Halysaah Page 9 By Khaleesat Haydar
Still bai dago kansa ba yace “Tashi na kika yi” Ta ɗan bude ido tana kallonsa tace “How?” Ya koma ya kwanta ya rufe ido yace “With the noise ur utensils were making in the kitchen” At first kamar bazata ce komai ba, sai kuma tace “To ai ba nan ya kamata ka kwanta kana bacci ba” Ya bude ido yace “Ok u intentionally woke me up kenan?” tace “Ni ban ma san kana parlon ba ai…” Murmushi kawai yayi bai ce mata komai ba, tana ɗan kallonsa a hankali tace “I made some breakfast, you can have some” Yace “Ok thanks, baki je schl yau ba?” Tace “Ba mu da lectures” Yace “Ohk, wani school kike?” Shiru tayi tana kallonsa, ya mike zaune yace “University of Maryland Baltimore? Loyola University Maryland? Morgan state University? Stevenson University? Johns Hopkins University?” Tace “Duk kuma a nan garin su ke?” Yace “Ohh, kina gari baki san makarantun dake garin ba?” Ta girgiza masa kai kawai still looking at him, shi dai bai kalleta ba yace “To ke wanne kike zuwa a cikinsu?” Ta sauke idonta tace “Na karshen da ka kira” Ya ɗan yi murmushi yace “John Hopkins kenan? Buh ni ban taɓa ganin ko me kama dake a schl din ba ai” Yayi dariya yace “Just joking kafin ki fara min kuka” Ta wani kallesa, duk wannan abun bai kalli direction dinta ba yana magana ne yana kallon agogon wrist dinsa, yace wani course kike yi?” Tace “Pharmacology” Sai a sannan ya kalleta yace “Really?” Ta gyada masa kai, yace “That’s a very good course, year what kike yanzu?” Calmly tace “Year 3” Ya gyada kai yace “Good, Allah ya bada sa’a” Ta sauke idonta tace “Ameen” Yace “Ban yi tunanin makarantar kike ba da na dinga dropping dinki in zan je ai, ko da yake ba lallai sanda zan je kina da Class ba….” Sunan wani lecturer dinsu ya kira mata, kawai ta ɗan yi murmushi tana kallonsa cause he is one of her favourite lecturer, yace “He took us during our Undergraduate Degree, and Master’s degree also, that was 3 years back, and he is still among my Supervisors currently….” Khaleesat dai sai kallonsa take, ta kasa hakuri har sai da tace “And you are still a student till date?” Ɗan murmushi yayi yace “I am a Medical Dr, pursuing my PhD on Cardiology” Khaleesat couldn’t stop staring at him, Yace “I have been studying since i was a baby” Tace “Amma lecturer kake son zama?” Er dariya yayi yace “Not at all Halysaah….” Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba tana kallonsa, ya dau wayarsa da ake kira ya mayar ya ajiye yace “Kin ci abincin ne a kitchen naga ban ganki da plate ba as usual?” Ta wani kallesa bata ce komai ba ta juya tayi wucewarta daki, shayi ta sha da cookies a kitchen sanda take girki, bayan ta gama girkin kuma taji bata ma jin yunwan shi sa bata zuba abincin ba, Khaleesat ta koma dakinta da kusan 45 minutes tana duba wani course dinsu ta laptop taji kamar ana knocking din kofar parlor, ta mike ta fito parlorn, tsaye taga Housemate dinta bakin kofar living room din har ya bude kofar, Safiyyah ce ta shigo parlon tana kallonsa tace “Hello” Ya dauke idonsa yace “Hi” Komawa daki Khaleesat tayi, Safiyyah tace “Pls is Khaleesat around?” Yace “Sure….” Dakin Khaleesat ta nufa, shi kuma ya tafi ya ci gaba da karatun da yake a parlor, Khaleesat ta mike tana kallon Safiyyah bayan ta shigo dakinta tace “Why are you looking this way Sophie?” Safiyyah tace “Wallahi kwanan nan zaki ji nayi ma matar can duka a kasar nan” Khaleesat tayi murmushi tace “Me kuma tayi maki again?” Gefen gado Safiyyah ta zauna kana ganinta kasan ranta a bace yake tace “Tun fa da kika je gidan mugun halinta ya ninku akan wanda take min a baya Khaleesat, she is trying all possible best to make the house miserable for me, dama yanzu ta dena ajiye min abinci kwata kwata, cornflakes da Golden morn sai ta boye a dakinta da sunan taje hada ma yaronta ne duk don kar in sha….” Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace “To Allah ya kyauta, ko zaki dawo nan?” Safiyyah tace “In dawo nan for what reason? ashe ma riba ta ci kenan idan na bar mata gidan, ai we die together with her in that house, babu inda zan dawo wallahi, kawai rabon ta ci duka ne ba wani abu ba” Lkci daya expression din Safiyyah ya canza daga bacin rai ta kamo hannun Khaleesat tana washe baki tace “Kee naga Housemate dinki ido da ido yau, dama haka yake gayen? Wallahi he is so well flavoured komai yaji, ina masa magana ma ko kallona bai yi ba amma ya amsa min cikin girmamawa, wallahi ya burgeni” Tana blushing ta karasa maganar nata, Khaleesat dai ta saki baki ta kasa cewa komai, can ta kalli kofar dakinta da sauri don ta tabbatar a kulle yake kar ace yana jiyo Safiyyah, sai kuma tayi kasa da murya fuska daure tace “Meye haka Safiyyah what if yana jin ki?” Safiyyah tace “Wallahi raina a bace yake amma yana bude kofar kawai na mance da abinda er iskar matar can ta min, a very calm gentleman, yace min Hi nace Hello… kuma kuna Hausa da shi ko turanci ku ke? Ni sai nake ga kamar ba bahaushe bane ba fa” Khaleesat ta hade rai sosai tace “Don Allah ki rufa mana asiri Sophie, What’s all this?” Safiyyah tayi dariya tace “Ni dai kinyi girki? Don wallahi yunwa nake ji” Khaleesat ta mike ta nufi kofa ta fita daga dakin, a corridor ta gansa zai shiga dakinsa, bai kalli ma wanda ya bude kofa ba yayi shigewarsa daki, Khaleesat ta tafi kitchen ta dibar ma Safiyyah abincin da ta girka, jin alamar har ya fito daga dakin nasa ta dawo parlor ta tsaya sai gashi ya shigo parlon, makullin motarsa taga ya dauka da wani littafi, ya daga kai suka hada ido ta fara kame kame tace “Ain’t you eating the food?” Yace “Oh, ok na manta” Kitchen din taga ya nufa ta bi sa da kallo, sai da ya shiga sannan ta bi bayansa zata gaya masa kar ya bar mata plate bai wanke ba, tsaye ta gansa kusa da abincin ya dau spoon ya bude tukunyar sannan ya debi shinkafar kadan ya kai baki, kallonsa kawai take da mamaki, ya juya ya kalleta yace “Bad habit right?” Sake dibar abincin yayi ya kai baki, daga haka ya rufe tukunyar yace “Kinga ni ba yunwa nake ji ba, I am full” Ta dinga kallonsa, bata san sanda tace “Ko in zuba maka ka tafi da shi?” Ya bude fridge ya ciro bottle water yace “Aa in na dawo anjima zan ci” Daga haka ya fita daga kitchen din ya nufi kofar living room ya bude, sai a sannan ya juya, ta dauke idonta, yace “See yah” Fita yayi ya kulle kofar daga waje. Sai wajen karfe shidda na yamma Khaleesat ta raka Safiyyah zata hau Uber da tayi ordering, Safiyyah na kallonta tace “Ya Mustapha dai ya hakura dake, jiya nake gaya masa gaskiya kina da wanda zaki aura a gida, don nima na gaji da damuna da yake yi shi sa kawai na gaya masa, ai ko ina gaya masa yace to shikenan dama tun farko ai da kin gaya masa he will understand” Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace “To ai kinga gwara haka” a haka suka rabu Khaleesat ta koma cikin gida, har goma na dare bata ji shigowar housemate din nata ba hakan yasa ta gane bazai dawo gidan ba ranan. Washegari da safe ta shirya ta tafi makaranta, bata dawo gidan ba sai kusan karfe hudu na yamma, tana shiga living room ta gane ya dawo gidan da bata nan, bedroom dinta ta wuce bayan tayi wanka tayi sallah ta canza kaya ta fito kitchen zata yi ɗan wake don shi ne a ranta, bayan ta gama hada duk ingredients din taji an bude kofar parlor, ta dai ci gaba da abinda take, kitchen din ya shigo ya ajiye ledan hannunsa yace “Good evening Halysaah” Tace “Ina yini?” Yace “Lafiya lau, Are you baking?” Ta kalli flour din da take