Uncategorized

Abban Sojoji Chapter 34 Book 2 Complete Novel

 

“`The father Of Soldiers“`

 

Story &  Written 

       By 

      Hafsat Bature

          (Boss Lady)

Ringing ɗin da wayarta ke faman yi ne ya tashe ta daga guntun baccin daya ɗauke ta, farkawa tayi tana faman yin Hamma, hannu ta miƙa tare da ɗaukar wayarta dake ajiye saman side drawer, duba screen ɗin wayar tayi don taga wanene ke kiranta, lokaci guda gabanta ya faɗi rass ba arziƙi ta miƙe zaune saman gadon tana duban sunan mai kiram nata, sam tagaza sa hannu ta ɗaga kiran saboda tasan mai zai biyo baya, 

  Kusan sau uku kiran nashigowa cikin wayar ta ta, amma taƙi ɗagawa daga bisa ni mai kiran nata yadaina kira,

  Can sai ga ƙarar shigowar Message cikin sauri tasa hannu ta buɗe sakon ta soma karantawa kamar haka

_Babu buƙatar yin Sallama! Malama hafsat kin ban mamaki,Na kwashi uban kuɗi nabaki donki gudanar mun da aiki na, amma sai gashi Labari ya risƙeni cewa Anganki kina yawo dasu agari,Don haka ina so ki mayar mun da kuɗina yau ɗin nan in ba haka ba kotu ce zata raba ni dake_!!!!!!!!

   Wata Irin nannauyar Ajiyar zuciya Hafsat tasaki afili take furta “Innalallahi wa’inna ilaihirraji’un, ni sam na manta da maganar wannan matar ashe tana sane da kuɗinta, gashi har na fasa su, yanzu dole ne na biya ta kuɗinta ko na samu salama, tabbas zata iya ja mun bala’e Ya zanyi ni! Gashi Yau Daddy zai dawo in yaji wannan abun tabbas Nashiga Ukuna!

  Yunƙurawa tayi cikin sauri daga saman gadon jikinta na sanye da dogon wando baƙi sai ƴar Riga fara mai dogon hannu ajikin rigar an rubuta *I Love Paris* 

   Hannu tasa ta ɗauki ribbom ɗinta da ke ajiye saman mirror, ta ɗaure sumar kanta dashi sannan ta fito cikin hanzari, a babban falon tasamu Jahad da hussana zaune saman 3 seater suna kallo a plasman dake facing ɗinsu, jin alamar tafiyar hafsat yasa su ɗagowa tare da haɗa baki wurin cewa “Barka da fitowa Aunty hafsat,” daker ta iya yi masu murmushin yaƙe tace “Yawwa My Twins,” sannan cikin sauri ta wuce upstairs direct izuwa bedroom ɗin aunty babba,

 tun kafin ta shiga ɗakin nata take faman kwala mata kira Mommy!mommy!!Mom!!” 

