Uncategorized

Abban Sojoji Page 56 Book 2 Complete Novel

 

“`The father Of Soldiers“`

 

Story &  Written 

       By 

      Hafsat Bature

💋Boss Bature💋

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖

Am really sorry 4 the late post👌

Wata irin zufa ce ta soma tsastsafo mashi a jikinshi kamar wanda aka tsamo daga cikin ruwa,lokaci guda yashiga Sakin atishawa yafi talatin a jere suke fitowa daga bakinshi,daga bisani kuma a hankali launin kwayar idonshi ya bayyana,komai nashi ya dawo yarda yake,ganin shi kwance a ƙasa yasa shi yin hanzarin miƙewa tsaye yana tunanin wai menene yakai shi ƙasa kwance?me ya faru dashi ne?hannu yasa yana shafo zufar dake a gefen fuskarshi har lokacin bata daina zuba ba,hakan yasa ya nufi toilet tare da shigewa ciki don yayi wanka,

Bai jima da shiga ba sai ga Jahan ya faɗo ɗakin yana atare da kanal yousouf,tsayawa su kayi abakin ƙopar ɗakin,Jahan na mamakin Ina ayyan daya bari cikin wani hali yashe a ƙasa 

Kallon shi kanal yousouf yayi tare da cewa”Kace mun Ayaan ya faɗi ƙasa jikinshi na kerma,gashi kuma ni banga Ayaan ba,” 

  Fuskarshi aruɗe yace”Ya yousouf nikaina abun ya ɗaure mun kai,nan fa nabarshi kwance cikin wani yanayi yanzu kuma babu shi a wurin,” jin hakan yasa hankalinsu tashi su duka biyun,

  tsayawa su kayi kowa da abunda ranshi ke bashi,suna cikin tsayuwar nan sai ga Ayaan ya buɗe ƙopar toilet tare da fitowa jikinshi ɗaure da towel,ga danshin ruwan dake ajikinshi alamar wanka yayi,abun ba ƙaramin ɗaurewa jahan kai yayi ba hatta kanal yousof ɗin,shi kuwa hankalinshi kwance har zai gifta ya hangesu tsaye ta wutsiyar idonshi,hakan yasa ya ɗan ja da baya tare da juyawo yana kallon su,cike da mamaki yace”Ya yousouf!Jahan!meya faru naganku a tsaitsaye kunyi curko curko?ko lafiya,”? 

   ajiyar zuciya jahan ya sauke tare da tunkarar shi kai tsaye ya rungumo shi ajikinshi yana ɗan bubbuga bayanshi yace”babu komai ayaan,nashiga damuwa ne ɗazu dana ga ka yanke jiki ka faɗi nayi tunanin kowani mummunan abune zai faru dakai that’s why nayi deciding kiran ya yousouf don yazo ya duba min kai,” ya ƙarasa maganar tare da raba jikinshi daga na Ayaan,

   “Nifa lafiyata lou,babu abunda ya faru dani,kawai jiri ne ya ɗan ɗebe ni but now Alhamdulillah har wani ƙarfi nake ji ajiki na,ko in gwada maka ka gani,” yarda yayi maganar tare da ɗaga masu damtsen hannunshi ba ƙaramin dariya ya basu ba,girgiza kai kawai kanal yousouf yayi tare da juyawa ya fuce daga ɗakin,

   wucewa Ayaan yayi ya nufi mirror,cikin sauri Jahan ya bishi tare da hugging ɗinshi ta baya ya kwantar da kanshi a saman kafaɗar Ayaan,

   Shiru Ayaan yayi yana tunanin mai jahan ke ƙoƙarin yi mashi ne,menene dalilin rungumar da yayi mashi ne hada wani kwantar da kanshi a saman shoulder ɗinshi,bai ƙarasa zancen zucin nashi ba,yaji hannun Jahan agabanshi yana ƙoƙarin zame towel ɗin jikinshi,aikuwa a wani irin firgice ya ka6e mashi hannunshi tare da yin wurgi dashi gefe guda,sannan ya juyo fuskarshi a ɗaure yace”Jahan bana son iskanci!menene haka?bakasan me ka kama mun bane?so kake ka ciremun towel ɗin jikina ne!”

