Hausa novels

Karfe A Wuta Chapter 12 By Ayshercool

Yau ma ba ta sake zani ba, a yanayin da Walid ya iske Viper, ya sha duk abun da yake tunanin zai sha, ya bugu yayi bacci, amma jikinsa ya mutu murus, ya kasa baccin.Idanunsa sun yi jawur, tamkar ana iza wuta, jijiyoyin kansa sun kumbura, sai buɗe idonsa yake yi yana lumshewa.Walid ya kalli ɗan mama ya ce “Ɗan mama kai ka ke kawo masa kayan nan ko?””Wallahi bani bane ba, da kansa ya fita ya samo abun sa, ban kawo masa komai ba”.Ya mayar da idonsa kan Viper ya ce “Ka na ji na?” Ya ɗaga kai ya kalli Walid alamar eh.”Wai ba zaka daina fita ba, sai wani abu ya faru tukuna, ka sake sakamu a matsala?”Viper ya kalli walid, amma yayi masa shiru.Shikenan, ina son zamu fita da kai, zan nuna maka wani abu mai ban mamaki”Viper ya ce “Walid” ya kira sunansa da dakakkiyar muryarsa.Ya amsa da boss “Boss””Meyasa ba ka da zuciya ne?” Yayi maganar cikin maye.”Na ce bana son sake ganinka”Walid ya ce “Saboda duk sheɗancina, ɗan halak ne ni. Ya zaka bi ni mu je?””Ba zani ba””Yakamata ka fara sanin dalilin da ya sa yarinyar nan ta matsa a kan lallai sai ta haɗu da kai, ina…..Cikin hargowa ya ce “Wai wace irin yarinya ce? Meye haɗina da ita? Wacece ita me take nema a wurina?” yadda ya firgice sai da Walid ya matsa baya da sauri.Ya cigaba da cewa “Kowacece, a kawar da ita, bani da alaƙa ta kusa ko ta nesa da kowace mace, kar ka kuskura kar kuma ka fara, idan ba haka ba duk abun da ya biyo baya kai ne sila”Walid ya ce “Na ji na fahimta, easy ka yi haƙuri”.Ya ja tsaki, ya yinƙura dan ya tashi da niyyar ya fita, amma jiri ya ɗebe shi yayi baya, cikin zafin nama walid ya riƙe shi, ɗan mama ya taimaka masa, suka kwantar da shi.Ɗan mama ya ce “Da gaske ka ke wai sai ka haɗa shi da yarinyar? Kuma akwai alaƙar tsakaninsa da ita?”.Walida ya ce “Shi nake son tabattarwa”.”To ya ce baya so, amma kai ba ka tunanin ko ƙarya take yi?”Walid ya ce “Ƙaryar ma take yi, amma yakamata su haɗu”Ɗan mama ya sake cewa “Sai ka haɗa sun kenan, idan ya illata ta fa?”Walid ya ɗora yatsansa a kan leɓensa alamar yayi shiru, dan ya san Viper idonsa biyu kuma yana jin sa.***A office ɗin su Nasir kuwa, hira ta yi hira, ake gaya wa Nasir, wani ɗan majalisa ne, yayi belin yaran madaki da aka kama, ya saka aka sake su.Cikin takaici ya ce “Allah wadaran naka ya lalace, muna tufka suna warwarewa, mun zama tamkar bayinsu, kullum cikin ganin gazawarmu ake, alhalin muna iya ƙoƙarinmu”Suka cigaba da tattaunawa, a kan yadda manyansu kan yi musu karan tsaye, a kan harkar aiki, da hana ruwa gudu.Ramma ce take ta murƙususun ciwon ciki, hankalin mahaifiyar ta a tashe, take ta ba ta jiƙe-jiƙen magunguna, da ta zuƙa kaɗan sai amai, ba ta iya cin abinci ga wani irin zazzafan zazzaɓi da yake damunta.Kullum ta na ɗaki, ko tsakar gida idan ba dole ba, bata fita, saboda yadda labarin cikin nan ya watsu ya cika garin su, dama ta san isa sai ya bayar da labari, tun da ɗan cikin garinsu ne, ku ma shi ne ya tabattar da akwai cikin.Cikin matsananciyar damuwa ta dubi ramma ta ce “Sannu ramma, na baiwa sani kuɗi ya sayo miki maganin zazzaɓi, kin ga haryanzu babu shi shiru bai dawo ba”.Cikin kuka ta ce “Mama mutuwa zan yi”.”Ki yi haƙuri ramma, ba zaki mutu ba, kina karya mini gwiwa, ki