Hausa novels

Zakuna Biyar Page 33 By Princess Teema

Duba saƙon Aryan ya fara yi, a daidai lokacin guru ya shigo, ya gama shirinsa cikin pj’s milk color, gaban nasa computer ya zauna tare da kunnata. Nashi saƙon ya fara dubawa, sai da suka gama suka ɗago kai a kan Vir dake pressing wayansa, ya ɗauke hankalinsa daga kansu, Aryan ne ya ce. “Bro wannan ɓangaren aikinka ne, ya za’ayi hakan ta kasance? Dik wani fitina kenan daga WS ya fito? Su ne ke shirya komai?”. Ɗago fararen idanunsa Vir ya yi, irin kallon ƙasan nan yai masu kafin ya ajiye wayansa a gefen pool da kafafunsa ke ciki, yana da sanyin murya sosai, daga yadda yake magana zaku san mutumun ne dake da natsuwa sosai, baya son hayaniya kamar dai IRON FIST ɗin.”Kwarai, sune matsalar duniya bakiɗaya, in har muna son gyara, to dole mu fara tarwatsasu, dik wani ta’addanci da kake gani a Avaris ɗaukar nauyinsa ake yi, ka manta karfin gwamnati ne?”…… Kai Aryan ya girgiza alamar a’a. Cigaba Vir ya yi da cewa. “A irin karfi da gwamnati ke da shi ta’addanci bai isa ya yi 24 hours a ƙasa basu tarwatsa shi ba, musamman ƙasa irin Avaris, kasar dake da komai, dik wani abin da ake nema suna da shi, ban taɓa ganin ƙasar da ALLAH yake sonsu irin wannan ƙasa ba, har mamaki abin yake bani wani lokaci”. One after the other words ɗinsa yake fita cikin natsuwa kamar Lion ne yake magana.Guru ne ya amsa da. “Gaskiya ALLAH yana sonsu fiye da yadda ake tinani, ba dan haka ba shirin da aka yi a kansu wlh da basu yi saura a duniya ba, amma dik abin da aka shirya masu sai ALLAH ya basu kofar kaucewa, kaɗan ne yake samunsu”….. Aryan ya tari numfashinsa da cewa. “Kuma a haka basa godewa ALLAH ba, kullum suna cikin complain, da sun san abubuwan da ake shirya masu wlh da sun tabbata suna godewa ALLAH”. Guru ya cigaba da cewa. “Suna da man fetur wanda shi ne yafi sanuwa a duniya matsayin karfin tattalin arzikinsu wanda kuma a zahiri ba shi bane! An ɓoyewa duniya da ƴan ƙasan ainahin tattalin arzikinsu, an barsu da tinanin cewa fetur ita ce abin da suke da shi mafi karfi a cikin arzikin da suke da shi, dik bama wannan ba, WS ta fara ƙoƙarin rushe amfanin fetur a duniya, sun fito da wani tsarabe-tsarabe wai fetur na fidda hayaki wanda zai iya lalata sararin samaniya, wanda kuma ba dan al’umma suke wannan ba, so kawai suke su gyara yanayin sararin samaniyar ne saboda waɗan nan jiragensu da suke son yin gwanjonsu wa duniya, watau jiragen da basa amfani da mai, (wanda na faɗa maku a baya) shi ne suka fito da ƙage wa fetur, suna son dakatar da amfani da shi, kunga a nan ma Avaris zata shiga wahala, saboda sun fi kowa dogara da fetur a duniya, abubuwan hawansu, komai da fetur suke amfani da shi”…. Ya ɗan nisa tare da cigaba da cewa. “Amma da yake ALLAH yana son mutanen Avaris me yafaru?”…. Aryan ne ya ce. “To ai an ɓoyewa ƴan kasan abin da yafaru”…….. Nisawa ya yi tare da cewa. “Ana tsaka da wannan rikici na ƙoƙarin kashe fetur a duniya sai ALLAH ya baiwa Avaris arzikin aluminum da ake haɗa battery na motocin da suke ikirarin za’a koma amfani da su, a wannan gaɓa ma sun so Avaris ta ci wahala, amma sai ALLAH ya basu wannan arziki wanda ƙasashe ɗaiɗaiku ne suke da wannan arziki a duniya, sai me ya biyo baya?”……….. Lion ya amsa da. “Sai suka kwantar da maganar hana amfani da fetur, suka kuma shiga Avaris dan kwasan wancan arziki ba tare da ƴan ƙasa sun sani ba”. Aryan ya ce. “Hmmmmm Arewacin Avaris tana da manyan ma’adinan ƙasa sama da 30, wanda suka haɗa da, gold shi ya fi yawa ma, amma mutanen Avaris basu sani ba, jahohi 6 suke da gold a Avaris, amma mutane basu sani ba, kuma gold bana wasa ba, yau sama da shekaru 15 suna ɗeban gold ɗin su fitar da shi waje, amma har yanzu bata ƙare ba, sun fitar da kuɗin ƙasan kawai sun kai wata banki a duniya sun ɓoye, su basu taimaki ƴan ƙasa ba, su basu isa su cinye kuɗin ba dikka ba…..”Vir ya ce. “Bakin zalunci ne kawai, aikin mu zai bi ta kan wannan banki da suke ɓoye kuɗi a ciki ɗin ma ai, one day one time su jira diran IRON FIST a kansu! Dik sai sun ɗanɗani azaba irin wanda suke ganawa mutanen Avaris, ba zamu ragawa ko mutum guda ba!!”. Cikin kunar rai yai maganar, kaman Lion yake, akwai zafin zuciya da saurin hawa, yanzu haka shi da Lion da Aryan ji suke tamkar su gansu a gaban WS, da wani irin azaban da zasu yi masu sai sun san lallai hannun IRON FIST suke!Cigaba guru yai da cewa. “Aryan, bayan gold ma akwai manyan ma’adanai kamarsu tantalite wanda da shi ake yin capacitors a wayoyi, taba da laptops, akwai Tin wanda da shi akeyin solder, kayan lantarki, kwalaye masu hana abu yin tsatsa, suna da columbite da shi akeyin kayan jirgin sama, roba mai jure zafi, alloy, amma yau an wayi gari Avaris bata da jirage guda 10 masu kyau na kanta, ko in ce na ƴan ƙasa, sai kame-kame, idan gwamnatin ƙasar ma zata sayi jirgi sai second hand, idan kaga jirgi mai kyau a Avaris to na ƴan kasuwa ne bana gwamnatin ƙasar ba, ga shi kuma suna da columbite da suke sayarwa ƙasashen dake son cigaba suna haɗa jiragen sama suna keta hazo!”. Ya ja dogon numfashi kafin ya cigaba da cewa. “Suna da iron ore wanda da shi ake yin karafuna, siminti, injuna da ginin layin dogo, amma yau an wayi gari Avaria dik wani inji mai kyau idan ka gani daga wajen Avaris aka saya aka shigo masu dashi, basu da kamfanonin haɗa dik waɗan nan, sai dai a ɗebi ma’adanan a sayarwa waje, ƴan ƙasan dik basu san da akwai wannan ba! Baya ga shi akwai lead zinc, akwai lithium, gemstones, sapphire, garnet, amethyst, tourmaline, sannan suna ma da coal dayawa, musamman arewa maso gabas na ƙasar”.