Hausa novels

Ajiya A Duhu Book 1 Page 20 Complete Novel

🅿️➖2️⃣0️⃣……..Shahidah ta kira Ammie ta sanar mata da komai game da abinda RK yazo ma Maanal da shi. A mamakin Shahidah sai ji tai Ammie na maimaita kalmar Alhamdullah. Kasa daurewa tai ta ce, “Ammie kin amince kenan kema tayi aikin?”.     “Sosai kuwa Shahidah. Dan wannan wata mafita ce da masalaha UBANGIJI ya kawo mana. Ban sanar daku bane kawai amma tunda muka baro Abuja na dawo gidan nan a cikin cakwakiya ake da tashin hankali duk kuma akan batun auren Maanal da Yazeed ne. Namayi mamaki da kikace yau kusan kwana biyar bai leƙoku ba tunda yana Abujar shima.”     “Wlhy kuwa bai zoba Ammie, nama zata ko yana Kaduna ko yayi tafiya ne wani waje. Amma naga yana ƙoƙarin kiranta a waya yaji lafiyarta. Wai Ammie miya faru ko ɗaura musu aure kukai? Ko har yanzu Mamma ɗin ce ke tijarar bata son?”.    Ƴar dariya Ammien tayi da faɗin, “Kefa daɗina dake shirme Shahidah. Auren lafiya kuma yarinyata na a wannan halin na ciwo mai girma irin wannan hauka nake zan bari a mata aure bada amincewarta ba. Akan dai Hajiya Yaya ne da batun auren……”    Tsaf Ammie ta zayyanema Shahidah yanda komai ya faru da kuma matsayar da ake akai yanzu.         “Kai wannan mata ALLAH ya rabamu da masifarta Ammie. Ita dai ta sani mu ALLAH yasa haka shine mafi alkairi ma, dan wlhy garama ta auri Rafeeq ɗin amma haɗata kishi da wannan ƴar iskar yarinyar sangartacciya ai wani hatsarinne. Zasu iya haɗe kai su dinga cutar da ita watarana mu wayi gari zuciyar tata ta buga. Amma kinga Rafeeq ɗin nan wlhy Ammie yana da hankali da tarbiyya. Damma Maanal ɗin ce taƙi sakin jiki da shi kin dai san halinta”.       “Karki damu a hankali ne. Kudai ku cigaba da tayata da addu’a. Watarana ai sai labari. Amma in sha ALLAHU batun Yazeed kam nima bana mata fatansa kuma suje can su ƙarata. Yanzu ki bani zuwa gobe zan yi magana da Daddyn naku, idan ya tirje sai shi mijin naki ya masa magana ko naje Zaria na haɗashi da abokin nasa.”      “Shike nan ma Ammie wlhy dama haka kikayi”.    “A’a bari dai na fara masa magana dan bana son butsutsunsa. Yaya jikin autar?”.    “Alhamdullahi Ammie jikinta na ƙyau sosai. Dan naga har ta koma karance-karance novels ɗin nata na fama. Gata can ma tana shiri Abban Barru yace idan ya dawo zai kaita bookstore ta samo wasu”.       “To Masha ALLAH, ALLAH ya ƙara lafiya. Nima zan shigo na sake ganinta in sha ALLAHU zuwa next week haka komai ya ƙara lafawa.”   “ALLAH ya kaimu Ammie muna nan muna jiranki. Itama Amal tace next week zata dawo”.      “To shike nan idan naga zai mana dai-dai sai kawai mu taho tare, amma ni ranar zan dawo gaskiya”.    “Kai Ammie miyasa bazaki kwana ba?”.    “Daga dubiya sai kawai na kama kwana. Tunda ina jinku kullum a waya ai Alhmdllh ya wadatar, ba kuma sai na zauna na kula da tsohon mijina ba da ƙananun ƴaƴana”.   Dariya sosai Shahidah ta sanya. Daga haka sukai sallama….