  Murmushi Jahan ya saki tare da cewa”Ayaan banason irin wannan wasan pls,ka riga da kasan abinda nake buƙata a wurinka,”

   Fuska ayamutse Ayaan ke kallonshi,ganin hakan yasa jahan tunanin cewa kodai bai jin daɗine duba da abunda ya faru dashi ɗazu,bai ƙara yi mashi magana akan abun ba saboda yasan cewa jarabar tashi zata motsa ne kuma zaizo ya sameshi ne,komawa yayi saman gadon tare da kishingiɗawa yana kallon Ayaan daga kwancen da yake,

Ganin yarda jahan ke zuba mashi ido ko kawar dakai baiyi,hakan yasa shi tsuke fuska tare da barin gaban mirrorn ya shige can cikin ɗakin don ya sanya sutura,sa6anin da basa jin kunyar wannan bawani abu bane awurinsu in ɗaya ya tu6e kaya agaban ɗayansu.

❤🤍💛

Around 3:30,sehrish ta farka tana faman murza idanu,ba ƙaramin bacci tasha ba,sai hamma take saboda wata irin yunwa dake cinta,dama ko a school bata wani ci abun kirki ba,hannu tasa tare da yakice hijabin dake jikinta tayi wurgi da ita gefe guda,sannan ta zuro ƙafafunta tare da saukowa daga saman gadon,tsayawa tayi tana kallon school bag ɗinta da tayi wurgi da ita ƙasa bakomai ya faɗo mata a rai ba face Ruwan addu’ar da Malamin nan mai farin glass ya bata,ƙarasawa tayi tare da zuƙunnawa ta janyo bag ɗin,tana dudduba cikinta sam babu roban ruwan aciki,abun ya ɗaure mata kai,hannu tasa tare da zazzage kayan cikin jakar duka amman babu robar ruwan,

  Tunanowa tayi da abunda Amrish ta faɗa mata”Ga ruwan addu’ar da malaman yace na baki,kuma yace indai bakiyi amfani dashi ba,ƙusumbi zai fito maki abayanki,”waro ido waje sehrish tayi tuna wannan maganar ta amrish nan take yatsun hannunta suka shiga kerma hatta la66anta,gaba ɗaya duk tabi ta rikice ba don komai ba sai don tsoran ƙusumbin da akace zai fito mata,mugun tsoran ƙumbin take yi saboda taji ana cewa aljanune ke ajiya a cikin ƙusumbin,ƙyamar abun take ji,

   Hawaye ne suka soma wanke mata fuskarta murya na rawa tashiga furta”innalillahi wa’inna ilaihir rajiun, nashiga ukuna!wayyo Allah na,yanzu ya zanyi?nan fa na ajiye robar ruwan nan amma yanzu na duba babu ita…..yanzu shikenan ƙusumbi zai fito min ya suffata zata koma tare da ƙoƙo abayana…………’fashewa tayi da matsanancin kuka,anan wurin ta tsugunna tana matse kwalla duk tabi ta rikita kanta,sai da tayi mai isarta sannan ta miƙe tana faman shasshekar kuka takai hannu tare da tattara books ɗinta tana mayar dasu cikin school bag din,bayan ta kammala ta ɗauke jakar taje ta ajiyeta,

   Rage kayan jikinta tayi,ya rage daga ita sai white short da half vest,sannan ta shige cikin toilet cike da kasala,

