Zakuna Biyar Page 16 By Princess Teema
Ihu amarya ta fara kurmawa, ta gudu cikin bedroom, cikin zafa ya bita ciki, tamkar babu hankali a kansa, ko da yake dama a irin wannan lokaci ba man kai suka cika ba na faɗa maku, dan a lokacin su kaɗai suka san ya suke jinsu, bare sun karɓi alluran karshe na fita horo, amarya tana tsakiyar dajin dake kewaye da zakuna, dan kuwa a kanta wannan allura zai fara aiki, kunga kuwa ita ai ta bar tarihi.Duka ɗaya yai wa kofar bedroom ɗin nata ya ruguje, dan shi irin kofar wood ɗin nan ne. Ciki ya shiga, saman gado ta haye tana ihu. Aikuwa taka saman gadon ya yi da takalmarsa, tana ƙoƙarin gudu ya damki gashin kanta, dama ɗankwalinta ya cire tin da ta gudo ta baro parlo.Tsabar razana da tashin hankali fitsari ta saki a zaninta a wajen. Ina ai bai san tana yi ba, waje ya jata da gashin kan nata, yana fitowa ya daddage ya buga mata kai da jikin bango kusa da ɗakin nata. Wani irin azababben ihun da ta zunduma sai da gabaɗaya unguwar ta amsa. Ummie fa ja da baya ta yi, dan wlh ta ji tsoron tinkararsa, ta ce ba shi bane, an canza mata shi, bata tashi sanin haɗarin soja ba sai yau, kun san shi fa soja ko kakinsa firgita zuciya yake yi bare shi da yake horon AZURE kuma sabon passing out daga bar two bama bar one ba, ai amarya sai sorry.Da gudu Ummie ta nufi kofar gida dan ta buɗe jama’a su kawo masu ɗauki, ita da kanin nata yau tsoron tinkararsa take yi. Tana buɗe kofar ta ga jama’a a tsaitsaye a kofar gidan, da sauri ta ce. “Jamilu ku zo ku taimaka mun kada ya kashe amarya!”. Muryanta na rawa ta yiwa matasan unguwar magana.Da gudu suka faɗo cikin gidan, daidai lokacin Zaynish ya kwashe kafafun amarya ta zube ƙasa kamar kayan wanki, kun san sojoji sun kware wajen iya kwashe kafafun mutane su zubar dasu a ƙasa.Dik matashin da ya shigo da gudu yana ganin kalar uniform ɗin sai ya ja wata uwar birki, ba ɗan sanda ba ne bare a iya zuwa a sasanta, shi wannan daga nesa idan aka ga kakin kawai canza hanya ake yi in dai akwai tsama a tsakani. Matasa sun fi goma babu wanda ya iya karisawa wajen ya rikesa, wasu ma ai a miliyan suka juya da gudu suka bar gidan.Makwabta mata da sun shigo sun ga mai dukan amarya zasu juya da gudu. Hankalin Ummie ya yi mugun tashi, ga shi ko kaɗan bata da zarrar iya zuwa ta kama shi, kuma ita kaɗai ce in ta kama shi kun san ba zai kai mata duka ba, zai daure, amma ina ta tsorata.Wannan shegiyar takalmar tasu yasa ya fara ball da amarya, daga karshe ya kwance wannan shagiyar tattauran belt ɗin nasu, dukanta ya fara yi tamkar wanda aka saukarwa wahayin duka. Wani irin gigita Ummie ta yi, tsoronta kada ya yi kisan kai. Da sauri ta ce. “Jamilu dan ALLAH ku kama mun shi”. Wanda aka kira da Jamilu ne ya ce. “Aunty Ummie kina gani soja ne fa ba police ba, gaskiya ni ban shirya mutuwa ba”…… Da sauri na jefensa ya ce. “Kai ma kenan da kake matsayin abokin ɗan banga, mu kuma mu ce me? Ai kawai sai dai mu ce ALLAH ya jikan amarya idan ta mutu, dama ta ishemu a layin nan”. Kuka hawaye bibbiyu Ummie take yi, da kyar ta iya cewa. “Ku kama shi ba zai yi maku komai ba, kanina ne, dan ALLAH ku dakatar da shi”…… Ai ina dik cikinsu babu wanda ya motsa bare su yi yunkurin kama shi…… Dukan ALLAH tsine uwar mai karya Zaynish ya yi wa amarya, farfashe mata jiki ta ko’ina , har sai da yaga ta daina motsi, sannan ne ya dakata yana cigaba da huci.A fusace ya juyo da kallonsa a kan Ummie, haba ai a miliyan su Jamilu suka yanka kofar gida, sun ga zaki ya juyo, ka ji gudun karti wasu ta saman gini suka dira waje. Ita kanta Ummie kaɗan ya hana ta saki fitsari a in da take tsaye, ba dan tasan ciki ɗaya suka kwanta ba, ko mai wuya ba zai cutar da ita ba da wlh babu abin da zai tsayar da ita itama, tuni zata gudu, amma ta daure ta tsaya.Dimfarota ya yi tamkar wani mayinwacin zaki, a gabanta ya tsaya, with harsh voice ya ce. “Dama irin zaman da kike yi a gidan nan kenan? Meyasa baki sanar dani ba? Ina Faisal ɗin yake? Sai ya faɗa mun idan jaka aka bashi ko ance mashi baki da gata ne!”. Tashin sense, yau babu batun Yaya Faisal, Faisal kai tsaye, ba shakka da comrade Faisal na nan yau da shi ma ya gane ALLAH da girma yake.Wani irin kerma da jikinta yake yi ne yasa ta gagara iya rike kanta, kasa ta durkushe tana cigaba da kallonsa har cikin ido, ta gagara bashi amsa. Tsawa ya daka mata da karfi wajen cewa. “Wacece wannan? Kuma ina Faisal ɗin na ce? Sai sun faɗa mun a gidan uban waye kika bi maza? Idan basu faɗa mun sun bani shaida ba billahil lazi sai na lahira ya fisu jin daɗi”. Hannu bibbiyu tasa ta dafe kirjinta dake barazanar tarwatsewa, still kallonsa take yi ta gagara yin magana, allurar tasa ta motsa, baya iya fahimtar a wani hali take ciki bare ya sassauta mata murya, sai ma tsawa da ya sake daka mata tamkar zai kai mata duka, daga karshe ma yasa hannu ya miƙar da ita tsaye, yana cigaba da huci ya ce ta lissafa mashi masu ce mata tana bin baza, da alama wannan kalma ta fi komai ƙona mashi rai. Har lokacin baiwar ALLAH ta gagara yin magana. Jama’a sun cika kofar gidan dam, amma kowa yana tsoron shigowa, wasu matasa ma aka samu suka kira ƴan sanda. Mota biyu ƴan sanda suka zo, take jiniya ya karaɗe umguwar, zaku ce yaki ake yi, jama’a an yi cirko-cirko.