Halysaah Page 78 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 78…
Khaleesat tayi picking call din ta kai kunne tayi shiru, after some seconds ta mayar da wayar cikin jaka ta kalli Safiyyah tace “Makulli zai amsa” Safiyyah tace “Toh shi ina na shi makullin? Haba, he is a kind of person that is way too organized da har za ace zai manta makulli a gida, ai irinsu are always cautious of everything, ta yaya zai mance abu me muhimmanci kamar makulli, shi dai yasan me yasa ya kira ki amma ba wai makulli ba” Khaleesat tace “To ni dai bai taɓa requesting makulli a wajena ba sai yau, probably he was carried away shi yasa ya manta, waye baya mantuwa” Safiyyah tace “To meye na wani karesa?” Khaleesat tace “A’a ba karesa nake ba, naga kamar you are trying to put meaning into everything” Safiyyah tace “Ko me yasa Housemate zai wani hada ku waje daya salon ku saba, ke dama gashi zuciyarki kamar ta yara mutum na maki kirki sau daya to har abada yana da kirki a wajen ki” Khaleesat bata san sanda ta fara dariya ba tace “Wa yace maki mun saba? An ce maki har yanxu baya masifarsa ne? Kawai dai bayan masifar tasa he will still be kind to you and give u a listening ear that’s one thing about him, kin tuna abincin da na kawo school ranan har kika hanani kika cinye duka?” Safiyyah tace “Ehen sai aka yi yaya?” Khaleesat tace “To shi ya dafa” Safiyyah ta bude baki tace “Ban gane shi ya dafa ba, wannan abincin da nayi ta santin sa kina nufin girkinsa ne?” Khaleesat tayi dariya tace “Wallahi…. he can cook so well fiye da tunanin ki, amma iya jollof rice, sai rice and stew da Alfredo pasta kawai ya iya, i notice su ne favorite food dinsa, he can also make you different kind of salad and fruit salad, yana son su sosai….” Safiyyah ta hade rai, sai kuma ta taɓe baki tace “To shi ne ya burge ki kike haƙilon bani labari? Nasan Housemate ma babu abinda bai iya girkawa ba kawai chance ne baki basa yayi maki ba, beside he is always busy ina yaga lokacin wani girki” Dariya sosai Khaleesat tayi tace “See me see trouble, ni kin ji na ce maki Housemate bai iya ba? To in gaya maki bai ma iya din ba, sanda muke old apartment dina ba sai dai in dafa ya diba ba, shi ko wanke wanke bana tunanin ya iya balle shara da gyaran gida” Tana dariya ta kare maganar, Safiyyah ta wani kalleta tace “Abinda shi ba mace bane ta yaya zai iya wanke wanke ko kuma ya fara girke girke a kitchen kamar wani da ya taso cikin mata, girki da gyaran gida ai sai mata, ni tun da aka haifeni ban taɓa ganin Yarima da girki ba ma sai wannan karan, kawai dai wahalalle ne wannan Yariman….” Khaleesat ta kasa daina dariya tana kallon Safiyyah tace “OCD fa garesa, baya cin abincin wanda bai yarda da shi ba shi yasa yake kayansa da kansa, kika sani ko a can masarautar su akwai masu yi masa girki? Even here in America ai yana cin abincin Cook din gidansu….” Safiyyah tace “Ashe ma kawai kina zaune da wanda ke maki kallon gagarumar kazama ne tunda baya cin girkin ki, in ni ce ma bazan zauna gida daya da shi ba yana min kallon katuwar kazama, shi ne har kike bada labarinsa kina babbaka dariya bayan ya gama raina tsaftar ki, to meye abun dariya a nan, sannan kawai daga barin ki da shi a gida shi ne zaki je ki sake masa fuska har haka bayan kin san ɗan uwansa mutuwar son ki yake? Ai kamata yayi tsakanin ki da shi a gidan gaisuwa sama sama, don Housemate dinmu bazai ji dadin ganin kina washe ma