  Ta jima acikin toilet din kafin ta fito jikinta ɗaure da towel,har lokacin idanunta na cike tab da hawaye,zulluminta ƙusumbin da akace zai fito mata,saboda tasan in hakan ta faru hatta Junaid sai ya guje ta,shi da yafi kusa da ita,da wannan yanayin ta kammala shirya kanta cikin wando palazzo maroon colour tare da halter shirt black colour,just imagine it ba ƙaramin kyau rigar tayi mata ba,ta ɗame jikinta sam rigar bata da hannu amma ta rufe ƙirjinta har neck ɗinta ta zagaye shi,komawa tayi gaban mirror tana feshe jikinta da turaren nan nata mai ƙamshin gaske,kafin daga bisani ta ɗauko ribbom launin wandonta maroon colour,tattare gashin tashiga yi zata ɗaure shi amma ina duk yadda taso ta haɗe shi wuri guda ta ɗaure abun yaci tura,har wani huci takeyi saboda 6acin ran yaƙi ɗauruwa,tana cikin dambe da gashin,taji ana kwankwasa mata ƙopa,dakatawa tayi da ɗaure gashin tace”Wanene,”

  “Auntynki ce,”muryar azmee ce ta bata amsa daga waje,

   ƙarasowa Sehrish tayi tare dasa hannu ta buɗe mata kopan,sanye take cikin hijabi hannunta ruƙe da cazbaha fuskar nan ɗauke da murmushi tace”irin wannan kyau haka?

. sunnar dakai sehrish tayi tare da cewa”Ina yini aunty azmee,”

  “Lafiyalou,tun ɗazu naso nazo na dubaki amma bansamu hali ba,ya school ɗin”?

  “Alhamdulillah Aunty azmee,”

“ina fata kina lafiya,naga kamar akwai damuwa a fuskarki”?

  girgiza kai sehrish tayi tace”a’a lafiyata lou,dana dawo ne bana ɗan jin daɗin jikina shine na kwanta nayi bacci sosai banjima da tashi ba,shiyasa fuskata take a haka,”

  Jinjina kai azmee tayi tare da cewa”okey,nagane ina fata kinyi sallah,

  “A’a yanzu nake shirin yi,”

Azmee tace”okey ya kamata ki hanzarta yi time har zai wuce,”

  Ta ƙarasa maganar tare da juya zata fita,tsayawa ta ɗanyi tare da jiyowa tana cewa”Oh namanta ban faɗa maki ba,ɗazu da safe da kika tafi school,hayaam ce taje kaima Sgr breakfast ɗinshi,’

  Jikin sehrish ne yayi sanyi tunkan ta ƙarasa jin abunda takeson faɗa mata tasoma jin jealous a zuciyarta,

  “Yanzu kenan itace zata cigaba da kula da part ɗinshi tana kai mashi abinci”?yarda sehrish tayi maganar taba azmee dariya,saboda a wani irin yanayi na tashin hankali tayi tambayar,

   “Kin tari numfashi na baki bari na ƙarasa maganar ba ai,Hayaam takai mashi abinci amma baici ba yace ta mayar dashi saboda shi ba’a sharing a aikinsa,yafison mutum ɗaya daya fara yi mashi aiki yaci gaba da yi batare da an canza mashi wani ba,ko kuma mutum biyu na mashi aiki at thesame time bayaso,”

   Wani irin ƙayataccen murmushi sehrish ta saki,farin ciki kamar anyi mata albishir da gidan Aljanna,tama rasa bakin magana sai faman zabga murmushi take,

   Azmee taci gaba da cewa”yanzu haka tun safe ba’a gyara mashi bedroom ɗinshi ba,na dai kai mashi breakfast ɗinsa,amma ban gyara ba saboda ba aikina bane,aikinki ne don haka da zarar kin kammala salla ki hanzarta zuwa ki gyara mashi part ɗinshi before ya dawo,”

   Dakyar Sehrish ta iya amsa mata da toh,kamar jira take azmee tabar ɗakin tana fita tashiga daka uban tsalle tana rawa don murna,

