Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 28 Hausa Novel

Tun ƙarfe goma sha ɗaya na safe Rayyan ya bar office don ya je da wuri yau din saboda wani aiki da ya taso, gida straight ya koma yayi wankan juma’a don yana so ya fita da wuri yana so ya fara biyawa wurin salim da ya rasa gane kanshi a kwanakin.A shirye ya fito cikin shigan manyan kaya don fa shi yana son manyan kaya haka kawai bai cika son sa kananun kaya ba kaman yadda yake saka manya ɗin, governors yard ne da aka yi wa dinkin zamani ya zauna mishi sossai da sossai, ko da ya fito ɗakin Mammi ya fara yi ya sameta zaune tana azkar ɗinta da bata rabo da shi.”Sannu da hutawa Mammi”Ya faɗa yana zama gefenta “Sannu Saraki ashe ka dawo har ka yi wanka”Ya gyaɗa kai”Ina so zan fita da wuri ne zan biya wurin Salim””kwana biyu kam bai shigo ba, ko da shike lafiya shi ke ɓuya ko?”Murmushi kawai ya ɗan yi zai yi magana sai ga Afeefah ta shigo hannunta riƙe da tray mai dauke da plate na abinci.Bata san yana nan ba da bata shigo ba don fa ita duk abin da zai haɗa ta dashi kiyayewa take saboda yadda bata samun natsuwa a area ɗin da yake gashi abin laifi baya mishi kaɗan yanzu ya hau faɗa da masifa, a gaban Mammi ta ajiye tray ɗin ya bi trayn da kallo kan ya kalli Mammi dake godiya ya ce “Ba dai wannan abin za ki ci ba?”Daga ita har Afeefah kallonshi suka yi abinci ne ya zama abu? “Me yayi?”Bai amsa Mammi ba sai Afeefah da ya kalla da idanunshin nan yace “Kashe ta kike son yi?”Wani irin faɗuwa gabanta yayi jin zancen kisa, hankalinta sai ya so tashi idanunta duk ta zaro waje tana so tayi magana amma Muryar rawa yake, tana da trauma na batun kisa da ita kanta bata sani ba, amma yadda ake jefanta da kalmar kisa yayi affecting mind ɗinta ta yadda ko ya aka ambaci kisa aka danganta ta da shi sai hankalinta ya tashi.Tsawa ya daka mata cikin muryarshi da ke razana ta “Na ce kashe ta kike son yi? Me yake damun ki da za ki dafa kowani shirme ki kawo mata?”Ganin yadda ta sake firgita Mammi ta dafa shi.”Saraki…! Wai me haka ne? Meyasa kake haka? Idan ka bi ta a hankali ai za ta fahimta ba sai ka yi mata faɗa ba, kuma ni na saka ta dafa min ba gaban kanta tayi ba””Mammi ina Merry?”Yayi tambayar ranshi a hasale, idan da bayanan sai Mammi ta ci abincin nan don ya tabbatar ko don wahalar da wannan yarinyar tayi ta dafa zata iya ko loma kadan ne don yarinyar ta ji daaɗi, Dukda Couscous ne amma akwai abubuwa masu yawa da bai kamata ta saka mata ba ciki.”Merry bata ji daaɗi ba jiki da jini, Abeeha na school shiyasa nace ta dafa ɗin amma na tabbatar bata gane bayanin da na mata bane ba da gangan tayi hakan ba”Tsaki ya ja ya ɗauki tray ɗin ya fice.A ƙasa ta zube tana sauƙe numfashin tsoro yadda yake zaro mata ido kawai take gani, Mammi ta dafa ta “Ki yi haƙuri Afeefah duk ya firgitaki””Mammi ban san akwai abubuwan da bai kamata ki ci ba ciki kiyi haƙuri laifina ne””ba wani laifin da kika yi na kirki Alaiyahu da kuma tomatoes da kika saka ciki duk