Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 29 Complete Novel

*ASM Bk2029*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

 

 

…….Juyawa yay walking majestically ya koma inda ya ta so ya zauna idon shi a kanta,

 

“zaki ta tsayuwa ne?” Ya tambaya had’i da d’age mata gira wani kuka cikinta ya fara yi, kaman k’wai ya fashe mata a ciki ta fara moving zuwa gefe inda wata kujerar take ta zauna tana cigaba da kallon shi, “From all indications kema kin gane husband to be en naki ko?” wani wahalallan miyau ta had’iya bata dae ce komae ba,

 

“I ave been wondering wata kucakar Dad ya sama man matsayin Mata a Wannan tsukukun k’auyen ashe ba kucakar bace mara kunya ce mai zagin iyayen Mutane” still bata ce mashi komae ba yaci gaba “But duk da haka am so happy Dad has made a right Choice for me, it’s nice meeting you my lovely wife” bakin Fatuu fa ya mutu murus ba kamar da ta ga irin murmushin da yake saki tasan ba har zuciya yake fad’ar abubuwan da yake fad’i ba,

 

“Kin bi ni da ido ko baki farin ciki da ganin husband en naki bane shiyasa ko Welcoming dina bazaki ba balle in sa ran za’a gaida ni, koda yake I know who my wife to be is ba lalle in ta iya gaida Mutane ba” d’an motsa baki tay sai kuma ta sunnar da kai katsa yayin da a cikin ranta ta furta innalillahi Wa’inna ilaihir raji’un, sam ta kasa bud’e baki tace wani abu don ba k’aramin Al’ajabi ne ya kamata ba, a hankali ta saci kallon shi taga still kallon ta yake hakan yasa ta idasa dagowa cikin trembling voice tace “ina wuni an zo lpy” d’an tafa hannu yay yace “Wow what a sweet voice, lafiya lou wife hope na same ki lpy?” tabdijan ya gama kashe Fatuu da mamaki duk yadda tay zaton zai mata ba haka take gani ba ganin tayi kasak’e tana bin shi da ido yasa ya d’age mata gira yace “Wife Kaman ke baki farin cikin gani na a matsayin wanda aka za6a maki ba ko” murya a hard”e tace “a’a nayi” jinjina kai yay yace “To ya Katsina fatan kin zo lafiya” tana d’an kikkafta ido tace mashi lafiya lau yaci gaba “dama ina ji ana cewa Katsina akwae beautiful babes masu ilimi da wayewa yanzu na shaida haka even though ke d’in asalin yar nan ce amman su suka maida man ke yadda nike son wife ena ta kasance” ya k’arasa yana wani juya yaudararrun idanun sa, sunnar da kanta tay k’asa don Maganar tashi ba wanda ta tuno mata sai Haisam Saboda shi ne ya maida ta yadda take,

 

