Halysaah Page 163 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 163…Tunda Ajay ya fita gida bayan ya dan yi driving din wasu mintuna yaji bazai iya ba don ko gabansa baya gani clearly, parking yayi ya jinginar da kansa da kujeran motar yana jin kansa na juya masa ya fara sauke numfashi a hankali, after a while ya dau wayarsa da kyar yayi dialing number driver dinsu, yana dagawa ya gaya masa ya fito bakin titi ya samesa, bayan kusan minti goma sai ga driver din ya iso bakin titin, Ajay ya bude motar a hankali ya sauka daga driver seat ya koma back seat, drivern na ganin haka ya fahimci so yake ya tukasa yayi maza ya shiga driver seat din sannan ya juya da ladabi yace “Ina muka nufa ranka shi dade?” A hankali Ajay yace “Hanyar Kabuga” Drivern yace “To in sha Allah Daga haka ya ci gaba da driving din, Ajay ya kalli wayar hannunsa yayi dialing number Khaleesat, Safiyyah ta gama shiryawa kenan zata fita daga dakinta zuwa dakin Cousin sis dinta ganin har sannan Khaleesat bata fito ba, vibration din da taji a handbag din Khaleesat yasa ta juya ta koma ta dau jakar ta bude ta ciro wayar ciki, screen din ta dinga kallo ganin Ajay ne ke kiran wayar, ta dan yi murmushi ganin yanda Khaleesat tayi saving din number tasa, sai kuma ta zauna gefen gado ta fara tunanin ta daga ko kar ta daga, don ita kanta bata ji dadin kalaman da yayi ma kawarta ba, wato he is trying to portray that Jay comes before her, he can chose Jay over her, not even minding her own feelings ko kuma halin da zata shiga, they need to teach him a little lesson gaskiya ta yanda ko da wasa bazai kara irin wannan furucin ba, zuwa yanxu ya kamata yasan Khaleesat ta fi kusa da shi akan Jay, bayan wayar ya katse ta sauke ajiyar zuciya, kiransa ne ya sake shigowa wayar ta ajiye kawai ta mike ta dau nata wayar dake gaban mirror ta fita daga dakin ta tafi dakin da Khaleesat take, kwance ta sameta idonta a lumshe, Safiyyah ta karasa ta zauna kusa da ita tace “Bacci kika koma Khaleesat?” A hankali Khaleesat ta bude idonta tana kallonta, Safiyyah ta matsa kusa da ita tace “Are you okay?” Girgiza kai Khaleesat tayi cikin sanyin murya tace “I am feeling feverish” Safiyyah tace “Since when?” Khaleesat tace “Kawai da na tashi yanxu nake jin haka, ki kashe AC din dakin Safiyyah kashe ACn tace “Plss bana son ki sa ma kanki damuwan komai Khaleesat, bacin rai ne yasa kike jin haka but everything will be fine in sha Allah, is there anything u are craving for, I mean for breakfast?” Girgiza mata kai kawai Khaleesat tayi don babu abinda taji yake ranta, Safiyyah tace “A’a ya kamata ko tea ne ki sha” Bata jira cewarta ba ta ajiye wayarta ta mike ta fita daga dakin, not long after sai gata ta dawo da Cup din shayi ta zauna kusa da ita tace “Ga shayi ki sha sai ki koma ki cígaba da baccinki” Khaleesat na kallon cup din shayin tace “Ina ji kamar zan ji tashin zuciya idan na sha” Safiyyah tace “To sha kadan, ko zaki ci Irish?” Da sauri Khaleesat ta girgiza mata kai, Safiyyah tace “Ko a dama maki Custard?” Nan ma Khaleesat tayi saurin girgiza mata kai, sai kuma ta mike zaune ta amshi cup din shayin dake hannun Safiyyah, Safiyyah dai sai kallonta take tana dan murmushi, Khaleesat ta jingina da gadon dakin jin she is feeling fatigued and tired sai ta fara tunanin ko don saboda tafiyar da suka yi jiya ne from Tanzania to Abuja, then to kano, Safiyyah tace “To ki sha mana kar yayi sanyi kawata” Ba musu Khaleesat ta kai shayin baki ta fara sha a hankali