Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 22 Complete Novel

*ASM Bk2022*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
…….wayar Abbas dake gefenshi ta fara ringing ya kai idonshi kan screen d’in yana ganin mai kiran ya dakata yana murmushi ya kai hannu yay picking kafin ya karata a kunnanshi yace “Latest Ango Mutanen US…..” Jin hakan yasa Fatuu ta kalleshi da sauri yaci gaba da fad’in “Mutanen Waje ya gajiyan hidima da tafiya” Haisam d’in ya amsa mashi da Alhamdulillah cigaba da fira su kae har Abbas d’in na tambayar shi lokacin da zai ci gaba da aiki yace sai Next week Abbas yace “Allah ya kaimu” amsa mashi yay da Amin ya d’an yi shiru Abbas d’in yace “gani tare da Mom Zaraah mun dawo daga bank an bud’e Account d’in amman mun tsaya Eatery muna cin Abinci” yar dariya Abbas d’in yay jin amsar da Haisam d’in ya bashi yace to, daga haka ya cire wayar Fatuu dake kallonshi lokaci guda ta yanke a ranta koma yace a batan ko bai ce ba, ita dama tasan ya daina damuwa da ita ne kawae don yayi Amarya tana cikin zancen zucin taga Abbas ya mik’o mata wayarshi yace gata, bin shi da ido tay yace “Vedio call ne zaku yi da Ya Handsome d’in ki” yay Maganar yana yar dariya jiki mace ta mik’a hannu ta amshi wayar kafin ta kalli screen d’in har saida gabanta ya d’an fad’i da suka had’a ido dashi, yana zaune kan leather sofa ya d’an kishingid’a jikinshi sanye da armless data bayyanar da suffarshi abunka da zuciya tuni Fatuu taga ya canja mata yayi mata wani irin Fresh, bin shi da ido tay ta kasa ce mashi komae Abbas dae ya ci gaba da cin Abincin shi,
“Zaraah ina wuni” ta ji cool voice d’inshi ta fad’a, d’an tura baki tay ta d’auke idonta don tasan da biyu yace haka can ta sake kallonshi taga still kallonta yake cikin shaky voice tace “..ina wuni, an je lpy” shiru yay mata ta fara yamutsa fuska ta k’ara gaidashi ya k’ara yin shiru d’an tura baki tay kaman zata sa kuka tace “to kayi hakuri” wani d’an guntun murmushi yay dama da biyu yak’i amsawa just yana son ganin reaction d’in da face d’inta zatai displaying, bin shi da ido kawae tay can yasa hannu ya shafi beard d’insa yace “ina fushi dake” da sauri tace “to mi nayi maka?”
“An d’aura man Aure but u couldn’t call and rejoice wit me” d’an motsa baki tay ta sadda kai tabbas bata kirashi ta taya shi murna ba kuma har Haulat saida tace mata ta kira shi amman ta k’iya, d’agowa tay a hankali still kallonta yake duk ta kame kanta cikin rawar murya tace “to don Allah ka yi hak’uri Ya Haisam dama inata so in kira” d’an ta6e baki yay baice komae ba ta tura mashi baki fuskarta a yamutse alamar ya tanka amman yak’i cewa komae sai kallonta yake kawae sai da ya ga dama sannan ya tambaye ta ya Exams tace mashi Alhamdulillah yay mata fatan Alkhairi ta amsa sai lokacin ta tambayeshi ya Aunty Fanan yace tana lafiya daga haka yace zasu yi magana ta d’aga mashi kai ta mik’a ma Abbas wayan yana amsa yace “wai ina Amaryar ne ta barka kai kadae zaune”? Ya bashi amsa da tana Bedroom cike da jan Magana Abbas yace “d’anyen aure amman kai kana Parlor ita tana Bedroom ko har kun fara fad’a ne” yar dariya Haisam d’in yay jin wata magana ta Abbas d’in sai kace wasu k’ananun yara wai har sun fara fad’a sigh yay