Hausa novels

Halysaah Page 113 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 113Da daddare Khaleesat ta fito wanka kenan taji ana knocking kofar dakin hotel din, tun bayan da Ajay ya fita wajen karfe biyar ya kawo mata abinci ya sake tafiya take ta zaune ita kadai a hotel room din har yanxu da karfe tara da rabi yayi, hijab dinta ta saka har kasa don towel kadai ne daure jikinta ta nufi kofar ta bude tana kallonsa, kallo daya yayi mata ya shiga cikin dakin, ta juya ta bi bayansa still looking at him, ya ajiye ledan hannunsa kan Centre table din dakin, da tsadadden darduman da ya dauko daga gida sannan ya cire Jacket din jikinsa, a hankali ta dau doguwar rigar da zata saka na bacci dake gefen gado ta nufi bandaki, bayan few minutes ta fito daga bandakin ta ajiye hijab dinta da ta linke, ta ɗan kallesa ta gefen ido taga duk hankalinsa na kan abinda yake yi a wayarsa yana zaune kan kujeran dakin, gun ledan da ya ajiye ta tafi ta dauka don ledan restaurant ne, bata ci abincin da yawa ba ta sha drink din ta ajiye sauran abincin ta zauna gefen gado ta jingina da furniture din gadon ta fada duniyar tunani, ta kusa 30 mins zaune maganganun su Hadiyah na dawo mata da irin tarban walakancin da su Aunty suka yi mata a parlor, that not being enough Jay ma yaki ko da kallon inda take shi ma da ya ganta, gaisuwanta ma without much concentration ya amsa mata, duk cikin abubuwan da aka yi mata yau wannan ne yafi yi mata ciwo har cikin ranta, she felt really hurt and pained, hannu ta kai ta goge hawayen da taji na silalowa daga idonta a hankali, don kar ma ta fashe da kukan dake cin ta kawai ta jawo wayarta ta kunna data ko zai yi distracting dinta from what is making her wants to cry, bata expecting ko wani important WhatsApp message da ya wuce na Ummanta sai Sophie sai ko Aunty Farida, sosai gabanta ya fadi bayan ta ci karo da message din Jay, babu ko kiftawa ta dinga kallon message din da ya rubuto mata kamar haka “An maki wani abu ne a gidan?” And he is even online at the moment, cikin sanyin jiki ta masa reply tace “A’a” After few minutes sai ga wani message din nasa yace “Then why did you leave the House?” Wasu sabbin hawaye taji na taruwa idonta ta tura masa “Ba komai” Sai ga message dinsa yace “Alright, take care” har cikin ranta take jin kaman kaso tamanin daga cikin abinda ke damunta a ranta ya ragu, baƙin cikin da take ciki yau taji kamar an yaye mata shi lokaci daya, kallon message din nasa na karshe ta dinga yi babu ko kiftawa, cikin sanyin jiki ta sake masa message tace “Plss me yasa idan nayi maka message kake ignoring? I want to speak to you plss” Without waste of time sai ga shi yayi reply kamar haka “Hum! About?” Ta goge hawayen dake zuba idonta tace “Many things” Ya sake cewa “Hmm, Like?” Tace “Plss spare me even if it’s just a little of ur time ka saurareni don Allah” Yace “Kina ina yanxu?” Ta dinga kallon tambayar da yayi mata zuciyarta na bugawa, a hankali ta juya suka hada ido da Ajay, ta sauke idonta sai kuma ta dauke kai daga direction dinsa, tana kallon message din da Jay yayi mata ta mayar masa da reply tace “Nima ban san wajen ba” after few seconds Jay yayi mata reply yace “Forward ur location” Khaleesat ta kusa minti daya tana tunanin ta tura din ko kar ta tura, don tana tura masa location din hotel zai gani, a hankali ta juya ta kalli Ajay taga idonsa na kan wayarsa, kawai ta tura ma Jay location din nata ta WhatsApp, ta fi minti talatin zaune tana jiran reply dinsa amma bai yi ba kuma yana online, daga karshe tayi masa message tace “Kayi shiru” Nan ma dai har bayan minti ashirin bai mayar mata reply ba ta ga ya ma sauka, hawaye ya cika idonta ta kashe data dinta ta ajiye wayar ta kwanta ta rufe jikinta da farin duvet din kan gadon, bata san sanda bacci ya dauketa ba wajen karfe sha biyu bayan ta gama zubda hawayenta. Biyu da yan mintuna na dare Khaleesat ta farka ta dalilin