Aunty babba da fitowarta kenan daga bathroom waist dinta daure da farin towel tana faman tsane gashin kanta da karamin towel tace”daughter lafiya kike mun irin wannan kiran na tashin hankali !!!,” Shiga ciki hafsat tayi tana cewa “Mommy akwai matsala wlh!   Dakatawa da tsane gashin kanta tayi sannan ta juyo ta kalli hafsat tare da cewa “Matsala kuma ta me kenan”?Cikin tashin hankali hafsat tace “Mommy wannan matar data ban kuɗi don na zubar mata dasu hussana da jahad, wlh itace ta kira ni yanzu, ban ɗaga kiran ba shine ta turo mun saƙon cewa na biya ta kuɗinta ko kuma ta haɗa ni da hukuma!!Ta ƙarasa maganar tana jira taji mai Aunty babba zata ce, abun mamaki sai taga ta fashe da dariya mai sautin gaske…….  Cikin ruɗu hafsat tace “Mommy na faɗa maki tashin hankalin da nake ciki maimakon ki tayani jimami amma sai naga kina dariya saboda me!?  tsagaitawa da dariyar Aunty babba tayi sannan tace”Hafsat kenan to ni menene ruwa na aciki? Ki mayar mata da kuɗinta mana shine kwanciyar hankalin ki,”   Muryarta tamkar xatayi kuka tace “Amma mommy sarai kinsan cewa nariga da na ta6a kuɗin nan kusan dubu ɗari takwas nayi amfani dasu aciki, Bani da kuma hanyar da zan biya su shiyasa nazo wurin ki saboda nasan akwai kuɗinsu Jahad wanda yaya Omar ya bayar ayi masu hidima, Inaso ki bani su don na biyata kuɗinta,”  Turusss ! aunty babba tayi kafin tayi Uwar shewa tace “Ahayyeeeee ! Anzo wurin dana fi so !! tabbas don kuɗi akwaisu kuwa suna kwance cikin bank account ɗina suna bacci, Ko sisi wlh baxan baki ba !! Har ni zaki watsa ma ƙasa a ido saboda waɗancan tsintattun yaran da ke da kan ki kika ce zasu iya zama nakiyar da zata tarwatsa mun plan ɗina, amma sai gashi akan idona kike nuna masu soyayya don ki 6atamun rai Ko?, don haka kije kiji da matsalar ki ! Ni babu ruwana acikin lamarin ki!!!  Ido cike taf da kwalla hafsat ke kallonta cikin tsananin 6acin rai da ƙuna har ta nufi hanyar fita daga ɗakin ta tsaya tare da juyowa ta kalle ta tace “Mommy naji duk abunda kika ce ! Nayi mamakin yarda kike tada jijiyoyin wuya akan kuɗin da bada gumin ki kika same su ba! Kuɗin nan Mallakin Su hussana ne! saboda su Omar yabada ayi masu hidima, ke kuma kika kwamashe su Saboda son zuciyarki, don haka muddin kika ce zaki hanani kuɗin nan, zan kira yaya Omar ne na tona maki asiri game da duk irin cin Zalin da kika yima Twins ɗinsa………….’ dakatawa tayi da maganar tana faman haƙi,  Aunty babba kuwa wani irin shu’umin murmushi tasaki kafin tace “and then So What Hafsat! Go ahead ki faɗa masa wlh ko ajiki na! Ni nasan yarda zan fidda kaina wlh, kece a ruwa bani ba, Ni dan Allah fuce mun daga ɗaki…………  tayi maganar tare da nuna ma hafsat hanya alamar ta fuce mata daga ɗakinta, murmushin takaici kawai hafsat tasaki kafin tasa kai ta fuce daga ɗakin, cikin tsananin jin 6acin rai Fuuuuu ta wuce izuwa downstairs ta wuce bedroom ɗinta, wuri ta samu gefen gadonta ta zauna cikin tashin hankali tana cikin wannan tunanin message ya sake shigowa cikin wayarta data bari saman gadon,Hannu tasa ta ɗauki wayar tare da buɗe saƙon ta karanta kamar haka

“ina tsammanin jin alert ɗin kuɗina, a yau ɗin nan in ba haka ba, nasamu labarin cewa yau general ishaq zai dawo wato Abbanki, kai tsaye zanzo har gidan ku, adai-adai lokacin dana tabbatar cewa ya iso gari zan shigo na tada maki 6alli”