daure. Amma anya ba zamu yadda a cire cikin nan ba? saboda rufin asirinmu, kuma kema ki huta”Cikin sauri ta girgiza kai ta ce “Mama tsoro nake ji”Rasa abun yi ya sanya maman ramma, sakata a gaba suka cigaba da kuka tare, a zuciyarta ta din ga ja wa Abdul duk wani nau’i na masifa da jafa’i.Yau sumayya za ta je program gidan honorable Indabo, maimakon ta kasance cikin farin ciki, a dalilin zata shiga gidan babban mutum kamar sa, amma ta gaza nutsuwa da yin farinciki a kan hakan, sai wata irin fargaba da faɗuwar gaba da take fama da ita.Sai da ta fara shiga wurin aiki, ta gabatar da ayyukanta na ranar, sannan ta fara harhaɗa kayan aikin da za ta yi amfani da su.Gaba ɗaya jikinta babu ƙwari, sai tsananin tsoro da fargaba.Murtala ne yake ta kwantar mata da hankali, tare da nuna mata, hakan ma wani cigaba ne, ta sani ko daga program ɗin su daidaita da honorable ɗin.Jin sa kawai take yi, tare da murmushin yaƙe.Har bakin motar gidan radiyon da za a kai ta a ciki, yana ƙarfafa mata gwiwa, “Sumayya, abun da zan gaya miki shi ne, ki san iyakar ki a kan program ɗin nan, iya tambayoyin da aka rubuta miki, ki yi masa su zaki yi masa, kar ki ƙetare su ki jawo wa kanki matsala, ƴan siyasar nan ba kowa ne mai imani a cikin su ba””In sha Allah uncle murtala zan kiyaye, na gode sosai”Ta shiga motar ta zauna, direban ya ja suka tafi.Nabila kuwa tana office tare da barrister Habib, dan yanzu ya saukko ya fara yaba mata, tana ƙoƙari, ya fuskanci kawai shiririta ce take damunta a kan aikin, da rashin mayar da hankali.Tana yi tana kallon agogo, kar ta saɓa lokacin da a ka bata.”Barrister” ta kira shi, ya ɗago yana sauraren ta.”Ban sani ba ko kana jin radiyo”Ya ce “Ina ji mana, meyafaru?””Cases da dama, idan suka faru mussaman na masu ƙaramin ƙarfi, sai in ga barrister bunkure ta tsayawa mutane, wai ita ba dan kuɗi take aikin ba, dan barrister ce da ba kowa yake iya ɗauka ba, amma tana tsayawa marasa ƙarfi, ko kuɗi ne suka yi mata yawa?”Barrister Habib ya girgiza kai ya ce “Ke dai kawai ayi sha’ani””Ka san wani abu kuwa? Akwai wani case da wata mata, ta je gidan radiyon su sumayya, ta kai koken an yi wa ƴar ta fyaɗe, an dawo mata da ita daga gidan aiki, ta je gidan da yarinyar take aiki, an hana su shiga, ta kai wurin ƴan sanda, amma ana ta yi mata yawo da hankali, wai yaron ɗan manya ne. To na ji an ce ta shiga case ɗin, amma haryanzu babu wani update, ka san da na so na jarraba sa’a ta, nima na shiga case ɗin ayi da ni, na tausayawa matar da yarinyar, amma na san ana babbakar giwa, wa zai ji ƙaurin zomo, na san ba za ta saurare ni ba ma”.Barrister Habib ya tattara hankalinsa a kan Nabila ya ce “Nabila””Na’am””Just be yourself, ke dai ki kalli mutum a riga kawai, Naja’atu kura ce da fatar akuya, ba wata abar burgewa ba ce, da zaka yi koyi da ita ba. Yarinyar ƴan siyasa ce, babu wani taimakawa masu ƙaramin ƙarfi, ta fake da wannan ne, dan sunanta ya ƙara fitowa, kuma ya rinjayi ɓarnar da take aikatawa, ai mun yi karatu da ita tare, ƙwalluwar shegiya ce, ke abun bai baki mamaki ba, ace kowace shari’a idan ta tsaya maka, zaka yi nasara, ace komai kai ka ke nasara akwai ayar tambaya ai, dan haka ki yi ta kanki kawai.Duk da mu ma ɗin wasu lokutan, muna take gaskiya, amma yanayin aiki ne