Uncategorized

Macijine Shi Page 27-28 Hausa Novel

Na mammy kabeer

Elegant online writers📚📚
Free book 
Page 27/28
________________Tafiya suke cikin sararin samani,yayin da Fattu ke ruƙunkume da Adeeb jikinta naci gaba da rawa,kuma har lokacin idanunta akulle suke.
Ɗan juyowa Adeeb yayi yana mai kallonta ,shi mamakin tsoro irin na fattu yake,sam baiga abun tsoro ahawa jirgi ba,dubi yadda ta wani uzzurawa kanta,ko idanu ta kasa buɗe wa.
Ni kuwa nace malam Adeeb fattu fa ko ganin jirgi baya taɓa yi ba ,bare ta hau,ai dole ta shiga cikin cakwakiya,akaranta na farko.
Kallon fuskarta Adeeb keyi kamar bai taɓa ganin taba,haka kawai yake jin wani bakon al’amari tare dashi, jin yadda fattu ta ruƙunƙumeshin nan ,sai yake jin hakan yayi masa daɗi sosai,saidai yana tsoron abinda zuciya da gangar jikin sa ke ɓuƙatar aikatawa,idanu ya kirawo lips ɗinta ƙuri,cikin wani irin mugun son ya sunbacesu,gabansa sai bugawa yake,har wani lasar lips ɗin da yake ,yana hasko yadda zai sunbaci lips ɗin fattun.iyakar ƙokari Adeeb yayi dan hana kansa aikata abinda zuciyarsa ke tsananin muradi, amma ya kasa,dan jinsa yayi gaba ɗaya yanayinsa ya sauya ,ahankali cikin mugun son isar da saƙon zuciyarsa  ya nufi ɗan bakin  na fattu, har wani rawa bakinsa keyi,
Yana gan da kai bakin nasa cikin nata ne ,fattu tayi waral!da idanunta,ma’ana ta buɗe idanun nata ba zato ba tsammani,karaf kuwa idanunsa ya sarƙe dana juna,da sauri Adeeb ya runtse idanunsa tare da kawar da kansa can gefe,saidai bai daga daga rankwafowar da yayi ba,jikinsa gaba daya yana manne dana fattun,wani irin abu yakeji mai kama da mayen karfe ,yana fusgarsa zuwa ga aiwatar da burinsa, kiss fa only kiss Adeeb you can do it ,dan ka samawa kanka  mafita daga yanayin da kake ciki.
Zuciyar Adeeb ke bashi wannan shawarar,ahankali ya ƙara bude idanunsa wanda suka fara sauya yanayi daga fari tas zuwa wani irin sirkin jaaa da wani ratsin pink.
Kallon fattu yayi wacce itama shi take kallo tana wani rarraba idanu,Ita dai batasan me yake nufi ba,taga ya kwanto jikinta ne ,ƙila ahaka ake tafiyar ,amma kuma me yasami idanunsa haka,idan bata mantaba ,yanayin da idanunsa ya shiga yanzu,kusan kalar da idanunsa yake ne lokacin da yake macijinsa, kodai macijin zai ƙara zama ne?na shiga uku na idan yazama maciji yanzu yazanyi?ina zamuje cikin wannan halittar mai kama da kifi?nan da nan tsoro ya kama fattu ƙara rikoshi tayi sosai cikin muryar tsoro tace “Hamma menene?dan Allah karka ƙara zama maciji kai kadai nake dashi,idan ka koma maciji ya zanyi,waye zai fitar dani daga wannan cikin kifin da muka shi?ta faɗa cikin salon shagwaɓa taba mai zubda hawaye.
Da ƙarfin gaske Adeeb ya runtse idanunsa, yana mai furta “ya Salam wannan yarinyar zata kashe ni fa”dan yanayin yadda tayi maganar ba ƙaramin tasiri yayi akan Adeeb ba,hakan saiya ƙara masa jin wani iri ajikinsa,gani yake kamar da gangan tayi hakan ma.