Ƴan sanda biyar ne suka diro ƙasa daga bayan motocinsu, da farko sun tsaya a waje, sai su Jamilu suka faɗa masu ai kisan kai za’ayi a cikin gidan, hakan yasa suka danno kai ciki da gudun gaske, a lokacin shi kuma yana tsaye gaban Ummie ya titseyeta kan lallai ta faɗi masu mata ƙazafin zina, yau sai sun bashi hujja ko kuma dik su ci ubansu ne, ba zai ɗauki nonsense ba, yana matsayin position 3 a bar 2 ɗin za’a kawowa rainin wayau? Tab!. Da gudu ƴan sandan suka kewayesa suna faɗin ya natsu ko su harbesa har da ɗaga bindigu su nunnuna shi. Nan fa su Jamilu suka dawo cikin gidan dan ganin gulma, da a basu kabari gara su bayar.Ai a miliyan Ummie ta ware, sai kuma ta fara ƙoƙarin kare Zaynish ɗin, muryanta na rawa a fara ƙoƙarin cewa ƴan sandan su yi hakuri su je rigimace ta cikin gida. Bata kai ga yin magana bama wani ɗan sanda ya ce. “Madam bai yi maki komai ba ko?”…….. Da kyar ta iya ƙoƙarin buɗe baki zata yi magana, amma ta gagara saboda rawar da jikinta yake yi. Shi kuwa wani irin juyowa ya yi tamkar bujumin zaki, dikka ƴan sandan sai da gabansu ya faɗi, baya suka ɗan ja suna faɗin kada ya motsa. Kallon tsab ya yi masu kafin ya ce. “Your gun down!”. A sigar bada umarni ya yi maganar, dan ya ga dik ya fi ƴan sandan rank, dikkansu constables ne, ko soja dake bar one ya fisu rank bare shi da yake na uku a bar 2, ai ya wuci waɗan nan. Jin yadda ya yi magana cikin bada umarni in a harsh way ne yasa suka ɗan ja baya, sun sha jinin jikinsu, slowly suka yi ƙasa da bindigunsu kamar yadda ya umarta. Ganin basu yi gardama ba sun yi biyayya ne yasa ya ɗan sauko ya yi masu bayanin waye shi, da sun yi gardama lallai da sun ɗanɗani karfin dukan hannun horon Azure yau, dan wlh yadda yake jin kansa tsab zai iya dukan zaratan maza 20 ko sama da haka, shi fa abokin balai ma yake nema yanzu ko zai sosa hannunsa dake mashi ƙaiƙayi, wai baku ga Vash a gida yana can yana ta faɗa da neman masifa bane? Ai haka suke bayan horo, dik su rikiɗe su zama wasu zakuna. Ba karamin girgiza ƴan sandan suka yi ba jin waye shi, sannan ya ce masu zasu iya tafiya babu ruwansu da case ɗin nan. Sai a lokacin Ummie ta ce. “Ku yi hakuri kanina ne, faɗar gida ne, ba wani abin zai mun ba”. Tana magana dai idanunta a kansa sosai. Ganin tsananin kamanninsu na buzayen nan ne yasa suka yarda ƙaninta ne, dan dik wanda ya ganta ya gansa, dan ma dai shi wannan gashin nasu ma buzaye ya cika mashi kai sosai, yasa fuskansa ta ɗan rame, amma dik da hakan kamanninsu sosai.Da sauri ƴan sandan suka karɓi umarni tin da sama da su yake, da gudu suka fice a gidan, sam basu lura da an sumar da amarya ba, su a zatonsu iya Ummie ce kawai. Ai suna fita su Jamilu suka bi bayansu, dan tsoron kada Zaynish ya bi ta kansu.Suna fita Ummie ta yi ta mazan kama hannun Zaysh ɗin tin da taga ya ɗan sauƙo, shi ma sai a lokacin alluran ta ɗan sauƙa ya iya ganin firgicin dake kan fuskanta, ɗan rungomo shoulder ɗinta ya yi tare da cewa. “Sorry Ummie, wannan firgita dik na mecece?”. Ai da sauri ta rumgumesa ganin dama ya samu ya ɗan sauƙo, sabbin hawaye ne suka fara wanke mata fuska, da kyar ta iya cewa ya je ɗaki dan ALLAH ya basu dama ta kira jama’a a kai amarya asibiti, zai yi mata gardama ta ce. “Zaynish ALLAH idan ka mun gardama zuciyata zata iya bugawa, ka je ɗaki dan ALLAH”. Ganin yadda ta firgita sosai ne yasa ya hakura ya wuce cikin room ɗinsa, da sauri ta ɗauko wayarta ta kunna, number Faisal ɗin ta kira. Bugu ɗaya ya ɗauka, da yake bai san me yakefaruwa ba sai ya ce. “My ƴar aljanna yanzu nike son kiranki in ji kun iso ne, dik kewarki ta dameni”.Da kyar ya iya danne kukanta, ta harhaɗo natsuwa tare da girmamawa a garesa kafin ta fara faɗa mashi abin dake faruwa, bata ɓoye mashi komai ba. Fusata ya yi, ya fara yi mata faɗa da cewa dama amarya na jifarta da kalmar mazinaciya shi ne bata taɓa faɗa mashi ba? Meyasa dik rashin kunyar da amarya take yi mata take ɓoyewa bata faɗa mashi?.Shiru ta yi tana sauraron faɗar tasa har ya kammala, sannan ne ta ce. “Ka yi hakuri, ban son haɗaka faɗa da matarka ce, amma ka yafe mun mijina”….. Shiru shi ma ya ɗan yi kafin ya ce. “Zaynish ya mun daidai, dan ko ni ne hukuncin da zan yi mata kenan, na sha faɗa mata tai maki biyayya, dan ita ƙaƙaba mun ita aka yi, ke kuma ni na ganki na ce ina so, kuna da bambanci, idan tana son zaman lafiya dani ta girmamaki, watau shi ne idan na fita take maki abin da take so ko? To ku kyaleta a wajen babu wani asibiti da za’a kaita!”