Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 2 Hausa Novel

 WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

                    TWO📍

        Fita tayi da sauri saboda tasan inta cigaba da tsayuwa komai zai iya faruwa….. 

Wayam yagani kamar wacce ta bace,sai kawai yabi iska da kallo yana mamakinta a ransa,yana kuma fadin duk addu’ar dayazo ranshi,gashi ko zaa kashe shi bazaice ga wani mugun abu dayagani a tattare da ita ba,saima perfect roundish-almond eyes daya gani,ajiyar zuciya ya sauke,beneath his breath yace “she’s indifferent!” sannan ya cigaba da lectures…..

          Da karfi ta bude back seat tashige,tanajin wani zazzabi na kamata meanwhile ranta na kara baci,itafa tsap saita hakura da school din gabadaya,dama ganin damanta ne harta maida hankali tana zuwa class,tunda tasan kano duniyannan ba ubanda ya isa yamata dole a komai,tsaki ta kara ja aranta tana bawa kanta hakuri,at the same time tana fadawa kanta this is a minor thing,ta kyaleshi kawai,saboda tasan in tasa a ranta toh wlh sai yaji a jikinshi…..

      Zira hannunta tayi tana kokarin zare car key din ganin beja motar ba,ai da sauri ya zare kafin hannunta ya karasa,a kidime yake cewa “I’m so sorry ma’am,I’m really sorry,let me drive you”…. Hannu ta kuma mika mishi alamun ya bata car key din…… Shiko ko marinshi zatayi ya gwammaci yayita bata hakuri harta hakura ta barshi yaja motar,dan yasan idan takarbi car key dinnan tashi ta kare…….. Marairaicewa ya sakeyi  ya hade hannunshi biyu alamun roko ya sake cewa“Please ma’am help my life,I’m extremely sorry,let me drive you”………. Janye hannunta tayi badan ta tausayamai ba kotaji wani abu a ranta saidan kawai batasan jayayya,kar kuma abinda ba ruwanshi ya shafeshi…….. Wani ajiyar zuciya ya sauke a fili  yana godewa Allah a ranshi,dan haryayi give up wlh,kawai dai yayi trying luck dinshi ne yayi insisting,sarai ya santa no nonsense woman ce!… Yaja motar a guje suka bar wajan………….

         Parking yayi a gaban Transcorp Hilton,ya fito da sauri ya bude mata yana mika mata jakarta daya zuba drugs din da suka tsaya suka siya dan jakarma a motar take barinta,karba tayi batace komai ba tashiga hotel din… A fifth floor lift din ya tsaya kamar yanda ta saita,tsayawa tayi bakin guest room 302,ta dauki key a jakarta ta bude tashiga da sallama chan ciki……… Kulle kofar tayi ta hau kan bed tana zuge jakar hannunta,ta dauki drugs din ciki,har zata rufe jakar sai kuma ta hango wayarta,wayarda sai tayi wata bata tabata ba,gashi ba wanda ya isa yace mata dan me?,kuma sarai indirect ana fadamata badai zaa fada straightforward bane,tabe baki tayi sannan ta zaro wayar,tana jujjuyata,tana kuma kiyasta wani abu a ranta,taji wasu na hira suna cewa anyi har 14 pro max,amma shine aka barta har saida taji a gari ita bata mallaketa ba!……. Sai tayi tsaki ta kunna 13 pro max din dake hannunta……. Tashi tayi ta nufi mini fridge din dake dakin while wayar na kunnuwa,ordinary bottle water ta dauka dan batasan abu me sanyi kwata kwata shiyasa ko connecting fridge din bata tabayi ba….. Glass cup ta hado dashi tana zuba ruwan a ciki ta balli drugs din ta cire niqab din ta watsa a baki tana lumshe ido,she’s so addicted da intayi kwana daya bata sha ba gabadaya saita fita hayyacinta,ta sani sarai tana abusing drugs,to amma ya zatayi da abunda ta tashi taganta tanayi for years?………

       Ringing din wayarta ce yasa ta dan bude ido,shiyasa fa bata san kunnawa saboda batasan damuwa,Shikuma dama yayi connect da wayarsa duk sanda ta kunna waya sai anyi alerting dinsa kawai sai dai taga kiransa…….