Shiru hafsat tayi gabanta na wani irin faɗuwa tuni idonta sun canza launi, bata da wata mafita daya wuce ta koma ma mommyn nata, ta lalla6a ta tasamu tabata kuɗin ta mayar ma jarababbiyar matar nan, ko sun rabu lafiya,   Zumbur ta miƙe tashi ga yin sintiri acikin ɗakin nata cikin tsananin damuwa, Sallamar Jahad ce ta katse mata dogon tunanin da ta shiga, “Jahad har kun gama kallon”? ta tambaya yayin da take ƙaƙaro murmushi a fuskarta,   Jahad tace “A’a aunty an fara kiran sallar la’asar ne shine nashigo nayi sallah,” Hafsat tace”Allah sarki, na lura bakya wasa da sallah Jahad, da zarar lokacinta yayi komai kike saina ga kin dakatar dashi don yin ibadah,”Murmushi jahad tasaki tare da shige wa ciki tana cewa “aunty babu abunda yakai sallah muhimmanci acikin dukkan aiyuka, babu wani jin daɗi na duniya da zai sanya na manta da yin ibadata abisa lokacinta……….’  Wayar Hafsat da tayi ringing ya hana jahad ƙarasa jawabin nata, cikin sauri hafsat taƙarasa ta ɗauki wayar tare da dubawa, ganin numbar matarnan ce tsanya ta, yin wurgi da wayar, hankali tashe ta fuce daga ɗakin……… Shiru jahad tayi cikin mamamki ganin yarda hafsat tayi wurgi da wayarta ga fuskarta da alamun damuwa hakan na nufin wani abu na damunta,   “Ya Allah ka yaye ma aunty hafsat damuwar dake damunta, ka kawo mata mafita Alfarmar Annabi Muhammad (S.A.W),” ta faɗi acikin ranta sannan tashige cikin toilet donyin alwala,kai tsaye Hafsat ta koma ɗakin Aunty babba, lokacin da ta shiga har ta kammala shirya kanta cikin  atampha Embellished mai tsadar gaske da kyau, tana zaune saman stool agaban mirror tana shafa jan baki abakin ta, Hafsat ta shigo, wuri tasamu gefen gadonta tazauna tana kallonta,Juyowa Aunty babba tayi ta kallota tare da sakin Murmushi tace “My daughter, Look at my face how do i look? Kinsan yau Abban ki zai dawo, Shiyasa na taƙarƙare ina masa kwalliya, yau inajin kaina tamkar sabuwar amarya,”    Fuska a ɗaure hafsat tace”Kinyi kyau,”Aunty babba tace “Ae ko baki faɗa ba, nasan cewa ni kyakkyawa ce, tun da gashi nan ke ma albarkacin kyau na kin samu har kinyi ɗan haske da dogon hanci ga gashi har kina taƙama,”   Hafsat tace “hmmm mommy kenan, amma dai kinsan cewa Hanci na ba irin naki bane ko? kuma da kike maganar kyau kar ki manta Abbana fa kyakkyawa ne hausa fulani,” Tsoki aunty babba tasa ki tana cewa “Menene wani hausa fulani, Jinin Larabawa ake magana, kowa yasan mu da kyau babu jinsin da suka kai mu kyau aduniya kaf,”  ɗan guntun murmushi hafsat tasaki kafin tace”Ae shi kyau mommy ba’a fuska yake ba, ko a Surar jiki, a zuciya yake!! Duk kyan mutun muddin zuciyarsa baƙa ce, to ya tashi abanza mummuna ne shi,’Jin abunda hafsat tace ne yasa ta ajiye jan bakin dake hannunta tace “Tashi ki fuce mun daga ɗakina ! Bansan ma uban me yakawo ki ba,”   Shiru hafsat tayi batare da ta motsa daga inda take ba, illa kawai ta zuba mata ido,”baxaki fuce mun daga ɗaki na ba”? ta faɗi fuska aɗaure,   Sassauta murya hafsat tayi tare da cewa “Kiyi haƙuri mommy in na 6ata maki rai, zuciyata ce bata mun daɗi……..’  Aunty babba ta katse ta da cewa “don zuciyarki bata maki daɗi shine kika zo na wanke maki ita? Ko me?   girgiza kai hafsat tayi tare da cewa “kusan hakane mommy, ni yanzu zuwa nayi ki taimaka mun na mayar ma matar nan kuɗinta, ta addabe ni da kira, narasa ya zanyi,”  Murmushi aunty babba tasaki tare da juyowa sosai tana fuskantar hafsat tace,”Na Amince zan baki kuɗin ki mayar mata, amma bisa wasu sharuɗɗa! In kin bi muzauna lafiya daga ni har ke!?  jinjina kai hafsat tayi tace “ina sauraronki, wasu sharuɗɗa ne?  aunty babba tace “Inaso ki amince da maganar Fitar da yaran nan daga cikin rayuwarmu !!!!!!    ɗagowa hafsat tayi aɗan razane tana kallonta…………..Murmushi Aunty babba ta saki kafin taci gaba da cewa “Abun da nake son ki fahimta hafsat, ko da mun bar Omar ya ɗauki yaran nan ya tafi dasu can gidansu, wlh baza su ta6a samun kwanciyar hankali ba, domin kuwa Ke kinsan wacece Ammi ta tsani mutumin da bai da asali ya ra6i jinin ta, koda Omar yakai su can wlh ba zasu tsira ba!domin kuwa Ammi na zuwa zatasa a Kore su daga gidan! don haka yakamata kiyi tunani akan hakan kwarama cikin ruwan sanyi mu rabu dasu Lafiya,

  Shiru Hafsat ta ɗanyi na wani lokaci kafin tace,”Yanzu mommy Idan na Amince, su kuma yaran Yaya rayuwarsu zata kasance?ina za akaisu? Ina tsoran Rayuwarsu ta salwanta !