mafarkin da tayi about Jay, ta mike zaune ta dinga bin dakin da kallo don wuta ne mara haske a kunne, she was wondering if ita kadai ce a dakin, tafi minti goma zaune bata motsa daga inda take ba, can dai ta koma daya side din gadon tana leka kasa a hankali, Ajay ta gani kwance kan darduman da ya shigo da shi daxu yana sanye da jacket ya saka eye mask for sleep alamar baya son haske, dakin yayi sanyi sosai saboda Ac dake kunne, gashi dama tun da suka zo kasar ta lura yafi America sanyi, duvet din jikinta ta cire ta rufa masa ta koma ta kwanta tayi using second bedsheet din kan gadon ta rufa da shi. Da asuba ko da Khaleesat ta tashi taga duvet din a jikinta, ta mike zaune ta juya tana kallon inda yake tsaye yana sallah, sauka tayi daga saman gadon tana gyara hularta ta shiga bandaki. Khaleesat na idar da sallah bayan ta gama azkar dinta abu na farko da tayi shine kunna data din wayarta ko Jay yayi mata reply din message dinta, amma taga har sannan bai mata reply ba kuma ya hau not long ago, sosai taji zuciyarta ya karaya, ta ajiye wayar cikin sanyin jiki lkci daya idonta ya kada, kamar ance ta daga kai taga Ajay yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi, babu yabo babu fallasa taji yace “What is it?” Without looking at him tace “Nothing” Gaishesa tayi ya dauke kai bai amsa ba, ta mike ta tafi edge din gado ta kwanta ba tare da ta cire hijab din jikinta ba, ji take kamar an kwaso mata damuwar da taji ya tafi jiya an maido mata kayanta, lumshe ido tayi after sometime bacci ya dauketa….. Ajay ne ya shigo dakin hotel din fuska daure yace “Baki da hankali ne zaki bar ni zaune a mota tun daxu are you okay?” Khaleesat ta gama daure gashinta da take yi ta juya tana kallonsa bata dai ce komai ba, bai sake ce mata komai ba ya dauke idonsa ya juya ya fita daga dakin, ta dau veil din kayan jikinta tayi rolling dinsa sannan ta dau handbag dinta ta saka takalmi ta nufi kofar dakin hotel din ta fita, walking slowly ta nufi Indrive din dake jiranta outside of the hotel, sau daya Ajay ya kalleta ta madubin motar da yake ciki ya dauke ido kamar bai ganta ba, har ta iso ta bude back seat ta shiga ta kulle. Da gangan Ajay ya bari suka je Venue din convocation din Hadiyah extremely late, don har an gama taron ana ta hotuna ne suka isa wajen, ita dai Khaleesat tana biye da shi a baya gabanta sai faduwa yake, front dinsa ya nuna mata hakan yasa ta shiga gaba yana biye da ita, tun daga nisa take kallon yanda familyn suke ta hotuna cikin farin ciki da annashuwa ba iyayen ba ba ‘ya yan su ba, Hajja kuwa na zaune daga gefe cike da izza ga fruits an ajiye mata gabanta, Hadiyah sai makale ma Jay da yayi mata side hug take kamar zata shige jikinsa su zama daya ko kunya babu ana masu hoto, kana ganinta kasan tana cikin farin ciki mara misaltuwa, Khaleesat dai ta sauke idonta daga kallonsu tana tafiya a hankali, lokaci daya duk aka yi noticing Ajay da Khaleesat that were walking toward the scene, gaba daya aka maida attention kansu barin ma Khaleesat, Ba iya su Hadiyah da cousins din ta ba, hatta iyayensu kowa kallon Khaleesat yake barin Aunty, cause whatttt?? she look expensively beautiful, gaba daya dressing dinta ya doke duk na yan matan wajen har me convocation, komai na jikinta is screaming nothing but pure luxury gashi tayi wani nutsattsen kyau duk da babu make up fuskarta pink lips dinta kuwa sai sheki yake, tsadadden kayan jikinta ya kara haska farin fatar ta, Walid ya dinga kallonta kamar zai cinyeta, Khaleesat was only feigning smile ganin all eyes were on her hakan yasa beauty point dinta ya dinga lotsawa ciki, amma tsabar yanda duk ta rikice da yanda suke kallonta sai da ta harde kafa wajen tafiya wanda hakan yasa kirkis ya rage ta fadi banda Ajay da yayi saurin tarota, yana facing dinta speaking calmly yace “Are you a bush gal?” Kamar wanda ya tuna abu sai kuma ya saketa within few seconds suka ci gaba da