“na fa san kina Magana so ki daina acting as if baki magana ko yana maki wuya, ki saki jiki ki kuma bud’a baki ki man magana kaman ranar da kika zage ni” da sauri ta d’ago ta kalle shi ya bud’a mata ido d’an yamutsa fuska tay cikin breaking voice tace “ni fa ba zagin ka nayi ba kuma Kaine ka fara zagi na ai” Shegen murmushin shi ya saki yace “kika rama kuma ko, anyway ai baki ji nace kin yi laifi ba ya wuce koma kin yi ai Amarya bata laifi if u wish yanzu ma zaki iya zagi na I won’t feel offended” ya ilahi ya rabbil alamen mutumin nan nema yake ya tarwatsa ma Fatuu zuciya, shiru suka d’an yi sai faman k’are mata kallo yake can yace “Wife ina buk’atar ruwa or I should serve myself ?” a hankali ta juya ta kalleshi sai kuma ta mik’e ta nufi gaban shi ta duk’a ta fara kokarin zuba mashi lemu hannunta har d’an rawa yake, bayan ta zuba ta d’ago da niyyar bashi taga gaba d’aya hankalin shi na a wani wuri a jikinta hakan yasa ta d’an d’ukar da idonta don taga abunda yake kallo ashe saman boobs d’inta da sukae fam fatar wurin fari fat da ita ya kafe da ido yana kallo sakamakon wuyar rigar da yake a bud’e sosae, da sauri ta ja gyalen ta rufe wurin hakan ya sa shi dawo wa cikin hayyacin shi ya kalleta da murmushi kafin ya kai hannu ya amshi glass cup d’in had’i da furta “thanks my beautiful wife” mik’ewa tay ta koma ya bi bayanta da kallo har ta zauna sannan ya kai cup d’in baki ya fara sipping lemun saida yasha kaman rabi sannan ya ajiye ya kalleta ta d’ukar da kanta tana d’an wasa da yatsunta taji ya d’an yi gyaran murya hakan yasa ta kalle shi yace “Wife miye labari” d’an watsa hannu tay tace “babu” yace “What about preparations na bikin mu?” Kaman bazata ce komae ba sai kuma tace “ana yi” gyara zama ya d’an yi yace “Ok dame dame zaku yi ne?” tace “ba komae” d’an buda ido yay alamar mamaki yace “Haka zaku yi bikin ba wasu programs kaman zaki auri enermy en ki” ido kawae take bin shi da shi yaci gaba “koda yake baki da Friends anan ko?” Kai kawae ta d’aga mashi ya jinjina nashi,

 

“To yanzu kaman nawa kike buk’ata na abunda kike ganin zaki yi like gyaran jiki and so on” ya tambaya, tace “zanyi ba sai ka bani ba” yar dariya yay ya d’an shafi sumar shi yace “Ashe wife en nawa Hajiya ce” shiru bata ce komae gaba d’aya sai taji ta k’agara ma ya tafi kota koma ciki don gaba d’aya kanta a d’aure yake bata da natsuwa,

 

“Gobe sister d’ina zata zo zaku je wurin tailor zai taking measurement naki sai ki shirya” kallon cikin ido tay mashi yace “let me have ur digits so dat lokacin da zasu zo sai in sanar maki” karanto mashi phone number d’in ta tay bayan ta gama ya kira jin wayan na ringing ba anan ba yasashi tambayar inda wayan take tace tana cikin gida yace to in ta koma sai tay Saving harda fad’i mata sunan shi Khalid ya tambayi nata tace mashi