Ciwon Sanyi na mata (female infection) Ciwon sanyi ko kuma nace toilet infection ko vaginal infection duka yana Magana ne akan abu daya dukda dai wasu mutanen sunkan rabasu gida daban daban. Ciwon sanyi (infection) wani sako cuta ne da ke damun al’aurar mace har ma da maza wanda wan nan cuta ya zama ruwan dare ko kuma nace ya yawaita, Wannan cuta na mu mutane ta hanyar kaikayin gaba me zafi, warin gaba, fesowar kuraje masu masifan kaikayi, fitowar farin ruwa, ko wani kala na daban, ko jin zafi a lokacin da ake jima’i, yawan jin zafi a lokacin fitsari, da sauransu dai.
CIWON SANYI KALA 3
Ciwon sanyin da yake damun mata kala kala ne. Amma zamu kawo guda uku wanda shine yafi damun mata sosai kuma muyi muku bayanin su daya bayan daya
Sune kamar haka:
- Sanyi na bakteriya (Bacterial vaginosis)
- Sanyi na fungi (Yast Infection ko Candidiasis)
- Sanyi da ake dauka ta hanyar jima’i
SANYI A DA LILIN BAKTERIYA (BACTERIAL VAGINOSIS)
Bakteriya yana daya daga cikin babba da ke janyo wannan cuta na sanyi, a cikin mata 100 da suke da ciwon sanyi, kashi 50 suna dauke da bacterial vaginosis ne, wannan yana samuwa ne saboda canji na bakteriya ɗin da jikin mace, akwai bakteriya. masu bada kariya a gaban mace wanda ake musu suna da “normal flora”. Idan wannan bakteriya sukayi karfi suka yadu sosai gaban mace sukan zama alamun cuta kamar ‘Gardnerella vaginalis’ sai su kara da ciwon sanyi a jikin mace.
Duk macen da ta samu wan nan bakteriya a jikin ta ko kuma daya daga cikin ciwon sanyi ta na fado to sai tayi kokarin neman magani saboda lafiyar jikin ta dana mijin ta akwai magani kala-kala na hausa kona Islamic kona boko saiki nema wanda hankalin ki yafi kwanciya dashi, ina da maganin sanyi (Infection) kala daban daban amma karna fada muku a nan ya zama kalar ciwon sanyin ki daban kuma wanda zakiyi anfani dashi daban kinga beda anfani kenan, amma kije inda zaki nema magani ki nema ko ayi min Magana wajen comment kota email nawa saina fada ma mutum kalar maganin da zai nema.
WANDA FUNGI KE JANYOWA (YEAST INFECTION KO CANDIDIASIS)
Wannan ciwon sanyin (infection) na faruwa ne a sakamakon karuwan cutar ‘fungus’ wato Candida albicans a cikin al’aurar mace. Gaban mace yana dauke da wannan alamun amma basa cutar da mace har sai sun kara yawa zuwa wani lokaci. Suna kara yawan ne idan suka samu danshi na ruwa ko wani abu, ko rashin barin gaban ya dinga shan iska musamman da dare.
Su wan nan cutar ba gaban mace kadai suke aiki ba suna iya yaduwa a cikin jikin mutum. Mata da yawa suna cutar da wannan cutar a wani lokaci a wahala. A cikin kashi 100 kashi 50 sun kamu da shi, cuta ce mai hatsarin gaske a jin mace idan ba a addu’a da wuri ba musamman ga masu ciki komai zai iya faruwa da wan nan cikin ko abinda ke cikin.
ALAMUN YEST INFECTION
- Kaikayin gaba me zafin gaske saboda infection
- Radadi a farji kafar an zuba barkonu
- Fitan farin ruwa mai kauri
- Jin zafi a lokaci yin jima’i
- Saman gaban mace yayi jawur duk ya zage yana zafi
- Fesowar kuraje masu azaban kaikayi
Shima dai yana da nashi maganin daban dana bakteriya ba iri daya bane saboda ko wani koyan cuta daban yake yana da jami a nema magani wanda ya dace da ciwon da akeyi inba hakan ba zaaiyi ciwo daban magani daban sai aga magani beyi ba kuma a rasa mene ne matsalar.
WANDA AKE KAMUWA TA HANYAR JIMA’I
Shi wan nan kalar cutan na sanyi (infection) ana iya daukar shi ne ta wajen jima’a wan nan shi yake nuna mata zata iya daukar ma mijin ta haka nan miji zai iya shafa wa matar sa, kila ta dakko shi ne a wani wajen ko kuma shi yana da wata matan ya dakko daga wajen ta.
Mata yafi nunawa a jikin su saboda yawan kaikayi a cikin gaban su ko kuma kuraje acikin farjin nata saboda alamomin basu cika nunawa jikin namiji ba, da yawa har sai ciwon ya nuna jikin mace, wajen neman maganin sai ya gane shima yana da shi. don dole sai sunyi anfani da maganin dukan su.
ALAMOMIN SANYI NA MAZA
- Zafi wajen yin fitsari
- Zafi bayan fitar maniyyi
- Fitan farin ruwa lokaci bayan lokaci
- Kaikayin gaba ko fesowar kuraje
ALAMOMIN NA MATA
- Zafi a wajen yin fitsari
- Kyaikayin gaba me zafi
- Warin gaba akoda yaushe
- Fitan ruwa mai launin yellow ko fari tas akoda yaushe.
KADAN DAGA ABINDA KE JANYO MANA CIWON SANYI (INFECTION)
- Anfani da bayi mare kyau na makarnta ko wani public toilet
- Rashin gyara gaban mace ko wanke shi da abinda be kamata ba
- Jima’I da me ciwon sanyi (infection)
- Anfani da wandon me ciwon sanyi
HANYAR DA ZAKU KARE KANKU DAGA CIWON SANYI (INFECTION)
- Yawan anfani da magani ko wani iri musamman mata.
- Masu zina kuji tsoron Allah ku dena ana dakko shi wajen karuwai ko mazan bariki.
- Saka maganin matsi a cikin farki wanda beda asali.
- Masu ciwon sanyi (infection) kuma su nema magani don karsu shafa ma wasu.
ABINDA ZA’A KIYAYE A LOKACIN DA AKE MAGANIN CIWON SANYI (INFECTION)
Yana da kyau a maganin ciwon sanyi a duk lokacin da akaji alamun shi bawai har sai yayi karfi ba asha wahalan sa kafin ya kawo, kuma nema wajen maganin daya dace bawai yan bunburutu ba wanda basu san abinda sukeyi ba, san nan yana da. kyau a dena anfani da wandunan da ake sawa a baya a duk lokacin da ake amfani da maganin sanyi (infection) in kuma baki da halin canza wan dunan ki saiki jikasu a cikin ruwan zafi koda ma wanda ya tafasa ne, bayan yasha iska sai a wanke ya kasha duk cutar dayake cikin sa kenan.