tafiya, this time around he let them walk together ba kamar daxu da take gaba yana bin ta ba, Aunty taji wani abu ya tokareta a kirji ta juya ta kalli Hajiya Nafisah, Hajiya Nafisah tace “Uhum” irin na takaicin nan, Ummi Mahaifiyar Hadiyah kuwa hade rai tayi sosai ta ci gaba da harkar gabanta a wajen, Mami dai ko bin ta kan Khaleesat bata yi ba tana ta kokarin sallamar wasu ɓakin ta da za su tafi, Hadiyah ta dinga kallon designer bag din hannun Khaleesat da rings din fingers dinta sai kuma ta dauke kai tana jawo wasu frnds dinta da suma suka tsaya kallon Khaleesat, ta kira me hoto yayi masu hoto duk don ta kawar da attention dinta daga kan Khaleesat, Tun da Jay ya kalli Khaleesat sau daya ya dauke kai daga direction din, Shahuda kuwa sai kallon doguwar rigar jikin Khaleesat take with sheer jealousy, sauran yan matan ma dai kowacce zaka ga hassadarta kwance fuskarta kiri kiri, duk wani African in ya zo wuce wajen sai ya sake kallon Khaleesat, Ajay ya karasa har inda Hajja ke zaune ya gaisheta, Hajja na kallonsa tace “Junaid sai da aka kare convocation zaka zo saboda Allah? To menene amfanin zuwan ka kenan muna kokarin komawa gida?” Ajay yaki tanka ta ya dau Apple din kusa da ita, ya gaida su Gimbiya Firdausi dake gefenta duk suka amsa masa babu yabo babu fallasa, kallon Mami yayi ita ma ya gaisheta ta amsa, Khaleesat ta duka gaban Hajja ta gaisheta cikin sanyin murya, neutrally Hajja ta amsa tana kiran jikar wata aminyarta da ta hango wai ta zo ba ayi hoto da ita ba, Khaleesat ta kalli su Gimbiya Firdausi su ma ta gaishesu, har sai da Hajja ta kallesu tace “Ana gaishe ku” sannan suka amsa don yi suka yi kamar basu ji ba gaba dayansu kuma, still at that ma Aunty bata amsa gaisuwar ba fuskar nan nata a murtuke kamar bata taɓa ko murmushi ba, Khaleesat ta ɗan kalli Walid da ke gaisheta yana kallonta, sunkuyar da kai tayi ta mayar masa da gaisuwan, A takaice Ajay ya amsa gaisuwan Cousins dinsa, Jay kuwa dama tuni ya bar wajen yana answering phone call, Baby tayi fari da ido tana kallon Khaleesat tace “10/10 kika yi kyau….” Su Iklima duk suka juya suna kallon Baby, ita dai Khaleesat murmushi kawai tayi ta kalli Baby tace “Thank you” Ganin har sannan Khaleesat na durkushe Hajja tace “To ki je ki yi ma Hadiyah Allah sanya alkhairi mana, ga can kannen mijin ki kuma sai ki duka a nan” Mikewa Khaleesat tayi cikin sanyin gwiwa ta ɗan kalli Ajay dake kallonta, sai kuma ta karasa har inda su Hadiyah suke hotunansu tana Kallonta tayi mata congratulations, Hadiyah tayi kamar bata san da ita take ba sai jawo cousins dinta da kawayenta take suna hotuna happily, duk da tun da taga Khaleesat Happiness din nata yayi vanishing kawai pretending ta ci gaba da yi take fara’an da bai kai zuci ba, wata kawar Hadiyah dake ta kallon Khaleesat kamar ta samu TV tace “Hi, I love your dressing, you look beautiful” Khaleesat tayi mata murmushin karfin hali tace “Thank you, and you too” Hadiyah ta kara jin wani kololuwar bakin ciki ya tokareta kawai dai ta ci gaba da sabganta bata nuna ba, Shahuda dama barin wajen ma tayi gaba daya, babu wanda ya bi ta kan Khaleesat dake ta tsaye a wajen da suke hotunan, daga karshe cikin sanyin jiki ta koma gefe ita kadai ta tsaya, ganin Ajay ne ma yasa duk suka kama kansu babu wanda ya tsaya disgata a wajen cause he is looking at each and every one of them, ita kam Khaleesat time to time take satan kallon inda Jay ya koma ya tsaya da Maminsa tana masa magana, ta kalli wajen for the 4th time kawai suka hada ido da shi and he took his eyes off her ya juya baya, a hankali ta sauke idonta, duk Ajay na kallo, bayan Jay ya gama magana da Mami ya tafi gun wani abokinsa ya tsaya, wayarsa ya ciro yana dannawa, Khaleesat ta bude jakar ta jin shigowar message wayarta, ta ciro wayar tana kallon message din babu ko kiftawa, Ajay dai kallonta kawai yake daga inda yake tsaye, can yaga ta juya a hankali ta kalli inda Jay