Fateema yana murmushi ya furta “Fatima Zaraah” har saida kirjinta ya buga damm, ganin yana kokarin mik’ewa yasa tace bai ci Abincin ba yana wani kashe mata ido yace he’s Ok bai jima da ya ci Abincin ba but next time in ya zo zai ci daga haka ya mik’e itama tana ganin hakan ta mik’e ya nufo in da take ya tsaya suna facing juna ya kafeta da mayaudaran idanunshi seductively ya furta “Hope ban yi laifi ba da ban ci ba kar next time a ki dafa man don nasan girkin ki must ba as hot as u’r” wani dam dam k’irjin ta ke yi ganin yadda yake mata Magana ba zato ba tsammani sai ji tay ya kawo hannu ya janyota ya had’e jikinsu a gigice ta shiga kiciniyar kwace jikinta saidae ta kasa a rud’e tace “Don Allah ka sake ni kar wani ya shigo fa ayi tunanin wani abu nike yi” gaba d’aya ya zuba ma lips d’inta ido yadda tay Maganar ba k’aramin tafiya tay da shi ba kokarin had’a face d’in su yake a kidi’me Fatuu ta tattara duk k’arfinta ta tura shi tay baya ta fad’a kan kujerar da ta tashi, wata yar iskar dariya ya saki yace “Wife zaki ji ma kan ki ciwo fa and miye abun rud’ewa haka kaman na aikata wani abu ba daidai ba, ko basu yi informing naki an biya sadakin ki bane?” Kasa cewa tay komae sai numfashi take fitarwa da sauri da sauri duk ya gama tsorata ta, still dariyar yake yace “I forgot wife en tawa Secondary graduate ce but at least be romantic Babe” daga haka yasa hannu a cikin Aljihun rigarshi ya fiddo rafar yan dubu dubu guda biyu ya d’aura mata akan cinyarta kafin ya sake sa hannu a aljihun ya fiddo farin glass ya sa a fuskar shi yana murmushi yace sai sun sake had’uwa daga haka ya fice, Mutuwar zaune Fatuu tay tama rasa tunanin da zata yi akan shi da k’yar ta iya yunk’ura wa ta mik’e jikinta har lokacin rawa yake ta nufi cikin gidan a kan hanya ta had’u da Mino tace mata taje ta kwaso kayan abincin da suka kai tace to, a Falo ta iske yadikko zaune tana ganinta tay mata Murmushi tace har ya tafi ta d’aga mata kai kafin ta wuce cikin d’aki tana shiga ta cillar da takalmanta ta cire gyalen shima ta wurgar ta haye gadon sai zare ido take tunani kala kala acikin ranta ba kamar akan had’a jikinsu da yay hakan yasa ta fara shakkun anya ba gaskiya bane yana neman mata in ba haka ba mi zai sa daga fara haduwar su yau ya had’a jikinsu bama wannan ba kadae har fa kusan had’a bakunan su yay ba don ta samu ta fizge ba, wata zuciyar kuma ta ayyana mata ai yace don an biya sadakin ta ne to amman ai ba’a d’aura masu aure ba ko, gashi sam ta kasa yadda da yanda ya sake mata sai take ganin kamar akwae dalilin hakan, tana ta zancen zuci har Yadikko ta shigo bata sani ba saida ta zauna ta kira sunanta sannan ta kai idanunta kan ta, tambayarta tay lafiya dai ko taga ta shigo ta kwanta ko wani abun ya faru ne ta k’ak’alo murmushin yak’e tace mata a’a lafiya lou,