Cousin brother dinsa hakora ba” Khaleesat ta hade rai tace “To ni yanxu ce maki nayi abu na hadani da shi a gidan ne wai?” Safiyyah ta daga hannu biyu sama tace “A’a kar ki canza baki Malama, bana son karya, yanzun nan kika gama yaba ma mutum kina cewa he is kind and caring amma kina neman lauye magana, in ba sake masa kika yi ba ta yaya kika san he is down to earth? Wato ke kawai kulasa kike yi kaca kaca a gidan ma kenan” Khaleesat tace “Ni dai wallahi ban ce maki haka ba kece dai baki fahimce ni ba, mutumin da ba magana ma sosai yake min a gidan ba” Safiyyah tace “Oho dai ni har kin bata min rai wallahi, sai kace wata kuturwa meye na dinga cin abincinsa da ya dafa da baza ki dafa naki ba” Khaleesat dai kallonta take, Safiyyah na gyara ɗankwalin kanta tace “Housemate ai bazai ji dadi ba fisabilillahi, ni ma kaina ban ji dadi ba balle shi da baza a rasa sa da kishi ba tunda duk mun san yana sonki” Ita dai Khaleesat bata ma san me zata ce ba, amma da gaske Ajay ko lkcn kulata ma baya da shi a gidan, iyaka yayi masifa in ta debar masa abinci kuma wani lkcn late take komawa gida shi yasa ma bata girkin in taga yayi sai ta debi nasa, kuma kaɗan yake dafawa kamar abincin rowa, can ta taɓe baki tace “Wai ke ance maki yana da time dina ne a gidan, shi fa kawai ya kalli football ko wrestling or boxing sai kuma ya buga PS5 dinsa” Safiyyah ta kalleta da sauri tace “Ke haba, da gaske? yaushe ya kawo PS5 din?” Khaleesat tace “Oho kawai gani nayi nima” Safiyyah tace “Ki ce wataran idan naje gidan baya nan za mu buga” Khaleesat tayi dariyar da bata yi niyya ba tace “Za ki buga dai, ni ba ruwana” Safiyyah tace “Kin tuna na saurayin former Housemate dinki Nancy, a sannan fa kema kika iya, Mutumin kirki haka ya bar mana ps4 dinsa a gidan da yaga muna so, kullum sai naje apartment dinki saboda shi lokacin muna level 2, mu yi ta buga game” Khaleesat tace “Hmm na tuna, ai yanxu ma idan naga yana yi sai in makale in ta kallo, kamar inje inyi” Safiyyah tayi kasa da murya tace “Wani rana da wani rana ne baya zaman gidan?” Khaleesat tace “Every Saturday saboda ina tsayawa school mu yi karatu baya zama gidan sai sanda zan dawo da yamma yake dawowa shi ma” Safiyya tace “Tunda dai ba mu muka kawo karatun nan duniya ba, gobe kawai in kin taho school sai mu koma apartment dinki tare da sauri mu buga PS5 din, abinda ma mun gama karatun course din da za muyi ran Monday in de ba haram za mu kara karantawa ba, kawai mu je mu shoshale a apartment din ki da Ps5” Khaleesat ta zaro ido jin wayarta na vibrate tace “Lahh, na manta ban kai masa key din ba” Safiyyah tace “Je ki kai masa ki dawo mu ci gaba da maganar mu, ai ni ban san yana da ps5 ba” Khaleesat ta mike ta bar wajen, duk da hadarin dake gari Safiyyah ke ce mata taje ta dawo su ci gaba da magana ko a jikinta idan ruwa ya musu duka. Khaleesat bata karasa inda Ajay yayi parking ba aka fara yayyafi, tana isa wajen ta bude front seat ta mika masa makullin apartment din, zata kulle motar yace “Kwana za ki yi a makarantar?” Tayi shiru bata ce komai ba, can tace “To zan je in ma kawata sallama” Yace “Ohk” Juyawa tayi ta koma inda ta baro Safiyyah, Safiyyah na ganinta tace “Kin ga an fara yayyafi, mu koma department mu ci gaba da maganar mu…” Khaleesat tace “Gida ma zan wuce” Safiyyah ta tabe baki tace “Motarsa za ki shiga kenan? Dama abinda yasa ya kira ki kenan ya ga hadari” Khaleesat tace “To ba