruwan da ta gani babu iyakarsa, iya su uku ne a Canoe din sai Canoeist dinsu, tun da suka fara tafiya Khaleesat ta rufe fuskarta a jikin Ajay cause she was so uncomfortable, ko kallon ruwan bata son yi, Ajay ya daga kai ya kalli Jay dake kallon ikon Allah, taɓe baki Jay yayi alamar suna da aiki, ya ciro Nosemask dinsa ya saka, Ajay ya ɗan yi murmushi ya rungumota jikinsa tayi lamo fuskarta a kirjinsa ta boye don kar ta dinga kallon ruwan, bayan wani lokaci da fara tafiyarsu Khaleesat ta ɗago kanta da sauri daga jikin Ajay, ya rikota tun kan yace komai ta fara kwararo masa amai a jiki don yaki saketa, tas ta amaye duk lemon da ta sha daxu, Ajay na kallonta da damuwa ya dinga yi mata sannu, Jay yace “Allah ya sauwake” Ko kallonsa Khaleesat bata yi ba, mai paddling din Canoe din ma sai sannu yake mata, Ajay ya cire shirt din jikinsa da aman ya taɓa ya rage iya singlet a jikinsa, ya fara goge mata jikinta da inda aman bai taɓa ba da rigar hannunsa, kallon Jay yayi, Jay ya dauke kai don kar ma ya sa ran zai basa Jacket din jikinsa, Ajay dai bai ce masa komai, murya can kasa Khaleesat tace “Kayi hakuri” Yana kallonta yace “It’s okay Jeeddah, are you feeling relieved now?” Ta gyada masa kai, ta fara kokarin cire jacket din jikinta zata basa ya saka, yayi kasa da murya yace “Don’t worry my love, I don’t want you to catch cold” Tayi shiru tana kallonsa, Jay dai wani direction yake kallo daban, amma zuciyarsa taki barin ya hana Ajay rigarsa don shi haushinsa sai da yace kar su taho da Khaleesat amma yana shakkar yi mata magana gashi duk sun ma fita wahala a hanya don babu abun haushi a tafiya da ya wuce tsaye tsaye a hanya, after some minutes Jay ya kasa daurewa ya cire Jacket din jikinsa ya ba Ajay. Daga karshe suka isa other side of the river bank, Jay ne ya fara sauka daga cikin Canoe din, sannan Ajay ma ya fita, yana stepping kafarsa kan soil din Abinsi mood dinsa ya so ya canza bayan wasu memories sun dawo masa birjik cikin kansa, hannu ya mika ma Khaleesat ta kama hannunsa sannan ta mike, da taimakonsa ta sauka daga cikin Canoe din tana bin kauyen da fishing ne major occupation dinsu da kallo, kauyen kewaye yake da ruwa ga kwale kwale masu yawa a bank din ruwa ta every direction, Ajay ya ciro nosemask dinsa ya saka, Khaleesat ta kallesa a hankali tace “Nima zan saka” Ya ciro wani mask din ya saka mata da kansa, tafiyar kusan minti sha biyar suka yi a kafa, duk inda suka bi kallonsu ake, Ajay yaki sauke Mask dinsa don wasu daga mutanen garin sun san shi, a haka suka iso karamin compound din Ozhi, sai a sannan Ajay ya sauke nosemask dinsa yana kallon yarinyar dake zaune kan tabarman kaba, yarinyar ta mike a hankali tana kallonsa babu ko kiftawa, mahaifiyarta dake fifita wuta a murhu ta saki maficin hannunta ita ma ta mike tsaye tana kallon Ajay da wani expression a fuskarta, da gudu yarinyar ta tafi ta fada jikinsa ta rungumesa, Jay ya dinga kallonsu, Ajay ya sauke idonsa, slowly hugging the girl in return, a hankali yace “Amisoh….” Hawaye suka fara zuba idon yarinyar, Khaleesat ta dauke idonta daga kallonsu, Ajay ya sake yarinyar yana kallon babanta da ya fito daga cikin hut dinsa yana kallonsa babu ko kiftawa.



