Hausa novels

Fentin Zina Page 21 Hausa Novel

*****Tunda baba malam yayi wannan maganar inna bata sake cewa komai ba har aka sallameta da yamma suka koma gida.Ameena ta kammala girki kenan ta zuba a flask tasa a basket ta Shiga daki domin dauko hijab ta tafi sai ta jiyo sallamarsu daga kofar gida, ta ajiye hijab din ta fito cikin dari dari tace sannu goggo ya mai jikin?Dan tabe baki goggon tayi tace da sauki.Ta dan kalli inna ganin ko kallon inda take bata yi ba sai hakan ya kara sanyaya jikinta tace sannu inna ya jikin?.Karamin tsaki inna taja ta shige dakinta.Hawaye taji sun taru a idanunta tacewa fateema, ga abincin nan dama yanzu nake shirin zuwa asibitin sai kuma gashi kun dawo ki dauka ki shigar musu dashi tunda kinga ni inna ko kadan bata son gani na yanzu ta tsaneni.Ta karasa hawayen da take kokarin dannewa suka zubo ta juya da sauri ta shige daki.Girgiza kai fateema tayi ta dauki basket din ta Shiga dakin inna dashi tana kokarin ajiyewa inna ta daga mata hannu tana fadin dauke mun wannan abun a dakina kafin fushina ya sauka a kanki.Harta juya goggo tace kawo ki ajiye kana ta kalli inna tace bana son diban albarka kinji ko, duk wannan abunda kikeyi dai bazai maido da hannun agogo baya ba kuma bazai gyara komai ba saima dada batawa da zaiyi don haka na hane ki da sake furta wata kalma ko in saba miki.Ita kam fateema tuni ta ajiye ta juya abunta tana mai mamakin kapiya irin ta innarsu.Dakinsu ta shiga ta tarar Ameena tana kwance tana sana’arta wato kuka, zama tayi kusa da ita tana sassauta murya tace.Adda wannan kukan dakikeyi ba shine mafita ba saima karin ciwo da kuna da zaki samu kanki a ciki, kiyi hakuri ki rungumi kaddarar ki a yadda tazo miki.Tashi zaune tayi ta tsaigaita kukan ta share hawayenta tace fateema ta ina zan daina kuka, bayan kinsan halin da nike ciki, koda nasan na aikata kuskure amma zuciyata ta kasa daukar irin hantara da kyaran da nike fuskanta daga iyayen mu kofa gaisuwata basu amsawa wallahi nayi nadama kuma ina mai tabbatar miki zuciyata gab take da bugawa muddin irin haka zata ci gaba da faruwa a cikin gidannan.Kada kice haka adda, girman laifin da kika aikata da zaki iya fuskantar fiyeda irin wannan daga garesu, ki sani a halin yanzu Allah ne kadai yasan irin kunar da take cikin zuciyar su amma duk da haka sun zabi suyi shiru saboda gudun furta munanan kalamai a kanki sannan sun zabi sassauta zuciyarsu har lokacin da zatayi sanyi gudun yin hukunci cikin fushi, wannan kadai ya isa ki duba ki musu uzuri kuma kiyi hakuri da duk halin da zasu nuna miki na tabbata na dan lokacine komai zai wuce, ba don basu kaunar ki bane suke hakan kema kin sani.Gyada kai Ameena tayi ta huro iska daga bakinta ta jingina kanta a jikin gadon tace na fahimta, Allah ya bamu ikon cin wannan jarabawar ya kuma kare ‘yan baya da fadawa cikinta.Ameen fateema tace ta mike tace barin yi alwala magriba ta gabato yanzu sai kiji ana kiran sallah.Toh dan Allah idan kika yi ki saka mun ruwan dumi a butar sanyi nike ji sosai.Juyowa tayi tace Allah sarki sannu kinji, idan kinyi alwalar sai kisha magani zaki danji dama dama sannu, tana gama fadin haka tayi waje, Ameena ta juya kwayar idonta tana kallon sama cikin tunani har fateema ta dawo dakin tace da ita adda kije ga ruwan na ajiye miki kusa da ban daki.Nagode fateema Allah ya saka da alkhairi.