. Cikin faɗa da iya gaskiyansa yake maganar.Ummie baiwar ALLAH ba zata iya ɗauke kai ba’a kai amarya asibiti ba, da sauri ta hau rokonsa kan ya yi hakuri a kaita. Da kyar ya yarda, sannan ya ce bari ya kira kannensa da kannenta su zo su ɗauketa.Cike da mamaki ta ce. “Kai ka yi nisa ne da ba zaka zo ka kaita ba?”….. A natse ya ce. “Bana garin ne, na je tsakanin Adamawa da Taraba”. …… Zazzaro ido ta yi kafin ta ce. “Ma ka je yi can?”. “Wani abokina ne ya ce mu je haƙar gold a wajen, ya ce ana samun alkhairi sosai a wajen, akwai sabon wajen da aka gano yake da gold a wajen, to shi ne na ce bari in jarraba tin da aiki ya gagara samuwa, ki tayani da addu’a ƴar aljanna, ki mun addu’a in yi farar tafiya”….. Dik da bata so tafiyar ba dan tasan yadda ake mutuwa a wajen harkar gold ga wahala, amma hakan bai hana ta daure ta zuba mashi addu’a sosai ba, ya ji daɗi ya dinga amsawa da amin, sai da ya zuba mata kalaman kauna sosai, sannan suka yi sallama yana faɗa mata zai turo kannen amarya yanzu, kuma yana umartanta da ta shige ɗaki yanzu, sannan ta gaida mashi da kaninsa Zaynish ta kuma bashi hakuri da abin da ya faru. Da okey ta amsa tare da yi mashi fatan alkhairi, daga haka suka yi sallama ya katse kiran, gagara komawa ɗaki ta yi, haka ta samu fili a wajen ta zauna har lokacin da ƴan uwan amarya suka zo suka ɗauketa, basu yi wa kowa magana ba, dan already Faisal ya faɗa masu cewa akwai zaki jarumin jarumai a gidan, su kula su kuma haɗe malaman jikinsu waje guda, idan ba haka ba jikinsu ya faɗa masu ma, shiyasa basu yi magana da kowa ba suka ɗauketa suka fita, hegiya ta ji maza ta sume.Ita kuma Ummie da aka tafi da amarya sai ta bi bayan Zaysh izuwa ɗakinsa dake gidan, kuma yana ma da ɗaki a gidan uncle ɗinsa, kawai Ummie ta matsa mashi su sauƙa a gidanta da safe sai suje gidan uncle ɗin ne, baya son zama a gidanta yanzu da ya kara girma, a da dai lafiya lou ya zauna lokacin yana yaro.Zaune ta iskosa yana danna waya, ya sanya sim card ɗinsa ta nan gida Naija, da alama wani abin yake son yi. A kusa da shi ta zauna zata fara magana kenan taga yasa waya a kunne, cikin sanyin murya suka gaisa da uncle ɗin nasa, sannan ya faɗi mashi ya dawo, sun iso lafiya. Watau Zaysh ɗan halak ne na gasken-gaske, dik da halin da matar uncle ɗinsu ta jefasu a ciki hakan bai hana shi yana yabawa uncle ɗin nasa kuma yana kara gode mashi ba, and kome zai yi sai ya fara sanar mashi kafin ya yi, tamkar uba haka ya ɗaukesa dan yasan ba laifinsa bane, ba shi ya muzguna masu ba, matarsa ce ta yi komai. Bayan sun gama gaisawa da uncle sun yi sallama ne ya miƙe tsaye, da sauri Ummie ta rike hannunsa tare da cewa. “Ina zaka je?”……. A taƙaice ya amsa da. “Wanka”. Sakesa ta yi tare da miƙewa tana faɗin ya zauna bari ta haɗa mashi ruwa. Da a’a ya amsa mata, ya kara da cewa ita da bata da lafiya, ta zauna shi bari ya haɗa da kansa tin da shi ai ba bakon gidan bane.Zama ta yi tana sauke numfashi a hankali-hankali, shi kuma ya fito ya ɗebi ruwa a bokiti ya wuce toilet dan ya yi wanka. ————————-🔥C-P.Basu dawo gidan ba sai da suka yi sallar ishai, sannan suka shigo. One by one suka tsala wanka, suka shirya cikin sleeping dress iri guda, sannan suka shiga ɗakin aikinsu. A gaban computers ɗinsu suka zauna, Lion ne ya kunna wani video na zanga-zanga da ake yi a ƙasar AVARIS, natsuwa dik suka yi suna kallon video mai tsawon mintuna 33, sai da suka gama kallo tsab sannan ya tsayar da video tare da cireta gabaɗaya.”What are you thinking?”. Lion ya faɗa tare da kunna wata recorder. Shiru dikkansu suka yi na a ƙallah 2 mins, sannan guru ya ce. “Batu ne a kan rashin tsaron dake Avaris ko?”……. Kai kawai Lion ya ɗan girgiza alamar a’a kallonsa a kan Champion da ya shiga duniyar tinani na daban. “Yakamata mu sanya ido a kan Avaris sosai, saboda rashin tsaro ya yi yawa, wahala da yunwa sun yawaita, abin mamakin kuma kasar Avaris ita ce ta uku a dukiya da karfin tattalin arziki da albarkatun ƙasa, meyasa kuma take zuwa matsayin sahu na gaba a yunwa, wahala, rashin tsaro, ma’aikata babu albashi, sojoji ba’a biyansu yadda yakamata, dik duniya babu barrack ɗin da ya kai AZURE yaye ɗalibai masu kaifi, fikira da basira, ga horo na musamman da ko ba bindiga zasu iya gwabza yaki, to amma meyasa sojojin basa iya kama ƴan ta’addan? Meyasa komai yake tafiya a juye?”