Hausa novels

Zakuna Biyar Page 30 By Princess Teema

Scanning na ƙwaƙwalwar babyn suka yi, Dr James na kallon Dr Mark and Dr Kamal da suka tsare na’urar dake ɗaukar girman kwakwalwar yaron. Kallon na’urar shi ma ya yi kafin ya sake kallonsu, a lokacin dik suka ɗago suka haɗa ido, wani irin kallo suka yi wa juna kafin Dr Mark ya fara kashe na’urar, sannan suka fitar da yaron. Rungumesa Dr James ya yi izuwa wajen wani bed, kwantar da shi suka yi kafin su fara kokarin ɗibar jininsa. Dik abin da suke yi su sister Maya suna kallonsu, da yake sister Maya ta fi raunin zuciya har idanunta sun fara ruwan hawaye, dik ta kiɗime, saboda wannan ba side na aikinsu bane, amma dik da haka sun fahimci gwada yaron ake yi, kowacce a cikin ranta tana tambayar kanta meyasa suke mashi wannan uban gwaje-gwajen yana ɗan jariri?.Bayan sun kammala suka fito da babyn, sister Zinta ya zo ya miƙawa baby, jikinta na ɓari ta karɓa, da karfi ta sauke ajiyar zuciya ganin yaron ya dawo lafiya lou. Ɗago ido ta yi karaf suka haɗa ido da Dr James, wani irin spark ta ji zuciyarta ya yi, ALLAH ya gani tana tsananin son wannan guy ɗin.Ɗan shagala ya yi da kallonta na ƴan mintoci, sai da darling ya fara kuka ne ya fargar da yana kallonta, da sauri ya zare kallonsa daga kanta yana ɗan wani ƴan kame-kame kaman mara gaskiya. Dr Kamal and Dr Mark sai kallonsu suke yi suna sakin one side smilling na munafurci, sun san Dr James ya gama faɗawa, yana masifar son Zinta, amma yaki bada kai, sai ya dinga basarwa.Baiwar ALLAH bata san komai ba, sonsa kawai ta sani. Ganin su Dr Mark suna kallonsa ne yasa ya wuce gaba, har ya kai kofa zai fita kuma sai kuma ya juyo, a kanta ya sauke kallonsa, while shi take kallo tana faman jijjiga babyn. “Idan mun tashi aiki ki sameni a office”. Daga haka ya sa kai ya fice ba tare da jiran amsarta ba.Sister Maya ce ta ce. “Sir please ayi hakuri a dawo mana da nurses ɗin can ko mutum 10 ne su tayamu aikin nan, akwai wahala, ba zamu iya ba”. Cike da tsoro ta faɗa, muryarta na rawa. Idanun Dr Kamal a kanta ya amsa da. “Za’ayi hakan”…….. Ta yi matuƙar mamakin jin kalamansa, bata taɓa zatan samun sauki daga garesa ba, ashe yana da saukin kai, sai ta ji wani irin sonsa ya shigeta, bata san time da murmushi ya kubce mata ba. Ni kam na ce yaro yaro ne, saboda dai akwai abin da suke so a wajenku ne, amma ban da haka ai ba zasu sauƙaƙa maku ba.”Keep smiling beb”. Dr Kamal ya faɗa tare da juyawa ya nufi kofar fita, kara faɗaɗa murmushinta ta yi, rufa mashi baya Dr Mark ya yi. Suna fita Maya ta daka tsalle tare da haye jikin Zinta, cike da farinciki ta ce. “Sister ashe 3D suna da kirki, kinga sun amsa buƙatarmu a karo na farko a rayuwarmu”……. Zinta da gabaɗaya soyayyar Dr James ya gama narka zuciyarta ce ta amsa da. “Sun wuci haka, sister son Dr James yana neman yi mun illah”. Hannu Maya ta sanya ta karɓi darling, sumbatar yaron ta fara yi tana ta murmushi kafin ta ce. “Zai zama naki ne, ki kara dagewa, dan naga wani irin kallon da yai maki yanzu tin da muke a hospital ɗin nan ban taɓa ganin ya yi wa wani irin wannan kallo ba”.…….. Tana murmushi ta ce. “Nima ban taɓa ganin ya yi irin wannan kallo ba, kina gani ya jima yana kallona, his eyes melt my heart all”. Rungumeta Maya ta yi, suka cigaba da tattaunawa suna farinciki. Da fitar su Dr James da kamar mintuna biyar sai ga nurses guda goma sun shigo, zazzaro idanu Maya ta yi kafin ta ce. “Lafiya?”.Ɗaya daga cikinsu ce ta ce. “Dr Kamal ne ya ce mu dawo nan, daga yau zamu dinga tayaku aiki”. …… Wani irin farinciki Sister Maya ta ji, ta kara rungume darling tana murmushi. Zinta ta ce to su tayasu su ƙarisa gyara babys ɗin, da sauri suka zo suka cigaba da aikin.A can gefe kuwa, Dr Kamal and Dr Mark a tare suka karisa office na Dr James, zaune suka iskosa, ya kwantar da kansa a saman kujerarsa, ga hannunsa a kan laptop, da alama aiki yake yi ya shiga duniyar tinani. Taɓa shi Dr Kamal ya yi saboda bai ji shigowarsu ba.Slowly ya sauƙo da kallonsa a kansu, nisawa ya yi kafin ya ce. “Soyayyarta yana nema yi wa zuciyata illa”……. Dr Kamal ya ce. “Ga alama nan mun gani”. ….. Dr Mark ya ce. “To what are you waiting for?”. Cigaba da pressing na laptop ɗinsa ya yi tare da cewa. “Jira ya kare, daga yau na mallakawa kaina ita, dama tin asali kaina na halittawa ita, ba zan sake jira ba”……… Zama Dr Kamal ya yi a saman chair. “I love Maya, but ba yanzu zan mallakawa kaina ita ba, zan bari sai gaba”. Dr Kamal ya faɗa. Siririn tsaki Dr Mark ya ja tare da cewa. “Ya batun aikin W-S?”. Shi bashi da lokacin mace a cewarsa…. Shiru Dr James ya ɗan yi kafin ya ce. “Aikinsu babba ne, dogon project ne, yanzu kuma wai jarirai 2000 suke da buƙata”.Ɗan zare idanu Dr Kamal yai kafin ya ce. “Apart from 500 da muka basu last two months ago? To me zasu yi da su?”