are high potassium veggies da bai kamata in ci ba su ne fa kawai sai zubin da yayi yawa kasancewar Couscous ɗin daga wheat ake samun shi, amma ai ina da ido kuma zan iya miki gyara shi dai kawai zafin kanshi ne dayawa”Dukda halin da take ciki sai da ta ɗan murmusa kaɗan, yau public holiday shiyasa bata je school ba itama Abeeha wani research take yi shiyasa ta tafi Merry wacce ke da karatu na musamman akan nutrition ɗin irin masu ciwon Mammin bata da lafiya shiyasa ta shiga kitchen ɗin ta girka ba wai don gwaninta ko nuna iyawa ba, jikinta ya yi sanyi bata ma zauna wurin Mammin ba ta fice kar ya dawo ya sameta.Shi kam kitchen ɗin ya koma, a hankali masu aikin suka zame suka fice sanin kila da kanshi zai yi girkin kaman kuwa sun sani, a take ya fara shirya abincin Mammin, idan ka ga yadda yake aiki za ka zaci wani professional Cook ne cikin taka tsantsan da tsantsar tsafta da Allah yayi mishi, wanke hannu kuwa ko me ya taɓa sai ya je ya wanke hannu da handwash ya dawo, ko sau ɗaya kayanshi bai taɓa komai ba har ya gama ɗan small portion na chicken salad wanda da breast ɗin kawai yayi amfani duk wani ƙashi babu ciki, babu gishiri ya gasa da herbs kawai da lemon, ya haɗa salad din wanda lettuce ne sai cucumber da Bell peppers da albasa kaɗan, ba mayonaise ko cream ya saka ciki ba sai ya zuba man zaitun pure one a cikin dan karamin bowl ya saka 1 tsp na vineger ya kaɗa da ‘yar habbatussauda kaɗan ya juye a cikin salad din ya gauraya ya zuba a cikin wani bowl mai kyau. Shinkafa ce ‘yar kaɗan ya dafa mata half cup ya haɗa da ruwa don bata shan wani sugar ko juice ya ɗauka ya nufi ɗakinta.Murmushi ta saki tana mishi godiya, ita bata yi mamaki ba don kafin yayi hiring merry da kanshi yake yi mata duk abinda zata ci shi ya uzzurawa su Abeeha har suma suka iya duk cimar ta da yanayin awon duk sun haddace, godiya ta mishi yace “Mammi babu fa wannan tsakanin mu har Abada, abin da ya zama min dole ne nayi”Daga nan ya mata sallama ya koma ɗaki ya sake gyara jikinshi kan ya kara turare ya fice daga gidan.Kai tsaye gidan su Salim yayi, kasancewar yanzu ba kaman da ba ta babban parlor ya shiga da sallama, Mommy da ke zaune ta zabga tagumi ta ɗago ta amsa a hankali, ya zamu wuri ya zauna yana gaisheta “Lafiya ƙalau Rayyan ka shigo?”Samha dake kuka ya ɗan kalla kan ya kalli mommyn “Lafiya kam mommy?””Ba ƙalau ba Rayyan, ban san me zan ce ba ban kuma san ta ina zan fara ba amma tabbas Salim baya cikin lafiya da natsuwar shi… Rayyan ko za ka bashi shawara? Ko zaka mishi faɗa? Don saleem bai ɗauke ni uwa ba kuma, saleem ya fi gane maganar matarshi akan nawa yanzu ya bar nan bayan ya fasa bakin Samha don kawai ta roƙe shi kuɗin makaranta suna shirin exams bata biya ba matarshi ta sa baki sai tace mata ba da ita take ba da ɗan uwanta take shikenan har ya kai abin duka kuma yace ba zai biya ɗin ba rashin kunyarta ya biya mata? Saleem dai ina mishi magana ya ɗaukeni banza? Innalillahi wainna ilaihi rajiun…”Wasu