Uncategorized

Abban Sojoji Chapter 40 Book 2 Complete Novel

 

“`The father Of Soldiers“`

 

Story &  Written 

       By 

      Hafsat Bature

          (Boss Lady)

Kitchen ya wuce yana ganin sehrish ya soma sakin murmushi, sallama yayi masu sannan ya shiga, amsa mashi su kayi gaba ɗayansu, sannan ya matsa wurin sehrish dake agaban chopping board tana yayyanka kayan lambu,

  “Reesh idan akwai abun da kuka kammala inaso ki shiryamun a tray zan kai ma yaya Ayaan da Yaya jahan ne, yunwa suke ji ssae,” ya faɗi yana yamutsa fuska tamkar shike jin yunwar, zuba mashi ido sehrish tayi tare da cewa “junaid ! meya faru dakaine? waya mare ka har haka”?

   Cikin sauri junaid yasa tafin hannunsa ya rufe gefen fuskarsa yane cewa”ki daina ɗaga murya sehrish kada wani yaji, banaso wani yaji kiyi shiru kawai da bakin ki,” 

Jikinta ne yayi wani irin sanyi aranta tana mamakin yarda akai har wani ya aza tafin hannunsa a fuskar junaid ga sahun yatsu nan sun bayyana raɗau a fatar fuskarsa yayi jawur wurin,

Jinjina kanta kawai tayi tare da cewa “Shikenan bari na shirya maka abincin ka kai masu,” ta faɗi tana kallonsa cikin jin tausayinsa,

Ajiyar wuƙar hannunta tayi sannan ta wuce ciki donta haɗa masa, hannu yasa ya ɗauki knife ɗin da ta ajiye yaci gaba da yanka mata lettus ɗin data bari, 

Azmee ce ta taya ta zuba masu acikin warmers duk tana jin magananun da suka yi ita da junaid, aranta tana mamakin marin da taji sehrish ta ambata anyiwa junaid, har satar kallonsa tayi taga yarda fuskarsa tayi jawur gefen da aka maresa ga alama nan tabbas in wani yaji acikin gidan sai an tada husuma,

   Ruƙo tray ɗin tayi a hannunta zata wuce takai masu cikin sauri junaid ya ajiye wuƙar ya tare ta da cewa “kawo na kai masu,”miƙa mashi tayi yasa hannu ya kar6a yana kallon fuskarta da murmushi yace “thank u,” itama murmushin ta sakar mashi duk tashiga damuwa akan yanayin fuskarshi,

 Yana karba ya fuce yakai masu, yadda yabarsu haka ya same su, sunyi zugudun suna kallon junansu, Jahan na ganinsa ya saki fara’a tare da cewa “Yawwa heart beat mun gode sosai da irin kulawar daka ba mu, duk ka damu akan mu,” murmushi junaid ya saki a lokacin ya ajiye masu tray ɗin kayan abincin asaman table ɗin,

   Jikin Ayaan har kerma ya keyi wurin ɗaukar jug ya zuba lemu mai sanyi acikin cup yana kwankwaɗa, abun ya ɗaure ma junaid kai ashe dai da gaske yunwar suke ji,

   Shima jahan jiki na rawa ya shiga zubama kansa abincin, cikin sauri junaid ya wuce wurin freezer ɗinsu ya buɗe tare da ɗuko masu cool drinks ya kawo masu agabansu,

  Hannu jahan yasa ya ɗauki bottle water yana kwankwaɗa har yana kusa shaƙewa, agalabaice ya ajiye robar ruwan sannan ya kalli Junaid dake tsaye akansu yace “Allah yayi maka albarka junaid, kaje ka ci gaba da wasan ka,” 

  Juya junaid yayi ya koma kitchen wurinsu sehrish, tana ganinsa tace “Za’a a ƙara masu abincin ne”? Girgiza kai junaid yayi tare da cewa “zuwa nayi na taya ku aikin, bana jin daɗin zama ni kaɗai ne,”

 Azmee tace”so kake kaja mana ko? taya za’a ganka acikin kitchen kana tayamu aiki, kaima kasan ba zaiyiyu ba,”

  turo bakinsa yayi tare da cewa “Aunty azmee nifa ba wani abu zanyi mai yawa ba, kawai zan taya sehrish yanka kayan lambun ne,”