……….. Siririn tsaki Dr James ya ja kafin ya ce. “Sabuwar addinin da suke son kirkiranwa duniyar nan ne suke plan a kansa, zasu reni waɗan nan babys ɗin, su koya masu abu guda, watau addinin da suke so, idan yaran suka kai 18 years sai su bayyanasu a duniya, zaku ji ana cewa wasu sabbin mutane sun bayyana da sabon addini, mutane da dama zasu bi wannan addinin saboda hujjojin da suka shirya, sun shirya ɓatar da hankali mutane, kun tina project da suka sanya muka kai masu kan tattara bayanan jama’a?”. (Kun tina su Lion sun faɗi cewa a plan na WS akwai fito da addini guda ɗaya? Kuma akwai satar bayanan mutane dan ayi amfani da kwakwalensu? To ga maganar ya fito a bakin Dr James kun ji.)Jinjina kai Dr Kamal and Dr Mark suka yi, cigaba ya yi da cewa. “To da wannan zasu yi amfani wajen dakushe tinanin mutane, zasu canza masu ra’ayi ta dole, zasu juya abubuwa da dama, nan da shekaru kaɗan ne, yanzu wuyarta kyankyasan babys ɗin ne, sun hura mun wuta, suna neman ɗaura mun pressure kan nan da next year in basu 2000 babys, ga waɗancan mutane dake son 1000 babys, sannan WS again sun ce suna buƙatar babys mata zallah guda 1000 nan da 2 years masu zuwa, abubuwan sun yi mana yawa, ga ƙarancin mahaifa, dole mu san tsarin da zam yi a shekara mu samu koda 2000 babys”.Dr Kamal ya ce. “Su waɗan can me zasu yi da babys mata? Sun manta dokarmu ne? Bamu kyankyasan mata mu sayar, maza kawai muke sayarwa, ko mu da muka kyankyashewa kanmu mata ai da akwai dalili, dan su mana aiki ne, meyasa zamu karya dokanmu a kan wannan aiki?”. …….. Siririn tsaki Dr James ya ja kafin ya ce. “Kasan sun ce mai gidansu dijjal ya kusa bayyana, shi ne suke buƙatar babys mata dan su raina mashi, hanya suke share mashi ai”.One thing about this 3D, Dr James shi ne kaɗai yasan dik wani sirri na kasuwancinsu, kuma shi kaɗai yasan su waye WS, dik abokan kasuwancinsu shi kaɗai yasansu, kuma shegen wayau ne da shi, yasan da cewa su Dr Kamal abokansa ne kawai da suka haɗu a makaranta, shiyasa yaki yarda ya haɗasu da abokan kasuwancin nasa wai dan ma kada watarana su ci amanarsa, ba komai yake buɗe masu ba, ko computer daddyn Lion shi kaɗai yasan password ɗinta, shiyasa kuka ga komai shi ne ke masu bayani.Haka suka cigaba da tattaunawa suna tsara yadda project ɗin zai tafi har ya basu abin da suke da buƙata.————————–🔥CRYSTAL PALACE.Bayan Lion ya kammala wayarsa da Mr president cikin room ɗinsa ya dawo, a kusa da guru ya zauna tare da miƙa hannu ya bugi heronsu. Da sauri zakin ya ɗago kai, wani irin mugun kallo Lion ya kurga mashi kafin ya nuna mashi hanyar sauƙa daga gadon da hannu ba tare da ya yi magana ba.Ai a kule hero ya ɗago hannu zai kai mashi yagushi a jiki da waɗan nan shegun faratunan nasa guru ya tare. Shi kuwa Lion da ya tsaya yana jiran ya kawo hannun ne ya sake watsa mashi harara, da alama yau zazzafar faɗa suke yi, kun san wani lokaci idan ta kwaɓe masu faɗa sosai suke yi, kuma dan balai Heron ya fi son Lion, kuma Lion ɗin ne mai bashi mugun wahala a gidan. Mari Lion ya kai mashi a fuska tare da ɗaure fuska sosai, ya sake nuna mashi hanyar sauƙa. Hannu guru yasa yana ɗan shafa wuyan heron alamar rarrashi kafin ya nuna mashi hanyar sauƙa. Cikin zafa ya diro ƙasa tare da girgiza jikinsa da karfi, ya wani buɗe, kai ya ilahi, a gaskiya zakin nan ƙato ne, ga uban gashin da suka bar mashi a jiki wanda ya ƙara mashi girma da kyau, dik bayan watanni shida suna bashi alluran kashe mashi hakwara, hanasa cizo da sauransu, and suna ciyar da shi nama sosai, shiyasa ya yi kato matuƙa, wannan ka ci karo da shi ai sai ka kwanta kawai ka ce ka mutu.Ko kallon in da yake Lion bai yi ba, ya gyara ya kwanta tare da jawo bargo, ya lumshe jade sleeping eyes ɗinsa, a cikin ransa ya fara karanto addu’ar barci. While shi kuma guru ya kashe masu light na ɗakin, ya kunna dim kafin ya kwanta shi ma, ya jawo wayansa ya fara pressing. Shi kuma hero ya kwanta a kasa saman carpet dake gaban bed ɗin nasu.After some minutes barci yai awon gaba da su dikka. A lokacin shi kuwa Aryan yana can yana ganawa waɗan nan mutane uku azaba, can underground room ya kaisu, ɗaki ne da su kaɗai suka san in da yake a faɗin ƙasar, a nan suke kashe na kashewa, su hora na horarwa, su ganawa wanda zasu ganawa azaba azaba. Dik wani nau’i na kayan azabtar da mai laifi akwaisa a wannan ɗaki. Ba yadda bai yi da mutanen nan kan su faɗa mashi meyasa suke bibiyar rayuwar Seraphina ba, amma sunki faɗa mashi, har kunne ɗai-ɗai ya yanke masu, amma suka kafe fir cewa wlh su basu san komai ba, kawai an kirasu ne a waya aka basu wannan aiki, basu san wanda ya basu ɗin ba. Aryan bai yarda da su ba, dan haka cikin fushi ya datse maƙogwaron ɗaya daga cikinsu, ya razana biyun da su faɗa mashi su ma ko su baƙonci lahira. Ƙoƙarin fahimtar da shi suka yi kan cewa su basu san komai ba, amma ina bai yarda ba.Kuma da gaske ne basu san komai ba, kawai contract aka basu na su kawota, su kuma suka baiwa Aunty Saffiya suka cire nasu kamisho. Harta number da aka kirasu aka basu aikin ɓoyayyar number ce. Karɓar wayoyinsu Aryan ya yi, faceluck ne security ɗinsu, dan haka ya saita fuskokinsu ya