*ASM Bk2016*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*This page is dedicated to Hajiya Kubra (Mommy) Allah ya k’ara girma da daukaka da nisan kwana Amin🤲🥰*
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
………Yana shiga gidan Parlor ya nufa ganin ba kowa yasa ya wuce direct d’akinta tun kafin ma ya shiga ya jiyo shesshekar kukanta ya kai hannu ya d’aga labulen,tana zaune a k’arshen gado ta had’e kai da gwuiwa ga gashinta duk ya tarwatse, har ya shigo ya tsaya a tsakiyar d’akin yana kallonta bata sani ba goya hannuwan shi yay a k’irji idonshi akanta yama rasa mi zaice mata, a hankali k’amshin turaren shi ya fara kurd’ad’awa yana kai ma hancinta ziyara tun tana jinshi sama sama har ya cika mata hancin ta tabbatar k’amshin Ya Haisam ne hakan yasa ta d’ago a zabure idanunta suka sauka akanshi, zare ido tay tana kallonshi da idanuwanta da suka canja kala sunyi jawur gashi sun kankance sosae tsabar kuka duk a tunaninta sun ma tafi, lokaci guda ta kama kanta ganin kallon da yake mata ta fara jan jiki tana matsowa ta zo bakin gadon cikin hard’ewar murya tace “Y..ya ha.i..sam” shiru bai amsa ba yana cigaba da kallonta sai yan kame kame take tana kallonshi can yay sigh da wata irin murya yace “is this the Promise u ave made to me Zaraah” girgiza mashi kai tay tana yamutsa fuska kaman zata sa kuka,
“Why, why all dis Zaraah kina son in tafi da damuwa ne?” tun kafin ya rufe baki tafara girgiza mashi kai ganin yadda yake Maganar da damuwa kwance akan fuskarshi shiru yay yana kallonta cikin muryar kuka ta fara fad’in “Don Allah kayi hakuri Ya Haisam wllh kukan ne yake zuwa da kanshi nayi nayi ya daina yak’i” ta k’arasa tana had’iye kukan wani irin tausayinta ne ya kamashi slowly yay moving zuwa gaban gadon ya samu wuri can gefenta ya zauna da sauri ta sunkuyar da kanta don duk kamshin turaren shi ya cika hancinta shiru ya d’anyi yana kallonta can yafara Magana Slowly “am so sorry Zaraah I caused u pain am sorry” ya k’arasa da breaking voice ya d’an cije baki d’agowa tay ta kalleshi hawaye na sauka daga idonta da sauri ya kai hannu cikin pocket d’in rigar shi ya fiddo farin hanky ya mik’a mata ta amsa ta fara goge kwallan yana ta kallonta yama rasa tunanin da zaiyi ji yake kaman kar ya tafi ko don ta daina damuwa but he knows isn’t possible ita kuma ga exams d’inta kuma yasan ko taje ma in ta dawo still sai ta damu na wani lokaci saboda rashin shi sai faman dirzar ido take bata da niyyar tsayawa a hankali ya kai hannuwanshi ya kamo duka hannayenta ya sauke su k’asa suka kalli juna cikin ido picifically yace “kiyi Hakuri Zaraah am feeling almost d same thing am not happy zamu yi nisa da juna after being together for gud 3 years but we can still be together though we’re in distance right?” Jinjina mashi kai tay alamar eh, yace “ok ki daina damuwa pls” nan ma kai ta jinjina mashi shiru ya d’anyi sai kuma yace “tunda baki son rakani ba wani abu lokaci na tafiya zamuyi Magana” daga haka ya saki hannuwan nata ya mik’e har ya juya yaji ta kira sunanshi da disasshiyar murya ya juya ya kalleta ta saukko daga kan gadon ta mik’e a hankali tace “zan raka ka” fuska a d’an sake ya d’an bud’a ido yace “really?” Kai ta d’aga alamar eh d’an murmushi yay ya nufeta yace ina ribbom d’inta ta juya kan gado ta d’aukko tana kokarin sawa ya mik’a hannu ya amsa yay mata alamar ta duk’o da kan kallonshi tay cikin ido sai kuma a hankali ta duk’ar da kan ya matsa dab da ita ta yadda har kan nata ya d’an gogi broad chest