   Aunty babba tace “Hafsat don me zaki damu akan haka? ni in dai kin Amince zan sa akai yaran gidan marayu acan zasu samu kulawa, kuma dama can yafi dacewa dasu, in yaso sai mu runƙa zuwa muna kai musu Ziyara tare da tallafi koya kika ce?

    shiru hafsat tayi na wani lokacin sannan tace”Shikenan Mommy na yarda da hakan, Amma yaya Omar fa? In yazo yaya zamu ce mashi in ya tambayi twins ɗinsa?

    ɗan murmushi aunty babba ta saki ba ƙaramin daɗi taji ba jin yarda hafsat ta amince yanzu komai zai fi zuwa mata da sauƙi,

    taci gaba da cewa “Hafsat duk yarda zamuyi kada mu bari Abban ki yasan da yaran nan har izuwa gobe, Akwai wanda nayi ma magana zai zo gobe insha Allah, Shi zai kai su gidan marayun, Sannan maganar Omar tunda har yakai yanzu bai zo ba, inajin cewa tabbas akwai abunda ya tsaida shi wannan ba matsala bace kibar mun komai a hannuna ni nasan yarda zance mashi ya yarda………………

  Jinjina kai hafsat tayi jikinta a matuƙar mace saboda sabon da tayi da Su hussana da jahad sam batason rabuwa dasu amma kuma babu yarda zatayi this is the Only solution !!!

   Ajiyar zuciya ta saki tare da kallon Mommyn nata tace “Shikenan Mommy, ni zan wuce ɗaki sai naji ki ………… Muryarta na rawa take magana cikin sauri ta ƴunƙura tare da miƙewa ta nufi hanyar fita ɗakin tana jin Muryar Aunty babba tana cewa “Yanzu zan tura maki da kuɗin ki mayar mata abunta, kar taja mana bala’e

  Hafsat bata ce komai ba saboda yanayin da ta shiga, cikin sauri ta fuce kai tsaye ta shiga bedroom ɗinta,

  Lokacin da ta shiga ta samu su hussana da jahad zaune saman darduma suna karatun Al’qur’ani da kansu, sai taji zuciyarta ta ƙara karaya, cikin sauri ta faɗa toilet tare da rufo ƙopa tana faman shessheƙar kukan rabuwa dasu…………………………………..

__________________SEHRISH__________

Sam bakin ta yaƙi rufuwa don Murya, tun ɗazu ta shimafiɗa uniform ɗinta saman gadonta tare da sandal ɗinta da kuma school bag ɗin duka, ta tasa su gaba sai kallonsu take yi,bakomai take tunani ba face yarda zata fara shiga school gobe Talata, irin wankan da zata ɗauka,tana daga zuƙunne saman gadon nata sae faman sakin murmushi takeyi, hannu tasa tare da shafa uniform ɗin data jera tana cewa “daga gani zasuyi mun kyau,oh ni reeshi yanzu zanyi new friends a makaranta, da na banza da na kirki, Allah dae ya haɗa ni dana gari, ba wanda zasu canza min tunani na ba, ina ƴar talaka dani,” ta faɗi da ƴar dariya, 

Turo ƙopar Azmee tayi tare da shigowa tana cewa “Da alama yau sehrish kin manta da shiga kitchen ko? kin barni da aiki narasa dalilin dayasa kika zubama kayan makarantar nan naki ido,sai kace ba mallakin ki ba”?

   tayi maganar yayin da take ƙarasawa ciki, ɗagowa sehrish tayi ta kalle ta fuskarta washe tace “Am sorry aunty azmee, Yanzun nan nake shirin fitowa wlh, na kammala salla ne shine nake ɗan ƙara binsu da kallo,

   girgiza kai Azmee ta ɗan yi kafin tace “maza ki tattara kayan nan, ki mayar dasu cikin wardrobe, Kizo maza mu kama aiki,’ 