buɗe wayoyin, ciki ya shiga ya fara bincike. Da yaga number ɓoyayyar number ce, sai ya shiga message ɗinsu, nan ya ga an tura masu dala miliyan 50 kan su kawo Seraphina. Lokaci guda ya wani irin zabura ya miƙe tsaye yana kallon sms ɗin. Zazzaro eyes ɗinsa a kan screen na wayar ya yi, ya ilahi, hasbiyallahu waniimal wakil ya maimaita sama da sau 30 kafin ya ɗago da kallonsa a kansu. Lallai ba shakka da wannan account ɗin aka turawa mommynsu Lion kuɗi, kuma da wannan account ɗin aka turawa Dr Hushaima kuɗi, dama ya ɓoyewa Lion cewa da wannan account da aka turawa Dr kuɗi da shi aka turawa mom ɗinsu kuɗi, akwai abubuwan da Aryan ya ɓoyewa Lion sosai dangane da case ɗin daddynsu, saboda kada zuciyar Lion ta buga, yana tsananin sonsa sosai, so ya gwammaci ya rufe abin shi kaɗai kada ya rasa ɗan uwan nasa.Tabbas Aryan yasan cewa an yi wa daddyn Lion tiyata an ɗebi sperm ɗinsa, domin kuwa shi ne mutum na karshe da ya yi magana da daddyn, a lokacin da ya kira table phone nasu dake parlo a gida, lokacin suna yara da basu wuci 10 to 12 years ba, Lion yana sama yana karatu, shi kuma da wani babban amininsu mai suna MAHVIR wanda suke ce mashi VIR ko Barde, suna zauna a parlo suna buga game na ludo. Da table phone ɗin yai ƙara Aryan ne ya je yai picking, a lokacin ba zai iya tantance a wani hali daddy yake a ciki ba, amma tabbas yana tsaka mai wuya, a wannan lokacin ne daddy ya faɗawa Aryan abubuwa dayawa, ciki har da tiyatar da suka yi mashi, ya ce yasan kashe shi zasu yi, ba zai rayu ba, Aryan ya faɗawa Zayra’an ya ɗauki Nirash su dikka su gudu, mom ɗinsu ta ci amanarsu, a wannan rana ne suka san cewa mom ce ta jefasa cikin wannan hali.A wannan rana daddy ya faɗawa Aryan abubuwa da dama, sai dai a lokacin saboda ƙarancin shekaru Aryan bai damu da son sanin su waye suka yi mashi hakan ba, kuka kawai yake yi yana tambayarsa ina yake yanzu. Da gudu Vir ya yi kansa yana tambayarsa lafiya? Aryan bai iya amsa mashi ba, hakan yasa Vir ya yi sama da gudu ya kira su Lion da guru dake ɗaki. Kafin su sauƙo wayar ta katse, daddy ya katse kiran, da alama kwace wayar daga hannunsa aka yi, lokacin da suka sauƙo ne Lion ya rungume Aryan yana tambayarsa menene yake faruwa. Da kyar Aryan ya faɗa mashi yadda suka yi da daddy, mom ya sayar da daddy gabaɗayan shi, dan haka ya umarci da su gudu yanzu, dan mom tana hanyar dawowa. So a wannan rana ba komai ya faɗawa Lion ba, dan abin zata mashi yawa, ace mahaifiyarka ce zata aikata wannan zalunci, dan haka sai ya rufe wasu maganganun ya barwa kansa sanin wasu abubuwan.Cikin abin da ya rufe har da wannan account ɗin, da Lion yasan cewa da wannan account da aka turawa mom ɗinsu kuɗi da shi aka turawa Dr Hushaima hakika da Lion zai kashe Dr da Seraphina da kansa, saboda tsananin takaici, amma yanzu Lion yana ganin kamar wasu ne suka baiwa Dr contract na daban dik ba tafiya ɗaya bane.Sosai Aryan ya gigita gani dik account ɗaya ne. Cikin tsananin fushi ya ɗauki wuƙa ya datse maƙogwaron dikkan maza biyun, jikinsa na wani irin tsuma, kirjinsa na tafarfasa, a fili ya ce. “Koma wanenen lokacin waiwayarka ya isowa IRON FIST, tabbas ni kaɗai na isheku koma su wanenen ku!!”.A wajen ya bar gawarwakinsu, ya fito ya shiga motarsa, dan yasan suna da masu tsabtace masu wajen. Kai tsaye ya nufi komawa gida, sai hasbiyallahu waniimal wakil yake nanatawa a cikin ransa, dan kirjinsa na dab da tarwatsewa zuciyarsa ta fito waje tsabar tashin hankali.Yana a kan hanyar komawa ne aka kira wayar wancan mutumin, dama ya tawo da wayoyin. Picking ya yi tare da karawa a kunne. Daga ɗayan ɓangaren aka ce. “Ɗauko yarinya ɗaya kawai ya gagareku, to idan ba zaku iya ɗaukota ba ku sare mana kanta, kwakwalwarta da kuma eggs ɗinta ƙawai muke da buƙata ba wani abin ba…….”. Wata mahaukaciyar birkin da Aryan ya taka sai da shi da kansa ya yi gaba ya buga kansa da jikin glass, wayar hannun nasa ta faɗi.Ba komai yasa ya yi wannan firgicewa ba face irin murya Harleen sak da ya ji, tabbas ba wai kunnensa bane, irin murya Harleen ne, wlh babu banbanci, kai zai iya rantsuwa wannan shi ne ma.Amma dan ya tabbatar sai ya lalluɓo wayansa cikin kiɗima, hannunsa har wani kerma yake yi, jikinsa na wani irin tsuma, number Harleen ya kira, at this time sai ya ji wayar busy alamar ana call da ita, hakan ba ƙaramin ƙara gigita shi ya yi ba, lokaci guda ya ji tamkar an yi formatting na brain ɗinsa, ya ji kamar ba shi ba. Dropping phones ɗin ya yi a saman seat, kifa kansa a saman steering motar ya yi, jim for almost 30 mins ya yi, bai ma san time da aka katse kiran ba, sai da ya wastsake ya dawo cikin hayyacinsa, ya yi ƙoƙarin koran shaiɗanin da ya shiga kansa, dan shi yasan Harleen bashi da power ɗin iya aikata wannan abin, idan har da sa hannunsa, to akwai jiga-jigan dake bayansa waɗan da suka tsaya mashi, wanda sam baya fatan hakan, yana fatan ALLAH yasa kamannin muryan ce kawai.Da kyar ya iya kunna motarsa ya nufo gida. A tinaninsa zai sami su Lion suna barci, sai ya isko Lion a zaune a parlo rike da laptop yana pressing, ya ɗan yi barci ya farka. Bai yi mashi magana ba ya nufi hanyar wucewa cikin room ɗinsu, jikinsa har yanzu tana wani irin rawa na tsananin ɓacin rai, baya son motsa laɓɓansa da suka yi mashi mugun nauyi. “Aryan!”