Kansa banda juyawa ba abinda yake,yayinda zuciyarsa ke ta bashi shawarar kawai ya sunbaci fattun .cikin rashin sanin abinyi Adeeb ya ɗora bakinsa kan na fattu,ba tare da ɓata lokaciba ya fara kissing ɗinta kamar ya sami lolli pop,zaro idanu fattu tayi cike da tsantsar tsoro da mamaki,meye hakan kuma Hamma keyi?me yasa yake shan bakina?kodai shima yana cinye mutane ne?shikenan Ni fattu naga ta kaina ,wayyo Allah na,daga cikin fiki saikuma shanye baki?nan da nan fattu ta fara rawar jiki fiye da da,cikin zuciyarta tana take ta faman haure haure da ƙoƙarin ture Adeeb,amma kuma azahiri ta kasa koda ɗaga dan yatsanta ne bare tayi yunƙurin kwacewa.
Shikuwa Adeeb ɗora bakinsa kan bakin fattu keda wuya ,gaba ɗaya haddarsa ta zube,tuni ya nemi inda kansa yake ya rasa,kissing ɗin bakin fattu kawai yake kamar Mayunwacin zaki.
Kusan minti shida zuwa bakwai Adeeb na abu ɗaya,cikin kwancewar kai da rasa tunani,fattu kuwa tun tana jin abinda yakeyi kamar waiwayi yake mata har ta fara jin wani azababben zafi da raɗaɗi ,dan ji tayi kamar zai tsinke mata lips,tuni ta fara kuka tana ɗan bubbuga damtsen hannunsa.
Hankali da tunanin Adeeb ne suka dawo jikinsa lokaci ɗaya,kuma ya fahimci abinda yake aikatawa da Fattun, cikin wata irin azama da hanzari ya  dago kansa tare da cire bakinsa daga cikin na fattun.
Da sauri ya zareta daga jikinsa yana mai mikewa cikin hanzari ya nufi wani daki,yana layi kamar ɗan maye.
Yana shiga ɗakin ya kulle ƙofar tare da zamewa ajikin ƙofar ya zauna dabas. Dafe kansa yayi yana mai runtse idanunsa.”meye hakan ?me na aikata kenan?wane irin kallo yarinyar zata rinƙa min yanzu?ohh my God ,why Adeeb !why am I losing my control over her?”Adeeb ya faɗa Afili yana  mai tsakumo sukar kansa wacce ke kwance lub-lub.
“Me ka aikata ba dai-dai ba Adeeb bakayi laifin komai ba ,kuma ba abin ƙi kayi ba just colm down”wani sashe na zuciyar Adeeb ne ke sanar dashi wannan maganar cikin yanayin rarrashi.
Ahankali ya sauƙe wata ƙaƙkarfar ajiyar zuciya yana mai rarrafawa ya kwanta akan wani ƙayataccen gado dake cikin ɗakin.kwanciyar rigingine yayi tare da kumshe idanunsa.ba abinda ke masa gizo sai moment ɗin daya kasance cikinsa yanzu nan.tabbas bai taɓa jinsa cikin wata ni’imtacciyar rayuwa makaman iyar wadda ya fito daga cikinta ba yanzu,wannan yarinyar da yake mata kallon baby he can’t imagine ace wai just kissing ɗin ta zai sanya shi cikin wannan yanayin ba.
Kusan minti goma Adeeb ya ɗauka a kwance yana ta saƙa da warwara,gaba ɗaya ya kawowa kansa matsala,yana zaman zamansa ,yanzu inbanda amsawa ba abinda mararsa keyi.
Tsaki yayi akaro na barkatai kafin ya mike cikin ƙarfin hali ya buɗe wata ƙofa ya shiga, wanka yayi ya tsarkake jikinsa kafin ya fito sanye da wata jallabiya, danaga ya buɗe wani guri ya zarota.
Zama yayi abakin gadon daya kwanta dazu,yana tunani,me Yakamata yayi yanzu? Gara kawai ya fuske ya fita,idan ba haka ba yarinyar zata rinka masa wani iri. Kallo ne.dan haka mikewa yayi tare da ɗaure fuskarsa sosai kafin ya fito  daga ɗakin.