yace mashi tana hutawa ne bata jin dad’i, d’an buda ido Abbas yay kafin yace “Subhanallahi mi ya same ta ne naga lafiya lou ku ka tafi” bin shi da ido yay kawae Abbas d’in ya k’ara tambayar shi abunda ya same ta yasan in ba fad’i mashi yay ba bazai k’yaleshi ba hakan yasa shi ce Masha is Nausea daga tafiyan da sukai amman duk da haka saida Abbas d’in yace “amman dama tana hakan naga ta saba hawa jirgi sosae fa” ya k’are Maganar yana guntse dariya Haisam d’in yace zasu yi magana da sauri Abbas yace “No yakamata mu gaisa ai muyi mata ya jiki ga ma Mom Zarah itama zata gaidata” ya d’aga ido ya kalli Fatuu yace “Auntyn ki ce bata lafiya zaki gaidata ko?” Tura mashi baki tay yay yar dariya ya maida idon kan screen d’in yace ma Haisam Zarah zata mata sannu ya kai mata laptop d’in ya amsa da Ok kafin ya yunk’ura ya mik’e, had’add’an Bedroom ne mara hayaniya sosae komae na cikinsa fari ne tass sai d’an ratsin baki kadan a wasu wuraren, tana kwance ta kudundune cikin lallausan farin bargo ya tunkareta saida ya aje laptop d’in ta kalli can gefe kafin ya fara tada Fanan d’in a hankali ta fara motsi kafin ta yaye bargon daga fuskarta suka had’a ido, yar harara ta wurga mashi tana kokarin rufe fuskar k’asa k’asa yace Abbas ne zasu mata sannu shi da Zarah wani kallo ta wurga mashi tun kafin tace wani abu ya riga ta fad’in it’s connected yay mata nuni da laptop d’in da ido, shiru tay ta fasa yin Magana ganin bata da niyyar tashi yace mata “sit up” d’an yamutsa fuska tay dama fuskar duk a harmutse take tay jajir abunka da fara ga idanunta ma sun d’an kumbura da gani dai tasha kuka gashin kanta ma duk ya harmutse haka lips d’inta ma sun d’an kumbura suma, cikin disasshiyar murya tace “but u know I can’t am feeling pain al over my body” kallonta kawae yake yana tuna gumurzon da suka sha da ita wanda gaba d’aya ita taja har yay losing control yasa ta jigata sosae sam baiji dad’in hakan ba don da bakinta ta rink’a gaya mashi she hates him tunda shi mugu ne baida tausayi duk da yasan Azaba ce tasa ta fad’in hakan abun ne ma ya isheshi yay zaune a Falo har ya kira Abbas d’in a waya don su gaisa ko ya rage damuwa, matsawa yay ya kai hannu ya taimaka mata ta zauna ta jingina da heardboard sai faman fad’in ahhh take bayan ya zaunar da ita ya kai hannu can gefe ya d’aukko mata hula yasa mata duk abun nan Abbas na jin su duk da bada sauti sosae suke Maganar ba shi dama yasan ba wani ciwon tafiya dake damunta sai kace yau ta fara tafiya ai koda ma tana yin hakan to badae har abun ya kaita ga kwanciya ba ashe mazan gaske taji ya ayyana a mind d’inshi, juyo da laptop d’in yay ta kalli screen d’in suka had’a ido da Abbas dake mata murmushi itama da k’yar ta d’an yi mashi na yak’e yace “sannu Amaryarmu ashe baki ji dad’i ba yanzu yake fad’a man wai Nausea na damunki” d’aga ido tayi tay ma Haisam dake tsaye ya goya hannuwanshi a broad chest d’inshi wani kallo kafin ta kalli Abbas tay murmushi kawae bata ce komae ba yace ga Zaraah zata gaidata ta d’aga mashi kai ya mik’a ma Fatuu wayar kaman bazata amsa ba amman ba yadda ta iya ta kar6i wayar ta kalli Screen d’in suka had’a ido da Fanan kafin tace wani abu Fanan d’in tace “Zaraah how are u?” A hankali tace mata