   “Ban amince ba junaid, wai ni yau ba ka zuwa wurin buga ball ɗinka ne? ina laptop ɗinka ne? kaje ka kunna kallo kayi mana ko ka buga game,”

   Ruƙe qugu yayi tare da cewa “Aunty azmee korata kawai kike son yi ne, to Allah ba inda zani ƙafata ƙafar sehrish, tazo mu tafi tare,” ya faɗi da shagwa6a

  Dariya su kayi gaba ɗayansu, sai lokacin sehrish tace “junaid ɗina shigo ciki ka samu wuri ka zauna, zan haɗa maka Cornflakes, kana sha kana kallon yarda muke girki,”

   Murmushi ya saki sannan ya shige ciki tare da samun wuri saman dinning chairs na kitchen din ya zauna yana jiranta,

  Jinjina kai azmee tayi tare da cewa “Shaƙuwarku fa da junaid ƙara gaba take yi, don na lura kema bakyaso yayi nisa dake,”

  Sehrish tace “Aunty azmee yana ɗebe mun kewa sosai, ina jin shi tamkar ƙanina ne shiya sanya…. .  ‘

Muryar junaid ce ta katse ta da cewa “Wanene ƙanin naki”? 

 Cikin sauri sehrish tace “bafa maganarka muke yi ba” tayi maganar yayin da tasa hannu a cup board ta zaro kofin tare da wuce wa wurin dispenser saboda ta ɗebi ruwan zafin da zata haɗa masa dashi,

“Koma meye dae zanji ne,” ya faɗi yana ɗan hararar ta daga inda yake,

Bayan ta haɗa masa takai masa nan ya zauna yana sha suna fira tare dashi,

________________________________

After magrib prayer motocinsu suka dunga shigowa cikin gidan da gudun gaske atare suka yi parking ɗinsu, Abbansu ne tare da SGR suka fito, motar dake bayansu kuma Su irfan ne tare da jabeer da khaleed, kana ganin su kasan sunji jiki, amma su da sauƙi babu alamar rauni ajikinsu sun dai jigata ne,

  buɗe motar dake bayan tasu suka yi wadda fawan ne kwance acikinta, gaba ɗaya jikinsa sahun bulali ne ta ko’ina, saboda hasken fatarshi duk zanen bugun da miyagun su kayi mashi ya fito raɗau jawur wani wurin ma harya fashe, amma da yake ya samu emmergency treatment duk ansanya mashi magani awurin, babu riga ajikinsa gajeran wando ne kawai guntu suka barshi dashi, asaman ƙirjinsa hada ɗinki akayi masa, ba ƙaramin jiki ya ji ba yaji gata sosai,

Amstrong ne babban na hannun daman SGR ya fiddo shi tare da Irfan suka tallabo shi sannan suka wuce dashi cikin gidan, har lokacin bai dawo cikin hayyacinsa ba saboda hodar da suka shaƙa mashi,

   Suma sauran mutanen da suka halarta domin yi masu jaje duk suka harhaɗu nan suna tayi ma Abbansu Allah kyauta, daga bisani suka haɗu gaba ɗayansu izuwa cikin gidan,

   Tun da Sehrish taji dirar motaci tarasa samun kwanciyar hankali burinta taga su wanene suka zo, a lokacin sun kammala aikace-aikacensu na kitchen fitowarta kenan daga wanka, ta buɗe closet dinta ta zura doguwar riga sannan ta matsa jikin window tana leƙensu bata samu damar ganinsu da kyau ba saboda mutanen dake zagaye ta ko’ina,

Jiki asanyayae ta rufe window in gabanta na faduwa tsoranta kar ace wani ne ya rasu, hannu ta aza akanta tana ambaton “innalallahi wa’inna ilaihirraji’un ya Allah kasa ba wani bane ya mutu,” 

Cikin sauri ta bar wurin tare da  buɗe kopar ɗakin nata ta fito waje a lokacin itama Azmee tafito daga ɗakinta a ruɗe jikinta na sanye da zumbuleliyar hijabi alamar salla ta kammala yi, ko addu’a bata tsaya yi ba ta fito saboda jin jiniyar shigowar motocinsu,

   tsayawa su kayi gaba ɗayansu suna son ganin abunda ke faruwa, gaba daya sun rikice ganin yarda Amstrong da irfan suka shigo da Fawan duk ciwuka ajikinsa saman 3 seater suka zaunar dashi saboda masu zuwa dubiya,