   Sam ta manta da maganar roban ruwanta da take nema,

   Sai da tayi salla sannan ta koma gaban dressing mirror ta shafa jan baki launin wandonta maroon colour ba ƙaramin kyau yayi mata ba,bayan ta gama ta kara feshe jikinta da turare sannan ta koma wurin wardrobe ɗinta tare da ɗauko mayafinta,ta yafa shi ajikinta,ta ɗauko takalmi  baƙi ta zura a ƙafarta Open toe mai ɗan tsini,sai gashi ta fito ɗass da ita,

   hannu tasa tare da buɗe door din ɗakin ta fito tare da kama hanyar fita daga corridor din,

  Adaidai lokacin Hayamm ta fito daga masaukinta,itama ta ɗauki wankan lace mai ɗan karan kyau,riga da skirt ash colour,kayan sun matseta sosai,daga saman rigar kamar boobs ɗinta zasu fito waje gaba ɗaga,skirt ɗin kuwa wata tsaga gare shi tun daga guiwar ƙafarta tafara har wurin ƙafarta kana hangen fatar ƙafafunta,high heels ne a ƙafarta tana tafiya sautin na fita kwas kwas,ta cuge ɗaurin ɗan kwali abunta yarda kasan wadda zata gasar miss world

   jin takun tafiya yasa sehrish jiyuwa bayanta,har sai da gabanta ya faɗi da tayi arba da hayaam saboda wankan data ɗauka tayi uban makeup kamar wata aljana,bakin nan yasha jan janbaki ta wani cuno shi irin na masifaffu,

    Tuni sehrish tasha jinin jikinta ganin irin wankan da Hayaam ta ɗauka,ba ƙaramin kyau tayi ba kuma zata ja hankali sosai,

   kawar da kai sehrish tayi tare da juyawa zata tafi,muryar hayaam ce ta katse ta dacewa”Wait inason magana dake ƴan mata,”

   tsayawa sehrish tayi tana jiran jin me zata ce mata,

  Koda Hayaam ta ƙaraso,bin sehrish tayi da wani irin matsiyacin kallo tun daga ƙasa har sama sannan tace”nasan gabanki ya faɗi kuma kin tsorata da ganin irin kyau da kuma kyawun sura da Allah yayi mun,”

   ɗaure fuska sehrish tayi batace komai,

  Hayamm taci gaba da cewa”so nake ki fahimci cewa ni ba sa’ar yinki bace!bansan wani irin shisshigi kike ma Sg rafayet ba da har kika samu matsayi a wurinshi,inaso na gargaɗeki ne, kuma naja kunnanki akan ki fita daga sabgarshi saboda yafi ƙarfinki nesa ba kusa ba,don na lura abunda kike hari kenan,in ma banda haɗama irin taki ina zaki kai mutum kamarsa?dan Allah jibarki fa ƴar ƙarama dake amma sai kankanbar tsiya,wai ma menene connection ɗinki da mutanen gidan nan ne? tayi tambayar tana kallon sehrish yayin da fuskarta ke ɗauke da shu’umin murmushin nan nata,

  jikin sehrish ba ƙaramin sanyi yayi ba don tuni idanunta sun cicciko da kwalla,daƙyar ta iya shanyesu sannan ta dake tare da cewa”Bansan meyasa kike gayamun waɗannan maganganun ba,da alama dae baƙin cikin ɗazu ne da sgr ya ƙumsa maki shine kikeson ki huce akaina,sannan kuma yaushe nace maki inason shi ne da har kike cewa yafi ƙarfi na?bama wannan ba,Naji kina magana akan cewa menene alaƙata da mutanen gidan to bari na baki amsa,”

  matsawa sehrish tayi dab da Hayaam sannan tace”Ni yar aikinsu ce,biya na suke ina masu aiki kuma suna jin dadin aikina shiyasa nasamu kar6uwa a wurinsu,kuma ina alfahari da hakan,wannan shine alaƙata dasu,ke kuma fa?ƙanwar matar yayansu ce fa?ina alaƙa take anan?