don Safiyyah bata hada mata shayin da zafi ba sanin cewar bata shan shayi da zafı, kadan ta sha ta mayar ma Safiyyah sauran tana girgiza kai tace “I feel like i am going to throw up Sophie” Safiyyah tace “To ki kwanta, or will you mind taking some fruits?” Girgiza mata kai Khaleesat tayi ta koma ta kwanta, Safiyyah tace “Amma baki ji kina son cin komai ba?” Nan ma dai girgiza kai kawai Khaleesat tayi, Safiyyah ta mike ta fita da cup din shayin, tana fita wayarta ya fara ringing, Khaleesat ta juya tana kallon wayar taga sunan Jay a gaban screen din wayar, ta mike zaune da mamaki ta jawo wayar still looking at the screen tana kallon numbersa ta gane number lokaci daya, kiran na katsewa ta ajiye wayar ta koma ta kwanta, bayan kusan minti biyar sai ga Safiyyah ta shigo dakin, zaunawa tayi kusa da Khaleesat tana rike da wayar Khaleesat din da ta taho da shi daga dakinta tace “You know what Khaleesat?” Khaleesat ta mike zaune tace “A’a” Safiyyah tace “Ajay ne yake ta kiranki, ya kira yafı sau biyar yanxu haka” Khaleesat ta wani hade rai tace “Plss i don’t want to speak to him, hope baki yi picking ba?” Safiyyah tace “Ban yi ba, amma fa na dan ji tausayinsa, a whole Ajay kira har sau biyar” Khaleesat ta jefa mata wani kallo tace “Saboda ba ke ya gaggaya ma magana ba dole ya baki tausayi ai” Tana fadin haka ta kwace wayar a hannun Safiyyah ta kashe gaba daya tace “Kar ya sake kirana idan ba haka ba in fasa wayar gaba daya wallahi” Tana kai wa nan ta koma ta kwanta tana huci, sai kuma tace “Karshen bond yaje su zauna da Jay har abada mana, kuma tunda yace zai sakeni sai ya ban takardar nan don bazan zauna da shi ba, yaje can su zauna da Jay su yi rayuwarsu till eternity” hawayen da ya kawo idonta ta fara gogewa wasu na sake taruwa, Safiyyah dai ta kasa ce mata komai, can a hankali tace “Ajay didn’t mean all what he said Khaleesat, kiyi masa uxuri pls, i believe he is frustrated and confuse” Khaleesat ta fashe da kuka sosai tace “Bazan masa uxuri ba wallahi, why didn’t he consider my own feelings sai Jay kawai? Ya nuna min zai iya rabuwa da ni amma bazai iya rabuwa da Jay ba, to su je su zauna tare” Safiyyah bata sake cewa komai ba, ita kanta tasan Ajay ya kwafsa, after a while Safiyyah ta dau wayarta sai taga kiran Jay, kallon Khaleesat tayi tace “Dama an kirani baki gaya min ba” Khaleesat na goge idonta tace “Na ma manta, ur phone rang” Safiyyah tace “Housemate din ne ma, shekaranjiya naga status dinsa na gaishesa shine yake ce min yana Kano, nace ashe ya shigo garinmu, and he asked a ina muke a Kano, sai nace masa Sharada, to yace min yau zai koma Bauchi but he will be coming to see a friend here in Sharada idan ya shigo zai kirani, idan kuma bai kirani ba to bai zo Sharadan ba ya wuce Bauchi kenan, let me call him back Tana fadin haka tayi dialing numbersa ta sa handfree, bayan yayi ring sau biyu ya katse sai gashi ya biyota, Khaleesat dai kallon Safiyyah kawai take, Safiyyah tace “Good morning Yaya Housemate” Yace “Morning how are you” Tace “Lafiya lau ya Kano?” Yace “Alhamdulillah” Tace “Yanxu na ga miss call dinka ko ka shigo Sharadan ne?” Yace “Eh da na kira baki daga ba har na juya, i am together with my frnd wanda na zo wajensa” Safiyyah tace “A’a gaskiya ka juyo, ko minti biyar fa ba ayi da ka kira ba Yaya Housemate, dama can ba da sunana ka zo Sharadan ba” Ya dan yi murmushi yace “Juya mota wahala, why not leave it next time idan Allah ya sake dawowa da ni Kanon” Safiyyah ta