 

“To Allah yasa dae kun fahimci juna yayi maki kuma” d’an ta6e baki Fatuu tay a sanyaye tace “koma bai man ba yadikko ya zanyi dole ai in Aure shi ko” shiru tay tana kallonta gaba d’aya tausayinta take ji don daga yanayin ta sai taga kaman bai mata ba, tambayarta tay ya akai taga bai ci komae ba Fatun tace “Yace ya k’oshi sai ya sake dawowa zai ci” jinjina kai tay tace mata to ta taso suje ta ci farko taso ta k’i tace ta k’oshi saida Yadikkon ta matsa mata sannan ta saukko lokacin ta nuna mata kud’in da ya batan na abubuwan da zata yi tace to ta ruk’e a wurinta. Da daddare tana cikin yin shirin kwanciya sai ga kira ya shigo wayarta koda ta duba bata gane mai kiran ba hakan yasa tak’i d’agawa taci gaba da abunda take sai gashi an sake kiran, zama tay bakin gado ta d’aga ba tare da ta ce komae ba on the other hand taji ance “Wife ko kin yi bacci ne” rass gabanta ya buga jin muryarshi sai lokacin ta tuna da d’azun ta bashi no dinta har ya kira yace tay Saving, sake maimaita tambayar da yayi mata yay sai lokacin tace mashi a’a yanzu zata kwanta,

 

“Gani na kasa bacci Saboda tunanin ki wannan shi ake kira da luv at first sight all I need in ji ki gefe na hope kema hakan?” shiru tay mashi har saida ya k’ara tambayar tata sannan ta tura baki tace “a’a” tana jiyo sautin dariyar shi yace “Don’t worry Babe zan koya maki yadda kema zaki rink’a jin hakan game da ni” shirun dae ta k’ara ita duk ta fara tsorata ma da shi haka ya dingi yi mata kalaman soyayya harda tambayarta wace tarba zata mashi a first night d’in su ita dae a tak’aice take bashi amsa wani wurin kuma ta mashi shiru jin shiru shirun nata yay yawa yasa shi tambayar ko ta fara jin bacci ne tace mashi eh yace bari ya barta ta kwanta harda cewa tayi bacci mai dad’i kuma tayi mafarkin shi shima zai yi nata ita dae shiru tay mashi tana niyyar cire wayar taji sautin wani matsiyacin kiss da yay mata har cikin dodon kunnanta da sauri ta cire wayar ta k’ura ma screen d’in ido kirjinta na beating very fast can ta runtse idanunta sai ga kwalla sun fara zubowa ba kowa ne ya fad’o mata a rai ba face Ya Haisam ji take inama shine yake nuna mata so haka ba wannan ba da take tunanin duk k’arya ne da biyu yake mata hakan ba don yana sonta tsakani da Allah ba, tana ta tunane tunanenta har bacci yay awon gaba da ita,

