Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 66 Complete Novel
![Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt](https://aihausanovels.com.ng/wp-content/uploads/Screenshot_20231027-164547-300x250-1.png)
ASM Bk2066*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
………Tun bayan data shiga ta gaishe da shi ya amsa bata k’ara ce mashi komai ba ta juyar da kanta tana kallon gefen hanya, lokacin da suka iso Unguwar suna zuwa gab da gidan su ta juya ta kalle shi yana kallonta ta mirror ta d’an cije baki had’i da d’an yamutsa fuska, dage mata gira yay ba tare da ya kalleta ba yace “What?” A marairaice tace mashi don Allah ya bari ta shiga gida ta gaida gwaggo idon ta akan shi taga ya d’an girgiza kai alamar a’a, 6ata rai tayi idanunta sukai rau rau tana ta d’an kikkafta su bata yi tunanin zai k’i barin ta ta shiga ba, suna shiga kwanar gate tace mashi ya aje ta anan ta shiga ta k’aramar kopa ya parker ba tare da ya ce komai ba, saida ta juya zata bud’e kopar taji voice d’in shi yace ta bari wani time zata je yanzu in taje za’ai mata fad’a ne, juyowa tay ta kalle shi fuskarta a d’an kwa6e ya bud’a mata ido alamar taji ta jinjina mashi kai sannan ta juya ta bud’e, bayan ta fita yaja Motar ya tunkari gate ita kuma ta shige, tana isa part d’in a bakin kopar parlor ta cire takalmanta kafin ta wuce ciki, tana shiga Bedroom tay sensing k’amshin Haisam a ranta ta raya ko ya shigo d’akin ne, wata zuciyar ta ce k’ilan wanka yazo yayi, wucewa tayi ciki ta aje jakar ta ta cire Hijab sannan ta dawo wurin gado ta fad’a alamar ta kwaso gajiya, tana kwanciya taji k’amshin ya cika mata hanci fiye da yadda taji shi da ta shigo, hancinta ta kai jikin zanen gadon ta shinshina nan ta tabbatar da k’amshin shi ne ke tashi a jikin zanen sosae, cigaba da bin jikin zanen tai tana sunsunawa kafin ta d’ago mamaki shimfid’e akan fuskar ta, tambayar kanta ta shiga yi mi zai kawo k’amshin shi haka a wurin in dae ba kwanciya yay ba wata zuciyar ta bata kwanciyar yayi kenan, jikinta ne yay sanyi tay shiru a ranta tana raya kenan had’a gado da ita ne bai son yi, sosae abun ya dame ta don har Fuskar ta ta bayyana, ta d’an d’auki lokaci haka can ta tuna da bata yi salla ba ta saukko jiki sa6ule ta wuce laundry room, Alwala tayo tazo ta kabbara salla har ta gama bai shigo ba ta wuce Toilet don tayi wanka, bayan ta fito shiryawa tay cikin sabuwar doguwar rigar Atamfa tana tsaye a gaban mirror tana d’an yin light make up yayin da a ranta take ta juya kwanciyar da yayi akan gadon tana haka ya turo k’opar ya shigo suka had’a ido ta cikin mirror d’in, ganin yayi tsaye yana ta kallon ta ba tare daya ce komai ba yasa ta juyo ta kalle shi lokacin yace mata ga Abinci can an kawo ta fito ta ci ta d’aga mashi kai daga haka ya juya ya fita ta bi shi da ido, Bayan sun gama cin Abincin ta gyara wurin ta wanke komai a ranta ta yanke tafiya part d’in Hajiya don ta bashi wuri k’ilan ya k’ara kwanciya kan gadon in zai yi bacci, tana can har yamma suka fara aikin girkin dare da Saude, suna cikin yin girkin ne ta tambayi Sauden akan yau da safe ita ta dafa mata indomie, yar dariya tayi don ta d’ago dalilin yin tambayar tata tace mata ba ita ta dafa ba wanda ya kai mata shi ya dafa, ganin Fatun tayi d’an jimm yasa tace mata tayi mamaki ko ta d’aga mata kai tace “nima sosae nai mamaki lokacin dana fito na gan shi a cikin Kitchen yana dahuwar, na kuma rud’e don abu ne da ban ta6a gani ba, ni tunda nike da shi ban ta6a ganin yazo ko bakin Kitchen d’in nan ba balle ta kai shi da yin girki, bamma yi tunanin ko ruwan zafi ya iya dafawa ba sai gashi da yin girki kuma da ga ji Abincin yayi dadi don baki ji yadda k’amshi ya cika wurin Kitchen d’in ba” Murmushi kawae Fatuu ke yi a cikin ranta tana raya a haka kai kace Saboda yana son ta ne yayi amman kawai kulawa ce, ji tay Sauden ta k’ara cewa “ni bansan zaki Makarantar bane ai da nayi maki Breakfast din da wuri, saida ma nace ya bari in yi amma yace in bar shi kawae dai in rink’a tashi da wuri ina maki” shiru Fatuu tay still da murmushi akan fuskar ta Saude ta shiga tsokanar ta tana fad’in ai daga yau da tayi sallar Asuba bazata koma ba kar tayi ma Ango laifi kan Amaryar shi, sai bayan da tayi sallar isha’i ta koma part d’in su tare da Abincin nasu, lokacin da suka yi shirin kwanciya tana zaune akan gado tana yin rubutu ya shigo tana ganin shi ta san mi ya shigo yi da kanta ta d’auki pillow d’in ta mik’a mashi ya amsa Fuskar shi a sake ya furta mata thanks da kuma Gud night ya juya tabi shi da kallo ta d’an kwa6e fuska.