d’inshi a nutse ya fara tattara gashin don ba kaman na Fanan bane nata yafi cika hannu sosae bayan ya gama ya d’ago da ita yana mata murmushi ita kuma tana mashi wani kallo a hankali ta furta “I will miss u Ya Handsome” kawae sai ya janyota yay hugging nata very tight ya d’aura ha6arshi saman gashinta, sosae itama ta k’ank’ameshi idonta a rufe wata kalan natsuwa taji tazo mata yayin da scent d’inshi ke k’ara narkar mata da zuciya tana cikin hakan taji cool voice d’inshi yana fadin “I will miss u too Zaraah, I will miss ur everything ur smile,jokes and d whole moment we spend together……” Yadda Maganar ke sauka acikin kunnanta yasa ta k’ara kankameshi yana jin yadda kirjinta ke sama da kasa saboda numfashin da take da sauri da sauri hakan kuma yasa Haisam d’in jin wani bak’on yanayi a tattara dashi wanda sam bai ta6a jin irin hakan ba a tare da Fanan, ita da bai ma jin komae in ya had’a jiki da ita don koda Maganar Aure ta shiga tsakaninsu tana nan a matsayin da ya d’auketa cikin ranshi sai daga baya ne data k’ara girma ya fara jin canji game da hakan shiyasa yake kokarin kiyayewa bai cika son suna had’a jiki da ita ba sai ta kama ita ce dae in zai biye mata to kullum suna manne, jin abun na k’aruwa sosae yasa da sauri ya d’agota don shi kanshi yasan bai kamata ya had’a jiki da ita ba har saida ya nemi tsari yay istigfari cikin ranshi, sam ta kasa kallonshi don da k’yar take ma bud’e idonta wani bak’on yanayi take ji a jikinta, shima juyar da kanshi yay gefe trying to get ease kafin ya kai hannu ya kamo hannunta ya kaita gaban mirror bai iya tanka mata ba da hannu yay Mata alamar ta gyara fuskarta ta kai hannu ta d’auki puff d’in powder tana goge fuskar idonta akan shi suna kallon juna ta cikin mirror d’in suna haka wayarshi ta fara ringing ya kai hannu cikin pocket d’in rigarsa ya fiddo yaga Hajiya ce ke kiran nasa yay picking yana d’auka tace mashi yana inane yasan dai jirgi bai jiran Mutum ko yace mata he’s on his way heading there d’aga haka yay cutting ya maida wayar Fatuu na kallonshi yace mata ina veil d’inta ta matsa wurin wardrobe ta ciro hijab tasa ya kama hannunta suka fita, back door ya bud’e mata da kanshi bayan sun fita ta shiga ta zauna ya rufe shi kuma ya bud’e gaban ya shiga ya ja Motar, a kai kai yake kai ido kan mirror ya kalleta wani lokacin su had’a ido wani lokacin kuma ta duk’e tana goge kwalla can ta d’ago kawae taga yana mik’o mata hanky kallonshi tay kafin ta mik’a hannu ta amsa, a hankali take kai hanky d’in fuskarta ta d’an goge kwallan in suka had’a ido dashi sai ta sadda kan kasa, basu d’au tsawon lokaci ba suka k’araso Airport bayan sun yi parking sun fito ya nufi inda su Hajiya suke Fatuu da Tk na bayanshi, Hajiya na ganinshi ta sha mur ganin Fatuu yasa bata dae ce mashi komae ba gwaggo ma tunda suka had’a ido da ita sau d’aya bata yarda sun k’ara ba don taga kallon da tay mata mai kaman harara Abbas kuwa sai murmushi yake mata a sanyaye ta gaishe dashi kafin ta nufi wurin Hajiya ta gaidata tana kallon fuskarta ta amsa kafin ta dafa shoulder d’inta tace “kiyi hakuri kinji Fateema ai ba an rabu ba kenan da zaki damu kanki har haka, dubi idanunki yadda suka kumbura kukan ya isa haka kinji” kai ta d’aga mata lokacin kuma aka fara sanarwa nan da mintuna biyar jirgi zai k’araso don haka matafiya su shirya Hajiya ta juya tana k’ara yin sallama dasu gwaggo da Abbas suka ce sai sun zo daga haka suka nufi cikin departure Haisam ya mik’a ma Abbas hannu suka yi sallama shima