. Guru ne ya faɗa cike da damuwa sosai a ransa. Champion ne ya ce. “Babu wani abin da yake tafiya a juye guru, komai a daidai yake tafiya cikin tsarinsu, sai dai ƴan kasar ne suke ganin kamar komai a juye masu yake saboda an juya tunanin kwakwalensu”. Ya faɗa without looking at them, da alama yana jinsu amma ba dikkan hankalinsa bane a kansu.One thing, da guru da Lion suna da alaƙa mai karfe da AVARIS and AZURE BARRACK shiyasa suke damuwa da ƙasar sosai, kullum aikinsu a kan shawo kan matsalar kasar ne, dan Avaris tana daga cikin top ten ƙasa masu shan bakar wahala a duniya, kuma tana cikin top ten na ƙasashe masu karfin tattalin arziki da albarkatun ƙasa da ruwa, to me matsalar? Abin da kowa ya gagara ganewa kenan, amma alƙalamina zai faɗa maku me matsalar!.”Zancenka gaskiya ne Champion, amma a tinaninka meyasa Avaris tana da yelwar arziki, ga wadataccen noma, idan ka duba a kididdigar da muka yi suna iya noma abincin da ƙasar zata iya ci ba tare da sun ji yunwa ba, meyasa suke fitowa neman abinci? Manoman dake noma suna fama da yunwa da bakar wahala, meyasa?”. Cewar guru…. A wannan karon Champion baya tare da su, so bai ma ji tambayar ba. Shiru ne ya biyo baya for almost 5 mins, dama shi Lion kullum a karshe yake magana, sai ya gama jin dik abin da zasu faɗ, ya gama jin ra’ayin kowa kafin ya faɗi nasa ɗaya tamkar da dubu. Kamar dai ni Princess Teema, sai na gama jin ra’ayin kowa nike faɗar tawa ra’ayin a karshe!.Jin room ɗin ya yi shiru ne yasa guru yasa hannu zai taɓa Champion Lion ya dakatar da shi tare da cewa. “Wannan abu ne da yake a tsare! Idan har aka bar Avaris da wadataccen abinci, suka ci suka ƙoshi to the next thing abin da zasu fara yi shi ne nemawa kansu da ƙasarsu cigaba wanda hakan zai haifarwa da WORLD SYSTEM damuwa”. Ya ɗan dakata kafin ya cigaba da cewa. “Kasan a duniya yanzu babu ƙasar dake da haziƙan mutane kuma ƴan baiwa irin kasar Avaris, sun san cewa idan jama’ar kasar suka farka to dik duniya sai sun jira, shiyasa suke kashesu da yunwa dan ma kada su samu kwarin gwiwar yin wani tinani bayan na abinci”. Cike da rashin fahimta guru ya ce. “To amma ta ya za’ayi a shiryawa babbar ƙasa irin wannan wahala da yunwa?”. Watau kun san me mutane? Su Lion karshe in dai a ɓangaren tinani da hangen nesa ne, ga karfin hasashen dake tabbata, wlh dik hasashen da suka yi tabbatacce ne. Ni dai a jikina ina jin Avaris exactly Nigeria tamu ta gargajiya, ku me kuke jinta? Amma mu je zuwa, alkalami ya fi tokobi! Kumun addu’ar in samu cikar burina na warware gaskiya a cikin wannan labari kamar yadda na so, wlh complete storyn nan ina ɗaukarsa tamkar gaske ne sai abin da ba’a rasa ba, tamkar yadda kwakwalwar su Lion take da kaifin hangen nesa da hasashe game da tinani haka ƙwaƙwalwata take, dikkan abin da zai faru da idon basira nike kallonsa, ina fatan dik wacce zata karanta littafin nan daga yanzu ba za’a sake raina mata wayau ba!. Shiru Lion ya yi na ɗan lokaci kafin ya ce. “Wannan abu ne mai sauƙi, manyan ƙasar sun zauna meeting na sirri da manyan ƴan kasuwa dake shigo da kaya, sun umarcesu da ɗaga farashin kayan abinci ta yadda talaka ba zai iya sayan foreign food ba, daga nan su kirkiro fitinar ƴan ta’adda suna shigowa sai a rufe wasu bodojin ƙasar”. Ya ɗan nisa kafin ya cigaba da cewa. “Idan suka ɗaga kayan abinci suka kuma rufe boda sai su ƙarawa takin noma kuɗi ta yadda takala dole ya ci bashi a lokacin yin nomansa, dan kuɗin da ya lissafa zai kashe a farko yanzu komai ya tashi ya ninka kuɗinsa, kuma dole ya saya dan yana buƙata, kafin ya gama noma bashi tai mashi yawa ta yadda yana cire amfanin gona dole ya biya mutane bashinsu, idan ya noma buhu goma ne, to buhu 6 zai tafi a biyan bashi, saura huɗun ba zasu ishesa ya ci a gida da iyali ba bare har a je ga lissafin ajiye wani kuɗin dan noman shekara mai zuwa, kaga kafin wata shekara ta zago ya sake cin bashi dan ciyar da iyalinsa, lokacin noma ya sake cin bashi dan nomawa, idan last year ya samu ragowar buhu 4 to this year in ya biya bashi da kyar ya tsira da buhu 2, a haka ake haifarwa da ƙasa mugun yunwa da wahala, shiyasa zaka ga kaya a wajen Avaris da mugun arha, amma a cikin ƙasan ya ninka kansa sau biyar”. “Kaga buhu biyu bai wuci ya ci na ƴan kwanaki ba, sun kare, kaga bashin da zai sake ci wannan shekara da ta fi ta wancan shekara kenan, idan ya ci ya gama noma abincin da ya noma ba zata isa ya biya bashi bama bare ya rage na ci, daga nan zai fara gudun biyan bashi, ya ci ba zai biya ba saboda babu yadda zai yi, idan ya biya bashi da abincin da zai ci a gida, yunwa ta mamaye ƴaƴa da ƴan uwansa, daga nan yunwar take farawa har ta mamayesu ta ko’ina, ga bashi da rashin madogara, makarantun yara ya tsaya, rashin sana’a, abubuwa su caƙuɗe, yunwa tasa dole