___________★        Kamar yanda Ammie taima Shahidah alƙawari ta tunkari Daddy da batun aikin Maanal. Sai dai kuma kamar fa yanda tai tunani ya nuna ɓacin ransa. Ya kuma tujareta da masifa dan dama yana riƙe da takaicinsu ita da Hajiya Basariyya a rai. Kasa magana Ammie tai sai duƙar da kanta kawai tai tana saurarensa. Sai da yay mai isarsa yay shiru dan kansa sannan ta tashi ta kwanta dan dama itace da shi a yau ɗin. Wasu irin hawaye ne masu zafi suka dinga rige-rigen sakko mata. Sosai tausayin kanta dana iyalanta ke ƙara girma a zuciyarta. A rayuwarta tayi farin ciki ne da samun ƴancin kai na shekarun ƙuruciya kawai. Amma tun daga randa aka lulluɓa mata zanen aure zata iya cewa daga lokacin ƘADDARARTA ta fara. Daga lokacin ta fara tantance gatan iyaye da ɗacin rabuwa da su. Daga lokacin komai ya canja, sunanta na Asiya sarauniya ya canja zuwa Asiya baiwa. Eh dole tace bauta, duk da a zahiri baza’a kalli rayuwar tata ata mai bauta ba kasancewar wasu abubuwa sun mata ado a bayyane. Sai dai wanda yasan ainahinta ne kawai zai san minene mizanin bautar da take magana da ƴancin kai. Ansha gwagwarmaya na tsawon shekaru kafin ALLAH ya iyakance, iyakancewar bai zama sauƙi ba kai tsaye, wata sabuwar jarabawar aka sake shiga, ta yanda zaren ƙaddarar ne ya kawota a wannan matsayin da take a yanzu kuma. Bazatai butulci ma UBANGIJI ba, domin kuwa Alhamdullah, ta samu canje-canje masu yawan gaske a sabuwar rayuwarta, sai dai anan ɗin ma ta gamu da wata jarabawar rayuwa a cikin mugayen kishiyoyi da kansu kawai suka sani……        “Asia! Kuka kike yi?”.    Furucin Daddy ya katse mata tunaninta. Da sauri ta saka hannu cikin dabara ta share hawayenta, sannan ta juyo garesa fuskarta da murmushi. “A’a Daddyn Hameed wane irin kuka kuma. Kawai dai na kwanta ne”.      “Humm Asia kenan, nasan kuka kike, kina kuka saboda kina ganin kamar na tauye hakkin ki dana ƴaƴank…..”    “Ya arrahaman”. Ta faɗa da sauri tana mai gaggawar ɗaura tafin hannunta a saman bakinsa. Zuuuu hawayen da take riƙewa suka shiga zirarowa. Kanta ta fara girgiza masa da sakin kukan gaba ɗaya. “Dan ALLAH kada kace haka Daddyn Hameed, ban taɓa raba ɗayan biyu a tsakanin su Maanal da sauran yaranka ba. Ni kaina inama mantawa bakai ka haifesu ba, saboda kana musu dukkan abinda uba kema ƴaƴa. Kana musu abinda mahaifinsu ya gagara musu. Taya zan kasance butulu waje rarrabe gaskiya da akasinta. Dan ALLAH ka gafarceni idan nayi kuskure, wlhy ban nema amincewarka ga Maanal tayi aiki dan baƙanta maka rai ba ko ƙasƙantar da dokar ka b…..”     “Shiiiii!! Ya isa kukan haka to”.Daddy ya faɗa yana mai jawota jikinsa ya rungume murmushi shimfiɗe a fuskarsa. A hankali yake shafa bayanta cike da lallashi. Tsahon minti ɗaya kafin ya furta, “Nasani Asia. Na kuma yarda dake ɗari bisa ɗari. Domin nasha gwadaki akan yaran nan batare da kin sani ba ke kanki kuma kina cinye jarabawar. Babu abinda zance dake sai godiya. Domin tabbas a cikin matana kina gaba a wadda nake alfahari da ita. Bance miki suma sauran sun gaza ba ko basu da martabar da nake kallonsu da ita ba. A’a ku dukanku kowa da inda yake