  Lokacin da sehrish takai ƙarshen maganarta,waro ido waje Hayaam tayi tana kallonta,bata ta6a tunanin cewa yarinyar zata iya mayar mata da martani ba ashe itama ba kanwar lasa bace,ranta ba ƙaramin 6aci yayi ba,tuni idonta sun canza launi saboda fusatar da tayi,

   Sehrish kuwa murmushi ta saki tare da juyawa ta kama hanyar tabar wurin,

  Wani irin tafarfasa zuciyarta keyi mata,tama rasa mai zatayi ma sehrish ta huce don tsabar takaicin maganar da ta yada mata,

   “Da ace ban mayar mata da martani ba,dani zan kwana da baƙin ciki,” sehrish ce tayi maganar a lokacin da take ƙarasa shiga part ɗin sgr,

   Sai faman murmushi take saki abunta,wucewa tayi cikin bedroom ɗinshi,wannan daddaɗan ƙamshin turaren nasa ne yayi mata maraba da zuwa,duk da baya cikin ɗakin amma ƙamshinsa ya gauraye ko’ina,

   Lumshe idonta tayi tare da buɗesu a hankali suka sauka akan shimfiɗeɗen gadonshi,tunawa tayi da abunda ya faru jiya atsakaninsu nan take taji wani irin yanayi atattare da ita,nan take tashiga tariyo dukkan abunda ya faru jiya a tsakaninsu,musamman lokacin daya kwantar da kanshi asaman chest ɗinta sai taji shi tamkar babynta,hmmmmmm

   shiga ciki sehrish tayi batare da 6ata lokaci ba,tashiga gyara mashi bedroom ɗin nashi,tamkar sabo haka ta Canza mashi kamanni,bayan ta kammala da bedroom ɗin,ta cire mayafinta tare da ajiye shi daga gefen gadon sannan ta koma cikin toilet ɗinsa don ta gyara mashi,

Bata jima da shiga ciki ba,sgr ya dawo cikin gidan,har yanzu wankan ɗazu ne ajikinshi,na warp shirt da black trouser,da alama a ɗan gajiye yake,kai tsaye ya nufi upstairs part ɗinshi,hankalin Hayaam ba ƙaramin tashi yayi ba lokacin data ga gifcinshi yana ƙarasa hawa upstairs ɗin,taso ta tarbe shi tayi mashi sannu da zuwa kota samu yasan ya idonshi acikin nata,amma bata samu damar yin hakan ba,saboda fargabarshi da take ji,

 

   A wani irin gajiye ya shiga bedroom ɗinshi yana faman lumshe blue eyes dinshi saboda baccin da yake ji,yana ƙarasawa ciki yasanya hannayenshi tare da ɗebe rigar jikin shi gaba ɗaya,ya azata asaman laundry basket dinshi,zame belt ɗin wandonshi yayi sannan ya zame shi daga jikinshi ya ajiye shi asaman rigar,ya rage daga shi sai shorts ajikinshi,

   Komawa yayi tare da hayewa saman royal bed dinshi ya kwanta don ya ɗan runtsa,sosai ya miƙe saman gadon yana faman sauke ajiyar zuciya har bacci yayi awon gaba dashi,almost 6 mins sai ga sehrish ta fito daga cikin toilet ɗinshi,tunkarar gadon tayi saboda ta ɗauki mayafinta sai da ta kusa dab da gadon sannan idonta suka hango mata Boss Man ɗin nata kwance yana bacci,wani irin bugu taji zuciyarta tayi mata har sai da taɗan ja da baya tana kallonshi,hannu tasa tare da ɗan murza idanunta donta tabbatarwa idonta abunda take gani wai ko gizau ne,amma zahiran taƙara shaida cewa sgr ne da kanshi ya dawo,

    Hankali kwance yake baccin shi,ya zagayo da left hand dinshi ta saman sumar kanshi,yayin da hannun damanshi ke asaman shafaffen cikinshi,