yara su fara ɗauke-ɗauke, daga nan shaye-shaye”. Lion ya dakata hankalinsa a kan computersa. Champion ne ya ce. “Wannan ma naga ba zanga-zanga rashin tsaro suke yi ba bayin ALLAH, zanga-zangan yawan faɗuwar tamkoki mai da ake samu ne a kwanakin nan yana masu ɓarna, yana kashe masu al’umma sosai, shi ne suke zanga-zanga kan gwamnati ta biyasu gidajensu da wata tankar mai ta ƙona”. Guru ne ya kalli Champion da ya ajiye wayar dake hannunsa yanzu, dama tin ɗazun da kuka ga ya yi shirun nan sauraren wayar da Seraphina take yi da Rimsha a yanzu yake yi, yanzu ta sake kiran Rimsha tana faɗa mata tana tsoron gidan, kuma ita kaɗai ce, tana kuka tana faɗa mata. Gabaɗaya sai ya ji hankalinsa ya tafi kan ya je ya ganta, yanzu da suka gama wayar ne shi ma ya ajiye wayan nasa ya mai da hankali kan aikin da suke yi. Bai san dik abin da yake yi Lion na sane da shi ba, su fa mata haramum ne a wajensu, sun haramtawa kansu, kada ku ɗauka da wasa ake yi! Da gaske suke yi, yanzu idan har Lion ya kama Champion kan macece take ɗauke mashi hankali zai rabasu ne, saboda ba zasu tsayar da aikin da suka fara ba, kuma ga shi kunga zancen Lion ya fara tabbata, mata suna da ɗaukewa mutum hankali, kunga tin ɗazun maganar arziki ake yi shi kuma Champion ya tafi jin gulma na hirar su Rimsha, sun ɗauke mashi hankali. Guru ne ya ce. “Gaskiya kwana biyun nan ana samun fashewar tankar mai a Avaris sosai, kuma tana sanadin rayuƙa da dama, to motocin man ne dik sun mutu, amma manyan ƙasar sun kasa sayan sabbi”. Champion ya ce. “Kuma kansu zasu yi wa idan sun sayi sabbin ma, amma ba zasu saya ba”.Nisawa Lion ya yi tare da ɗaukar cube ya fara murɗawa, ya koma baya ya jingina da jikin chair da yake kai a zaune, sannan in cool way ya ce. “Da balain son kuɗin nan nasu kuna tinanin zasu taɓa yarda su karɓi asara ne? Kada ku manta fa idan man ya zube asararsu ce, to zasu yarda haka kawai su yi asara ne?”.Shiru su Champion suka yi suna nazarin kalamansa. Katse masu shirun ya yi da cewa. “Shi kansa faɗuwar tankan man plan ne ga ƴan ƙasa”…… Champion ya ce. “Confirm, suna sake tankar ne saboda abubuwa biyu, na farko ko su juya akalar tinanin al’umma zuwa kan wannan case ɗin su aikata wani babba laifi, ko kuma su faɗar da ita domin kashe mutanen dake yankin, da gayya suke faɗar da ita, ko direbobinsu basu sani ba, dik shiri ne, in ba haka ba ba ta yadda za’ayi su dinga tabka asara haka, yadda suke mugun son kuɗin nan”. Guru ne ya ce. “Na fi tinani suna yin hakan ne domin su ɗauke hankalin ƴan ƙasa su aikata wani babban laifi”. “Dalilai uku yasa suke hakan, na farko dan ɗauke hankalin ƙasa, ko zasu fitar da dukiyar ƙasa kamar su gold zuwa wani waje, ko zasu shigo da wasu manyan mutane cikin ƙasar, ko kuma zasu fitar da ƴan matan da suke sacewa ana kaisu waje dan kasuwanci da su ta hanyar karuwanci”. Cewar Lion. Jan numfashi Lion ya yi tare da sauƙewa a hankali kafin ya cigaba da cewa. “Idan sun shirya jefar da tankar mai, akwai wata chemical da ake cewa hydrochloric Acid, suna saita daidai in da suke son tankar ta fashe ne, sai su yi diluting ɗinsa da ruwa, su zuba ruwan da zai daidata chemical ɗin ya kuma ɗauki tsawon lokacin da zai isa wajen can ɗin, sai su zubawa tankar mai ɗin ta daidai in da suke son ya fashe, idan drivernsu ya ɗauki motar lafiya lou zai tafi da ita, wannan chemical ɗin tana cin wajen da aka zuba ɗin a hankali, sai ya isa in da suka tsara unexpected zai ga tankar ta fashe mai ya fara zuba, za’ayi duban duniyar nan a rasa dalilin fashewar tankar, dan chemical ɗin sam bata nuna alama, haɗewa sa ruwa take”. Ya dakata yana sauke ajiyar zuciya.”Yanzu me mafita?”. A cewar guru. Champion ne ya amsa da. “Yakamata mu tsaya tsayin daka dan tsabtace Avaris, gurɓacewarta ta yi yawa over, ga cin hanci ta yawaita”…….. Guru ne ya amsa da. “To jami’an Avaris ai dole ake tilasta masu cin hanci, shi ma wannan shiri ne domin jami’an su zama karnukan farautarsu, dole suke tikasta jami’an Avaris da su yi masu biyayya ta hanyar azabatar da su da karamin albashi, idan suka basu albashin da ba zai iya ciyar da su ko na sati biyu ba, kunga yunwa zata sanya dole su fara karɓar cin hanci dan ciyar da family ɗinsu, dole a wannan lokaci zasu karɓi dik wani aiki da na sama da su ya basu dan su samu abin da zasu baiwa ahali, yunwa ita ce babban makamin da shuwagaban Avaris suka rike wajen sanya kowa ya bautawa buƙatunsu, talaka na fama da yunwa an kawo mashi aiki da zai samu 10k dole zai karɓa ko dan yaran da ya baro a gida suna jiran baba ya dawo ya kawo aci abinci”. Ya kai karshe cikin tsananin takaicin abubuwan dake faruwa a duniyar yau.Nisawa Lion ya yi tare da cewa. “Ba laifin shuwagabannin Avaris bane, suma umarni ake basu ta yadda idan basu yi ba za’a kashesu, WORLD SYSTEM ita ce matsalar duniya gabaɗaya, kowani shugaba ya hau mulki dole zai bi umarninsu ne in har yana son ransa”. Guru ne ya ce. “Wai to su ɗin su waye ne?”