*****A dakin inna kuwa bayan sallahr magriba baba malam ya shigo ya zauna suka gaisa sannan ya dubi inna yace ya jikin naki?.Inna tace Alhamdulillah.Toh Allah ya kara afuwa.Inna da goggo suka amsa da ameen.Baba malam ya dora da cewa gameda maganar Ameenatuna zauna nayi tunani sosai da halin da kike ciki naga rashin dacewar ci gaba da zamanta a cikin gidannan domin hakan zai iya jawo wata baraka wacce ba’a san da ita ba don haka na yanke shawarar zata koma gidan ki ke yaya da zama har sanda zata haihu ta yaye yaro sai musan me Allah zaiyi a gaba.Da sauri goggo ta cabe zancen da cewar wa? Ni wai kake nufi ko wata daban? Gaskiya bazan dauki dattin zina a gidana ba kana ji ko, ku nemo inda zaku kai ‘yar ku yo uwarta ma ta kyamaceta waye kuke so yaso ta? Bazan iya ba gaskiya.Dukkansu shiru sukayi sakamakon sanin abunda ta fada gaskiyane saidai basu ji dadin data kira ‘yarsu da dattin zina ba sai dai basu da ta cewa tunda dan kuka shike jawa uwarsa jifa.Inna ce ta katse su da fadin ina ganin me zai hana a tura ta can wurin Rabi’atu kanwata a garin jos inyaso tayi zamanta a can har sanda Allah yaso nasan bazata ce a’a ba.Kunga ni bawai naki daukarta da wata manufa bane don naga kamar ranki ya baci ina mai baku hakuri sai dai kunsan yanayin rayuwa cewar goggo kenan.Babu komai ai, inji cewar baba malam, ya kara da cewar babu damuwa sai a tuntube ta kawai idan yaso sai ta tafi koda cikin satin nan ne.Ya fadi haka tare da mikewa ya fice.Inna sai data kadaice ita kadai a dakin sannan ta dauki wayarta ta kira Rabi’iatu tayi mata bayanin komai sannan ta dora da fadin dan Allah kada sauran ‘yan uwa susan meke faruwa duk wanda ya tambaya a fada masa aure aka mata mijin ya mutu shine ta dawo gurinki haihuwa.Daga ta cikin wayar tace insha Allah kada kiji komai zanyi iya kokarina wajen kiyayewa saidai fa konsan mutanen mu da bin diddigi dole zasu gano gaskiya sannan hakan zai zama kamar karin zubewar mutumci ne a gare mu, bai kamata ayi musu karya ba amma shawara ce.Hum toh shikenan wallahi ina cikin rudu ne Rabi’iatu har bansan a wani mizani zan ajiye matsayin wannan al’amarin ba, kwata kwata naji na tsani yarinyar nan bana kaunar ganinta don zan iya shaketa ta mutu kowa ya huta a yadda nikejin zuciyata tana zafi.Inna hakuri zakiyi ki tausasa zuciyar ki babu wanda ya isa tsallake kaddarar sa ki dauka a haka din sai ki samu salama duk da cewar abun babu dadi amma ki sani Allah baya kuskure, zai jarbceci daga bisani ya zamto alkhairi a gareki idan kikayi tawakkali dukkan abunda Allah zai aikowa bawa daidaine saidai yaki yiwa mutum dadi, dan Allah ki daurewa zuciyarki kada kiyi mata baki.Babu komai Rabi’iatu zanyi kokari amma ki sani idan ina ganinta bazan iya dannar zuciyata ba shiyasa na zabi ta dawo gurin ki, ki rike amana ki kula da ita.Kada ki damu zata samu kulawa fiye dama tana gurin ki.Nagode si munyi magana jibi insha Allah zata taso.Allah ya kaimu ya kara rufa mana asiri.Ameen. Daga haka suka katse wayar,.Koda baba malam ya dawo ta sanar dashi yadda sukayi da Rabi’iatu sai yayi na’am da zancen tafiyarta jibin don haka ya kwalla kiran fateema, ta shigo ta tsugunna ta gaishe shi yace kirawao Ameenatu.Ba jimawa Ameena ta shigo tana rabe rabe, baba malam ya maka mata hararar da saida hantar cikinta suka kada a hankali cikin firgici ta zauna tana addu’o’i a zuciya na samun rangwame.Maganar baba malam ita ta dawo da ita daga dan karamin tunanin data fada, yace Ameenatu kin bani mamaki kin kuma bani kunya sannan kin mana yankan kauna kin shammace mu, abunda kikayi mana kina ganin kin kyauta kenan? Wannan wace iriyar rayuwace kika zaba wa kanki Ameenatu? Kin tozarta mu, kin watsa mana kasa a idanu kin wulakanta mu sannan kin