waje daya za mu ba in ma saboda hakan ya kirani? Dama dawowa nayi in maki sallama sae gobe” Safiyyah tace “Ai shikenan” Khaleesat tace “Ko kuma tunda hanya daya ne mu je yayi dropping din ki kawai mana” Safiyyah tace “Wa?? Gwara inyi trekking inje gida, salon ya koreni, kema da kike iyayin cewa in shiga motar ba kyaleki zai yi ba…. Hadawa zai yi ya fatattake mu” Khaleesat bata sake ce mata komai ba suka nufi inda Ajay yayi parking, suna karasawa wajen Khaleesat tayi shiru ta tsaya ganin babu motarsa, can ta ɗan kalli Safiyyah ta gefen ido, Safiyyah dake ta waige waige tana neman motar Ajay tace “Ina motar tasa?” Khaleesat tace “Kawai mu tafi mu hau Uber” Da Safiyyah ta fara baɓɓaka dariya har da durkusawa kasa, tun Khaleesat na daurewa har ta kasa ita ma ta fara dariyan, da kyar Safiyyah ta dago tsabar dariya har da hawaye tace “Har kina min iyayin in shiga ayi dropping dina ke me sabon Housemate, yanxun nan kika gama kakkaresa sai gashi ya shuka maki rashin mutunci, an gaya maki Ajay zai canza halinsa ne” Khaleesat ta taɓe baki ta bude handbag dinta ta ciro waya zata yi ordering ride, har suka rabu da Safiyyah dariya take mata kamar zata shide, ita dai ko tanka ta bata sake yi ba…. Jay na zaune motarsa yana waya da Mami yaga Khaleesat ta sauka daga Uber din da ya ajiyeta, ya bi ta da kallo har ta shiga apartment dinta bata lura da shi ba, Muryar Mami yaji tana ta masa magana, ya ɗan sauke boyayyen ajiyar zuciya a hankali yace “Idan na dawo za mu yi magana Mami it’s nothing to be worried about, in less than 3 weeks zan dawo Nigeria in sha Allah” Daga daya bangaren Mami tace “Jawwad kana tunanin da akwai wani abinda zaka tambayeni da zan ki maka ne? Plss tell me what you want, hankalina bazai kwanta har nan da sati uku ba, ko kuma in taho Maryland din ne?” Jay yace “A’a Mami ba sai kin zo, ba wani abu bane da zaki damu kanki, idan na dawo za mu yi magana” Mami dai tayi shiru, alamar bata gamsu ba. Khaleesat na shiga apartment dinta ta ji alamar Ajay yana kitchen, ta karasa kitchen din ta tsaya a bakin kofa tana kallonsa fuska daure tace “Ba sai kace min kar in dawo bazan same ka a wajen ba…” Ba tare da ya kalleta ba yana slicing fruits yace “Saboda ina tsoron ki” Tace “Amma ai da bazan koma wajen ba har ruwa ya doke ni….” Sai a sannan ya juya ya kalleta, lokaci daya taga ya ajiye wukan hannunsa da sauri yana kallon finger dinsa, dariya tayi tace “Dama wa yace maka haka ake slicing abu da wuka?” Ko kallonta bai yi ba har sannan yana kallon finger dinsa, Ita ma dai kallon hannun take don bata ga jini ba, can ta karasa kitchen din tace “Ai ba haka ake yanke hannu ba, idan da gaske ne jini za a fara gani yana zuba” Tana fadin haka ta bude tap ta wanke hannunta da liquid wash ta dau karamin towel ta goge hannun sannan ta karasa kusa da fruit din da yake slicing ta dau wukan tace “Let me just show you how to handle a knife in case of next time” Slicing fruit din ta fara, ya wani kalleta daga sama har kasa, can ta daga kai ta kallesa tace “Hope you are watching how i am using the knife?” Juyawa taga yayi ya nufi fridge ita dai ta ci gaba da yanka fruit din tana kallonsa, wasu fruits din ya debo alamar ya bar mata wa encan din, bata san lkcn da ta jefar da wukar hannunta a gigice ba jin wani sharp pain sai ga jini ya biyo baya, ya juya ya kalleta at first ta so ta daure, kawai taji ya fara dariya irin ta mugunta da yake ma