. Lion ya ambaci sunansa. Shiru ya ɗan dakata da tafiyar ba tare da ya juyo ba. Kallon tsab Lion ya mashi kafin ya ce. “What are you trying to hiding for us?”Wani irin yawu mai ɗaci ya haɗiye, da kyar ya iya juyowa, nisawa ya ɗan yi kafin ya fara kokarin motsa lips ɗinsa da suka gagara yin magana. Sake binsa da kallon mamaki Lion ya yi, sai kuma ya nufi ajiye laptop ɗin ya miƙe.Daga cikin laptop ɗin wani golden voice mai sanyi da mugun daɗi ya ce. “What’s going on there bro?”. Ɗaura laptop ɗin a saman table yai, in a low way sosai ya ce. “Some minutes VIR”. Ba tare da ya jira amsarsa ba ya miƙe ya nufo Aryan dake tsaye.Yana zuwa ya riko shoulders ɗinsa yana sake tambayarsa lafiya yake kuwa?. Faɗowa jikinsa gabaɗaya Aryan ya yi, take sautin numfashinsa ta canza, ya yi ƙoƙarin rike kansa amma kamar ba zai iya ba, zuciya shegiyar aba ce, shi da Lion akwai zafin zuciyar balai, ya gagara magana ko kaɗan. Sosai Lion ya ji matuƙar mamakin jin bugawar zuciyar Aryan ta canza, tana fita da karfi-karfi irin wanda ya razana da abu haka, abin mamaki IRON FIST da razana? Meya razana mashi ɗan uwa? Lion ya tambayi kansa. Ni kam na ce ba dole ya razana ba, ace ƙaninka uwa ɗaya uba ɗaya ka ji muryansa a irin wannan waje da yanayi, dama can ga abubuwan da ya faru, ka ɓoyewa Lion abubuwa da dama, ka barsa a zuciyarka kai kaɗai saboda son da kake yi mashi, ka shanye zafin kai kaɗai baku raba ba, kuma ace da sa hannun wani naka ai dole ka kuɗime.Tin ɗazun ƙoƙarin karyata kansa Aryan yake yi, yana ƙoƙarin tursasawa zuciyarsa ta yarda kamanni ne kawai ba wai murya bane iri guda, amma abinku da shaiɗan, ya hana mashi yarda da hakan, ya hana zuciyansa sukuni………….. Rage tsawonsa Lion ya yi, ya ɗauki Aryan cak ya saɓa a saman shoulder ɗinsa, kai tsaye room ɗinsu ya kaisa, a saman gado ya kwantar da shi, ya dawo parlo ya ɗauki laptop ɗinsa da waya.A tsakiyar ɗakin ya tsaya tare da cewa. “Vir goodnight, my heartbeat is not feeling well”…….. Ai Aryan ya wuce bugawar zuciyar Lion, dan wani irin son da yake mashi baki ba zata iya faɗa ba, shiyasa wani lokaci yake ce mashi shi ne bugawan zuciyansa, idan babu shi zuciyansa ba zata buga ba!.Vir dake zaune saman bed ne ya amsa da. “I want to see him”. A sanyayye yake magana, wani haɗaɗɗen korean guy ne, fari kal tamkar madara, kuna ganinsa ba tambaya kun san korean ne, kyakkyawan gaske ne, lips ɗinsa purple color, while gashin gerarsa tamkar zasu haɗe gasu bakinkirin yana wani sheki, kashin kansa tamkar wanda aka kifawa huka, amma ya bayan wuya yana yana da ɗan tsawo har ƙasan wuyansa, ta gaban goshi kuma a daidai saitin gerarsa gashin ya tsaya, nasa ɓangaren shi ma ya haɗu.Babban aminin su Leo ne tin na yarinta, yanzu haka wani Mission suke yi yasa yake ƙasan Russia baya tare da su, tsawon shekaru uku aikin zai ɗaukesa, yanzu saura mashi watanni biyu kawai ya dawo, a tare suke aiki, amma wannan aiki da ya tafi Lion ne ya tura shi, kuma aikin sirri ne, a gaba zaku san wani irin aiki ne, muje dai zuwa.”No goodnight”. Lion ya faɗa. Ba tare da ya jira amsar Vir ba ya katse video call ɗin, ya kashe laptop ɗin tare da ɗaurawa a saman laptop table dake gefen bed ɗinsu. Saman bed ɗin ya hau, ya riko hannun Aryan yana kallon kyakkyawan fuskansa da take cike taf da damuwa, kura mashi idanu Lion ya yi na ƴan tsakanni kafin ya ce. “To much of pressure, all for what?”. Ya faɗa yana ɗaura ɗayan hannunsa a saman gashin kan Aryan. Nisawa Aryan ya yi tare da riko hannun Lion sosai. “Bro give me sleeping pills or injection now”. Ya faɗa a lokacin da ya ji kansa na barazanar tarwatsewa. Sauƙa ƙasan bed ɗin Lion ya yi. Waje ya fita, jim kaɗan ya dawo hannunsa rike da sirinjin allura. Zuwa ya yi yai mashi, sannan ya fita zuwa mayar da alluran, kafin ya dawo Aryan ya yi barci. A maimakon ya kwanta yai barcin shi ma, sai ya zauna ya tofa wa guru da Aryan ɗin addu’ar barci, sannan ya sauƙo ƙasa.Waje ya fito ya koma ɗakin aikinsu dan ya binciki Aryan sosai, meyake damunsa? Meyasa ya gagara yin magana? Ya gagara yin barci sai da allura? Bugawar zuciyarta ta canza, meyafake faruwa?. Gara ya bincika da kansa ya gani.After some times.Aryan ne tsaye a parlon gidansu Seraphina, hannunsa rike da waya, yau ya yi balain kyau cikin hoodie farare tas, ya sanya hular kayan a kansa, daga ta ciki kuma ya sanya p-cap, ya zura hannu ɗaya a cikin aljihu, ɗayan hannun yana pressing phone, sai tashi daddaɗar kamshi yake yi.Madan ce ta fito, a mutunce suka gaisa kafin ta wuce cikin kitchen. Yana tsaye a wajen Aunty Safiyya ma ta fito, gaisuwa ita ma ta ɗaga mashi, dikkansu ba tare da ya ɗago ya kallesu ba ya amsa, amma all they’re movement yana sane