Fitowa Ayaan da jahan sukayi daga ɗakinsu suma jin hayaniyar dake cikin gidan ganin fawan a wannan yanayin yasa su ƙarasawa da gudun gaske suka zube saman guiwowinsu agaban shi cikin tsananin tashin hankali suke cewa “fawan meya faru dakai haka? Waye yayi maka haka? Innalallahi wa’inna ilaihirraji’un,

  Daker fawan ke iya kallonsu duk da baya iya tantance su wanene agabansa amma yaji muryarsu, juyawa su kayi suna kallon Irfam da jabeer don son jin ƙarin bayani,

   Jabeer yace “Fawan bazai iya yi maku magana ba a halin yanzu baima san ko ku su wanene ba, addu’a kawai zakuyi masa,’ jin haka yasa hawaye soma zuba daga idanunsu,

  Shigowar da mutane suka soma yi ne yasa su samun wuri ƙasa suka zauna kowa ya zabga tagumi, kana kallon fuskar Abbansu kasan cewa acike take da tashin hankali saboda arayuwarsa ya tsani abunda zai ta6a masa jininsa, 

Ganin SGR ya shigo yasa sehrish jin faɗuwar gaba, gaba ɗaya babu annuri a fuskarshi, white shirt ɗin dake ajikinsa duk shedar jini ne daya fallatsar masa hada hannunsa,

ba jinin kowa bane face jinin waɗanda suka farmaki su fawan, mugun bugu sukayi masu na fitar shari’a gaba ɗayansu suna a headquater dinsu an killace su can domin horar dasu da kuma yin bincike akansu,

Tuni jikin sehrish ya soma yin kerma saboda tashin hankalin da tagani ajikin SGR tunaninta ya gama bata cewa ko harbinsa akayine da bindiga shiyasa taga jini, hannu tasa ta rufe fuskarta tana kuka da gudun gaske ta juya ta koma ɗakinta saman gadonta ta faɗa tana cigaba da kukan,”

  Abun ya ɗaure ma azmee kai ganin yarda sehrish ta gudu tana kuka kuma tasan ba don komai bane fa ce sai don ganin jini a jikin rigar sgr da hannunsa,

   Ganin manyan mutane sun fara cika babban falon yasa azmee komawa cikin ɗakinta jiki asanyaye, zama tayi tana jiran mutane su ragu sai taje ta dubo shi,

   Hannu Abbansu yasa ya ruƙo na Ayaan yace “taso ina son magana dakai,”

 Tasowa ayaan yayi daga zaunen da suke yabi abbansu suka ɗanyi nisa da mutane sannan ya kallesa yace “Ina junaid yake”?

  Ayaan yace “ina ji yana a ɗakinsa bana tunanin ya fita, Amma abba tayaya hakan tafaru da Fawan? Suwaye suka yi mashi haka? ya fadi idonsa cike tab da hawaye,

  Dafa kafaɗarsa abbansu yayi shima fuskarshi tamkar zaiyi kuka yace “Ayaan bamu son ko su wanene ba, Babban yayan ku da Omar sune suka je wurin da suka farmake su, kuma sun samu nasarar kashe wasu daga cikinsu, yanzu haka akwai mutun 3 daga cikin miyagun suna a headquater ɗin mu,”

   “Abba don Allah karku kyalesu akashe su kawai,” ayaan ya faɗi cikin jin ɗaci aransa

  “Ba zamu ƙyalesu ba ayaan, mutanene masu haɗarin gaske, babban tashin hankalin ɗaya daga cikinsu da muka aza shi saman kujerar lantarki muka bashi horo ya bamu wasu bayanai nacewa macace take basu Umarni duk wani kashe-kashen da suke yi a ƙasar nan,”! 

   waro ido Ayaan yayi cikin tsananin mamakin abunda Abban nasu ya faɗa masa, aruɗe yace “What! Mace kuma Abba? mace wannan dana sani?

  “Of course Ayaan, ba kai kaɗae ba kowa daga cikin mu yayi mamakin jin hakan, yadda akasan mata da rauni amma har acikinsu asamu wata mai ƙarfin halin haɗa tawagar ƴan ta’adda masu farmakar mutane suna kakkashe su, Amma koma wacece insha Allah zamu ganota bi’iznillah zata ɗanɗani kuɗarta!”