yace mashi sai yazo haka Tk da gwaggo duk suka yi mashi fatan a sauka lpy, juyawa yay side d’in Fatuu ya d’an kalleta for few seconds sai kuma ya tafi ba tare da ya ce mata komae ba har yayi kaman taku ukku zuwa hud’u yaji ta kira shi hakan yasa ya dakata ya juya nufo shi tay tana zuwa gaban shi ta mik’a mashi hanky d’inshi da ya bata a cikin Mota kaman bazai amsa ba sai kuma ya amsa ya juya yana niyyar cigaba da tafiya yaji Muryata tana fad’in “Thank u Sweetheart Ya Handsome, thank u for all dat u have done to me May Almighty Allah reward u Abundantly, ina rokon Allah ya dawwamar da kai cikin farinciki har abada kamar yadda kake sa bayinsa farinciki, Allah ya jibanci lamuranka ya baka y’ay’a wanda zasu ji k’an ka, Allah ya…..” Kasa k’arasawa tay ta duk’e a wurin tana wani irin kuka mai cin rai duk abun nan yana tsaye cak ba tare da ya juyo ba yana jin yadda take Maganar cikin breaking voice dake bayyana she’s in serious pain runtse idonshi yay can kuma ya bud’e yaci gaba da tafiyar saida zai shige wurin sannan ya dakata ya d’an juya suka had’a ido tana a durk’ushen sai kuka take can ya juya ya shige, kowa ta bashi tausayi har gwaggo saida jikinta yay sanyi ta sani sabo ba abunda bai sawa ba kamar su sabonsu na Musamman ne, Abbas ne ya nufeta ya duk’a ya kamo hannunta ta d’aga kai ta kalleshi tana gunjin kuka ya jinjina mata kai alamar ta mik’e, Mota ya nufa da ita ya bud’e baya yace ta shiga gwaggo ma ta bud’e d’ayar kopar ta shiga yace ma Tk ya taho da Jeep d’in yace to, tunda suka taho hanya take aikin kuka kanta na kan kafafunta ta rufe fuska Abbas sai bata hakuri yake har dae ta k’ule gwaggo ta fara surfa mata fad’a cikin harshen fulatanci Abbas na bata hak’uri duk da baisan mi take cewa ba amman daga ji yasan fad’a take mata, suna akan hanyar jirginsu Haisam d’in ya wuce, Allah sarki Ya Haisam d’in mu shikenan ya tafi wayyo Fatuu I feel ur pain ko baki son Haisam dole ne ki ji zafin tafiyarshi🥹, suna k’arasowa kopar gida gwaggo ta bud’e Motar bayan tayi ma Abbas godiya ta wuce gida abunta da k’yar ta iya bud’e Motar ta fita sakamakon k’afafunta da sukae mata nauyi sai faman shessheka take tana niyyar tafiya bayan ta rufe Motar Abbas ya bud’e ya fito har ta juya ya kira sunanta ta juyo da runannun idanunta ta kalleshi ba tare da ta amsa ba cikin muryar lallashi ya fara Magana,
“Am so sorry Zaraah, i know how are feeling but I want u to know Allah yana jarabtar bawa ba don baya son shi ba and if u’r destined for sadness there is always a reason all u need is to put ur trust in Allah, shine kadae mai maida abunda ake tunanin bai ta6a yuwuwa ya yuwu cikin tsananin sauki, so all I can say to u is kiyi HAKURI kiyi HAKURI” kai ta jinjina mashi tasa hannu tana goge kwallan ya kuma cewa “Da gaske baki son zuwa Abujan?” Da sauri ta d’aga mashi kai alamar eh, shiru ya d’an yi, ya gama fahimtar ta sosae yasan what she’s going through abune mai tsananin rad’ad’i a zuciya, sigh yay yace “ko in kawo maki Abdul ya taya ki zama kafin mu dawo tunda itama Grandma d’in naki zasu je tare ma zamu H,Zakeen yayi mun Magana” murya na rawa tace “a’a ka barshi shima ai yana son zuwa” shiru yay yana kallonta tabbas Abdul na son zuwa kullum sai yayi Maganar bikin Baba Zakee ya fiddo da sabbin kayan da aka d’inka mashi saboda bikin, can yace “is Ok zaki iya tafiya amman don Allah ki daina damuwa haka kinji nasan ba zai yuwu cikin sauki ba dole sai a hankali amman try ur possible best kiga kin cireta a ranki ki focusing kan karatunki ba kamar da final Exams dinku is approaching kar ki bari hakan yaja maki Matsala don O level is very important shine tushen kowane karatu Mutum ke son yi without O level u’r going no where” kai ta jinjina mashi yaci gaba “in kina da wani matsala kar kiji komae ki sanar dani H,zakee yace ya siya maki waya right?” Shiru ta d’anyi alamar tunani sai kuma ta girgiza mashi kai don ita dae tasan bai bata waya ba,