  Ji tayi bazata juri kallon surar jikinshi ahaka ba saboda gudun jefa kanta cikin matsala,don ba ƙaramin fisgarta yake yi ba,kamar irin magnet din nan,

   Har ta kama hanyar fita daga bedroom din nashi cikin sauri taji jelar gashinta na gogar hannunta,tsayawa tayi Cak tunawa da Mayafinta data ajiye asaman gadon nashi kafin tashiga gyara mashi toilet ɗinshi,a hanzarce ta juya tana kallon inda ta ajiye mayafin,waro ido waje tayi cike da fargaba ganin yarda sgr ya mamaye mayafin nata gaba ɗaya,ya kwanta asaman shi,tabɗijan can

   Tunani tashiga yi kodai ta tafi tabar mashi mayafin tunda ba iya ɗaga shi zatayi ba,wata zuciyar kuma tace,idan ya farka ya samu mayafin naki asaman gadonshi bakya tunanin cewa zai iya zargin wani abu akanki?dole ya tuhume ki akan miya kawo mayafinki saman shimfiɗarshi,haka in kika fita ba mayafin wani ya ganki kin fito daga part dinshi haka fa,kiyi tunani sehrish barin mayafin risky ne,haka zalika daukarshi ma zai iya zama risky,

  Runtse idanunta tayi tamkar ta fasa ihu saboda tsabar takaici,taji haushin cire mayafinta da tayi tun farko da bata jefa kanta cikin matsala ba,

   Nan fa tashiga tunanin yarda za’ae ta dauke mayafinta batare da Sgr ya farka daga baccin shi ba,

  cikin sanɗa sehrish ta soma tafiya a hankali tana tunkararshi a tsorace batare da sautin takon tafiyarta na fita ba,

  Sai da tazo dai dai kusa dashi sannan tashiga cizon yatsa tana tunanin wai ma taya zata janyo mayafin daga jikinshi,Sehrish da kasada,

Hannu tasa tare da ɗan kamo mayafin daya leƙo daga bayanshi tana janshi a hankali don ya sulalo daga bayanshi,amma ko motsi wannan baiyi ba don ba ƙaramar danna sgr yayi mashi ba,gaba ɗaya nauyin jikinshi na akan mayafin taya zata iya janye shi!?

  tun tana jan mayafin a hankali yana turjewa har takai ga hasala tashiga janshi da ɗan ƙarfi har sai da sehrish tashiga fitar da wani irin gumi a fuskarta,sakin mayafin tayi tana faman huci,duk da haka bata daddaraba,sai tasa hannu tare da dafa mattress ɗin ta haye saman gadon kaɗan daga gefenshi,hannu takai zata ruƙo mayafin karaf idonta suka sauka akan farar fatar ƙirjinshi,mayar da idonta tayi akan damtsen hannunshi,haryanzu akwai sauran zanen nan nashi na tattoo bai ƙarasa gogewa ba gaba ɗaya,tun farkon zuwanshi 9ja tare da zanen ajikinshi ya dawo kamar tambari ne na mukaminshi ba ƙaramin kyau yayi mashi ba,

    Gaba daya sehrish ta shagala da kallon surar jikinshi,kafin tayi wani aune,Sgr yayi wani irin kwakkwaran juyi zai gyara kwanciyarshi,aikuwa gaba ɗaya ya haɗa da sehrish yayi juyin tare da sanya hannunshi yayi hugging ɗinta tighly a faffaɗan kirjinshi,duk a tunaninshi pillow ne ya rungumo hakanne yasa ya matseta sosai a ƙirjinshi kamar yarda  ya saba rungume pillow in zaiyi bacci wani sa’in,tashin hankali da ba’a sama shi date,