irin hawaye masu zafi take zubarwa bata taɓa zato ko tsammanin irin wannan butulcin daga Sabrina ba, shi karan kanshi Rayyan yayi mamaki don kowa ya san saleem ya san yadda ya ɗauki mahaifiyarshi da ƙannenshi, shi ɗin mai biyayya ne ko da ko baya so zai yi don ya faranta ran mahaifiyarshi, ya san dai saleem ya chanza mishi amma bai zaci har mahaifiyarshi da yan uwanshi ba, sai ya kira shi ba zai ɗaga ba kuma ba zai kira shi back ba, sau biyu yana zuwa headquarter baya samun shi shiyasa ma ya yanke ya zo gida ya same shi, Dukda shi namiji ne kuma ba kaman sauran maza ba amma daga maganan mommy ya fahimci akwai ayar tambaya mai girma akan saleem.Bai gama tunanin ba aka fara sallama, sameerah dake zaune shiru gefe ta miƙe ta nufi kofar.”Mun zo daga companyn gadaje da kujeru ne mun kawo order ɗin da aka sanya wannan address ɗin…””Anya gidan nan ne? Ko zaka kira Layin da aka yi order ɗin?””Toh bari na ƙira”Kira yayi cikin mintuna biyu sai ga saleem da Sabrina sun sauƙo, ganin Rayyan ya sa ya je ya bashi hannu suka gaisa “Saleem kana lafiya?”Yayi tambayar yana sake nazartar abokin nashi da ya ji wani irin tausayinshi ya tsarga mishi.”Lafiya me ka gani?”Girgiza kai kawai yayi ya ce “Zauna za mu yi magana”Babu musu saleem ya zauna Sabrina za tayi magana ya ɗaga idanu ya zuba mata haka kawai kwarjinin shi ya wani irin cika ta, duk yadda ta so tayi magana kasawa tayi sai ta nufi kofa ta fice tana kwafa.”Me ya sameka? Me ke damunka abin da baka yi ba tun kana ƙarami zaka yi shi yanzu da ka mallaki hankalin kanka? Saleem uwa ba Abar wasa bace ba kowace uwa ba, ba irin mahaifiyarka da tayi dedicating lafiyarta, karfinta da kuruciyarta don ganin ta gina rayuwarka ba… Ta gina ka ne don ka girma ka tallafi kannenka, yau idan baka biyawa su Samha kudin makaranta ba wa kake tunani zai biya musu? Me ya hau kanka haka saleem?”A tausashe yake maganan, saleem bai ce komai ba ya zauna shiru duk yadda Rayyan ya buga ya kaɗa akan ya faɗa mishi menene matsalar bai ce komai ba, daga karshe Rayyan ya ce “Saleem ka ba Samha kudin makaranta yadda ka saba bata”Ɗago ido yayi ya kalleshi shima shi yake kallo zuciyarshi na rawa, tabbas akwai ayar tambaya akan dabiun saleem sai dai ba zai yi saurin yanke hukunci ba, yana zaune nan sai da saleem ya dauki tsawon mintuna biyar kan ya zaro wayanshi yayiwa Samha transfer ɗin kudin yadda ya saba bata, mommy ta duƙar da kai tana kuka mai ciwo. Da zafi abin da zafi kana gani a sauyawa danka rayuwa daga yadda yake zuwa wani abu daban.”Je ka shirya mu tafi masallaci”Bai ce komai ba ya miƙe ya haura sama, Rayyan ya runtse ido a hankali sama da seconds goma ya buɗe sun dan sauya, Miƙewa yayi ya fice bai kula godiyar da mommyn ke mishi ba, a gaban motar shi ya tsaya yana kallon Sabrina da ke tsaye ana sauƙe wasu kwalaye cikin store nazarin ta sossai yake yi chan ya ɗauke idanu ya sauƙe kan saleem da ya fito, yana kallo sai da yaje wurinta suka yi magana ta ɗaga ta kalleshi kan