 

Washe gari bayan sun kammala yin breakfast ta gyara d’akin sai ga kiran shi wai ya kira ya ji ya ta tashi tace mashi lpy Lou anan yake sanar da ita ta shirya around 1:00 za’a zo atafi da ita ta amsa da to, lokacin ta sanar ma yadikko ita kuma ta kira Baffanta a waya ta gaya mashi yace to ta dawo lafiya ta so ace Mino ta dawo daga Makaranta ta rakata, wurin karfe d’aya saura tana cikin shiryawa yadikko ta shigo cikin d’akin ta sanar da ita game da zuwan wadda tazo tafiya da ita wato Sadeeya tace to, doguwar rigar shadda sabowa dal acikin irin kayan da Haisam yayi mata Navy blue tasha aiki blue da fari yayi kyau sosae ta sa yan kunne da sark’a sai Agogo duk silver sai farin mayafi haka takalma ma high heels ne farare ta d’auki yar clutch dark blue, a saman kujera Sadeeya ta zauna ita da wata yarinya da zata yi shekara bakwae da suka zo tare tana sanye da jeans da t-shirt kanta sanye da hula da bayanta ya d’an yi tudu alamar gashin ta a fake yake, itama Sadeeyar a shekaru zata yi shekara 25 zuwa 26 itace k’anwar Khalid ta biyu, ta farkon wato Yayar Sadeeyar tayi Aure, a ABU Zaria Sadeeya ke karatu itama fara ce saidae bata kai Khalid haske ba sannan ita da Chairman take kama duk da ta wani 6angaren ta d’an yi yanayi da Khalid d’in tana da d’an jiki ba kamar khalid ba, sanye take da doguwar rigar atampa d’inkin Abuja Boubou ta kashe daurin kallabi hakan ya bayyanar da wutsiyoyin kitson dake kanta da ta tubke, da fara’a lokacin da yadikko ta fito ta sanar mata Fatun na fitowa tana k’arasa shiryawa ne itama tana fara’ar tace Ok ba damuwa, ruwa da Abinci yadikko ta kawo masu Sadeeyar na cikin shan ruwan Fatuu ta fito ba shiri ta cire cup din daga bakinta ta bi ta da kallo wanda ke bayyanar da mamaki akan fuskarta, sam bata taba tsammani ganin ta hakan ba duk da ta samu labarin ba anan take ba batai tunanin ganinta a waye haka ba ba kuma kaman da taji Secondary graduate ce, kujerar dake gefen su Fatuu ta nufa ta zauna fuska a d’an sake ta gaishe da Sadeeyar da sauri tace “Ah Auntyn mu ni ai yakamata in yi wannan” tay Maganar tana ma Fatuu dariya ita dae d’an murmushi kawae tay kafin tace sun zo lafiya Sadeeya ta amsa mata da lafiya lau, shiru sukae Fatuu ta lura da kallon da take mata hakan yasa ta d’an juyar da kanta gefe, can Sadeeyar tace “Auntynah if u done we can go driver is waiting for us outside” juyowa Fatuu tay ta kalleta sai kuma ta kalli Abincin gaban su a nutse tace “But u aven’t ate d Food” d’an lumshe ido Sadeeya tay kafin tace “bamu jin yunwa ne amman tunda kin yi Magana bari mu d’an ci” tana niyyar tashi don ta zuba masu Sadeeyar tace mata ta bashshi bari ta zuba masu yarinyar da suka zo tare sai kallon Fatun take can ta d’an duk’a saitin fuskar Sadeeya tace “Aunty Sady who is she?” d’agowa tay tana yar dariya tace “she’s ur New Aunty Ya Khalid’s bride” waro ido yarinyar tay Sadyn tace taje ta gaida ta ta nufi Fatun tana zuwa ta tsaya gabanta ta gaishe ta da turanci Fatun ta amsa mata ta tambayi sunanta tace mata Basma, ba wani mai yawa Sady ta ci ba ita basma ma bata ci ba suka tashi don tafiya Yadikko tace ma Fatuu ta biya dasu su gaisa da Yaya ba don ta so ba ta amsa mata da to kawae itama Yadikkon gudun tsegumi yasa tace su je don zai iya zama abun Magana, kaman ko yaushe tana zaune da yan taya