tausasa min da kuma inda yake tsaurara min, amma kina da manyan lambar yabo kashi-kashi a gareni da bazasu lissafu ba Asia. Hakama su Shahidah, ni kaina biyayyarsu a gareni da girmamawa yakan sani manta ma bani na haifesu ba, ina jin alfahari da su, ina kuma godema ALLAH daya bani su matsayin ƴaƴana a yanzu. Ba aiki bane bana son Maanal tayi, domin nima na fahimci hakan zai taimaka mata ya ɗauke mata kewa musamman da nima nasan harkar zane-zane hubby nata ne. Kawai dai ina jin haushinki ne da tunanin baki son haɗa jini dani, shiyyasa yau ba fanshe haushin ta nan, sai nake ganin kamar baki son wannan haɗin da nake sonyi ne Asia. Alhalin ni kuma na ƙwaɗaitu ƙwarai da gaske da son ganin jinina ya sake gauraya da naki kozan cigaba da samun nagartattun zuria daga tsatsonki a cikin zuri’ata. Hakan zai sake dunƙulemu ya curemu waje guda. Tun akan Amal naso nayi wannan haɗin, sai na fahimci hankalin Yazeed akan Maanal yake shiyyasa na ƙwallafa raina a kanta.”       “Kayi haƙuri Daddyn Hameed sam ba haka bane kamar yanda kake tunani. Ka fahimceni dan ALLAH. Wlhy koda bana aurenka zan iya bama Yazeed auren Maanal. Domin ya taimakemu a gaɓar da muke matuƙar bukatar taimako. Zanma iya cewa ALLAH ya ƙaddara Manaal nada sauran kwana ne a duniya amma ya saka sanadin hakan a hannun Yazeed. Domin da ace kwannata ya ƙare tun a randa muka fara haɗuwa da sai dai wani zancen ake ba wannan ba. Dan haka ban taɓa jin bazan bama Yazeed Maanal ba. Kawai dai hankalina na matuƙar tashi kasancewar bakowane ɓangare bane ke buƙatar wannan haɗin, hakan kuma zai iya cutar da Yazeed ɗin kansa da ita kuma Maanal ɗin dake fama da rauni irin na ciwo mai haɗari. Amma yanzu masalahar da aka samu zai taimaka komai ya zama dai-dai itama ta samu sassauci haka shima Yazeed ɗin. Dan koba komai Hajiya Yaya mahaifiyace tana da tata darajar. Sannan Yazeed ya san komai daya shafi rayuwar Maanal, basai anyi sabon zama da zagaye-zagayen faɗa masa da fargabar zai amsheta ko zai canja ra’ayi”       “Hakane Asia. Na kuma fahimceki yanzu ɗari bisa ɗari. Zan kuma cigaba da addu’ar zaɓin ALLAH akan al’amarin insha ALLAHU. Sannan abinda ya shafeta ki daina wani damun a kansa kanki ai ƙaddara ce, bata wuce kan kowa ba kuma, ALLAH kuma shine shaida bataje takai kanta ba domin yin hakan jarabawace, wanda ma suke aikatawa kai tsaye ko suke zuwa bariki su kama ɗakin kansu suke auruwa cikin salama da kwanciyar hankali yanzu a ƙasar nan balle ita. Saboda haka na amince Maanal tayi aikinta. ALLAH ya sanya albarka ya kuma sa hakane yafi alkairi.”     Wani irin daɗi ne ya ratsa zuciyar Ammie. Ta ƙanƙame Daddy da ƙyau tana amsawa da amin. Shima murmushi ya saki mai faɗin gaske da karɓarta sosai ya rungume. A ransa kuwa yana sake ganin fara aikin Maanal ɗin wata masalaha ce. Dan zai fake da shi bayan anyi auren suyi zamansu acan, ita kuma wannan zaɓin uwar Yazeed ɗin anan cikin gidan yake son ta zauna tare da su saboda wasu dalilansa……      Tofa, mi kuke tunanin wai ya faru da Maanal ne?