(Gombewa how far? A Nigeria kuma nasan kuna da arzikin coal sosai! Hakane ko? Ba iya Avaris ba, kuma kuzo ku faɗa mun me kuke yi da naku? Gombawa daku nike fa, Gombe ikon God, kuma kuna da tatalin arzikin ƙasa dayawa fa, to ALLAH yasa ya amfaneku idan kun gano kuna da shi!.)Cigaba guru yai da cewa. “Akwai limestone wanda ake siminti da shi, suna da gypsum, kaolin, bentonite, manganese, phosphate, granite, dolomite, quartz, copper, nickel, graphite, asbestos, uwa uba suna da uranium wanda da shi ake haɗa wutar lantarki, nuclear, nuclear da manyan ƙasashe ke ta faman rikici a kansa, wanda dik ƙasar da ta mallaketa ake mahaukacin tsoronta, amma yau an wayi gari abin da ake haɗata yana a Avaris, amma Avaris bata da ishasshen wutar lantarki ma bare aje kan nuclear wanda kun sani ko family nuclear basu da shi bare asalin nuclear wanda zai iya tashin ƙasa gabaɗaya, abin taƙaici sai dai wasu can su zo su masu dabara su kwashi uranium a fita da shi, su je su wadata ƙasashensu da wutar lantarki, su kuma wadata ta da makamai da suke dawowa su sayarwa Avaris ɗin”.Lion ya tari nunfashinsa da cewa. “Kuma makaman da suke sayarwa sojojin Avaris ɗin ai very local ne! Basa taɓa sayar masu masu inganci, alhalin daga ƙasarsu suka kwashi uranium ɗin”. Ya kai karshe yana sunkuyar da kai, tin ɗazun shi da Vir sun yi shiru ne saboda tafarfasar da zuƙatansu yake yi, idan suka ce zasu buɗe baki zasu iya haɗiyar zuciya su mutu tsabar takaicin abin da ake yi wa al’umma!.(To mutanen Adamawa state sannunku, na ce ba a Nigeria kaf na ji ku ne kuke da arzikin uranium a ƙarƙashin ƙasarku kamar na Avaris, na ce fatan kuna yin abin da ya dace da shi ko? Fatan kun san da shi kuma kuna ƙoƙarin ganin ko an sayar a gyara maku gari da kuɗin ko?😭💔)Guru ya cigaba da cewa. “Suna da crude oil, watau ɗanyen man fetir wanda a cikinsa ake cire maku su gas da sauransu, baya ga haka kuma suna da natural gas, Iskar gas, suna da bitumen, glass sand, kaolin, gypsum, granite, laterite, manganese, talc, wolframite, lignite”. Ya kai karshe yana girgiza kai, takaici tamkar zai haɗiyi zuciya ya mutu, ace dikka wannan uban tattalin arzikin, kuma dik masu mugun tsada da duniya take nema, amma ace yunwa kawai ta gigita ƴan ƙasar, basu da abin da zasu ci, alhalin da kuɗin uranium da zasu dinga sayarwa ƙasashen waje kawai zai wadaci ƴan ƙasan dik abin da suke so, sai dai ina…….. Abin mamaki da takaici sai su tara kuɗin da har ɗan auta a zuriarsu ya girma ya kare rayuwansa da zuri’arsa kuɗin da suka tara rabi bai ƙare ba, kuɗin da ɗan adam bai isa ya karan da shi ba, kuma kullum ƙara sata suke yi, sai ka rasa me zasu yi da kuɗin! Ka rasa ina zasu kai son duniyar da zamu tafi mu barta, duniyar da tamkar wuni muka zo, babban abin takaici sai su kai kuɗaɗɗen kasashen waje su ajiye, ƙasar da suka ajiye kuɗin ta yi ta juya kuɗin tana amfanuwa, su nan suna sake satar wasu su fitar, wani ma yawan kadarorinsa dake wasu ƙasashe wlh har ya mutu ba’a san in da suke ba, wani ma tsabar ya sata ya sata idan ya sayi wasu kadarori a ƙasashe yana mancewa da wasu su salwanta, wani kuma ya mutu iyalansa ma basu san yana da kuɗi a ƙasa gaza ba! Sun dai sata sun fitar, ya ALLAH ka dubemu da idanun rahma!!.Aryan da jikinsa har wani tsuma yake yi saboda takaici ne ya ce. “Dik wannan tattalin arzikin da ALLAH ya mallaka masu amma ƴan ƙasar basu da wani abin yi, sun zauna basu da aiki kullum sai dai ka gansu a media suna faɗar addini, aƙida ko ƙabilanci, ko yunwar cikinsu basu iya gama maganinta ba, kaga matashi har matashi, mai ji da rai da lafiya, madaki karti, sai ya shiga ɗaki ya saita camera ya hau zagin wata ko shiga faɗar da bata shafesu ba, wasu matasan da basu san ciwon kansu ba ma sai ka samesu da musayar yawu a media a kan kwallon kafa, ko faɗa da mata”..Wani irin numfashi Vir ya ja tare da saukewa a hankali, ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa na takaici kafin ya ce. “An kashe masu zuƙata ne, an dasa masu tsoro, an kashesu da yunwa, ai babban makaman da suka rike shi ne rikita al’umma da yunwa, kana jin yunwa kowani irin aiki aka baka zaka yi dan ka ci abinci, sannan wannan tsoro da aka dasa masu ba zai taɓa barinsu ba, and kada ku manta WS bata ɗaura shugaban da ƴan ƙasa suka fi karfinsa!!”.Aryan ya amsa da. “Ai idan ba ga ALLAH mutanen Avaris suka koma ba wlh babu abin da suka isa yi wa shugabanninsu! Saboda WS bata ɗaura shugaban da ƴan ƙasa zasu iya fito na fito da shi, suna gani ana zalunntarsu amma ba zasu iya yin komai ba, sai dai su yi ta banbami suna cika baki a media!”. Iska mai zafin gaske Lion ya furzar daga bakinsa, wai yana matsayin leader na IRON FIST kuma ace a ƙasarsa, ƙasar mahaifinsa ake wannan ɓarna? Ya ALLAH, shi kam zai iya haɗiyar zuciya saboda takaici, lallai lokacin yin aiki ya yi, lokacin kawo karshen dik wani azzalumi ya yi. Dama ina baku manta ba IRON FIST sun tafi hutu ai! Tin da suka kashe ministar ba sun ce sai bayan shekara ɗaya ko biyu zasu sake yin aiki ba? To shiyasa kuka ji sun yi shiru suna ta bincike kawai, yanzu lokacin komawa bakin aiki da gaske ya yi, Seraphina zata rage ganin daddy Aryan, dama san suna hutu ne yasa yake da ishasshen lokaci!.Da kyar Lion ya iya cewa. “Gano WS babban abu ne, aiki ne ma matuƙar wahala, amma zamu tsokanesu ta yadda da kansu zasu bayyana kansu!”