kokarin kwabawa tace “No” Yace “What are u using flour for?” Bata yarda su hada ido ba tace “Dan wake” Da mamaki yace “Meye shi?” Ta wani kallesa ganin da gaske jiran amsarta yake tace “Dan waken ne baka sani ba?” Yace “Ban san shi ba” Tace “Toh zaka gansa” Turning stick ta dauko ta fara kwabin danwaken shi dai yana tsaye yana kallo, yace “Hey, why did it change to that color? Ko dai ba flour bane?” Ta ɗan kallesa amma taki basa amsa, yana ta kallo with astonishment har ta gama kwabin, sannan ta wanke hannu ta fara saka dan waken a ruwan dake tafasa kan gas, shi dai kallonta kawai yake, can yace “To haka ake cin sa?” Tace “Aa da bread ake ci” Sounding amused ya kalli sauran bread din dake a kitchen din yace “Really?” Bata san sanda tayi murmushi ba batare da ta sake ce masa komai ba don taga da gaske ya yarda da Bread za a ci ɗan waken, he couldn’t stop looking at her and the food har ta gama, ya ga ta soya man gyada, sannan tayi dishing din abincin a plate, ta saka eggs din da ta bare a gefe, ta dauko roban yaji, yace “Dama wai wannan abincin ne? To ai na san sa when i was a kid, idan munje wajen Grandma dinmu tana mana” Without looking at him tace “Da ka girma ne ka dawo America ka mance sa kenan” Dariya yayi ya karasa cikin kitchen din yace “Ohk, Can i taste some inji yanda yake?” Komawa gefe tayi bayan ta saka cokali a danwaken, ya dau cokalin ita dai kallonsa kawai take har ya ɗan juya ɗan waken ya debi seed biyu ya kai baki, she couldn’t stop looking at him yana tauna abincin gently as if trying to figure out the taste, can ya karyar da kai yace “It’s nice, i like it, i still remember the taste, it’s nice” Murmushi kawai tayi, ya sake diban abincin ya kai baki, tace “To kaje da shi, i will make another one” Yace “Aa bazan iya cinyewa ba ai” Yana fadin haka ya dauko wani plate din ya debi ɗan kadan a ciki yace “Thank you” Ta karasa ta amsa cokalin a hannunsa ta kara masa ɗan waken ta saka masa kwai daya, ya kalleta ya ɗan bude ido yace “Thanks Halysaah, but seriously I can’t finish all this” Tace “Eat and remain” Ruwa ya dauka a fridge ya fita daga kitchen din. Khaleesat na idar da sallan Isha’i ta fito parlor zata dafo black tea don tana son tayi karatu har zuwa karfe dayan dare, tunda ta shiga daki daxu da yamma bata sake fitowa ba sai lkcn, bacci ta tarda Housemate dinta yake yi a 3 seater, da mamaki take kallonsa ganin wai bacci yake bayan Isha’i, ita bata ma san yana gidan ba sai yanzu da ta fito, kallon wayarsa dake gefensa tayi ganin yana haske, ta leka screen din taga an rubuta A-jay, kiran na katsewa taga 5 miss calls aka yi masa, kamar ta tashesa sai kuma dai bata yi hakan ba, ta dau wayar kawai tana dubawa taga babu password balle pin a jiki, cire wayar tayi a silent mode sannan ta mayar inda ta dauka tayi wucewarta kitchen, ta gama dafa shayi ta fito parlon kenan taji wayar ya fara ringing loudly, da kyar ya bude idanuwan sa, ita dai ta koma kusa da kofar kitchen din ta makale a jiki, ya ɗan kalli wayarsa ya jawo yana duba screen din, ɗaga kiran yayi ya kai kunne yayi shiru har sannan yana lullumshe ido, can ya ja tsaki ya ajiye wayar sannan ya mike zaune, har sannan bai ganta ba ita ma bata bar jikin kofar da ta makale ba, mikewa tsaye yayi daga karshe yana lumshe ido, gani tayi kamar baccin yake yi a tsayen, ta wara ido tana kallonsa with shock , sai da yaga ya kusa faduwa sannan ya bude idonsa sosai, ta kai hannu bakinta saboda dariyar da taji ya taho mata, tafiya yayi ya isa jikin pillar dake parlon ya jingina ya rufe ido, kasa daina kallonsa tayi da mamaki, he stood there for almost 3 minutes yana bacci, ringing din wayarsa ne yasa ya bude ido da sauri as if frightened, kitchen ta shige don bata son yin