ya zo da haka, kuma nata ya ƙazanta”.Nabila ta yi ajiyar zuciya ta ce “Biri yayi kama da mutum”Nabila a zuciyarta ta ce “Idan haka ne, ba gaba da gaba yakamata na yi da ke ba, tona miki asiri zan yi”Habib ya ce “Ya dai?””Nothing sir, jikina ne yayi sanyi kawai na gode sosai da bayaninka”Ba tare da neman iznin kowa ba, ta ɗauki jakarta ta fita.A in da ta tsaya shekaranjiya, nan ta je ta sake tsayawa, tana fatan Allah ya sa ba jirgata za su yi ba.Ta shafe a ƙalla awa guda a wurin, har ta sare zata tafi, matashin da ya kai mata waya, liti yayi mata magana da ita, ta gani a gabanta.Bai ce mata uffan ba, ya miƙa mata wata takarda.Sunan wata unguwa ne a jiki,da dai-dai wurin da zata je ta tsaya, saboda tsabar wauta da rashin hankali, ta yi masa godiya ta tari abun hawa ta nuna masa takardar.Mai baburin ya gaya mata kuɗinsa, babu neman ragi, ta afka ciki ta ce su tafi.Lissafin da take ma a zuciyarta, na mamakin yadda Naja’atu tayi mata kallon ƙasƙanci ne, ta wulaƙanta ta alhalin ma ba wata mutuniyar arziki ba ce.Babban abun da ta fuskanta, ƙasar nan ba zaka taɓa samun wasu damarmaki ba, har sai ka taka wani babban matsayi na musamman, ka shahara sai dai hanyoyin bi a shahara ɗin ne, ko da kasada ko ka kauce hanya.Ta yi wa kanta alƙawarin, dole za ta bibiyi case ɗin yarinyar nan, ba naja’atu ba, ko a hannun ƙaramar hukumar bunkuren case ɗin yake, sai ta bibiya, ai da ƙananan kasada ake babba, ga kuma babban target ɗin ta, Viper, ta san idan aka kama shi, dole a sara mata, ta shiga cikin mata da suka kafa tarihi.Da wannan gurguntaccen tunani na Nabila, mai cike da wauta da rashin lissafi, suka cigaba da tafiya can ta ce “Malam, wai haryanzu ba a zo ba?””Ba ki taɓa zuwa unguwar ba ne?”Ta ce “Eh, sai yau zan fara”Ya ce “saura kaɗan in sha Allah”Sai dai gabanta ya fara faɗuwa, tun bayan da ta ga sun bar cikin mutane, sun fita wajen gari. Dai-dai wani gidan gona ya ajiyeta, wurin duk shuke-shuke, da alama akwai mutane a daf da wurin, amma sai an yi tafiya kan a tarar da in da suke. Shi kansa titin wurin, babu ababen hawa da suke kaiwa suna komowa a wurin.Sai rukunin manya manyan kamfanunnuka a wurin, na shinkafa da na taki, wurin shiru sai ƙarar injinan da masana’antun ke amfani da su.Sai da ta sallami mai a daidaita sahun, sannan ta fara tunanin, to ina ma za ta nufa?Tsayawa ta yi, tana waige-waige, kawai ta hango wani mutum ya tunkarota, nan ta fara ja da baya, tana tunanin ko zurawa za ta yi da gudu.”Mu je” ya ce mata a kausashe.Ta turje ta ce “Ina?””Ba ke ce baƙuwar Viper ba, mu je”A raunane cike da tsoro ta ce “A’a, ka kirawo shi mu yi magana a nan, ni dama kaya nake son saya a wurinsa”Cikin mamaki ya kalleta ya ce “Wani irin kaya?””Wanda yake sayarwa” tayi maganar a tsorace tana kallon Walid.Ya gyaɗa kai ya ce “Baki san waye shi ba amma? Kin yi kasada nafi muni, wuce muje kafin na saraki biyu a wurin nan”Cikin rawar jiki ta ce “Dan Allah ka yi mini rai, ni ka kirawo shi nan kawai”.”Wallahi zan saɓa ki a ka, wuce mu je”Salati Nabila ta din ga yi, dan tun da ta yo dakon kasadar nan, sai yanzu ta ga zunzurutun wautar da ta aikata.Ya sakata a gaba, suka nausa bayan kamfanunukan.A can gidan honorable kuwa, yana da office a cikin gidan sa, in da yake ganawa da mutane na