….. Kallon juna suka yi, basu gane in da Lion ya dosa ba, suna son karin bayani, hakika sun san gano WS ba abu bane mai sauki, dan WS ɗin na farko ba mulki suke yi, basu a cikin siyasa, su mutane ne dake rayuwa kaman sauran mutane, kila ma suna kusa da kai a halin yanzu, suna rayuwa very simple, amma suke naɗa masu mulki, abin mamaki, su fa basa son hawa gujerar mulki, da suna son hawa da sun hau, su dai suna gefe, amma dik wata kafunci da zalunci suke shiryasa, idan kuna jin ana faɗin masu naɗa masu mulki to su ne. Tsabar ɓadda kama ma suna tafiya ba security, ba ɗan sanda, babu sojoji, ba zaku taɓa tinanin su bane, kuma suna ko’ina, kunga kuwa kamasu abu ne mai matuƙar wahala, dik duniya harta shugabannin da suke ɗaurawa a kan mulki babu wanda yasan kamanninsu, kai haɗarin mutanen nan ya zarce yadda kuke tinani, su ne mutanen da ko kana kan mulki in baka bi umarninsu ba a cikin ƙasa da 5 mins zasu iya kasheka, baka isa ka guje masu ba, suna koina, suna da ido dake ganinka a dik in da kake, wlh haɗarinsu ya fi na nuclear, sai dai mu ce ALLAH ya karemu ya kawo mana karshen dikkan wasu azzalumai! Aryan da ya fi kowannensu fahimtar Lion ne ya ce. “Kana nufin siyasar Avaris zamu shiga?”……. Vir ya amsa da. “Ta hakance kawai zamu tsokanesu su bayyana kansu, dan a halin da ake ciki ka kuskura ko magana ka yi a kan shuwagabannin Avaris ɓatar da mutum ake yi, idan kana da rabon rayuwa a daka maka warning a sanya maka tsoro!”. Jinjina kai dikkansu suka yi, dan kuwa haka ne, suna gani a media ta kasar, suna bibiyar dik wani motsin Avaris sosai……… “Ba zamu shiga siyasar Avaris ba, amma dik wani gurɓatacce shugaba zamu tugesa, zamu farkar da matasan Avaris mu cire masu tsoro, hakan zai yi matuƙar tayarwa da ws hankali, dole zasu nememu da kansu dan su ga bayanmu! Kunga daga nan zamu kamasu a sauƙaƙe”. Cewar Lion ɗan baiwa mai basira da wayon kama azzalumai, kai Lion ne ya cancanci sunan Smart fa!. Jinjina kai suka yi, lallai haka ne, wanna shawara ta yi, zasu kamasu a sauƙaƙe! A natse Vir ya ce. “Ya batun bank ɗin can?”……. Zuba mashi idanu suka yi, alamar suna jiran karin bayani, Lion ne ya ce. “Zamu gane wace bank ce kuma a wace ƙasa take”. ……. Aryan ne ya ce. “Awww bank da suke kai kuɗin Avaris ko?”…….. Jinjina kai Vir yai. Lion ya ce. “Zamu gane, kuma zamu kwashe dik kuɗin Avaris dake wajen, In Sha ALLAH zamu gina ƙasar Avaris da shi!”.Kai suka jinjina alamar shawarin ya yi. Aryan ya ce. “Wani plan ne a ƙasa a kan aikin?”…….. Lion ya ɗago da idanunsa a kan Vir wanda shi ma shi yake kallo, while su Aryan dikka Vir ɗin suke kallo. Kyafta masu idanu sau biyu ya yi kafin ya ce. “Next week zan shigo, ina zargin wannan bank ɗin yana tsakanin ƙasashen nan guda, France, America ko England!”. Shiru suka ɗan yi, can Lion ya juyo da karfi ya sauke kallonsa a kan Aryan, in a cool way ya ce. “Aryan daga wani bank aka sakawa matar can (mom ɗinsu) kuɗi? Me sunan bank ɗin?”. Yanzu tinanin ya faɗo mashi a kai. Shiru Aryan ya yi, sai yanzu shi ma ya ji yana zargin wannan bank ɗin. Yana ɗan zazzare idanu kaman mai wani tinani ya ce. “Wani bank ne wanda ban taɓa jin sunansa bama a duniya sai a wannan rana, kuma tin daga wannan rana har yau ban sake jin sunansa ba, sunan ma isn’t complete name, just alphabet ne kawai, something WS-STSW-BANK, haka sunan yake”. IRON FIST akwai ƙwaƙwalwa, tsawon shekaru bai manta sunan bank ɗin ba.Wani pen dake gefensu Lion ya ɗauko, ya jawo wani book dake gefe, WS-STSW-BANK ya rubuta a kan littafin, ya cire WS farko, ya WORLS SYSTEM, ya cire STSW na biyu, ya rubuta STARS WORLD BANK, ya haɗa a ƙasa ya rubuta WORLD SYSTEM STARS WORLD BANK!Sun sha madarar mamakin ganin yadda a cikin sauƙi ya fitar da sunan, ya ALLAH, watau brain kyauta ne daga ALLAH da ya baiwa IRON FIST, Lion gifted ne!!. To yanzu sun gano sunan bank ɗin, saura su gano a wace ƙasa take!.Wani numfashi Lion ya ja wanda kana ji kasan na takaici ne, can ƙasan maƙoshi ya ce. “Any danger is from ws, dik wani balai ma daga can yake fitowa, watau bank ɗin ma nasu ne kenan, da kyau!”. Aryan ne ya ce. “Ni yanzu damuwata ɗaya ne, su Nirash, sun tafi Mission, kuma a Arewacin Avaris, wanda dani da ku dik mun san dik wani motsinsu ana sane da shi, kada ku manta ƴan ta’addan ɗaukar nauyinsu ake yi, kunga kuwa ba za’a bar wasu sojoji su kawo karshensu ba, saboda moriyar abin da ws suke ci”.Guru ya ce. “Su Nirash basu san komai ba, yakamata mu taimaka masu, dik wani motsinsu ƴan ta’addan suna gani, kunga sun shirya masu tin ma kafin su zo”……… Vir ne ya ce. “Su Nirash jinin IRON FIST na gudana a jikinsu”.Lion ya ce. “Dik cikinku kada wanda ya kuskura ya taimakawa su Nirash, ku kyalesu, muma a lokacin da muka yi Mission ai bamu san ƴan ta’addan na ganinmu ba, da muka ji wahala ne muka yi experiencing ɗin suna ganinmu har muka nemanwa kanmu mafita, dan haka su Nirash sune magada IRON FIST ko bayan ranmu! Su zasu zauna a kan kujeran da muke, saboda haka babu wanda zai taimaka masu, su yi faɗa su kaɗai, su sha azaba su kaɗai, su