lafiya lou kafin tace ya jiki ta amsa mata da da sauki, shiru Fatun tay tana ta kallonta ita kuma sai d’an yatsine yatsine take tana sa hannu tana dafa forehead d’inta can ta kalli Fatun tace “naga baki zo biki ba gwaggo ta fad’a man kina Exams” jinjina mata kai Fatun tay tace Allah ya bada sa’a ta amsa da Amin daga haka ta mik’a ma Abbas wayar shima ya k’ara yi mata Allah ya sawake Haisam na d’auka yace mashi zasu yi magana kawae yay disconnecting don yasan halinshi yana iya mashi wata Maganar da bata kamata ba a gaban Zaraah, tun da su ka gama wayar taji komae ya fita mata a rai zuciyarta harta yanke mata Fanan d’in ciki ne da ita don tana jin k’awayenta in suna ma wad’anda zasu yi aure cikinsu da sun gama Makaranta Addu’ar Allah yasa suna zuwa first night su samu ciki wata tara su zo suna, Abbas ya lura da yanayinta da ya canza yace mata ta ida cinyewa su tafi ta d’aga mashi kai kawae haka ta rink’a turawa ba don tana jin dad’in su ba, bayan sun gama ya biya suka tafi ya maida ta gida kafin ta tafi yay mata fatan Alkhairi a jarabawarta tay mashi godiya sannan ta tambaye shi yaushe zai kawo mata Abdul wuni yace karta damu in ta gama exams in dae suka samu Hutu zai kawo shi yay mata hutun yanzu dae ta dage tayi karatu sosae Allah ya bada sa’a ta amsa da Amin daga haka suka rabu, koda ta shiga gida sosae tay yak’i da zuciyarta wurin kauda damuwa ta d’aukko littattafan da zata karanta ta fara karatu.
Washe gari Laraba Misalin k’arfe tara na safe suka shiga paper d’in practical physics sam bata yi mata wuya ba duk da lokacin da aka rink’a koya masu tana cikin damuwa sosae amman kuma ta fahimta tunda tana da brain mai kyau, kafin lokacin da za’a gama ma ita har ta gama ta taimaka ma Haulat wurin da ta kakare ko da Malaminsu ya zo Lab d’in yay going around yana ganin yadda suke yi yana zuwa kanta ya duba da murmushi yace “Weldone Sp kinyi komae daidai” d’an murmushi tay yace ta d’an taimaka ma na kusa da ita wanda basu gane ba tace to amman tana tsoron supervisors dake cikin lab d’in kar tay laifi yace ba wani abu sun yi magana dasu, aikuwa sosae ta shiga taimaka ma sauran students tana nuna masu yadda zasu yi, bayan sun fito ne kuma ta rarraba ma wasu daga cikin k’awayenta abubuwan bikin Haisam da ta kwaso, zo ka ga yadda Students suka rud’e suna yaba kyaun da sukae wasu na cewa sun ji sanarwar bikin a Radio wasu a Tv, wasu harda Addu’ar suma Allah ya basu mijin Novel yayin da wasu ke tambayarsu su d’in Matan Novel ne da zasu samu mijin Novel haka sukae ta shak’iyanci sosae suke ta Fatuu dariya wata har tana ce ma Fatun itama tasan mijin Novel zata aura tunda tana da suffar Matar Novel ita dae dariya kawae tayi yayin da cikin ranta ta ayyana na samu kuma na rasa, har Malamai duk wanda yazo wucewa yaga Calendar d’in ko wani abu mai hotonsu sai ya tsaya ya tanka har discipline master d’insu da ya gani yace yana so shima aka bashi Calendar dasu jotter, basu koma gida ba a Cikin Makarantar suka ci Abinci har Abbas ya kirata yay mata ya Exams haka gwaggo ma da Kawu Amadu, k’arfe 3:00 suka shiga next paper ta IRS wannan ai ko awa ba’ayi ba ta gama ana fara amsa duk suka bada don itama Haulat d’in ta gama cike da farinciki suka koma gida.
