Mijin Marigayiya Page 47 Hausa Novel
Kwanci tashi sai da Khadeeja ta kwashe shekaru biyu tana aiki a gidan rediyon nan a matakin internship sannan aka sami gurbi aka dauketa cikakken aiki, aka saka mata albashinta Naira dubu saba’in.Ba karamin dadi ta ji ba da samun wannan ci gaban domin tun da ta fara service ya zama wasu hidimomin nata ita take yiwa kanta kamar kayan shafe-shafe, turare wani lokacin ma har da sutura. Bata sani ba ko haka yake yiwa Najan ma tunda itama tana da albashi ko kuma ita kadai yake yiwa hakan.Sai dai bata da lokacin da zata bincika ko kuma ta tambaya don haka take rayuwarta yanda taga zata iya.Afaf ta shiga Jami’ar Bayero ta Kano inda take karantar Computer Science yayinda Habib yake SS3 yayinda Nasreen take JSS3 ita kuma Shukra tana primary 5.Zuwa yanzu duk bakon da yayi kwana daya a gidan zai gane cewa gidan ya kasu kashi biyu; Shukra da Halifa wadanda su ‘yan dakin Khadeeja ne da kuma Afaf da Nasreen wadanda su ‘yan dakin Naja ne. ko a wajen tarbiyya ‘yayan dakin Khadeeja sun fita da ban da ‘yayan dakin Naja. Domin ita Khadeeja tarbiyyar take basu da kulawa saboda Allah kamar yanda take yiwa Hammad, ita kuma Naja hankalinta yana kan yanda zata kwace gida ta mallake maigidan don haka duk abinda zai saka shi farin ciki shi da yaransa shi take yi; ko da kuwa abun ba daidai bane.Lokuta da dama idan taje wajen malamanta tana samu ta fara juya Mustapha, sai dai abun bai fiya dadewa ba. Da zarar ta fara samun yanda take so sai kuma ta sake rasa kan maigidan nata. Tayi iya bakin kokarinta ganin ta inda zata samu ta hadashi fada da Afafa amma ta gagara; saboda son da yake yiwa Afaf ba kadan bane. Kuma kusan duk wani abu da zai yi to da Afaf yake shawara. Haka aka yi a farkon shekarar nan da zai canza mota; da kansa yake fada Afaf ce ta zabar masa motar bayan ita bata ma san zai canza motar ba sai da aka kawo motar gidan. Haka kuma aka yi da zai canza fentin gidan; Afaf ce ta zabi wanda take so aka yi, sai daga baya matan gidan suka ji labari.Lokuta da dama Naja ta so su hade kai da Khadeeja ko da su samu su kwaci Mustapha daga hannun ‘yayan ne, amma bata sami hadin kai ba. Domin har yanzu zaman nasu dai babu yabo babu fallasa. Shi yasa ma Najan takewa Khadeeja kallon bata san me take yi ba saboda yanda ta bari yara suke controlling miji.Ita kuwa Khadeeja bata taba daukan alakarsa da yaransa a matsayin matsalarta ba, matsalarta daya da shi rashin adalcin da yake nuna mata tsakaninta da Naja. Idan dai abun a nuna kulawa ne da kauna to Naja yake nunawa, amma idan abu ne wnda za ayi masa hidima shi da yaransa to sai yace a kaiwa Khadeeja.Duk wani kokari da zata yi ta ga ya nuna mata so da kauna tayi amma abun ya ci tura; har ta gaji ta zuba masa ido. Lokuta da dama idan tayi magana sai dai ya dinga kokarin nuna mata cewa ya fi sonta kuma ya fi trusting dinta shi yasa yake saka ta hidimarsa da ta yaransa. Ta gaji da jin wannan tatsuniyar shi yasa ma ta hakura ta daina korafi; kawai dai duk abinda zata yi zata yi, abinda ba zata yi ba kuma haka zata zuba masa ido ya karaci barazanarsa amma bata yi.Haka rayuwarsu ta cigaba.