. Champion ya ce. “Mutane ne kamar kai”……. Lion ya amsa da. “Haɗarinsu kuma ya fi nuclear, su ɗin ba mulki suke yi ba, ba shugabanci ba, hasalima basu a siyasa ko sarauta, su akewa laƙabi da masu naɗa mai mulki, su suke zaɓar shugaban da suke so ya yi mulki a kowace ƙasa, kuma dole ya yi masu biyayya ya aikata dik abin da suka sanya shi, idan ba haka ba, su kashesa ko su ɓatar da shi, su ɗin su ne ke juya duniya a yau, sai abin da suka so mutane su sani suke sani”. Ya ɗan dakata yana fito da bayanai a kansu a cikin computer dake a gabansa, bayanai ne da ya sha wahala, ya shafe tsawon lokaci yana haɗasu, dan shirya mission na musamman a kansu. Champion ne ya ce. “Suke juya sojoji ta sigar da babu wanda zai sani har su kansu sojojin, suke juya manyan da suka amsa sunansu manya, suke juya harta talaƙawa, dik wata ƙasa a duniya da kuke ganin kamar suna da power ko su ke juya duniya to ku sani suma umarni suke karɓa daga wannan team na WORLD SYSTEM ɗin, wannan WORLD SYSTEM ɗin su ke tsara komai da suke son ya gudana a kowacce ƙasa, baku ji sunansu ba? WORLD SYSTEM, su biyar ne, amma mutum ɗaya ya fi dikkan shuwagabannin manyan kasashe girma da karfin iko game da haɗari, kowa a karkashinsu yake ba tare da kowa ya sani ba”.Lion ne ya ce. “Sune a next mission namu”…….. Shiru room ɗin ya yi, dukkansu suna tinani daban-daban, lallai kuwa sun ɗauko dala ha gammo, mission kan WORLD SYSTEM, na yarda da gaske su Lion sun sayar da ransu, basu tsoron mutuwa, sun shirya mata a koda yaushe. Yanzu wasan zai fara, su Noor zasu yi mission a kan IRON FIST, su kuma IRIN FIST zasu yi mission a kan WORLD SYSTEM, kungiyar da suka fi haɗarin ma haɗari. Ni dai na shirya tsab dan bin kowani team a wannan tafiya, dik wacce ta shirya ta haɗo kayanta mu wuce, batu ake na gaskiya da gaskiya, reality amma a novel, get ready my people, wannan karon bamu zo da wasa ba!. Sun jima suna tattaunawa a kan wannan matsalar, har zuwa 12 na dare, sannan suka miƙe suka nufi dining room. Dinner suka ti sama-sama saboda dare ya yi, shi Lion ma green tea kawai ya sha, Champion ya sha Amercano, guru ya ɗan sha coffee, daga haka suka nufi room na Leo. Sun sha madarar mamakin ganin idanunsa biyu, ya dukufa a kan laptop dole-dole sai ya ɗan samu wata makama a kan IRON FIST, aiki tukuru yake yi, dik wasu kisan da IRON FIST suka yi sai da ya bankaɗo bayanai, amma babu wata makama ko alamar da za’a iya gane su. Dik kisan da zasu yi sun subarwa da mutum jini, bugu da kari sun fi yin kisa da poison ko Chemical, kansa ya ɗauki zafi sosai, ruwa roba biyar ya shanye amma bai iya gano komai ba, idan ya binciko wani kisa nasu sai ya miƙe ya fara kewaye a cikin ɗakin yana tinanin yadda aka tsaya komai, ya kewaye room ɗinsa ya fi sau hamsin, amma dai babu wata haske, tin yana aiki a kan gado har ya sauƙo ƙasa.Brothers ɗin nasa suna shigo ya ɗago ido a kansu, da sauri ya miƙe ya koma saman bed yana kallonsu. Ɗan kallon juna suka yi kafin su karisa in da yake, cike da damuwa ya ce. “My love please come and help, my brain is about to tarwatsewa wlh”. Champion zai yi magana Lion ya rigasa da cewa. “Babu wanda zai taimaka maka, da kanka zaka yi komai”. Daga nan ya kafawa su Champion dokar kada su kuskura ko da sunan wasa su taimakawa su Leo a kan wannan mission da zasu tafi, su je su yi faɗa da kansu su yi nasara, idan har zamu taimaka masu kenan babu amfanin su kaisu AZURE ai, su kam waye ya taimaka masu a lokacin nasu mission ɗin? Ba su suka kwaci kansu ba? Dan haka su Leo su kwaci kansu suma.Kuma Lion yana da gaskiya, kunga abin da ake jiran su goge su maye gurbinsu kenan wayau IRON FIST, idan suka fara tayasu aiki ta ya za’ayi su jajirce su zama mazan gaske? Ai kunga gara a barsu su ci ƙwaƙwa su tsira da kansu. Lion ya ce ko mutuwa suke yi babu wanda zai taimaka masu, bama zai bibiyu mission ɗin nasu ba, su je su fafata su zama mazan gaske, kuma da gaske yake yi wlh, dan ya gana su Champion ma bibiyar Mission ɗin nasu Leo, ya ce su fafata da kansu, suma su shiga tsananin rayuwa ko mutuwa, daga nan ne dik wata sauran tausayi zai bar ransu, zasu zama mutane in ji Lion.Da haka suka yi wa Leo goodnight bayan sun karfafa mashi gwiwa, suka wuce izuwa room ɗinsu. Hankalinsu a kwance suka kwanta, Lion ya ce ya basu nan da kwanaki biyu su yi tinani a kan WORLD SYSTEM, shi ma zai yi nashi tinani, after two days zasu sake yin zama a kansu dan yanke hukunci kafin su fara ainahin bincike a kansu!.Suna kwanciya