da shi, kallonsu ne kawai bayayi. Wucewa ta yi ta bi bayan Madam ita ma, still yana tsaye Aisha ta fito sanye da uniform, sket baki zuwa gwiwa, da riga fari mai dogon hannu, sai socks farare kal-kal, gashin kanta a ɗaure gida biyu, ta sanya mashi ribon, tana rike da school back ɗinta. Har ƙasa ta durkusa ta gaida shi, ita ma ba tare da ya ga in da take ba ya amsa, miƙewa ta yi ta koma saman sofa ta zauna, a daidai wannan lokaci sai da Suhana ta fito, sanye take da kayan barcin da suka fitar da surar jikinta, ta ji mugun daɗin ganin Aryan a tsaye, a tinaninta zata ja ra’ayinsa da surar jikinta ne, dan ALLAH yai mata halitta mai kyau ba karya, ta yi zubin shahararrun karuwai masu yin surgery su cike nan da can ɗin nan, sai dai ita bana surgery ɗin bane, kyauta ce daga ALLAH, goodbye and welcome dik a cike masha ALLAH.Sai dai bata san IRON FIST jikin mace ba shi ne a gabansu ba, idan sun yi ra’ayi matan da suka ninkata a komai zasu samu, kai in suna so kowacce dare da irin matan da zasu kwana, amma wannan ba ita bace ɗabiarsu ba, su da maza da mata dik kallon abu guda suke masu, dik kyan mace da wani surarta wlh basu kallonta kamar mace, tamkar namiji suke kallonta saboda tin ainahi basu sanya abin a ransu ba, sun cirewa kansu feeling da sauransu.Ko Seraphina da Aryan yake kauna soyayyar tsakani da ALLAH yake yi mata ba dan surarta ba, saboda ya fara son Seraphina ne tin babu komai a kirjinta, tin tana JSS1, kawai jinin ɗan uwansa ne yasa yake sonta a farko, daga nan ta rikiɗa izuwa soyayya, amma bayan haka wlh dik kyan surarki tamkar bango haka suke ganinki.A gabansa ta tsaya, tana wani yauki da yanga ta ɗaga mashi gaisuwa. Shiru babu alamar ya ga wata halitta wai Suhana a wajen. A daidai wannan lokaci Seraphina ta fito sanye da uniform irin na jikin Aisha, da alama makaranta guda ya sanyasu.Matsawa Suhana ta yi tana ƙoƙarin ɗaura hannunta a saman nasa tana faɗin. “Meyasa baka son amsani ne? Ko kana tsoron faɗawa so……”. Bata iya karisarwa ba ta ɗauke wuta ɗiff saboda wani marin da ya ɗauke fuskanta da shi!. Take ya sulale ta baje a ƙasa bata numfashi, yarinya ta sha marin IRON FIST, ALLAH yasa idan kika farfaɗo kada ki rasa kunnuwanki ki daina ji gabaɗaya, dan ba karya kin sha irin marin wanda IRON FIST suke yi wa maza! Kin maru ba karya.Sosai Seraphina ta razana, da gudu ta juya ta koma cikin ɗaki jikinta na kerma, dan ita ta san dukan Aryan, abin ba’a cewa komai. Bayanta ya bi cikin zafin nama, dama lokaci na kurewa ita kaɗai suke jira. 7:20 ta yi. Zaune ya iskota a gefen gado tana hawaye without any reason. Cike da mamaki ya ce. “Are you okay?”. Zabura tai ta miƙe tsaye, jikinta na kerma ta ce. “Daddy please don’t slap me, i promise you that ba zan sake yin laifi ba, for give me”. A ruɗe take maganar, ga hawaye tamkar an buɗe tap.Ƙarisowa in da take ya yi, ya ciro hankey daga aljihunsa, hawayen ya goge mata tare da damƙa mata hankey ɗin a hannu, sannan ya riko hannunta suka fito parlo ba tare da ya yi magana ba. Duƙawa ya yi ya ɗauki bag ɗinta da ta jefar a ƙasa ta gudu, ya nufi waje da ita. Da sauri Aisha ta taso ta rufa mashi baya suka bar Suhana a baje a sume. Ganin ba dukanta zai yi bane yasa ta saki jiki, ta ƙanƙame hannunsa tana sauke ajiyar zuciya. Bai ce mata ko ƙala ba har suka shiga cikin mota, haka bai ce mata ko kala ba har suka nufi haɗaɗɗen school na cikin CRYSTAL PALACE ɗin. A parking lot na wajen ya tsayar da motar, da sauri Aisha ta fita ta basu waje, ɗan ɗaure fuska ya yi, on a serious note ya kara ja mata kunne a kan karatu, ba ruwanta da kowa, banda abubuwan da ya hanata, daga karshe ya ce mata. “Kinga yanzu ni mijinki ne, idan kika kuskura kika yi shirmen da kika yi a junior set ɗin nan zaki shiga wuta ne, kuma dakuwa zaki yi ne a hannuna, dan yanzu ni kaɗai nike da mallaki kuma da iko dake!”. “Daddy dama yanzu ka zama mijina?”. Tana murmushi ta faɗa. Hararar kauna ya ɗan wurga mata kafin ya ce. “Bar shiririta, ki yi karatu sosai, ni mijinki ne mana yanzu, kinga yau ce first day ɗinki a school ɗin nan, dan haka ki yi karatu sosai”……. Wani irin daɗin da ta ji ne yasa ta faɗo jikinsa. Ɗan ɗaure fuska yai tare da cewa. “Tashi mun a jiki bari in ta fi”……… “Kai daddy kai fa ka ce sai ka zama miji zan dinga kwanciya a jikinka, to yanzu ba ka zama ba?”