tabe baki tace “Shi motar ce juyata ke da wahala kamar wanda ke tuka trailer?” Dariya yayi yace “I mean ban ga nearest U-turn ba balle in juya” Safiyyah tace “Ai shikenan, sai anjima Ya Housemate Allah ya tsare hanya….” Yace “Ameen, amma gaya min address din duk ranan da na shigo Kanon sai in zo mu gaisa” Tace “To in ka shigo din zan gaya maka in sha Allah” Yace “C’mon turo min ta message in ajiye…” Tayi er dariya tace “To sai Anjima” Yace “Ina jira fa” Tace “Ohk bari in tura sai kayi ta ajiya” Daga haka ta katse wayar ta tura masa address din unguwan nasu har da house number, Safiyyah ta ajiye wayar tace “Housemate bazai taba canzawa ba, bai fa yi niyyar zuwa bane shi ne zai ce juya mota wahala kamar me jan Daf din Dangwate” Khaleesat tace “Hmm, or are you hiding anything away from me Sophie?” Safiyyah ta zaro ido ta rike haba tace “Waaa? Rufa min asiri me zan boye maki? Ina ni ina sauran Hadiyah take ko Harira?” Sai kuma ta rufe baki da sauri tana dariya tace “Au ashe fa yaya Housemate ne, gaskiya ina jin kunyarsa ba zanyi yabbing dinsa ba, amma plss ki rufan asiri it’s nothing ooo” Khaleesat ta mike zaune tace “To meye a ciki, kema kin san he is one of the Sweetest and kindest guy on earth dai ko?” Safiyyah tayi dariya har da tafe hannu tace “Amma dai bai kai mijinki ba ko?” Khaleesat ta wani tura baki tana kallonta can tayi murmushi ta koma ta kwanta, lokaci daya kuma ta wani hade rai bayan ta tuna abinda Ajay yayi mata, Safiyyah tace “Ai kam nima nasan Housemate mutum ne, kuma naji dadi da kema baki mance haka ba, kawai dai bai yi sa’ar mace bane, ina masa fatan Allah ya basa mace ta gari” Khaleesat tace “Idan kece fa?” Safiyyah ta hade rai tace “Plss stop this rough play mana, naga kamar yanda nake son ki da alkhairi baki sona da shi, ina ni ina Housemate mijin er iskar nan Hadiyah” Safiyyah ta kalli wayarta dake ringing taga shi yake kira, kallon Khaleesat tayi tace “Ko har sun isa Bauchin ne…” Picking call din tayi ta saka handsfree, daga daya bangaren yace “Gani a kofar gida” Dariya tayi tace “Kai Yaya Housemate dama wasa kake min?” Yace “Minti biyar ko in juya motata” Ta katse wayar ta ajiye tana kallon Khaleesat tana dariya tace “Ji min mutumin nan ashe wasa yake, gashi nan har ya iso” Khaleesat tayi murmushi tace “Kinga ki dena masa wannan shegen dariyar kamar warce aka ma alluran laughing gas, tsakaninki da shi kawai dan murmushi amma ba ki dinga wage baki kina dariya ba” Wani dariyan Safiyyah ta dinga yi tace “Ji jaraba, meye hadina da shi da zan dinga murmushi bayan kasancewarsa old Housemate din Coursemate dita? Abeg oo don’t go there plss, married man din zan dinga yi ma murmushi sai kace gantalalliya, a’a mu samari muke ma murmushi ba mazan aure ba” Tana kai wa nan ta mike tace “Bara in je in dawo” Khaleesat ta bi ta da kallo har ta fita, wayar Safiyyah ya fara ringing Khaleesat ta mike zaune ta dau wayar taga Ajay ke kiranta, hade rai tayi ta ajiye wayar ta koma ta kwanta…. Safiyyah na fita kofar gidansu ta tarar da Jay tsaye jikin motarsa ya rungume hannu yana jiranta, har zata fara dariya ta tuna abinda Khaleesat tace mata, yace “Ashe ba ku da nisa sosai da gidan frnd din nawa” Tace “Da gaske? Ina friend din?” Ya nuna mata cikin mota, abokin ya sakko ya zagayo suka gaisa da Safiyyah da fara’a sannan ya koma cikin mota, Safiyyah tace “To ya Kano Yaya Housemate?” Yace “Alhamdulillah, ya mutanen gidan?” Tace “Lafıya lau wallahi, Mami tana lafiya?” Yace “Sure she