   Jinjina kai Ayaan yayi yana cewa “Insha Allah Abba, Allah ya tonu asirinsu aduk inda suke, abun yayi yawa wlh rashin imanin nan har ina? mutun baya tuna cewa shima wata rana zai mutu yabar duniyar ne?shin menene ribarka idan ka kashe wani bayan kai baka isa ka hana kanka mutuwa ba?

   Kafin Abbansu yace wani abu muryar kanal yusif ta katse su da cewa “Abba ka matso kusa mutane suna son magana dakai,” 

 Amsa mashi yayi da “toh gani nan zuwa” sannan ya kalli ayaan yace “Abun dayasa na tambaye ke game da junaid kasan halin shi, muddin ya fito yaga halin da fawan ke ciki tofa zai iya sume wa ko ya zauce, dan Allah kusan yarda za’ae ku hana shi fitowa daga ɗakinsa indae yana ciki,” 

   Ayaan yace “Shikenan abba bari naje na duba shi,” cikin sauri ayaan ya wuce upstairs ɗakin junaid, a hankali ya tura ƙopar ɗakin cikin sanɗa ya shiga, abun mamaki samun shi yayi saman gadon shi zaune ya toshe kunnan shi da headphone yana kallo acikin laptop ɗinsa baya jin duk wata hayaniya da akeyi acikin gidan, 

   Murmushi Ayaan ya saki sannan ya ƙara ja mashi ƙopar ɗakinsa dakyau ya rufe masa ita, sannan ya juya ya sauko down wurin su,

Har wurin dare mutane suna ta zarya agidan sai wuraren ƙarfe 9:30 sannan suka fara raguwa, tuni Sgr ya wuce part ɗinsa saboda ya gyara jikinsa ga matuƙar gajiyar da yayi idonsa ma kansu daƙer yake buɗesu ga yunwa ga bacci, har lokacin zuciyar shi tafarfasa takeyi duk in ya tuna irin artabun da su kayi tare da miyagun nan, duk da sunci nasara akansu sosai, bakomai bane ya tsaya masa aran shi ba face wannan maganar nace wa macace take ɗaukar nauyin tawagar miyagun dake kashe-kashen, yaci alwashin cewa sai ya gano ko wacece ita, 

yanayin salon nata ya nuna cewa hada ɗaukar fansa take yi,’ 😳😳😳

A asibiti marshal omar ya barsu hussana a hannun Camila kafin zuwa da safe zaisa a sallame su,

shi da major suka wuce izuwa gida saboda kiran wayarsa da ake ta faman yi ga kuma tsananin damuwar daya shiga game da halin dasu Fawan ke ciki,

daker sehrish tasamu ta fito sam tagaza samun natsuwa ta ko ina, ta damu da yanayin da taga Sgr da kuma halin da fawan ke ciki, a ƙopar ɗakin azmee ta tsaya sannan ta kwankwasa tare da jiran ta buɗe mata,

   tana tsaye azmee ta bude ƙopan tana kallonta tace “kin gama kukan?

 Shiru kawai tayi tana wasa da yatsun hannunta, 

“hmmmm me kike yi ma kuka ne ɗazu”?

Cikin sanyin murya tace”babu komai Aunty azmee kawai nadamu ne da halin dana ga fawan,’

  Jinjina kai azmee tayi tare da cewa “gsky yaji jiki sosai, nima na tausaya masa bawan Allah, Yakamata muje mu duba shi, dama na jira ne mutane su ɗan rage sosai,”

Sehrish tace “ae nagama babu kowa a falon bansan inda suka kai shi ba,”

“Sun kwantar dashi ne, a ɗakin da suke kwantar da mara lafiya, bari nazo mu tafi tare, inyaso in mun dawo sai mu jera masu dinner ɗin duk da nasan abune mai wuya ma a samu wanda zai iya cin abincin, don duk suna cikin damuwa,” tana fadin haka tashige cikin ɗakin bada jimawa ba ta fito sanye da mayafi, sannan suka jera da sehrish izuwa ɗakin dake anan downstairs,

A buɗe suka same shi don haka su kayi sallama, muryar kanal yusif ce ta amsa masu tare da cewa “ku shigo ciki mana,” 

   shiga ciki sukayi sehrish har tsoran kallon jikin fawan takeyi, wanda ke kwance saman gadon idonshi arufe alamar ya samu bacci,

Ayaan da jahad ne zaune daga gefen gadon sai kanal yusif dake atsaye,

Azmee tace “Yusif ashe haka abu ya faru? Mu ba mu sani ba”!