 Itafa yanzunma ba dauka zatayi ba(She’s so confused on how he gets to know anytime her phone is on),saida aka kira so bakwai sannan aka hakura,sai sannan ta dago ta kunna data,tana kunna data video call ya shigo,kamar karta dauka sai kuma wani tinani ya fado mata kawai ta danna answer button……

     Kallonta yake with so much adoration tin daga kan kwantaccen gashin gaban goshinta zuwa perfectly curved girarta,da lumsassun breathtaking idanunta dazai iya cewa tinda yake da ita befi sau biyu ya taba ganin ta waresu sosai ba,dukda kasancewarta mutum mai kallon mutum kai tsaye saidai idanun nata ne zaka gansu a lumshe koda yaushe,a hankali ya sauko kan pretty button nose dinta,ya tafi kan small full lips dinta yana kissima wani abu arai,sai kuma yaji gabanshi yayi mugun faduwa……. A hankali ya furta “Astagfirullah!”……. Jin hakan yasa ta dago tana mishi kallonnan nata kasa kasa da tasan yana birkitashi kuma yana mishi warning akan mata kallon kurillan nan,ai ko da sauri yayi lowering gaze dinshi ya fara kame kame…….

      “Please stop looking at me that way,it’s driving me insane” yayi breaking silence din da kyar,janye idonta tayi tinda taga ya horu yanda takeso……….

“Wifey,I miss you so much!”  Ta sake tsintar muryarshi yana fada…. Still bata kulashi ba,kuma dama yasan sai yayi dagaske kafin tace wani abu…

“Haba my knight in shining amour,pls say something mana uhm?,your hubby has miss everything about you so much,ko saina miki kuka zakimin magana?” Ya fada looking so pitious yana bin dakin da kallo….

“I love you no matter what you do,but do you have to do so much?Anyways let’s be weird and wonderful together my weirdo?”….. Ya fada yana bin hijab din jikinta da kallo…….

Duk wannan zubar dayake ko dagowa batayi ba bare yasa ran zata kulashi,wani abu ya tina yayi banging study desk din daya ajye system akai yace “Damn it!

   “Assalamu alaikum”….. Ya fada kamar wani mufti,sai a lokacin ta dago tace “wa alaikassalam” cikin wani irin lukewarm melodious voice me dadin sauraro……. “Sorry ustazah(lol),ashe banyi sallama ba,yanzu duk flows dina sun tafi a banza kenan?”….

“How’re you?” Ta fada nonchalantly….. “I’m not fine at all”….. “And who cares?”…….. Murmushi yayi saboda ta tina mishi da wani lyrics na wakar ‘Under the influence’ by  Chris Brown,a hankali yafara miming line din cikin gentle masculine voice dinshi“And you be like baby who cares?,but I know you care,bring it over to my place…….”Ya isa!”……. “Kai why did you stop me,harfa na shiga shauki”…. “Hmmm “ tace tana tina dalilin picking call dinshi……. 

“ To kicire hijab din mana kisha iska tinda dai ba wanda ze kallemin ke yanzu,“ Ya fada duk da yasan idan ta cire hijab dinma tsap zai iya suma,amma still ya gwammaci ta cire ya kalleta,inyaso sai ya suman😂……

“Meye damuwarka”?ta fada a hassale,amma sai mgnr ta fito a hankali sbd yanayin sanyin muryarta ga abunda tasha ya fara mata aiki….. “Allah ya huci zuciyarki wifey”………..

“14 pro max” yaji ta fada bayan dan wani silence kadan,sai ya dinga wondering menene wannan,gashi yasan inya tambayeta bazata fada ba,Chan kuma sai ya gano….. “Sorry wifey,inata kokarin reaching dinki for the past one month akan hakan,na siya miki ma,I didn’t send it because baki bani permission ba,kar a kawo ki dawo dashi,expect it tomorrow……

   “I need 5m today!” ta fada ba tareda tabashi amsar maganar wayar ba” zaro ido yayi yana mamakin me zatayi da kudin,shi ba kudin yakeji ba,aa me zatayi dashi……. “Okay amma saidai in turo miki 1m kinga baa mana salary ba yanzu,gashi nayi lots of things recently,but I promise you ana mana salary,you’re my first budget,kinsan I always put you first my reality”…..  Tabe baki tayi tace “ka tambayi ubanka mana!”…..Sai yaji wani abu yadakeshi har cikin kwakwalwarsa,amma ya daure yace…“Oh yeah,your wish is my command ma’am,besides you promise to pay me a visit over here,yaushe zakizo?”…… “Duk sanda naga dama!”….. Ta fada a gadarance, badan sanyin murya da Allah ya mata ba da yace she’s the perfect definition of ‘if rude and arrogant was a person’!,amma waya isa ya fada to her face,besides he loves her flaws ma!……….