Ranar Laraba bayan ya d’aukko ta daga Makaranta sun gama cin Abinci ta gyara wurin, tana cikin Bedroom ya turo kopa ya shigo tana zaune a bakin gado ta juya ta kalle shi, daga bakin gadon ya tsaya Fuskar shi a sake itama da murmushi take kallon shi ya d’an d’auki lokaci ta fahimci kaman wani abu yake son cewa amman kuma yayi shiru, tambayar shi tay ko akwai abunda zata yi ya girgiza mata kai slowly taji yace in tana so taje gida yanzu da daddare zai zo ya d’aukko ta, waro ido tay baki bud’e take kallon shi ta kasa ce mashi komai don Maganar tazo mata a bazata, ganin yadda tayi yasa shi d’an d’age mata gira yace ko bata son zuwa ne aikuwa da sauri ta mik’e tana girgiza mashi kai had’i da yin murmushi ta hau yi mashi godiya farinciki bayyane akan fuskar ta ta nufi wurin wardrobe don ta shirya ya bita da ido, ba 6ata lokaci ta gama shiryawa da wata rantsattsar sabuwar shadda a cikin kayan da aka kawo mata ta ca6a ado ta fito a Amaryar ta sak sai k’amshi take bazawa, lokacin da ta fito yana zaune akan kujera yana lallatsa Computer ya d’ago ido yana kallon ta har ta k’araso ta tsaya daga gefen shi tana ta murmushi shima murmushin ya mayar mata tace mashi ta tafi ya d’aga mata kai ta juya, har ta fice idon shi na akan kopar sai bayan wani lokaci ya janye idon ya maido shi kan abunda yake, tana tafiya tana faman sakin murmushi sai kace wadda ta shekara bata je gidan ba, lokacin da ta iso kopar gidan shagon Kawu Amadu a kulle yake dama tunda suka wuce da aka d’aukko ta daga Makaranta taga shagon a kulle, a ranta ta raya k’ilan yana Makaranta daga haka ta shige cikin gidan, daga bakin k’opa ta tsaya tsakar gidan wayam ba kowa tana murmushi ta kwad’a sallama ba’a amsa ba saida ta k’ara d’aga murya tayi wata sallamar sannan ta jiyo Muryar gwaggo ta amsa, d’an lek’o da kanta tayi don taga waye nan tay arba da Fatuu dake tsaye tana mata murmushi, hannu gwaggo ta kai ta rufe baki sai kuma ta janye kan ta koma ciki bada jimawa ba sai gata ta fito hannun ta ruk’e da tsintsiya ta d’agata alamar bugun Fatun zatayi ita kuwa mi zatay in ba dariya ba ta nufe ta da gudu suna had’e wa ta k’ank’ame ta gaba d’aya harda tsintsiyar, dariya itama gwaggon tasa tana fad’in waya fito da ita Fatun tace Ya Haisam din ne ai yace tazo ko, d’aki suka nufa Fatun tay ma gwaggon side hug, bayan sun shiga a bakin gado suka zauna idon su a cikin na juna sai faman dariya suke ma juna, sosae gwaggo taji dad’in yadda ta ganta duk da Fuskar ta ta d’an fad’a amman wannan dama tun kafin ta tare ne Saboda ciwon laulayin da tayi amman ta k’ara haske fuskar ta sai sheki take fatar nan tayi lukui ko d’igon k’urji babu, Fatuu ce ta katse shirun ta gaishe da ita bayan ta amsa ta tambayi suna lafiya tace mata eh,
“Amman ya akai kika fito haka da wuri, bana ce banson ki rink’a zaryar zuwa ba miyasa wani lokacin baki jin magana” tay Maganar ta d’an d’aure fuska, a shagwa6e tace “Wllh shine fa yace in zo…” tunkan ta rufe baki ta katseta “to tunda kin matsa ba dole yace ki zo ba” da sauri ta ce mata wllh bata matsa mashi ba nan ta kwashe yadda akai ta fadi mata gwaggon ta gyad’a kai alamar ta yarda, tambayar ta tayi Kawu Amadu tace bai dawo ba yana Makaranta tace dama saida tayi tunanin haka, hira suka shiga yi kai kace sun dad’e da rabuwa, suna cikin yin Hiran Fatuu ke mata Maganar kud’in da suke a cikin Account d’in ta tace ana ta ajiyar su zata turo mata tayi wani abun dasu, gwaggon na yar dariya tace to ita mi zata yi da su tunda nata ne tayi wani amfanin dasu mana, tace ai ita ba abunda zata yi dasu,