ba jimawa Lion da guru suka yi barci, shi kuma Champion ya ɗauki wayansa ya duba layin Seraphina ko tana online, sai ya ga bata nan, ya kirata sau ɗaya da bata ɗauka ba ya fahimci ta yi barci, hakan yasa ya kashe wayarsa shi ma ya yi barci, ya so ne ya jita, dan kukan da ta yi ɗazun abin ya tsaya mashi a rai, ta faɗawa Rimsha ita kaɗai ce a gidan kuma tana tsoro.Kai inna biyewa rubuta komai fa zamu jima ba’a kai in da muke so ba, dan haka After some days. A ƴan kwanakin nan da suka wuce abubuwan da suka faru sun haɗa da Aryan ya ɗauko madam Rohisha da ƴar marainiyarta ya dawo da su wajen Seraphina, ya kuma nema masu school da suka gama dan komawa su yi senior set a can, ya kuma nema masu izinin dawowa gida su dinga kwana ba boarding ba, ya yi sa’a aka bashi, ya yi matuƙar murna sosai, dan baya son kwananta a school, gara mashi a C-P ɗin nan, dik time da ya tashi ya shigo ya duba lafiyarta. A gefe guda kuma su Noor soyayya ta kara kulluwa a tsakaninsa da V, yanzu sai shirin komawa barrack yake yi, nan da kwanaki uku zasu koma, kuma har yau basu haɗu da Leo ba, Leo ɗin ne ya ce bashi da lokaci, saboda yana nema kashe kansa a kan bincike, ba dare ba rana yana aiki ɗaya, har rama guyen nan ya yi, Zayra’an na ganinsa amma bai ce ko uppan ba, shi daɗi ma ya ji na ganin yadda kanin nasa ya dukufa kan aiki babu wasa babu kama hannun yaro, ko abincin kirki Leo baya ci, idan ya zauna a gaban computer sai ya samu wani ɗan haske yake matsawa, kansa tamkar zai fashe saboda ciwo, amma ya dage.Shi ma Noor ya dage da aiki babu kama hannun yaro, hakan yasa jiya suka yi faɗa da V, ta ce ya daina sonta, baya bata ishasshen lokaci, sati ɗaya baya da suka fara soyayya wuni suke yi manne da waya suna hira da juna, yanzu kuma idan ya yi mata message da safe sai ya shiga aiki, baya sake bi ya kanta sai can yamma, wayarsa ma kashewa yake yi, yana kara hora kansa da motsa jijiyoyinsa, a taƙaice dai basa waya sai dare, daren ma daga karfe 8 zuwa 10 suke waya sai ya ce mata goodnight, ko ta so ko bata so ba zai kashe wayar ya shiga aiki ne abinsa.Ba wai dan baya sonta ba, sai dan aikin dake gabansu yanzu ya zarce wasa, dole ya mayar da hankali idan ba haka bama Leo zai rabasu da ita ne, ita kuma bata gane ba, sai fushi take yi da shi, ya yi mata bayani amma bata gane ba, ita dai kawai lokacinsa take so, shi kuwa ya ce ta yi hakuri ba zata samu lokacinsa yanzu ba.To shi ne tun jiya ta yi fushi da shi, ya yi rokon duniyar nan a Whatsapp ta sauraresa taki yarda, daga karshe ma ta rufe wayarta, yanzu haka tin jiya bai ji voice ɗinta ba, dik ya kiɗime ya fita hayyacinsa, ga aikin da ta sha gabansa. Ya kira number Angelina da yake da shi, yasa ta bata waya amma ta ce ace mashi ya manta da ita, kada ya sake nemanta, Noor bai tashi sanin a sati ɗaya da ƴan kwanaki da suka yi suna soyayyar nan mugun sonta ya shigesa ba sai yau.Gabaɗaya yau ya gagara yin aikin ma, wlh sai kai komo yake yi tsakanin ɗaki da waje, ya rasa me yake yi mashi daɗi, jikinsa dik a mace, ita kawai yake tinani yake son jin muryarta, daga karshe ya yanke shawarar komawa AZURE gobe mai maimakon jibi, ya ce tin gobe zai koma dan ya samu ganinta ko hankalinsa zai kwanta. Jama’a kunga irin abin da Lion yake gudunwa IRON FIST kenan, shiyasa suka haramtawa kansu soyayya, da gaske ne idan kana soyayya wasu abubuwan ba zaka mai da hankali a kansu ba, kuma su a yadda suke ɗin nan dik yarinya da suka so ma sun cutar da ita ne, saboda sun san a kowani lokaci mutuwa zasu yi, bare yanzu da suke ƙoƙarin ɗauko mission ɗin da duniya dik ta gagara, abin dake ɓoye a cikin duhu suke shirin bangaɗowa duniya shi, kuma kun san gagarumin haɗari zasu jefa kansu, ga dai Noor, soyayya na neman hanasa abin dake da muhimmanci a kansa, ta yi fushi da shi ta jefa zuciyansa a cikin wahala da tinani, tasa ya gagara yin aikin dake gabansa, har yana tunanin zuwa wajenta gobe.A gefe guda kuwa Aunty Lisa na can tana abin da ta ga dama da zuciyar our daddy GAT ɗinmu, tasa bawan ALLAH ya zama yaro ɗan 20 years, sai juya shi take yi yarinyar nan, shi kuwa sai biye mata yake yi, ya zauna ya gama zuba mata sexy and romantic words yarinyar nan sai ta ce mashi. “Daddy all this fa westing of time ne”. Kuma ƴar kaniya har kwana mafarkinsa da kalaman nasa take yi, amma take cigaba da mashi abin da take so.Yau dai da ta kawo shi har wuya, ya yi ya yi su yi video call taki yarda, sai ya katse kiran tare da miƙewa ya koma gida, a take ya nemi bizar zuwa US, ga shi two days ago su Arya suka yi passing out ɗinsu, dama ya ce idan suka fita kafin su fara aiki zai kai su yawo, dan haka sai ya shirya masu tafiya gabaɗayansu. Da yamma jirginsu ya ɗaga sai US, bai sanar da