KAI KA FI CANCANTA… CHAPTER 1
Jamila Umar Tanko
(JUT)
FARKON LABARI
La’asar sakaliya garin Kano ya yi sanyi, ga yanayi irin na farkon shigowar damuna. Iska mai sanyi ta na kad’awa tana fifita duk wani mai rai da ke cikin wannan garin. Babu abinda za ka dinga hangowa sai korayen ganyen dake kadawa, tufafin jamaa yana kadawa, don haka jama’ar da ke giftawa su na tafe cikin nishadi ba tare da gajiya ko wahalar tafiya ba.
Alhaji Bakura matashin mutum ne dan kimanin shekaru arba’in cif-cif. Wanda ke tafe cikin tsaliliyar motarsa qirar INFINITI EX 32 SUV. Mai launin ruwan toka (silver), kasancewar sanyin iskar da ke kadawa tafi sanyin A.C motarsa dadi sai ya kashe ya bude gilasan wanduna, ya na tafe iska na kada shi. Nan da nan ya tsinci kansa cikin nishadi, kallo daya za ka yi’ masa annurin fuskarsa ya tabbatar maka da hakan. Dadin dadawa ma kid’a da wakar D’an kwairon da ke tashi a hankali daga cikin rediyon motarsa ya k’ara masa nishadi.
Mace duk kawaicinta da kunyarta idan ta kalli Bakura sai ta sake kallonsa saboda mutum ne kyakykyawan gaske mai kyawun fasali, Allah Ya tsara halittarsa a jikin Bakura. Dogo ne sosai mai bakar fata lallausa mai shek’in kyau, gashi da dogon hanci gami da dara-daran idanuwa, bakinsa madaidaici mai k’unshe da wasu kyawawan hak’ora masu matukar haske har da wasu siraran wushiryoyi a sama da k’asan hakoran, yana da bak’in dadashi wanda ya kara fito da tsananin farin hakoran.
Duk da kyawun da Rabbul samawati Yayi masa sai Ya yi shi mutum mai tsananin tsafta da son kwalliya hakan ya sake fitar masa da kyawawan suffarsa a fili. Kwalliya ba ta tafiya daidai Idan babu kudin da za’a sayi kayan kwalliyar, amma Bakura yayi sa’a Allah Ya hada masa dukka. Ya bashi arziki mai yawa don a yanzu haka shahararran dan kasurwa ne a cikin k’asar nan har ma da kasashen k’etare baya ga dinbin ilimin qur’ani da na boko da Allah Ya bashi. Domin mahaddacin kur’ ani ne, a bangaren boko kuwa Masters gare shi a bangaren Engineering.
Kallo daya za ka yiwa yadin dake jikin Bakura ka tabbatar da tsadarsa saboda kwanciyar da yayi luf a jikinsa don laushi, yadin mai launin ruwan madara(cream) sai ya saka bakar hula da bakin takalmi tsadaddu.
Kamshin turaren jikinsa kuwa duk ta inda ya gifta fiye da minti talatin kamshin baya barin wajen. Bakura dan mutanen Maiduguri kana ganinsa ka ga Kanuri kasancewar anyi masa tsage irin na barebari fashin goshi da tsage bibbiyu a kuncinsa, amma sai idan ka k’ura masa ido sosai sannan za ka iya tantancewa akwai tsaga a fuskarsa domin zanen bai fito rangadadai ba.
Mutum ne mai yawan fara’a da son zolaya idan ya ga dama, amma fa wasu lokutan akwai tsare gida, idan ya b’ata rai babu mai iya sa shi dariya. Dokoki ya gindayawa iyalansa da duk wasu da suke zaune a qarqashinsa kala-kala a, kuma dole su bi idan su na son su zauna da shi lafiya. Mutum ne wanda baya son raini, baya son rashin tarbiyya da rashin kamun kai. Baya son sakaci da addini.