    “Amma dai baa hotel dinnan zaki kwana ba ko habibty?” Ya fadi abinda ke ranshi tin dazu kamar me tsoron magana……. Ko kulashi batayi ba,ya kara cewa “kinsan people are so judgemental!”….. Kallon da bayaso ta mishi tace “Stop going through corners and say the hell that’s on your mind ,kaji na taba ce maka niba yar iska bace?,ko nayi denying shaye shayen da shima indirectly kace inayi?toh sai akayi yaya dan anyi judging dina,who cares?,just go to hell!”Ta fada tana cutting call din dan already taji idanunta sun fara giving up,dama tayi expecting hakan,tana cutting call din ko wani nannayyen bacci ya kwashe ta…… Shiko sai kiranta yake taki picking,chan ya fara jera mata messages,ko Allah zaisa tayi reply,still no reply,ajiyar zuciya ya dinga saukewa a jajjere,kuma mamakinta na kara kasheshi,be taba ganin mutum da abu kadan da baikai ya kawo ba yakesa shi zama so pissed off irinta,duk wayar da zasuyi ko haduwar da zasuyi saiya dinga lura da abinda ze fada kawai sbd karsuyi fada,amma ina dole saitayi picking offense….. Hannunsa ya dafe daidai saitin zuciyarshi yace”Allah dai yasa bakece ajalina ba Fatimah Zainab!”……. 

       “Dad it’s so urgent!”…… “It’s alright,zan turo maka yanzu”…., “Thank you dad”….. Befi 5mins ko da sauke wayar ba yaji alert,murmushi yayi tina irin karyar daya gama masa yanzu……. A take ya tura mata,sai kuma ya kuma tura mata small msg saying “You make things hard,but I still love you hard!”……… Itako bata masan abunda akeba tanata baccinta abunta…..

   A hankali ya fada duniyar tinaninta da abubuwan da har yau ya kasa samun amsa akai,wato “WACECE ITA?”,yana fatan Allah ya bashin aran rai haryasan wacece ita?,sai kuma ya koma tinanin ranar daya fara ganinta,ranar da baze taba mantawa ba……….

            

                 Flashback 

A gajiye ya shigo gurin 1am na dare,dawowanshi kenan daga UK,ya kawo musu surprise visit,yanda kawai kowa saidai ya ganshi da safe,murda kofar main parlor yayi,by luck saiya samu kofar a bude duk da beyi expecting ba,karar shara yaji daga far end din parlour,bin ko ina ya farayi da kallo harya hango ta…… “Hasbunallahu wa ni’imal wakeel,fata barakallahu ahsanul khaliqin,tsarki ya tabbata ga ubangijin daya tsara wannan halitta!”ya fada yana binta da kallo,kamar yanda take binsa da kallo……Wayam kuma sai yaga ba kowa,kamar wacce ta bace,kalle kalle ya farayi yana neman inda tabi amma bega ko alamun giftawar mutum ba,sai kawai yaji wani tsoro ya kamashi,yace kodai gamo yayi ne sbd shidai yaga halittar da duk wani lafiyayyan namiji bazai mata kallo daya ya dauke kai ba,saiya faro karanto duk adduar da tazo ranshi,daga wannan rana,daga wannan lokacin kuma bai kara gane kanshi a duk wani abu daya shafeta ba,ya sadaukar mata da komai nashi,harda rayuwarshi,take janshi kamar rakumi da akala…… Girgiza kai yayi ya cigaba da tinanin abinda ya wakana a ranar, a tsorace ya karasa cikin bedroom still yana ganinta a idonsa,yana cigaba da addu’a inma gamon yayi toh……. Wayarshi ce tafara ringing ta katseshi daga duniyar tinanin daya lula 

     End of flashback

      

 Da sassarfa ya fito daga cikin motarshi,ya fara tafiya da sauri saboda flight dinshi 7:30am gashi haryaga 7 tayi,gashi in be bar garinnan yau ba toh akwai matsala,saura kadan suyi karo da ita,ta maza tayi gefe tana binshi da wani mugun kallo ta cikin niqab din……… Kallonta kawai yadingayi yana mamakin me tazoyi a hotel,dan shi Allah ya bashi baiwar gane mutum,be wani ganta jiyaba amma zai iya rantsewa itace,bama wannan ba ance in zaka sha giya kasha ta dubu,toh mena boye boye bayan kiri kiri mutum yazo hotel,kuma sai yayi shirin ustazai?…… “Hmmm green snake under the green grasses”…… Be gama tinani ba yaji an badeshi da kura,sai kuma ya nemeta ya rasa,a kidime yabi motar da kallo,if he was not mistaken motarnan achan karshe ya hangota,toh how comes ace hartaje tashige anja motar? Impossible!,kodai kuma bacewa tayi? Dan baze manta da encounter dinsu na jiya ba,kawai yaga wayam,”toh kodai aljana ce?”  Ya fada yana kara bin hanyar da kallo…… Hanyar ya kuma bi da kallo yana karanto ayatul-kursiyyu a ranshi,sai kuma ya fara tambayar kanshi toh“WACECE ITA?”

Toh jamaa kubiyoni a sannu dan sanin WACECE ITA?…. Meanwhile bacewa tayi ko  motar tashige?

      ~Unique Barakancy~

Back to top button