kwaci kansu su kaɗai! Su zama mazan gaske”. Vir ya amsa mashi da cewa. “Suna gama wannan Mission ɗinma zamu turasu horon SSO kafin mu basu horon IRON FIST”……. Kai Lion ya jinjina alamar haka ne, dama abin dake ransa kenan, ya sha alwashin mayar da su Leo tamkar su, su zasu zama magadansu!.Sun jima suna tattaunawa suna tsara yadda zasu ɓullowa wannan al’amari. A can kuma Abba nata shirye-shirye wannan coming Friday nan da kwanaki uku kenan zai ɗaura auren Aryan, Harleen, ko sunƙi ko sunso, haka ko daddyn Noor yaki ko ya so su Aunty Luna sai sun zama surukansa ta karfi da ya ji…… Ni kam zanga yadda za’ayi wannan aure, ga Aryan a nan har Seraphina ɗin ma ya watsar saboda wannan shegiyar zuciyar tasu ta gado, Abba ya ja mana aiki. Shi ma daddyn Noor yana ruwa, ko yaki ko ya so sai ya baiwa Abba auren yaransa, ga kakan Noor ɗan zafin rai shi ma kuma ɗan hau, ni ban san yadda za’a kaya bama a wannan al’amari.Sai around 1 na rana suka tashi tattaunawar, a nan ne kuma Aryan ya ɗauko wayansa dan ya kira Faryan, sai a lokacin ya tina da Seraphina, siririn tsaki ya ja, ya so sherata amma sai ya ji ba zai iya ba, sonta ya rigada ya mamaye zuciyansa. Su Lion sun miƙe sun nufi room ɗinsu dan wanka da shirin zuwa masallaci, while shi kuma Aryan yana zaune, sun katse video call da suke yi da Vir. Number ɗinta ya shigar zai danna kira sai ya tina ashe ta fara zuwa school, ɗan dafe kansa ya yi da ya tuna ashe yau bai kaita school ɗin ba, siririn tsaki ya sake ja kafin ya shiga binciken kwanaki biyu me take yi a waya. WhatsApp ɗinta ya fara shiga, dan ya yi connecting da wayansa, dik wani chat ɗinta suna sauƙa a wayansa. Kunna voice nata ita da Rimsha ya fara yi yana sauraro, wani wajen ya ja dogon tsaki, wani wajen ya haɗe fuska, unexpected ya isa in da Rimsha ke zugata kan ya kyale daddynta ta rungume Uncle Faryan, ai bai san lokacin da ya wastsake ya zabura kamar zai miƙe daga kujerar da yake ba, sai kuma ya koma ya zauna, cigaba da saurara ya yi.Jin takaici na shirin sanya zuciyarsa fashewa ne yasa ya dakatar da voice ɗin, abin da ya bashi takaici kuma yadda daren jiya Seraphina tai wa Rimsha voice cewa. “Nisha ki faɗawa Uncle Faryan ina son shi, daddy ya daina kulani, tin safe da ya kaini school bai sake zuwa ba, zan yarda da maganarki kawai in kyale daddy in so Uncle Faryan”. Ya ALLAH wani irin huci da Aryan ya fara yi, kishin ta motsa.Fita chat ɗin ya yi, ya shiga chat ɗinta da number Faryan da ya gani. Ai yana shiga ya fara cin karo da kalaman soyayya da Faryan ya dinga tashin kanta da su, ga shi shi kuma ba iya soyayyar nan yai ba.Ai wani irin zafin kishi ne ta motsa, jikinsa har yana rawa wajen fita ya laluɓo number Faryan, sai dai wayar a kashe ko da ya kira. Da sauri ya miƙe tsaye, har ya manta bai kashe computer ɗinsa ba. Yau ba sauƙa ƙasa, ta sama ya bi zuwa benen Khaiza’ans House. Yana shigowa ya isko Abba a parlo, bai ko kalli in da Abba yake ba, kun san basa shiri, shi Abba ya ce idan Aryan bai bashi hakuri ya janye kalamansa na ba zai yi auren nan ba, ya kuma yarda ya karɓi auren Aunty Lusi ba to kada ya sake yi mashi magana, shi kuma Aryan taurin kai da zafin zuciya, ga ɗan banzar izza, ya ce ba zai bada hakuri ba, kuma aure ba zai karɓa ba, har da cewa kada Abba ya yi ganganci yin wannan kuskure, dan zai jawa yar mutane wahala ne, dan ya rantse da ALLAH ba zai auri su Luna ba, mutum ɗaya zai aura kuma ita ce Seraphina! Abba na ganinsa bai ce mashi ko sannu ba, sama Aryan ya haye, kai tsaye ɗakinsu Faryan ya nufa. Nan ya isko Harleen ne kawai a kwance yana latsan waya. Yana ganin Aryan ya zabura ya miƙe zaune tare da haɗe natsuwarsa waje guda. “Ina Faryan?”. Ya faɗa yana ɗaure fuska!”……… “Ya fita, ina ga ya je ɗauko Rimsha daga school ne, dan 1:30 suke tashi, yanzu kuma 1:25″……. Takaici da kishi yasa bai jira dogon jawabin Harleen ba, yana jin Faryan baya nan ya je ɗauko Rimsha yasa kai ya wuce da sauri.Yana sauƙowa ƙasa Abba ya taresa da cewa. “Ka bani sadakin Vash and Rimsha, Harleen da naka”……. Ɗaure fuska ya yi kafin ya ce. “Zan dai baka sadakin Vash and Harleen, amma nawa kam babu shi!!”. Yana kai karshe ya nufi kofa, har zai fita ya sake tsayawa game da cewa. “Zan turo Faryan ya kawo maka sadakin mutum biyun!”. Daga haka ya fice abinsa.Wani irin shu’umin murmushi Abba ya saki, a fili ya ce. “Yaro yaro ne, dani kake zancen, zan yi maganinka ne, saura kwanaki uku”………. Shi kuwa Aryan yana fita school nasu Seraphina ya nufa, gabaɗaya hankalinsa ya tashi, kishin maza ta motsa, jikinsa har wani tsuma yake yi, har ya manta da cewa Abba ya ja ya tsani har Seraphina ɗin ma.Ko ya zata kaya a wannan school ɗin!. Ga Faryan, ga Uncle, ga daddy Aryan, ni kam na ce akwai tashin nuclear fa!. Muje hospital mu dawo. —————🔥WS-HOSPITAL.Yau kam 5:28 daidai sister Zinta ta samu isa office na Dr James, a wannan karon ma sister Lazy ta so tsayar da ita, amma sai taki tsayawa, dama kullum idan ta zo sister Lazy ke tsayar da ita, ta sanyata ɓata lokaci sosai a wajen tsaye, sai ta tabbatar ta wuce lokacin da aka buƙaceta sai ta ce to ta shiga.Yau kam ko da ta zo bata bi ta kan sister Lazy ba, ta wuce ciki, tana jin sister Lazy na kiranta ta yi banza da ita, dan ta yi alkawarin ba zata sake biyewa wata taɓata mashi lokaci ba. Zaune ta iskosa a saman chair hannunsa