Hatta yadda ake yin magana ya koyawa yaransa da matarsa, yadda za su dinga fitar da sautin maganarsu a nutse ba’a baragada ba. Idan ka shiga gidansa za ka tabbatar akwai tarbiyya domin qarami ya na girmama na gaba da shi duk qanqantar shekarun da ke tsakaninsu. Gashi d’an boko komai a tsare yake an rubuta a time table kamar lokacin tashi daga barci, lokacin sallah, lokacin cin abinci, lokacin makarantar boko da islamiyya, lokacin kallon talabijin ko hira, lokacin da yara za su dinga fita farfajiyar gidan da kekuna su zazzagaya. Haka lokacin fita wuraran shaqatawa ma an ware kamar Zoo, shopping a super markets, cinema da dai sauransu. Idan aka yi dogon hutu kuma an rubuta qasar da za’ ayi visa su dunguma su tafi har da wasu daga cikin masu aiki.
Tsanani irin na Bakura ba akan iyalinsa kad’ai ya tsaya ba, abun ya shafi ‘ya’yan makwabtansa ma. Za ka ga yaran makwabta sun ga mahaifinsu ba su razana sun daina fitinar da suke yi ba, amma su na ganin Bakura za su nutsu dan tsoro da kwarjini hade da girmamawa da suke yi masa. Domin shi halinsa ko wucewa ya zo yi ya ga yara su na rashin da’a zai dawo baya ya kira yaron yayi masa fada, idan ta kama da murde kunne ya murde, idan kuma ya ga ya san mahaifin yaron ko yarinyar lallai kuwa zai yi sallama a gidan ya fad’awa mahaifinsa cewar ga fitinar da d’anka yake yi a waje don haka a kula a saka ido.
Duk da wadannan tsauraran matakai da ra’ayi nasa bai sa jama’ ar unguwa da iyalansa sun tsane shi ba saboda Allah Ya gani tsakani da Shi ya ke duk abinda ya yake yi ba dan ganin ido ba ne, dan haka Allah Ya zamar masa jagora, Ya bashi farin jini a wajen iyayen yara da kwarjini a idon yaran gari.
Haka kuma a zamani irin wannan da wuya ka sami mutum mai arzikin da yake taimakon jama’ar gari da daukar nauyin iyalinsa irin Bakura. Mutum ne mai matukar kyauta da kyautatawa. A kullum kuma a koda yaushe bayarwa yake dare da rana mikawa yake, saboda haka ubangiji Ya ke sake buda masa.
*** *** ***
Akan Titin Lamido cresent ya ke tafiya da zummar zai tafi masallacin Sheik Aminuddin don daukar karatun yamma da na bayan magruba kamar yadda ya saba zuwa duk ranar jumaa da ranar asabar.
Tafiya yake yana bin waqa wacce baitocinta ke burge shi saboda an zuba hikima da habaici da zambo. Kamar daga sama ya ga wata budurwa ta tsallako ba tare da ta duba titi kafin ta tsallako ba. Saura qiris ya buge ta sai da ya yi da gaske sannan ya iya taka burki gami da yin sauri ya dauke kan motar, saura kadan ya afka cikin kwalbatin da ke gefen hanyar. Irin qaran da burkin ya yi, hayaqi da warin taya kai ka ce gagarumin hadari aka yi Allah Ya sa babu mota a bayansa.
Ya jima a zaune a cikin mota zuciyarsa na bugawa ba tare da ya san abinda zai yi ba kuma amma ya ji dadi matuqa da ya ga yarinyar a tsaye ba ta fadi ba dan haka ya tabbatar bai taba ta ba. Ya ci gaba da yiwa Allah godiya a bayyane.