bata sunan gidan mu, me muka miki da muka cancanci irin wannan hukuncin daga gareki iye?.Kuma sosai Ameena takeyi amma muryarta bata fitowa.Baba Malam ya cigaba da cewa, ada ko a cikin mafarki wani ya fada mun cewar Ameena zata aikata irin wannan abun zanyi musu sannan in karyata saidai ga mamakina kin karya duk wata yarda da nayi muku kin lalata amintakar dake tsakanin mu, me kike son cimmawa da hakan?.Wannan karon kukan ne ya bayyana cikin kukan take cewa baba nayi kuskure amma wallahi banyi nufin in tozarta ku ba kuma wallahi nayi nadama kuyi hakuriu yafe mun dan Allah ku gafarta mun koda zanga daidai a rayuwata. Ta karashe da matsanancin kuka.Ke dalla ki rufewa mutane baki munafuka wacce bata san darajar kanta ba wallahi zan miki duka saina kusan halakaci idan baki rufe wa mutane baki ba shashashar yarinya ballagaza cewar inna data taso a fusace.Ki bari haka rukayya bana son ki sake cewa komai dan Allah ki koma ki zauna.Malam daka barni na koyawa yarinyar nan hankali kilan ta farka daga barcin asaran da takeyi.Idan na isa dake ki koma ki zauna. Daga haka ya juyar da kai yana kallon Ameena dake risgar kuka kamar ranta zai fita, inna badon taso ba ta koma ta zauna.Baba malam yace.Hakika kaddara ta riga fata, bana son bacin rai ya kaimu ga aikata aiki irin na mutanen jahiliyya sannan daga baya muzo muna dana sani, abunda ya faru ya riga ya faru saidai fatan Allah ya tsare gaba ya kuma yafe mana toh amma ki sani idan kwatankwacin haka ta sake faruwa kinji na rantse da wallahi birne ki zanyi da ranki kuma babu wanda ya isa ya hana don haka kije ki hada kayanki duk abunda kikasan zaki bukata jibi zaki tafi can jos gida Rabi’iatu a can zaki cigaba da zama kuma inaso ki natsu ki zauna lafiya ki kuma kiyaye duk wani abu da kikasan ya sabawa addini idan har furucin ki na kinyi nadama da gaskiya kike fada ina so ki tabbatar mun zan baki wayarki bisa sharadin canja sabon layi sannan gobe zaki bani lambar shi wannan yaron idan ta kama ma sai muje gidan nasu tare domin ya zama dole ya sauki dawainiyar cikin dake jikinki.Cikin sunkuyar da kai tace insha Allah baba nayi alkawarin kiyayewa bazan sake bada kofa ga ko wace irin barna ta shigo rayuwata ba da gaske nayi nadama nadamar da bazata barni ba har abada, ina kuma rokon alfarma a wajenka.Uhum kallonta yayi yace ina jinki.Baba dan Allah ka bar maganar zuwa gidan su Ahmad don wallahi na tsane shi tamkar mutuwata kuma ya riga ya tabbatar mun bashida wata alaka da cikin kuma bazai karba ba sannan bansan gidansu ba dan Allah ka bar maganar shi na yadda Zan tafi jos in zauna a can kuma bazan sake maimata kuskuren dana aikata ba zan dukufa ne wajen neman gafarar ubangiji kuma ina rokon ku daku yafe mun kuma ku cigaba da sanya ni a addu’o’inku kamar yadda kuka saba. Ta karasa da kuka sosai.Kiyi shiru Ameenatu, Allah ya yafe mana baki daya na yarda dake na kuma gaskata karfin kaddara akan bawa mai imani Allah ya bamu ikon cin wannan jarabawar.Haka Ameena ta rarrafa ta isa ga inna ta rike kafafun ta tace inna ki yafe mun nasan ban kyauta muku ba dan Allah kiyi hakuri fushinki a gareni maaifa ce wallahi so daya ne kuma tsautsayine yaudarata yayi inna dan Allah ki yafe mun.Allah ya have mana, iya abunda inna tace kenan ta juyar da kai gefe ganin haka baba malam yace tashi kije mun gama magana.Sum-sum ta mike ta fita.Tana shiga dakinsu ta fada kan gado tana sakin ajiyan zuciya a jere a jere tana jin nauyin zuciyarta ya ragu da kaso saba’in da tara cikin dari. *EESHERT ADAMU*

Back to top button