is fine” Tace “To maa sha Allah, i so much appreciate the visit” Yace “You are welcome Safiyyah, zan koma…. Ki gaida mutanen gidan” Tace “Ohk but if babu damuwa ina son za mu yi wata er magana da kai Yaya Jawwad” Yace “Ohk, am all ears Safiyyah” Tace “To bari mu zauna a compound cause it’s confidential” Yace “Alright” Gate din gidansu ta nufa, ya kalli abokinsa yace masa yana zuwa sannan ya bi bayanta, kujeran dake compound din ta dauko biyu ta ajiye masa daya, ita ma ta zauna kan daya, bayan ya zauna yace “Ina jin ki Safiyyah Safiyyah ta gyara mayafinta cikin nutsuwa tace “Dama magana ne akan Ajay da Khaleesat” Jay ya sauke idonsa bai ce komai ba, Safiyyah dai Kallonsa kawai take, jin tayi shiru bata ci gaba ba, ya daga kai ya kalleta, sai kuma ya dan yi murmushi yace “Ina jin ki Safiyyah, what about them?” Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace “They had issues” Jay yace “Issues? Wani irin issue kuma?” Safiyyah tace “As I am speaking to you now Khaleesat tana gidan nan” Shiru Jay yayi wondering if ba su suka je can gidan jiya da daddare ba suka samesa, Can yace “I don’t know the type of issue you are talking about” Safiyyah tace “Daxu ta zo, ta kuma gaya min duk abinda ya faru” Jay ya gyara zama yace “Ohk, ai da sai kiyi abinda ya kamata kiyi masu without involving me Safiyyah, they trust you shi yasa har aka gaya maki, ke kuma sai ki gaya ma outsider sirrin su?” Safiyyah ta girgiza kai a hankali tace “Everything happen because of you” Jay na kallonta da wani expression yace “I don’t understand Safiyyah tace “Ajay ne wai yace mata zai saketa, saboda….” Katse ta Jay yayi yace “Kar yace saboda ni cause i won’t take that likely, idan yana da niyyar sakinta to kar ya danganta hakan da ni, I told him I hold no grudges against him and his marriage to saboda me zai ci gaba da fakewa da ni every now and then? He should stop involving me in his family matters pls, Ajay should stop painting me black and making me look like a demon” Safiyyah dai kallonsa kawai take, sai kuma ta girgiza kai tace “But i wasn’t expecting this from you Jawwad, na zata da na gaya maka zaka yi bringing an end to everything by speaking to them like the senior brother that you are, from the look of things Ajay meant his words, yana ganin idan ya rabu da ita shi ne za ku dawo yanda kuke a da dashi, nasan damuwar yanda ku ka yi splitting ne yasa yayi wannan furucin cause he definitely cares about you so much kai ma kuma ka sani….” Jay yace “Safiyyah…. ya fada ne not because zae iya aikatawa, ya fada ne don bakinsa yayi masa dadi, but kinsan me zai faru?” Ta girgiza masa kai tace “A’a” Yace “Zan kirasa inji yana ina, sannan idan za ayi permitting din ki a gida za mu je can tare, or you take an Uber to the House mu hadu a can gaba daya, zan kuma sake maimaita abinda na fada masa kwanaki so you keep bearing me witness.. Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace “Ai har da Khaleesat ya kamata duk mu je so that all this will end plss….” Jay yace “A’a babu ruwana da saka matar aure a motata….” Murmushi kawai Safiyyah tayi tace “Ko kuma kasan yanda ya kamata mu yi?” Yace “Ina jin ki” Tace “Why not ni inyi magana da Ajay ince ya zo nan gidan, idan ya so sai mu zauna parlon baki ayi duk maganar da za ayi, ita ma Khaleesat zan sa ta sauko zuwa parlon without telling her anything, shi ma Ajay din bazan nuna masa tana gidan nan ba, bazan kuma nuna masa kai ma kana nan ba, kawai cewa zan yi ya