.Nisawa ya ɗan yi. “Haka ne, to yanzu dai tashi ki wuce kada lokaci ya kure”…. Wai shi ya faɗa mata shi mijinta ne dan kada ta yi shirmen da ta yi a baya, kun ji kuma ta yadda ta fassara shi yansu kuma, kai shi dai yana cikin alkhairi dumu-dumu, Seraphina sai shirin ALLAH, rashin uwa babban musifa ce, ga rashin karatun addini, ai fin haka ma zata aikata, jama’a uwa rahama ce, rahamar da babu biyunta, a kullum ina ƙara faɗa maku, uwa number one ce!! Idan babu ita a rayuwar bawa hakika sai kunga banbancin rayuwarsa da waɗan da suke da uwar.Tana murmushi ta ɗago kai. Sumbata ya mannawa cheeks ɗinta tare da cewa. “Ki yi karatu sosai”……. Da okey ta amsa, miƙewa daga jikinsa ta yi, sumbatar ita ma ta manna mashi kafin ta buɗe kofa ta fito. Tana fita ta rufe kofar kenan sai ga motar Faryan ya kawo Rimsha.Ai cikin zafin nama Aryan ya tada motarsa ya bar wajen da gudu, dan ALLAH yasa motarsa na gidan Abba daban, motarsa na IRON FIST daban, so ba zasu ganesa ba. Ita kuwa Seraphina zata wuce Rimsha ya sauke glass ta kwala mata kira tin basu gama parking ba. Ai tana juyowa taga Rimsha bata san lokacin da ta dawo wajen motar da gudu ba. Faryan tin bai yi parking ba idanunsa a kanta, yana kashe motar ya riga Rimsha fitowa. Cikin sanyin murya da salon soyayyarta ya fara yaba kyan da uniform ɗin yai mata. Sosai ta dinga murmushi tana faɗin uncle Faryan na gode.A haka Rimsha ta fito ta samesu, hannunta ta kama tana faɗin. “Uncle zamu yi latti, ba kuna chatting ba?”…. Kai ya jinnina mata alamar e, daga haka ta ja hannun Seraphina suna ɗaga mashi hannu suka wuce. Kullum tana chatting da Faryan, Aryan kuma yanzu baya zama sosai saboda yana aiki tuƙuru na son gani ya gano wanene yake yi masu wannan abin? Ina mom ɗinsu Lion take? Abin da ya ɗauke mashi hankali kenan yanzu yasa baya bibiyar chat na Seraphina.Zuba masu idanu Faryan ya yi har suka kurewa ganinsa, nisawa ya yi tare da cewa. “Yah ALLAH ka mallaka mun wanna baiwa taka, ta tafi da zuciyata tafiyar da ba zan iya dawo da shi ba, ALLAH kada ka jarabceni da rasata ko kasako wani tseƙo a tsakani”…. Ya jima tsaye yana addu’ar kafin ya shiga mota ya tafi, kuma abin mamaki har yau bai faɗawa Seraph yana sonta ba, shi dai yana ta faman ƙoƙarin su shaƙu da juna, zasu sha hira sosai kamar masoya, amma bai taɓa faɗa mata yana sonta ba.Suna shigowa cikin school Rimsha ta ce. “Ke my star lady do you know something?”…….. Kai ta girgiza alamar a’a. “Uncle Faryan sonki fa yake yi! So sosai ɗin nan ma, please ki so shi kin ji?”..…….. Da yake ita Seraphina ta ɗauka so daban kuma aure miji ma daban, a tinaninta zaka iya soyayya da wani, wani kuma zaka iya cewa mijinka ne, dan bata ma san yadda ake ɗaura aure ko yadda auren yake ba, dan haka ta ɗauka wannan kalma ta miji kamar uba yake nufi, boyfriend kuma shi ne yaren da ta fi ganewa.San haka sai ta ce. “Ki bari ya faɗa mun da kansa”. Ta faɗa tana gyara goya jakarta a baya. “To shikenan zai faɗa maki ai nasani, da gaske yake sonki”. Jinjina kai kawai Seraphina ta yi. Kamar daga sama Seraph ta ji an ɗan taɓa bag ɗinta ta baya. Slowly ta juya dan ta ga wanene? Sai ta ga mutum ya juya yana tafiya, yana sanye da wandon jeans daga ta ƙasa, daga sama kuma jacket fara tas, kafafunsa sanye da boot, ya sanya hukar jacket ɗin a kansa, ya zura hannayensu a cikin aljihu, dik da ya juya mata baya hakika ta gano ɗan kwalisa ne koma wanene.Zuba mashi idanu ta yi har sai da Rimsha ta taɓata tana faɗin. “Ke me kike kallo haka?”…… Firgigit ta dawo cikin hayyacinta, zata yi magana Rimsha ta ciro wani ɗan teddy da aka manna a jikin jakar Seraphina ɗin tana faɗin. “Ya ALLAH, my star lady wannan teddy ɗin ya haɗu”. Da saurin Seraphina ta waro idanunta a kansa, lokacin guda ta saki wani ƙayataccen murmushi kafin tasa hannu ta karɓi teddyn, ɗan daidai da shi, an yisa yana haɗe da hannayensa waje guda, yana rike da wani heart da aka rubuta you’re so pretty a jiki, teddyn fari tas, shi kuma rubutun baki, irin kyautar nan na masoya.”A ina kika samu wannan haɗaɗɗen teddy ɗin Nisha?”. Seraphina ta tambaya….. Rimsha dake ta faman smilling ne ta amsa da. “A bayan bag ɗinki na gani an manna”.Da sauri Seraphina ta sauƙo da bag ɗin nata, sai ga wani parin takarda ya faɗo, ɗauka ta yi ta buɗe. “Please bless my morning with your cool smile blossom”. Shi ne abin da aka rubuta a jiki. Wani irin murmushi ne ya kubce mata wanda yasa wushiryarta ya bayyana.”Wait for me Nisha, I’m coming”…. Ta faɗa tare da juyawa da ɗan gudunta ta bi bayan mutum da ta ji ya taɓata ɗazun. Sai dai ga mamakinta ko alamarsa bata gani ba, waige-waige ta fara yi tana neman ta ina zata gansa.A haka Rimsha ta kariso ta sameta, riko hannunta ta yi tana faɗin. “Lafiya kike kuwa?”. …… Kai ta ɗan girgiza game da cewa. “Mu je kawai”……. A tare suka juya suka cigaba da tafiya, ta ƙanƙame teddy ɗin a kirjinta, ya yi mugun yi mata kyau. Suna barin wajen ya fito daga maɓoyansa yana sakin haɗaɗɗen murmushinsa irin na Noor ɗinmu na amana, watau familynsu Noor ba dai iya soyayya ba, yanzu zasu sace zuciya, ba’a takara dasu a fagen soyayya, dan mutum zai sha ƙasa ne. To waye ya faɗa mashi a nan school ɗin take kuma? Ga dikkan alamu ya yi bincike a kanta ne, kuma saboda ita ya nemi karantarwa a makaranta, abin da kunsan sun fi karfin hakan, amma saboda su tin ainahi sun iya bautawa soyayya shiyasa zai iya sauƙa izuwa kowani irin mataki dan ya samu soyayyarta. E KAM AKWAI BABBAN CASE! UNCLE ƊIN NOOR DA ZAFINSA YAKE TAFE. MU JE ZUWA.A ɓangaren Aryan kuwa, yana barin school ɗin gidan Abba ya nufa bayan ya ajiye motarsa a gidan Lion. A wannan lokacin kuma Abba ya