   Sehrish ta amsa mata da Toh sannan ta miƙe cikin sauri ta sauko daga saman gadon, Tattara kayan Uniform ɗin tayi takai su cikin wardrobe, bayan ta kammala ta ɗauki mayafinta saman gadonta, tayarfa shi akanta dama riga da skirt ne ajikinta, 

   Cikin sauri tabi bayan Azmee suka fuce izuwa kitchen,

  Cikin hanzari suka soma shirye shiryen fara girkin dare, suna cikin aiki Azmee nagaban gas tana tafasa nama, yayin da sehrish ke ta faman fere kayan lambu asaman Chopping board,

   Faɗowa junaid yayi cikin kitchen ɗin jikinsa na sanye da Kayan ball yellow sai faman zufa yake yi da alama shigowarsa kenan daga wurin ball, sam yagaza rufe bakinsa sai faman murmushi yake yi,

  “Wlh harka ban tsoro junaid, yarda ka faɗo suddenly,jibi jikin ka sai faman zufa kake yi,” Sehrish ta faɗi tana nuna sa da wuƙar dake hannunta,

  Juyowa azmee tayi tana kallonsa batare da tace komai ba,

  “Zuwa nayi in tunasar maki cewa, gobe ni zan kai ki school da mota ta,” ya faɗi yana faman sauke ajiyar zuciya,.

Sai lokacin azmee tace “Salon wahalar da kai junaid, ka bari tahau school Bus mana,ƙwara tasa ba da bin motar makaranta tun yanzu, amma in kace zaka runƙa kai ta ɗawainiyar zatayi yawa, kuma kasan sarai Babban yayan ku baya so kana fita ko?.ta faɗi tana kallonsa,. 

  turo baki junaid yayi tare da ɗan buga ƙafarsa yace “Nidai Aunty azmee zan kaita, just for tomorrow cos this is the first time da zata fara zuwa school ɗin yakamata tasan wasu abubuwan inaso zan nuna mata ne, tun da ni nasan school ɗin sosai….”

  gaba ɗaya kallon shi suke yi yarda yake magana cikin shagwa6a, yana faman bubbuga ƙafa 

Dariya azmee tayi don ta Lura rigimarsa ce ta tashi, dama aduk lokacin daya buga ball sosai yagaji alokacin rigimarsa tafi tashi,

  Sehrish tace “Shikenan junaid gobe kai zaka kaini school, amma yanzu kana buƙatar yin wanka ka ɗan huta,,”

   ɗan murmushi yayi jin abunda tace “Amma ina jin yunwa fa sosai,” ya faɗi yana kallonta

  “Shikenan kada kadamu yanzun nan zan kawo maka abinci,”

  “Yawwa My lovely sis,” ya faɗi tare da kama hanya ya wuce upstairs room ɗinsa,

   A tray ta shirya masa coffee tare da snacks, sannan ta fito ta wuce upstair domin takai masa, tana hawa saman stairs ɗin sai ga SGR shi da Marshal Omar suna nufo stair ɗin, ganin su zo dab da benen yasa ta saukowa gaba ɗaya don tabasu wuri su wuce, dukansu suna sanye da jean da t-shirt, sai faman sauri suke alamar akwai wani Uzuri dake gare su, suna ƙarasowa inda take tsaye tayi saurin cewa “ina yinin ku,” Omar ne kawai yasamu damar Amsa mata, amma shi SGR sam ko kallo ma hasalima baisan da mutun a wurin ba, gabanta ne ya faɗi don alamu sun nuna cewa ba ƙaramin abubane ganin yanayin fuskar kowannansu Especially Omar da ta sani, Kullum cikin sakar mata fuska yake duk in suka haɗu amma yau dakyar ya amsa mata gaisuwarta, 

  Bin su tayi da kallo, yayin da suka wuce kai tsaye hanyar fita falon suka nufa, har sun kusa fita Omar ya juyo ya kalle ta, bakomai yasa Shi juyowa ba fa ce tuna Hussana da jahad yau tsawon wata kenan baije ya dubo su, saboda busy ɗin daya shiga, yana da burin zuwa ɗaukosu amma aiyuka sun hana shi, Ajiyar zuciya yasaki tare da mayar da kansa suka sa kai suka fuce,

   sam sehrish tagaza yin motsi da ƙafafunta, hakanan ta dunga jin gabanta na faɗuwa, bata kai ga hawa benen ba, taji dirar motoci cikin gidan nan take ta sake jin faɗuwar gaba, cikin sauri ta haye upstairs ɗin da hanzari ta shiga bedroom ɗin junaid a lokacin yana cikin toilet yana wanka, ajiye masa tray ɗin tayi saman table, sannan tafito da sauri-sauri ta fito daga babban falon ta tsaya abakin ƙofar shigarsa, .  