   Tabɗijancan,ƙiris ya rage sehrish ta saki fitsari saboda tsabar tsoran da taji,hankalinta yayi matuƙar tashi,saboda tasan mai zai biyo ba in sgr ya farka yaganta manne ajikinshi,yasan na jiya taimakon shi tayi gudun karya faɗi,na yau kuma mai zai kira shi!?meya kawota saman gadonshi da har ta faɗa jikinshi!?

    yarda ya matseta a ƙirjinshi ko kwakkwaran motsi sehrish ba ta iya yi,ba ƙaramin ruƙo yayi mata ba,tunkan ya farka taga irin hukuncin da zai yi mata harta fara zubar da hawaye,kai tsaye kuma hawayen suke shafar fatar jikinshi,

  sai faman shessheƙar kuka takeyi ƙasa ƙasa yayin da la66anta ke gogar fatar breast dinshi,gaba ɗaya Wannan jan bakin data shafa ya koma a fatarshi,sosai zanen lips ɗin sehrish ya fito raɗau tare da kalar jan bakinta maroon colour,duk bata lura da hakan ba,saboda la66an nata amanne suke a wurin,

  Tana cikin wannan yanayin tajiyo takun tafiyar mutum a falonsa alamar ana tunkaro bedroom ɗinshi,hakan ba ƙaramin firgita sehrish yayi ba,nan take tashiga haɗiyar yawu a tsananin tsorace,

  Muryar Abbansu tajiyo yana cewa”Wai har yanzu rafayet bai dawo bane?inaso naji ko sunyi waya da Mommynshi ne game da zuwanta Nigeria,’

   “Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un,”sehrish ce ta ambaci hakan acikin zuciyarta,”Shikenan na mutu wayyo Allah na,ya Allah ka kawomun ɗauki,daga wannan sai wannan……’bata ƙarasa zancen zucin nata ba tajiyo muryar Marshal Omar yana bashi amsa da cewa”Abba ashe muna da manyan baƙi cikin watan nan,don munyi waya da goggon katsina ma ta sanar dani cewa mu shirya ma zuwanta don in ta tashi zuwan bazata zata yi kuma ba zata tafi ba har sai taga An shafa fatihar kowannan mu…..’ ya ƙarasa maganar da dariya a fuskarshi,

  Suna tafiya suna nufar bedroom ɗin sgr yayin da suke fira a tsakaninsu,

  Abban nasu yace”Albishirinka,”

  Cike da zumuɗi Omar yace”Goro,”

 “Fari ko ja”? Abban nasu ya tambaya fuskarshi ɗauke da murmushi,

 Omar yace”Fari,”

 ƙayataccen murmushi Abban nasu ya saki kafin yace”Uncle ɗinku Abusufyan shima yana nan tafe insha Allah,sannan Auntynku azeema tana nan tafe,uwa uba kuma Ammynku itama tana nan tafe,don haka ku shirya don ta sanar dani cewa muddin tazo sai an ɗaura auran kowannanku,da alama zata zo tayi yaƙi da tazuranci ne acikin gidan nan…..’ƙarasa maganar yayi muryarshi ɗauke da dariya,shima Omar dariyar yayi yana girgiza kai yace”Abba Allah yaso ni,ina da wadda nakeso,don haka ni bani da matsalar komai wlh,Alhamdulillah Allah ya kawota Lafiya musha biki,’

 Cike da mamaki Abban nasu yace”wai dagaske Omar kana da wadda kakeso?hakan na nufin kayi budurwa baka sanar dani ba”? 

