Fentin Zina Page 23 Hausa Novel
*****Shiru sukayi babu wanda ya amsa mata sai ta tabe baki tace kanku dai ake ji.Rabi dauko mun kazata a fridge shi kadai zanci in kwanta domin jikin nawa babu dadi dukka gabobina ciwo sukeyi.Toh dada! Mama rabi ta fada ta mike ta dauko ta dawo ta jawo karamin table din tsakiyar falon ta daura mata a kai ta koma ta zauna inda ta tashi.Dada tayi bismillah zata soma ci sai kuma ta kalli Ameena tace zo kici.Ameena bata ma san da ita take ba don idanunta na kallon kasa ne, har saida mama rabi ta dan tabata ta nuna mata dada.Kara maimatawa dada tayi har yanzu idanunta a kanta, Ameena ta sunkuyar da kai tace na koshi dada.A’a bazan yadda da wannan ba kuma kizo dai kici nace.Dada na koshi yanzu muka gama cin abinci ki tambaye su kiji.Ai fa dai naga alama kam, toh tunda baza ki ci anan ba idan kun tashi ke rabi ki dauko mata dayar sai ta tafi da ita can taci ina ga hakan zaifi.Toh dada an gode Allah ya saka da alkhairi, cewar mama rabi.A’a ba dai ku ba ita kadai na baiwa, dada ta fada tana nuna Ameena da hannu.Sunkuyar da kai ta kara yi tace nagode dada Allah ya saka miki da alkhairi.Jinjina kai dada tayi tace kici ki koshi kada ki rage musu fa, kinji ko!Insha Allah dada nagode.Toh shikenan godiyar ta isa haka, inji dada.Kadan suka kara zama mama rabi ta dauko mata kazar suka yiwa dada sallama suka fita tana kara jaddadawa Ameena kada ta tsan musu fah taci ita kadai.Koda suka isa dakin mama rabi dariya fateema ta fashe dashi sosai tana dukan hannun kujera.Mama rabi tace ke kuwa lafiya irin wannan dariya haka?Ta girgiza kai tace abun wancar tsohuwar ne yafa bani dariya kiji fa mama tana ta maimaita kada adda ta bamu bata san bazaima wuce makoshinta ba indai bata bani ba nikam, ta karasa tana dariya.Mama rabi tace kinga kiyi shiru da wannan dariyar zan saba miki tamkar mahaifiyata fa kikewa haka bana so ki daina.Kiyi hakuri mama abunne ya bani dari da fari na dauka tsohuwar ‘yar bala’i ce ashe dai tana da kirki.Ke ko ana miki magana ki bar abu kina karawa ya miki kyau, Ameena ta fada.Mama rabi tace rabu da ita ba ta raina ni ba goben nan sai insa ta a mota tayi gida kawai.Fateema ta hadiye sauran dariyarta tace kiyi hakuri mama kada ranki ya baci amma duk da haka nikam tsohuwar ta burgeni.Murmushi mama rabi tayi tace dada kam haka take, inta so kartawa mutum rashin mutumci bata duba alaqa ko dangantaka haka zalika kirkinta yana fadawa kan kowa inta so, sannan tana da mutunci kuma bata son raini dadin dadawa kuma abun hannunta bai rufe mata ido ba, idan ka iya zama da ita zaka ci riba sosai sabanin haka kuma zaka ji wuya.Allah sarki! Ameena tace.Nan suka ci gabada hira suna cin kazar har suka gama suka kwanta Ameena kam tana kwanciya bacci yayi awon gaba da ita ta bar fateema suna hira da mama rabi inda anan fateeman ta kara warware mata game da cikin Ameenar tun farkon al’amari har i zuwa yanzu.Sosai mama rabi ta kadu kuma tayi alkawarin insha Allah zata daidaita ‘ya da mahaifiyarta kafin ta kaiga komawa gida.Washe gari da sassafe saiga mai aikin dada tazo kiran Ameena wai tazo inji dada bata tsaya bata lokaci ba tabi bayan mai aikin zuwa part din dadan.Dada na ganinta ta fadada fara’arta tana cewa karaso jikata.Karasawa Ameena tayi zata zauna a kasa dada tace ta zauna a sama, Bin umurni tayi