“Ok amman tabbas yace ya siya maki waya nasan zata zo hannunki so zan amshi phone no dinki sai mu rink’a communicating” kai ta d’aga mashi yace zata iya tafiya har ta juya taji muryarshi na fad’in ” _Destiny may be delayed but cannot be changed Mom Zaraah_” da sauri ta juya ta kalleshi taga yana sakin murmushi ya jinjina mata kai alamar tabbatar mata da abunda yace kafin yace “kar ki wasa da ADDU’A” daga haka ya koma cikin Motar yay mata alamar ta shiga gida kafin yaja kopar ya rufe ya tafi tana tsaye tana kallon bayan Motar har yay nisa sannan ta juya da gudu ta shige gida d’akinta ta nufa tana zuwa ta fad’a saman gado ta dasa sabon kuka abunda yafi damunta shine yadda Abbas ya fahimci abunda ke damunta amman Haisam bai fahimta ba, tun dae gwaggo na jan tsoki tana sambatun abu yak’i ci yak’i cinyewa sai kace an rabu kenan har dae ta saduda ta nufi d’akinta ta fara bata hakuri gudun kada kukan yaja mata wata matsalar, a jikinta ta rungumeta tana ta bata baki har ta fara sauka can ta d’agata tace suje tay wanka kota ji karfin jikinta ta d’aga mata kai, saida ta rakata har bakin toilet d’in sannan ta juyo tana girgiza kai da d’an murmushi kan fuskarta, sosae taji dad’in jikinta bayan tayi wankan ta zura doguwar riga tana gama shiryawa sai ga Haulat suka zauna kan gado tana kwalla take sanar da ita Ya Haisam ya tafi ya barta ita kanta Haulat saida taji ba dad’i hakuri taci gaba da bata ganin tana zubda kwalla.
ABUJA NIGERIA
(Wata School mate dina ta ce dai Abuja kiran Allah sai kace Macca🤣)
Tuni jirginsu yay landing har anje an daukkosu gaba d’aya sun hallara a tamfatsetsen Parlon gidan mai d’auke da sets d’in Sofas sun kai ukku kama daga Royal sofas, Leathers da sauransu gaba d’aya sun jigunu komae na falon mai k’ayatarwa ne a tsare yake akwae dining area mai d’auke da dining table mai seats sha biyu haka duk inda set d’in kujeru suke akwae kayan kallo wato duk inda Mutum ya zauna zaiyi kallonshi ba tare da wani ya takura ma wani ba akwae manya manyan windows da zaka ga harabar gidan sosae kana daga cikin falon haka akwae manyan kofofi da zaisu kai ka wasu k’ananun parlos d’in masu d’auke da bedrooms, daga gefe da gefen dining area wasu had’addun tagwayen bene ne da zasu kai ka sama ma’ana sun sa dining area d’in tsakiya su Kansu abun kallo ne gaba d’aya yanayi da tsaruwar falon kai kace ba a Nigeria bane, in nace zanyi bayanin komae na gidan to tabbas har ranar d’aurin auren Haisam d’in sai tazo ban gama ba don haka na barma mai karatu ya idasa fasalta gidan da kanshi, zaka yi mamakin irin kirkin mutanen dake rayuwa a gidan don sai ka d’auka zasu yi girman kai amman sam ba haka suke ba bala’in kirki ne dasu sam daular da suke ciki bata saka su girman kai ba Haisam ma dae misali ne ai, gaba d’aya sun baje sai hirar biki ake dama sun k’agara Haisam d’in yazo kullum sai sun kira Hajiya game da hakan sai tace shine ya tsaidasu da tuni sun taho, sai tsare tsarensu suke yayin da hankalin Haisam gabadaya ya tafi kan tunanin halin da Fatuu take ci don ba k’aramin karyar mashi da zuciya tay