dawo daga gidansu Noor ransa a matuƙar ɓace. Ya je su sake ganawa da familyn Noor, in baku manta ba ai da ya je na farko daddyn Noor baya nan ko? To shi ne yaga yakamata ya koma ya gana da shi.Sai dai yana koma ya isko kakan Noor na wajen uba, wani masifaffen dattijo, shi daddyn Noor kun san bashi da matsala, da Abba ya faɗa mashi buƙatarsa sai daddy ya ce ai wannan ba wata matsala bane, in dai su Aunty Luna suna so shi bashi da wata damuwa dan basu addini guda. Abba ya ji daɗin hakan sosai.Sai kuma me? Wannan dattijon ya ce idan sama zata haɗu da ƙasa ba zai haɗa jini da wani addini ba idan ba mutane marasa addini irinsa ba!. Daddyn Noor ya yi ƙoƙarin faɗa mashi cewa ai hakan ba wani matsala bane, amma wannan dattijo ya ce daddyn Noor yai mashi shiru, har da karawa da cewa daddyn Noor bai san ciwon kansa ba, shi komai yana da sauki a kai, to shi ba zai ɗauki wannan iskancin ba.Na faɗa maku daman cewa Abba yana da mugun zafi, da zuciya, aikuwa sai ya ce da dattijon. “Da a cikin lumana babu cin mutuncina ko cin mutuncin addinina ka ce ba zaka bani aure ba, da zan hakura, amma tin da iko da karfi zaka gwada mun, ka zagi addinina, wlh, narantse da sarkin da ya busan rai sai mun haɗa jini daku, waɗan nan yara sai mun auresu, zan gwada maka mun fika ji da kai da izza, ba’a haifi wanda zai kalli Muhammad Khaiza’an ido cikin ido ya gaggaya mun magana ba!!”.Aikuwa dattijo ya hau shi ma, ya fara surfa balai, wai ko ya mutu idan daddyn Noor ya haɗa jini da su Abba bai yafe mashi ba, Uncle da daddyn Noor sun yi ƙoƙarin tausan dattijon, amma ina, yaki hakura, daga karshe dai suka yi baram-baram da Abba, har marinsa Abba ya kusa yi Uncle ya rikesa yana bashi hakuri.Daddy Noor ya ja Abba waje, ya dinga bashi hakuri, ya ce mashi. “Kasan yanayin tsufa, amma ka bari zan shawo kansa a hankali”…… Cikin fushi Abba ya ce. “Ka shawo kansa ko kada ka shawo kansa dik ya rage naku! Aure ne a wannan gida sai mun yi, ko kuso ko ma ku ku ƙi!!”. Babban magana!….. Daddy Noor ya ga ikon ALLAH, kai Abba akwai zuciya da saurin fushi, baya ɗaukar nonsense……. To daddy Noor, a matsayinka na uba ko ka bada auren ko kada ka bada Abba namu na gargajiya sai ya ɗaura wannan aure, yau ake yinta a CRYSTAL PALACE.A fusace Abba ya baro benen yana wani irin huci, zuciyarta ta ɗauki zafi, tin da ya shigo gida bai yi wa kowa magana ba, su Harleen sun kewaye shi suna tambayar lafiya? Amma ina, bai amsa kowa ba. A daidai wannan lokaci Aryan ya shigo parlon cikin fushi shi ma.Domin kuwa yana gab da shigowa gidan ya haɗu da daddyn Noor, bayan sun gaisa daddy yake ce mashi. “Na zo kara baiwa Muhammad Khaiza’an hakuri ne a kan abin da ya faru, idan ba damuwa ka mun sallama da shi”…… Cike da mamaki Aryan ya tambayi abin dake faruwa, daddy ya zayyane mashi komai, ransa idan ya yi dubu ya ɓaci, shi ne Aryan ya ce daddy ya bar masu kofar gida tin kafin yai ball da shi. Dole ya juya da koma.Shi kuma ya shigo cikin gida da fushi. Yana zuwa ya tsaya a tsakiyar parlo, kowa sai da ya sha jinin jikinsa da suka gansa a wannan yanayi. Cikin kunar rai ya ce. “Abba na faɗa maka bana son auren ana dole ne? Ba ga shi yanzu ka je ka ja an taɓa mana ƙimarka ba! A kan wata mace zaka ja wasu banzaye su faɗa maka magana! Ko so kake mu kashesu ne? Kasan zuciyarmu ba zata iya ɗaukar wani ya gaya maka magana ba meyasa zaka kai kanka wajen ƙasƙantattun mutane?!”.A fusace Abba ya ce. “Aryan sai ka auri wannan yarinya, dan sai na gwada masu ba’a ja dani!”. Cikin dokin zuciya ya faɗa……. “No Abba! Ba zan auri kowa ba”. Cikin fushi ya faɗa……. Da karfi Abba ya ce. “Zaka aureta Aryan!!”…….. A fusace shi ma Aryan ya ce. “Ba zan aureta ba na ce maka, wai Abba rayuwata ce ko naka? Kai zaka zauna da ita idan ka aura mun ita ne? Ko zan mutu idan ban yi aure a wancan gidan ba sai dai in mutu, amma aure ba zan yi ba!!”..A fusace Abba ya miƙe tsaye, jikinsa har yana wani irin kerma, ya nuna Aryan da sandar hannunsa, cikin tsawa ya ce. “Ko kaki ko ka so sai ka aureta, sai na gwada masu ba kowa ake taɓawa b!!”. Juyowa Aryan ya yi, suna fuskantar juna, cikin fushi, zuciya game da zugan shaiɗan ya ce. “Abba ba zan aureta ba!! Dik gidan nan ma babu wanda zai yi aure! Na kafa wannan doka! Ko kaki ko ka so Abba, ba shawaranka nike nema ba, wannan umarni na ne!! Babu wanda zai shigo da mace cikin gidan nan, ka faɗa mun auren me ya tsinanawa zuri’armu in banda wahala? Ka ce ka hana soyayya saboda an cutar da kai ta dalilinta, ka aurawa su babban yaya abin da basa so, me ya haifar? Wancan banzar (Mom Rimsha) ta zo ya shiga jikin yayana, ta kashe mana shi, mahaifiyar Vash, yaya yana zaune a gidan nan, ta ce sai sun je yawon ƙasashe shaƙatawa, a nan ya je suka yi haɗarin jirgi suka mutu, ka faɗa mun me mata suke tsinana mana a rayuwarmu idan ba balain da suke jefamu a ciki ba? Dole ne sai mun rayu da mace? Ka faɗa mun dole ne? Kai da kake tare da Ammie…….”