“amman tunda kince zaki d’aukko Mino ba sai kiyi amfani da su ba wurin karatun ta” yar harara gwaggon ta wurga mata ta d’an girgiza kai tace “Ke da na d’aukko ki na amshi kud’in karatun ki ne, tunda ni nasa kaina ai bazai gagare ni ba” shiru suka d’an yi can ta sake cewa “ina ganin ko a tura ma Baffan ki sai a siya maki shanaye dama rannan yake man Maganar Sadakin ki duk da Ard’o ya amshi wasu amman yace zai cika maki kinga sai a had’a da d’an kunnan zinarin ki a canzo” da sauri Fatun tace ita dai ba sai an bata wani sadaki ba suyi amfani dasu kawae gwaggo na yar dariya tace ai sai ta kira Baffan nata ta fad’a mashi tace to, sai can yamma Amadu ya dawo shima sosae yay farin cikin ganin Fatun anan d’akin Gwaggon ya zauna harda sakata ta d’ebo mashi Abinci a Kitchen tace to gwaggo na dariya tana fad’in yanzu fa Yayar shi ce ita ya zai sakata aiki, shima dariyar yake yace “haba dai yaya ta, ai koda goma ta lalace tafi biyar Albarka kuma ba’a ta6a canza ma tuwo suna ai”, bayan ta kawo mashi Abincin suka cigaba da hira Kawu Amadu nata tsokanar ta yana fad’in wai ita nan Matar aure ce ko shi ganin abun yake kamar wasa gwaggo tace “ai dole kaga hakan tunda kai baka da niyya ko Maganar auren ma banji kana yi ba” yana dariya yace “ai shi lokaci ne, ita ai tama fi ni rashin niyyar auren tunda kin ta6a ganin saurayi yazo kopar gidan nan wurin ta Saboda bata basu dama, komai tace ita likita zata zama sai ga shi ta tafi gidan Romeo karatun likitancin” gaba d’aya sukai dariya, ana gama sallar isha bada dad’ewa ba Haisam yazo shima yasha shadda wadda ta hau da ta jikin Fatuu don ajikin aikin tata akwae kalar daya sa sai baza k’amshi yake, a parlor suka zauna suna gaisawa da gwaggo ta k’ara yi mashi godiya sosae nan tace bari a kawo mashi Abinci yace a’a a barshi bai jin yunwa, daga baya sukai sallama taje tay ma Fatuu dake cikin d’akinta Magana suka fito tare ta rako su har kopar gida, bayan sunyi sallama da Amadu ya rako su har bakin Mota suka tafi, mik’ar hanya Fatuu taga yayi suka fito daga Unguwar suka hau titi sosae tana ta kallon hanya, wani k’aton Shopping mall suka je bayan ya parker Motar a inda aka tanada yace ta fito, da kanshi ya d’aukko shopping cart tana tsaye yazo yace ta d’auki duk abunda take so, rasa abunda zata d’auka tay don gani take kusan komae tana dashi k’arshe dai sai shi ya shiga d’aukar mata kayan har saida cart d’in ya cika ya bata yace ta kai wurin biyan kud’i sai ta d’aukko wani aikuwa ta marairaice mashi a shagwa6e ta hau rok’on shi kan a barsu hakanan itafa tana da komai, har jakunkunan kayan da Hajiya ta aiko mata ta fad’i mashi don a tunanin ta ko bai sani ba, k’arshe dole aka barsu hakanan d’in suka je suka biya aka kai masu kayan Mota bayan an juye a manyan Shopping bags, bayan sun baro wurin wani babban Cafe ya kaisu yace ta fito su ci Abinci, sosae Fatuu taji dad’in wurin kowa ya za6i abunda yake so aka kawo mashi da suka gama su ka tafi, a gaban wani babban cold store ya k’ara Parker Motar yace mata yana zuwa ta d’aga mashi kai bayan ya fita ya zagaya ya shiga wurin tana ta kallon shi ta cikin glass, ruk’e da babbar leda mai d’auke da tambarin wurin ya fito ya zagaya driver side d’in ya koma ciki, saida ya mik’a mata ledar sannan ya ja Motar, yana ta driving ganin ta aje ledar akan cinyoyin ta bata ko bud’e ba yasa shi d’an kallon ta yace nata ne, da d’an murmushi tace mashi Thanks har saida ya sake juyowa ya kalleta yaga tana dariya dama ya gane kwaikwayon shi tay, maida idon yay kan hanya yaci gaba da driving ita kuma ta bud’e ledar, su ice cream ne da youghort ta fiddo ice cream d’in ta fara sha, lokacin da suka iso gida tare suka d’auki kayan suka nufi part dinsu, saida ya kai mata su cikin daki sannan yace mata yana zuwa ya fito ya