After 2 Months,
A kwana a tashi ba wuya a wurin ubangiji, a yau su Fatuu na cikin tsananin farincikin da Allah ya nuna masu gama jarabawar su lafiya sai murna suke suna celebration don har anko sukae dogon skirt da yar top sai coat mai d’auke da year d’in da sukae graduation da department d’in da Mutum yay wasu sun sa himar wasu hula facing cap wasu kuma gyale sukae rolling sai d’aukar hotuna suke harda Malamai sukae d’an party, Fatuu ba tayi komae ba ta raba kaman da Jsce, gwaggo ta so yi mata abubuwa don har kud’i Haisam ma ya turo mata yace tay hidiman graduation d’in amman tace ma gwaggo duk asara ne ayi wani abun dasu kawae, tun wurin Azahar suka gama amman basu fita daga Makarantar ba sai wuraren La’asar a k’asa suka taho suna ta nishad’i ganin suna ta tafiya haulat tace mata ita dae gaskiya ta gaji amman Fatun tace aikuwa yau k’asa zasu je gida, suka ci gaba da tafiya har suka fara yin nisa sosae, suna cikin tafiya wata galleliyar Mota ta tsaya a gefensu da yake a gefen titin suke tafiya juyawa sukae a tare suka kalli Motar kafin suka juya don cigaba da tafiya kawae sai gani sukae glass d’in Motar ya fara sauka nan take sukae arba da mai tuk’a Motar wanda matashi ne zai iya kaiwa shekaru 28 haka wankan tarwad’a ne yana sanye da kananan kaya kuma da gani Hutu ya zauna mashi sosae, lek’o da fuskar shi yay da d’an murmushi yace “Barka dae yan graduation” Haulat ce ta tsaya ita kuwa Fatuu gaba tay abunta itama d’an murmushin tay tace mashi yauwa yace “I just passed sai na gan ku shine nace bari mu gaisa” tana murmushi tace sun gode d’an juya kanshi yay ya kalli Fatuu da tay gaba yace “ita friend en naki bata gaisawa da wanda bata sani bane” juyawa tay itama ta kalli Fatuu dake ta tafiyarta kafin ta maido idon kanshi tace “kusan hakane kasan ba kowa ake yadda dashi ba yanzu” yar dariya yay yace “hakane nima bai kamata in tare ku a bakin titi ba, in ba damuwa ki bani no d’in ita friend d’in taki sai in zo gida mu gaisa da ita” d’an jimm Haulat tay sai kuma ta juya ta k’ara kallon Fatun tunani ta shiga yi tasan ko ta bashi no d’in Fatuu aikin banza ne don ko ya kira ma ba saurararshi zatai ba don sam ta haramtawa kanta yin saurayi, dubara ce ta fad’o mata ta juya tace mashi “kayi hakuri ko na baka no d’in ba zatai maka wani amfani ba don ita d’in akwae sa rana a kanta dama da mun gama Makaranta za’ai bakin ta kuma gashi mun gama d’in to ba lalle ta saurare ka ba” d’an buda ido yay sai kuma yayi murmushi yace “Ok bansani ba ne amman ba wani abu Nagode sosae” tana murmushi tace to har zata juya yace su zo ya kai su subar tafiya cikin rana, juyawa tay da niyyar yi ma Fatun Magana kawai sai ta ga har ta tsaida masu Keke Napep kallon shi tay tace yayi hakuri ta riga ta tsaida masu abun hawa yace to ba matsala tace mata yana mata fatan Alkhairi Haulat d’in ta amsa da to daga haka glass din ya d’aga ita kuma ta tafi, lokacin da ta k’arasa Fatun har ta shige cikin Napep d’in itama sai ta shiga dama ita suke jira mai Napep d’in ya tambayi inda zai kaisu Haulat tace mashi Barhim sabuwar Abuja ya ja suka tafi, kallon Fatuu tay da yake mai Napep d’in ya kunna Wak’a tasan ba jin su zai ba tace “Wannan Mutumin fa don