Fattu kuwa lokacin da Adeeb ya zareta daga jikinsa ,zama tayi atsorace kan kujerar jirgin tare da ƙanƙame jikinta,wani irin abu yakeji ajikin nata wanda bata san menene ba,gefe guda kuma lips ɗin ta dataji yana mata zugi,hannu ta kai tare da taɓa lips ɗin ta ,aikuwa jinsa tayi yayi tauri gurin,alamun ya kumbura kenan.
Hannu ta sanya tare da share hawaye ta ,sannan ta kira kanta akan cinyarta tana kuka. Ita sam batasan meye hakan da Hamma yayi mata ke nufi ba,kuma gaba ɗaya jikinta yayi wani irin ,sam bata jin ƙarfi ajikinta,gashi har lokaci ji take kamar bakin Hamma nata yana cikin nata bakin.tana cikin wannan halin ne taji buɗe kofarsa .
Firgigit tayi tare da zabura tana kallon inda taji ƙarar.haɗa ido sukayi da Hamma nata kallonsa take ƙuri ,ganin har kaya ma ya canja ,ko a ina ya sami kayan oho”
Shikuwa Adeeb ganin sun haɗa idanu ya wani galla mata harara yana nufar kujerar dake dayan bangaren.
Binsa da kallo fattu tayi tana mai son zuwa inda yake , amma tana tsoron yadda taga ya haɗe fuska.
Ɗan juyowa Adeeb yayi jin cewar idanun fattu na kansa.
Harara ya ƙara zabga mata cikin basarwa yace ” karki cinyeni da ido fa,bayan kin gama cinyemin baki”ya faɗa yana saurin kawar da kansa,dan shi kansa saida yaji kunyar abinda ya faɗa.tunda yasan shine marar gaskiya .
Fattu kuwa shiru tayi tana tunani,yaushe ta cinye masa bakin?kodai hankalin mutum yana gushewane idan yana cikin wannan abun,har yayi abu bai sani ba.dago kai tayi tana mai kallon Adeeb kafin cikin muryar mamaki tace “Hamma to meyasa na cinye maka bakin?kuma amma ai naga ga bakinka anan ajikinka, saidai ma ni nawa bakin dake min zafi ” fattu ta faɗa cike da mamaki.
Dariya ce taso kama Adeeb amma ya manne sannan ya kalleta yace” inaga kina da aljanu ko?haka kawai ki ka kama shamin baki kamar kin Sami sweet , shine zakice min  bakinki na miki ciwo?
“Na shiga ukuna Ni fattu Wllh Hamma bansan nayi ba ,nima kawai ganinki nayi kana shamin bakina kagani nan gurin ma ya kumbura ciwo yakemin”fattu ta faɗa tana ɗan turo kanta tare da nuna masa lips ɗinta na ƙasa wanda ya tasa.
Kallon lips ɗin Adeeb yayi cike da  jinjinawa wauta irinta fattu,sam bata da wayo ko kaɗan,kafin yace “maganinki ai garin don banzarki kika kuwa kanki ciwo ,Ni ba ruwana, kuma saikin faɗamin inda kika koyi wannan abunda kikayimin”Adeeb ya faɗa yana hararar fattu.
Allah Sarki fattu kuwa tuni idanunta sun kawo ruwa,marairaicewa tayi tana mai juya kai,”Ayya Hamma  nisa ba mayya ba ina zanyi wannan aikin mayyun,wllh bansan nayi maka ba dan Allah kayi haƙuri,nima bansan menene hakan yake nufi ba,amma idan kaji haushi ka rama kawai”fattu ta faɗa tana mai shashsheƙar kuka tare da goge wahaye,tsakani da Allah ita ina tasan ma tayi masa wannan abun,ita ba mayyaba ba komai ba ina ita ina shan bakin wani,ai ƙazantane ma wannan.
Lallai ma yarinyar nan wato shine maye kenan ?hmmmm zakiyi bayanin maye.Adeeb ya faɗa cikin ransa yana mai jingina kansa da jikin kujera,dan sosai yaji kansa na ciwo wanan doguwar maganar da yayi. 