  Kamar dai ranar da SGR da Omar suka zo Nigeria tare da uban security guards na sojoji haka yau ma, tsoro ne yakama sehrish gudun kar ace US zasu  koma,  

   Tana ganin lokacin da suka shiga cikin motocinsu kuma nan take motocin ajere suka nufi dogon titin da zai fidda ka daga cikin gidan,

   Komawa ciki tayi da gudun gaske ta faɗa kitchen tana faman kwalama aunty azmee kira, a ɗan razane azmee ta juyo ta kalle ta tare da cewa “Sehrish lafiya kuwa kike ta faman kwalamun kira haka!?

  Cikin tsananin tashin hankali tace “Aunty azmee meke faruwa ne? Yanzun nan naga Babban yaya tare da Yaya Omar, sun fito fuskokinsu ba annuri kuma ga tarin motoci can sun fita dasu,” 

   tsayawa azmee taɗan yi jimmmmmmm tana ɗan tunani kafin tace “Tabbas ina hasashen cewa Us zasu tafi Saboda ɗazu da safe naji ƙishin-ƙishin ɗin cewa Momynsu matar Uncle ɗinsu donald tana fama da blood cancer, To ina da tabbacin cewa kodae ta rasu ne………..’

   Zaro ido sehrish tayi cikin tsananin tashin hankali take furta “Innalallahi wa’inna ilairaji’un Allah yasa bata mutu ba, Yanzu shikenan in suka koma ko yaushe zasu dawo…..’

   Murmushi Azmee tayi kafin tace “naga kin tayar da hankalin ki, nasan saboda Tafiyarsu Rafayet ne bawai don jin mutuwar ba,

    Hannu sehrish tasa tare da rufe fuska saboda hawaye da taji sun tafo mata,

   bin ta da kallo kawai azmee tayi cike da mamakin ganin  tana shessheƙar kuka, 

   Matsawa tayi kusa da ita tare da dafa ta tace”Sehrish !! Wannan kukan na menene? Ba dai don tafiyarsu bane? 

   shiru kawai tayi batare da tace komai ba, ita kaɗai tasan me take ji aranta, gaba ɗaya fuskarta ta damuje da hawaye,

    Jinjina kai azmee tayi tare da cewa “Ki koma ɗaki ki kwanta kawai,”

  Cikin kuka sehrish tace “a’a aunty azmee zanyi aikin,”

   Azmee tace “a’a banaso ki tafi kawai zan ƙarasa abuna,”

   Juyawa sehrish tayi tare da fuce wa daga kitchen ɗin ta koma bedroom ɗinta, saman gado tafaɗa tare da cigaba da kukan, To fa sehrish komai yasata yin kuka? Allah wa’alamu,

  Azmee kuwa ta jima tana mamakin dalilin kukan Sehrish tarasa gane mata, aranta tana cewa “Badai saboda tafiyar SGR take kuka ba? Don ta lura da yadda sehrish ke matuƙar ƙaunarsa, sam bata iya fira batare da ta, Amabaci sunan shi ba ita dae kawai tafison jin Ana maganarsa,nan zakaga sakewarta,

   “Lallai ne akwai Babbar Matsala, muddin abunda nake zargi ya tabbata,ya zama dole in ja ma Sehrish burki, don gujema kamuwa da CIWON ZUCIYA,”!! Azmee ta faɗi acikin ranta,

  _______________________

Sehrish kuwa Tuni wani Irin zazza6i taji ya rufe ta lokaci guda, jikinta har kerma yake yi wurin janyo bargonta dake asaman gadonta ta lullu6e jikinta dashi, tana faman fidda numfashi mai zafin gaske, sam tarasa ina zata tsoma ranta ita kaɗai tasan irin raɗaɗin da take ji acikin zuciyarta