ke ya tsaya har cewa yay na bashi no d’in wayar ki sai ya kira tunda baki tsaya ba amman nasan ba lalle ki saurare shi ba shiyasa nay mashi k’aryar an kusa bikin ki” d’an ta6e baki Fatun tay tace “gwara da kika ce mashi hakan ya kama gabanshi don kuwa ba sauraran nashi zan yi ba” idon Haulat a kanta ta d’an girgiza kai tace “Wai Fatuu miyasa kike korar samari ne, da wuya mu fito ba’a samu wanda ya nuna yana son ki ba Amman sam kin k’i ki fara saurarar kowa komi kice karatu to karatu yana hana ayi saurayi ne ko kuwa zaki ta karatun ne ba ranar da zaki aure??” wani kallon gefe tay ma Haulat d’in ba tare da ta ce mata komae ba Haulat taci gaba “nasan duk Saboda Ya Haisam ne baki saurarar kowa ba wani abu ba, zuwa yanzu yakamata ki cire son shi kwata kwata a ranki kema ki tsaya ki samu wanda zaki rayu tare dashi kada kita korar Mutanen kirki ba tare da kin sani ba, ki yi hakuri in na 6ata maki rai amman gaskiya nike fad’i maki kaman yadda ya samu abokiyar rayuwa wadda yanzu na tabbatar bata rasa juna biyu kema ki fara tunanin sama ma kan ki wanda zaku rayu tare ki hak’ura da ya Haisam don matuk’ar yana ranki to fa bazaki ma kanki abunda ya dace ba shawara ce nake baki a matsayina na mai son cigaban rayuwarki” a hankali tace mata ta gode kawae don kuwa son Ya Haisam na nan a cikin ranta ta rasa ta yadda zata cire shi, suna haka wak’ar da mai Keke Napep d’in ya kunna ta k’are wata ta shiga ta Labarina baitikan wak’ar suka fara kaman haka
๐ถ๐ถDawo bamu gama zama ba, dama ba mu raba jini ba, wai nikam mai naiwa kauna bata mi ni wuri ba labari da kai ne dawo bamu gama zama_๐ถ๐ถ
_๐ถ๐ถBan gani duhu haka na kwana, yanzu ma hakan na ishi rana, damuwa ta damu da gani na gashi ta raba ni da wani na, mi nai wa kauna ne guna bata iya zama ba, yafe man in na mutu so ne bai gama salo ba…๐ถ๐ถ_
Natsuwa sukae suna sauraran wak’ar dama Fatun kusan kullum sai ta saurareta ji take tamkar ita a kai ma wak’ar lokaci guda kwalla suka fara zubo mata sharrr da sauri Haulat tace ma mai Napep d’in “Malam don Allah in ba damuwa ka canja wata wak’ar” yace “yanzu kuwa Hajiya ai dama don jin dad’in ku muke sawa bari a canja maku” ya kai hannu yana yana k’ok’arin canzawa ana fara taken wak’ar Fatun ta saki d’an murmushin takaici don kuwa itama wak’ar kamar dae waccan ita wannan ma jinta take kaman ita ta raira ma kanta ita ta hamisu breaker ce mai taken ‘ _so gaskiya ne yadda yay min ni na gane, in dai amo ne kanshi ban daina shi zancen gaskiya_๐ถ๐ถ da sauri Haulat tace “Don Allah malam ka kashe wak’ar duka ta cika mana kunne” wannan karon juyowa yay yana niyyar yi mata Magana idonshi ya sauka kan fuskar Fatuu yana ganin kwalla yay d’an murmushi had’i da girgiza kai ya juya ba tare da ya ce komae ba a cikin ranshi ya ayyana ta Kamu da mugun ciwo ya kai hannu ya kashe gaba d’aya kaman yadda Haulat d’in ta buk’ata, suna gab da isa gwaggo ta kira Fatuu bayan ta d’aga ta tambayeta har yanzu basu taho bane don d’azun sun yi waya lokacin da suka gama Exams, ce mata tay gasu nan sun kusa isowa tace to ta taho harda Haulat ta amsa da to, dai dai gefen shagon Amadu dake a rufe mai Napep d’in ya tsaya suka fito bayan sun biya shi suka nufi cikin