  ɗaga kai Omar yayi alamar eh,wani irin farin cikine ya cika abban nasu har ya gaza magana sai faman sakin murmushi yake yi yana cewa”Ikon Allah,”

  A ƙopar shiga bedroom ɗin sgr suka tsaya suna cigaba da tattaunawa cike da nishaɗi atsakaninsu,

   Saboda tsabar tashin hankali har wani zazza6i ya lullu6e sehrish tuni temperature ɗin jikinta yayi wani irin zafi,zuciyarta har wani bugu takeyi daram!daram!!fargabarta karsu shigo su same su a wannan yanayin ita da sgr,

    Hayaniyar da suke yi ce,ta fara disturbing ɗin baccin nashi,hakan yasa ya fara motsi alamar zai farka,waro ido waje sehrish tayi cike da fargaba jin alamar zai farka,

   Hannunshi ya janye daga ruƙon da yayi ma sehrish,hakan ne ya bata damar kufcewa daga jikinshi,kamar walƙiya haka ta mirgina tare da faɗawa ƙasan gadon,sam bata ji zafin buguwar da tayi ba,tana faɗowar nan ta yunkura tare da miƙewa tayi wuff ta faɗa bayan labulan ɗakin shi,

  Shigarta ke da wuya,Abba da marshal suka shigo cikin ɗakin nashi atare bakunansu ɗauke da sallama,

   A hankali sgr ya soma buɗe idanunshi dake cike da bacci ga wata irin kasala data mamaye shi don baccin bai ishe saba,daƙyar ya iya sa hannunshi tare da dafa mattress ɗin ya tashi daga zaune tare da jingina back ɗinsa asaman pillow yana kallon Abban nasu tare da Omar sai faman lumshe ido yake yi,

   Zama Abban yayi daga gefen gadon nashi yana kallon fuskar kyakkywan yaron nashi yace”Rafayet bacci kuma a irin wannan lokacin?ko baka ga time bane?

  Sai lokacin sgr yakai idonshi akan diamond clock ɗin dake manne a bangon ɗakinshi ƙarfe 6:30 na yamma,

   lumshe idonshi yayi kafin ya waresu akan Abban nasu yace”Abba bansan time ɗin da baccin ya ɗauke ni ba”

   jinjina kai abban nasu yayi

 kafin yayi yunƙurin cewa wani abu karaf idonshi suka sauka akan jan bakin sehrish dake zane asaman breast ɗinshi,

  waro ido waje abban nasu yayi tare da cewa”Kai me nake gani haka kodai idona ne”?yarda yayi maganar a ruɗe yasa marshal Omar ɗan matsowa daga tsayen da yake ya russina yana ƙare ma Ƙirjinshi kallo,cike da mamaki Omar yace”ba shakka Abba,ba idonka bane wannan alamar sumbata ce,ga zanen la66an mace nan raɗau asaman fatar kirjinshi,

   Gaba daya sun gama confusing ɗin Sgr,sam bai gane inda zancen nasu ya dosa ba,”

     Hankali atashe Abbansu yace”Rafayet tell me the truth!wa kayi feeding haka har ta goga maka jan baki asaman breast dinka!!!”

   Saboda tsabar kiɗima tuni jikin sehrish ya soma tsastsafo da wata irin zufa,duk da sanyin ac dake gauraye da ko’ina,

     Ganin yarda sgr ya dabarbarce kamar bai gane kan me suke magana ba,hakan yasa omar ƙarasawa gaban dressing mirror ɗinshi,yasa hannu tare da ɗauko ƙaramin madubin dake ajiye asaman shi,

  Ƙarasowa yayi wurinshi tare da saita mashi madubin yarda zai gani da kyau,

  Ware manyan idanunshi yayi yana kallon zanen la66an dake asaman chest ɗinshi cike da tsananin mamakin a ina ya same shi…….

Domin Sauke Littafin book 3 Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃

*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI.  MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*

*LOCATION KANO*

08062073990

Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka 

Wadrobe balls 

Madarar kulleccham 

Vaseline kulleccham 

Kajiji

Halut

Couscous 

Khumrah 

Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku

Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka 

Wadrobe balls 

Madarar kulleccham 

Vaseline kulleccham 

Kajiji

Halut

Couscous 

Khumrah 

Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku

It’s not just good …it’s finger linking good faster than fast food, better fine dining.

Snack

Awarah 

Farah

Zobo

Samosa

Cup cake etc 

Contact me 09063302182or 09012179727

Back to top button