Har wuraren Sallar Magrib sehrish bata motsa ba, tana nan yarda take ƙudundune cikin barko,tamkar mai bacci alhalin nan Idonta biyu jikinta ne kawai da bayayi mata daɗi, Acan ciki kuwa fitowa junaid yayi bayan yasha baccin sa, ya sauya kayan jikinsa izuwa riga da wando, lokacin daya sakko down yayi mamakin ganin Azmee ita kaɗai tana faman jera masu dinner a dining, ƙarasawa yayi cikin sauri yana cewa”Aunty Azmee ina sehrish ɗin ne? Ita bazata fito ta tayaki ba? Azmee ta ɗan ɗago ta kallesa tare da cewa “Junaid ni kaina bansan meke damun Sehrish ba, Lafiya lou fa muke aiki da Ita, amma tunda tazo ta tambaye ni game da babban yayanku da Omar da taga sun fito fuskarsu cikin wani irin yanayi, kuma taga Sun fita tare da motoci dayawa, shine nake ce mata may be Us zasu je, tunda ɗazu da safe naji ƙishin ƙishin ɗin cewa Matar Uncle ɗinku donald tana fama da blood cancer may be ta rasu ne…..shine fa kawai sehrish takama kuka har nace mata ta koma ɗakinta kawai ni zanyi aikin,”    ta ƙarasa maganar cikin damuwa, Junaid kuwa shiru yayi hankalinsa ya rabu gida biyu, sam ya rasa gane inda maganar Azmee ta dosa, cikin mamaki yace “Us kuma? Taya babban yayan mu zaibar ƙasar nan batare da sani na ba? Anya kuwa aunty Azmee am just doubting about it bana tunani Us zasu je, kuma Matar uncle donald bana tunanin ta rasu gaskiya, tunda da naji ko a wurin Abban mu ne, Ni dai Allah yasa ba wani abu bane ya faru mummuna,” ya faɗi cikin tashin hankali kafin ya wuce yana cewa “Bari naje wurin Sehrish ɗin naji meke damunta,”

Azmee tace “to shikenan,”

A hankali ya tura ƙopar ɗakin yashiga da sallama, tsayawa yayi yana kallonta yarda take ƙudundune cikin bargo, A hankali ya kira sunanta “Sehrish……….’ shiru bata amsa masa ba, ƙarasawa yayi izuwa gab da gadon nata yaɗan zauna gefe tare da sa hannu ya yaye mata bargon dake jikinta, dogon numfashi taja tare da cewa “Junaid ka mayar mun da bargona, Sanyi nake ji,”   Junaid yace “Reesh wai meke damunki ne? Aunty azmee ta faɗamun cewa kinbar kitchen kina faman kuka? Cikin kuka tace “Junaid wai dagaske ne cewa Babban yaya da Yaya Omar us zasu koma yau? Sakin baki junaid yayi yana kallonta cikin tsananin mamaki amma bai kawo ma ransa komai ba sai cewa yayi “Sehrish dama akan wannan kika shiga damuwa? to ki kwantar da hankalin ki, Yaya Omar da yaya Rafayet bana tunanin sun bar ƙasar nan ne, Aunty azmee ce kawai tace maki hakan a hasashen ta, just calm down ur mind My lovely sis… . ………..jin abunda junaid yace yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da miƙewa zaune daga saman gadon tana cewa “ngde da jin hakan junaid, naji ma anata kiran sallar magrib bari naje nayi alwala,” junaid yace “to shikenan nima bari naje nayi salla,pls reesh karki ƙara sa damuwa irin haka, kuma in kin kammala sallar, ki fito muyi dinner atare,” Murmushi ta sakar masa tare da cewa “Ok my lovely bro, da zarar nayi sallah zan fito nima,” lumshe ido junaid yayi tare da buɗe su akanta fuskar nan ɗauke da Murmushi, sai da yaga sehrish tashiga toilet sannan yafuce hankalinsa a kwance……………………..❤

remain 2 pages free su ƙare, wanda baiyi payment ba ya hanxarta Yi, Abban Sojoji 300 ne, discount da nayi na Abbban sojoji fans group ne kawai 200, Vip kuma 700, bank details ɗin da za’a tura,3196407426 First bank, Bature Hafsat Muhammd Evidence of payment 08103884440

Back to top button