su Arya ga in da zasu je kai tsaye ba, kazalika bai sanar da Aunty Lisa yana zuwa ba, while Noor bai san V na hanya ba, ya bari sai da suka yi dirar mikiya a airport sannan ya kira daddy Noor ya faɗa mashi suna US yanzu.Ai da sauri daddy ya umarci ƙaninsa uncle ɗin su Noor da ya ɗauki motoci da guards aje a ɗauko mashi bakinsa a airport. Noor bawan ALLAH yana ɗaki yana ta faman shirye-shirye kan cewa gobe zai wuce AZURE ya je ya ganta, ya gama shirya rucksack ɗinsa, yana kwance a saman bed rike da waya yana ta faman neman numberta. A daidai lokacin suka danno cikin gidan, da yake su kullum suna cikin yin baki daga ƴan siyasa, sarakuna, manyan ƴan kasuwa sai basu wani damu dan sun ji manyan baki sun zo ba, dik suna cikin ɗakunansu, Aunty Lisa na kan gado tana aikin wana hankalin GAT a Whatsapp ɗinta bata san ga shi ya shigo gidansu ba. Aunty Luna na kwance cikin bargo tana shirin yin barci, Aunty Lusi tana waya da wani abokinta, kunga Noor kuma yana ɗakinsa, kwanan nan da yake yasa aiki a gaba sam baya samun lokacin zama da su Aunty Lisa su sha hira.Tin da suka diro cikin ƙasar su V suka saki baki suna kallon haɗuwar New York, basu tashi rikicewa bama sai da suka shararo kan titin da zai sadasu da cikin CRYSTAL PALACE. Basu kaɗai ha har daddy GAT sai da ya juya ya saki baki yana kallon yanayin tsarin wajen, dogayen glasa tower dake wajen ya ilahi, ga shi dare ne kowani bene ya bada hasken sky blue light, abin ba’a magana. Kai tsaye sai side na gidansu Noor aka nufa da su, Arya dik kamewarta da basarwarta da suka shiga main parlon su Noor sai da ta zuba kauyanci, dan ta ga abin da bata taɓa gani ba, CRYSTAL PALACE ba dik kai ba wlh. Tun da suka shigo main parlo V ta ɗaura idanunta a kan hoton family dake manne a bango ta san ina suka zo, da sauri ta matsa kusa da Angelina, a kunne ta raɗa mata cewa wlh nan gidansu heartbeat suka zo.Da sauri Angelina ta ɗago tana kallon hoton dake manne a bangon ita ma, bata kai ga yin magana ba sai ga daddy Noor ya sauko ƙasa ta wata ƴar siririyar electric staircase. Fuskansa a ɗauke da fara’a ya tarbesu yanai masu sannu da zuwa. Da gudu V ta je ta rungumesa tana faɗin. “Oyoyo daddy”…… Su Arya dai suna baya suna kallonsa, while shi kuma daddy GAT yana ta faman baza ido yana neman ta ina zai ga tauraruwar tasa da ya yi wa bazata, bai san ma tana can tana faman danna mashi typing a Whatsapp ba, ko kaɗan bata kawowa ranta saboda ita zai iya barin dik abin da yake yi ya zo ba.Ita ma V sai baza ido take yi ƴar kaniya, burinta kawai ta hango heartbeat ɗin nata ko zata ji sanyin zafin da zuciyarta take yi mata tin jiya, ƴar kaniya dik tana firgice saboda tin jiya bata ji voice ɗinsa ba, haka ta zauna ta dinga kunna previous voice ɗinsa a Whatsapp ɗinta tana sauraro, amma taki yarda ta karɓi waya, wai ita nan ta yi fushi. Ai ganin iyayenta sai gaggaisawa suke yi, sun zauna zaman hiransu yasa ta ga bafa zata iya hakuri ba, cikin dabara ta ce. “Daddy ina Aunty’s and uncle ɗina?”. Ba tare da daddy Noor ya san da ita Noor yake waya ba ya amsa mata da. “Noor ina ga yana office ɗinsa dake kusa da room ɗinsa yana aiki, su Lisa kuma suna ɗaki”…….. “To daddy ina son ganinsu”. Ta faɗa a ɗan shagwaɓe. Da sauri ya kira robot dan ya yi mata rakiya. Nan fa daddy GAT ya ce su Arya dik su bita zuwa wajensu Lisa. Arya na ɗan haɗe rai suka miƙe zuka bi bayan robot ɗin, da yake horon AZURE ne su ko tsoron robot ɗin basu ji ba, kofar side na Noor ne a farko bayan na daddy, dan haka a nan robot ɗin ya fara tsayawa tare da ce masu nan ɗakin Noor ne. Da sauri V ta nufi kofar tana faɗawa su Arya su je wajen Aunty Lisa bari ta fara duba heartbeat ɗinta. Takaici ne ya kama Arya, a ƙule ta ce da robot ɗin. “Kaimu ɗakin da babu kowa sai gado”. Ita bata son zuwa wajen mutane ne sam-sam. Ba musu robot ɗin ya kai su in da suka buƙata, daga nan ya fito ya dawo parlo. Sai hararar robot ɗin Arya take yi kamar wacce aka yi wa dole, ita bata so su zo gidansu Noor ba ko dan haukace masu da V take yi a kansa, ta so daddynta ya kama hotel ne kawai.Lisa dai har yanzu bata da labarin GAT ya zo ƙasar ba, shi kuwa yana parlo suna hira da daddy, daga karshe daddy ya ce su je room ɗinsa ya yi wanka, sai ya zo su yi dinner. Da okey ya amsa, burinsa kawai ya ga Lisa, da haka suka miƙe zuwa room na kusa dana daddy Noor dan ya yi wanka a can.Murɗa handle na door ɗinsa V ta yi ta shiga, ɗan karamin parlo ta fara cin karo da shi wanda ya ji kayan more rayuwa, ga makeken hotonsa manne a bango yana murmushi a tsakanin three sisters ɗinsa. Hararar hoton ta yi tare da murguɗa mashi baki kamar Noor ɗin ne a gabanta take gani. Da sauri ta nufi in da take zaton nan ce bedroom ɗinsa.