Bai ƙara cewa komai ba sai kumshe idanunsa da yayi ya jingina jikin kujerar,ba abinda yake gani sai lips ɗinsa cikin bakin fattu,ahankali yake sakin murmushi, ta gefen bakinsa,haƙiƙa al’amarin yayi masa daɗi sosai .
Fattu kuwa ganin ya lunshe idanunsa yasa ta ɗan juya ta kalli window.
Kan bala’i me zata fani,?gani tayi kamar ta saka hannunta ta kamo gajimare ,kuma saitaga kamar asama suke.
Ɗan Dada leƙa kanta tayi sosai,yadda zata hango da gaske a sama suke ko a ƙasa,aikuwa wllh asaman suke,hana wani wawan ihu da fattu ta kurma tare da buga tsalle ta fito daga kan kujerar nan tayi kan Adeeb,ba  Adeeb  kadai ba ,hatta tareeƙ saida ya jiyo ihun fattu.
Arazane Adeeb daya lula duniyar sa ta nishaɗi ya buɗe ido tare da mikewa tsaye cikin tsoro,kawai saijin fattu yayi ta fado kansa tana ihu”wayyo Allah na Ni fattu na shiga ukuna ,Hamma ka taimakeni,wllh duniyar sama suke tafiya ,dama saida nace bazan shiga cikin wannan  kifin ba  amma saboda mugunta ka shigo dani gashinan sai sama akeyi damu, wayyo Allah Hamma ka fitar dani daga nan wayyo baffa an,e….a.yyy.y..oooo ga….ji…immarr,sai kawai ta tafi luuuu tayi baya zata faɗi.alamun ta suma.
Da sauri Adeeb ya dariya zuwa jikinsa,kumatunta yake ɗan bugawa yana faɗin”hey! hey!! wake up  HULWA wake up please,Adeeb ya faɗa cikin mugun damuwa ,komawa yayi ya zauna tare da riƙe ta ahannunsa, dan bubbuga kumatunta yake yana kiran HULWA !HULWA,amma ina HULWA kam tayi kisan zango.
Gefensa ya danna wata yar jar danja ,saiga wata ƙaramar ƙora ta buɗe ,ruwane da lemuka kala kala aciki da alamu dai fridge me,robar ruwan ya ɗauko tare da budewa,Ahankali yake tattara mata ruwan yana shafawa akan fuskarta amma ko motsi batayi ba.
Hankalinsa yayi mugun tashi,sosai hannunsa ya kai saitin zuciyarta ya taɓa,da sauri kuma ya zare hannun nashi,sakamakon karo da yaci da tudun ƙirjin fattu.
Ɗagota yayi tare da ɗora bakinsa kan nata ,sannan ya toshe hancinta,ya fara hura mata iska ,amma nan ma shiru,bayi motsiba,
Cikin mugun tashin hankali Adeeb ya ƙanƙame fattu ajikinsa yana faɗin “AM sorry HULWA Please wake up  ” ya faɗa yana mai kara ƙankameta ajikinsa.nan da nan idanunsa suka fara rikiɗewa zuwa kaloli daban daban ,wani irin huci yake yana zazzage idanu jikinsa ya kama bari.idan kaga Adeeb a wanna lokacin tabbas zaka shiga cikin kuɗu da tsantsar tsoro ,dan gaba ɗaya kamaninsa sun sauya. Shiba mutum ba Shiba aljan ba.
Cikin wanan halin suka sami isowa Misra,kai tsaye wani guest haose ɗin Adeeb na sirri Tareeƙ ya nufa ,suna sauka kuwa ,Adeeb ya kinkimo fattu da gudu yake sauka akan jirgin,kai tsaye yana zuwa jikin ƙofar ya fara daddanna wasu nonbobi jikin wata ƴar na’ura,cikin second kofar ta fara budewa tana faɗin well come back prince Adeeb Muhammad Ashraf , long time no see” kota kanta baibiba yayi cikin gidan da gudu,kai tsaye wani daki ya shiga ,yana zuwa bai jira wata wata ba daddanna wani guri tare da shigewa cikin wani ɗan banzan haɗaɗden  jacuzy  mai matuƙar girma da kyau,ruwane ya fara zubowa daga samansu, mai sanyi sosai,wanda idan haka kawai aka zubawa mutum ruwan  nan tabbas sai yayi jinya. 