 Kanal yusif yace “Wlh kuwa aunty azmee abun babu daɗin ji, ƴan ta’adda ne su kayi masu kwanton 6auna, amma anci nasarar Cafke wasu daga cikinsu,”

  Cikin nuna jimami aunty Azmee tace “Allah ya kiyaye gaba, ya tonu asirin waɗannan mutanen, wlh duk jikina ya mutu dana ga fawan acikin wannan halin bawan Allah, Allah dae ya tashi kafaɗunsa,”

  Suka amsa mata da ameen, sai lokacin sehrish tace “Yaya yusif ya mai jiki”?

  Yace “Alhamdulillah da sauƙi sosai harma ya samu bacci,”

   Tace “Allah ya bashi lafiya,”

  “Ameen ,” suka amsa mata 

Kanal yusif yace “Aunty azmee ku matso kusa dashi kuyi mashi addu’a yana buƙatarta sosai,” matsawa su kayi atare kusa da fawan suna yi masa addu’a tare da tattofa masa, daga bisani su kayi masu sallama suka fito waje

  Kitchen suka wuce atare don sun shirya abincin dining azmee tace “bari na haɗa maki, ki kaima babban yayansu nasan zai buƙaci wani abun,”

   “Toh,” ta amsa mata, suna cikin kitchen ɗin haroon ya shigo cikin babban falon daga waje ya shigo ciki hango sehrish da yayi yasa shi wuce wa cikin kitchen ɗin, kamar yarda ya saba fado masu batare da sallama ba haka ya shiga,

   ɗagowa su ka yi suna kallon shi hankalin shi kwance tamkar baisan meke faruwa ba, azmee tace “haroon me kake buƙata ne”? 

  tsoki ya ɗan ja tare da cewa “tun yaushe nake ta faman zarya ina jiran a jera mana abincin dare amma shiru babu, so ake akashe ni da yunwa ne”? yayi maganar fuska aɗaure yana kallon sehrish wadda tuni ta kawar da kanta,

  Azmee tace “kayi haƙuri haroon, saboda halin da su fawan ke ciki ne ga kuma mutane shiyasa ba mu samu damar fitowa ba mun jera,”

  Uban tsoki ya kuma bugawa wanda har sai da suka ɗan razana suka kallesa yace “And then so what? Mutuwa fawan ɗin yayi ne da zaku fake da cewa halin da yake ciki ya hana ku jerawa mutane abincinsu”? Ya tambaya a ƙule

 Mamakine ya kamasu jin abunda yace yadda ya nuna ko ajikinsa halin da fawan ke ciki,

    nuna sehrish yayi da hannu tare da cewa “Ke! ki kawo mun abinci na yanzun nan a bedroom ɗina ina jiran ki,

  Cikin sauri sehrish tace “Ni babban yaya zan kai mawa yanzu, sai dai ko in aunty azmee ta jera a dining ka zauna ka ci,’ 

  Zaro ido haroon yayi afusa ce yace “Ke! Ni kike fadama cewa wani wai babban yaya zaki kaima abinci”? Ke ga futsararra ko”? ya tambaya yana faman huci

   da ido azmee tayi ma sehrish alamar tayi shiru da bakinta, tsit tayi bata kuma cewa komai ba,

  cike da bada umarni yace “Ina jiran ki ki kawo mun idan kuma ba haka ba zaki ga mai zai biyo baya,” yana faɗin hakan ya fuce daga kitchen ɗin,

  Murya tamkar zatayi kuka tace “Aunty azmee nifa bazan kai masa ba Allah,”

  Azmee tace “sehrish ki daure ki kai masa, nikaina na tsorata da yarda yake mana magana, ina tunanin kamar yayi shaye-shaye ne baya cikin hayyacinsa,”