ta gulma su ukku lokacin da suka shiga cikin d’akin Yaya na d’aura idonta kan Sadeeya ta gane yar gidan Chairman ce hakan yasa ta nuna mata gefen gado tace ta zo ta zauna ita dae Fatuu tsaye tay Sadeeya ta shiga gaishe dasu da fara’a suka amsa suna ma Basma wasa, Yaya ce ta tambayi Sadeeya daga gidan Chairman ko tace mata eh sun zo zasu tafi da Amarya ne za’ai mata awon d’inki ta jinjina kai alamar gamsuwa daga baya ta mik’e tay masu sallama suka fita ba tare da Fatuu tace ma kowa komai ba, bayan fitar su Yaya ta ta6e baki had’i da yamutsa fuska cikin harshen fulatanci tace “Yi ma yarinyar can aure ba k’aramin rufa mata Asiri akai ba don Allah kadae yasan abunda take aikatawa a can, kuji irin yadda take saka sutura kai kace itace d’iyar Chairman d’in ma a ina ita kakar ta ta taga kud’in da zata rinka d’inka mata suturun da da gani masu tsada ne” Hasiya ta kar6e “ai fa dama da gani idonta a bud’e yake wllh” Yayar tace “kin ga an za6a mata miji daidai da ita kenan” haka suka cigaba da yi ma Fatun kazafi, suna fita kopar gida Driver ya fito ya bud’e ma Fatuu kopa bayan ya gaidata ta amsa mashi a sake Sadeeya ta zagaya d’ayar kopar ta shiga Basma kuma ta shige gaba, Tafiyar kamar Minti 35 ta kawo su a bakin k’aton gate d’in gidan Driver yay horn mai gadi ya lek’o kafin ya koma ya bud’e masu ya shigar da Motar, bayan sun fito da murmushi Sadeeya tay ma Fatuu jagora zuwa cikin gidan lokacin da suka shiga Main Parlor d’in gidan ba kowa hakan yasa tace ma Fatuu su je cika ta nufi wata babbar kopa suna shiga wani madaidaicin Parlor ne da bai kai na farkon ba, zaune akan sofa 3 seater Hajiya Rabi’atu ce jikinta sanye da doguwar rigar Atamfa a gefenta kuma wata mata ce itama tana sanye da doguwar rigar shadda kafad’arta d’aya rataye da gyale da gani bak’uwa ce tayi, suna shigowa duk suka kalle su da sauri Sadeeya ta d’aga gyale ta rufe saitin Fatuu tana dariya tace “Mom sai kin biya zaki ga face en bride d’in mu” tana rufe baki Basma ta ruga ta fad’a saman jikin Mom d’in nasu tana dariya tace “Mom she’s very beautiful” d’an buda ido Mom d’in nasu tayi sai kuma ta d’aga basmar ta mik’e tana dariya ta nufi Sadeeya tana zuwa tasa hannu ta d’an tureta gefe tana fad’in sai ta ja mata rai zata bari taga Daughter d’in ta gaba d’aya harda k’awar tata sukae dariya, had’a ido sukai da Fatuu bayan ta janye Sadeeyar ta bi ta da kallo hakan yasa Fatuu ta sadda kan ta k’asa, tana sakin kayataccen murmushi tace “U’r highly welcome My Beautiful Daughter nayi matuk’ar farin cikin ganin ki” a hankali Fatuu ta d’ago ta kalleta a sanyaye ta gaishe da ita tana ta fara’a tace su je ta zauna sai su gaisa sosae tay patting shoulder d’inta suka wuce, kan one seater ta Zaunar da ita kafin ta koma inda ta taso itama ta zauna k’awar tata tace “in ce Amaryar Khalid d’in ce” ta amsa mata da itace tace “Ma sha Allah kyakkyawa da ita Allah yasa Alkhairi ya kaimu Ranar” duk suka amsa da Amin idon Momy akanta tana ta mata murmushi ita dae Fatuu sai faman sussunar da kai k’asa take, “Daughter fatan an zo lafiya” ta tambayi Fatun a hankali tace mata lpy lau ta k’ara cewa “Ya Grandma d’in taki ance a wurinta kike zaune” wani iri Fatuu taji jin an ambaci gwaggo kafin ta d’an kalleta tace tana lafiya, “Ya karatun ki ai kin gama ko” kai Fatuu ta d’aga tace eh,