——–Tun kafin ta yaye Hammad al’adarta ta dawo, don haka kai tsaye ta tafi asibiti ta karbo kwayoyin family planning; ko Mustaphan ma bata gayawa ba sai da ta karbo. Ba wai haihuwar ce bata so ba, kwai dai bata da tabbas din zaman auren. Kullum Mustapha nuna mata yake itace jakar gida yayinda Naja itace matar gida; don haka duk da yana kula da yaransa sosai kuma yana son su amma bata jin zata iya tara masa wasu yaran balle ma azo inda zata yi magana a ce tayi hakuri ta zauna don yaranta.Tunda ta karbi kwayar nan bata taba yin fashi ba kamar yanda likita ya sanar da ita, ko da kuwa ba itace da kwana ba haka take shan kwayarta. Amma a ‘yan kwanakin nan gaba daya ta rasa gane kan jikinnata; wasu abubuwa take ji kamar na mai laulayi.A hanyarta ta dawowa daga office ta tsaya a chemist ta siyo pregnacy test strip, har ta zo gida tana fargaba saboda duk wasu alamu na ciki sun gama bayyana a tare da ita. Sai da ta bari tayi baccin dare sannan ta dauki fitsarinta na sassafe ta gwada da shi; kafin sakamakon ya bayyana a jikin ‘yar takardar gaba daya ta gama rudewa. Ko da taga layukan guda biyu sun bayyana batare da wata matsala ba sai da zuciyarta ta kusan bugawa, ta muttsike ido ta sake kalla amma har yanzu layukan suna nan guda biyu. Haka ta hakura ta mike ta dauro alwala sannan ta fito daga bandakin ta tayar da sallar asuba.Bayan ta idar da sallar ta zauna a kan daddumar ta yi shiru; ta daga hannu zata yi addu’a amma ta rasa ta inda zata soma. Gaba daya ma bata san me take ji ba. ‘Alhamdulillah.’ Ta fada a fili kamar me yin rada.Haka ta karasa azkar dinta sannan ta mike ta shiga hidimarta.Dole ta hakura ta daina shan kwayar family planning din da take sha saboda kada taje ta cutar da abinda yake cikinta.Sai bayan kwana biyu ta dan sami natsuwa sannan taje asibiti aka sake yi mata gwajin, aka tabbatar mata tana dauke da ciki na sati shida. Bayan ta dawo daga asibitin sannan ta sanar da Mustaphan.Wannan gwajin da ta yi kuma sai ya zama kamar ta kunno laulayin gaba daya. Babu inda yake mata ciwo amma tana fama da kasala sosai sannan kuma ga rashin son cin abinci. Haka dai ta cigaba da lallabawa.…………Ranar kwananta ne don haka Mustapha a dakinta zai kwana. Yaran duk sun kwanta a dakinsu yayinda Hammad da Shukra suke kwance a dakin bakinta wajen Hafsa.Yana zaune a gaban mudubinta yana aiki a computer dinsa yayinda ita kuma take kwance a kan gado tana game a waya. Ya bar aikin ya juyo yana kallonta ya kirawo sunanta, ta bar gane din ta mayar da hankalinta kanshi sannan ta amsa.Yace ‘Umm! Ina so dama na sanar dake bana zamu je aikin Hajji da Naja. Da dake zamu je amma kin ga ke laulayi ya saka ki a gaba don haka na cire sunanki na saka nata sunan.’Ta dan yi shiru saboda yanda maganar ta zo mata a ba-zata; idan dai ba wai bata ga dai-dai ba ma kamar dai ganin da ta yiwa Najan shekaran jiya ta ga kamar itama tana dauke da yaron ciki; ko da bai fito ba dai amma ita Khadeejan taga wasu alamu. Domin a lokacin har ta ji kunya tana fatan Allah ya sa ba ganewa Najan tayi ita tana dauke da ciki ba taje itama tayi. Kallon da ya kafeta da shi ya sa ta yi firgigit ta dawo hayyacinta tana cewa ‘Ma sha Allahu, Allah ya nuna mana. Amma ai ana zuwa da masu ciki kuma zan iya; in dai an yi niyyar kaini to a bani kujerata zan je.’Yayi dariya ‘Haba aikin hajin fa ba wasa bane kuma ba akwabce ake yi ba, ko so kike muje wahala ta sa ki sami miscarriage? Kuma ya za ayi na daukeku mu tafi saudiyya gaba dayanmu? Mu bar yaran a wajen wa? Kin san Hajia yanzu ba lafiya ce da ita ba.’‘Hakane, to ai sai Najan ta zauna ni naje tunda ni ka fara yin niyyar biyawa.’‘To ai na gaya miki ke ga ciki, da ace baki sami ciki yanzun ba dake zamu je amma ki yi hakuri sai shekara mai zuwa in Allah ya nuna mana.’Ta tashi zauna ta kara marairaicewa tace ‘Idan na mutu a haihuwa fa?’Ya harareta yace ‘Ka fadi alkhairi ko kayi shuru.’Ta sunkuyar da kai tana murmushin yake; yayinda ya juya ya cigaba da aikinsa…