nufi part d’in Hajiya, cire gyalenta tayi ta hau jera kayan cikin Wardrobe harda nata dama tana ta so ta jera su, sosae taji dad’in kayan ba kamar English wears d’in ciki don tana son k’ananun kaya, bayan ta gama shirya komai wad’anda ba yanzu zata yi amfani dasu ba ta sasu daga can k’asan wardrobe d’in, takalmanta kwasa ta fita cikin Corridor suma ta jera su a jikin shoe rack inda takalman Haisam d’in suke, bayan ta gama ta wuce Kitchen tana shiga ta saki baki tana bin kayan Abincin da ta gani a ciki su kwalayen indomie da spaghetti, macaroni su doya da dankali harda buhun shinkafa gasu madara, milo, Cornflakes harda custard, sugar harda crates d’in k’wai ya kai biyar ba dai abun da babu na kayan Abinci irin na yan gayu, taji dad’in ganin kayan a ranta ta raya zata fara yin girki kenan, shirya kayan Abincin ta shiga yi lokacin data gama ta gaji sosae ta wuce d’aki tana shiga ta nufi laundry don yin wanka, saida ta gama shiryawa ta kwanta akan gado tay rubda ciki tana latsa Computer d’in ta ya shigo, bayan ya cire agogon hannun shi ya d’aura kan dressing mirror ya wuce laundry tana ganin haka ta tashi ta d’auki laptop d’in ta fito daga d’akin don ta bashi wuri ya shirya. Washe gari Alhamis bayan ta dawo daga Makaranta sun ci Abinci a parlor suka zauna shi yana kallo ita kuma tana typing a laptop d’in ta jikinta sanye da k’ananun kaya riga da skirt sun kamata da yake roba ne kanta sanye da hula, suna cikin zaman taji yayi Magana ta d’ago ta kalle shi da alamun bata ji ba tace mashi Magana yake, saida yay d’an jimm sannan yace abunda ta kawo mashi rannan zata zubo mashi nan take ta gane su cin cin yake nufi, d’aga kai tay alamar to da d’an murmushi ta mik’e ta nufi Kitchen a ranta tayi mamakin cewa da yayi ta zubo mashin, tunda ta mik’e yabi bayanta da kallo har ta shige cikin Corridor sannan ya d’age kanshi ya kalli ceiling had’i da d’an lumshe ido, a saman c-table ta d’aura bayan ta zubo mashi ta kalle shi har lokacin yana a yadda yake tace mashi gashi sannan slowly ya sauke Fuskar ya d’an d’aga mata kai ta koma inda take ta zauna, a nutse ya fara ci Fatun ta rink’a satar kallon shi wani lokacin su had’a ido ta d’an yi mashi murmushi, kiran sallar la’asar da aka fara yasa shi mik’ewa ya nufi hanyar corridor, after some minutes ya fito yana gyara hannun rigar shi da gani Alwala yayi ya nufo cikin parlon Fatuu ta d’aga ido tana kallon shi, ganin yadda ta kafe shi da ido yasa shi dakatawa ya tambayi da wani abu ne cikin yar in ina tace dama so take ta tambaye shi har yanzu yana zuwa Gym, shiru ya d’anyi sai kuma ya d’aga mata kai tay d’an jim tana jujjuya ido da alama magana take son yi ta kasa, d’an moving yay ya tsaya ya tambayeta ya akai, marairaice fuska tay tace dama so take taje ne wani kallo taga yayi mata kaman harara ta d’an tura mashi baki had’i da rausayar da kai, jimm yay can yayi sigh yace taje ta shirya har bata san lokacin da ta saki yar k’arar farin ciki ba ta k’ame hannuwan ta had’i da d’an runtse ido, sototo yay yana kallon ta tana bud’e idon suka had’a ido ganin yadda yake kallon ta yasa ta kai duka tafukan hannuwanta ta rufe fuska alamar kunya yay d’an guntun murmushin gefe ya juya, yana fita ta tattara komae ta nufi Bedroom da sauri don ta shirya, salla ta fara yi tana gamawa ta hau shiri ba 6ata lokaci ta shirya cikin wando skin tight bak’i da top bak’a ta d’aukko sabuwar jallabiya cikin siyayyar da aka yi mata ta d’aura saman kayan ta nufi gaban mirror tana rolling veil d’in lokacin ya shigo ya wuce laundry, daga gida ya shirya don jakar shi bata nan tare suka fito suka nufi parking space suka hau Mota don yanzu bike d’in shi bai nan.