 

“Mom ya kika ga Amaryar Ya Khalid?” Sadeeya ta tambaya Yar dariya tay ta furta “Tubarkallah Daughter d’in nawa, sai fatan Allah ya kaimu ya basu zaman lafiya da fahimtar juna” duk aka amsa da Amin, kallon Sady tay tace taje tasa a shirya table ta amsa da Owk ta mik’e ta fita suka cigaba da hira da bak’uwar tata sai dae akai akai take juyawa ta kalli Fatun da murmushi wani lokacin su had’a ido, bayan Sady ta dawo ta sanar da Momy an shirya tace to suje da ita taci Abinci Fatuu tace ta k’oshi amman tace dole ta ci ai nan gidan su ne yanzu ta mik’e suka fita da Sadeeya, bayan fitar su k’awar tata ta kalleta tace “a ina take ne?” Momy ta bata amsa da a Kt take zaune tace “University ta gama ne naji kina ta gama karatu?” d’an girgiza kai tay tace “No, I mean Secondary school” jinjina kai tay tace “yanzu nan Secondary graduate ce haka wayayya da ita kai kace yar Jami’a ce” Momy ta amshe “Wllh Hajiya Safeena nima cikin raina saida nayi mamakin ganin ta haka don I never thought zan ganta haka duk da nasan ba a k’auyen take ba har na fara tunanin akwae abubuwan da yakamata a k’ara zubawa acikin lefenta” Dariya Hajiya Safeena tasa tace “to da ba’a sa na kirki bane komi?” Itama Momy dariyar take tace”Ah ba laifi an sa kaya masu kyau to saidae ganin dressing d’in jikinta yanzu gaskiya we need to add wasu kayan taje tay ta d’aukar wanka tana kashe mijinta da gayu” gaba d’aya sukae dariya ta k’ara cewa “Yarinyar ta burge ni sosae wllh yanzu na fahimci dalilin da yasa Yalla6ai shima ta kwanta mashi a rai har yay sha’awar had’a auren na su gashi yace tana da kokari sosae” cigaba da yabon Fatun sukae daga baya Hajiya Safeena ta tafi, sai da akai la’asar sannan Driver ya sake d’aukar su ya tafi dasu shagon d’inkin bayan sun gama komae duk a tunanin Fatuu za’a wuce da ita gida ne amman sai suka koma gidansu Sadeeyar lokacin Magrib ta gabato, bayan sunyi salla gaba d’aya a Main Parlor suka zauna Sadeeya da Basma wadda itace auta sai Haidar wanda Basma ke bi mawa, Fatuu duk ta k’agara ta bar gidan suna zaune Momy ta fito da murmushi ta zauna tana facing Fatuu tace “Daughter kin k’i sakin jiki dae kuma nan d’in gidan ku ne so just feel at home” d’an murmushi kawae tay bata ce komae ba suna haka sai ga Khalid ya shigo da yar guntuwar sallama, damm kirjin Fatuu ya buga da suka had’a ido da sauri ta sunkuyar da kanta k’asa yana sanye da Jeans da T-shirt kujerar da Fatun ke zaune ya nufa ya zauna kan hannun kujerar yana bin ta da kallo a hankali ta d’ago ta kalle shi suka had’a ido ta gaida shi yana sakin murmushi ya amsa mata ta maida kan k’asa suma su Momyn duk murmushin suke sosae taji dad’in yadda Khalid d’in ya nuna ta yi mashi tun jiya da ya dawo shima Chairman yaji dad’in hakan don suna tare bayan ya dawon ya fad’a masu, kallon Momyn tashi yay yace “Mom how do you see My Wife?” Yar dariya tay tace “the Match was absolutely perfect” hannu ya kai ya shafi Beard d’insa yana cigaba da yin murmushi ya k’ara juyawa ya kalli Fatuu ganin kaman bata saki jiki ba ya kalli Mom d’in nashi yace sun ma yi fira kuwa tana murmushi tace “ai ta k’i sakin jiki tana ta bak’unta” d’an ta6e baki yay yace “kuma tana Magana Kaman parrot fa” da sauri Fatuu ta d’ago kai ta kalleshi ya d’age mata gira Momy tace “Ashe mu ne ba’a son yin firan da mu” Khalid yace “No nima bata saki jiki da ni ba jiyan ina Maganar can baya ne” da d’an alamun mamaki Momy tace “Kenan dama ka santa” yace “Yes we once met a rugan su” kallon shi kawae Fatuu ke yi tana zare ido gabanta na fad’uwa tsoron ta kar ya ce ta zage ta ya lura da yadda ta d’an razana hakan yasa Ya rink’a sakin wani shu’umin murmushi sai dae bai k’ara cewa komae ba can ya kalli Sady yace “Ya preparation na biki, ita tace bazata yi komae ba cos bata da Friends anan” da sauri Sady tace “dat’s not a problem ai tunda akwae Family and Friends d’in mu” tambayarta yay mi zasu yi tace zasu yi Kamu da Bridal shower Momy ma zata yi Walima yace lafiya lou duk abunda ake buk’ata tay mashi Magana tana murmushi tace “Ok bro” kokarin tashi ya fara yi Momy ta tambayi inda zashi yace zai je sallar Isha ne tace to in ya gama yazo sai ya maida ta tana jira su gaisa da Daddyn su ne shiyasa bata sa an maidata ba yace ai yayi zaton zata kwana ne har saida Fatuu tay mashi wani kallo Momy na dariya tace so yake a biyo sawunta tunda ba’a ce zata kwana ba, Bayan gama sallar Isha d’in Chairman ya dawo Momy ta kai Fatun falon shi don su gaisa cike da farin ciki ya amsa gaisuwarta yay mata an zo lafiya, tana a falon Khalid ya dawo ya zauna nan Daddyn ya yi masu nasiha ya nuna yaji dad’in yadda suka kar6i juna had’i da yi masu Addu’oi ita dae Fatuu kanta na a k’asa ta rasa mi yake mata dad’i komai ganin shi take tamkar mafarki ba gaske ba, bayan ya gama Momy tace ma Khalid suje dare na k’ara yi yace Ok had’i da mik’ewa Dad d’in nace mashi ya kula sosae yana dariya ya d’aga mashi hannu alamar Ok, tare da Momy dasu Sadeeya aka rakota harda ledar turarurruka dasu Humra aka bata tay godiya, ji take kaman tace bata son ya kai ta saidae ba yadda ta iya haka ta bud’e front seat ta shiga Sady ta rufe mata kopar tana ce mata sai tazo kaita gyaran jiki suna daga mata hannu ya ja Motar suka tafi……………….

.

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button