dariyar da ya taho mata a wajen, sai a sannan ya ganta bayan ta shige kitchen da sauri, ya fara bin parlon da kallo as if trying to understand what was happening, lkci daya idonsa yayi clearing gaba daya ya fara sosa kai, at first bai yi niyyar bin ta kitchen din ba, can kuma dai ya nufi kitchen din, ta ajiye kofin shayin hannunta ta dafe cabinet tana dariya ciki ciki, tana ganinsa ta hade rai tana juya shayinta da cokali as if nothing happened, fridge ya bude ya dau ruwan gora yana kallonta yace “You are still awake?” Ta ɗan kallesa tace “To karfe nawa ne yanzu da zan yi bacci, as if i am you” Bai ce komai ba ya fita daga kitchen din, murmushi tayi ta bi sa da kallo, daukan shayin tayi ta bi bayansa, taga ya dau makullin motarsa da waya without looking at her yace “Good night Halysaah” Bata san sanda tace “To kar fa kaje kana driving bacci ya dauke ka a kan steering” Bai kalleta ba sai murmushi da yayi kawai ya nufi kofa, ta bi sa da kallo har ya fita sannan ya kulle kofar ta waje, karasawa kusa da window tayi ta ɗan bude curtain kadan tana kallonsa har ya shiga motarsa a garage yayi reverse, sai da ta daina hangen motarsa sannan ta sake curtain din a hankali, tafi minti uku a tsaye wajen ta jingina da window, daga karshe tana tafiya a hankali ta wuce dakinta bayan ta kashe wutan parlon….. Washegari Khaleesat na sauka daga Lyft bayan ta dawo school taga motar Housemate dinta heading toward the garage, kafin ta karasa apartment din nasu har ya shiga ciki, murda kofar tayi taji a bude ya bar mata alamar ya ganta shi ma, tana shiga parlon yana fitowa daga kitchen rike da Lemon gwangwani me sanyi, ya karaso cikin parlon yace “Are you just coming back from school?” Gaishesa tayi, yace “Good evening Halysaah” Bedroom dinta ta wuce ta bar sa a parlon, it’s almost 6pm na yamma kuma Safiyyah ce ta bata masu lkci tana mata bayanin wani course dinsu da tace bata ganewa, wanka Khaleesat tayi ta sauya kayan jikinta zuwa kananun kaya sannan ta saka hijab ta fito parlor, yana parlon har sannan yana operating laptop dinsa, ganin zata shiga kitchen yace “Ki bari ki hutu, zan fita sai na siyo abinci” Khaleesat ta kallesa tace “I am cooking noodles” Yace “Ohk then” Tana fadin haka ta wuce kitchen, Ya mike ya wuce dakinsa da laptop dinsa, cikin mintunan da basu da yawa Khaleesat ta gama dafa noodles din da take, ba da yawa ta dafa ba don bata san ko zai ci ba, zata yi dishing din abincin a plate taji ana knocking kofar parlor, ta ajiye plate din hannunta sannan ta fito daga kitchen din, Housemate dinta ta gani har ya fito shi ma to check on who is at the door, amma ganinta kawai ya juya ya koma dakinsa, karasawa tayi ta bude kofar, lkci daya taji komai ya tsaya mata cak ta dinga kallonsa babu ko kiftawa kamar ranan ta fara ganinsa, Yana kallonta daga sama har kasa yace “Meye kike kallo na haka Malama?” Tayi wani yake zuciyarta na bugawa tana in-ina da kyar tace “Ya Abdul, I.. I.. was surprised, san..nnu da zuwa” Da sauri ta juya ta koma parlon, ya bi bayanta yana duba wayarsa dake vibrate a hannunsa alamar ana kiransa, ita dai ta koma bayan kujera ta tsaya kamar munafuka tana kallonsa zuciyarta na bugawa sosai, kana ganinsa kasan ba a lkcn ya shigo America ba, probably tun daxu ya shigo ya sauka hotel, ya ɗaga kiran da ake masa ya kai kunne, tana ganin haka ta juya ta nufi corridor din dakunan apartment din tana waige waige, ganin attention dinsa na kan wayar da yake ta bude kofar dakin Housemate dinta ta shiga da sauri ta kulle kofar, Housemate dinta ya juya yana kallonta da mamaki, gaba daya a rude take ta nufesa tana yarfe hannu ta duka kusa da shi, ya mike still looking at her with surprise yace “Are you alright Halysaah?”07087865788✍🏻