ba a Airport d’in nan hotonta yak’i barin zuciyarshi jefi jefi yake saka masu baki suna hakan har aka yi Magrib duk suka tashi don yin salla Haisam da sauran mazan harda Mahaifinsu suka nufi Masallaci dake gefen gidan kaman dae na gidan Hajiya shima kalan fentin gidan ne sai dae su sai sun hau Mota suke fita su je don ba hanya ta cikin gidan kuma tafiyace in ace suje a k’asa don kafin ma a fita daga harabar gidan har a shanye jikin gidan a isa Masallacin aikine, sai da suka yi har Isha sannan suka dawo lokacin kuma an gama shirya table duk suka hallara harda Saude tana gefen Hajiya saida Senator Alee yasa Haisam yay masu Addu’a kaman yadda suka saba duk in za’a ci Abinci sai yasa wani yayi Addu’a, a nutse suka fara ci bayan ya gama Addu’ar still tunanin Fatuu yake bai wani ci da yawa ba ya mik’e duk suka ce badae har ya k’oshi ba yace ehh Senator ya ta6e baki yace “Wato Son har yanzu baka cin Abinci sosae ko?” Hajiya tay karaf tace “bai kuwa ci ba don d’aga k’arfe ba da tuni shida muciya basu da maraba” duk aka sa dariya Senator Alee yace “to Ango ne dae kai u need to be eating more Food” nan ma dariyar akai su Jidderh na sussuna kai shidae d’an murmushin gefen baki yay ya juya ya fara hawa staircases da d’an gudu gudu cike da k’warewa Senator na fad’in ya dawo ya k’ara Abincin ya d’ago mashi hannu kawae, wai saman benen ma ma sha Allah, ko ina walwali ke tashi saboda hasken da k’ayatattun fitilun wurin ke saki su kansu sai Mutum yay kauyanci akansu, yana kaiwa k’arshe dakakkar kopar dake kallonshi ya tura ya shige, to jama’a gamu a wata Aljannar duniyar, had’addan Falo ne mai d’auke da leather chairs ruwan Madara fess dasu suma L-shape ne Carpet da Curtains suma duk ruwan Madara ne sai tarkacen kayan kallo dasu surround sound systems akwae frames masu kyau da hotuna, yana shiga bai tsaya falon ba bedroom ya wuce shima dae ya k’awatu da tsadaddun furniture kai kace d’akin wata yar gayun Amarya ne sam tsarin d’akin baida hayaniya ga Ac nata aiki, a bakin gado ya zauna ya fara k’ok’arin kiran Amadu kwatsam kafin yay sending kiran sai ga kiran Fanan ya shigo still yay yana kallon screen d’in har kiran ya katse yana tsinkewa wani ya sake shigowa he ave no option dole yay picking kiran don in ya k’i d’agawa ta kira taji yana waya bazata ji dad’i ba kuma tunda suka iso ta kira yace mata suyi waya anjima ko ba haka bama shi d’in ba mai wulakanci bane, waya suka shiga yi cike da shauki tun suna yi a zaune har ya gaji ya kwanta yana facing ceiling sosae suka 6ata lokaci suna wayar wanda yawanci kan dae Maganar bikinsu ne sai da ya nuna mata yana jin bacci sannan ta k’yaleshi saidae koda ya duba Agogo dare yayi sosae don sha d’aya ta kusa, kifa wayar yay saman cikinshi can kuma sai ya mik’e ya nufi toilet after some minutes ya fito sanye da bathrobe ya nufi press bayan ya gama shiryawa cikin sleeping dress ya nufi gado saida ya latsa switch hasken d’akin ya d’auke kafin ya kwanta kanshi saman pillow nan take zuciyarshi taci gaba da tariyo mashi yanayin Fatuu a Airport a hankali ya fara reminiscing old times tun ranar farkon had’uwarsu har zuwa yau wani wurin yay murmushi wani lokacin dariya wani sa’in ya girgiza kai can ya kai hannu ya d’aukko wayarshi ya shiga gallery duk wani hotonta dake a wayan saida ya kalla wani ma ko ita Fatun bata san dashi ba a haka bacci yay awon gaba dashi ba tare da ya fita daga images d’in ba wayar a saman cikinshi………..
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.