ta gyaɗa kai saleem ya wuce ya zo ya shiga motar suka fice daga gidan.”Saleem idan ka ga Afeefah a yanzu za ka iya aurenta?”Shi karan kanshi bai san ya jefawa saleem ɗin tambayar ba don ya jima yana mishi yawo a rai kuma yana son tabbatar da zarginshi kan Sabrina. Sunan Afeefah ya sake maimaitawa a ranshi don dai bai taɓa ambatar sunan a fili ba ma sai yau.”Aure? Ai ina da aure”Ya amsa shi muryarshi babu wannan karsashin idan yana maganar da ya shafi Afeefah, kaman ma wata ce chan daban da bai wani sani ba.Bai ja maganan ba ya yi shiru, dole su tashi tsaye akan Saleem da alama zautar da shi ake shirin yi, amma yayi matukar mamaki irin mamakin nan da bai taba zaton hakan zai iya faruwa da saleem daga aure ba, auren ma na dangi ba bare ba.****Zaune take gaban Mammi don sai da ta tabbatar ya fice kan ta dawo, abincin ta tsurawa idanu yadda ya tsara shi kaman wani chef tana mamakin yadda ya iya girki haka, Mammi bata ce komai ba ta shiga cin abincin sai da ta gama tsaf ta dubi Afeefah tace”Afeefah akwai maganar da nake so mu yi da ke ko kuma in ce akwai alfarmar da nake so na roƙe ki ban san ko za ki iya yi min ba, ba abu bane da ya saɓawa shari’ar musulunci abu ne da muddin kika amince min Afeefah zan yi matuƙar farin ciki fiye da zaton ki”Afeefah ta gyara zama jin maganar serious ne, kuma a yadda Mammi ta ɗauke shi da muhimmanci ya sa itama ta ji ta bashi muhimmanci itama”Tashi ki dawo nan Afeefah”Miƙewa tayi ta koma kusa da ita yadda ta roƙa hannayenta duk biyu ta riƙe “Afeefah na dauke ki ne tamkar Abeeha, ba zan taɓa yin wani abu da zai cutar da rayuwarki ba amma ban san yadda za ki ɗauki maganar ba..””Mammi yanzu fa kika ce ni tamkar Abeeha ce a gareki nima kuma ba ni da uwar da ta wuce ki, wlh duk abin da kike so matuƙar zai faranta miki kuma bai saɓawa shari’a ba ni mai amincewa ne Mammi, faɗa kawai za ki yi in cika shi na san ba za ki taɓa cutar da ni ba.”Afeefah ta katse ta ganin kaman contemplating take na gaya mata abin da take so, ita kuma tana da yakinin koma menene Mammin za ta roƙa ba sharri bane.”Afeefah za ki iya auren Saraki??”Afeefah ji tayi kaman kunnenta bai ji mata daidai ba, bata motsa ba don bata gama fahimta ba jin Mammi ta yi shiru tana kallonta yasa tace “Mammi ina sauraranki in shaa Allahu zan yi duk abin da kike so””Afeefah abin da nake so shine kafin na mutu in ga na haɗa aurenku ke da Saraki…! Shin za ki iya auren shi? Za ki iya yi min wannan alfarmar?”Wani irin shock ne ya ratsa Afeefah daga kanta har cikin tafukan sawayenta, a matuƙar razane ta zare hannunta daga na Mammi ta miƙe tsaye zuciyarta na wani irin bugawa kaman zai ratso kirjinta ya fito”a..ure? Ni Mammi? Ni… Ni Afeefah da Wanchan mutumin…??”Don ji tayi ba zata iya ƙiran sunanshi ba ma ko Rayyan ɗin ko Saraki idan tayi hakan kaman wani zunubi ne da muddin ya ji ta sai ya sauya mata kammani, kallon kanta take yi daga sama zuwa kasa ta ɗago ta kalli Mammi kaman wacce ta zauce…

Back to top button