Sai bayan Magrib suka dawo a cikin kwanar gate ya ajeta yace zai je ya dawo, sosae Fatuu taji dad’in jikinta tana shiga Bedroom ta wuce toilet tayo wanka don ta had’a gumi sosae, bayan ta fito doguwar riga mai gajeran hannu mara nauyi ta sa ta d’an shafa mai da humra ta fesa turare, saman gado ta zauna tana latsa wayar ta a haka har lokacin isha yayi ta mik’e tayi salla, bayan ta gama jakar ta ta d’aukko ta Makaranta anan ta fara duba books d’inta, tana cikin karatun ya shigo yayi wanka yana sanye da k’ananun kaya tay mashi sannu da zuwa bayan ya amsa yace ta fito su ci Abinci tace to ta mik’e, bayan sun gama ta kwashe kayan da sukai amfani ta kai Kitchen saida ta wanke komai kaman ko yaushe ta koma dining d’in ta gyara table lokacin data gama Haisam d’in bai cikin parlon don yana gama cin Abincin ya fita, bayan duk ta gama abunda zatayi Bedroom ta koma ta zauna a kan gado tana cigaba da yin Karatu, ji tay ta fara jin bacci ta tattara littattafan ta maida a cikin jakar ta saukko ta maidata inda take sannan ta dawo ta haye gado taja duvet ta rufe rabin jikinta, bata dad’e da kwanciya ba har ta fara gyangyad’i ya turo k’opar ya shigo ta bud’e ido tana kallon shi shima ita yake kallo ya nufi gadon, duk a tunanin ta pillow zai d’auka kaman ko yaushe amman sai taga ya zauna daga bakin gadon ta can 6angaren da yake har saida ta d’an ji mamakin hakan da yayi don bai ta6a hakan ba, shiru suka d’an yi ya kauda idon shi yana kallon gefe ta lura kaman magana yake son yi, sai da ya d’an d’auki lokaci sannan taji cool voice d’in shi yace “You will sleep without switching off the light” yay Maganar idon shi a kanta ta d’an had’e lips d’inta sai kuma a hankali tace ta manta ne ta fara k’ok’arin tashi ya gane wutar zata kashe taji yace ta bari zai kashe in zai fita ta d’aga mashi kai amman duk da hakan sai ta tashi daga zaune, shiru suka d’an yi idon shi na kallon gaban shi ita kuma sai kallon shi take a ranta tana mi yake son ce mata ne,
“Am leaving tomorrow” bayan wani lokaci ya d’an kalle ta taji ya fad’i haka, bin shi da ido tay da alamun rashin fahimtar Maganar tashi taji ya k’ara cewa “I mean am going back to Us, zan je Abuja gobe daga can zan wuce” yanayin yadda yake Maganar kaman bai so don dole yake yin ta, ido kawae Fatuu take bin shi dashi ta d’an bud’e baki da gani Maganar tazo mata a bazata ne zuciyarta ta fara bugu da k’arfi don kaman saukar aradu haka taji Maganar wai zai koma Us duka yaushe aka kawota da zai tafi, goben fa zata yi sati d’aya amman shine zai ce zai tafi haka take ta ayyanawa a cikin ranta, tana haka taji Muryar shi yace bata ce komai ba sauke kanta tayi k’asa nan da nan kwalla suka fara taruwa ta shiga kokarin maida su da k’yar murya na d’an rawa tace mashi “Allah ya kaimu, ya kiyaye hanya” shiru bata ji ya amsa ba tasan kallon ta yake hakan yasa tak’i d’agowa don tasan data kalle shi tana iya yin kuka, sun d’an d’auki lokaci a haka shiru can taji ya kira ta da Fatuuh ta amsa ba tare da ta kalle shi ba ya tambayeta da matsala ne, jin tambayar tay kaman ta rainin wayau ta girgiza mashi kai kawai alamar babu komai, mik’ewa yay ya nufi hanyar laundry sai lokacin ta d’ago tana kallon shi, yana shigewa wani irin kuka ya taho mata tasa hannu ta toshe bakin ta da sauri ta koma ta kwanta ta kife fuskar ta jikin mattress, after some minutes taji k’arar bud’e kopar shi da sauri taja duvet ta lullube har kanta, sanye da bathrobe ya fito saida ya kalleta kafin ya wuce ciki, shiryawa ya fara yi yana yi yana kai idon