Abin mamaki yarinyar ba ta firgita ba ko kadan ta juyo ta dube shi a fusace ta harare shi ta yi tsaki ta ce ” ka je a koya maka tuqi, banza kawai.” Ta tsallaka da sauri ta ci gaba da tafiya har tuntube take yi, kallo daya za ka yi ma ta ka tabbatar a gigice take. Daga nan ya tabbatar abinda ya biyo ta ya fi kadewar mota firgici.
Ya ji kalamanta tamkar a mafarki yadda yarinya qarama ‘yar cikinsa ta tsaya ta zage shi bayan laifinta ne ma.Ya ji zafin zagin nan sosai, ya tabbatar ba ta da tarbiyya. Amma bai gama yanke hukunci gaba daya ba don ta burge shi kasancewar sanye take da dogon hijabi tun daga kanta har idon sawun kafarta, ya na yi mata kyakykywan zaton ba rashin tarbiyya ba ne firgicine kawai ya sa ta zage shi. Ya bi ta da kallo ya na mamakin irin sauri da ta ke yi. Tana tafe tana ta waiwaye-waiwaye kamar marar gaskiya har. Ya ji a jikinsa in bai bi bayan yarinyar nan ya bincike ta ba bai yiwa kansa adalci ba. Ya juya kan motarsa da sauri ya fara bin ta a hankali. Wani lungu ta shige, tun kafin ta shiga ya hango ta yaye burgujejen hijabin nan da yake burge shi ta cusa a leda, sai ga mace cikin matsatstsun kaya ta bayyana. Babu jimawa ta fito sanye da riga da wando da wata ‘yar jaka da takalmi mai tsini, wani dan yalolon gyale ne ta yafa akanta ana hango gashin kanta gara ma ace babu gyalen.
Ya ji gabansa ya yanke ya fadi daga nan ya fara jin sanyin zagin da ta yi masa tunda ya tabbatar ba mutuniyar kirki ba ce, za ta yi abin da ya fi haka ma. Ya yi sauri ya d’aga gilasan motar dan kada ta gane shi. Tagumi ya yi kawai yana kallonta nan da nan ya fita daga cikin hayyacinsa ganin halin da yarinyar nan ta shiga, yayi matukar tayar masa da hankali.
Yarinyar ta dubi motar Bakura duba sosai don ta gani ko akwai mutum a ciki ya na kallonta ko kuwa parking kawai a kayi ba kowa. Amma ta kasa gane inuwar mutum kasancewar ba farin gilashi ba ne ya na da dan duhu, na ciki na ganin na waje na waje baya ganin na ciki .
Sai hankalinta ya kwanta ta wuce ta na rangwada ta nufi wajen wata farar mota kirar AUDI A4 4dr dake can gefe guda a ajiye.
Babu alama mutum a ciki kasancewar gilashin motar bakikirin ne.Ta tsaya a jikin motar a daidai wundon direba ta na kwankwasawa, fiye da mintuna biyar ba’a bude ba, sai daga baya aka bude kofar motar. Sai ga wani dogon saurayi wankan tarwada mai dogon hanci gami da dara-daran idanuwa, ya bayyana, ya fito ya tsaya a gabnta.
Hakika saurayin ya hadu yana da kyau wanda duk wata mace za ta so shi a matsayin saurayinta, sai dai kyawun d’an miciji ne idan ka zauna da shi za ka san bashi da tarbiyya gara ma ka zauna da kumurcin miciji akan ka zauna da mai irin halayensa.
Sanye yake da bakin wando jeans da farar riga matsatstsiya ‘yar qarama mai dan qaramin hannu, fuskarsa cike da wani kwabcecen gilas baqi qirin.
Takalmin qafarsa kuwa wani danqareran kambas ne tattaura mai launin fari da baqi irin na samarin zamani, wanda idan aka jefe ka da shi ko aka taka ka da shi ka tabbatar gadon asibiti zai yi bakuncinka. Yatsun hannayensa dukka goma zobbuna ne rangada rangada. Askin kansa kuwa kai kace shataletalan titi ne (round about) da rassan titina guda hudu gabas da yamma kudu da arewa, wanda duk ta inda aka bullo za’a hadu a tsakiya.