mussaman.Hankalin sumayya ya ɗan kwanta, bayan da ta ga mutane na shiga suna fita a gidan, da alama ba shikaɗai ne a gidan ba, kuma gidansa ne da yake zaune da iyalinsa.A harabar gidan aka dakatar da wanda suka rako sumayya, aka ce itakaɗai za ta shiga.Wani security yayi mata jagora, zuwa wani sashe na gidan, ya kaita wani falo, ya ce ta jira a nan, ta samu wuri ta zauna, a kan kujera, tana zaune a falon office ɗin, tana ɗan kalle-kalle, tana jira kamar yadda aka umarceta.Cikin office ɗin kuma, Barrister Naja’atu ce suke magana da honorable.”Ni fa na yi iya ƙoƙarina, amma da alama mutanen nan, su na da taurin kai, juyin duniya sun ƙi saduda, sai iƙrarin a karɓar musu hakkinsu suke yi, ina ga kawai a ɗauki matakin da ya dace a kan ta”.Indabo ya ce “Lallai dama haryanzu akwai masu ƙi faɗi a talakawa?””Akwai su fa, ku kuna gefe, mune muke shiga cikinsu da rufe bakunanansu a kan ɓarnar da ku ke aikatawa, sai dai kan mage ya fara wayewa, babban abun damuwar sun gaya mini an tabattar musu tana da ciki”Yayi saurin ɗaga kai ya kalleta “Ciki kuma? Sau nawa yayi mata fyaɗen ne?”Ta ɗage kafaɗa ta ce “Wannan kuma shi za ka tambaya, ba zan iya cigaba da ɓata lokacina a kan wannan kucakan mutanen ba, ina da abubuwa masu muhimmanci kawai ayi abun da ya dace”.Yayi ajiyar zuciya ya ce “Abdul, ban san lokacin da zai yi hankali ba, ina tsoron lokacin zaɓe, a samu wani ya fito da miyagun halayensa, in the next couple of years, sonake ya samu ref, ko deputy governor a tsayar da shi takara, saboda yarjejeniyar da muka yi, da jam’iyya kenan kafin na yarda na zauna a cikinta, amma al’amarin sa kullum ƙara lalacewa yake yi”Barrister Naja’atu ta ce “To, gara dai ka san abun yi””Anyway, shikenan, ki tura mini address ɗin su ita yarinyar, za ayi abun da aka saba” ta miƙe tsaye ta ce “No problem”Ta buɗe ƙofar office ɗin ta fito, kallo ɗaya sumayya ta yi mata, ta gane ta, saboda yadda Nabila take ɗora hotonta a status ɗin ta a baya.Cikin son tabattar da abun da Nabila ta gaya mata, a kanta, ya sanya  ta tashi da sauri tana murmushi ta ce “Barrister Naja’atu Bunkure, baya goya marayu, dama zan ganki ido da ido?” Sumayya ta yi maganar tana murmushi.Kamar ta ga kashi, ta yatsuna fuska ta ce “Sannu”.Sumayya ta maze ta ce “Na tsinci dami a kala yau, ni ƴar jarida ce, a cikin ayyukan da ki ke gudanarwa, zan so yi miki tambaya ɗaya zuwa biyu, na san masu sauraronmu, za su ji daɗin hakan, kasancewar ki abar so da koyi ga al’ummar mu, mussaman mata. Dan akwai sister na, die hard fan ɗin ki ce, ita ma lawyer ce.Cikin fusata Naja’atu ta ce “Ke saurara mana, daga ganina sai tsare ni ki hau zuba dan kina ƴar jarida, who permits you to do that?”Sumayya ta dake ta ce “No, barrister, ba as ƴar jarida ba kawai, as a woman and one of your fans, ko ƙorafi ne da ni, ta yaya zan same ki ki tsaya mini, atleast ko mintuna uku ki bani mana, dan Allah. Na san ƴan jarida wasu lokutan mu na da zaƙewa amma a duba roƙona” kamar ta zagi Sumayya, ta tsani baƙin naci irin na ƴan jarida, amma sanin halin su na yanzu sai su samu abun ɗorarwa ta ɓata mata career ya sanya ta danne ta ce “Ina jin ki”Fitowar honorable, ta sanya ta yin shiru, ya kalli sumayya ya ce “Mu je in da zaki ɗauki program ɗin”Tana ji tana gani, Naja’atu