shi kanta ko kwakkwaran motsi tak’i yi, bayan ya gama yasa kayan bacci ya nufi bakin gadon ya kai hannu ya d’auki pillow taji yace Good Night bata motsa ba balle ta amsa mashi irin ita ala dole bacci take saida ya kashe mata hasken d’akin gaba d’aya ya kunna mata lamb ta gefen da yake sannan ya juya ya nufi kopa, tana jin k’arar fitar shi ta bud’e fuskar taci gaba da kukan da take yi k’asa k’asa, saida tay mai isarta don kanta tayi shiru, duk yadda ta kwaso gajiya amman gaba d’aya bacci ya k’aurace ma idanunta sai juye juye take tana zancen zuci, saida dare ya raba sannan da k’yar baccin ya d’auketa shima ba wani mai nauyi ba, ana fara kiraye kirayen sallar Asuba ta farka da wani irin yanayi mara dad’i jikinta yayi weak har wani zazzabi zazzabi take ji, cike da k’arfin hali tayi shirin zuwa Makaranta ko breakfast d’in kirki ta kasa yi haka ta d’an tsattsakura ta barshi, tunda suka hau hanya ta juyar da fuskar ta gefe har suka isa Makarantar bata kalle shi ba saida zata fita sannan ta d’an juya suka had’a ido tace mashi ta gode ya fiddo kud’i ya bata bayan ta amsa ta bud’e Motar ta fita, ko a Class ma Fauzy ta lura da yanayinta ta hau tambayar ta abunda ke damunta tace mata kawae bata lafiya da zazza6i ta kwana amman ta sha magani, nan ta hau tsokanar ta wai kodai har ta biya Ya Haisam saidae kawae tay mata d’an murmushin yak’e, bayan an tashi ya zo ya dauketa, tunda ta koma ta shige d’aki ta kwanta sai daga baya ya shigo ya iske ta a kwancen ko Uniform bata cire ba ya tsaya daga bakin gadon yana tambayar ko bata lafiya ne da k’yar ta d’aga ido ta kalle shi ta girgiza mashi kai ya bita da kallo ta maida nata k’asa taji yace to ta tashi ta shirya zasu yi lunch a part d’in Hajiya ta d’aga mashi kai kawai ya juya ya fita, a daddafe ta shirya don har lokacin jin jikinta take ba dad’i tasa riga da skirt na lace iya powder da lip glow kawai tasa suma don kada a gane mata ne, lokacin data gama shiryawa bai nan tasan bai wuce Masallaci ya tafi don an fara hud’uba ta fito ta wuce part d’in Hajiya, bata samu kowa a parlon ba ta wuce Bedroom d’in ta bata same ta ba a ciki ta fito ta wuce d’akin Saude itama bata nan ta raya k’ilan suna Masallaci ta nufi Katifar Sauden ta kwanta sai daga baya ta mik’e ta nufi toilet tayo Alwala, bayan sun dawo ne ta fito ta iske su a parlor taje ta gaishe da Hajiya har tana tambayar ta ya akai bata zo sunje Masallaci ba tace lokacin da tazo har sun tafi shine tayi a d’akin Aunty Saude, daga baya Sauden tazo tace ma Hajiya ta shirya table tace masu su tashi suje su ci Abinci, da k’yar Fatuu ke turawa ba don tana jin dad’in Abincin ba, ita ta fara tashi Hajiya tace badai har ta koshi ba da d’an murmushin yak’e tace mata eh tace amman ai bata wani ci na kirki ba tace ai taci ne a Makaranta shiyasa ta gyad’a kai Fatun ta wuce idon Haisam a kanta, d’akin Saude ta koma bayan barin ta wurin Hajiya tace “Yanzu har sai yaushe zaka dawo in ka tafi?” Shiru ya d’an yi idon shi akan Abincin gaban shi kaman mai nazari can ya d’ago ya kalleta yace mata saidae yaje zai gani, gyad’a kai tay da alamun damuwa tace “banso ka tafi da wuri ba haka tunda Yarinyar nan ba’a dad’e da kawo ta ba, amman kana da kwakkwaran dalili yakamata ace ka koma aikin kaman yadda kace tunda kusan watan ka biyu kenan rabon ka da aikin fa, an taho bikin aboki sai kuma jinya kusan wata guda, yanzu da dawowar mu kuma inaga sati biyu kenan, ita kanta Fanan d’in nasan ta k’agara ka koma don ma tazo Germany d’in” d’an dakatawa tay sai kuma taci gaba “ba don karatun Fateemar ba ai da ka tafi da ita ala bashshi kasan yadda zakai in ka je, amman dai kai k’ok’ari in ka koma ka sanar da ita zancen auren naku sannan kayi k’ok’arin fahimtar da ita don kada kuma a tauye hakkin Fateema tunda itama zata so ku kasance tare ba kamar yanzu dai bai kamata ace har ka tafi ba, nima zanyi k’ok’arin sanar da iyayen naku bayan ka tafi, Allah ya shige mana gaba” a hankali ya amsa da Amin, bayan sun gama yace ma Hajiyar zai je G.r.a ya dawo, gab da sallar la’asar ya dawo ya nufi part d’in su ganin bai ga Fatun ba ya gane bata dawo ba, shirya kayan da zai d’auka anan yayi cikin trolley d’in shi, ba wasu kaya masu yawa ya d’auka ba ya bar wasu bayan ya gama aka kira sallar la’asar ya tafi Masallaci, bayan an gama sallar ya dawo ya zauna akan kujera yasa hannu ya d’an ruk’e ha6ar shi kaman mai yin tunanin, ganin lokaci nata tafiya don 4:30 jirgin su zai tashi yasa shi kai hannu ya d’auki wayar shi, kiran Fatun yay bayan tayi picking yace tazo yana jiranta a part d’in su a sanyaye ta amsa da to, bada jimawa ba ta turo kopar parlon ganin shi zaune yasa tayi yar sallama ya amsa idon shi a kanta har ta k’arasa shigowa ta zauna daga d’ayan 6angaren, ganin yadda ya kafeta da ido yasa ta juyar da face d’inta gefe tana haka taji yay sigh ya fara magana, ce mata yay yanzu zai tafi duk abunda take buk’ata tayi ma Abbas Magana, jin yayi shiru yasa ta d’an juyo suka had’a ido da k’yar murya na rawa tace mashi to ta maida kanta k’asa, wani irin kuka ne ke taho mata sai k’ok’arin maida shi take tana haka taji yace taje Bedroom ta d’aukko mashi trolley d’in shi ta mik’e ba tare data ce komai ba ta nufi hanyar corridor yana ta kallon ta har lokacin hannun shi na ruk’e da beard d’in nashi, janye da trolley d’in ta fito yana ganin ta ya mik’e tsaye, daga gaban shi ta tsaya ta mik’a mashi a hankali tace gashi bai amsa ba ya kafeta da ido kawae, jin yayi shiru yasa ta d’ago idanunta cike da k’walla ta kalle shi suka had’a ido da sauri ta juyar da fuskarta, k’ara ce mashi tay gashi ba tare data kalle shi ba taji yace “Won’t u accompany me to the Airport?” Shiru bata bashi amsa ba don tasan tana bud’e baki zata saki kuka sai yamutsa fuska take ta gumtse baki, hannu ya kai ya kamo hannun ta ya matso da ita har lokacin Fuskar ta na gefe, kiran sunanta yay aikuwa kaman tana jira ta k’wace hannun nata ta juya da gudu ta nufi hanyar corridor, tana shiga ta nufi gado ta fad’a ta fashe da kuka mai cin rai, ta d’auki lokaci tana ta rizgar kukan, ganin bai biyo ta ba yasa ta gane ya tafi hakan ya k’ara tunzura ta, tashi tay zaune kallabin ta ya kwance fuskar ta jage jage da hawaye idanunta sun yi ja a fusace ta fara magana cikin kuka “Yanzu na tabbatar baka sona Ya Haisam baka kaunata, kawae ka amince kaci gaba da zama dani ne hakanan ba don kai rayuwar Aure dani ba Saboda ni ban kai matsayin da zan zama matar ka ba, da kana sona na tabbatar bazaka tafi yanzu ka barni ba, shiyasa ka tafi wurin matar ka da kake so ka bar ni, hada cewa duk abunda nike so in ma Ya Abbas Magana wato Saboda baka son in rink’a ma magana ko, to shikenan bazan kira ka ba kasha soyayya da matar ka lafiya zan ma fita daga rayuwar ka kwata kwata sai ka huta” tana kaiwa nan ta sake fashewa da kuka ta fad’a saman gadon, ta jima haka har idanunta sun d’an kumbura can ta mik’e ta nufi mirror ta d’auki wayarta dama da ta shigo d’aukar mashi trolley ta d’aura ta anan, call log ta shiga ta kira lambar Fauzy tana fara ringing ta d’aga tace “Amaryar mu ya