ta zauna a sama din ta shiga gaida ita tana amsawa.Dada ta umurci mai aikinta data matso da kulolin nan kusa, ta hau bubbudewa Ameena tana cewa ki zabi wanda zaki ci a cikin nan idan kuma zaki dan tattaba su dukkansu toh ki fara yanzu.Ameena kuwa idonta ne ya sauka akan alele mai kyau yaji manja da kifi da miyan jajjage nan take ta hadiyi miyau ta nuna shi da yatsa tace wannan zanci dada.Ayya wannan ko? Toh zaki ci a sama ne ko zaki sauko sai kifi jin dadin ci.Dada zan sauko, ta fada tana sauka daga kujerar cikin zakuwa da son ganin ta fara ci.Zubawa tayi yanda take tunanin zai isheta ta soma ci, dada ta ja kofin jug dake gurin ta dauki karamin cup ta zuba mata kunun gyada sai da ta cika kopin kana ta mika mata.Ungo kina ci kina sha har ki gama kiyi sauri kada ya huce.Toh dada ta fada tana karban kopin ta kurba kadan ta girgiza kai cikin santi tace dada kunun nan yayi dadi zan sha sosai.Sha abunki idan bai ishe ki bama za’a karo miki.Nagode dada Allah ya saka miki da alkhairi.Kada ki damu meenaluwa aike yanzu abun a kula dake ne duk da ba abun arziki kika yi ba amma ba’a biye miki ba dole a kula dake da abunda ke cikin ki tunda a haka taki kaddarar tazo hadi da sakacin ki da rashin kamun kai idan ba haka ba ina zaki sake da na miji har irin haka ta shiga tsakanin ku.Ameena tunda dada ta sako wannan maganar sai taji duk kwadayinta a kan alele da kunun gyadan ya kau, madadin taji dadin shi saima dacin shi data ji, ta jaye plate da kopin daga gareta.Dada ta dubeta tace lafiya kika janye abincin? Tun kamin kikai ga cin rabi.Dada naji baya mun dadine kuma, na koshi zanje in kwanta da yamma zan dawo muyi hira.Hum kedai kika sani daga fadar gaskiya toh Allah ya bada sa’a.Kiyi hakuri dada ni ba haka nike nufi ba. Ta fada tana mikewa tace mu yini lafiya.Daga haka ta fita daga dakin ta koma dakin mama rabi ta samu suna karyawa da wainar da mama rabi ta aika a siya musu anan makwabtan su nan take taji ranta ya biya ai kuwa ta zauna tasa hannu ana fateema tana fadin BISMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM.Fateema ta bude baki tana kallonta daga bi sani tace ya dai malama adda kamata yayi ki jira a miki tayi kamin kisa hannu ai.Naki wasane Ameena ta fada tana mai kai lomar wainar bakinta, koda ta soma taunawa wani irin dadi ne ya ziyarci harshen ta har zuwa cikin makwagoronta sai ta lumshe ido cikin jin dadi tace bayan ta hadiye.Um mama idan zan samu wannan kullum ai inaso shi zanyi ta ci bazan gaji ba.Murmushi mama rabi tayi don ta fahimci harda gudummowar kwadayi irin na masu ciki ya saka ta fadin hakan.Adda ki dinga ci a hankali mana! Ki duba fa har kin kai karshen plate din, cewar fateema tana nuna mata plate din da dan guntun wainar ke rage a ciki.Ke ki dauki wani plate din ki zuba wani ki bar mata wannan din inji mama rabi.Yauwa mama gara kam don wallahi banma wani ci ba amma take korafi nifa wainar ce tamun dadi Allah. Ta fada tana jayo kular wainar gabanta ta kara zuba wani ta tura wa fateema kular tace ki diba.Mama rabi ta kalleta tace kici idan ma bazai isaba sai a karo tunda nasan bai kare ba a wurin su.A’a mama idan naci wannan ma ya ishe ni….. *KUYI HAKURI DAN ALLAH NA SAMU KAINA A CIKIN UZURI NE AMMA INSHA ALLAH DAGA GOBE ZAKU SAMU PAGE MAI TSAYI NAGODE* 🙏 *EESHERT ADAMU* *MATAR MAJEEDADI* ✍️