zo, wallahi ya Jawwad idan ba hadasu kayi ba kayi masu magana baza su taba samun rest of mind din zaman aure ba more especially Ajay, amma idan kayi masu magana as the elder brother that you are ka hada masu da nasiha nan za su tabbatar da gaske babu komai a ranka, and they will leave comfortably as married couple” Jay ya dan yi murmushi yace “Yanxun ance maki they are not leaving comfortably ne….” Safiyyah ma dai tayi murmushi tace “Ni dai plss do this Ya Jawwad” Ya daga ido ya kalleta ta marairaice tace “Don Allah, do this Yaya Housemate” After few seconds yace “Alright, you can call him Safiyyah” Tace “Kai amma naji dadi kuma Nagode for doing this to me Ya Jawwad, bari in dauko wayata….” Mikewa tayi ya bi ta da kallo yana tunanin if he can truly do this, ya lumshe ido ya girgiza kai, sai kuma ya dafe kan na kusan minti daya, can ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya ya mike ya fita daga compound din ya koma cikin motarsa, ya tada motar yana kallon abokinsa yace “Mu je za mu dawo anjima” It didn’t take Safiyyah long to convince Ajay to come over to her parent House, don ta lura ido rufe yake neman Khaleesat, yana isowa gidan ta tafi har visitor parlor da shi, ya zauna kan kujera yana kallonta da damuwa yace “Don Allah tana nan ne Safiyyah?” Safiyyah na kallonsa ganin duk a daburce yake tace “You need to calm down Yaya Junaid Jingina yayi da kujeran da yake zaune trying to calm himself down kamar yanda ta fada, tace “Ina zuwa” Daga haka ta fita daga parlon, Jay da ya dawo unguwan this time around shi kadai ba tare da abokinsa ba, shi ma tayi masa iso har zuwa visitor parlor din, sau daya ya kalli Ajay ya tafi ya zauna kan kujera, Ajay ya daga kai ya kalli Safiyyah da ta langwabar da kai tana dan murmushi, sai kuma tace “Ina zuwa….” Fita tayi daga parlon, Ajay ya dan kalli Jay suka hada ido, Jay yace “Sannu da aiki…. Safiyyah na komawa sama ta dauko ma Khaleesat gyalenta bayan tace ta zo downstairs su gaisa da babanta ya dawo, Khaleesat ta mike zaune da kyar tace “Wallahi ina jin kamar jiri Sophie, I don’t know ko zan iya sauka downstairs” Safiyyah tace “Zaki iya, kawai dai ku gaisa ne fa ki dawo ki kwanta” Khaleesat ta daure ta sauka daga kan gadon, Safiyyah ta rike hannunta suka fita daga dakin, a haka suka sauka downstairs ta tafi da ita har visitor parlor, tun Khaleesat bata karasa shiga parlon ba taji kanta na juya mata saboda kamshin turaren da parlon yake, banda Safiyyah tayi saurin rikota da tuni ta fadi kasa, Ajay bai san sanda ya mike da sauri ba ganin zata fadi, and he immediately sat down back bayan ya tuna Jay na parlon, Khaleesat ta kalli Safiyyah sannan ta kalli wa enda ta gani zaune parlon, lokaci daya ta fixge hannunta daga na Safiyyah a fusace tace “Meye haka kika min Safiyyah? Safiyyah tace “Mu je ki zauna” Cikin fushi sosai Khaleesat ta fashe da kuka tace “Bazan zauna ba wallahi, kuma idan na maki Allah ya isa sai ya bi ki, ba dai saki na yace zai yi ba, ai sai ya sakeni tunda ya fadi haka don bazan sake zama da shi ba, na gama zama da shi har abada, yaje can ya zauna da dan uwansa da yace yafi ni, ai nima ba ni nace a aura min shi ba balle yace dan uwansa yafi ni, sannan he is deceiving his self idan yana tunanin in ya sakeni zan yarda in auri dan uwan nasa kamar yanda yace, this is the least thing I will do in this life, iyayena ba gantalallu bane haka nima, kuma bana son ganinsu gaba daya….” Tana kai wa nan ta fice daga parlon tana kuka sosai.