. Bai iya karisa maganar ba Faryan ya yi tsalle ya rufe mashi baki, dan ya lura yayan nasa ya fita hayyacinsa, ɓacin rai da shaiɗan sunsa ya manta da waye ma yake magana, an kure zuciyansa ne.Babban abin da yai mashi zafi yadda aka dinga gayawa Abban nasu magana dan kawai ya je neman auren da su sun ce basa so, a yau Abba ya sa Aryan ya ƙara tsanan mata, har ita Seraphina ya ji ta fita mashi a rai, ya ji ya tsaneta.Cikin fushi ya kwace kansa daga Faryan, yana huci ya nufi waje, yana wani irin taku na jarumta, jikinsa har wani girgiza yake yi saboda ɓacin rai.Yana fita ba’a fi 2 mins ba Abba ya yanke jiki ya faɗi tsabar balain zuciya, take numfashinsa ta ɗauke. Ammie kam ta rasa bakin magana, abin ya fi karfinta.Sai da ta ga Abba ya faɗi ne ta kurma ihu wanda ya jawo hankalin su Faryan a kansa. Da gudu suka yi kansa suna ambatan sunansa, sai dai ina, baya motsawa, cikin zafin jini suka ɗaukesa izuwa cikin mota, ba tare da ɓata lokaci ba suka yi CRYSTAL PALACE HOSPITAL da shi.Ammi kuwa zarya ta fara yi a parlon tana addu’ar ALLAH ya yayyafawa wannan musifa ruwa, tasan halin zuciyan Abba sarai, addu’a take mashi ALLAH yasa kada zuciyar ta buga, dan hakan tsab zai iya faruwa a irin fushinsa! Suna shiga CP-HOSPITAL suka nemo nurses suka zo da bed domin a ɗaukesa. Da yake asibitin gabaɗaya kewaye yake da Camera, suna fito da Abba suka ɗaura shi a saman bed ɗin gabaɗaya camerorin dake wajen suka fara ɗaukansa. Lokaci guda jiniyar agajin gaggawa na asibitin ta fara ƙara wanda hakan ya janyo hankalin dik wani likita a kan su duba laptop ɗinsu su ga menene.Suna duba cameras ɗin suka ga Abba a kwance a kan gado. Wani nurse ne ya ce da Harleen wanene wannan? Ya faɗa yana nuna Abba. Harleen ya amsa da. “Muhammad Khaiza’an by name, ya yanke jiki ne ya faɗi………”. Bai iya karisar da maganar ba sakamakon amsakuwar da ya ji a asibitin ya amsa da kiran sunan Muhammad Khaiza’an.Ya ALLAH ai tin daga kan Chief medical directors, medical officers, specialist doctors, obstetricians da bama aikinsu bane sai da suka nufi wajen, su specialized doctors, senior nurse, nurse, laboratory technician, receptionist, cleaners ma baa barsu a baya ba, technicians, health assistants, kai harta manyan securitys dake wajen sai da suka yi gudun tseran cetan ran bin gadan! Tin daga kan hawa na goma consultants suke gangarowa da gudun gaske tamkar ba manyan mutane ba, ai wasunsu ma gani suke elevator bata gudu, dan haka suka biyo escalator wanda ita ma tattaka stair ɗinta bibbiyu uku-uku suke yi suna tsallake wasu, suna gudu suna cin karo da wasu ma na gudun nufar wajen, lamarin da yai mugun gigita dik wanda yake a cikin C-P-H a yau, basu taɓa gani irin wannan tashin hankali ba, sai da suka ga consultants dake hawa na goma dik sun diro ƙasa ne ma suka ƙara gigicewa, yau ba ji da kai, ba tsare ma jama’a hanya idan zasu shiga elevator, da kafafunsu yau dai suka sauƙo. Tambayar da kowa yake yi wa kansa shi ne wanene wannan dattijon da ake gudun cetan rai a kansa? Waye shi da har su Chief medical directors dik suka yo ƙasa a dalilinsa?…… Cikin ƙasa da mintuna goma harabar C-P-H ya cika tam da maikatar lafiya, ai jama’a basu tashi sanin C-P-H tana da balain tarin ma’aikata har haka ba sai yau, watau suna nan kenan?. Sosai Harleen yai mamakin ganin yadda daga kiran sunan Abbansu C-P-H ta rikice har haka, duba yadda ma’aikata suka rikice daga jin cewa Muhammad Khaizaan ya ɗauke wuta, to ko su da suke ƴaƴansa ai basu yi wannan birkicewa ba. “To waye Abbanmu?” Harleen ya jefi kansa da tambayar da babu mai amsa mashi. Intently ya maido da kallonsa a kan Faryan da gabaɗaya kansa ya kulle shi ma, tambayar kansa shi ɗin ma yake yi waye Abbanmu? TASHIN SENSE shekarunsu almost 31 a duniya amma wai suke tambayar kansu wanenen ma mahaifinsu tukun nan!.Slowly Faryan ya kallesa, kamar baya son motsa bakinsa ya ce. “Harleen, I am completely confused, don’t you think Abba is the owner of this C-P-H? Coz bana jin ko mamallakin wajen ma zasu yi wannan rikicewa a kansa”…… “Faryan, I think more than that, kasan CRYSTAL PALACE HOSPITAL mamallakin CRYSTAL PALACE ne ai, ba yadda za’ayi Abba ya mallaki C-H-P kawai, dole sai in C-P mallakinsa ne”. “If that should be the case we have to think more than that”. Cewar Faryan …….. Jinjina kai Harleen ya yi. Silent for almost 2 mins ne ya biyo baya kafin Harleen ya ce. “Faryan your words have the scent of truth! Ban taɓa ganin Abba ya biya kuɗin hayan gidanmu ba, in short Abba bashi da C-P note-B, ban taɓa gani ba, dole akwai abin da ya saɓa, Abba has hidden many things from us, and If that’s the case, we should start investigating now”.Suna nan suna zancen tuhume-tuhumensu an shigar da Muhammad Khaiza’an special ɗakin, bama su san wani ɗaki aka shiga da shi ba, saboda suna can suna tinani. Sai da suka farga babu kowa a wajen ne suka fara neman ina aka kai Abban kuma?.Ni ma na ce ina aka kaisa? Zaku sani ne, ba kuma nan kuna surutan banzanku ba, ga shi an yi gaba da shi.

Back to top button