🥺. Sannan zamuga yanda wannan cakwakiya zata ƙare😂🏃.__________★        Wani irin farin ciki ne ya mamaye Maanal lokacin da saƙon Daddy ya risketa akan amincewarsa tayi aiki. Su kansu su Shahidah sai da suka tsaya suna kallonta ganin yanda taketa murmushi yau kamar ba Maanal ba. Sai suma hakan ya sakasu a farin ciki. A karo na farko na tarihi Maanal taima RK text massage da albishir ɗin amincewar Daddy. Ai ba’a haɗa awa guda ba sai ga bawan ALLAH a gidan. Yau ko lallaɓatan da Shahidah keyi na taje ta samu RK ɗin ba’ai ba. Yana kiranta yace gashi a gidan sai gata babu jimawa ta fita. Tunda ta fito ya zuba mata ido, sai ya zam tana takune tamkar da bugawar zuciyarsa. ALLAH ya jarabcesa da son wannan halittar ƙwarai da gaske. Yana kuma fatan mallakarta in har hakan shine alkairi a garesu. Maanal ta tsani kallo, dan haka sai da ta masa tsogumi akan kallon ƙurillar da yake matan. Baice komai ba face basarwa yana sakin murmushi. Itama sai ta sharesa kawai ta shiga gaishesa. Ya amsa mata da kulawa, kafin ya ɗora da tambayar yanda abubuwa suka kasance. A taƙaice ta faɗa masa, bai damu ba dan ya gama karantar ta zuwa yanzu. Bata da son yin doguwar magana sai idan itace taso hakan da kanta. Shine ya dinga zuba mata zance da yanda abubuwa zasu kasance. Ya kuma tabbatar mata nan da kwana biyu zaizo ya amshi takardunta. Ya kuma buƙaci ta ɗan zazzana wasu samples na agogunan zaizo ya amsa gobe idan ALLAH ya kaimu dan zai sake nunama mai Companyn. Duk da dai ya nuna masa wanda ta zana a asibiti. Ta tabbatar masa babu damuwa zatayi ɗin, daga haka sukai sallama ya fice ita kuma ta shiga gida.      Kamar ko yanda sukai alƙawari a wannan daren ta nutsu ta zana agoguna masu shegen ƙyau da ɗaukar hankali fin kala goma. Dan har gabannin asuba tana wannan aikin. Hakan ya saka mata makara. Tana yin sallar asubahi kuma ta sake kwanciya. Bata farka ba sai ɗaya saura. Ta samu RK yazo ya amshi zanen ma. Dan sun sanar masa tana barci yace kada a tasheta a barta tai barcinta, a bashi zanen kawai. Yana kuwa amsa bai jima ba ya wuce abinsa. Sai da ta tashi take jin yazo ɗin ya amsa. Har ta ɗauka waya kamar zata kirashi sai kuma dai ta fasa kawai. Tata tsumayen nasa kiran amma shima sai bai kira ɗin ba har dare. Sai da tana shirin kwanciya ne ma saƙonsa ya shigo.        _“Ina Kaduna yanzu haka. Mun gana da Daddy da Ammie, na kuma amso takardunki suna hannuna. Amma sai da safe zan dawo Abuja in sha ALLAHU. Kiyi barci cikin aminci tare da mafarki mai nutsuwa gimbiyar mata”_.     Baki kawai ta taɓe tare da jefa wayar saman gado ta cigaba da saka maɓallan rigar barcinta. Sai kuma ta tsaya cak kalamansa na dawo mata. Ya gana da Daddy da Ammie kamar yaya? Kai itafa shishshigin mutum nan ya fara bata tsoro. Kaji bala’i ko mi ya kaisa Kaduna?. Rashin mai bata amsa ya sakata jan ƙaramin tsaki ta haye gadon kawai ta kwanta. Addu’a tayi kamar yanda ta saba sannan ta kashe wutar ɗakin tana sauke ajiyar zuciya………✍️

Ajiya A Duhu Complete Novel Document Txt

Back to top button