yake, Jay ya ɗan kalleta bayan sun hada ido ya dauke kai ya mayar da wayarsa cikin aljihu, Wani Apple din Ajay ya dauka zai bar vicinity din Hajja ta bi sa da kallo tace “Ahmad Junaid” Juyowa yayi, sai kuma ya dawo ya tsaya kusa da ita yana jiran jin me zata ce, tayi shiru kamar bazata ce komai ba don babu abinda ya tsaya mata a rai irin yanda taga daga shi har Jay babu wanda ya kalli inda wani yake balle yayi ma wani magana, kamar ma basu taɓa sanin juna ba, duk tunaninta ko ba komai suna gaisawa, can ta kallesa, shi dai cin Apple din hannunsa yake with calmness yana kallon Khaleesat dake danna wayarta alamar she is sending a message, sae kuma ta juya ta kalli Jay that is looking at his phone too shi ma ya ɗan juya ya kalleta, Ajay ya dauke kai daga direction dinsu ya kalli Hajja yace “I am listening” Ajiyar zuciya Hajja ta sauke tace “To shi ma hotunan baza kayi da yan uwanka ba kenan kake nufi ko me? Ban ga alamar kayi niyyar zuwa taron nan ba don da kayi niyyar zuwa ba sai da aka watse taro zaka zo ba” Ajay yace “Ni zan je in samesu mu yi hoto?” Hajja ta kalli Baby da ta zo daukan Apple tace “Ke Hauwa kira min Hadiyah” Baby tace to sannan ta tafi, sai ga Hadiyah ta zo fuskarta babu wani fara’a, to cover that up tace “Wallahi na gaji kaina ma ciwo yake min, da ma mu tafi gida kawai” Hajja tace “Hadiyah ba ku yi hoto da yayanki da matarsa ba” Hadiyah ta kauda kai tana ɗan yatsine fuska sai kuma ta juyo tace “Oh haka ne fa” Kiran me yin hoton tayi sannan ta koma gefen Ajay ta tsaya me hoton ya fara daukansu hoto, Hajja ta kara aika baby taje ta kira Khaleesat, after snapping 2 pictures with Ajay Hadiyah ta zaro ido tace “Wayata fa? Waye na ba wayata ko nayi misplacing dinsa ne?” Da sauri ta bar wajen irin zata je tambayo cousins dinta da kawayenta wanda ta ba wayarta a cikin su, nan kuma hoto ne da Khaleesat bazata yi ba, Hajja ta daga kai ta kalli Ajay tace “Kai yanxu abinda kayi jiya ka kyauta Junaid? Ko da yake bari mu karasa gida tukunna ba maganar nan wajen bane” Dai dai nan Khaleesat ta iso gun Hajja bayan Baby taje ta kirata, ta kalli Ajay da ya juya ya bar wajen sannan ta duka gaban Hajja tace “Ga ni Hajja” Gimbiya Firdausi ta karaso kusa da Hajja tace “Hajja ga mota za a fara kai ki gida” Bata rufe baki ba sai ga Jay ya iso gun yana kallon Hajja, calmly yace “Hajja za ayi dropping din ki gida, the driver is around” Hajja tace “Toh” Kallon Khaleesat Jay yayi yace “Are you following Hajja Home?” Gimbiya Firdausi ta kallesa tace “Kamar ya kenan? Manyan ta basu fara tafiya ba sai ita Jawwad, wannan kuma wani lissafi ne, ae su Hadiyah zata bi ba Hajja ba, Hajja da Fulani kawai za aje ayi dropping a dawo a motar” Jay dai bai ce komai ba, Gimbiya Firdausi ta kara da cewa “Tun da ta shigo zuri’a babba haka ai kamata yayi ta dinga sakin jiki tana shiga yan uwan mijinta ba ta dinga rabe rabe ba” Jay ya kalli Khaleesat calmly yace “Go nd meet them, naga baku yi hoto ba” Ita dai Hajja babu abinda tace a wajen, Khaleesat ta mike a hankali ta nufi inda su Hadiyah suka taru, sai da ta isa wajen ta fara waigen inda zata ga Ajay amma bata gansa ba, kamar yanda suka mata daxu yanxu ma babu wanda ya bi ta kanta harkan gabansu kawai suke suna nishadin su, Shahuda ta lura Ajay baya surrounding din alamar ya bar wajen, hakan yasa ta karasa har gaban Khaleesat fuska daure tace “Wai ke halan mayya ce da dole sai kin zo inda muke? Tun daxu muke avoiding dinki amma sae kara cuso kanki kike wajen mu, Waye ajin ki a nan ko kuma uban wa ya gayyace ki?” Su Iklima duk suka juya da sauri don ganin ko Ajay na wajen sai suka ga baya nan, haba nan duk suka kallo Khaleesat, tana ganin haka bata sake tsayawa ta ji abinda za su fada next ba ta juya ta bar wajen ta koma can wani waje daban ta tsaya cikin sanyin jiki tana dube duben inda zata ga Ajay……*

Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788*

Back to top button