ta tafi.Can wani surƙuƙi ya ja ta, da sai da ta fara jin tsoro, sai dai duk in da suka ratsa, akwai ma’aikata.Sumayya ta sha mamakin, irin dukiyar da aka yi ɓarna, wurin gida wannan gida da kamar ba za a mutu a bar shi ba.Daga ita sai shi a ƙaton falon, mai ɗauke da ɓangarori daban-daban.Yayi mata iznin zama, yana ƙureta da idonsa, ta fito da kayan aikinta, ta fara saitawa, tana ta addu’a a zuciyarta, dan kaɗaicewar nan ta su kawai, hankalinta a tashe yake.Nabila kuwa, Walid sakata yayi a gaba, har suka zo ƙofar wani gida, a can bayan kamfanunukan nan, babu kowa a wurin, ba gida gaba babu a baya, sai ma wani uban dutse idan ka yi tafiya can gaban gidan, ba ta taɓa zaton akwai irin wannan wurin a kano ba.Ya kalleta ya ce ta shiga.Jikinta yana rawa ta ce ba zata shiga ba, sai dai ya kira wo mata shi nan waje, wanda har a lokacin idan ta ganshin, ba ta san me za ta ce masa ba, tsabar fitina ce da son ta ɗaukaka ko ta halin ƙaƙa ya sanya take wautar.Wani makami ya zare mata, mai kama da kibiya ya buga mata tsawa ya ce “Ki shiga na ce” sai a lokacin ta tabattar da ta tafka babban kuskure, haɗi da wauta mara amfani, idan suka illata ni fa?” Ta tambayi kanta cikin tashin hankali, haka ta shiga, yana bin ta da wuƙa.Ɗan mama yana ɗan matsakaicin tsakar gidan, yana wankin kayansu, jin kukan mace ya sanya shi ɗaga ido, cikin tsananin mamaki.Sai dai yayi wata irin zabura ya ja da baya, yana bin su da kallo.Yana cikin ɗaki a tsaye ƙyam, kamar an gina shi, ya bawa ƙofar baya, yana kallon bango. Ya sha ya bugu, amma bai samu yadda yake so ba, tunanin da yake son dainawa ya kasa, dan haka yana tsaye, yana ta nazarin abubuwa daban-daban a cikin ransa.Ɗan mama biyo su yayi, yana bin Nabila da kallo.Turus Nabila ta yi, duk da ba ta ga fuskarsa ba, amma yanayin suffar jikinsa, sai da ta ji tamkar ta zunduma ihu, kallo ɗaya zaka yi masa ka san madakin maza ne, ingarman namiji ne, da Allah ya yi shi da tsawo da kuma kakkauran jiki.Idonta ya sauka a kan miyagun makaman da suke ɗakin, kamar za aje yaƙin duniya, gefen katifar da take ɗakin kuma, sirinjai ne, da kwalaban allura a wurin, sai kuma satchets na magunguna da kwalabe da kwalayen sigari. Ban da warin sigari, da wani irin ƙauri da ba ta gama tantance ko na menene ba, babu abun da yake tashi.Tirƙashi! Ai ko lokacin da aka rufta ta, aka turata dabar madaki, ba ta ga abun da ya razanata ba, kamar yanzu ba, dan tarin ƴan dabar da ta tarar na su wasa ne, ba su firgita ta ba, tun da ta samu ƙwarin gwiwar yi musu magana.”Boss, ga ta na kawo maka ita, sai ka ji dalilin da ya sa take nemanka”Babban abun da ya ƙular da Viper, bai wuce watsi da umarninsa, da Walid yayi ba, tun da fari ya gargaɗe shi, a kan kawo masa wata mace, dan ba shi da alaƙa da su, amma ya yi burus da maganar sa.Kasancewar ya sha sai dai buguwar ta gagara yadda yake so, ya sanya ƙwayoyin suka taimaka wurin tunzura shi, ya waiwayo a fusace domin ya sauke wa Walid rashin mutunci.Sai dai gabansa yayi wata irin mummunar faɗuwa, adadin bugun zuciyar sa ya ƙaru da sauri da sauri, wani irin gumi ya fara tsatstsafowa ta kafafen gashin sa, jijiyoyin jikinsa suka kukkumbura.Shi dai ya san a farke yake, ba iya bacci yake mai nauyin da zai ɗauke shi, har ya sa shi