gidan mai Napep d’in ya bisu da ido a ranshi yake ayyana “Gata dae tubarkallah ko wani ya yaudareta ko kuwa wani take so ta rasa shi Allah kadae ya sani” daga haka yaja ya tafi, suna shiga cikin gidan suka jiyo Wak’a na tashi ta happy graduation Fateema Zarah a cikin falo da sauri suka nufi falon suna shiga sukae turus a bakin kopar da tsananin mamaki akan fuskokinsu gaba d’aya an k’awata falon da flowers da balloons cards da sauransu kaman dae irin decoration d’in birthday a bangon dake kallon Mutum in ya shiga an had’a rubutun Happy Graduation Fateema Muhammad Ardo and Haulat is’haq a tsakiyar d’akin kuma k’aton cake ne saman table da sauran abubuwan ci, da gudu Fatuu ta nufi gwaggo dake tsaye tana masu dariya ta kankameta cike da farincikin surprise da suka mata sakin ta tay ta nufi Kawu Amadu dake gefe shima ta rungume shi sai kuma ta fashe da kuka duk suka sa dariya Amadu ya hau goge mata kwallan yana fad’in yau ranar Murna ce don daga yau ne ta hau matakin cikar burinta ta jinjina mashi kai yace yana mata fatan nasara cikin muryar kuka tace ta gode haka Haulat ma saida gwaggon ta rungumeta duk suka yi mata fatan sa’a tana ta dariya tay masu godiya, ci gaba da celebration d’insu sukai su hud’u gwanin burgewa Fatuu sai rawa take da wak’arta da aka yi mata ba tare da ta sani ba hakan aikin Amadu ne yaba wani abokin shi yay mata kuma tayi dad’i sosae daga baya Fatuu da haulat suka yanka cake Amadu na masu Videos da iPhone d’in wani abokin shi da ya aro Saboda hakan, sosae su kae hotuna kuma sunyi matuk’ar yin kyau sai bayan Magrib sannan Fatuu ta raka Haulat bayan an d’ibar mata komae cake d’in ma mai yawa aka bata tanata godiya, Fatuu na dawowa tasa Kawu Amadu ya tura mata pics d’in da videos ta shige d’aki ta fara aikin d’aura su a Status kan kace mi aka fara mata comments na taya murna wasu ma duk suka d’auka suma suka d’aura sai farinciki Fatuu ke yi jin yadda ake ta yabawa har wasu Friends d’insu na cewa shine ko a gayyace su, tana cikin duba wad’anda suka d’aurata kwatsam taci karo da na Haisam da mamaki ta bud’e hoton farko wanda akai mata ita kadae a gaban rubutun cikin falon tayi dariya duk dimples d’inta sun lotsa sosae a k’asan shi ya rubuta ‘Wishing u success in ur Exams beloved sis Zarah’ na gaba kuma wani d’an short video ne tana ta dariya had’i da yin Magana sam bata ma san anyi mata shi ba can kuma ta tura yankin cake a baki duk ya 6ata mata gefen baki kai da ganinta a Videon zaka fahimci tana cikin tsantsar farinciki sosae tasa Dariya da ta ga Videon wato tun kafin Amadu ya turo mata ya tura ma Haisam, tana cikin hakan kuma sai ga kiranshi ta d’auka ta gaishe dashi bayan ya amsa yace mata congratulations tace mashi thanks waya suka cigaba da yi wadda rabon da su jima suna yin waya har ta manta har ta tambaye shi Fanan yace tana wurin aiki da yake su can rana ce tace shi yana ina yace shima yana wurin aiki k’arshe ma cewa yay bari ya maida Video call tace to dama akwae haske d’akin koda ya maida tana ta sakin murmushi shima haka suka ci gaba da yin firan har yana nuna mata Office d’inshi na can ta yaba sosae da had’uwar shi don irin manya Office d’in da take gani ne a Fina finan turawa.