rike da cup na coffe yana sha, dik abin da suke yi da sister Lazy kullum yana ganinsu fa, dama ya bari ne yana son Zinta ta fara kwatawa kanta ƴanci, hakika yau ya ji daɗin ganin tadda ta yi banza da sister Lazy, lallai ta fara hawa kan hanya, ta fara zarra ita ma.Na ce ba mu faɗawa Dr James yana haƙawa kansa rami ne ko dai mu kyalesa? Ya kafe dole sai ya cirewa Zinta dik wani tsoro, mu faɗa mashi ubansa zata ci idan ta daina tsoron kowa ne ko dai mu kyalesa? Mu tina mashi cewa jinin IRON FIST take ne ko dai mu kyale sa? Yanzu yana jin daɗin ta fara kwatawa kanta ƴanci a wajen Lazy, hmmmm gobe kuma sai kanka dan ubanka! Ai in suka gane darling ɗinsu alluran cuta kai mashi ma daga nan zaka ga zarra irinta IRON FIST, dan billahil lazi ba zasu yarda ka kashe wannan yaron ba yadda ya shiga zuƙatansu!.Tin da ta shigo ya zuba mata idanu, yana kallonta, har ta ƙariso gaban table ɗinsa, daidai lokacin 5:30 daidai ya buga. Tana ƙoƙarin durkutsawa a ƙasa a gaban table ɗin ya miƙa mata hannunsa yana ware tafukansa…… Da sauri ta ɗago da kallonta a kansa, sai ta ga babu alamar wasa a kan face ɗinsa, sake kallon hannun nasa ta yi kafin ta sake kallon fuskansa, ta tsorata sosai, bata ma gane nufinsa sosai ba, ga shi bata ga sakin fuskan da zata tambayi me yake nufi ba.Jikinta ne ya fara kerman tsoro, idanunta na rawa daga hannunsa zuwa face ɗinsa. Cup ɗin hannunsa ya ɗaura a saman table, ya sanya ɗayan hannunsa yai ƙasa da nose mask dake face ɗinsa, ya ALLAH, ashe haka yake kyakkyawa sosai?.Zazzaro eyes ɗinta a kan face ɗinsa da kyau ta yi, unexpected ta ga ya kashe mata ido ɗaya, blinking eyes ɗinta sau biyu ta yi dan ta tabbatarwa da kanta abin da take gani, da gaske ne shi ya kashe mata ido.One side smiling ya sakar mata tare da jinjina mata kai alamar ta zo. Jikinta ya yi sanyi sosai, dik da tana tsananin sonsa, ta jima tana fatan wannan rana ya zo cikin rayuwarta, amma yau da ya zo sai ta tsinci kanta da jin tsoron da shakkar tinkararsa.Gagara motsawa ta yi, tana jin tamkar mafarki ne kawai. Miƙa hannunsa ya yi, da yake basu da nisa, kama nata hannun ya yi, jawota ya yi ta taho garesa, a saman laps ɗinta ya zaunar da ita. Ai ji ta yi tamkar ba ita ba, tana jin tamkar ba’a duniya take ba, bata yarda gaskiya bace, ta fi yarda mafarki ne.Hannu yasa ya tattare hair ɗinta zuwa gefe guda, ya kwanto da kansa wajen shoulder ɗinta ta gefen wuyanta, tamkar zai yi mata raɗa a kunne, ya ɗaura ɗayan hannunsa a saman shafaffen cikinta, can ƙasan maƙoshi ya ce. “Tsorona kika ji ne?”. Wani irin jan numfashi ta yi tare da saukewa a hankali, sai yanzu ta gane ba mafarki bane da ta ji voice ɗinsa a kunnuwanta. Ajiyar zuciya ta kara daukewa tare da ɗan juyo da face ɗinta ta gefen da ya kwantar da kansa, kirjinta na bugawa da karfi, can ƙasa ta ce. “Na ƙasa yarda da gaske ne, ina jin kamar mafarki nike yi”.Sumbatar gefen cheek ɗinta ya yi kafin ya ce. “Ba mafarki bane, bai kamata ki razana ba tin da kin jima kina sona ko?”…… Kai ta jinjina mashi alamar e haka ne…….. “Kin shirya rayuwa dani?”. Ya faɗa yana shafa mararta zuwa saman cikinta. Rashin sani ya fi dare duhu, da sauri ta gyaɗa mashi kai cewa ta shirya rayuwa da shi. Juyo da ita da kyau ya yi, ya rungumeta sosai a jininsa, ya ɗan matseta kaɗan, ya ɗago da kai suna fuskantar juna……. “Kin shirya mallaka mun kanki?”. Ya sake faɗa can ƙasa. Nan ma kai ta gyaɗa mashi alamar ta shirya……. “To nuna mun kin shirya ɗin in gani”. Yana magana yana moving hand ɗinsa a jikinta, from her back to her neck……. Ɗago idanu ta yi suka kalli juna, ta ɗan turo baki kafin ta ce. “To ka rufe ido”……. Ya ɗan buɗe idanunsa a kanta kaɗan kafin ya ce. “Kina jin kunyata ne?”……. Kai ta jinjina alamar e. One side smiling ya sakar mata kafin ya ce. “Yanzu fa kin zama tawa, shi ne kike kunyata? Ya zakiyi a ranar da zan ce ki mun wanka mu fita office?”. Ya ALLAH bata taɓa expecting jin irin waɗan nan kalamai daga garesa ba, sai ta ji gabaɗaya notikan kanta suna warwarewa, ta kara zaucewa a kansa, dama kenan ya iya soyayya dik wannan tsare gida da iskancin da ya cika mashi ciki, ya ALLAH.Jin shiru bata amsa shi bane yasa ya ce. “Ki gwada mun kin shirya rayuwa dani ba sai na rufe ido ba”…… Kai ta jinjina, ta sanya hannayenta ta saƙalo wuyansa, sai ta rufe idanunta kafin ta ɗaura soft lips ɗinta a kan nasa. Kissing ɗinsa ta fara yi a hankali.Yah ALLAH. Ji ya yi gabaɗaya ya bar wannan duniya, hakika yana sonta sosai, irin son nan na in babu ke babu ni. Ai tallabo bayanta da kyau ya yi, ya ɗan kwantar da ita kaɗan, cikin wani irin romantic mood ya fara kissing ɗinta.A daidai lokacin sister Lazy ta turo door na office ɗin ta shigo hannunta rike da takardu na sakamakon aikin kowani SECTION da aka kawo rahoto yau, ta zo submitting ne. Ai tana ɗaura idanu a kansu bata san lokacin da ta saki takardun hannunta dik suka watse a ƙasa ba.