   “Aunty azmee nifa bazan kai masa ba,kema da kan ki kince baya cikin hayyacinsa yanzu in naje zai iya kai mun bugu,”

   ganin ta dage akan cewa ba zata je ba yasa Azmee cewa “to shikenan bari ni nakai masa, ke kuma ki kaima Sgr nasa,” ajiyar zuciya sehrish ta saki tare da cewa “to,”

bayan sehrish ta kammala shirya masa a tray ta wuce upstairs part ɗinsa, sallama tayi ba’a amsa ba don haka tashiga daga ciki, babu kowa acikin falon alamar yana a cikin bedroom ɗinsa,

   takawa tayi izuwa ƙopar bedroom ɗin nasa tayi masa sallama kusan sau uku sannan ya amsa mata da cewa”Come in,”

  Shiga ciki tayi zuciyarta na dar-dar lokacin da ta aza idonta akanshi yana zaune gaban dressing mirror saman chair din dake gaban madubin, ya sanya tafin hannayensa ya tallabo gefe da gefen fuskarsa ya zabga tagumi agaban mirror, sam babu riga ajikin shi daga shi sai short green colour, da alama ma daga wanka ya fito yagaza yin komai shine ya zabga tagumin, Sumar kanshi duk ta barbazo ta rufe masa gefen face dinsa, da wasu siraran gashi da suka sauko ta saman fuskarsa idonshi na arufe saboda gajiyar da ta lullu6e ga66ansa da kuma baccin da yake ji ga kuma yunwa duk shi kaɗai

tsayawa sehrish tayi jiki asanyaye tana kallon shi tsananin tausayin shi ne yakamata ganin yarda ya zabga tagumi da hannayensa biyu, alamar baya jin daɗi

  Ta jima tana kallon shi kafin ta ɗanyi gyaran murya tace “dama abinci ne na kawo maka, bansan ko kana buƙata ba,” ta fadi adan tsorace gudun kar tayi kuskure a maganarta,

   daker ya buɗe bakinsa tare da cewa”keep it on the table, then i wanna see u,” gabanta ne ya faɗi rass ! jin abunda yace na yana son ganinta ƙarasawa tayi ta ajiye masa dinner din saman table ɗinsa, sannan ta matsa kusa dashi ta tsaya sannan tace “gani,”

  Hannu yasa ya ɗauko wata ƙaramar kwalba ta magani daya ajiye a saman mirror din sannan ya miƙa mata tare da cewa “rub it on my back,” ya fadi tare da kifa kansa saman gaban mirror ɗin yadda zata samu damar murza masa maganin,

tama rasa ta ina zata fara shafa masa shi, gaba daya duk tabi ta rikice wai yau itace sgr da kansa ya bata magani don ta shafa masa abayansa, jikinta har kerma yakeyi tsoranta kar ta fasa masa fatar bayansa saboda hasken fatar fes tamkar in kasa yatsa jini zai fito,

  Matsawa ta ƙara yi dab dashi sosai sannan ta buɗe mufin kwalbar, tasa yatsa ta lakuto maganin tare da ɗan russinawa ta lakuta masa shi abayan, sannan tasanya hannunta a hankali tana shasshafa masa shi, tun da Allah ya halicce ta bata ta6a jin skin mai tsananin laushi da daɗin tabawa ba irin fatar bayan sgr, 

Shi kuwa ajiyar zuciya kawai yake saukewa saboda relief daya fara samu sosai na ciwon da ga6o6insa suke masa, tun sehrish nayi masa da hannu ɗaya har takai ga ajiye kwalbar maganin ta sanya duka hands ɗinta a faffaɗan bayansa tana yi masa massage, a tunaninsa in ta kammala zata cire hannunta ne, amma sai yaga ta zarce gaba ɗaya babu alamar zata daina shafa masa gashi kuma yaji ko’ina na bayansa yaji maganin sosai, shiru kawai yayi bai ce komai ba, almost one hour kenan sehrish na shafa masa magani har sai da ya ɗan ɗago da kansa daga kwancen da yake tare da cewa “Har yanzu maganin bai shafu bane”? Cikin sauri ta janye hannunta tare da ɗagowa tana kallonsa suka haɗa ido ta cikin mirror,

  gabanta ne taji ya ƙara faɗuwa rass ganin yarda kwayar idonsa ke shining sai taga tamkar tana canza launi ne daga blue zuwa green,.  

  sunnar da kanta tayi ƙasa tana faman haɗe yatsun hannunta dake dankare da maganin data shafa mashi,

lumshe idonsa yayi tare da sake buɗe su yace “kin haɗo mun da coffee ne? ya tambaya a kasalance hakan ba ƙaramin kashe ma sehrish jiki yayi ba, tuni ta nemi natsuwarta tarasa sai ta kama en ena tana faman wurwurga ido