Jay, sai a sannan ta fashe da kuka sosai, ta juya zata fita daga kitchen din ya tura kofa yace “Waye zaki zubar ma jini a parlor, jira ya gama tsiyayewa a nan kar ki bata ma mutane gida” Kuka kawai take zata fita ya tsaya bakin kofar yaki barin ta fita, sai kuma ya hade rai yace “Baza ki je ki wanke hannun ba” Ta koma jikin bango tana kuka a hankali tana kallon finger dinta da ta gaftare, Yace “Sorry… but that serves you right” Tap din kitchen din ya bude mata, bata ko kallesa ba ta tafi ta fara wanke hannun tana duba how deep the cut is, shima kallon finger din yake don wajen har yayi ja, ya tafi ya bude fridge ya dauko Venegar ya bude ya zuba mata a hannun, wani ihu ta kwala ya bude kofar kitchen din yace “Fita” Fita tayi daga kitchen din tayi ido hudu da Housemate dinta dake zaune parlon yana danna wayarsa, goge idonta tayi a hankali ta nufesa, ta zauna kasan carpet tana kallonsa cikin sanyin murya tace “Good evening” Sai a sannan ya kalleta yace “Evening Halysaah, how are you?” Tace “Alhamdulillah” Yace “Ya preparation din exams?” Tace “Lafiya lau, yaushe ka zo?” Yace “Just now…” Finger dinta ta nuna masa a hankali tace “I just hurt my self” Yace “Sorry, Allah ya sauwake” Tayi shiru bata sake cewa komai ba, ya ci gaba da danna wayarsa, after some minutes Ajay ya fito daga kitchen din da bowl din fruit Salad da ya zuba ma orange drink da zuma, sau daya ya kalli Jay ya tafi ya zauna ya fara shan fruit salad dinsa ya kunna TV ya kamo tashar kwallo, ta gefen ido Khaleesat ta ɗan kalli Ajay, sai kuma ta kalli Jay that is just pressing his phone, abinda Safiyyah ta ce mata daxu ne ya dawo kanta, lokaci daya jikinta yayi sanyi, after almost 5 mins ta kalli Jay a hankali tace “Should i make the fruit salad for you too?” Jay ya kalleta yace “No i am full Halysaah” Ta sunkuyar da kanta, after a while tace “Ina son zan tafi sama in canza kaya, amma pls kar kace zaka tafi since it’s raining, idan na gama zan sauko” Jay ya ɗan yi murmushi yace “Take your time Halysaah” Mikewa tayi ta wuce sama, shi dai Ajay kallon TV kawai yake yana shan fruit salad, sai da Khaleesat ta wuce sama sannan ya kalli Jay yace “Yau bazan kwana a gidan nan ba because i have somewhere important to go, so ur staying in this apartment for today means nothing….” Jay yace “Ka fasa tafiya Nigeria din ne, i tot u said few weeks after i return zaka je” Ajay yace “Me ake yi a Nigeria din? Duk sanda nayi niyyar tafiya ai ba sai ka tuna min ba…” Ko da Khaleesat ta sauko downstairs kusan karfe shidda taga Housemate dinta baya parlon, kallon Ajay tayi tace “Housemate dina fa?” Game dinsa kawai yake without looking at her balle ta saka ran amsa, shiru tayi tana kallonsa kafin ta nufi kitchen, fruits din da take yankawa daxu kafin ta yanke hannu ta duba bata gani ba a kitchen din, ta duba waste bin bata ga alamar fruit din ba, ta sake dawowa parlor tana kallonsa tace “To ina fruit din da nake slicing daxu?” Without looking at her yace “Na zubar” Tace “Amma ban gani a waste bin ba” Yace “Ke kika zuba a waste bin din da zaki gani?” Tace “Ko dai ka shanye ba” Bata jira cewarsa ba ta juya ta koma kitchen din, after some minutes ta fito da bowl din fruit bayan tayi yanda taga yayi da fruit Salad din sa daxu, ya bi ta da wani kallo har ta wuce sama, wayarta ta dauka ta kira Jay, har ya katse bai daga ba, bayan few minutes sai gashi ya biyo kiran, kamar zata yi kuka tace “Shi ne ka tafi bayan nace kar ka tafi” A hankali yace “To in na zauna me zaki bani?” Ta ɗan yi murmushi tace “Abu me dadi mana” Yace “Uhm… Abu me dadi kamar me? Kin san abubuwa masu dadi kala kala ne” Tace “To ai dawowa zaka yi sai in baka” Yace “Salon in zo ki fara sunkuye kai ki ki kallona balle ki ban abu me dadin” Dariya tayi tace “A’a bazan yi haka ba wallahi” Yace “Sure?” Tace “Yeah” Yace “Ohk, bari ayi magrib….” Ta marairaice tace “Nasan ba zuwa zaka yi ba, haka ka min ranan nan” Yana murmushi yace “Zan zo, amma a mota zaki sameni bazan shiga gidan ba” Tace “Toh sai ka zo” Yana katse wayar ta dau fruit salad dinta ta fara sha, sosai yayi mata dadi saboda orange juice din ciki… Wajen karfe takwas kiran Housemate dinta ya shigo wayarta, ta mike daga kan darduma da take zaune ta dau wayar tayi picking ta kai kunne, calmly yace “Ina jiran ki” Ta ɗan yi murmushi tace “To” Katse wayar tayi ta nufi kofa ta fita daga dakin ta sauka downstairs, Ajay dake waya ya bi ta da kallo ta shiga kitchen, gun da Ajay yake ajiye tsadaddun Chocolates dinsa ta bude tayi tsalle ta dauko daya, kiris ya rage ta fadi kasa, ta dai kulle wajen da sauri sannan tayi unwrapping chocolate din ta boye a Veil din jikinta, sannan ta fito daga kitchen din ta nufi kofar parlor zata bude kofa yace “Ke” Juyawa tayi ta kallesa sai kuma ta langwabar da kai tace “Housemate dina ne ke jirana a waje” Yace “Shi yasa kika yi wanka da turare kenan” Ita dai bata ce komai ba ta fita daga parlon ta nufi inda ta hango motar Jay tana tafiya a hankali, kallonta yake har ta iso gun motar ta bude front seat a hankali ta shiga ta zauna, ta ɗan kallesa tana murmushi taga kallonta yake babu ko kiftawa, sauke idonta tayi a hankali tace “Good evening” Yayi kasa da murya yace “Ina abu me dadin?” Murmushi kawai take, after some seconds tace “Close ur eyes” Lumshe idonsa yayi, ta dake ta kamo hannunsa ta saka masa chocolate din sannan ta sake hannun da sauri ta kauda kanta, bude ido yayi yana kallon Chocolate din, sai kuma yace “A’a ni ba Chocolate nake so ba…” Ta ɗan kallesa kamar zata yi kuka tace “Me tsada ne fa” Yace “I appreciate it amma ba shi nake so ba, ni abu me dadin da nake so daban” A hankali tace “To meye shi? Sai in siya maka” a hankali yace “Halysaah nake so” Dariya tayi tana kallonsa tace “To ai ni ba abu me dadi bace” Yayi kasa da murya yace “Wa yace maki?” Tace “Eh mana ga dai su Chocolates da Lollipops” Yana kallonta kasa kasa yace “Duk kin fi su, baza ma a hada ba….” Shiru Khaleesat tayi as if everything is beginning to dawn on her, bata sake yarda ta kallesa ba, shi kuwa kallonta kawai yake, kamar me rada yace “You are not saying anything again” Ta ɗan yi murmushi tana tunanin ta yanda zata yi diverting zancen, da sauri tace “Daxu Safiyyah ke tambayata kai, wai bata ganka ba kwana biyu” Yayi murmushi yace “Why are you diverting the conversation?” Dariya ya bata amma tayi murmushi kawai tace “To ai don kar ku hadu da ita kace ban gaya maka bane” A hankali yace “Kin san yanda nake jin ki a rai day by day kuwa Halysaah? Ina jin kamar idan na rasa ki abu zai iya samu na” Khaleesat ta daga idanuwanta ta kallesa amma ta kasa cewa komai, kamar yanda shi ma yayi shiru yana kallonta yana jin wani sabon sonta na mamayan zuciyarsa, Jinginar da kansa yayi jikin kujeran motar ya lumshe ido.
Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence 07087865788