Ɗan razana Sister Zinta ta yi jin an buɗe kofar, da sauri ta fara ƙoƙarin zame bakinta daga nasa tana son waigawa taga wanenen?. Sai dai ina, ya hanata dama, domin kuwa kara ƙanƙameta ya yi, ya shiga tura mata tongue ɗinsa a baki, ya kara matseta a jikinsa, ya hau bata wani irin salon da yasa ta manta ma da an buɗe kofa. Shi da office ɗinsa, kuma yasan wacece zata shigo mashi a irin wannan lokaci, dan haka bashi da matsala, gabaɗaya hospital ɗin a ƙarƙashin ikonsa suke ai, dan haka sai sun jira!!.Ganin wannan chair isn’t comfortable for them ne yasa ya miƙe da ita a jikinsa, bakinsu na cikin na juna, ya koma saman doguwar sofar dake cikin office ɗin, dama dan hutawarsa aka yi mashi. Kwantar da ita ya yi tare da zame bakinsa daga nata slowly, ya ɗan raba jikinsu yana kallon face ɗinta, gabaɗaya ta mance da cewa an buɗe kofa. Lazy kuwa ta yi mutuwar tsaye, hawaye sun gama wanke mata fuska, bata taɓa tsammanin akwai wacce Dr James zai fara haɗa jiki da ita ba ita Lazy ɗin ba! Ta so shi kamar ranta, kullum mafarkin yadda zata same shi take yi, ashe shi ba ta ita yake yi ba!. Necktie na wuyansa ya fara kwancewa, dama ya cire suit na sama, saura long sleeve shirt na ciki da tie na wuyansa and trouser. Kwance tie ɗin ya yi, ya hau ɓalle botiran rigar jikinsa, idanunsa a kan kyakkyawan face ɗin Zinta da ta rufe idanu ruf, lips ɗinta suna ɗan kerma alamar tana cikin mamaki har yanzu.Zare rigar jikinsa ya yi bayan ya kammala cire botiran, kwantowa kanta ya yi, ba ruwansa da Lazy na tsaye, romancing ɗin Zinta ya fara yi irin sosai ɗin nan yana wani numfashi sama-sama. Takaici yasa numfashin Lazy ya fara yin sama-sama, cikin fusata ta ƙariso in da suke, kishi yasa ta rarumo laptop ɗinsa zata bugawa sister Zinta dake kwance idanunta a rufe.Da hannu ɗaya ya rike laptop ɗin, kwacewa ya yi tare da ɗauketa da wani gigitaccen marin da yasa ta yi baya-baya ta faɗi ƙasa. Sister Zinta na kokarin buɗe idanu sai ji ta yi ya ɗauketa cak zuwa ɗakin hutawarsa dake cikin office ɗin, yana shiga ya rufe kofar da key ya bar Lazy zube a ƙasa, takaici yasa ta rushe da kukan bakinciki.Shi kuwa ya shinfiɗe Zinta a saman sofar dake ɗakin, ya cigaba da romancing ɗinta sosai, tin tana kame jikinta har ta sakar mashi jiki, ya rabata da kayan jikinta kaf, ya juyata son ransa, amma bai yi sex da ita ba, ya dai murjeta son ransa, har ya yi realizing, sannan ya tashi daga kanta, ya faɗa cikin toilet dake ɗakin. After 30 mins ya fito sanye da bathrobe ash color, yana rike da wata ash towel yana goge kyakkyawan gashin kansa. Yadda ya barta haka ya fito ya sameta, ta gagara motsawa saboda kashe mata jiki da ya yi. A gaban sofar ya tsuggunna tare da kai hannu ya tattara gashinta da ya zubo har kan face ɗinta saboda murzanta da ya dinga yi.Can ƙasa ya ce. “Are you okey?”…… Slowly ta waro idanunta, kai tsaye sai kan kyakkyawan face ɗinsa. Ƙasa da ido ta yi kafin ta ce. “Jikina yana mun wani iri, na ƙasa motsawa”…….. Hannunsa ɗaya ya ɗaura saman shafaffen cikinta, ya ɗan shafa zuwa gabanta yana ɗaure fuskan nan da ya saba na tsare gida kafin ya ce. “Dole jikinki zai yi haka, dan bai taɓa jin makamancin abin da ya ji yau ba, amma anjuma idan na sake ba zai yi hakan ba”. Murmushi ta sakar mashi kafin ta ce. “Zaka sake wani?”……. “Meyasa kika tambaya?”. Yana ƙara ɗaure fuska ya faɗa, watau idan suna soyayya ya sake fuska, da sun gama ya zama tantiri har da haɗe rai…….. Nisawa ta ɗan yi kafin ta ce. “Na yi tinanin daga yanzu ba zaka sake kulani ba”……. Shiru ya ɗan yi, sai kima ya shafi soft cheek ɗinta kafin ya ce. “Kullum ma zan yi ko kina so ko baki so, dan ke ɗin tawace ni kaɗai ko ki so ko karki so!”……. Kuji hege! Ka ji karfin hali, wai ko ta so ko kar ta so! To da yake jikinka ne ai dan ubansa da bamu san waye bane ma!!.Watau Dr James fa ya gane nufinta, ita ta zaci dan biyan buƙatansa kawai ya kulata yau, bata san wlh bai taɓa son wani abu yadda yake sonta ba, so na musamman yake yi mata, da alama soyayyarta shi ne kaddaransa a rayuwansa, dan kuwa in yai wasa sonta zai iya zame mashi wani abin a lokacin da zata gane waye shi ta guje shi. Ɗan banza kuma yana more jikinta yana haɗe mata, wai kuma yana sonta!(Ni ina fatan ya sha azabar zuciya ta dalilinta, ina fatan ya tare da ita yadda yake son, ya kara sonta sosai, amma bana fatan ta haifa mashi yara, dan bana mata fatan haɗa jini da shi, amma zan so ya ɗanɗaneta, ya sota mahaukacin so! Ta zo ta gane waye shi, ta gujesa, wannan zafin kawai ya ishe shi, ALLAH ya jarrabesa da in babu ita a gefensa babu barci bare kwanciyar hankali ɗan banza!!)Ta ji daɗin kalamansa dik da cikin tsare gida ya faɗa, tabbas soyayya mugun wasa ce, kome ya yi ita burgeta yake yi. Ta yunkura zata miƙe, da sauri ya taimaka mata ta miƙe zaune, ɗan shafa kirjinta ya yi kafin ya ce. “Je ki yi wanka ki zo ki koma bakin aikinki”. Yana kai karshe ya miƙe, wani ɗan glass room dake gefe ya shiga.Jim kaɗan ya fito sanye da wasu suit ɗin a jikinsa, ba tare da ya kalli in da take ba ya ce. “Ki yi saurin komawa bakin aikinki”….. Kamar zata tambayesa ba ya ce anjuma zai sake kasancewa da ita ba, sai kuma ta ji nauyin tambayar, ta tashi jiki ba kwari ta shiga toilet ɗinsa. Tana wucewa ya bi bayanta da kallo, sai da ta shiga cikin toilet ɗin ya fice abinsa. Yana fita bai isko Lazy a office ɗin ba, wayansa da agogonsa ya ɗauka, waje gabaɗaya ya fito, nan ya isko Lazy a office ɗinta tana kife da kai saman table tana kuka. Ko kallon in da take bai yi ba ya sanya kai ya wuce waje.Yana wucewa ta ɗago da kallonta a kansa, sai da ta tabbatar ya tafi, da sauri ta miƙe ta dawo cikin office ɗinsa, kai tsaye ta shiga ɗakin da suka yi chaskalensu da Zinta. Tana shiga ta ji motsin ruwa a toilet, da zafanta ta nufi can. Tana murɗa handle ɗin kofar ta buɗe, ciki ta afka, sundume cikin jaccuzi ta isko Zinta, tana wanka a natse. A gaban Jaccuzin ta tsaya tare da rungume hannaye a kirji, cike da zafin kishi ta ce. “Ke karya karuwa, dabba jaka fito waje yanzu!”