Bakura ya na zaune a cikin motarsa ta mudubin saman gilashin gaba ya na hango bayansa ya na dubanşu tsaf cike da takaici ya rasa dalilin da ya sa zuciyar sa ke bugawa dan fargaba da b’acin rai.
Gabansa sai faduwa yake yi tamkar, ‘yarsa ce ta fad’a hannun tantirin niga irin wannan. Sai dai kaşh sun yi masa nisa ba zai iya jiyo abinda suke cewa ba. Ya yi zuruf ya fito daga cikin motar ya rufe, sai ya yi tamkar sabgar gabansa yake yi kamar bai san abinda suke yi ba, ya na tafiya ya na wayencewa kamar bai san da su ba amma wajensu ya tunkara. Bai yi wahalar qarasawa inda suke ba ya fara jiyo abinda suke fada tar a kunnuwansa. Sai kuwa ya ci sa’a akwai wani qaramin masallaci da famfo a wajen. Ya qarasa wajen famfon ya bude ya dinga kurbar ruwa yana wanke fuskarsa, ya kasa kunnuwansa sai ya ji yana jiyo komai ba tare da sun gane su yake saurara ba. Sunan daya ta ambata shi ne Abdul majid shi kuma ya ambaci sunanta Sajida.
Abdulmajid ya ce da Sajida ‘ni ba bawanki ba ne, kuma ba direbanki ba ne da zan yi miki waya fiye da awa daya sai yanzu ki ka fito. Daga an yi magana sai ki ce Baba da Umma ne suka hana ni fitowa. Ai babbar matsalar iyaye ‘yan gargajiya kenan komai sai ace addini kuma addinin na su duk kame-kame ne, sun hana yaransu shakatawa a banza. Wallahi ba dan Allah Ya jarrabe ni da sonki ba da tuni na rabu da ke, tun sanda tsohonki ya hana ni zuwa qofar gidanku, har yanzu ina jin zafi da quna irin wulakancin da tsohon nan ya shuka min a gaban mutane har yanzu bai bar zuciyata ba. Ke ana son a wayar dake a kwatar miki ‘yancinki amma kin k’i yarda, kin zauna ki na bin dokar ‘yan gidanku gidadawa. Wai ku ustazai, malamai kuma almajirai.”
Babu abinda Sajida take yi sai karkarwar jiki, babu furucin da yake fita daga bakinta sai ” Abdul majid kayi hakuri, dan Allah dan Annabi ka yi hakuri.”
Abdul majid ya yi mata wani kallo na wulakanci ya zare bakin glashin dake fuskarsa ya tabe baki.
Ya ce “ki na nufin da wadannan kayan na jikinki za ki bi ni party? Ki na nufin da dogon wando da gyale zan shiga dake wajen hadadden party da hadaddun abokaina? Ke bakauyiya ce har yanzu kin kasa wayewa.”
Sajida ta dubi jikinta sama da kasa ta rasa illar dake tattare da ita. Wandon jeans ne hadadde kuma matsatstse shine ma ya siyo mata daga America, haka itama rigar a matse take.
Tunanin da take yi ya katse ya ce “dole in kai ki wani kanti in siya miki kaya, mini skirt za’a saka iya cinya da zurmukeken takalmi mai tsini irin mai zif din nan har gwaiwa da riga shimi iya kirji wacce ba ta rufe cibiya ba, kuma babu ke ba zancen dankwali, kin ci sa’a ma ki na da gashi ba sai an qara miki ba.”
Sajida ta zabura ta dubi Abdul Majid cike da fargaba ta ce “riga iya kirji?”
Ya daka mata tsawa ya ce “to meye, ki na nufin ba za ki iya sawa ba ne?”
Tsoransa take, sonsa ta ke don haka ba ta iya yi masa musu.