Bubbuga kumatun fattu yaci gaba dayi yana kiran sunanta”HULWA ! HULWA!! HULWA!!! Har sau uku,Ahankali fattu ta fara bude idanunta tana lumshewa, kafin ta buɗe su duka, da sauri kuma ta ƙankame Adeeb tana mai cewa”dan Allah Hamma kafitar dani dana cikin kifin na wllh tsoro nakeji,Hamma, fattu ta faɗa tana mai rawar jiki.
Janyota Adeeb yayi zuwa jikinsa yana mai sakin wata kakkarfar ajiyar zuciya,”AM sorry HULWA ba abinda zai sameki ina tare da ke ,Please karki ƙara suma irin haka,saura kaɗan zuciyata ta buga” ya faɗa cikin rashin sanin abinda yake faɗi.
” Hamma mufita dan Allah” fattu ta sake faɗa.
Ahankali Adeeb ya riƙe kumatun fattu yana kallonta kafin yace “ki nutsu HULWA ba acikin jirgin muke ba yanzu,mun fita kalli kigani we are in toilet now ,bazan taɓa barin wani abu ya samekiba ,domin kuɗin mallakina ce kuma amanata, sannan ma….saikuma yayi shiru ,tare da cire hannunsa daga kan fuskar ta,fitowa yayi daga cikin ruwan ,sannan ya kamo hannunta ya fito da ita ,sai rawar sanyi yake,wani ɗaki ya kaita tare da zaunar da ita akan wani makeken gado,a baidamu da yadda jikinta ke jiƙe ba,wani ƙaton bargo ya dauko ya lulluɓa mata,sannan ya nufi jikin wani bango,nidai naga ya danna wani guri,kawai naga bango Ya dare,kaya sun bayyana.ehe mana bango Ya dare zance,tunda idan ka kalli gurin bazaka taba tsammanin akwai wata ƙofa dazata bude ajikinsa ba.
Wasu kaya naga ya dauko masu kama dana sanyi riga da wando sannan. Ya dawo kusa da fattu da ke binsa da kallo yace “kisa wannan kayan ,kinji,zanje in shirya nima yanzu zan dawo ” ya faɗa yana mika mata kayan.
Karba tayi cikin rawar hannu tana mai binsa da  kallo harya fice daga ɗakin.
Bin dakin fattu tayi da kallo,ikon Allah wai nan ɗin ɗakin mutum ne ,saikace wanda aka tattaro duk kayan jin daɗin duniya aka ajiye aciki. 
Ahankali ta mike ta cire kayan jikinta sannan ta sanya riga da wando da Adeeb ya bata,kayan sunyi mata kyau sosai,saidai wando yayi mata tsayi rigar ma haka,kasancewar Adeeb dogone sosai,hakan yasa rigar ta sauƙo ta rufe mata manyan mazaunanta.sanna kuma rigar tana da hula,hmmmmm nan da nan fattu ta koma wata irin ƴar balarabiyar nan tayi mugun kyau cikin kayan .
Kayan data cire ɗin ta dauka tare da rikews ahannunta tana tsaye ,tana waige waige kallo ɗaya zaka mata kasan afirgice take.
Bude ɗakin Adeeb yayi bayan yayi noking yaji shiru,
“Masha Allah ” shine abinda Adeeb ya iya faɗi lokacin da yayi arba da fattu cikin kayan nan.
Shima yana sanye da wata farar jallabiya ajikinsa da hirami akansa.yayi kyau sosai cikin shigar tasu ta larabawa.
Cikin ɗakin ya nufa yana mai jure fattu da idanu,ita kuwa kanta na ƙasa,riƙe da jiƙaƙkun kayanta.
Cikin wata irin murya mai kama da mutum na jin barci Adeeb yace “Hulwa” 
Ahankali fattu ta daga kanta tana kallon bayan Adeeb ɗin dan gani ta ina hulwar zata fito…..
Muje zuwa masu karatu,
Mrs babi ce💘💘💘

Back to top button