 “Its ok, idan babu akawo mun shi,” ya faɗi tare da mayar da idonshi ya lumshe su,

Juyawa sehrish tayi cikin sauri ta fuce izuwa kitchen donta haɗo masa, a lokacin har azmee ta kammala shirya masu abincin dinner ɗin a dining amma babu kowa asaman shi alamar basu kaiga fitowa ba,

 tayi mamakin hakan duk da tasan cewa duk suna cikin damuwa ne,bata ji daɗin hakan ba, tasa ba ganin mutanen gidan cikin raha suna nishaɗi suna cin abinci yau kuma wayaam babu kowa, Yau da gobe kenan,

   tana acikin kitchen ɗin bayan ta kammala haɗa masa coffee din ta ruƙo cup ɗin a hannunta, sai ga haroon ya faɗo mata kamar daga sama cikin sauri taja da baya hankalinta atashe, daga shi sai vest da singlet, shu’umin murmushi ya saki yana kallonta yace “ke shine nasa ki kaimun abinci kika ƙi ko? Ke ga isassa mai walkin sa harni ɗan masu gida zan saki aiki, ki bijire mun,” ya faɗi yana kallonta

  Murya na rawa sehrish tace “kayi hakuri dama na fara kaima babban yaya ne, kafin na kawo maka nakan……’

 Bata ƙarasa ba ya katse ta da cewa “Sorry for your self sehrish! wlh kin shiga uku ! kin jefa kanki cikin masifa, daga rana irin ta yau inaso kullum ki kasance cikin yin sallar dare kina rokan Allah akan ya kare ki daga Sharrina,” zaro ido tayi tana kallonsa jin abunda yace cikin tsananin tashin hankali tace “saboda me zaka ce haka”? laifin me nayi maka, dan Allah kabarni inyi rayuwata cikin salama,”

  Fashewa da dariya yayi kafin ya tsagaita da cewa “kinsan wani abu?kina da kyau sosai musamman idan kika tsorata idanunki ba ƙaramin fizgata sukeyi ba, idan kika amince a shirye nake dana aure ki, kuma zan shiryu nadaina duk wani abu da nake yi, amma idan kika bijire mun I pity u wlh,” cikin sanyin murya yake yi mata magana,.

  Tamkar zatayi kuka tace”Dan Allah na roƙe ka kayi hakuri nidai ka fita daga cikin rayuwata, kabarni dan Allah kaje can ka samu mace irinka ka aura, amma ni ina da wanda nake so,” tayi maganar tare da bi ta gefensa gabanta na faduwa ta wuce cikin sauri,

  murmushi kawai haroon yayi tare da jinjina kansa aransa yace “nasan ba kowa take hari ba face wancan mai zubin ifritan, ni kuma ba zan ta6a bari hakan ta faru ba, target ɗina na farko da zanyi zan fara 6ata sunanki ne a wurinsa,” yana fadin hakan ya saki shu’umin murmushi tare da wuce wa room ɗinsa

 

Maganganun da haroon ya faɗa mata sun tsaya mata arai, tunaninta ya rayuwarta zata kasance nan gaba acikin gidan batasan me haroon zai yi mata ba,

tana tunanin tana tattaka stairs ɗin jiki amace, adai² lokacin Marshal ya shigo gidan cikin sauri saboda yarda yake agajiye shima, har sai da ta juyo daga saman stairs din ta ɗan kalle sa, ta other side ɗin yabi ya wuce part ɗinsa da hanzari sam bai lura a ita ba,

   bakomai bane ya faɗo mata arai face yaran da taji yace zasu zauna gidan Uncle Abusufyan ɗinsu, ko ya ɗauko su? ta tambayi kanta 

cikin sauri ta wuce part ɗinsa bedroom ɗinsa ta shiga da sallama ya iznin shiga, a lokacin harya dawo gefen bed ɗinsa ya zauna yana cin abincinsa, yau ba sai ya jira anyi saving ɗinsa,

  ƙarasawa tayi kusa dashi sannan ta samu wuri agefen plate ɗin abincinsa ta ajiye masa cup ɗin,” 

A hankali ya furta “thanks,’ a tunaninsa zata tafi amma sai yaga tayi masa tsaye akansa, sam bata son ta tafi tabarshi saboda a ganinta in ta tafi bazai ƙarasa cin abincin bacci zai iya ɗakarsa,