Ta ce “zan saka mana.” Ta dubi agogon dake daure a hannunta daga dukkan alamu ta qagu ta koma gida don kada a nemeta. Wannan karon ma tsawa ya daka mata mai firgitar da wanda ke kusa da su, ba ma wacce aka yiwa ba. Nan da nan jikinta ya hau karkarwa.
Ya ce “duba agogon me kike yi, ko yau ma an baki lokacin da za ki komą gida ne?”
Sajida ta na karkarwa
ta ce “a’a ba duba agogo nake yi ba, yi hakuri.”
Ya ce “to zagaya ki shiga mota mu tafi.”
Sand’a ta ke kamar wacce kwai ya fashe ma ta a ciki, saboda ba ta son shiga motar amma tsoransa ta ke ta kasa ce masa ba za ta je ba.
Bakura ya dago da sauri zuciyarsa tamkar ta fashe, tashin hankali ya rufto masa lallai kuwa zai shiga wani mummunan hali idan har ya bari yaron nan ya fita da yarinyar nan ya je ya ba’ta mata rayuwa ba tare da sanin iyayenta ba. Tabbas abin zai dad’e bai fita daga cikin zuciyarsa ba zai ga kamar ya ci amanar musulumci da iyayenta da ita kanta.
“Tabbas yaron nan ya na niyyar ruguza tarbiyyar da iyayenta yarinyar nan su ka dade su na gina mata.” Ya fada a ransa.
Sai ya ji wani hawaye mai zafi ya surnanu masa, yaransa ne kawai su ka fad’o ma sa a rai, gaba d’aya ya ji ya shiga zargi anya kuwa shima ba ci gaban mai haqar rijiya ya ke yi ba kuwa, kullum haqa ya ke amma ya na qara yin qasa. Anya kuwa ba tufka ya ke yi wani ya na warware masa a waje ba kuwa? Ya tuna hadisin da Manzon Annabi (S.A.W) ya koyar damu ce wa “idan ka ga ana aikata 6arna to ka hana da hannunka, idan ba za ka iya ba to ka gyara da bakinka, idan ba halin haka to ka qi abin a zuciyarka wannan shine mafi raunin imani.”
Nan da nan ya ji a ransa zai iya zuwa ya hana da baki tunda bashi da ikon gyarawa da hannu. Ya zabura zai je wajensu kenan don ya ba ta shawara da baki ya ce kada ta bi shi. Sai ya ji Abdul Majid ya ce da ita “da fatan kin fad’a a gida cewar kwanaki biyu za ki yi ko?”
Gabanta ya fadi ‘rass’ ta dafe kirji ta tambaya cikin firgici “kwana biyu?”
Ya yi mata tsawa ya ce “toh meye abin fargabar, ban isa da ke ba ne? A Abuja Nicon Hotel za’a yi casun kuma sai qarfe d’aya na dare za’a fara dan haka daga nan ma Abuja za mu wuce.
Sajida ta zagayo da sauri in da yake ta tsugunna a gabansa ta fashe da kuka ta ce “Abdul majid ka taimake ni, ka rufa min asiri kada ka yi fushi da ni. Da ka san ta yadda aka yi na fito yanzu ma da sai ka tausaya min. Sai da na yi dubara da magiya Babana ya bari na fito da zummar zan je gidan su Asiya kawata in karbi qur’ani. Mintina talatin ya ba ni kasancewar gidan babu nisa ya na gida ya na jirana. My dear, idan na bi ka Abuja har kwana biyu kashe ni ne kawai ba za’ a yi a gidanmu ba, ka rufa min asiri. Ina sonka Abdul Majid fiye da yadda na ke son rayuwata.”
.
Fatan kowa zai bada nasa gudumowar, like comments da share, mu samu ci gaba akan sauran littatapai tunda wannan sabon littafi ne a gidan nan, a samu a gama da wuri.