mafarki yake, balle ya ce mafarki ne, kuma ya san a hayyacinsa yake, domin kuwa bai yi buguwar da hankalinsa zai gushe ba.Sai dai a zahiri, sam yanayin sa bai nuna irin halin da ya shiga ba, dan babu abun da ya canza a tattare da shi, ya zuba mata manya-manyan jajayen idanunsa.Tirƙashi! Jin ka ya fi ganinka! Nabila za ta iya cewa, tun da Allah ya sa ta buɗi ido a duniya, ba ta taɓa ganin mutum mai kwarjini da razanarwa kamarsa ba, kodayake ai ya wuce ta kira shi kwarjini, sai dai mai ban tsoro.Yadda ake faɗarsa a baki kawai, ta ɗauka wani ƙaramin alhaki ne kawai, sai dai yanzu ta tabattar da  ya wuce duk yadda ta yi tsammanin ganinsa sa.Ashe waɗanda take gani ƙaryar daba suke yi, ga ɗan daba na gaske yau ta gani,kamar ta fashe da kuka a cikin zuciyarta ta ce “Na shiga uku, wani tsautsayin ne ya kawo ni? Daga ni sai su idan suka kashe ni fa? Na san ko gawata ba za a gani ba, balle ayi mini salla, kamar yadda addini ya tanada”So take ta ɗaga ido ta kalle shi, amma abu ya gagara, saboda daga kallo ɗayan da ta yi masa, ba ta fatan sake yi masa na biyu, duk da zuciyarta na azalzalar ta, ta sake yin hakan, ba zata iya tantance abun da take gani a cikin idanuwanta ba, da kuma ma’anar irin kallon da yake yi mata ba.Ƙoƙarin sake satar kallonsa tayi, amma suka yi ido huɗu, tayi saurin sunkuyar da kanta ƙasa, saboda mummunar faɗuwar gaban da ta ziyarci zuciyarta, tabbas cikakken mashayi ne duba da yadda launin idanunsa suke, sai dai Allah ya yi shi da siffar girma da cikar zati, ya isa a kira shi da cikakken namiji.”Shi kuwa wannan meya haɗa shi da aikin daba, a irin ƙira da Allah ya yi masa, da aikin office ya dace, ko na tsaro, ya ɓata wayonsa, da ya ƙare a shaye-shaye da daba.Duk da ta sunkuyar da kanta, a tsakiyar ƙirjinta take jin kallon da yake yi mata.Walid ya zagaya saitin kunnensa ya ce “Ka ga abun da nake gaya maka?”Jinjina masa kai kawai yayi, taku ɗaya yayi, ba tare da Nabila ta ankara ba ya danƙi wuyanta.Ba wani riƙon kirki yayi mata ba, amma idanuwanta suka yo waje, jikinta ya hau kyarma, tamkar ana kaɗa mata gangi.Ta saka hannunta ta riƙe nasa, numfashinta na fita da sauri da sauri, cike da tsoro take ta gwagwarmayar ƙwatar numfashinta, saboda yadda take jin yana barazanar barin ƙirjinta.Ba ta ƙara tsinkewa da lamarin ba, sai da ta ji tsini a cikinta, ga wani irin azababben zafi da ya ratsa fatar cikinta.Ba ta san bata tsorata ba, sai da ya buɗe baki yayi magana.”Wacece ke? Me ki ke nema a wurina?!!”Numfashinsa ya sauka a fuskarta, warin sigari ya daki hancinta, jikinta ya hau tsuma.A rikice Walid ya ce “Boss zaka kashe ta fa, ka kalli abun da ka ke yi”Bai saurari walid ba, ya sake buga mata tsawa, tare da ƙara nutsa wuƙar da ya saita a cikinta.”Viper, jini ya fara zuba daga cikinta, ka dawo hayyacinka mana” yayi maganar yana ƙoƙarin kai hannu ya ƙwace wuƙar hannunsa.Idan ka taɓa ni, kai zan cakawa!” Yayi maganar yana kallon idon Nabila da suka yo waje, ga jikinta ya saki, sai numfashi da take yi da kyar.Buɗe baki tayi, da niyyar ta yi magana, amma jikinta ya saki, ta daina ganin komai sai duhu.”Viper kar ka kashe yarinyar nan” Amma kan walid ya yi wani yinƙuri, Viper ya watsar da ita a wurin, ta faɗi sumammiya.

Ayshercool

08081012143

Back to top button