Hannu yasa ya ɗauki cup of coffee ɗin data kawo masa sosae yasha, bayan ya kammala ya ajiye shi, sannan ya gyara kwanciyarshi ya kwanta luf abunsa, ya janyo blanket ɗinsa ya rufe har zuwa chest ɗinsa nan take bacci ya ɗauke sa, 

bata bar bedroom ɗin nasa ba sai da ta tabbatar tayi masa addu’a tukunna tasa hannu ta kwashe kayan abincin acikin tray ta fuce dasu a hannunta,

   Kitchen ta koma da hanzari ta haɗa ma Marshal Omar nasa shima acikin tray sannan ta wuce masa dashi part ɗinsa,

tana shiga a lokacin ya fito sanye da jallabiya fara wuri ya samu asaman 3 seater ya zauna hannunsa ruƙe da wayarsa ganin sehrish yasa shi sakar mata murmushi tare da cewa “kamar kinsan a yunwace nake abunda nake jira kenan,”

  Murmushi ta saki tare da ƙarawa ta ajiye masa tray ɗin asaman table ɗin dake a gabansa sannan tace “Ya mai jiki ya omar, naji abunda ya faru Allah ya kiyaye gaba, ya tonu asirin su,”

  “Ameen Ameen,” ya amsa mata, hannu tasa ta buɗe warmer tare da ɗaukar plate da saving spoon zata zuba masa abinci taji yace “baki tambaye ni twins ɗina ba”? Murmushi ta ɗanyi tare da ɗagowa ta kalle shi tace “dama ƴan biyu ne”? Yace “eh kamannin su ɗaya sak, ke ma haka fuskarki irin tasu ce sak komai da komai,”

   gabanta ne taji ya faɗi jin abunda omar yace dakatawa tayi da zuba mashi abincin tana son tunano wani abu arayuwarta amma sam takasa tunawa, tabbas tana jin cewa akwai wani abu da ta manta arayuwarta mai matuƙar muhimmanci agare ta, a duk lokacin da tayi ƙoƙarin tunawa sai taji zuciyarta tayi mata wani irin nauyi sosai,

“Wata rana zan kawosu ku ga juna, saboda inaso ki ga abun al’ajabin da nake son nuna maki,”

Cikin sauri tace “Shikenan ya Omar Allah ya kaimu lokacin nima zanso nagansu,”

ta jima suna dan fira dashi kafin daga bisani ta bar part ɗin nasa ta koma ɗakinta, 

 Bayan Omar ya kammala cin dinner ɗinsa fitowa yayi tare da wuce wa ɗakin da suka kwantar da fawan

  Yanayin daya samu Twis zaune zun zuba mashi ido ga kanal yusif shima zugudum duk cikin jimami, gyaran murya yayi duk suka ɗan ɗago kana yace “ku tashi ku je ku kwanta, tun da ya samu bacci” 

  Amsa mashi su kayi da “toh” sannan suka miƙe tare da fuce wa daga ɗakin shima yusif yayi yabi bayansu, zama Omar yayi daga gefen fawan dake ta faman sharar bacci, addu’o’i ya shiga karantowa yana tatto fa masa, ya jima yana yi masa addu’a sannan ya tashi yabar ɗakin tare da tufe masa ƙopa,

****************

Wuraren ƙarfe sha biyu ya fito cikin sanɗa hannunsa ɗauke da pillow yana duddubawa yaga in ba kowa duk sunyi bacci lokacin murmushi ya saki tare da cewa “sheggu saboda wancan ɗan shilan shine duk suka susuce har suka gaza cin abinci, bari na ƙarasa shi lahira sai in ga ya zasu yi, zasu bi shi ne

 Yana faɗin hakan ya wuce ɗakin da suka kwantar da fawan cikin sanɗa ya tura ƙopar tare da sa ƙafa yashiga cikin, bin shi yayi da kallo jinjina kansa yayi sannan ya lalla6a ya haye saman gadon tare da ɗaga pillow ɗin ya taushe ma fawan hancinsa dashi , nan take fawan yafarka tare da zazzare idanunshi yana mutsu-mutsu sam bashi da sauran ƙarfi ajikinsa da zai iya kwatar kansa……….. … …

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Back to top button