kika koma gida” fashe mata da kuka Fatuu tay a rud’e Fauzy ta saki salati ta hau tambayarta lafiya cikin kuka tace “Fauzy na gaya maki ya Haisam bai sona gashi nan har ya tafi ya barni” a kid’ime ta hau tambayar ta ina ya tafi ya barta tace mata ya koma Us, cike da mamaki Fauzy ta maimaita abunda tace Aunty Mareeya dake gefen ta tana sauraron su ta kai hannu da Sauri tana fad’in ta bata wayar, bayan ta amsa ta kira sunan Fatun cikin muryar kuka ta amsa tace “naji kina cewa ya koma?” Tace “Eh Aunty Mareeya yanzun nan ya tafi kuma bansan da zai tafin ba sai jiya da daddare yake fad’i man” salati Aunty Mareeya ta rafka ta kai hannu ta ruk’e ha6arta cikin bacin rai tace “Amman wannan anyi d’an jakar uba wllh….ke yi hak’uri na zagar maki miji raina ne ya 6aci, to wai miyasa zai tafi duka sati guda da kai mashi Amarya, mi ya koma yi ne yaushe yace maki zai dawo” cikin kuka tace “nifa Aunty Mareeya ce man yay kawae zai tafi bai fad’i man ko wani dalili ne yasa zai koma d’in ba kuma bai ce man ga ranar da zai dawo ba” salati ta k’ara sakawa sai faman fad’in kai take,
“amman Zarah wani abu bai shiga tsakanin ku bane?” Ta jefa mata tambaya, ta fahimci abunda take nufi tace mata eh, da tsantsar mamaki tace “Yanzu kina nufin tsawon sati gudan da kikai kallon ki kawai yake ba abunda ya wakana” k’ara amsa mata tay da eh, cike da takaici da har muryarta ta nuna tace “Amman dai wannan anyi sak’ago wllh, sai kace ba jini a jikin shi, to ko dai bai lafiya….Amman ma ai mu shaida ne in ma bai lafiyan tsabar iskanci ne ba wani abu ba, haka suke dama irin Mutanen nan akwae ban haushin tsiya wllh…” Dakatawa tay tana numfasawa can ta d’aura “Yanzu ina magungunan da aka siyo maki kina ta amfani da su ne?” tace “a’a, tun bayan da aka kawo ni na daina sha dana ga……” Shiru tay ta kasa k’arasa Maganar Aunty Mareeya tace “Yauwa Nagode ma Allah kin yi kyaun kai gara da kika daina amfani dasu duk da haka nasan kin k’waru, don Allah kiyi hak’uri Zarah kin ji, nasan dole ki shiga wani hali komai anyi maki ne don a nema maki k’ima” amsa mata tayi da to, taci gaba “bari mu zuba mashi ido muga iya gudun ruwan shi, ki k’ara hak’uri kinji in sha Allahu zaki ci ribar hakurin da kikai, ina nan dake sai reshe ya juye da mujiya a lokacin kuma zaki murza kambun sarautar ki sai yadda kika so zaki yi, in dai bada wani kwakkwaran dalili yay maki hakan ba bi’iznillahi ta’ala shima sai ya yi kuka share share” sosae ta shiga kwantar mata da hankali har saida taji ta d’an saukko sannan su kai sallama Fauzy ma ta rarrashe ta tace mata tana nan zuwa daga baya sukai sallama, tana niyyar aje wayar taji kira ya shigo ta kai idonta taga sunan da ta sa ma Abbas ya bayyana, d’an jimm tay kaman bazata d’aga ba can ta kusa yankewa tay picking ta kara a kunne, tun kafin tace wani abu ya tambayi tana ina tace mashi tana cikin d’aki yace yana a parlor ta fito a hankali ta amsa mashi da to, gyalen ta dake saman gado ta d’auka ta yafa ta nufi k’opa, dan jimm tay a bakin k’opar a ranta ta shiga raya komi ya kawo shi can dai ta kai hannu ta bud’e kopar ta fita……..
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 da 3 Naira 400 ne za’a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za’a turo shedar biya ta wad’annan nos din 09013804524 ko 08169856268
…
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page :Â Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page :Â @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel:Â Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.