. To ita sister Zinta da bata san me karya kuma me karuwa ɗin bane ta bita da kallo, ita Lazy ita tasan ma’anar karuwa tin da ita daga wajen hospital ɗin ta fito, ita kuma Zinta tasan a nan dai babu karuwa, bama ta san me hakan yake nufi ba. “Ba zaki fito na ina magana!”. Lazy ta faɗa a fusace…….. “Baki ga ina wanka bane, ki je waje idan na gama ai zan fito”……. Eyeee baki Lazy ya saki tana kallonta, yaran dake tsananin tsoronta ne yau Zinta ke mayar mata da martani. Ai a fusace ta yi kanta zata daketa Zinta ta miƙe tsaye, tana dalla mata wani mugun kallo ta ce. “Ki taɓa yau ki sha mamaki!”.Watau yau Zinta ji take yi tana daidai da kowa tin da suka yi wannan chaskalem da Dr James, dama power ɗin Lazy dikka ba dan saboda tana aiki a karkashin office ɗin Dr James bane? To ita yau ba aiki a karkashinsa kawai ba, cire mata kayansa ya yi, a gabanta taga komai ɗinsa, sun zama ɗaya da shi, abin da babu wata nurse da ya taɓa kwatanta haka da ita, kunga kuwa kowa sai ua sararawa Zinta, ta ciri tuta kuma dole yanzu su dinga bata girma, zata zama aunty ɗin dik wata nurse dake hospital ɗin nan, ita kanta Lazy zata dawo karɓar umarni ne, idan suka yi wasa ma kowani hukunci Dr James zai ce su je wajenta ita zata yanke! Kai watau akwai dirama a wannan asibitin ba kaɗan ba wlh.Ganin haka yasa sister Lazy ja da baya, san tasan tin da Dr James ya yi wannan chaskalen da ita fa to ta wuci dik yadda ake tinani, in ta kuskura ta taɓata zata jawa kanta ne, dama wai ta zo yi mata barazana ne ta ce ta fita harkar Dr, to yanzu da alama barazanar ma ba zata yiwu ba dole ta canza salon kirsa da makircin dan kwaro Dr daga hannun ƴar shika sweet 18!. Juyawa ta yi a fusace ta bar toilet ɗin tana huci, ita kuwa sister Zinta tai wankarta, ta fito ta mayar da kayan jikinta, daga nan ta fita izuwa wajen sister Maya.Tana zuwa ta sameta sai fama da babys take yi, rungumeta sister Maya ta yi, ta jata suka zauna a gefen bed ɗinsu, labarin abin da ya faru ta hau bata tana murna. Ai kuwa sister Maya aminiyar kwarai, ta yi mugun tayata murna, ta dinga kara mata shawarin kan yadda zata rungume zuciyansa gabaɗaya, ta zama ita ce Big Aunty a hospital ɗin nan, kowa ya dinga girmamata!.Ta yi farinciki sosai, haka suka tashi suka cigaba da kula da jariran nan.After some hours.Daga babys har masu kula da su sun yi barci, around 1 na dare 3D suka yi diran mikiya a ɗakin babys ɗin nan, kunna light na ɗakin suka yi, tamkar yadda suka yi ranar, babys guda biyar suka zaɓa, kunga saura 50 out of 55 kenan ko?. Babys ɗin suna ta zuba barci abinsu, while masu kula da su ma sai barci suke yi, har 3D suka fita da babys ɗin nan basu farka ba. Kai tsaye SECTION E suka shiga da yaran, bakin Queen Of Surprise ɗinku ya yi kaɗan ya iya zayyana maku yadda SECTION E yake, a halin yanzu ba zan ce komai ba, amma a gaba zaku ji karin bayani, dan ya zarce dik yadda kuke tinai.SECTION E ya fi dik sauran SECTIONS na hospital ɗin girma da yawan ɗakuna da kuma jan wutar lantarki!. Dan ko’ina haske ne tamkar rana, kana shiga cikinsa zaka zaci gari ya waye saboda hasken dake ko’ina.Kai tsaye wani ɗaki suka shiga, ɗakin nan cike yake maƙil da injuna nau’i ka daban-daban. A gaban wani trasnferen glass ball mai girma suka tsaya, glass ball ɗin daga ta sama ne ball wanda kana iya ganin cikinsa, daga ƙasa baki me mai duhu baka iya ganin komai, sannan daga ƙasa wajen bakin yana da kunnuwa guda huɗu. A gefensa glass ɗin akwai beds na babys, dikka 3D suna sanye da kayan aiki, kama daga kan hand gloves, nose mask, da dai sauransu. Cirewa babys guda biyar ɗin nan dikka kayan jininsu suka yi, suka kwantar da yaran a saman wannan gadon. Dr James ne jagaba, yaran har lokacin suna barci, saboda sun sha wanka da ruwan zafi sosai, ga kayan sanyin da aka zuba masu, an gasa masu jiki sun kuma sha madara mai ɗumi sun ɗumama cikinsu, kunga ai sai barci. Bayan sun kwantar da su, Dr James ya danna wani madanni dake jikin gadon, take jikin gadon ya kawo wani blue light, yana kawo wannan blue light ɗin babys ɗin nan dikka suka farka, take suka fara girgiza, suka zazzaro idanunsu tamkar kwayar zata faɗi ƙasa, dikkansu suna son yin kuka amma sun gasa.Ja da baya kaɗan 3D suka yi, ba komai suka kunnawa wannan gado ba face shocking na lantarki, suna son razana yaran ne saboda jikin yaran ya basu abin da suke so, sai sun razana sosai jikinsu zai saki wannan sinadarin da suke buƙata, shiyasa suke sakasu a shocking na wuta, su ɗaurasu a gadon socking. Wani irin jijjiga da karfi yaran suka fara yi, hannunsu da kafafunsu yana wani irin kerma, idanunsu tamkar zai faɗo ƙasa, lips ɗinsu na ɓari sosai. Ya ilahi ya lillahi. Ko gezau 3D basu yi ba, suna tsaye tamkar babu zuciya a kirjinsu, suna ganin yaran nan sai da suka yi tsananin razana, sannan Dr James yasa hannu ya danna wannan madanni ya kashe lantarki.Yana kashe lantarki yaran suka fara ƙoƙarin kuka, sai dai bai bari sun samu damar yin kuka ba ya danna wani madanni gadon ya ɗaga sama da yaran, ya danna wani madanni jikin wannan glass ball ɗin, take kofa ta sama a