Bayan sati d’aya da yin candy d’in su Haulat tazo gidan ta sanar da ita zata tafi Nijar kuma bazata dawo ba har lokacin bakin ta dama a can za’ayi, Fatuu bata ji dad’i ba har tana ce mata ba sai bikin ya kusa ba sannan zata tafi tace itama tayi tunanin hakan to amman innarsu tace taje ta zaga dangi kafin bikin don ta dad’e bata je ba, Ranar Juma’a da zata tafi har tasha Fatuu da Kawu Amadu suka rakasu da yake da yayanta Usman zata tafi suna ta kuka suka rabu Fatuu tace mata sai sun zo biki, Allah sarki Haulat k’awar Arziki.
Satin Haulat d’aya da tafiya lokacin ya kama satinsu biyu da gama Makaranta ran Asabar Fatuu ta dawo daga islamiyyar safe tana tafe tana ta tunane tunanenta da suka zame mata jiki don yanzu wani irin kad’aici ne ke damunta, ba Haisam ba Haulat gashi Hajiya har yanzu bata dawo ba balle ta d’an rink’a zuwa can a haka har ta k’araso gida tana shiga tun a zaure ta jiyo Muryar gwaggo cikin harshen fulatanci tana ta fad’a, lokacin da ta k’arasa a tsaye ta ganta gaban kitchen sai kai da kawowa take ga wayar Amadu kange a kunnanta tana yin waya, tsayawa tay tana bin ta da ido hakan ya bata damar jin Maganar da take a lokacin kamar haka “Sam bazan yarda ba wllh! Lokacin da aka bani ita ai ba ace man za’a rabani da ita ba hasali ma kowa ba son ta yake ba anata muzguna mata sai yanzu da aka ga ta zama Mutum shine za’a nuna man iko da ita, to bari kaji bazan ta6a yarda ta dawo ba sai dai komae zai faru ya faru na shirya ma hakan!!!” daga haka ta katse kiran ta juyo a fusace ta mik’a ma Amadu wayar kafin ta wuce d’akinta fuu tana ta kwafa, juyawa Amadu yay ya shige d’akinshi yayin da Fatun tay tsaye jikinta duk yayi sanyi yaushe rabon data ga gwaggo na fad’a haka sam ta kasa fahimtar inda zancen da ta ji tana yi ya dosa, har zata nufi d’akinta sai kuma ta juya ta nufi d’akin Amadu lokacin data shiga yana zaune a gefen katifa yayi jigum da alama shima abun ya dameshi sosae, d’aga kai yay ya kalleta ganin hakan yasa ta duk’a tana kallonshi itama, a sanyaye ta tambayeshi abunda ke faruwa, farko shiru yay mata yana dai ta kallonta saida ta marairaice mashi kaman zata sa kuka tana had’ashi da Allah sannan ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi yama rasa ta ina zai fara ganin dae ta zuba mashi ido ne yasa yay k’arfin halin cewa “Dama Baffan ki ne ya kira yace zai zo ya tafi dake wai Ard’o ya bada auren ki” wani bugu k’irjinta yay ta zaro ido tana kallonshi kafin cikin sark’ewar murya tace “y…ya bada au..aurena, ni…d’in???” Kai ya d’aga mata alamar eh, a razane tace “Waye ya ba aurena??” Shiru ya d’anyi shima duk damuwa ta bayyana akan fuskarshi can yace “Chairman Alhaji Lawal ya nema ma d’an shi wai Dr Khalid Auren ki tun lokacin da muka je shekara ukku da ta wuce shine ma yace a barki sai kin gama Secondary don da tun lokacin Ard’on yace ya bashi…………….
.
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page :ย Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page :ย @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel:ย Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.