cikin glass ball ɗin ya buɗe, gadon da ya yi sama da babys ɗin ya zubasu a cikin wannan glass ball ɗin.Yaran suna ta ƙoƙarin yin kuka amma basu samu dama ba, suka rufe glass ball ɗin, sun danna yaran wani kan wani, ga rashin iskan shaƙa bare su yi numfashi.After like 2 mins da zuba yaran ciki glass ball ɗin ya fara jujjuyawa da yaran yana sama ya sake yin ƙasa da su, ya ilahi, yaran nan sai da suka fita hayyacinsu, sai idanu kawai zaku ga suna zarewa, gwanin nan tausayi!. Jim kaɗan wani waje daga ƙasan cikin glass ball ɗin ya buɗe wanda ƙasan shi ba’a iya ganin me a ciki, baki ne, dikka jariran cikin wajen suka faɗa, take ƙasan ya rufe, yana rufewa wani ƙara ya fara fitowa tamkar farfasa kasusuwan ɗan adam, inji ne a ciki ya fara kara.After kamar 30 mins daga gefen glass ball ɗin ta ƙasa Dr James ya ɗauko wani gaton boket ya saka a wajen, ya buɗe wajen kunnen ball ɗin, take wani irin jini jajir ya fara zuba tamkar an buɗe tap. Dr Kamal ya ɗauko boket shi ma ya buɗe ɗayan kunne, a nan kuma ɓargon cikin ƙashin babys ɗin ne ya fara fitowa tamkar jelly, shi kuma Dr Mark ya buɗe side ɗin da ƙashin yaran yake fitowa ya fara tarewa a boket.A takaice wannan inji ta niƙa yaran ne, ta ware jininsu daban, ɓargonsu daban, kazaliƙa ƙashinsu daban, ƙashin nasu ma injin ya niƙa shi ya yi laushi sosai tamkar gari…… Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, hasbunallahu waniimal wakil, astagfirullah wa’atubutu ilai, ya rab, ya rahman, ya rahim, ya malik, ya kuddus, ya salam, ya mumin, ya muaimin, ya aziz, ya jabbar, ya mutakabbir, ya ALLAH……….😭Karin haske, a cikin jinin jariri akwai wani sinadari mai suna hematopoietic stem cells da suke amfani da shi, waɗannan sinadarai ne dake samar da sabbin ƙwayoyin jini, a likitance ana ce mashi red & white blood cells. Sannan suna amfani da jinin wajen warkar da cututtuka da dama har ciwon leukemia, sankarau. A takaice da jinin jariran nan suna kirkiran magungunan cututtukan da suke kirkiranwa duniya! Jinin jariri yana sabonta kwayoyin halitta. Sannan a cikin jinin akwai sinadarin erythropoietin, sinadarin da ke samar da jan jini, a likitance ana ce mashi red blood cells, sannan akwai sinadarin fetal hemoglobin da suke cirewa, wannan nau’in haemoglobin ne da ke cikin jinin jariri, wanda ke da ƙarfin ɗaukar iskar oxygen fiye da na manya. Sannan akwai sinadarin mesenchymal stem cells, da interleukins & growth factors, sai alpha fetoprotein, wanda a hankali zan faɗa maku me suke yi da waɗan nan sinadaran, tare daku zamu zaƙulo komai mu warware In Sha ALLAH. Kun ji na jinin, to shi kuma ɓargo fa?.Akwai sinadarin wharton’s Jelly da suke amfani da shi a ɓargon jariri, wannan wani abu ne mai kama da jelly da ke cikin ɓargon ƙashin jariri wansda sai sun firgita jariri jikinsa ke sakin wannan sinadarin ta yadda in sun kashesa zasu iya samu, wannan sinadari yana ɗauke da hyaluronic acid da collagen, a yanzu ba zan faɗa maku me suke yi da sinadaran nan ba, dan tashin hankalin zai maku yawa, amma gaba zaku ji komai In Sha ALLAH.To bayan wannan sinadari na wharton’s akwai glycosaminoglycans, da kuma chondroitin sulfate, sannan akwai exosomes, da umbilical cord stem cells da dik suke amfani da shi daga cikin ɓargon ƙashin jariri, wanda in muka natsa cikin labarin zaku ga komai dallah-dallah da idanunku, zan daure in rubuta maku komai, ba zan rage koda abu ɗaya ba In Sha ALLAH! Yadda na tsara labarin nan, dik taɓa zuciyansa ba zan canza ba, na sha kuka wajen rubutasa tamkar raina zai fita, amma haka na daure, ina typing ina kuka saboda tashin hankalin ya kai tashin hankali, ace da jinin jariri suke haɗa wasu magunguna, jaririn da bai ji ba bai gani ba, bai san komai ba, ba imani ka ɗauki jariri kasa inji ta marƙaɗa shi, ya rab, wai wani irin zuciyace a kirjinsu 3D?. Ga wasu sinadaran da suke cirowa daga ɓargon ƙashinsu, ya ALLAH, ko waɗan nan sinadaran kuma me suke yi da su? Alƙalamina zai waware maku komai.Kwashe komai tas suka yi, suka fita da jinin izuwa wani ɗaki dake kusa da wajen, a nan suka ajiyesu cikin wani katon freezer, sannan suka fito daga cikin wajen, sai gobe za’a fara ƙoƙarin haɗa magunguna, dama kashe jariran kawai suke yi cikin tsakiyar dare yadda babu ma wanda, zai gansu.Suna fitowa SECTION D Dr James ya koma. Su Dr Kamal kuma suka koma gidansu, wlh bawan ALLAHN nan Dr James tamkar ba jarirai rai biyar ya danna cikin inji ta niƙasu ba, ko kaɗan bai damu ba, ya shiga cikin ɗakin da su Zinta suke, tana barci ya saɓeta a saman shoulder ɗinsa ya fito, kai tsaye gidansu ya koma, dama in baku manta ba ɗazun ya ce mata anjuma zai sake yin abin da ya yi da ita ai, to shi ne ya zo ɗaukarta.Ya ilahi, me suke yi da waɗan nan sinadaran da suke cirewa daga ɓargon ƙashin jariri? Mesuke yi da sinadarin cikin jinin jaririn? Daga gani abubuwa masu muhimmanci da tsadar gaske suke yi da su, ki tsaya ki karanta abin da suke yi da sinadaran. Watakila kema kina amfani da wannan abin bisa rashin sani! Sai ki san me kike amfani da shi!. Tambaya shin idan su Maya suka farka zasu gane an ɗauki jarirai guda 5? Ko ba zasu gane ba? Idan suka gane me zasu yi? Wani mataki zasu ɗauka? Ya rabbi, idan kana raye babu abin da ba zaka gani ba, ya ALLAHU ka kawo mana karshen dik wata fitina, ALLAH ka dubemu da idanun rahama.

Back to top button